Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
babu abinda yakeyi yana Asibiti gurin Hajiya ko ya tafi gida ya huta. 'Qila ma yana can tare da wannan Jamilar har yana jinhaushi dan an tabata wai yar uba amma sun wani daukaketa kamar ciki daya suka fito' ta raya a zuciyarta, a fili taja tsaki dan ita abinda yasa ta qara tsanarta kenan kasancewar ta ba ciki daya suka fito dasu Khalil din ba. Haka kawai ta bata musu lissafi su kuma sun wani jata a jiki kamar uwarsu daya gaba daya ita kam bata ga dan uban da zata hada kai dashi ba, dan Kishiya ne fa. 'Idan kuma da gaske Nuratu take da tace Khalil din yace ya fasa auranta fa dalilin daya saka yaqi daukar wayarta har yayi rejecting tareda kashe waya gaba daya?' Zuciyarta ta sake raya mata, seta miqe zaune babu shiri ta dafe qirji, Khalil ya fasa auranta tabi ina taga haske Jama'a??? PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA πŸ‘‡πŸ» 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYARπŸ₯°πŸ‘Ή (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 10 Last free page Tun Umaimah na daukar abin wasa har ta fara shiga rudanin rashin sanin abinda Khalil yake nufi da qin daga kiranta. Raba dare tayi tana kiran wayarsa, ya kunna amma haka zata qaraci qara ta tsinke ba tareda an daga ba, ta tura masa da SMS sunfi nawa shima babu amsa, WhatsApp kuwa idan ta tura saqon ma baya tafiya tsabar rudanin da ta shiga bata san ashe Datar ce bata kunna ba. Kafin safiya idanunta sunyi zuru zuru kamar wadda ta kwana tana zawo saboda rashin bacci da damuwar data kwana a ciki. Tana idar da sallar Asuba ta sake gwada kiran layin, call waiting aka gaya mata. Qirjinta ya buga Dam har seda ta saka hannu biyu ta dafe wayar ta subuce daga hannunta. Tun haduwar sa dashi a irin wannna lokacin tasan da ita kadai yake waya, ze kirata idan ya tashi sannan idan ya dawo daga masallaci ze sake kiranta zuwa gari yayi haske kafin suyi sallama toh dawa yake magana yanzu? Ta tambayi kanta. Wayar ta dakko ta sake danna kiran layinsa, still yana waya cikin sa'a ringing biyu taji ya daga da sallama, seda ta saki wata ajiyiyar zuciya kafin cikin karyewar zuciya ta kira sunansa tace "Khalil, me nayi maka? meyasa kaqi daga wayata tun jiya daga baya ma ka kashe wayar gaba daya?" "Am kinga Umaimah ina wani important call ne yanzu kiran da kike tayi yana diverting attention nawa shiyasa na daga ki bari idan na gama zan kiraki" Khalil ya fada daga daya bangaren kafin ta sake cewa wani abu ya datse kiran se kawai ta cire wayar daga kunnenta ta bita da ido kamar zata ganshi a ciki, ita yau Khalil ya kashewa waya. Tagumi tayi hannu bibbiyu gaba daya kwakwalwarta ta cunkushe ta kasa samun damar yin wani tunani, me tayi masa da ze dauki zafi haka? Ita dai a saninta indai akan abinda ya faru jiya ne beci ace yayi fushi me yawa har haka ba indai ba kuma daman yana neman hanyar da ze wulaqantata bane tuntuni amma meye abin daukar zafi anan. Bata san tsahon lokacin data dauka tana tufka da warwara ba seda ta jiyo muryar Mama daga tsakar gida tana kwala mata kira tayi firgigit ta miqe ta fita. Kallo daya Maman tayi mata bayan data amsa gaisuwarta ta nuna mata inda kwanukan wanke wanke suke tace "Ga wanke wanke da shara nan, ki dama kunu kafin a kawo markaden qosai, da wuri Abban ku ze fita sannan za'a kai gidan rasuwar can" tana gama fada ta juya abinta ta bar Umaimah a tsaye kamar wadda aka dasa. Wanke wanke, shara, suyar qosai duk ita kadai? A cire shara da suyar qosan ma dai a duniya abun data tsana yabi bayan wanke wanke kuma kowa yasan da wannan musamman irin na gidansu da yake da mugun yawa kamar kwanukan gidan biki. Ta waiwaya ta kalli kamfacecen tsakar gidan nasu dayayi kaca kaca da ganyayyakin bishiya da qasa saboda iskar da akayi cikin dare jiya wannan kafin ma ta gama ai bayanta ya karye wai ma ina su Nazifi da Arma da suke aikace aikacen tsakar gidan shine za'a ce ita zatayi yau? Yaushe rabon ma da a raba aikin gidan da ita tunda ta shiga Higher institution dan idan ma an sakata ba zatayi a dadin rai ba daga qarshe ma aka dena cewa tayin sedai idan yan hankalin suna kanta taga Maman na aiki ta karba ta qarasa shine yau za'a dawo da abinda ya wuce. "Au kina tsaye tun dazu ko babu abinda kikayi? Ai shikenan ki bari Alhajin ya fito baki hada abin karyawa ba zakiyi bayani" Mama data sake fitowa cikin shirin fita ta fada tana kallonta. Tsintsiya ta dauko ta fara sharar kamar mara laka a jiki ba tareda ta tankawa Maman ba daidai lokacin Anty Saratu ta fito daga dakinta suka gaisa da Maman ta juya tana kallon Umaimah tace "Aa, Umaimah ce da shara yau kuma ina su Arman tun dazu fa naji motsin shigowarsu, nima yau baccine yafi qarfina wallahi se yanzu na samu na miqe" "Na basu markaden qosai sukai, bari naje Yusuf na jirana a waje Rabi'a aka kai Asibiti haihuwa yanzu Yaya ta kira take gayamun babu kowa a wajenta" (Rabi'a yar yayarta ce da suke uba daya). "Toh se kin dawo Allah ya raba, idanan gama abin karyawa a biyo ku dashi" Anty ta fada tayi hanyar kitchen tana ci gaba da cewa "Bari toh na dora ruwan kunun kafin su kawo markaden, Allah ma ya taimaka ruwa be sauka ba jiya yanda aka baje itacen nan a waje da yau mun gayawa aya zaqinta". Har Maman taje qaramar qofar fita daga gidan ta juyo tace " Saratu karki kama mata aikin nan, ita zatayi komai zuwa anjima idan ban dawo da wuri ba ki bata abinda za'a dafa na rana tayi" ta juya ta fice daga gidan. Hawayen takaici ne suka zubowa Umaimah wato da wannan uban aikin za'a horata kenan? Ai wallahi gara kullum a yi mata bulala goma akan wannan uban shara da wanke wanken gidanga qarin girki da itace, ina zata tsoma ranta wai? Ba'a bar mutum yaji da abinda ya dame shi ba za'a rikito masa da wani bala'in. "Halan wani laifin kika mata ko Umaimah?" Antyta fada taba kallo ta amma yanda kasan da dutse tayi magana haka tayi,bata damu ba ta shiga hada murhu ta dora ruwan zafi kafin ta dakko qullin kunun ta shiga damawa daidai sanda Almajiran suka kawo markadan qosan, Wanke wanken tace suyi, sega Abba ya fito daga dakinsa da waya a kunnensa. "Kai kuje abinku idan an gama abinci ku dawo ku dauka, daga yau kun bar aikin nan har zuwa sanda za'a ce ku ci gaba" Ya fada yana kallon su Nazifin, suka tsame hannu daga kumfar da suka kada tareda daurayewa kafin suka fice daga gidan. "Wai Alhaji ya haka ne? Ya zaka hana su yin wanke wanken bayan kasan aikinsu ne yanzu waye zeyi?" Anty ta fada bayan data dakata daga buga qullin qosan da takeyi. Ba kiji Abinda Malika tace bane da zata fita? Ga wadda zatayi nan. Kema ki tashi daga wannan