Mama ya dauki matarshi ya
kai ta gidan Ahmed don ta gano Wasila matar Ahmed da dansu Khalifa, anan suka hadu da Ahmed da Amin har da Wasila- suka yi ta
rarrashinta akan ta tausayawa mijinta ta koma
gida.Asma'u ta ce "Shin me ku ke so na gaya wa Mama bayan na riga na ce mako biyu zan yi gidanta?" Anan Ahmed ya shirya mata dabara don haka
tana komawa gida ta yiwa Mama Karya ta ce
"Rijistar da suka yi kwanan baya KarKashin
65
fungiyar manyan likitoci yanzu
an fara neman
su zasu yi course na makonni biyu." Mama ta ce "Tun da haka ne sai ki koma
gida saboda Abba ya sami rangwamen
kaiki da daukoki." Dare na yi Aminu ya zo ya
tafi da matarsa, daga nan suka sake bude sabon shafi na rayuwa. Haka dai rayuwar wadannan ma'aurata ta kasance
cikin soyayya da Kauna da kulawa da juna wannan shekara ne ta kammala karatunta na
likitanci cikin nasara, sai dai dan laulayin da take
fama dashi, yau da lafiya gobe babu, gashi likitan
da yake dubata ya ba ta tabbacin 'ya'ya biyu ne
cikinta twins amma kuma duk scanning din da ake jariran suna cikin Koshin lafiya. Satin da ya zo Asma'u ta ji dadin weekend
din dan ko manyan bakinta Salim da Mina ne
suka zo musu Sallama kafin su wuce Abuja, wani
sabon asibiti da Salim zai fara aiki, wanda mahaifinsa ya gina gami da hadin gwiwar wani attajiri amininsa mazaunin Abyja. Asma'u ta yi mamakin yanda Mina ta dawo
sai ka ce Balarabiya pashi cikin ya karbcta, ta Kara kvau, ta yi bul-bul da ita sai ka rantse bata
taba zaman Kauye ba, gashi abin sha'awa cikinta
ba mai laulayi ba.
66
Salim ya dubi cikin Asma'u yana dariya
"Gaskiya babynan namu yana wahalar da ke. Amin ya gaya min wai kin daina cin nama, tuwo
ne kurum abincin ki. Shi ne nake zaton duk yanda
aka yi manomi za ki haifar mana, in ban da manomi ne bebin mu ta ya ya zai hana Mamanshi cin komai sai tuwo." Kwanansu biyu suka wuce Abuja. Watanni
suka ci gaba da shudewa, cikin Asma'u na dada
girma, har watan haihuwar ta ya kama ranar da
ciwon naKuda ya kamata da gaggawa
ta dannawa Mama waya ta iso cikin hanzari, suka tafi asibiti,
lokacin Aminu baya nan yana can bakin aikinsa
ranar jirgi mai zuwa London zai tuKa daga Mama har Asma'u ba wanda ya sanar dashi halin
da ake ciki. Suna isa likitansu ne ya karbi haihuwar tata
kuma cikin ikon Allah komai ya zo da sauKi, Asma'u ba ta wahala ainun ba. Cikin awanni biyu
ta haifi
jariranta guda biyu tagwaye. Mama cikin tsananin muma ta rungume 'yan
samarin har kuka suka sa ta saboda tuna baya. Bayan Aminu ya dawo gida aka sanar dashi
rashin lafiyar Asma'u. kidime ya garzaya zuwa asibitin, amma abin farin ciki yana isa sai ya tadda
'yan jariransa gado suna boxing muma dai gurin
67
Amin ba sai an fada ba, ga 'yan jariransu sun fito duniya ga
kuma Ma'unsa ta sami lafiya. daren
ya yi ta buga waya yana
sanar da jama'ar su haihuwar Asma'u. Washe gari Goggo da mahaifiyar Salim suka
iso Kano ganin baby. Momy ta kwana daya ta koma yayin da ta bar Goggo gidan Asma'u suna da kwana hudu, Hajiya Hadiza ta iso daga Kaduna
tare da tawagarta, wannan shi ne zuwanta na farko
gidan diyar tata, tun bayan aurensu ba ta taba
zuwa ba, saboda kawaici.
ranar ne dai Salim ya iso tare da matarsa da kuma dimbin sayayyar kayan baby mai jegon
kanta ya yi mata dinkuna sama da kala goma. Ranar suna an bar wajariran sunansu Hassan
Ca Hussaini, gaskiya bikin sunan ya yi armashi 9sai, kusan duk danginsu sun sami halattar sunan
'yan tagwayen 'yan uwansu na Sokoto da na Kano
dana Kaduna duk sun zo, hatta 'yan uwan Salim
ba barsu baya ba, dalilin zumuncin da ke
tsakanin Salim da Asma'u kowa ya ga irin
kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu abin ya kan
bawa mutane sha'awa, gashi dai duk sun. yi aure
amma zumunc! bai yanke ba, an dai yi taron suna
an gama lafiya, duk mutane sun koma
garuruwansu.
