Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
ce, irin wannan ta ci ka muni, ko ta faye kiba da dai sauransu, shi ne yau don na gaya maka daya ranka zai baci, to yi hakuri, ni dai an jima a raka ni na gano Wasila." Da la'asar sansanya suka shirya zuwa makarantar horon malamai ta 'yanmata da ke nan cikin Zariya kowanne ya ci ado da gani ka san wajen 'yanmata za'a ziyara, Awalu ya tsaya ya sayi lemo da ayaba leda biyu ya rikewa Wasila. Yusuf ya dubi Awalu da gefen ido yace, "Ni fa tsiya ta da zuwa makarantun nan ayi maka ca da ido ka rasa wanda za ka tunkara don ya nemo ma ka wanda ka zo nema". Awalu ya се, "yi hakuri Malan yanzu za ka ga Wasila ta bullo ko daya daga cikin kawayenta." Daga can wata doguwar budurwa ta tsinkayo a guje dank kwali a hannu tana ta haki tare da kyalkyatar dariya ta ce, 'Awal!" Awalu da Yusuf suka dubi juna su kai dariya shi ma yace, "Ranki ya dade Wasila, wannan irin gudu haka?" Ta ce, "Awal na gan ka ba dole na yo gudu ba? To bisimillah ku zo mu je ga kujera can mu zauna." Suna zaune an shiga hirar nishadi ta samari da yan'mata sai ga Fa'iza da Binta sun iso kawayen Wasila ne, ko wacce ta nemi kujera ta zauna suka gayas da su cikin mutunci. Zuciyar Yusuf ta shiga tsarguwa yayin da idanusa su ka tsokalo masa abin sha'awa nan da nan jijiyoyinsa da gangar jikinsa suka shiga rashin kuzari a dalilin sha'awa da idaniyarsa ta jawo masa, daga can kuma kokon zucivarsa soyayya na ta yi 31 masa ruru mai radadi ba kowa ba ce Yusuf ya tsunduma da sonta da kaunarta farat daya face Fa'iza. Yarinya da take lukwi lukwi jikin ta kamar muzjajjen murjani, fuskarta kuwa yai lumilumi mai idanuwa kamar wadda aka halittasu da ruwan zanzan don walkiya, tana da fasalin baki mai kama da yankan reza. lyakan tunanin Yusuf bai taba ganin yarinya da ya rikice haka ba tamkar Fa'iza, nan da nan tunanin abinda ya gudana tsakaninsa da Awalu a dazun da safe ya dawo masa, ko dai an yi wani shiri ne yau a kan shi? Nan da nan ya ture wannan tunanin shi wanene, me ya ke da shi da har za'a so a raba shi da Dije a cinna masa Fa'iza? Abu ma fi saukin ganewa anan shi ne a yau ya hadu da irin matar da ya ke so. Ya shiga iyakar kokarinsa don ya cinna kaunarsa ga Fa'iza amma yarinya sai kawai ta dube shi ta yi mai murmushi, murmushin da ya ke kara rudar Yusuf. Wasila ta ce, "Yusuf tsakani na da Awal babu yaudara don haka bana jin zan iya yaudarar wanda ya ke tare da shi, a gaskiya Fa'iza na da wanda ta ke so, don haka kada ka wahalad da kan ka". Awal ya ce, "Don Allah ku kyale shi shima shirme ya ke yi, yau fa sauran kwana arba`in mu dauko masa Dije amaryarsa", Haba! Tamkar Awal ya soki Yusuf da fadan sunan Dije a gaban Fa'iza! Ya zaro ido ya ce, "kai Awalu wa aka sawa rana, don Allah idan ana wasa ban da wasan karyar aure. Ni dai Fa'iza don Allah don Annabi ina rokon alfarma ki bar ni na ci gaba da zuwa wajenki tunda dai ba aure aka daura ma ki ba". A haka dai ya dami Fa'iza da magiya ita kuma bata son yawan surutu akan dole ta amince masa amma ba wai don tana son shi ba a ranta. Fa'iza Abba diyar wani.mai kudice anan cikin Zariya itace ta farko