abinda ze motsa mata da Kishin nata dan yana matuqar sonta da gaske.
Ranar wata Juma'a bayan sun taso daga aiki ya dakkota ze kawo ta gida, suna tafe suna hirar su gwanin dadi dan sosai Balarabe yake ririta Umaimah duk wani abu da ze sosa ranta baya yinsa. Suna tafe sun shiga layinsu kenan aka kirashi a waya da yake wayar na ajiye a tsakiyarsu ne karaf Umaimah taga sunan me kiran 'Wife'.
Wani qululu daya taso mata ta hadiye ta kalli Balarabe da yayi tsilli tsilli da ido kamar wanda aka qure tace "ka daga mana ba kiranka ake ba" ta fada a dake, sosai take kokawa da abinda yake taso mata, so take ta koyi haquri da dauke kan da kullum ake ce mata bata dashi.
Shiru yayi yana aikin rarraba ido ga wayar se qara take dan kiran na katsea wani ya sake shigowa, Tsawa da daka masa akan ya dauki wayar kamar wani danta dan ta kasa riqe bacin ranta, kai Dole ma taci kutumar uban mutumin nan dan ya goge mata hadda iya hadda. Ya yaudareta yace mata matarsa ta mutu nufinsa se ta aureshi sannan zataje ta tarar da wata kome? Ai kuwa da a ranar daga shi har matar sedai suyi kwanan barzahu sedai duk yanda zaayi da ita ayi.
Daga inda take tana iya jiyo muryar matar se shagwaba take masa akan tana jiransa fa yazo ya kaita gidan biki ana rana bazata iya fita ta hau Napep ba, Allah sarki Balarabe zufa yake sharewa kota ina yanda kasan wanda ya zauna akan kunama, magana yake so yayi amma ya kasa se kawai ya kashe wayar ya ajiye yana kallon Umaimah data tsura masa ido kamar me nazarin ta inda zata shaqeshi ta aika shi lahira.
"Kace mun ta mutu, yanzu daga lahirar ta kiraka kenan?" Ta tambaye shi ido ta akan sa, Balarabe ya hadiye miyau qut saboda yanda tayi bala'in yi masa kwarjini nan ya shiga laluban kalaman da ze kare kansa dasu, dakyar ya iya cewa
"Dagaske nake Matata Sumayya ta rasu shekaru uku kenan yanzu, bayan rasuwarta da shekara daya akayi mun madadi da qanwarta da suke uba daya Surayya dukda bana sonta amma haka na karba ko dan saboda Yarana da banida me riqemun su saboda Mahaifiyata ta tsufa bazata iya kula dasu ba, amma ki yarda dani badan ina sonta na aure ba, nayi ne kawai saboda samun mafita, kuma yanzu a shirye nake dana rabu da ita saboda ke"
"Sedai ka saketa ka auri uwarka Balarabe, kuma yanda ka cuceni ka bata mun lokaci ka yaudareni kaima Allah yasa ayiwa yarka, wallahi ko kallon sani ka sakeyi mun se na maka rashin mutunchin da bazaka manta dani ba" ta fada cikin Fushi kafin ta bude motar ta fice, badan tana tsoron karta tijara shi a wajen a jiyota daga cikin gida ranta ya baci ba da wallahi seta masa rashin mutunchin da har ya mutu baze manta da ita ba.
Haka ta shige gida sukuku babu wanda yasan abi da ya faru tasha kukanta a daki washe gari tayi qaryar bata da lafiya dan haka bataje aiki ba.
Kiran gaggawa ta samu daga makaranta akan wasu takaddu basu cika ba na credentials dinta, dole ranar litinin ta debi original din duk wata takadda data san zaa buqata a makaranta ta tafi. Seda ta gama duk abinda zatayi a Academic Office har zata fice daga makarantar tace bari ta leqa Office din Sir Nasir su gaisa saboda anyi zaman mutunchi dashi.
