Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
kamar ta goyata don Kauna, don ¥3nzu idan ka dauke Aminu Mama ba ta da diyar ad take so zuciyarta kamar Asma'u, babu yadda Mama ba ta yi da su akan su jira Aminu ba, amma Asma'u ta ce sauri suke yi, saboda suna kan hanya. Mama ta matsa akan sai an kai Asma'u ta gano sabon gidan da aka ginawa Aminu,w anda zasu zauna, amma sabo da kunya irin ta Asma'u Kin zuwa ta yi, sai Salim aka raka ya gano gidan. Anan gidan Mama ta zauna yaje ya dawo, sannan suka yi sallama da Mama, suka dauki hanyar Sokoto. Mama ta yi farin ciki da kyautar tsarabar da Hajiya Hadiza ta aiko mata na Umra, dan wannan shi ne karo na farko da zasu Kulla kyakkyawar alaKa. Tun da suka tafi hanya Salim in ban da labarin sabon gidan Aminu babu abin da yake bawa Asma'u dan gaskiya gidan ya burgeshi sosai da sosai. Gidan ya hadu haduwa ma ta Karshe, tun daga kan ginin har irin tsarin furnitures din da aka shirya dakunan, komai ya yi kyau, ya yi tsari hatta kafet da labulaye an zuba wadanda suka dace da tsarin gidan babu abin da zai f: mutum burge sai tsarin babban falo nasu sai ka ce 'Tura, duk yanda Salim ya ke kuranta gidan 'Aminu ita Asma'u duk wannan Kyale-Kyalen sam bai dameta ba, ita burinta kawai ta ganta tare da Aminunta sun zama ma'aurata sun isa Sokoto da marece saboda tsabar gajya, duk Asma'u sai ta ji jikinta babu dadi gala6aice ta isa gida ta dan hada ruwan zafi ta yi wanka, sannan ta yi sallah ko abinci ba ta nema ba ta kwanta saboda ciwon kan da yake damunta can tsakar dare Karar waya ta farkar da ita daga barci, ta sa hannu ta dauka. "Hello ya kake?" "Haba Ma'una abin da kika yi kin kyauta kenan? Kuma ki zo Kano har ki tafiba mu gajuna ba." Ta dan yi murmushi "Oh sorry da Allah ai ba gurinka na je ba." "ft "To shi kenan na ji ya ya dai kun isa gida~ lafiya?" "Eh mun iso Kalau..." "Ya ya nake jin muryar taki wani so co/d? "Mhm ba wani abu gajiya ce dai kawai." No da Allah kar ki Boye min inda wata damuwa." gane?Ya saki 'yar dariya "To tunda kina sona ki Ni dai bani da wata damuwa sai ta sonka, ka Itama ta yi dariya "Ai ina ga haka din zaayl cikin nahiyar masoya in kin san kina buKatata hadiye ni mana?" kaga idan na yi haka tarihi ya maimaita kansa 46 kusa-kusa daren yau ma sai na zo gareki. "A haba da Allah daren yau sai ka ce wani jemage." "Yo ki ka sani ko nima fiffiken zan saka na tashi sama, na fa Kagu na ganki kusa dani." "Ai ni ban so ka wahala wajen tada fiffike ka bar shi kurum ni zan zo cikin barcinka." "A haba da Allah ai ba za ki iya ba." "Me zai hana? Zan iya mana." "Da dai ni ne zan iya zuwar miki cikin barci saboda na fi ki matsuwa da yanzu bani da buri da ya wuce daura mana aure na ji ki kusa da ni, ke fa mene ne burinki? rf "Mhm burina kawai na kasance tare da kai kullum nake dora ido akan kyakkyawar fuskar nan take mai dauke da Kayataccen murmushin da ke sanyaya raina." Tana gama fadin haka ta katse layin tare da kashe wayar da yake ta san ta tsokanoshi tn za ta biye mishi sai dai su kwana suna hirar soyayya. Aminu ya sake din lambar Asma'u ya ji ta rufe, "Wayyo Asma'u me mana ya sa ki ka yanke hirarmu mai dadi? Allah ya kawo ranar da zan mallake ki na nuna