68
Goggo kakar Asma'u ita ce ta zauna gidan mai jegon, saboda kula da jariran, yayin da Mama
ta kawo musu mai reno. Haka gaba dayansu suka maida hankali ga kula da jariran Asma'u Allab- Allah take ta yi arba'in ta je Kaduna wurin mahaifiyarta amma ana saura kwanaki biyu su yi arba'in sia ga wayar Salim, yana shaida musu Mina ta haihu ta sauka lafiya da diyarta budurwa. Asma'u ta yi muma Kwarai kwanansu uku ta
isa Abuja harda Goggo da kuma mai renonta, 'yar kyakkyawar jaririyar
ta fi kama da uwarta, daga haihuwa Salim ya yi wa 'yarsa huduba da sunan Asma'u, abin ya burge Aminu sosai. An yi shagalin suna Abuja, bayan an gama
kowa ya watse aka taKaita sunan jaririya Asma'u
aka dinga kiranta Asma. Bayan 'yan tagwayen Asma'u sun yi Kwari sai ta fara services dinta da
yake jihar Kano aka bar ta. Tana kammala bautar Kasa ta fara aiki babban asibitin Murtala Muhammed dake cikin bimin Kano. Hassan da Hussaini suna da shekara daya da watanni biyu Asma'u ta sake samun ciki, da da
farko duk ta damu amma da ta ga yanda Amin
yake masifar dokin cikin sai ta haKura domin dai
ta san ko duk shekara za ta rnnka haihuwa ba zai bari ta yi p/anning ba, tunda burinsa kenan ya ga
vida ya cika da 'ya'ya. Da cikin Asma'u ya isa haihuwa sai ta sake haifo 'yan tagwaye suma maza, lallai rabo sai mai
shi. Ranar suna aka radawa jariran Ahmed da Muhammad Salim, shekarar ne kuma Salim ya
sami tafiya wani course Kasar Amurka tare da
iyalinsa, KarKashin Kungiyar manyan likitoci ta duniya.
lokacin sun yaye diyarsu Asma'u
junior. Mina kuma tana da Karamin ciki, kuma dai duk shekarar ne Zaliha Kawar Asma'u suka dawo daga London ita da mijinta da yaransu guda biyu mace da namiji.
Jariran Asma'u suna da watanni uku ta koma bakin aikinta, da yake Asma'u yarinya ce mai Kwazo fannin aikinta ta Kwarai sosai aikin
likitanci tana taimaka mata da Kananan yara ta
sami daukaka asibiti, ta sami nasarori, 6angarenta ta zama babbar likitan gani duk wata
lalura da ta shafi mata Doctor Asma'u ta laKanceta babu wata cuta za ta shafi mace wacce Doctor ba
ta sani ba, dan haka mata masu matsala suke
rububinta, kowa buri yake ya ga garni gynic) Doctor domin akwai ta da bincike sosai. Mata masu ciwo suna 1ya ganinta sau uky sati gata da
tausayi da tattalin mara lafiya. Bayan shekaru hudu da haihuwar su Ahmed
Juniorta sake samun ciki ta haifi diyarta mace aka
sa mata sunan Zaliha aminiyar Doctor. Haka rayuwa ta ci gaba da wakana tsakanin Doctor Asma'u da mijinta da yaransu guda biyar.
l_okuta da dama akan ce wai maza basu da tzbbas,
to shi dai Aminu ya ba mara da kunya kuina ya
karyata wannan suna ya wanke miliyoyin maza dan kuwa ya yi wa matarshi Asma'u rikon mutunct sun yl zama na amana, suna tafiyar da
rayuwarsu cikin soyayya, Kaunar su kullum gaba
take ba baya ba. AlkKawarurrukan da ya caukar
tata babu wanda bai cika ba, bashi da wani buri
rayvuwa da ya wuce ya farantawa matarshi Asma'u. Komai ya samu daga ita sai
'ya'yanta, ga
kudi har kudi sun mallaki dukiya ta kece raini, ga wadata suna cikin daula ga arziKin kyawawan
'ya'ya Allah ya basu, ga ilimi da wayewar kai, ga
kuma uwa uba sun gina rayuwarsu cikin soyayya, tsananin Kauna da kulawar da Asma'u take samu wurin maigidanta abin har ya wuce misali, ya hadata ita da 'ya'yanta ya rungume. Koda yake
itama akwai biyayyar aure. Tamat Bi Hamdullah, sai mun hadu
littafina mai suna ALHINI. Daga 'yar uwarku, Kawarku, abokiyarku, antinku, Momin wasu daga cikin, ta ku kullum
Zainabu Abu Lawan Birget (Mrs Lawan Mu'azu) 08029460293.
Har kullum shirye nake da amsa wayoyin makaranta, ina maraba da saKonninku, mu kan so yi mana tsokaci ko sharhi game da rubucerubucenmu muna karbar gyara ko shawara ko
suka mai ma''ana idan an ci karo da kuskure yi mana afuwa, mu ma mutane ne kamar kowa, wadanda bamu wuce kuskure ba, duk dan Adam
ajizi ne, muna jiran ra'ayoyinku.
fhMu hadi littafi na gaba mai suna ALHINI.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels