Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
lailayo a zuciyarta ta dire kafin ta dora da cewa "Ranar nan yace Rabin jiki yar uwarsa ce yau kuma Jinin jiki?" Hannu da suka gaisa akan idon ta ya qara ingiza wutar abinda take ji, lokaci daya idonta ya kada yayi jajir taji kamar jiri na neman dibanta daga zaune lokacin da taji wata mata na cewa "Oh wannan qauna da shaquwa ta Khalil da Jamila an girma amma suna nan kamar lokacin yarinta". Miqewa tayi, dakyar take daga qafarta Nuratu tayi qoqarin kama mata hijab amma ina tuni ta fincike tayi waje gaba daya yan dakin suka rakata da ido. "Ko jikin nata ne ya motsa?" Khalil ya fada yana kallon Nuratu, ta gyada kai dakyar tana hadiyar yawu dan ita tasan ba jiki bane sedai idan Baqin HALIN KISHIN nata ne ya motsa, Khalil ya fita da sauri yana cewa "Bari na dubata, idan jikin ne se mu ga likita a nan ya sake dubata" yayi waje da sauri ya bi bayanta. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 9 Hangota Khalil yayi ta doshi hanyar waje yabi bayanta da sauri kamarta sani ta qarawa tafiyarta sauri, cikin sassarfa ya bita ganin har ta kusa isa gate din Asibitin ya daga murya yana kiran sunanta amma bata juya ba jefa qafunta kawai take tana tafiya, ji take ina ma data rufe ido ta bude zata ganta a gida tsabar yanda ta tsani Asibitin da Duk wadanda suke ciki sa. "Umaimah meye haka ne kina ji ina kiranki ina zakije ko jikin ne ya tashin miki?" Khalil ya fada bayandaya tararda ita yasha gabanta. Wani shegen kallo ta watsa masa, yanda ya ke washe baki yana riqe da hannun wannnan matar ya dawo mata seta kauce shi taci gaba da tafiyarta ya qara tare ta cikin fada fada yace "Wai ke meyasa kike haka, ina miki magana shine zaki wuce kici gaba da tafiya ina zakije? Idan wani abun ne ya faru ki gaya mun mana se muje na kaiki" "Allah ya kiyeye na sake shiga motar ka kaje dai kaci gaba da diban wadancan jakan marasa kamun kai da kake kulawa, tsabar rashin kunya a gaban uwar data haife ka da sauran mutane kake kama hannun wata qatuwa kuna dariya" "Jamilar ce baki sani ba? Meyasa idan wulaqancinki ya tashi se kin nemi abinda zaki cimun mutunchi ko yan uwana?" Ya fada yana kallonta cikin ido saboda yanda kalmar Jaka data alaqanta da yar uwarsa. Seda ta harare shi kafin tace "Toh dan Jamila ce se aka ce ku tsaya kuna iskanci a gaban mutane" "Iskanci Umaimah, nine nake iskancin?" Ya sake katseta yana nuna kansa da yatsa. Dauke kanta gefe tayi tana qunquni qasa qasa wanda tsaf ya jita "toh idab ba iskanci ba menene zaka wani kama mata hannu a tsakiyar mutane ita kuma se wani murmushi take tana yaqe haqora" ta fada. Seda Khalil ya hadiye malolon baqin cikin daya taso masa zuciyarsa tana ayyana masa rashin dacewarsa da wannan mara kunyar yarinyar qarara. Dakyar ya iya bude baki yace "ki jira na yiwa Nuratu magana ta fito na mayar daku gida" dan ko babu komai shi ya dakko su daga qofar gidansu kuma seda Abba ya jaddada akan su dawo da wuri dan haka dole ya mayar dasu daga baya ze zauna ya yankewa kansa hukunnci akan ta, dan ya fara hango dalilan da suka saka har mutum uku fasa auranta, sannan yaga tasa wautar qarara da yake qoqarin daukar ta ya kaita nasa gidan. "Ni? Ai wallahi bazan shiga motar ka ba ita dai da bata da zuciya taje ta zauna seka maida ita amma ni kaga tafiyata, kuma ka qaddara daga nan gurin babu ni babu kai kaje can cikin yan uwan naka ka auri daya idan zaka iya" Umaimah ta fada cikin tsananin rashin kunya kafin ta murguda masa baki tareda baza Hijabinta da yake har qasa ta tafi ta barshi a gurin kamar wanda aka dasa. Dakyar ya iya jan qafafunsa da sukayi sanyi ya koma dakin, yana shiga suka hau tambayarsa ina take lafiya dai? Ya rasa me zece musu ga tunanin maganar data fada masa da ke neman ruguzashi haka ya daure ya tattaro yawun bakin sa yace "Amai ne ya taso mata, gata can A mota Nuratu muje na mayar daku gida tace akwai sauran magungunanta da bata gama shanyewa ba". Nuratu da duk ta tsargu dan tun fitar sa wata daga cikin matan ta fara qananun maganganu akan taga wani kallon wulaqanci da Umaiman ta watsa musu kafin ta fita, aka samu wata ta goyi ganin zasu tada hayaniya Hajiya ta tsawatar musu, ita dai tayi tsuru, Jamilan ta zauna kusa da ita tana janta da magana amma ta kasa amsawa se murmushin yaqe kawai take tasan Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a wajen nan, Allah yasa kar tayi rashin hankalin nata data saba ta tarawa kanta mutane har magana ta dawo dakin su samu nayi shigowar da Khalil yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya dukda a kallo daya da tayi masa ta gane akwai matsala Umaimah tayi tsiyar, yana cewa ta tashi kuwa ta miqe tana qara yiwa Hajiya Addu'ar samun sauqi ta fice. Dama bata saka ran ganin Umaimah a waje ba tasan kuma shima ya fada ne kawai dan haka suna shiga motar tun kafin yayi magana ta kalle shi tace "Dan girman Allah Khalil kayi haquri, Al'amarin Umaimah se Addu'a se tayi abu kuma daga baya tazo tana nadama" "Gaskiya I'm sorry to say amma Nuratu sam yar uwarki bata da tunani, could you believe ni ta kalla ta kira da dan iska a matsayina na mijin da zata aura? Ba tun yau ba take fada mun maganganu marasa dadi amma ina mata uzuri sedai naga a kullum a maimakon abin ya rage gaba ya ke qarayi. Beside me nayi mata? Saboda kawai na gaisa da yar uwata shine ya bata damar da zata gayamun maganganu haka har tana fadin babu ni babu ita naje cikin yan uwana na nemi wata na aura me yake damun Kwakwalwar Umaimah? Ko kuma daman wannan rashin hankalin shine zafin kishin da take cewa tana dashi?. Indai haka ne na godewa Allah daya nuna mun ainihinta tun kamin na aureta na aurar wa kaina damuwa, kuma banga laifin duk wadanda suka fasa auranta a baya ba saboda sam Umaimah ba macen aure ba. Macen da zata iya tsayawa a gabanka ta gaya maka duk maganar datazo baki ta ba tareda tayi shayi ko taga qimarka ba ai ba matar aure bace, dukda ma dai ta fada da bakinta babu ita babu ni Allah yasa hakan shi yafi Alkhairi, ki shiga ciki idan Abba yana nan kiyi mun sallama dashi dan Allah tunda wuri gara mu sama ma kanmu sauqi Allah ya hada kowa da rabonsa" Khalil da yau zuciyar yan maza ta motsa masa ya fada daidai sanda ya tsaya kofar gidan su Umaiman. Ido kawai Nuratu ta saka masa tasan gaskiyar sa ya fada amma bata fatan yar uwarta ta rasa nagartaccen Namiji irinsa, shi kadai ne take tunanin ze iya chanza Umaiman gashi tun ba'aje ko ina ba shima ya sare da halinta yana zancen fasa aure. Bude baki tayi dakyar tace "Kayi haquri Khalil nasan halin Umaimah sam idan ranta ya baci bata sanin me take fada..." "Ranta ya baci da akayi mata me? Saboda na gaisa da yar uwata? Yayata ce fa uban mu daya. Haka kwanaki tayi mun saboda Jalila ta kirani twin sister na, ta ringa zagina har tana kirana da Mazina ci. A lokacin nayi mata uzuri a lokacin amma banda Yayi da babu wani abu da bata sani a kaina ba. Yan uwana mata babu wadda ban gaya mata sunanta na nuna mata hotunansu ta yanda ko a hanya suka hadu zata gane su ba. Saboda gudun bacin ran Umaimah na chanza layin da nake harkokin kasuwancina dasu. Ba dan ina tsoro ta ba, kamar uwar data haifeni duk sanda ta raya mata zata ce nabata wayata tayi bincike ban taba nuna mata rashin jin dadi akan hakan ba ko babu komai waya sirfi ce nima ina da sirrikana da ya kamata ni kadai nasan dasu amma ko mai da ko ina na bata damar shiga ta duba a wayata, hakan ne ya bata damar da zata tsaya ta zageni duk a sunan kishi? Kishi ko hauka? To nidai na haqura taje kawai Allah ya bata wanda ze iya da halinta" Khalil yayi saurin katse Nuratun a fusace dan ransa qara baci yake yi duk idan ya tuna maganganun data yaba masa. Bude baki tayi da niyyar sake magana ya bude motar yana cewa "kije dan Allah, ki bar Abban ma duk randa na sake biyowa nan haka nazo. Ki bawa Mama haquri nasan babu dadin amma hakan shi kadai ne abinda ze sama mun maslaha dukda ina son Umaimah amma bazan iya auranta ba, a waje tayi mun haka inaga na aureta na kai cikin gidana kinga wannan kome tayi ni na siya da kudina". Jiki a mace Nuratu ta fita daga motar daidai sanda Adaidaita ya tsaya a qofar gidan Umaimah ta fito daga ciki, kallo daya tayi musu daga Nuratun har Khalil din kafin ta maida ido ta kan Nuratu tace "kuma da kika shiga motarsa ke kadai Allah ya isa bazan yafe ba, idan ma Amana aka ci mutum yaje shida Allah" ta sake fada tana kallon Khalil kafin fuuu ta shige gida. Murmushin zallar takaici Khalil ya saki, ya fara hasashen yarinyar nan bata da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ko kuma dai saitin kanta na gocewa ne lokaci lokaci. koma dai yaya shidai he is done with anything concerning Umaimah, yana sonta amma dole ya haqura da ita dan beyi zaton Rigima da Hayaniyarta da Nasir ya ke fada ba ya kai haka. Koda yake ya so ya rufe shi ne amma banda haka ai kaitsaye kawai kamata yayi yace masa tana da matsalar saiti. Gata dai mace har mace amma babu cikakken hankali Allah kenan me yanda yaso. Haka ya juya Asibiti bangarorin zuciyarsa na mahawara da juna, tabbas yana son ta so me tsanani amma menene amfanin soyyar da babu kwanciyar hankali da girmamawa a cikinta. Idan ya tuna yanda take riritashi tana lelen sa idan suna yar dadi se yaji kamar baze iya rabuwa da ita ba, amma abinda tayi masa dazun ya saka shakku a zuciyarsa game da auranta. Tayi kishi da yan uwansa na jini inaga kuma duk randa tsautsayi yasa ta ganshi da wata, bama wannan ba ita rayuwa bata da tabbas. Har zuciyarsa bashida burin ajiye mace sama da daya musamman ace Allah ya cika masa burinsa ya bashi mace irinta amma babu wanda yasan gobe, idan qaddarar sa ta auran mace sama da dayan ce fa yaya zasu kaya? Yanda yanzu kullum ya kunna radio labarai ne marasa dadi akan mata sun kashe mijin ko sun kashe kishiyar toh maganin kar ayi kar a fara, indai soyayyace ze roqi Allahn daya saka masa ita a zuciyarsa ya cire masa ita kuma ze ci gaba dayi mata fatan Alkhairi ubangiji ya rage mata abinda yake damunta a zuciya amma tabbas baze siyawa kansa tashin hankali da kudinsa ba amma ta yaya ze tunkari Hajiya da wannan magana yanda take son Umaimah kamar ta goyata? Bama wannan ba, gaba daya fa auransu befi sati hudu masu zuwa ba anya idan yace ze fasa yaya iyayenta zasuji dan shi su yafi tausayawa, mutanen kirki, Mamanta ta dauke shi kamar dan cikinta basu boye masa komai akan Umaimah ba tun fara zuwansa gurinta dan hatta da takaddun Asibitin gwajin kwakwalwa da aka mata seda Abba ya nuna masa amma sam shi be fahimci Al'amarin ba, be taba zata haka abin nata yake ba se yanzu da tafiya take qara nisa daman hausawa sunce Hali zanen dutse ashe lokaci take jira ta fara zayyano masa su, toh koma dai menene ze jira a sallami Hajiya ta koma gida kafin yaje mata da wannan maganar. A can gidan su Umaimah kuwa rigima ce sosai ta sarqe tsakaninta da Nuratu dan tsayawa tayi daga cikin Gareji Nuratu na shiga ta hau kanta da kokawa itama batayi wata wata ba kuwa ta zage suka fara kwasar dambe dan a zuciye take da lamarin Umaiman, tayaya zatayiwa kanta asarar miji kamar Khalil wanda tasan muddin ta rasa shi bazata maida kamar sa ba sannan rantsuwar Abba ta bada ita sadaka ta tabbata kenan. Dambe sukeyi haiqan har cikin gida sosai kuma Nuratun ta zage tana jibgar Umaimah dan ko a qirar jiki zubinsu ba daya bane. Nuratu doguwa ce me garin jiki dan ta ninka Umaiman da tsabar tsaurin ido ne ma ya sakata cukumarta da dambe. Sosai ta lallasata, dan takaicin shekara da shekaru ta samu dama tana sauke mata shi yau akayi sa'a babu kowa a gidan dan suna fita ba dadewa akayi rasuwa a bayan layi dab haka su Mama da Antyn sun tafi Jana'iza se Salis ne kadai a gidan Dan Anty na biyu da suke sa'anni da Umaiman, shi kuwa yana leqowa daga dakinsu yaga abinda yake faruwa ya koma ciki harda turo qofa. Yaya Aminu ne yaje gidan, tundaga waje yake jiyo ihu da kururuwar Umaiman tana zagin Nuratu a ransa yace "abin ya motsa kenan, ai kuwa yau zaki ci ubanki daman ina da cikin ki ai" se ya juya ya koma motarsa. Dorinar da yake ajiyewa saboda horon yaran sa idan ta kama ya dakko har wani murmushi yake yana hasaso irin dukan da ze mata kafin su Mama su dawo dan sunyi waya ta gaya masa sunje jana'iza amma gasu nan zuwa. Yana shiga kuwa beyi wata wata ya shiga sakar musu duka kan me uwa da wabi saboda yanayin daya tarar dasu gaba daya kowacce jikinta na buqatar ya gaya mata. A zabure kuwa suka rabu kowacce ta hau sosa jiki dan dukan ya shige su musamman da daman rabi kaya rabi tsirara suke dan tun a Get aka tuge Hijabai da dambe yayi dambe kuwa aka ringa farke farken kaya. "Ashe baku da mutunchi a cikin gidan kuke mana kokawa se kace wasu yan tasha?" Ya fada a fusace yana kallon yanda kan ko wacce yayi buzubuzu kamar sababbin kamu se sosa inda ya tsula musu bulala suke, jikin bango suka maqale kowa tana sosa jiki, ya sake kallon Nuratu yace "Harda ke ina miki kallon me hankali ashe zama da ita yasa kema kin koyi hauka ko? Uban me ya hada ku fada?" Ya daka mata tsawa, se Umaimah ta fashe da kuka tace "Wallahi Yaya babu abinda nayi mata kawai ta hau ni da duka..." Bulalar ya kai mata duka da ita tayi azamar gocewa ta fada dakinsu da gudu tana masa Allah ya isa a zuciya. Kan Nuratu ya juya ya shiga surfa mata masifa uffan batace ba har yayi shiru dan kansa kafin ta miqe ta shige dakin Mama dan tasan idan ta shiga nasu Umaimah na ciki tabbas fada be qare ba shi kuwa Yaya Aminu samun su zeyi kamar jakai ya lafta. Baafi minti sha biyar ba kuwa su Maman suka dawo, Aminu ne ya fada musu abinda yazo ya tarar se a sannan Salil ya fito daga daki yace "Umaimah ce da laifi dan ta riga Yaya Nuratu shigowa ta labe a bakin qofa se ji nayi sun kaure da dambe". "Ai ko baka fada ba daman nasan itace da tsokana amma itama Nuratu da laifinta akan me zata biye mata har suyi dambe se kace wasu qananan yara" Maman ta fada. "Ki qyale su Allah ya taimaki wata yarinya ta sake mana dambe a gida wallahi se jikinta ya gaya mata dan se nayiwa mutum mugun duka a gidannan" Aminu ya fada, daki Mama ta wuce yabi bayanta bayan sun gaisa da Anty. Nuratu na ganin Maman ta saka kuka, babu bata lokaci ta zayyane mata duk yanda akayi a Asibiti da abinda Khalil ya gaya mata a hanya harda dalilin yin damben nasu. "Ai shikenan" Mama data gama saurarenta ta fada tana miqewa tsaye, Allah kadai yasan abinda taji a zuciyarta se kuma wanda Ubangiji ya jarabta da fitinanniyar yarinya irin tata. "Ai kuwa sena ci ubanta yau a gidan nan, kuma bata isa ba a wannan karon ta sake lalata magana tunda naga abinnata ya zamana tsantsar iskanci tana da buqatar a dawo da ita kan hanya" Aminu ya fada afusace yana miqewa shima se Mama tayi saurin dakatar dashi da cewa "Karka kuskura ka taba ta, baka ji abinda akace bane shima yaron yace ya fasa toh ka barta zaman gidan nan ne ko gata gashinan. Kuma kar naji zancen a bakin wani koda mahaifin ku ne kuwa, idan sunzo da kansu sun janye a lokacin ya sani. Amma Umaimah koh idan har ta bata wannan auran bazata maida kamarsa ba" ta qarasa maganar cikin rawar murya tareda daga kanta sama a qoqarin ta na dakatar da hawayenta daga zubowa dan daman daga yanayin muryarta suka gane kuka ne yake neman zuwar mata abinda ya qara sanyayawa Aminu da Nuratu jiki. "Dan Allah Mama karkiyi kuka, kin sani hawayen ki masifa ne a tattare da ita addu'ar dai ita zaki ci gaba dayi mata in sha Allahu wata rana se labari" Aminu ya fada sedai kamar me jira kuwa kukan ya kwace mata tace "Na gaji, nagaji Aminu da halin qanwarku. Kullun ta Allah da zullumin ta nake kwana nake tashi a raina, yanzu idan aka fasa auran nan karo na hudu fa kenan me kake zato mutane zace a kanta? Ni kadai nasan irin qunci da baqin cikin nake fama dashi akan lamarin auranta yanzu ina murna yan satittika suka rage ta tafi shine ta ja gwalo abinda ze saka a fasa ko ai shikenan" tana gama fada ta shige daki tana ci gaba da matsar hawaye. Nuratu dake nata hawayen a zuciyarta tana dana sanin sanarwa da Maman, amma tasan dole zata ji, kuma ita a nata dabarar ta fada mata da wuri ne saboda idan da yanda zaayiwa tufkar hanci ayi se gashi ta sake lalata al'amarin. "Indai junin mutum munafunci dason ya hadani da uwata sedai abinsa ya qare masa in sha Allahu badai aga bayana ba sedai mutum yaga nasa, kuma aure na babu fashi duk baqin cikin mutum" Umaimah da basu san da tsayuwarta ba ta fada tana jijjiga jiki irin na tsabar fitsara da rashin kunya, Aminu ne ya yunqura kafin ya tarar da ita ta kwas ada gudu ta koma dakinsu harda sakawa qofa sakata dan tasan a yanda ya zaburo tabbas ya riqeta toh ko be kasheta ba se tayi dogon Suma. Zama tayi akan gadonta gaba daya kuma seta rasa sukuni, hawayen da ta gani a fuskar Mama sun daga mata hankali dan ita ba jahila bace ba kuma mahaukaciya bace tasan illar da hakan ze yi mata wai me yasa a kullum itace sanadin Kukan Mama? Bama ita kadai ba duk wanda ya tashi qorafi a gidan akanta ta fita zakka a cikin su goma sha uku da aka haifa a gidan. Iya qoqari kuma tanayi gurin kaucewa duk abinda zaace tayi ba daidai ba amma sau tari ma tsokanarya akeyi idan ta maida martani kuma ace tayi laifi, ko kuma su dauki damuwar data shafeta su dorawa kansu kamar yanzu da wannan munafukar Yaya Nuratu taje ta fadi qarya da gaskiya ita sam bataga abin tayar da hankali a ciki ba. Aure ita ce me auren nan ko maza ashirin suka fasa auranta mijin tane bezo ba hakan kuma baze hana shi zuwa