miki zahirin Kaunata gareki ranar, zan nuna miki gundarin tsagwaron soyayya, dan wata Kaunar sai dai cikin daki. 47 Haba yarinya tunda ki ka Ki kowa domina nima zan nuna miki ba wata sai ke, ni dan halak ne kuma sai na nuna halacci." Ya dade yana sambatu shi kadai. Salim tun da ya koma Delta garin da yake Services bai sake zuwa gida ba, sai satin da za daura musu aure ya iso Sokoto ya rage kwanaki biyu daurin aure ya tarar da abokansa suna ta shirye-shiryen daurin auren, gida kuwa Daddy ya gama duk wani shirye-shiryen da ya kamata yi domin karbar daurin aure. Salim ya nemi Aminu waya domin jin abin da suke ciki, ya shaida masa ba Kano yake ba,_. wani aiki ne ya kai shi Abuja, amma su Ahmed suna can suna shirye-shiryen biki. Koda Salim ya tuntu6i Ahmed sai Ahmed ya yi masa bayanin irin abubuwan da suka shirya. Salim yaji dadin yanda su Ahmed suka tsara komai daki-daki. Daurin aure dai ya kama ranar Lahadi kuma gashi mahaifin Mina ya sawwaKewa jama'a zuwa garin Yola, don haka shi da 'yan uwansa nan Sokoto suka zo aka daura auren bayan an kammala daurin auren Mina da Salim sai mutane suka dunguma unguwar Rinjim Sambo Lowcost bisa jagorancin kwamishina Baban Salim an 48 daura auren Asima'u da Aminu Kofar gidan wan mahaifinta, gaskiya daurin auren ya yi armashi domin birnin na Shehu ya dinke da jama'a. Jama'ar Kano sun nuna halayyar tasu dan kuwa irin jerin gwanon da motocif Kanawa suka yi cikin garin Sokoto abin sai wanda ya gani. An yiwa maroKa abin da suke so don kuwa Kanawa sun watsa kudi sosai. yammacin ranar daurin auren ne Daddy uban Salim ya shiryawa amare da angwayen Kasaitacciyar liyafa, domin tayasu mura. Manyan mutane da dama sun halacci liyafar kuma take gurin Daddy ya yiwa amaren kyautar sabbin motoci kowacce ya manna mata makullin hannunta. Asma'u ta rusuna ta karba kunya ce amma Mina yana mika mata sai da ta rie ta dan sumbaci hannun Daddy sannan ta amsa. Nan da nan wuri ya kaure da da sowa, Salim kamar ya hadiyeta dan burgeshi da ta yi, babu wanda zai kalli Mina ya yi zaton wai ta taba Tayuwa Kauye. Washe gari motocin daukar amarya suka zo daga Kano aka shirya amarya Asma'u, da 'yan rakiyarta ranar ta ci kuka har ta gode Allah, ba komai ne ya sa ta kuka ba illa rabuwa da Goggo da kuma amininta Salim. Don ko mutuwa ma 49 sabo da shaKuwa ake kokawa tana jimamin rabuwa da Goggo, Kakarta mai Kaunarta mkai son ganin farin cikinta, waje daya kuma tana kewar Salim amininta, abokin shawararta mai Kaunarta mai son ci gabanta, wannan tunani ne ya sa ta Ki rarrasuwa, sai da aka je aka nemo Salim, ya Asma'u duk ta rikice komai kwance mata duk yi ta lallami yana ba ta baki. Da Kyar ya samu ya shawo kanta ta yi shiru. Mommy Babar Salim da kanta ta riKe hannun. Asma'u ta kaita har cikin motar Salim ta ce masa "To Salim ga mutuniyarka nan in ka rakata gidan mijinta sai ka dankKawa Aminu amanarta. Duk da Salim ya yi ta maza amma sai da ya share Kwalla, saboda tuna wasu al'amura da suka faru baya, sal yanzu ya ji wasu abubuwa sun tsirga masa Zuciya game da Asma'u, wannan shi ne karo na farko da ya ji ina ma shi ne ya auri Asma'u, nan take ya yi maza ya kawar da wannan tunanin. Kaico zuciya mai raye-raye da