Tun daga bakin qofa tutarensa yayi mata sallama, daga ciki take jiyo muryarsa yanayiwa Nasir din bayani akan abinda bata san ko meye ba. "Kinji Husky voice dinsa Umaimah" Kalaman Nabila suka dawo mata, lokaci daya taji ranta ya baci kamar ta juya se kuma ta tura qofar office din nan rai a hade kamar wadda ta kawo saqon mutuwa.
Nasir da Khalil suka juyo a tare suka zuba mata ido, Nasir ya saki murmushi yace "wata sabon gani, Hajiya Umaimah ce yau a office din mu bismillah shigo mana".
Qarasa shiga ciki tayi ba tareda ta kalle su ba tayi musu kudin goro ta gaishe su, haka kawai take jin haushin Khalil din da bema san abinda take ba se faman doka mata murmushi yakeyi.
"Yar unguwarmu kwana da yawa?" Khalil ya fada yana kallonta, kamar kuwa tana jira ta doka masa uwar Harara harda murguda baki, gani take kamar ma suna tare da Nabilan, qila ma soyya tayi nisa har suna shirin aure.
Jan ta Nasir ya ringayi da hira amma ina hankalinta na kan Khalil daya duqar dakai yana dannan waya yana murmushi, Albishir ne akayi masa, ya samu aiki da wani babban construction company a Lagos interview din yaje kwanaki har Nabila ta ganshi tareda wani abokinsa Taufeeq Babatunde wanda shi yayi masa hanyar aikin da yake Babansa babban mutum ne a Lagos din.
Yanzu yana gaya masa ne cewar comapany sun bude branch a nan Kano dan haka anan ze zauna.
Ita kuwa Umaimah gani takeyi ai da Yammata yake chatting zuciya tayo sama fuu ta fizgi jakarta murya a cunkushe tayiwa Sir Nasir sallama ta fice yana tsayar da ita amma taqi tsayawa.
Dagowa Khalil yayi jin an buga qofa da qarfi yace "lafiya? Me aka mata?"
"Kai zan tambaya dan tunda ta shigo kai naga tana harara da alama ka mata wani abun ne" Nasir ya fada yana dariya.
"Ni a ina zan ganta na wanta wani abu?" Ya fada yana daga hannu sama, Nasir daya miqe ya fara tattara takaddu yace
"Na sanin muku ba naji kace yar unguwarku ba waya sani ko tuni kun jone babu labari"
"Can da dadewa ne naganta a gidan mu an aiketa kai naman suna, ashe sister matar Habib Neighbor din mu ce, shine muka gaisa daga nan sau daya na sake ganinta tare da wadannan qawayen nata masu kalar rashin ji kusan six months kenan fa se yau na sake ganin ta ma ni" Khalil din ya fada cikin son kare kanshi.
"Nifa bance wani abu ba kake koro mun bayani kamar wani Lawyer, muje dan Allah ka sauke ni gareji na dauki motata nasan yanzu an gama gyaran, qarfe hudu zan kai Amir dressing Asibiti" Nasir ya fada bayan daya dauki abubuwan da ze buqata ya nufi qofa. Miqewa Khalil yayi shima yabi bayan sa yana cewa
"Dressing name? Meya samu Amir din?"
"Wallahi qonewa yayi da ruwan tea a qafa amma da sauqi inagadaga yau ma mun gama zuwa" Nasir ya bashi amsa daidai sanda suka isa gaban Motar Khalil din daya siya kwanannan Toyota Yaris Fara me kyau da ita.
Suna tafe yana masa qorafin rashin gaya masa qonewar Amir din suka isa get, rana ta take dan haka ana wahalar abin hawa.
Daga can gefe suka hango Umaimah a rabe fuskar nan kamar hadiri kai kace zata fasa kuka da alama tasha tsayuwa har ta gaji dan a jingine take da bango.
"Ga mutuniyarka can fa inaga ta rasa ride ne" Khalil ya fada yana kallo ta, se Nasir ya waiwaya shima ya kalleta yace
"Kai dai duk inda yarinyar nan take se idon ka ya hasko maka ita, toh ka mata lift ka kaita gida mana tunda hanyar ku daya"
"Bafa hanyar mu daya ba na gaya maka gidan sister tane a layin mu kai ka fiya matsala wallahi"
"Toh kaga daga nan seka gano Asalin gidan su mana ko ni me nace ne" Nasir ya fada yana qunshe dariya. Qarasawa kusa da inda take ya danna mata horn. Hararar da tayiwa motar idan da ace mutum tayiwa se ya kusa faduwa qila, ta qara tunzura baki gaba, ita ba akan titi take ba bare ace ta tare hanya amma koma waye ya kuskura ya qara mata horn seya gane kurensa.
Nasir ne ya sauje glass din bangarensa ya kalleta da murmushi yace "kina tsaye a rana abin hawa yayi wahala koh? Bismillah muje mu rage miki hanya".
Badan gajiya da ranar da ake kwallawa ba da babu abinda ze sa ta hau motar mutumin nan, tana qunquni haka ta bude baya ta shiga, sanyin Ac da qamshin turarensa suka sakata sakin ajiyar zuciyar dole seta qara bajewa tana jan iska a hankali, ta centre mirrow yake kallo ta ta sani amma tayi kamar bata san yanayi ba a ranta cewa take " shi kuma ciwon kallon mata ne dashi qilan.
A hanya Nasir ya sauka suka rabu akan da daddare Khalil zeje gida ya duba Amir din, Nasir ne ya bude mata qofa yace ta koma gaba, ba tayi niyya ba da taso ta mayar dashi Driver ne ya jata ya kaita gida amma ta daure ta sakko ta koma gaban.
Seda ya tsaya a wani guri ya siyo Youghort na L and Z manya guda uku masu Azabar sanyi da ruwan gora kafin suka ci gaba da tafiya. Youghort din ya miqa mata guda daya da ruwa ya ajiye ragowar
"Ban iya cin abinci a waje ba indai ba girkin Hajiyata ba sedai kona matata idan nayi aure shiyasa kullum wuni nake ina shan youghort idan bana gida" Khalil ya fada da son kawar da shirun da sukayi. Seta tabe baki, haka kawai ta samu kanta da cewa
"Amma ka iya zuwa Restaurant a Lagos kaci abinci har ka yi zance da yammata".
Kallon ta yayi cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa yace
"Waya gaya miki naje Lagos?"
"Aljanuna ne suka gaya mun" ta bashi amsa kai tsaye, se ya saki murmushu, tana da tsiwa, kamar a jininta abin yaje hakan kuma kyau yake qara mata daidai sanda suka zo kwanar gidansu bisa kwatancen data bashi tace ya tsaya a nan.
"Har munzo ne?" Ya tambayeta yana gyara parking. Kayanta ta shiga tattarawa tana cewa
"Aa ka sauke ni a nan na qarasa cikin layi, bana so aga ka sauke ni a mota"
"Saboda me?"
"Saboda zaayi mun fada ace waye kai?" Ta bashi amsa a qage, dan bata so wani ya ganta, jiya jiya Mama ta gama yi mata fada akan shige shigen motocin samari kullum da wanda ze sauketa a gida da sunan abokanan aikinta hakanba mutunchi bane yanzu se mutane su chanza mata manufa dukda ita ba wani abu ta aikata ba.
"Mu qarasa, idan kina gudun fada ne zan shiga har cikin gidan na gayawa Mamanku ni na kawo ki bazata ce komai ba" Khalil ya fada yana taka motar ya shiga cikin layin,
"Se kace tasan ka, nidai ka koma baya ka sauke ni kawai dan Allah hakanma nagode" ta fada kamar zatayi kuka, be kulata ba yaci gaba da tafiya bata da zabi ganin yana neman wuce gidan ta tsayar dashi, a gurguje tayi masa sallama ta fice a motar, Layin kamar anyi shara babu kowa saboda uwar ranar data kwalle ta samu ta shige gida, ita kanta tana jin yanda gaba daya jikinta ya game da qamshin turarensa wanda ya kama motar.
Tsakar gidan ma babu kowa se Anty dake girki a kitchen ta rabe daga qofar gurin saboda rana.
"Allah shi qara, baku iyayi masu tausayin miji ba kuka jajibowa kanku girkin ice ai gashinan kuna ji a jikinku" Umaimah ta fada a zuciya, a fili kuwa murmushin qeta tayiwa Antyn harda gaisheta da yi mata sannu da gida ta wuce dakinsu saboda ta hango qofar Mama a rufe qila bata nan.
"Kai Yaya Umaimah turarenki dadi, zanzo dan Allah ki sammun, Salman qaninta ya fada daidai sanda tazo giftashi, tana qoqarin bashi amsa Mama ta shigo gidan da sallama idonta akan Umaimah data duburburce, Addu'arta Allah yasa Maman bata ga shigowarta ba.
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*
*HALIN KISHI*
*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*
*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
Free page 6
Kallo daya Mama ta mata ta girgiza kai kawai ta shige ciki dan akan idonta Umaiman ta fito daga motar Khalil tana tsaye a soron gidan Maman Nana dan ta aiki Nanan tun tuni taji shiru ga babu yaron da zata tura shine tabi sahu da kanta. Ita dai fatanta kullum Allah ya shiryi Umaimah yasa ta ringa jin magana, bata zarginta da aikata wani abu amma wannan shegen rawar kan nata da kwashe kwashen ya isa ya janyo mata magana abinda batayi bama ace tayi.
Umaimah ko dakin su ta shige tunda dai batace komai ba idan ma ta gantan ai shikenan, ruwa ta fara watsawa saboda mugun zafin da ake ta saka doguwar riga me siririn hannu da hula ta nufi kitchen inda Anty take girki, yau Alhamis tasan dole a samu dan farfesun wani abun saboda kusan kowa na gidan yana azumi, litinin da Alhamis din kuwa se Abba ya siyo abinda zaayi romo aci da buda baki duk satin Allah.
Tundaga tsakar gidan kuwa ta fara jiyo qamshin dahuwar nama, ta hadiyi yawu tayi murmushi kafin ta qarasa daga qofar kitchen din ta kalli Anty da ido yayi ficifici saboda hayaqi ga zafin wuta gana gari tace
"Sannu Anty, an abinci ya sauka ne a sammin yunwa nake ji"
Murmushi Antyn ta mayar mata, harga Allah har cikin zuciyarta tana qaunar Umaimah amma a duk yaran gidan babu wanda ya rainata yake mata rashin kunya da diban Albarka irinta duk cikin taya mahaifiyarta kishi wadda ita sam ko a jikinta, tunda aka aurota bazata iya cewa yau ga ranar da Mama Malika tayi mata wani abu da sunan Kishi ba sedai sabani irin wanda kowanne yan Adam suke samu in dai an zauna amma kam maceceme tsananin kirki data kama girmanta haka tsayyaya ce aka yaranta kaf dinsu girmama Antyn suke hatta da Aminu da zasuyi Sa'anni idanya zo gidan yanda ze durqusa ya gaida Mahaifiyarsa haka ze durqusa mata wannan me ido atsakiyar kan ce se Addu'a kuma ita sam halin Umaiman ma ba damu ta yake ba.
Taf ta cika mata bowl da farfesun Naman rago daya ji kayan qamshi yawun Umaimah har tsinkewa yake,
"Ki duba fridge a dakina ki debi Zobo, akwai biredi akan Dining se ki hada tunda shinkafar bata sauka ba" Antyn ta sake fada tana kallonta.