ba sannan maganar Khalil da tace ta fasa wasa takeyi bacin raine kawai yasa shima kuma tasan haka ne idan an barsu daga nan zuwa dare ma zasu shirya kansu amma shine Mama zata dauki damuwa har tana zubda hawayenta. Tsaki taja tareda gyara kwanciya, tana so ta koma dakin ta bata haquri amma tasan muddin wancan zalimun na gidan ta kai kanta mahallaka ne gara ta bari se ya tafi, haka ta ringa juyi a gado hankalin ta sam yaqi kwanciya, yanzu fa idan Maman tana can tana ci gaba da kuka ai se tashin hankulan su mata yawa, ga abindatake ciki ga Hawayen uwa ita ina zata saka ranta? Miqewa tayi ta bude qofar,gara taje idan ma kashe ta Aminu zeyi sedai yayi din amma seta je gurin Maman, tana zare sakatar kuwa ta jishi yana yiwa Anty sallama, dakatawa tayi har tajiyo qarar bude qofar fita kafin tayi wuf ta shige dakin Maman Nuratu na durqushe gabanta tana ci gaba da bata baki bayan Aminu ya gama nasa ya tafi ta shiga, kallon banza suka aikawa juna kafin ta tattare fuska tana kallon Mama tace "Yanzu Mama kawai dan anzo an gaya miki qarya da gaskiya shine zaki ringa zubda hawayenki a kaina bayan kinsan abinda hakan ze iya janyo mun? Duk fa qaryace kawai baqin ciki ake mun dan an ga na samu wanda nake so yake sona anga kwana biyu muna zamab lafiya dake babu wani abu shine ake so a hada mu"ta qarasa tana Harara Nuratu da ta dauke kai dan yanzu tayiwa Maman Alqawarin bazata sake biye mata suyi fada ba amma badan haka ba seta sake gurje bakin yarinyar nan ta nuna mata banbancin dake tsakaninsu. "Idan daidai kikeyi Umaimah kin sani in ma akasin haka ne duka keta shafa, babu abinda yayi mun zafi da sabgarki duk yanda kika ga dama kiyi ba kuma zan sake bata raina akan abinda ya shafe ki ba in Allah ya yarda. Na kuma godewa Allah da ya saka bake kadai na haifa ba kinga idan kin sakani baqin ciki ina da wasunki da zasu sakani farin ciki dan haka kije kiyi duk yanda kimaga yayi miki rayuwarki ce ba tawa ba" tana gama fada ta miqe ta shige bandaki ta barta a tsaye dan daman tuni Nuratu ta fice itama daga dakin. Jiki a sanyaye ta koma dakinsu, kan gadonta ta kwanta tana tunani. ita da kanta ta san tana jawo mutane da yawa ciwon kai amma ya zatayi haka Allah ya halicce ta bata da ikon canza kanta (kodai kika mayar da kanki ba). Wayarta ta janyo ta shiga neman layin Khalil, badai duk akan auransa ne Mama take wadannan maganganun ba bari ta kirashi, da dai tayi alqawarin se tayi sati bata amsa wayar sa ba idan ma yazo gida bazata fita ba amma yanzu saboda farin cikin Mama da kanta zata kira shi ta bashi haquri, ita azo kawai ma ayi abinda za'yi idan ta kama wannan Juma'ar ma a daura musu aure kawai idan yaso duk randa aka a Shirya ayi bikin shikenan dai ta wuce gorin Mama da tsoron ko wanne lokaci ana iya fasa auran ta. Tana can tunani wayar dake ta faman ringin ta katse, sake kira tayi nan ma baa dauka ba seda ta jera masa kira goma amma ko daya be daga ba na qarshe ma rejecting yayi kafin aka kashe wayar ma gaba dayanta kamar yanda Computer ta sanar mata sanda ta sake kira Tayi sororo da waya a hannu tana kallo, tunda take dashi bata zaton ta taba masa kira biyu, duk sanda ta kirashi kome yake ze dakata ya kirata dan baya dagawa sedai ya kashe ya kira, ba qaramin abu yakeyi ba da ze saka ya kasa daga wayarta. Idan ma yana da wani uzuri me muhimmanci tun kafin lokacin yana sanar mata dan kar ta kira bata same shi ba amma shine yau tayi masa missedcalls 10 be daga ba bayan tasab

Chapter 8 of 9