saKe-saKe ya fada ransa, sannan ya daga kai ya dubi mahaifiyarshi sanyaye "Momi dan Allah ki bar Mina ta yiwa Asma'u rakiya dan sauran bikin can Kano za yl." Momi ta ce "Ni ban hanata ta bi ku ba, amma dangi aka taru kanta anar ashi daga Karshe da ka san gidanmu cike yake da baki mutanen Kauye._ ta ya za tatsallakesu ta taho?" Nan ya dauki waya ya kirata. "Ya Mina maza ki nemi direba ya kawoki yanzu-yanzu Kano zamu tafi, amma ki taho da kayanki wanda za ki saa wurin party muna nan Kofar gidansu Asma'u." Ba jima sosai ba sai gashi har sun iso, direban ya bude mata motar Salim, ta shiga gidan -baya ta kame, daga nan Salim ya bi jerin gwanon Kananan motocin daukar amarya suka jera reras, suka nufi Kano. Duk sauran motocin cike suke amma motar amarya su uku ne ciki, daga amarya sai Salim gai Mina dan haka suka sake sosai, suka yi ta hira har suka isa Kano dangin ango suka tarbesu, gami da kyakkyawar maraba, suka tarar da gida ya cika da 'yan uwa sun yi dafifi suna dakon isowar amarya. "Yan rakiyar amarya kwanansu daya Kano aka gama yinin biki aka kawo motocin da zasu 'maidasu Sokoto, tun da amarya ta iso ango bai samu damar ganinta ba, saboda gida ya cika da mata 'yan biki. Salim ne kurum yake zirga-zirga -tsakaninsu. Goggo ta ce "Kai dal aie wallahi kunyarka ragaggiya ce, tun da ka ga an taho da Mina ba Za ka bar 'yar mutane ta sake ba, sai faman zirgazirga kake cikin mata." Goggo kin fiye kwarwa an gaya miki wurinta nake zuwa? Ba ki san ni ne babban Kawar amarya gayyato daga jami'a, tun da ni ne mai masaukin baki ni kadai nake hidima da 'yan biki, kina gani Cikin dariya ya dan shafa Keya "Ke wallahi ba dole ne na shigo na duba bakinmu da muka Zaliha ta gudu London ta Ki zuwa bikin Kawarta." Asma'u ta sa musu baki "A'a kar ka ga laifin Zaliha baby namu ne ya ke wahalar da ita ni na hanata zuwa domin cikinta ya tsufa, amma da zarar ta haihu za ka ga sun dawo Nijeriya abin da kullum muna gaisawa waya, duk na san halin da take ciki." yammacin ranar bayan duk 'ya biki sun watse abokan ango sun shirya gawurtaccen partya wani katafaren sote/ partyn da ya hada tantagaryar 'yan boko, attajiran matasa, samari 'yan kwalisa, da kuma'yan mata masu ajikowaya halacci wurin partyn ya san Naira ta yi Kwakwaran motsi dan duk wani masoyin Aminu ya yi alwashin bikin Asma'u ne kadai ya kamata su nuna Kaunar da suke yi masa zahiri. Gaskiya kam partyn ya yi armashi an yi. abubuwa da'dama na burgewa, manyan abokan ango sun yiwa mawaka kyautar mashina an yi liki na bajinta, ba wai kudin Najeriya kurum aka dinga watsawa ba, a''a an yi liki da dollars an yi da kamsumiyya, kuma an yi da rafar Nijeriya, an bawa abokin ango dama domin ya ce wani abu. Ahmed kuwa ya yi bayani sosai mai gamsarwa daga Karshe ya mika shawarwarinsa ga amarya da ango, bayan ya zauna ne kuma aka kira babbar Kawar amarya, lokacin da Salim ya tashi matsayin Kawar amarya gaba daya ha// din ya dauki tafi da sowa. Sai da hayaniya ta lafa kowa ya nutsu, sannan Salim ya fara nashi bayanin cikin harshen Turanci kai ka ce wani baturen Birtaniya, ya bada tarihin soyayyar Asma'u da Aminu daga bisani ya rufe da dankawa Aminu amanar Kawarsa. Labarin soyayyar amarya da ango