wajen innarta, kyan Fa'iza da ke kwada maza ta same shi wajen innarta Hajiya Fatima. Fa'iza na da samari iri-iri amma wanda yayi tasiri a zuciyarta şhi ne Isma'il. Isma'il saurayi ne amma mai tashen kudi cikin matasa. Ransa ne kawai ya ke jin bai iya mallakawa Fa'iza don tsananin so. Shekara daya rak ya ragewa su Fa'iza da Wasila su 32 kammala karatunsu na sakandire a yarda Wasila da Awalu suka tsara tasu rayuwar shine da zaran Wasila ta kammala zai nemar mata ta ci gaba da N.C.E yadda za'a sami cikakkar malamar makaranta kafin shi kuma ya gama, ya je hidiman kasa ya dawo ya nemi aiki sannan ayi biki. Fa'iza kuwa ba su da wannan ra'ayin ita da Isma'il sun shirya tana gamawa sai aure zai mallaka matu kasuwancin da zai rinka kawo mata kudin kashewa. Bayan su Yusuf sun koma dakinsu a can cikin jami` a Yusuf ya fidda hula ya jefas shi ma Awal ya yi jifa da takalmansa, Yusuf ya ce, "Amma gaskiya yau ka yin min rashin mutunci Awal, menene na kawo maganan wata Dije can a gaban yarinya kamar Faʼiza?" Awal ya harare shi yace, "Ga ka nan mara mutunci! Wallahi ka ba ni kunya me rana aka aa ka je kai ta rawar jiki akan 'yar mutane?" Yusuf yaçe, "Wallahi Awal da gaske na ke, son Fa'iza na ke, saboda ita kuma a yau na kyale Dije ko za'a kashe ni ba na auren Dije ina ganin Fa'iza." Awalu ya yi shiru yana mamakin yadda dan lokaci kadan Yusuf ya canza, sai ma ya rinka ba shi mamaki domin wannan wauta ce saboda dai Fa'iza tafi karfin Yusuf. "Wai yanzu nan kai da gaske ka ke?" Yusuf ya bata fuska ya ce, “me ka ke nufi?" Awal ya ce, "Amma da ganin sigar irin halittan Fa’iza ka san ba irin matanmu ba ne. Fai'za siffar matan masu hannu da shuni ce ba mu ba yan cika takarda da surutu". Yusuf ya ce, “ka san abinda Allah zai maida mu can gaba?" Awal ya amsa,” amma yanzu mu ke magana ba lokacin da ba mu da tabbas ba”. Yadda duk Awal ya so ya nunawa Yusuf gaskiya amma Yusuf ya ki amincewa har shi ma ya gaji bayan Yusuf ya ce, to kai ai shirme ka ke yi domin baka warware baikon ku da Dije ba". Yusuf ya ce, "manta da wa`annan ba matsala ba ce yanzu, a wajena shawo kan Fa'iza shine matsalar" Awal ya ce, "ka rufa ma kanka asıri domin zuwan ka Bakori da rashin zuwan ka bai hana Baba Kado ya kai ma Dije idan ranar da suka diba ta cikа”. Yusuf ya nisa ya lumfasa ya ce, "ai ko gaskiyarka fa! Ya yi kasake shin me zai yi yanzu? Wasika zai rubuta gida wajen 33 gwoggo Halima da itama Dijen ko ko? To me ya dace yacе masu? Ya ce kawai a tsayar da biki a mayas da biki sai in har Dije ta koma karatu ta gama nan da shekara uku, in ko ba haka ba to aba wani, sai kuma ya canza shawara kai ina dalili ana auren dole ne ga namiji? ya fada a fili Awal ya juyo ya dube shi yace "maganar zuci ta fito fili, kada fa Fa'iza ta zauta ka, don Allah ka bi a hankali an san ba auren dole a yanzu, amma kuma bin maganan iyaye wajibi ne." Yusuf ya zurawa Awal ido sannan ya tambaye shi "me kaga zan yi?" Awal ya ce, "ka samu lokaci ka je ka yi ma Gwoggo Halima bayani da Mallan Tukur su za su san yadda za su warware komi." * * * Bai dai sami zuwa Bakori ba sai ana sauran sati hudu bikinsu, amma sau uku yana kokarin ganin Fa`iza a makaranta babu dai zancen bayas da hadin kai wajen Fa'iza sai dai ya. yi murna daya, ta ba shi ikon zuwa gidansu haka nan ta yi mai alkawarin idan ya je gidansu zata ba shi katin gayya na bikin cikar ta shekara goma sha takwas. Da yamma likis ya isa Bakori yana bude dakinsa ana kirar mangarib, ya kunna lantarki haske ya sawwaka a dakin, ya dubi bangon gadansa sai ya yi ido hùdu da hoton Dije ta zuba masa ido tana murmushi. Ya ja tsaki da ya dubi kirjinta ya gan shi kamas a ransa ya ce, kila ma wannan shekara zata fara kidanyar dangi, sannan ya tuno da yadda ya lakanci kirarta a dakin Inna Tambai, abin babu dadin tunawa wai shi wace ilar ce ma tasa ya amince masu? Dai dai lokacin da ya kan sami sakewa da mahaifiyarsa wato in dare ya yi suna zaune suna sauraren jakar magori a redio, sai Gwoggo Halima ta ce "amma na ji daddin zuwan ka a yau, saboda zanceń masu kankaran dakin can da za`a sa Dije wallahi sai wasa su ke da aikin don sun ga Malan kwana biyun nan yana fama da mura." Yusuf ya dan muskata ya gyara zama ya jawo wani gwangwani da gwoggo ke aje goro ya dauki daya ya tsaga, a rike a hannu kamar yaci ama bai iya ci ba, sai ya ce, "gwoggo 34 maganar dakin nan a bar ssi kawai" Ta yi har da ido ta ce "kamar yaya a bar shi?" Ye ce "a gaskiya gwooggo a yanzu kam ba zan iya auren Dije ba". Cikin Halima ya bada wani irin kululu har sai da Yusuf ya ji rugunniyar a fili ya dan kawad da kai gefe guda a zuciyarsa ya ce duk na shirya daukar wannan tashin hankalin da zan sa jama'a, zan daure sai na shawo kan ku. "Maitama ka san wanda ka ke fadawa wannan danyar magana?" Kansa a sunkuye bai amsa mata ba, ta sake cewa, "Maitama na roke ka don Allah don Annabi ka rufa min asiri, idan har wani ke zuga ka, ko kuma wata diyar ce take daukar hankalinka, to ka rufa mana asiri, kada kasa naji kunya a garin nan kun fahimci juna da Dije sannan kuma itace dai dai mu,don haka ban ga dalilin da zai sa ka ce ka fasa ba, ko wani abu ta yi maka?" Yusuf ya sa karamin yatsansa cikin kunnensa yana girgizawa, ya fada a hankali ya ce, "wallahi Dije bata yi min komi ba, aurenta ne dai ban yi. Ku yi hakuri Gwaggo da muguwan rawa an ce gwamma kin tashi." Halima ta rasa kalmar da zata yi mai anfani da ita don haka sai kawai ta ta yi tagumi ta sadda kai kasa. Yusuf ya mike. a sanyaye ya dan rusuna ya ce, "mu tashi lafiya gwoggo", ta amsa can kasan makogoranta. Da safe bai shiga gidan ba sai misalin karfe goma sha daya na safe, bayan sun gaisa da gwoggo ya ce mata, "Gwoggo yau da la'asar na ke son na koma ko goberda safe", ta hade rai tace, "Amma ya dace ka je ka gaida Malan domin na sanar da kai bai jin dadi", ya yi murmushi ya ce "Ai gwoggo da asuba ina kare sallah daga masallaci na zarce gidansa na duba sa, ai na ga jikin da sauki ma", ta kawad da fuska ta ce "ka sanar da shi cin mutuncin da za ka yi min ko a garin nan?" Ya ce, "Haba gwoggo, wannan ai ku za ku yi mai bayani bayan na tafi amma bai dace yadda ya ke jin murar nan ba na dame shi da yawan surutu". Ta galla masa harara ta ce, "sai ni da ka mayas shashasha wadda ba ka damu da ciwon zuciyartà ba, ai dole ka zo ka jagula min lissafi, to abinda na ke so da kai shi ne ba za aji wannan zancen 35 a baki na ba, don haka sai ka je ka sanarwa Malan Kado da kan ka'. Zuciyar Yusuf ta rinka ukan uku uku, wane irin zance Gwoggo ke yi haka? Wane shi da tun karan wannan tsoho, duk da dai bai auren Dije amma yana da nauyin Baba Kado, domin yadda Yusuf ke ji da Kado tamkar jininsa, haka nan yana tsananin kaunan Malan Kado har baya son ya tuna cewa `yarsa Dije zai yì ma cin mutunci, shi dai kawai addu'ar Yusuf ita ce Allah yasa Malan Kado kada ya dauki zafinsa a ransa domin ya so ya hakura da Dije albarkacin mahaifinta to sai rabon Fa'iza ya gitta. Ya ce, "A'a gwoggo. Bai dace ace na tari mahaifinta da wannan magana ba, ko don kada a bata sunan gidan nan", tace, "To sai ka je gidan 'yar uwarsa Tambaya amma ni kam da nauyi ace ni na fiddo da wannan magana cikin zuri'ar su Dije" Yusuf ya yi godiya a zuciyarsa saboda ta kwana gidan sauki, abinda zai gaya ma Tambaya bai iya fayyace ma Gwoggo Halima don haka sai ya amsa mata da saurinsa cewa za shi an jima idan ya yi la'asar. Yusuf ya kwanta ya shaki baccin ranarsa mai isarsa, sannan ya tashi ya fesa wanka ya zuba kayan da suka dace da shi, ya fesa turarensa, ya ja kofar dakinsa ya rufe ya kama hanya zuwa gidan Inna Tambaya. Ita ko mutuniyar tun a daren jiya ta ji labarin zuwan Yusuf wato Dije a wajen Malan Kado, to har azuhur ta ji bai aiko mata ba sai ta shirya ta nufi woggo Tambaya ta san dole ya je can sannan ya aika kiranta. Tana uwandakin Tambaya tana kwance da wani littafi Sirrin Boye ta ji sallaman Yusuf ta lumshe ido, ta rufe littafi tace, 'ka cika dan halas Yusuf angon Kubra' amma cikin ranta. Tambaya ta watsan da abinda ta ke yi ta nufo falo da bakonta suka tsinke hira ita da Yusuf shaf ta manta ma da cewa Dije na nan a daki kwance. Tambaya ta ce "Yusuf ina kara gaya maka kada ku matsawa kanku da laihe don haka kada mu ji an ce ka sanya da wani kaddanárku kamar fegi ko gona wannan aure don kulla zumunta za mu yi shi ba don wani abun duniya ba, Dije matar 36 ka ce, idan Allah ya azurta ku can gaba komi ka yi mata mutunci ka ne". Yusuf yace, "Ai Inna, zancen aure nan na mu bar shi." Tambaya ta dafe kirji tace, "mu bar shi kamar yaya?" Ya ce, "E, Inna ni kam ba zan iya zaluntar kai na ba gaskiya Dije ba irin matan da na ke da ra'ayi ba ce, don haka nayi tunani karshe na zo nan gaba na auro irin ra'ayi na ya kasance na ci amanar Dije kin ga idan na yi haka ban yi ma Baba Kado adalci ba, domin ina son Baba Kado tamkan yadda na ke son a ce shi ne ubana sannan ina girmama shi fiye da ko wanne dattijo a garin nan". Tambaya ta ce, "duk na san wannan, amma abin tambaya anan shi ne, wai Dijen ka riske ta da wasu halayen banza ne wanda ba su dace da ra'ayin na ka ba?" Yusuf ya juyad da kai gefe daya yace, "Ka ji Inna don Allah! Ina nuna maki ita kanta fasalin Dijen ne na ke dubawa na san bai yi mani ba, ba wai halin ta ba". Tambaya ta ce “fasali kamar yaya? Dije guda nawa ce? Duka duka yanzu ta shekara goma sha biyar yaushe makerin `yanmata ya gama kera ta? Wannan ba dalili ba ne Maitama". Yusuf ya ce, “Gaskiya Inna ina son mace mai cikar kirji sannan tana da tudun mazauni amma Dije fa haka take a shamude". Makogoron Tambaya ya bushe takaici ya turniketa, abun haushi goma da ashirin, ga yusuf na ta wulakanta mata. diya a gaban ta, sannan kuma tana tunanin yadda zata kalli jama'a idan an ce an fasa wannan aure. Sai ta daure ta ci gaba da lallashin Yusuf. Ta ce, “ina son na fahintar da kai wani abu daya Yusuf, ita dai diya mace namiji ke mikar da ita", ya yi sauri ya dube ta yace, "kamar yaya namiji zai mikar da mace?" Tambaya tace, "ka san Allah wannan kirjin na Dije da sauran abubuwan da ka ke hange jikin sauran mata, idan ta sami wata shidda nan tare da kai mikewa zata yi, in dai tana samun cima mai kyau tare da kwanciyar hakali. Kai kan ka sai ka yi mamakinta, saboda wallahi Dije ba irin busassun matan nan ba ne wahala ce, da rashin kwanciyar hankali ya takurar da ita haka." Yusuf duk yana jin abinda Inna Tambai ke fada, a ransa ya ce, "Ina! Don dai ba ki ga gimbiyar mata ba ne Fa'iza." Ya 27 knfasa ya ce, "inna Tambai ku dai yi hakuri don Allah a baiwa su Baba Kado hakuri, insha Allah idan hankula suka kwanta zan sami Baba Kado har gida na kara kwantar mai da zuciya". Ya rinka duba agogon hannu, wato nuna alamu son tafiya a dai na bata masa lokaci, ya mike ya ce, "To inna sai na zagayo gaisuwa wani lokaci." Tambai a cikin sanyin murya ta ce masa, "Ka sami wadda ran na ka ke so ko?" Da farko kamar ya ki gaya mata gaskiya, amma sai ya yi tunanin menene amfanin kin gaya mata zancen Fa'iza sai ya ce, "E, Inna na sami wadda na ke da sha'awa ta mallaki duk abinda na ke so a jikin mace". Tambaya ta zuba tagumi sannan ta sadda kai kasa, ta manta kwata-kwata a ina take don dacin rai, Yusuf ya sunkuya ya fita, ya tsugunna bakin kofa yana saka takalmansa amma bata ji abinda ya ke fadin ba, balle ta amsa masa. Yana isa gidansu ya tabbata ya dana bom a Bakori nan da awa daya zai tashi a gidan Baba Kado, don haka ya yanke shawara ya bar garin komi dare don kada tashin bom din ya hada da shi. Dacin ran da ya haddasawa Halima bata yi masa tararrabin cewa ya fasa tafiyar sai gobe ba domin ganin dare ya yi, sai kawai ta ce a sauka lafiya. Sái karfe sha daya da minti tara na dare ya shiga dakinsu, ya cimma Awal yana ta famar karatu, nan da nan suka dubi juna suka bushe da dariya, Yusuf ya sunce kayan jikinsa ya fice ya watso ruwa sannan ya dawo. Awal ya ce, “ina labari mutumin, na san dai yau hawayen Dije sai da ta cika ma hula taf." Yusuf ya ce, "kai wa ke ta Dije wannan ai nafila ce, ni da manya na kafsa masu hau-hauwan jini na samu na shawo kan su don kada ace na tayas da ciwo Insha Allah komi ya yi daidai yanzu na shawo kan Fa'iza kawai ya dame ni." KASHI NA HUDU Gwoggo Tambaya na nan zaune inda Yusuf ya bar ta, ta kasa hasala komi, tun tana jin she-shekar kukan Dije har ta 38 rinka jin ta tana kuka wiwi, can tambaya ta nisa ta ja habar zaninta ta goge hawayen da suka taru gefen idonta, ta се, "Wallahi dole Dije ki yi kuka Yusuf ya yi mana abinda mafarkinmu bai taba nuna mana ba, ke ki gane mun yaron wofi sai da mu ka saki jiki da shi sannan kiris ya rage mana mu kammala shirin kayan dakinki shi ne zai mana haka? Babu laihi Allah zai baki wanda yafi shi". Tambaya hawaye, idan ta yi ban maganar ta gaji sai ta yi shiru ta ci gaba da sakar zuci, sannan ta koma baiwa Dije baki. Dije kam kuka ta ke har bata san abinda zata koka mava ba, `shin rashin gwarzon masoya Yusuf, ko ko masifar su gwoggo Ankudi, ko ko surutun jama'a akan an baiwa Yusuf ita amma ya zo ya ce bai yi?' Mangariba na yi Tambaya ta je alwala Dije ta sille ta nufi gida, a bisa hanya jahilci ya zo mata wai ma ko ta je bisa titi mota ta nike ta ta huta da wannan muguwar rayiwa? Sai dai kuma Allah ya hana ka yanke ma kan ka hukunci komi kunci. Ta isa gida ta yi sallah ta kudundune, ta yi kuka ta yi kuka, har kuka ya nemi kan shi ya rasa, har garin Allah ya waye tangaran babu bacci a idon Dije. Da safe zazzabi da haraswa suka same ta, amma babu wanda ya kula balle ya tausaya mata. Tambaya ta aiko mijinta tunda safe cewa malan kado ya je tana son ganinsa. Shi kan shi Malan yadda ya ga Tambaya ya san babu lafiya. Ta gaya masa Yusuf dai bai yin aure amma bata fadi fallasar da ya yi ma Dije ba. Nan take Malan Kado ciwon kai ya taso, sai dai babu mamaki domin tun kwanakin baya da Malan Iliya ya raka shi asibiti an tabbatar da hawan jini a tare da Malan din. Ya ce, "Tambaya jiri na ke ji idan za'a sami kunkuniya а kicin din ki samo ki jika min”. Ta mike ta nufi daki ta fito da kwandaleliyar laya ta mika masa ta ce, "daura wannan Insha Allah zai laf”. Ya amsa ya daura ya dafe kan yana juyayin abinda Tambaya ta gaya masa wai Yusuf bai auren Dije! Can Tambaya ta katse shi ta ce, “A daren jiya Malan ban runtsa ba, nayi juyayin zancen da yaron nan ya zo ya gaya min duk yadda a kai Shiga tsakaninsu a ka yi, kuma za ka ce na gaya maka, wannan 39 asiri ne su Ankudi su kai ma yaran nan." Malan Kado ya dago kai ya tsurawa Tambaya ido babu tantama ya amince da zancenta sai dai menene abun yi, bayan bakin alkalami ya bushe. Ya lallaba ya koma gida Dije na tausayin kanta tana tausayin mahaifinta domin ta san bacin ran da zai shiga kwatan kwacin na ta ne. an ji. Kwana biyu zance ya zagaye garin bakori har su Ankudi Da hantsi DDije jikinta ya yi lankam ıa damuwa da bacin ran da Yusuf ya saukar mata, Ankudi ta zo ta tsaya inda Dije ke kwance ta sakar mata kafa a kashin baya. Dije ta yi kugi ta се "Wayyo Allah na!" Ankudi ta yi dariyar mugunta ta ce, "munafuka ki ke karyar ciwo, ashe inda aka kai tallarki sun ce su ma ba sa so? Kadan kika garii ja'ira mai bakar kafa, tashi maza ni ki je ga wanki can na tara ki wanke man." Dije na gindin rijiya ta yi kokari jikinta ya tsaya daidai amma ina sai makyarkyata ta ke yi, da ganinta dai ka san bata da koshin lafiya, ga Sabura da Ankudi na ts aye gefen ta suna ta yi mata shegantaku da cancakwati wai Allah ya yi ta mara fasali ga bakar kafa Dije dai na sunkuye: ta na murzar kaya yayin da idonta ke zubar hawaye. Malan Kado ya dade da shigewa yana tsaye daga can kofar shigowa duk irin cancakwatin da su Ankudi ke yi a kunnensa, da ya lura ba su da niyyar dainawa haka nan babu mai iya juyowa