aikin kije ki hadamun ruwan wanka da wuri zan fita" yana gama fada ya juya cikin daki abinsa. Umaimah ta kalla da tayi mutuwar tsaye da tsintsiya a hann, ta fara murnar Allah ya kawo mata dauki dan sharar da takeyi kadai jin bayan ta take kamar ze cire inaga ta kama sauran ayyukan se ga Abba yazo da wannan zancen kuma. Rau rau tayi da ido tana shirin fashewa da kuka Antyn tayi saurin dakatar da ita da cewa "Karma kiyi asarar hawayenki bari naje na same shi wannan wane irin abu ne? Itama Maman banda abi ta ina ita ina saka Amarya aikin wahala ku da ya kamata yanzu ku qara hutawa kafin a fara gyaran jiki idan wani abin kikayi ai hanyoyin horo da yawa ba lallai seta wannan hanyar ba. Ina baze ma sabu na ace za'a sakar miki wannan uban aikin ke kadai dole da sake" ta goge hannu ta ta wuce dakin Abban tana ci gaba da mita. Karon farko da Umaimah taji yau Antyn ta mata abin arziqi dan ko babu komai ta nuna tausayawa akan ta abinda uwa da uban da suka haifeta basu mata ba. Sharar taci gaba dayi tana share hawaye, a kan window ta ajiye wayarta yabda da Khalil ya kira zataji qara amma har sannan bataji ko qarar shigowar saqo ba ga wannan sabon bala'in da taje ciki kuma haka ta qarasa sharar ta kwashe, Ruwan kunun ya tafasa har sannan kuma Antyn bata dawo ba, tasan halin Abban sarai dan haka sahunta a likafa gara tayi abinda zata iya kafin ya fito ya nemi abin kari, ruwan ta sauke a garin juyewa ya dan zubo mata a qafa saboda gaba daya hankalinta baya kan abinda take yi ta kuwa saki qara ta wancakalar da tukunyar a qasa tana yarfe hannu tareda sosa inda ruwanya zuba. Daga cikin daki inda Anty da Abban suke dauki ba dadi suka leqo a tare, da sauri ta qaraso gurin tana cewa "meya faru? Badai qonewa kikayi ba?" Umaimah babu bakin magana se kuka take tana yarfe hannu, Anty ta dubi Abba daya ja ya kwafe a a tsaye tace "Ka gani ko gashi nan haka kawai kun jawo ta qona qafarta, fisabilillahi Alhaji me yasa kake haka? Duk fa abinda Nasiha da Addu'a basuyi maganin sa ba duka ko aikin wahala bazeyi ba. Yanzu gashi nan tun baa je ko ina ba ta qona qafa ta yaya kake zaton zata iya da aikin gidan nan ita kadai? Ko mu din da muke yi ai muna da mataimaka ballantana" ta ci gaba da mita dan itama gwanace a fannin kafin ta debo qulli ta zuba mata akan qafar bayan data tofa mata Addu'a tace "Tafi ki zauna haka kawai da safiyar nan an jawo miki" "Ruwan bada yawa ya zuba ba ba? Ko zamuje a duba mata qafar?" Abba ya fada yana kallo ta, se Umaimah ta girgiza kai har sannan tana hawayen tace "Aa Abba baze tashi ba tunda Anty tayi mun tofi, anjima se naje gurin Ya'u me Chemist ya bani magani" "Allah ya sawwaqe" ya fada tare da juyawa dakinsa. Umaimah ta dingisa ta dauki wayarta ta shige daki, seda ta wanko qafar a Bandaki kafin ta zauna kan gadonta tana sauke ajiyar zuciya fa ruwan kadan ne ya dan zubar mata, yanda abin yazo mata a bazata ne ya sakata sakin tukunyar ta fake da hakan ne kawai saboda ta samu mafita gashi kuma Allah ya fiddata. Number Khalil ta danna zata kira sega kiran sa ya shigo cikin azama ta daga tareda fashe wa da kuka kamar wadda aka cewa Mamanta ta mutu. Be ce mata qala ba ya barta tayi iya yinta, abinda ya ringa qarawa kukan nata qaimi shirun da yayi mata, ta saba idan tana so ta daga masa hankalo kawai zata kirashi ta fasa kuka shi kuma ya ringa lallashi da banbaki kenan har se tayi shiru amma yau yana jinta yai buris da ita dan kanta tayi shiru kafin tace "Wai me nayi maka Khalil kake Azabtar dani haka? Kasan yanda nake ji kuwa? Ko so kake se zuciyata ta buga na mutu sannan zaka yarda da sonka ya gama yi mun illah?" Daga bangaren Khalil dake zaune a office dinsa ya rufe ido ya dafe kansa da hannu daya, shi kadai yasan wahalar daya sha daga jiya zuwa yau saboda rashin magana da ita, gaza jure ganin tana kira baya dagawa yayi abinda ya saka ya kashe wayar gaba daya kenan daga baya kuma ya kunna ya sakata a cikin drawer kawai dan juriyarsa ta kusa qarewa. Yanzun da take wannan kukan jinsa yake kamar ana masa yayyafin ruwan zafi, ita take kukan shi yake jin zafin abin a ransa amma yaya zeyi? Umaimah bata dace dashi ba. Dole ta qarfin tuwo ya yakiceta daga ransa in har yana neman zaman lafiya a rayuwarsa amma yaga abin da kamar wuya dan ji yakeyi wutar son ta tana qara ruruwa a zuciyar sa a maimakon tayi qasa. "Khalil Khalil kana jina kayi shiru" Umaimah ta fada abinda ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kenan, gyaran murya yayi yana jin wani na taso masa akan abinda yake shirin aikatawa amma yasan shine kadai gatan da zeyi musu daga shi har ita, "Umaimah duk wannan drama da kike yi ta mecece wai? Kin manta irin zagin da kikayi mun jiya da irin kalaman da kika gaya mun? Kefa kika fada da bakinki babu ke babu ni na fita daga sabgarki to me kuma kike so nayi miki yanzu?" "Duk abinda na fada maka bacin rai ne ya saka, kasan yanda nake sonka nake kishinka wallahi Khalil idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na kashe kaina tsabar baqin ciki kuma duk abinda na fada maka ba daga zuciyata bane kawai raina ne ya baci amma ba da gaske nake ba" Umaimah tayi saurin katse shi. Se yayi wani dan murmushi kafin yace "Bacin rai se ya saka hankali ya gushe kuma? Sannan Kishi ya rufe miki ido kin kasa banbance yan uwana da sauran Mata, idan kinyi haka akan yar uwata ta jini da babu aure a tsakanina da ita Umaimah me ze faru kuma duk randa kika ganni da wata daban, kinga komai yana iya faruwa kenan. Bazan iya saka rayuwata a cikin matsala ba, zan aureki ne saboda ki yi daidai da tsarina ina sonki ina kuma samun farin ciki a gurinki bansan wannan rashin hankali shi kike kira da kishin da kika ce kina dashi ba, a ban aureki ba kin zage ni saboda wata kinga kuwa idan mu kayi aure tsaf zaki iya neman rayuwata dalilin wannan baqin HALIN KISHIn, Se yanzu na gano ainihin abinda ya saka sauran samarinki fasawa nima Allah ne ya soni da rahama ya kawo faruwar hakan da qila watarana ina bacvi sedai kawai na farka na ganni a lahira dalilin abinda bansan mafarinsa". "Allah ya tsareni da kashe ka, ina sonla Khalil dana rasa ka gara na rasa raina, dagaske zanyi fito na fito da duk wadda tace zata shiga tsakanina da kai amma bazan taba bari wani abu ya shafi lafiyarka ba, zan kareka da iya kar kulawata, zan baka farin ciki har qarshen rayuwata saboda kai din kaine Rayuwata" Umaimah ta fada tana fashewa da wani sabon kukan daya ke jinsa har cikin ransa, so yake yace tayi haquri ta dena amma ya rigada yayi making mind di sa akan tarayyarsu ba kuma ya son wani abu da ze karya masa lago, ko