ya bawa jama'a da dama mamaki, yayin da wasu kuma bayanin Salim ya tsaya musu zuciya, musamman wdanda basu san tarihin Asma'u da Aminu ba, an dai yi taro an tashi lafiya. Gaba daya an kammala da komai na biki sai fatan Allah ya bawa ma'auratan zaman lafiya da soyayya mat dorewa. Bakin tika-tiki-tik komai ya yi farko yana da LE ee Karshe, daren yau ne abokan ango suka yi masa rakiya dakin amaryarsa bayan an yi raha, an gama barkwanci irin na abokai sai Salim ya kamo hannun Aminu ya hada da na Asma'u, sannan ya yi musu jinjina. "Ya yi Al'Amin mai gaskiya da rikon amana na yarda kaine saurayi dan baiwa, yaro ga kudi ga boko ga kuma soyayya har kullum dai Asma'u amana ce gareka, ga ta nan amanatun amana." Sannan ya juya gareta, sai da ya sara mata sa'annan ya dan yi kirari "Ka ga Ma'un Goggo yarinya ga dollars ga kyawu, ga ki 'yar hutu ce ga wadatar ilimi, ga riKon alKawari. Haba nan da nan wuri ya kaure da ihu da sowa irin na 'yan boko Salim ya yi dabara ya sulale daga cikin jama'a ya zagaya ya janyo hannun Mina suka fice daga falon suka ma bar gidan gaba daya, suna shiga mota basu zame ko ina ba sai Aofe/ ya kama daki ya biya, aka basu makulli suna shiga Mina ta bata rai. Yana hawa gado ya jehota da filo. "Ke ji nan fushin me ki kewa mutane?" "Amma Yaya Salim wannan ma ai rashin kunya ne, ka san fa Momi da Goggon Asma'u suna gidan Babar Aminu, sai gobe zamu tafi tare dasu kuma yanzu suna can suna jiran in an sayl bakin amarya zan koma wurinsu kawai sai su ji ka daukeni na kwana wani wuri..." "Ke da Allah malama kin fiye tsoro waye zai gaya musu inda muka kwana, ko ganinmu zasu yi?" Ta sake tsuke fuska, kafin ta ankara ya mika hannu ya janyota jikinsa sun zube gado tana shirin zullewa ya shiga Aissing dinta, sannan ya sakar mata harshe cikin baki yana tsotsa, sai da ya tabbatar ya kashe mata sassan jiki ta zamanta hannu. Abokan ango sun gama siyen bakin amarya, sun tafi, ya dan rakasu ya dawo ya dan dubi kyakkyawar amaryar tashi nishadance "Shin Asma'u ya ya sunan wannan rana garemu?" Ta dan kashe ido gami da langabar da kai ikin kujera, "Ranar cikon farin ciki." Suka dubi juna suka vi murmushi, ya janyo nafila raka'a biyu, suka roki Ubangiji da ya Kara musu fahimtar juna da zaman lafiya mai dorewa. Bayan sun gama addu'o'insu Aminu ya mike ya bar ta akajn sallaya, yayin da ita kuma ta bishi da hannunta suka je suka yi alwala, suka yi sallar "To Madam zan dan shiga ciki, idan kin Murmushi kawai ta yi amma ba ta ce komai ba, sai da ta gama abin da take sannan ta y! shirin kwanciya. Wata masifaffiyar rigar barci ta zuba jikinta, yayin da ta feshe jikin nata da wani sassanyan turare. gajiye ta nufi sashen maigidan nata, har ta isa tsakiyar falon ba ta ga kowa ba, sai bedroom ta cimmishi. Fitowarshi kenan daga wanka, daure da tawul yana taje kai. Ganin shigowar Gimbiyar tashi sai ya dan juyo cike da farin ciki, yajefeta da wani sassanyar murmushi, da ke iya narka zuciyar masoya sannan ya ware hannayensa gaba daya yana yi mata nuni ta taho, da farko Asma'u ta tsinci kanta tana dan jin kunya amma can da ta tuna ba fa wani bane face gwarzonta Aminu, da gudu da sassarfa ta Karasa, ta isa gareshi, ta fada Kirjinsa suka rungume juna. Wannan shi ne karo na farko da masoyan suka ji dumin juna, laushin fatar jikinta.ce ta fara kidimashi har suka kai ga zubewa gado, ya mika hannu ya kashe koriyar wutar da ke kunne dakin, daga nan kuma sai komai ya fara kwance masa. Sun jima suna wasanni irin na ma'aurata kallo, ya dubcta gam da kada ido kammala da komai ina jiranki." 56 aq amma koda tafiya ta fara yia nisa sai labari ya sha bamban, don duk yanda Asma'u ta so puna jarumta sai da tsoro ya bakunci zuctyarta, da yake bakuwa ce wannan fanni, shima abin ya fara daure masa kai har ya dinga tambayar kansa shin kada dai ace Asma'u ba wanda ta bawa hakki duk cikin mazan da ta aura? Sai gashi zargin dake zuciyarsa dai yana neman zama gaskiya. 'Why' me ya sa ta aikata haka? Da asuba -bayan sun yi wanka, sun yi Sallah sun koma makwancinsu amma da ta gaji da tuhumar da Aminu yake mata sai ta y1 masa kuka cikin rarrashi ya ce "Haba Asma'u ko ba ki yi min tanadi ba ai na san kina sona, amma dan me ya sa za ki zalunci mazanki na baya, saboda ki faranta min, Maza uku ki ka aura, amma ki ka hanasu hakKin aure ace duk cikinsu babu wanda ki ka bawa kanki, ai ba ki kyauta ba, ni Aminu ina Kaunarki ne ba don wani abu naki ba, Allah ne ya hada mu matsayin masoya kuma koda kin tsufa gidan myinki na farko in dai ya sakeki zan iya zuwa gareki, tunda ina sonki, kuma ko kin haifi 'ya'ya goma zan aureki haka, dan haka bai kamata ki tauye hakKin kowa saboda ni ba, tunda kowa ya biya sadaki kuma shaidu sun shaida babu wani dalili da zai sa ki zaluncesu." Ta dan numfasa sannan ta fara magana cikin muryar kuka "To ni ya na iya da raina Amin? Ka dai sani kaine mutum na farko da na taba so rayuwata, haka nan kuma Kaunarka ce ta hanani sukunin aiwatar da komai, tare da mazan da na aura kowa da zuciya daya na aureshi amma sai na tsinci kaina da Kin hada makwancia da shi, kar ka ga laifina Amin so masifa ne, abubuwa da dama sun faru sabanin hankalina, duk yanda na dinga zaton zan danne sonka sia bayan ka bar Kasar na gano ashe hakan ba zai yiwu ba, idan mutum yana muradin abu har abada abin nan baya gaushewa, in za ka iya tunawa tun da Kuruciyata zuciyata da so da Kaunar ka nima tashi na yi na tsincl zuciyata mai sonka ba wai yin kaina ba ne.' Kalaman Asma'u gaba daya sun kashe masa jiki, ji yake wani shegen sonta yana dada ratsa zuciyarshi tamkar ya hadiyeta, sannan ya dawo da ita dan Kauna, shin anya ko akwai namijin da ya taba son diya mace tamkar yanda yake son Asma'u? Ya fada ransa, yayin da ya sake janyota jikinsa ya rungume yana lasar hawayenta, gami da rada mata wasu kalamai kunne. "Ni Aminu zan nunawa Ma'una maza suna da tabbas kuma namiji dan goyo ne, zan ci alwashin hakan har Karshen rayuwarmu, na aurcki 58 bisa so da Kauna zan zauna da ke cikin soyayya, zan riKeki bisa amana, zan cika alKawarurrukan da na dauka ba ke ba kishiya, kuma ba ni ba sake kallon wata diya mace, kuma in sha Allah ke da bacin rai ko wani Kunci kun yi adabo dan duk inda farin ciki ya ke zan nemo na kawo miki, kada ki manta ni ne Aminu, wanda ban ginu akan soyayyar kowa ba sai ta Asma'u." Ya dada yi mata kyakkyawar runguma ya matseta sosai akan Kirjinsa yana shafar gashin