ta gan sai ya yi gyaran mur ya, gaba daya su ka juya su kai mai ca da ido. Ya lumfasa ya ce, "Amma dai kun ji kunya, yanzu ku idan an ba ku iko ko dan yatsa kuna iya halittawa Dije? Amma mutane ku zauna ku rinka kushe ma yarinya halitta a gabanta, to don Allah cikinku duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyařa". Ya koma ya fice a fusace ya nufi gidan Tambaya yana huci ya ce mata, "ina ganin dai duk ayi a kare karshen ta gwauro zan zauna". Tambaya ta yi zuru da idanu ta dai san matsalar gidan Malan Kado, don haka bata nemi jin ba'asi ba, sai ta се 40 hakurin nan dai za ka yi amma yanzu duk wani dan motsi da za kayi Dije za ka kara shaława kashin kaji, ace ka kori matanka don an ki auren ta, abunda dai baka so shi za ka hakura ayi. Wato ka ga na dai san mahaifiyarta Amina ba son auren nan ta ke yi ba tafi kwadayin makaranta, saboda haka don ka fid da Dije daga wannan kangin fitinar ka ban ita kawai na kai ta wajen Amina ta samar mata makaranta in ka so ta rinka zuwa ma hutu kana ganinta". Malan Kado ya yi tagumi yana shawara da zuciyarsa, shi kan shi ya san ya dace ace Dije ta sami canjin yanayi ko ta zama mutun ta sami natsuwa zuciyarta babu kuwa inda ya dace sai wajen mahaifiyarta Amina. Malan ya dubi Tambaya ya ce, "kina ganin shu'umin mijin nan na ta zai amince?" Tambaya ta ce "Haba Malan don ba ka ga yadda Amina ta ke ba ne a gidan Isa, wallahi daga ita sai 'ya'yanta ka san tuni ya kori waccan uwangidan na shi da ya ga tana neman ta tsangwamawa Amina da 'ya'yanta sannan kuma gidansu rayuwace irin ta `yan boko, ba irin tamu ba, ka san shi Malan Isan ma'aikaci ne haka zuri'arsu don haka ka da ka damu, ka kwantar da hankalinka." Ya ce "To shi ke nan bari na koma gida na turo ma ki Dijen in ya so gobe in Allah ya kai mu sai ku tafi." Har yanzu Dije na gindin rijiya tana ta fama da wankin kayan Ankudi Malan Kado ya cimma ta, ya ce, "ke Dije maza shirya kayanki ki je gidan Tambaya anjima bayan an sakko masallaci ina nan zuwa". Dije fuskarta a kunbure hatta kwayar idonta kamar za su zazzago saboda masifar kuka, ta kwashi abinda ta san tana so ta nufi gidan Tambaya, kai idan ka ga Dije a wannan lokaci ka tausaya mata, tamkar mahaukaciya sabon kamu, duk ta kode ta yi jeme-jeme, ga kaya wasu a kwali yayin da wasu ta yamutsa cikin jakar leda. Tambaya ta sanya almajiri ya wanke mata kayanta fes, sannan ta nemi jaka mai dan mutunci ta zubawa Dije kayanta. Wanshekare tunda safe Malan Kado ya zo raka Tambaya da Dije tasha, suna tafe yana yi mata nasiha yace, "To Dije kin ga dai halin da muke ciki don Allah don Annabi ki kama kan ki, kada ki yadda batanci ya fito daga gare ki, yadda za'a ji dadin yi 41 mana dariya, ki tuna irin gwagwarmayar da mu ke ciki da ni de ke, haka nan duk halin da ki ka shiga kada ki manta da sallah, ke da duk nauyin da ya hau kan ki na addininmu ki kula da hakkinsu." "Ina kara gargadin ki tsare mutuncinki, mutuncin diyɛ mace shi ne kamun kai, tsare kai daga zina da duk saurar shedanancin zamani, kada kwadayin abun duniya ya rude ki hai ki fada hanyar banzu, don Allah ki dangana da abinda zan

Chapter 4 of 5