"Nagode" ta fada a fili ta juyaa ranta kuwa cewa tayi "Dole in sha ai tunda da kudin ubanmu kike hada sana'ar dama base kin gaya munba" Ta wuce dakinnata ta bid Frizer da take zuba zobon siyarwa a jarkoki suke sunyi sanyi sosai dan wasu har sunfara qanqara, yaron daya ke daukar mata ne ma be qaraso ba da tuni yanzu qila an gama wawason sa saboda yanda takeyin sa da kyau ga dadi sosai ake rububinsa.
Daki Umaimah ta baje, tana zama aka kawo wuta tayi Hamdala ta kunna Fankar sama data qasa ta shiga dangwalar Romon tana ci da biredi gefe ga L and Z dinta ta cika kofi tana kurba duniya sabuwa ga iskar fanka ta ko ina, bata ji shigowar Mama ba se maganar ta taji a kanta tana cewa
"Kwarai da gaske, baki dafa ba amma kece farkon ci koh? Toh idan kin gama kije ki gyaramun daki" Maman ta fada tana qare mata kallo.
Ajiyar zuciya tasaki dan a zatonta fada maman zata mata tace toh, seda ta qoshi ta kora da zobonta me sanyi ta huta kafin ta tafi dakin maman.
A palour ta tarar da ita da wata baquwa sun baje kuloli masu kyau suna dubawa da alama talla ta kawo mata dan se koda mata su take, gaishe da baquwar tayi ta shige ciki ta fara gyarowa, tana jiyo baquwar tana cewa Maman
"Hajiya na zata saiti bibbiyu zaki dauka tunda yan matan naki biyu ne ko"
"Aa yanzu dai dayan zan dauka ita wannan da saura idan lokaci yayi a siya" Maman ta bata amsa
"Ai kuwa da kin siya kin huta dan kinsan kullum qara kudi kayan suke abinda ka siya dubu daya yau gobe idan kika koma se kiji daya da dari biyar koma dubu biyu, wannan hauhawar fara shi dai Allah ya mana maganin sa" matar ta sake fada. Murmushi Mama tayi tace
"Yanzu dai bari na dauki na dayar da nayi niyya ita ce me garanti, wannan kinsan sau nawa ina mata tarin kayan kitchen? Da takaici ya isheni fitar dasu nayi na rabawa yan uwanta wasu na biki dasu duk randa Allah yasa ta tsayar da hankalinta ta fitar da Miji a kaita da abinda ya sawwaqa"
"Allah dai ya rufa asiri, in sha Allahu ma tareda yar uwarta zaki saka su a Lalle".
Baki Umaimah ta tunzura gaba, wayasani ma ko irin wadannan maganganun da maman take a kanta ne suka hana mijin tsayuwa ita kullum me laifi ce a idon Maman, Allah dai ya yanke mata ta tafi itama kowa ya huta a sannan zaa gane amfaninta ai.
Haka ta gyaro dakin ta wanke Bandaki tsaf lokacin matar sun gama ta wuce se Maman ita kadai tana waya da wanda yake kawo mata Manja daga Kudu da yake tana siyar da Manja da Mangyada, hannun kujera ta nema ta zauna tana jiranta harta gama.
"Ya akayi?" maman ta tambayeta,
"Na gama gyara ciki saura nan"
"Toh bismillah mana ko na hana kine" Maman ta sake fada, seta miqe ta shiga tattare kwalayen tace
"Ina zaa ajiye wadannan kayan toh"
"Saka su can dakin" Maman ta nuna mata dayan dakinta data mayar dashi na aje shirgi Wanda da Su Umaimah suke ciki kafin Yayyensu suyi aure su koma dakin da suka bari na tsakar gidan. Bude dakin tayi ta shigar dasu,
"Mama duk kayan can Yaya Nuratu zaa jibgawa su? Toh Allah yasa dai ta samu gidan da ze dauka koda yake ma gidan quaters ne ai kin ma san yanda suke sedai idan an a tafi dasu a dawo da wasu a san dai kin mata kaya da yawa kawai" Umaiman ta fada tana kade kujeru, da kallo kawai Maman take binta, a ranta tana nema mata shiriya daga gurin Allah dan lamarin nata kullum qara gaba yake.