kanta, daga nan barci mai Karfi ya daukesu, sai can misalin tara da rabi wayar Salim ta tashesu, Aminu ya dauka "Ya ya aka yi mutumin nema fa kake ka damemu."" "A haba da Allah ku yi ta barci haka sai ka ce wasu gajiyayyu." Ya yi dan murmushi "Yo mene ne marabarmu da gajiyayyun. Wai shin ina kuka shiga ne? Muka yi ta nemanku daren jiya." "A'aha ka san ni bana sanya, muna can garin masoya muna soyayya." Suka saki dariya gaba daya, "Ka fa fito mu yi sallama zamu tafi, dan su Goggo sun yi gaba tun sassafe." "Ai kana nufin ba za ka shigo ko sannu ka yiwa mutuniyar ta ka ba?" "Na yi mata sannu aikin me ta yi?" "A haba ai jinjina ta zama dole gareta domin kuwa jarumar jarumai ce." Sai da ya juya ya yi kissing dinta sannan ya diro daga gado ya je waje, gurin su Salim, babu yadda bai yi dasu su shigo su yi sallama da Asma'u ba amma Salim ya Ki domin ya san Asma'u tana iya sashi kuka. gaggauce suka yi sallama da Aminu suka kama hanyar Sokoto. Satinsu biyu suna murzar amarci mai cike da tsantsar soyayya, ko fita Aminu ba ya yl, sai dai gidan Mama, kullum suna manne da juna suna soyayya, sai da hutunsa ya Kare ya koma bakin aiki yayin da ita kuma Asma'u ta fara karatunta jamu'ar Bayero ta maida hankalinta gaba daya karatunta, sai kuma soyayyarta ita da mijinta da ya fi damunsu, amma suna yawan kiran Salim ko Goggo waya shima ba ya kwana biyu bai kira Asma'un ba, amma dai ya Ki zuwa Kano duk iya naci da roKon da takewa Salim akan ya zo yaKi. Ran nan Aminu na falo shi da Asma'u suna hirar Salim kwance take jikinsa ta yi matashin kai da cinyarsa hirarsu suke yi mishadance yayin da ya sa hannu yana shafar lallausan gashin kanta, ta ce "Ni fa gaskiya na matsu da na ga Salim zan yi masa Karya ko da na rashin lafiya dan ya zo 00 Jdubani." Ya yirdan murmushi "Gaskiya ba za ki hada baki da ni ki wahalar da Salim ba ki duba ki ga nisan Delta, in kin yi haKuri kwanaki kadan ya rage masa ya gama service ya dawo gida, yanzu ma rigimar da suke da Mina kenan, jiya yake gaya min waya wai ita ta tsorata da wasu alamu da take ji jikinta gara ya zo ya kaita asibiti, don in cikine cire da wuri wai ita kunya take kar Morm ta gane." Asma'u ta saki dariya "Ashe Mina tana shirin haukata Salim. Ka san ko yanda yake da son 'ya'ya?" Amin ya yi dariya "Ai duk son haihuwarsa bai yi ya ni ba, dan ko yanzu na matsu ki ce wani abu in kuma muka cike watanni uku babu motsin komai dole mu ga likita." "A haba da Allah kai ka fiye garaje, har yaushe muka yi auren?" Ya ce "Ni kam haka nan ban san dalili ba Allah ne ya jarrabeni da son haihuwa, ina son na ga na haifi 'ya'ya da yawa, shi yasa. nake da masifar son Kananan yara to bare kuma dan da zai fito daga cikin cikinki wanne irin farin ciki kike zaton zan ji ranar da kika haifo min baby gidan nan?" Murmushi ta sakar masa gami da shafa cikinta. Ahmed ya yi sallama gami da shigowa falon "Kai mutanen nan ba ku da kyau shin kullum ba ku da aiki sai soyayya?" Asma'u ta.dan zame daga jikin Aminu gami da tashi zaune tana murmushi, Aminu ya ce "To me ka ke so mu yi baya ga soyayya? Ka san in ba Madam na ji kusa da ni ba, bana samun nutsuwa bare kuzari. Ya dan dubi Asma'u "Ba fa ki samu zama ba Wasila ce