Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
da jefa tambaya wom "Da gaske kake ba zai zo ba?" Ya dan kanne ido yana yi mata dariya "Ashe duk abin naki gulma ne? Gaskiya Asma'u son gayen nan yana nema ya yi miki yawa kwanya." "Ka dai iya bakinka dan ko ina dauke da albishir, ina so in fada ina so in Ki fada." "A haba da Allah gara dai ki fada." "Ni na ma fasa." Nan da nan ya shiga lallami har da durkusa mata ta ce "Bari dai na baka labarin Mina." "Wacce Minar?" ya fada gami da zazzaro ido. "Oh Minar suna da yawa ne?" "O'o Kwaya daya gareni. Ta daga dan yatsanta "To ka ga daya, biyu, uku...'"Me ki ke nufi?" "Igiyar auren Mina gaba daya ta katse.... "Ki bari don Manzo?" Ya fada gigice. "Wallahi babu wasa, auren Mina ya mutu." nishadance ya dunkule hannuwa ya kai wa bango duka. "Lallai ashe zamu fasa zuwa Yola "Ka ji ka da garaje, wa ya ce ma ana zance akan idda? Ai ko za ka je gareta sai bayan wata uku, shi ya sa Mommy ta Ki gaya maka," gobe-gobe. 24. Ya ce "Wai tun yaushe auren Mina -ya mutu?" Asma'u ta ce "Ina jin zai kai kamar wata guda.""Kai amma wannan miji na Mina akwai dan arziki irin albarka." "Nima sai da na zuba masa albarka." "Kin san yanzu abin da za yi, dole mu je Yola bari Aminunki ya Karaso sai mu kai ki ki gano min lafiyar mina, amma mu ba magana za Mu yi mata ba, sai mu dawo mi yi ta Kirga kwanaki." -. Ta dan yi dariya "Idan kuma ka tsaya sanya ~wani ya yi maka shigar sauri, dan kuwa bazawarar Kauye farin jini gareta." "Don Allah sunan nan ya fita daga bakinki, yarinyar 'yar baby da ita ki dinga kira mata wani bazawara." Asma'u dariya kawai ta tsaya tana yi masa dan at san daga yanzu kuma basu da wata magana in ba ta Mina ba, ya sake sakin dariya har da sowa "Wayyo na gode Allah, nima aurena ya zo gaskiya na ji dadi da ki ka gaya min ai da kin Boye da kin cuce ni." ys Ta tsaya tana kallon shi, "Tun da na fada ina tukwicina?" Of oer "-©e a,' "Kar ki damu ran ba ki tukwici, bari Goggo ta dawo zamu tsara komai. Wai shin ina ma ta tafj ne?" "Ta tafi gidan 'ya'yanta sai da daddare za ta dawo." "Kai gaskiya na so ganin Goggo yau din nan." Salim ya je airport ya daukoshi kuma sam ya Ki yarda ya kai shi hotelya ce wannan karon shi ne mai masaukinsa, don haks kai tsaye gidansu ya zarce dashi, ya yi breakfast can ya dan huta, sannan ya karkata hankalinshi da son ya je ya ga Asma'u. Tun da Salim ya lura Aminu ya matsu da son ya je ga Asma'u sai ya yi ta tsokanarsa "Haba kar ka ba da gayu mana, shin ba ka san kai yaro ne maj tsada ba, ai bai dace ka yi gaggawar zuwa ta ganka ba. Kamata ya yi mu dan ja aji sai mun ja mata rai sosai, irin zuwa gobe din nan sannan miye gareta. "A haba da Allah an gaya maka zan iya wannan juriyar? In dai ba so kake na kwana ina maka kuka ba..." Amunu ya iso Sokoto tun da sanyin safiya, "Haba kuka? Sai ka ce wata Baby." 26 "Yo an gaya maka hawayen nawa tsada greshi, in dai akan Asma'u ne ai kullum sai sun kwarara. Salim ya saki 'yar dariya "Ba da kyau mutumina, ka ce ashe dai yau zan ga hawayen soyeyya." Suka uifé suna dariya "Ka ga ni fa Malam Kagauce nake bana jin zan iya kaiwa dare ban dora ido kyakkyawar fuskar mutuniyar ba." Salim yz ce "Ai ni vau dama ta samu dole ne na wana Asma'u ina jin ma sai na ga digon hawayenta ko kuma sia ta durkusa min gwiwa bibbiyu da ta gan ka." "Oh kai ka ce daman hawayenmu kake son gani ba wan abu ba?" Gaskiya kusan haka din ne dan ni hawayen soyayya yana burgeni. "Mhm tunda hawayen kake son ganj maza hanzarta ka je Yola ka gano na Mina." Suka kwashe da dariya gaba daya sai da suka gama barkwancinsu suka yi raha sosai sannan suka shiga hirar al'amuran duniya hirar tasu ta kwashesu tsawon lokaci sai da yamma Salim ya kwanta barcint shaKatawa ya bar Aminu falo yana karatun jaridar Weekly Trust ganin barcin Salim ya yi nisa bai yi pnanin tashinsa ba, dan kar ya yanke masa barcinsa kawai sai ya je ya yi wanka ya canja kaya, ya shirya tsab, sannan ya latubi makullin motar Salim ya fice. Bai zame ko ina ba sai Gwiwa Lowcost gidansu Asma'v, ya yi fakin motar harabar sidan Kai tsaye ya chiga ciki. Goggo ya iske, falo ta ganshi kamar jifa; nan da nan ta fadada fara'arta "A'a ka ga Turawa, mutanen Rasha, zawarcin nawa aka zo?" Ya Karaso ciki yana dariya "Da ba ki ce min Bayerabe ba, ai na samu." haba ai kai Bature ne Salim shi ne dan Yarabawa. gayar dake. "Anya? Ma'unke dai ta yl bulaguro.". Ya dafe kai razane "A haba da Allah?" "Yo zan tsokane ka ne? In za ka zauna mu yi Ya ce "To ina Gimbiyar sannan na ji dadin tadinmu gara ma kazauna in dai.ssoyayya ce ai nima na iya." Suka yi dariya gaba daya sariman ya durkusa ya fara gayar da ita. Asma'u da ke can dakinta, daga wanka ta fito take zaune gaban madubi tana kwalliya amma jikinta ya ba ta lallai Goggo baki ta yi, domin daga inda take tana tya juyo maganganu sama28 sama da sauri ta sa kayanta, ta shirya shigar wata yellow atamfa ta yi super English wax ta feshe jikinta da turare, ya fi kala biyar, da yake ma'abociyar son Kamshi ce, tana shirin daura dan kwali, ta juyo Karar wayarta can falon Goggo inde te jefar da ite, kujcra tuntuni. De cudunte ta nufi falou dan ia amsa wayar. Ganin da ta yiwa Aminu hakimce akan kujera ta yi turus, ta ja ta tsaya, ta zaro ido cike da mamaki yau ganin da ta yiwa Aminu ji ta yi wani irin sanyi yana ratsa zuciyarta, ta zuba mishi ido ko Kiftawa ba ta yi duk da ta san Aminu kyakkyawa ne, amma zuwansa Turai ya dada kyau fiye da da, ya yi fari sol kai ka ce Baturen Birtaniya, suna hada ido suka yiwa juna murmushi sai lokacin ta ji kunyar yanda ta fito Kanta babu dankwali. Ta sa hannu ta dauki wayar, Alhaji Yahaya suka gaisa gaggauce ta ce "Alhajin Allahn yi min afuwa zan kiraka da daddare." "Ai ko ba ki fadi ba na san Aminunki ya dawo, me yiwawa ma kina tare dashi yanzu." Ta saki yar dariya sannan ta katse layin ta Juyo ga Aminu. Ya dan yi mata sigina, itama ta kanne ido tana dariya ta cewa Goggo "Bari na raka Aminu gidansu Salim yanzu zamu je mu 29 ey wer dawo." Ta shiga daki da sauri za ta dauko dankwalinta da mayafi, Aminu ya bi ta da kallo, yayin da ya Kurawa dogon gashinta ido, yanda ya sha gyara duk ta tubke da ribon. Tana. fitowa ya amshe jakarta ya rataya suka jera har gindin meta, suka shiga ya tuKa suka tafi, sai da suka yi nisa da tafiya babban tit' sannan suka dau hanyar wani dan Kauye, ya sauka daga tit. ya dan gangara can gefen hanya, sannan ya kashe mota ya dan rage music din da suke ji, ya juyo ya dubeta. "Ya ya dai Madam?" Ta dan lumshe ido cikin wani kyakkyawan kallo, sannan ta sakar masa shegen murmushin nan nata mai kashe zuciya, amma farin ciki ya hanata magana. Wai yau ga ta ga Aminunta, abu sai ka ce mafarki. Suka yi shiru na dan lokaci, sanyin a.c. dake cikin motar ya ci gaba da ratsasu, suna ta shaKar Kamshin turaren juna. Ya sake juyowa ya dubeta, suka sakarwa juna murmushi, sannan ya yi gyaran murya Shin me ke zuciyazki yanzu?" Ta fara magana cikin muryarta mai taushi "So da Kauna kuma sannan wannan yammacin ya zo min da farin ciki." Ya dan gyada kai ate da murmushi "Ko za ki tya tuna rabonki da farin ciki irin wannan?" "Kai gaskiya ba zan iya tunawa ba, domin dai na dade ban yi irin wannan farin ciki ba, na dai san lokacin da mijina Yusuf ya sakeni na yi farin ciki, amma kuma cikin awanni Kalilan sai farin cikin ya juye ya zama bakin ciki, lokacin da na je ga Ahmed ya shaida min wai ba ka nan ka tafi Turai to baya ga wannan lokacin gaskiya ba zan tya cewa ga wani kebabben lokaci da farin ciki ya bakunci zuciyata ba." Ya yi dan murmushi Gaskiya nima na shiga Kunci iri-iri rayuwata, amma yanzu zuciyata fest take komai ya riga ya wuce bana son tunawa abin dai da na sani dukkanmu mun sha wahala dalilin soyayya, amma yanzu ta zama tariht, dukanmu 'yan halak ne kuma zamu nunawa juna halacci ina so kawai ki bani hadin kai in fito neman aure yi komai gama cikin Kankanin lokaci. Zan yi duk cuku-cukun da ya kamata domin karatunki ya koma Kano." "Amma na dauka za ka yi min uziri jinkirta maganar har sai na Karasa karatu." Ya watsa mata idanu "Lallai gaisheki da dauriya in har ke za ki iya wannan dauriyar to ni ba zan iya wannan haKurin ba, dan bana jin zan iya kaiwa mako uku ba tare da na mallaki abin 31 sona ba, idan har makonni uku suka wuce ba tare da an yi bikinmu ba, zan iya shiga wani hall...... "Amma muka yi hakurin shekaru ma bare na wasu watanni? "Amma dai kin sani wancan lokutan bamu da damar auren juna, yanzu kuwa babu wata miskila muna da damar yin hakan ya kamata mu yi amfani da damar da muka samu mu hanzarta yin aure, dan mu mallaki junanmu hankalinmu ya kwanta, kin ga sannan zamu gane waye ya fi son wani cikinmu." Ta dan Kura masa ido "Kenan kana shakkun son da nake yi ma?" "No ba haka bane Mamace take gardamar cewa son da nake yi miki ya fi wanda kike min to sai gashi kuma da na zo gidanku Goggo tana Korafin wai Kaunarki ta fi tawa, gashi nan sona zai illata ki." Ta saki 'yar dariya tana dubansa "Tunda abin zama mujadala ai sai nemo musu alKalanmu Ahmed da Zaliha ko Salim su zasu raba gardama. Ya Kura mata ido yayin da ya mayar da maganar wasa "Don Allah don Annabi Asma'u ki yi min alfarma guda daya?" "Wacce iri?" Ta buXata hanzarce. 32 ae rn neil "Ki amince da aurenmu yi cikin mako biyu zuwa uku, walldhi mahaifiyata ta damu Kwarai da halin da nake ciki. Yanzu ma jira take na je mata da KwakKwaran bayani. Haba Asma'u ai ko ban fada ba kin san ina son ki, son da ya wuce tunanin duk wani mai tunani, ina Kaunarki Kaunar da ta wuce kwatancen mai kwatance ko kina shakka akan hakan?" Ta dan girgiza "Kai ni ban taba shakka akan hakan ba." "To idan kuwa haka ne me zai hana aurenmu wannan lokacin tunda muna son junanmu bamu da haufi akan Kaunar da mu kewa juna tunda har mun yarda da kanmu dan me ya sa zamu tsaya muna azabtar da zuciyoyinmu? Ko ke kina ganin idan muka dauki dogon lokaci bamu mallaki juna ba ba zamu cutu ba? Ke tunaniki in wani ya cutu cikinmu mun yiwa soyayyarmu adalci kenan?" Ta yi shiru yayin da ta nisa cikin tunani. Aminu ya fiddo wayarshi ya kira lambar mahaifiyarshi, bayan ya gaishe ta cikm girmamawa suka fara tattaunawa. Ta ce "Abba in ce dai yarinyar nan ba ta ba ka matsala ba?" Ya yi murmushi "Wallahi Mama ki kwantar 33 -_ da hankalinki babu wata matsala, Asma'u ta kusan zama tawa ba ki ji ni cikin nishadi ba. Yanzu ma muna tare, ba abin da yake zukatanmu sai farin ciki da annashuwa, ga ta nan Mama don Allah ki yi mata addu'a irin wacce kike yi min." Ya mikawa Asma'u wayar, sai da ta dan rusuna sannan suka gaisa da Mama ta ce. "Haba diyata Asma'u ya kamata ki rinKa jin tausayin mutumin naki, ki dan rangwanta masa nima tausayi yake bani. Cikin dariya ta ce "Shi kenan Mama ki yi hakuri na tuba, ba zan sake ba." Ita ma ta yi dariya "To Asma'u yanzu mene ne magana game da aurenku? Sai da ta yi dan dam! Sannan kunya ce ta ce "Mama ai magana na hannunki sai yanda ki ka ce dan ni ko gobe ki ka ce daura aure shi kenan. Ta yi 'yar dariya "Shi kenan diyata na gode, tun da kika hani wuKa da nama in sha Allahu nan da sati biyu ma kin zama amarya. Suka yi dariya gaba daya, sannan suka yi sallama, ta ajiye wayar. Ya juyo ya dan dubeta tare da sakar mata wani shegen murmushi "Iye «vaya ga amarya?" Ita ma murmushi kawai ta yi, wayarta ta 34 dade tana Kara amma ko kula ta ba ta yi ba, har ta gaji ta katse, hirarsu kawai suke mai dadi, dan haka ba ta so wani abu ya katse musu hirar. Amma ko da ta ga an sake bugowa sai ta dauka tana ganin Salim ne ta kara kunne "Hello sorry please wallahi Salim ban san kai ba ne." Cikin dariya ya ce "Ku ji ni da mutane, wai shin ina ku ka shiga haka?" Ta saki 'yar dariya "Tun da baka san inda muke ba to buri in gaya maka, muna nan garin masoya." "Wai me kuke ne?" "Soyayya mana." Gaba daya suka kwashe da dariya. Aminu ya amshi wayar ya ce "Haba Malam kar Ka fa takura mana da yawan kira, kama zuwa Yola mun fasa ba zamu'ba." Ya ce "Ayya komai za ku fada ku yi ku gama za ka dawo hannu nan gaba sai ka durkusa min, ba kana son ganin Asma''u, ina so ka sanar da ita cewa maraki fa ba abokin tafiya ba ne." Cikin dariya ya ce "Ahaf, shime kake kafin lokacin da zan durkusa maka ai ni kuma ina garin angwaye." "A haba da Allah kun ma isa ai duk gaggawarku dole ma ku jirana..." "Kai ina ana maganar sati biyu yaushe zamu tsimayi mai watanni biyu, gaskiya ba zai yiwu ba." Asma'u ta fizge, ta katse layin "Manta dashi damunmu yake son yi." "Ba ruwana idan na tafi ke zai tsiya." Jimawa aka sake bugowa, Aminu ya dauka. Satm din ne dai Sorryplease ku daure ku dawo da wurl, ma nan gidan Goggo ina jiranku da Allah wata unguwa nake son ka rakani. Idan ka biyewa Asma'u ba za ta bar ka ka taho ba." Cikin murmushi ya ce "Shi kenan kar ka damu ga maw nan akan hanya." Yajuya ga Asma'v ne ya ke so mu fita yawo, dan Allah ki yi hakuri ma koma gida yana can yana jirana, kia san Salim ya fi Karfin komai gurina. Wallahi Asma'a dalilinki ina Kaunar Salim sosai, in baya ga Ahmed babu wanda ya wuce Salim gurina. Suna isa gida suka tarar Salim yana zaman jixansu yana gaban Goggo suna tattaunawa. Kaya ne tule falon Goggo wanda Salim ya zo da gaba daya tsarabar Turai ce, wanda Aminu ya yiwa Asma'u, bayan Salim ya nunnuna mata ta dan girgiza kai gami da kallon Aminu. "Gaskiya kar ka sake yi min hidima irin wannan, ni kai nake so ba wai abin hannunka ba, ka gane? Don haka bana so ka ke min wahala." "A haba da Allah Malama ina wahalar take." Salim ya mike "To ranki ya dade mu tafi kin sallameshi?" Ta dan zumbura baki "Kuna iya tafiya, amma ka tabbatar ka dawo dashi." Suka yiwa Goggo sallama tare da alKawarin zai zo gobe kafin ya wuce zuwa Kano. Washe gari tun da wuri Asma'u ta shiga kicin ta shiryawa Amuinu breakfast sannan ta yi wanka ta shirya, tana ta Allah-Allah ta ga ya iso. Sanye take cikin wani yadi material pink colour an yi masa wani tsadadden dinki, da yake gwanar kwalliya ce, yadin ya amshi jikinta ta yi kyau sosal.Aminu bai iso ba sai kusan goma da rabi na safe, duk yanda ta so boye damuwar ta sai da Aminu ya gane, anan fa ya yi ta rarrashinta har da durKusa mata "Haba Gimbiya yi min afuwaa dan saki murmushin da zai sanyaya min zuciya don Allah ki yi hakuri, 'amma ko ina da laifi na Salim ya fi yawa, dan ko shi ya hanani fitowa da wuri, amma duk rabin hankalina yana gareki, yanda tunaninki ya hana mini barci daren jiya hakan na wayi gare dake zuciyata, bana son ki dinga damuwa kin sani ko ina nake zuciyata tana tare dakc." Ta dake cikin shan mur "Kenan kana nufin har ka zo ka tafi ba za ka ci rin abincin gidanmu ba ko? Shi kenan na gode." Ya dan ta6e baki cikin tsokana "Wane ni ai ban isa ba, in ban ci girkin Gimbiyata ba, na wa zan ci?" farin ciki Ahmed yakira Asma'u waya "Kin ga mutuminki ya gudo Sokoto ko sallama bai-yi min ba saboda na ce ya tsimaye ni sal satin sama mu taho tare." Ta fadada murmushinta "Yo. don me zai. jiraka har sai ka gama yanga." "To ai gashi nan ya ZO sai ku hadiye juna mu ga Karyar soyayya." "Mhm ai ba mu masoyan da suka yi,hakan-ba bare mu ma mu yi." "Yo 21 5a) fara ta kanku domin mu san kuna 38 Suka saki dariya gaba daya. Asma'u ta bawa Tabawa mai aikinsu umarni shiryo musu. breakfast bryosu dasht. Daga nan ta ja Aminu zuwa lambun gidansu ta shimfida musu darduma tsakiyar madaidaicin lambun suka zauna nishadance suka yi breakfast tare, duk yan soye-- soyen da ta yi mai babu wanda ba) ci ba. Sun yi hirarsu sosai, irin ta masoya zukatansu cike da rr rs soyayya." Ta saki 'yar dariya gami da kashe wayar. Sai bayan Azahar Salim ya zo ya kaishi airportya hau jirgi ya tafi gida. Asma'u dai ba ta so tafiyarshi cikin kwana daya ba, to amma da yake ya riga ya gaya mata uzururrukan da suke gabanshi dole ta Kyaleshi, ya tafi. Washe gari Salim ya zo ya sa ta gaba ya