Bata damu da shirun da Maman tayi ba taci gaba da cewa
"Qilama ni da bakya ta tawa na fita samun babban gida, kinga lokacin ai a tasheki a tsaye ki rasa yanda zakiyi"
"Allah baze hanani yanda zanyi ba dan ubanki keda bakinki sam besan abinda ze fada ba, fita ki bani guri na fasa gyaran daman idan baki yi niyyar abu ba se kin san yanda kika jangwalo aka ce ki barshi" Maman ta fada kamar zata kai mata duka, Dariya ta sheqe da ita ta shiga cewa
"Haba Hajiyar mu easy mana, nifa wasa nake miki. Yo ko yanzu aka ce a fito Hajiya ai a shirye kike Allah dai ya bar manake Hajjaju".
Ganin da Mama tayi tana neman mayar da ita wata abin tsokana yasa ita ta bar mata dakin ta koma tsakar gida inda inuwa ta dan fara sauka suka shiga hira da Anty Saratu.
Umaimah ko tas ta gyara dakin ta goge ta saka qamshi, tada zafin nama idan ta saka kanta ta iya aiki sosai dan wannan horon Mama ne duk yaranta seda ta tabbatar da ta horasu yanda duk inda sukaje bazata ji kunya ba, daman Umaimace me son jiki a ciki, amma idan ta tashi yin aikin kuma zatayi shi dakyau.
Dakinsu ta koma ta kwanta kafin rana tayi tana so taje kitso, tana hawa kan gadon wayarta dake jikin chaji ta fara qara, kamar bazata daga ba se kuma ta janyo ta ta amsa kiran ba tareda tayi magana ba.
"Amincin Allah ya tabbata a gareki" Aka fada da muryar da tanaji ta gane waye, murmushi ne ya kufce mata,
"Tareda kai, ina fatan kaje gida lafiya?" Ta bashi amsa.
"Ban sani ba, da kin so kiji aike zaki kirani ba se yanzu dana kira zaki tambayeni ba" Khalil ya fada daga dayan bangaren,
"Thats remind me, a ina ka samu number na?" Umaimah ta fada tana gyara kwanciyarta da kyau akan Gadon,
"Baqauya kawai, wayace miki har yanzu ana tambayar ina aka samu number budurwa ne"
"Ni ba baqauyiya bace" ta fada a sakalce tana tura baki, akan me zece mata baqauya, ita da take yar tsakiyar birni bama shi dan bayan badala ba.
"Toh yi haquri yar birni" ya fada yana dariyar yanda tayi maganar kafin yaci gaba da cewa,
"Dadin tuqina ya saka kin manta da folder credentials dinki, kinga da a commercial car ne da yanzu se ki tafi gidan redio cigiyan wanda ya tsinta".
Dafa baki Umaimah tayi tana tashi zaune tace
"Subhanallahi, wallahi na manta shaf kuma ban lura ba. Dase nazo daukar wani abun sannan ne zan ga babu su"
"Daman kinji tuqin babban Driver ina zaki tuna" ya sake fada cikin sigar tsokana, seta mayar masa da cewar
"Babu wani nan, bayan nama fika iya tuqin kanayi a hankali kamar me tsoron hanya"
"Oh haka kike ce? Toh next time idan mun hadu za'a gwada se muga wanda yafi wani iyawa"
"Allah ya kaimu zan kuwa baka mamaki" ta fada cikin tabbatarwa bayan a zahiri inda ake takawa ma mota tayi tafiya bata sani ba, ba kuma dan babu inda zata koya ba Aa koda basu da Mota a gida banda ta Abbansu amma Yayyenta mata masu aure kowacce nada motar hawa, ita dan karambanin nan ma yasa ta hau bata taba ba tafi gane ta kame a kujera a jata.