ba ta da lafiya, kuma ina zaton haihuwa ee ce. Asma''u ta hangame baki "Wayyo Wasila: Allah dai ya raba lafiya." Aminu ya ce "To bari mu kai Madam ta kar6i haihuwar. Da sauri ta shiga ta shirya. Bikin Salim da Mina ya zo Aminu ya kai Asma'u da Mama Sokoto tun da suka isa Asma'u take ta mumar ganin Goggo. Ba su jima da zuwa ba, Salim ya iso bayan ya gaida Mama suka kebe da Asma'u. Salim ya fara tsokanarta, "Kin gan ki kuwa? Kai gaskiya amarcin ya kar6cki." -62 land Ta ce "Wai me ka ga na yi?" "Wallahi gani na yi duk kin canja min. Kai Asma'u ban yarda da ke ba duk yanda aka yi ciki ne da ke," Ta dan Kura masa ido "Kai Salim bana son tsokana ni bani da wani ciki." "Kin san Allah ture zancen wasa akwai alamun ciki tare da ke." razane ta dan dafe Kirji "Ni da nake shirin tafiya service ya ya zan yi da ciki?" Cikin murmushi ya ce "Ai ba wani abu sai mu yi duk KoKarin da zamu yi domin su bar kia Kano, lallai yau ina da daddadan labarin da zan fadawa mutumin, amma idan kin Karasa gidanmu zan yi miki fest don mu tabbatar, amma na fi zaton ciki ne dake." "To ni dai kar ka gayawa Amin har sai mun tabbatar, ka san halinsa da doki bari na gaya masa zan je gaida Momi in ya so sai ka daukeni mu tafi." "Kin san idan ki ka je Mommy ba za ta bar ki ki dawo ba." "Ai dama can zan kwana saboda na sami gaisawa da Daddy, dan tun jiya na yi masa waya na sanar dashi za mu zo. Mina ce kawai ba ta san yau zamu zo ba." 63 =~ "Ai Mina ta koma Yola tun satin da ya wuce, can za ku je dauko amarya kin san halinta duk ta bi ta damu kanta da maganar ciki." Asma'u ta saki 'yar dariya "Mhm Mina kenan, wai shin cikin har ya fito fili ne?" "O'o ba wani fitowa da ya yi kurum dai ita take shirmenta, nake jin dai bai fi (two months) ba ke da ita za ku yi kunnen doki." Tun Sokoto cikin Asma'u ya tabbata, Aminu ji yake kamar zai hadiyeta don tsananin farin ciki, murnarsa Kin boyuwa ta yi har sai da Mama ta ji itama da yake dokin samun jika take abin ya yi mata dadi. Asma'u ta sauka gidan Mama duk ta bi ta Da aka gama bikin Mina suka dawo gida Sal shagwaggwabe wai ita gajiya ta dameta. Nan fa taga tattali gurin Mama, da yake dama tun tarewarta ta ture gwamnatin Aminu ta zama ita ce yar lele,yar gaban goshin Mama, so na duniya babu irin wanda uwar Aminu ba ta nunawa Asma'u ba. To bare kuma yanzu da take dauke da cikin jikanta. Aminu sam bai ji dadin yanda'Asma'u ta tare gidan Mama ba, domin duk yanda ya so ya sake da matarsa yana jin kunyar mahaifiyarshi, gashi ya yi iya Jallami akan su koma gida amma Asma'u 64 ta Ki yarda wai ita sai ta huta, saboda ta san muddin suka koma gidansu fitinarsa ba za ta bar ta ta sami hutun da take buKata ba. Musamman gashi gidan Mama tana samun wadataccen barci da daddare, ga tattali da gatan da take nuna mata. Ta yi shagwa6a soon ranta in ta ga dama ma cinyar Mama take barci, idan gidanta ne da zarar Aminu ya fita wurin aiki ba ta da wanda zata yiwa shagwaba gidan, daga ita sai mai aikinta sai kuma mai gadi. Kwanan Asma'u hudu Aminu ya ji ba zai jure ba dan kewar matarsa ta dameshi musamman makwancinsu ko barci ba ya ityawa, domin yanda Asma'u ta yi masa sabo mai wahala. Aminu dai ya je har gidan

Chapter 3 of 4