matsa mata akan sai sun tafi Yola sun gano Mina. Sai da ta wanashi ta gama ja masa rai sannan dan kanta ta dawo tana jin tausayinsa, saboda yanda ya matsu dole sai ya je ya ga yarinyar, hankalinsa zai kwanta. Lallai so masifa ne ta fada ranta. Yamma liKis ce ta kaisu garin Yola, sai da suka fara zuwa gidan Hajiya Binta yar mahaifiyarshi anan suka yi sallar La''asar suka ci abinci, sannan suka dauki hanyar Kauyen su Mina, ba laifi suma yanzu rigar tasu ta hade da gari. Al'ummarsu sun ci gaba, duk mutanen garin sun waye, musamman ma matasansu da suka dan yi karatun boko, har gasar sayen motoci suke yi, sai ¢\ka ga matashi ya sayar da shanu ya sayi motar thawa, ya yi ta yawo gari yana fantamawa. Suna isa gidansu Mina gaba daya mutanen idan suka yi ta murnar zuwansu. Asma'u ta sami akkyawar tarba daga gurin Mina, amma kunya 39 14 ta hanata yiwa Salim magana, tun da suka gaisa ba ta ce masa komai ba, sai dan murmushi da ta dinga jifansa dashi. Bayan sun dan huta ya shiga wurin Baffansa Mina ta ja Asma'u dakinta suka sake suka yi hira sosai anan Asma'u cikin hikima ta dinga nunawa Mina irin matsanancin son da Salim yake mata abin ya bawa Mina mamaki saboda ta ji wai har yanzu Salim sonta yake don ita zatonta tuni ma ya mance da wata Mina, anan ta shaidawa Asma'u dududu bai fi wata daya kacal ta gama idda ba. Salim ganin da ya yiwa Mina ba Karaminfirgitashi ta yi ba, domin Mina da ya sani tana Karamar yarinya gashi yanzu ta zama mace sosai ta dada kyau ta dada fari ta goge sosai, dama can ba ta yi kama da mutanen Kauyen ba, dan ko ruwan ta na wayayyu ne bare kuma da ta yi aure birni gashi myin da ta fito daga hannunsa mai kudi ne ranar dai kusan kwana suka yi suna hira Mina ta saki jiki da Asma'u sosai ta dinga bayyana mata irin yadda take jin Salim zuciyarta, da yanda sonsa ya yi tsamari zuciyarta, har ta kasa kyautatawa mijinta, har ya gaji ya sakota. Kwanan su Asma'u daya suka koma Sokoto daga nan kuma ta yi shirin tafiya Kaduna domin yiwa mahaifiyar ta sannu da zuwa, sun je Umra sun dawo ita da mijinta. Sai da Salim ya kai Asma'u Kaduna sannan ya dawo ya tafi da ita, cikin makonni biyu Mama ta shirya komai da komai sai da ta gama shirinta sannan ta sanar da 'yan uwan mahaifin Aminu Kannen Babansa su hudu ne suka tafi Sokoto nemawa Aminu auren Asma'u gaba daya dangin uban Asma'u. Sun kar6i iyayen Aminu mutunce wata miskila ko sa'in'sa nan take suka .e zasu bawa Aminu auren 'yarsu bayan sun koma Mama ma ta zo Sokoton ita da aminiyarta yayin da Goggo ta yi musu jagora gidajen iyayen Asma'u, suka yi musu godiya. cikin satin ne dai Aminu shi da Ahmed suka sake zuwa Sokoto suka hadu da Salim suka je gaishe-gaishen surukai duk wani wanda ya Kaduna suka gaida mahaifiyarta da maigidanta bayan sun koma garuruwansu suka shiga shiryeshiryen biki. Dan ma Baban Salim ya dan kawo musu jinki. Ya ce "Su yi hakuri daga bikin saboda 41 kamata gaishe shi cikin dangin Asma'u sun je masa nan kuma suka rankaya sun masa sami hadawa da na Salim, dan haka duk wani shirye-shirye tsanake su Aminu suka yi binsu, da yake dama tuni Ahmed ya kammala da ginin gidan da Aminun zai zauna cikin 'yan kudaden da Aminu yake turowa ta banki, daga can. Shi ne Ahmed ya gina masa katafaren gida gini na zamani, kuma ya saya masa wata tsadaddiyar mota irin ta tsere sa'a. Salim yana garin Delta yana can yana ta Kirga kwanaki har gani yake kwanakin sun ki gudu.Saboda Salim, Mina ta Ki zaman Kauye ta dawo cikin garin Yola gidan Hajiya Binta Kanwar babanta da yake ta san Salim yana yawan gaisawa. da Hajiya waya domin baya sati guda bai bugo waya gidan ba. Hajiya Bita dai da ta ga son Salim ya yiwa Mina yawa da kanta ta nemi Salim waya ta ce masa "To Salim, Mina fa ta gama idda sai ka san abin da kake ciki." Ai kuwa nan da nan bai jira ba Bata lokaci,_ washe gari sai ga Salim ya dira garin kamar an jehoshi, karo na biyu da suka sake dulmiya soyayya, bayan wancan ta baya. yanzu sun sake dora wata akai duk yanda Salim yake zaton Mina za ta bashi matsala, saboda kunya irin tasu ta fulani amma sai ta bashi mamaki, dan kuwa ya sami hadin kanta ta sake dashi suka yi ta hirar 4) soyayya labari 1T1-1F1 babu wanda basu yi ba, har labarin gidan mijinta da ta fito sada ta bawa Salim.Kwanansa uku Yola suna tare da Mina 'guna soyayya sai da Hajiya ta ga bashi da niyyar tafiya tukunna ta koreshi saboda rashin kunyarsu ta isheta haka nan. Cikin kwanaki uku sun hanata sakewa, dan ko lemo Salim zai sha sai Mina ta cika tambulan ta bashi baki, idan kuwa ita ba ta bashi ba to shi zai ba ta dan haka ya dirkonsu, Hajiya Binta ta fatattaki Salim ta ce ita kam ba za 'al wannan iya-shegen gabanta ba. Kafin Salim ya tafi sai da ya hadawa Mina waya saboda su dinga hira cikin sirri. Dan kuwa -tunda Minah ta yi waya kusan kullum sai sun raba dare suna hirar soyayya, lokuta da dama sai tsakar dare sawu ya dauke yake kiran Mina waya wanl Sa'in ma Sai ya yi barci ya farka, ya kan kirata. Nan da nan Mina ta goge ta fada duniyar soyayya, Sai ka ce ba bafilatanar Kauye ba, wani abin ma in ta yi har mamaki abin yake bawa Salim, satin da ya gabata ya je Sokoto ya sanar da Daddy maganar Mina, Daddy ya ce ya ce "Kar ka damu da yake tuwona maina ne tuni mun gama magana da Baffanka abin da ya rage kawai sati mai zuwa za kai kayan aure, amma mun y! 43 shawara da mahaifiyarka daurin aure kawai za yi, tarewa ba yanzu ba, sai ka Karasa bautar Kasa ka dawo gida sai yi bikin tarewa, ka ga in ka kammala service kai ma za ka fi samun nutsuwa." Salim kamar ya ce "Wayyo Allah!" Don shi sam ba haka ya so ba, to amma kunyar Daddy ta hanashi musu, shi kam da son samu ne kawai yi aure kawo masa matarshi in ya so duk sati ya ke zuwa Weekendgida. Nan take ya yanke shawarar zai lallami Momy akan ta dawo da Mina Sokoto, domin ya san Momi wayayya ce ba za ta hanashi sakewa da matarshi ba, amma muddin Mina tana can komai ya yi Yaddiko Korafi za ta yi ta yi musu ta ce sun yi rashin kunya, sun fita daga al'adar fulani. Kwananshi daya Sokoto ya tafi Kaduna dauko Asma'u, sannan suka biyo ta Kano ya kaita ta gaida mahaifiyar Aminu, lokacin Aminu ba: ya gida da yake ya fara aiki, da wani kamfani na zirga-zirgar jiragen sama, Mama ta yi murna Kwarai da zuwan Asma'u ta dinga ina ka sa ina ka ajiye da ita, ji take

Chapter 2 of 4