Hira suka danyi kafin ya mata sallama da cewar idan ya samu dama zuwa dare ze kawo mata, idan kuma bezo yau ba se dai zuwa Litinin dan washe garin juma'a zeyi tafiya zuwa Dutse akwai aikin da sujeyi acan kuma se ranar Lahadi ze dawo.
Wannan waya da sukayi ba qaramin nishadi ta saka Umaimah ba, ta ringa walwala, su kansu mutanen gidan seda suka ringa tambayarta Albishir din me ta samu da take farin ciki haka sedai tayi murmushi tace babu komai.
Be kawo mata a daren ba, ai kuwa baqin ciki ya mata dirar mikiya ya shafe walwalar data wuni a ciki dan tun magriba ta fesa wanka dukda batayi kwalliya ba amma ta saka kaya da suka qara haska tah tayi fes, shiru har akayi isha babu shi babu kiran wayarsa tun tana zuba ido qarshe se jiyo radion da Abba ya kunna tayi a tsakar gida ana wani shirin siyasa da yake ji qarfe Goman dare.
Ita kadai ta ringa zuga tsaki tana juyi a gado, kamar ta kirashi amma in ta tuna daman ya gaya mata ba lallai yazo a yau din ba se ta Kanne, yanzu har se ranar litinin zata sake ganinsa kenan? Wannan abu ya mata ciwo da yawa.
Haka ta cinye weekend gashi ko a waya be kirata ba, sundai yi magana ta whatsapp ta saka status ya duba suka gaisa daga nan be sake ce mata komai ba.
Ranar Litinin bayan magriba suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shiga
"Wai ana sallama da Umaimah a qofar gida" yaron ya fada, se tayi tsam daga abinda takeyi ta kalle shi. Wane dan rainin hankalin ne ze aiko sallama da ita? Tasan dai duk masu zuwa gunta se sun kirata a waya shi wane isashshen ne haka da ze aiko ba tareda tasan da zuwan sa ba.
"Kaje kace ba ta nan" ta fada se Mama tayi saurin dakatar dashi tana hararta tace
"Je ka tambayo wane ne kace tana zuwa"
"Mama fa ni bamuyi da kowa ze zo gurina ba kawai se a aiko kice ace ina zuwa indai mutumin kirki ne ai seya fara sanar dani kafin yazo" ta fada kamar zatayi kuka dan tasan tabbas baze wuce irin yan yawar samarin nan masu bi gida gida suna sallama da yammata ba.
Banza Mama ta mata taci gaba da lazumin da takeyi, sega sallamar yaron ya sake dawo yace "wai Khalil ne, kuma yace sauri yake yi kizo ki karba saqon".
"Khalil?" Ta fada a fili tana kallon yaron kamar shi ze bata amsa kafin ta shiga qarewa kanta kallon, Zani ne da T shirt a jikinta tunda tayi wanka da La'asar ta sakasu se qaurin manja takeyi saboda suyar wainar fulawa take a lokacin. Miqewa tayi ta nufi daki, Mama da tunda akace Khalil ta zuba mata ido tana so ta tuno ina ta taba jin Umaimah ta ambaci sunan tana tunanin Umaiman ta fito ta chanza kayan jikinta zuwa baqar doguqar riga ta yafa mayafinta,
"Mama bari na karbo, credentials dina na manta ranar a makaranta shine ya kawo min" ta fice da sauri.
Su biyu ta gani tsaye jikin mota sunsha kwalliya kamar masu zuwa gurin daurin aure,
"Allah yaso