wannan doguwar maganar da suke yi ji yake kamar ze rasa qarfin guiwarsa. "Wallahi Khalil ina sonka, idan kace zaka barni rayuwata zata shiga cikin garari, zan iya rasa raina idanka rabu dani saboda na rigada na saddaqar maka da ruhina. Nayi maka alqawari zan zama me maka biyayya bazan taba tsallake umarninka ba, bazan sake tayar maka da hankali akan wani abu ba zan shanye komai saboda farin cikinka koda hakan yana nufin yankewar numfashi na saboda na sani wata rana kishinka ze iya zama ajalina" Umaimata sake fada cikin wani irin kuka me tsuma zuciya da ya saka jikin Khalil daukar rawa, a maimakon ya samu nutsuwa da kalamanta sema qara shiga rudu da tashin hankali yakeyi, tabbas yana son Umaimah ko yace yana Qaunarta, amma ita a nata bangaren wannan ya zarce Love sedai a kirashi da Obsession. "Umaimah ki dena kuka haka, kiyi haquri amma bana tunanin zamu rayu tare, wannan tsananin kishinda kike dashi a kaina ze iya zamar mana tangarda a cikin rayuwar auranmu saboda a kullum zuciyarki zata ringa raya miki abubuwan da ba haka suke ba, kinga kuma ke yanda kike handling bacin rai, bana so muyi abinda wata rana za muzo muna dana sani. Ina sonki amma bazan iya auranki ba, Kiyi haquri muyi Addu'a Allah ya hada kowannen mu da Alkhairinsa" Khalil ya sake fada abinda ya janyo tsayawar ji da tunanin Umaimah na wani lokaci, sedata kwashi kusan minti biyar shi kansa A nasa bangaren seda Numfashinsa ya rage sauri na wasu sakanni kafin yaci gaba, jiran amsa yake daga bangarenta amma yaji shiru, har ya yi tunanin ko Network ne ya dauke yaji yo ta tana magana cikin wani irin sauti me kama da wadda kw komawa da numfashinta tace "Khalil daman ka shiga rayuwa ta ne saboda kaga bayana? Waya turo ka? Me nayi wa wani daya zabi hukuntani da irin wannan hukuncin me tsanani, kasan yanda Sonka ya yi wa zuciyata illah? Ka qaddara a ranka Khalil tunda na rasa ka babu wata mace data isa ta rabeka, yanda zanqare rayuwata babu aure kaima haka idan kuwa har kayi gigin kula wata to tamkar ka siya mata tikitin tafiya lahira ne dan kuwa sena kasheta, muddin ina numfashi sena kashe duk wata Mace data shiga cikin rayuwarka. Saboda ni aka halicce ka babu macen data isa ta ratsa zuciyarka bayan ni, idan kuma kana ganin wasa ne ka gwada Khalil, ka gwada kula wata mace wallahi sena ga bayanta" ta qarasa tana sakinwani siririn kuka daya saka Khalil zabura ya miqe dan tunda ta fara magana hankalinsa yayi qololuwar tashi, kafin yace wani abu ta kashe wayar. "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" yake maimaitawa yana zagaye office din, dukda kasancewar Ac a kunne take amma zufa ce take keto masa ta ko ina kamar wanda yake naquda, wannan shi ake kira da anyi gudun gara an tadda zago. Shi daya ke neman rabuwa da ita saboda gudun tashin hankali gashi ya gayyatowa kansa babban tashin hankalin daya shallake na da. Kisa fa take iqirarin yi akansa kenan shi kansa tasa rayuwar a cikin hadari take, idan har zata kashe wata saboda shi toh shine ze zama target dinta na farko kenan yanzu yaya zeyi? Meye mafita? Zabi biyu gare shi a yanzu, kodai yayi jahadi ya auri Umaimah ya siyi tashin hankali da kudinsa ko kuma ya barta ta zama barazana ga rayuwar duk wata mace da ze kula, duk cikin wadannan zabin kuma babu wanda yake jin ze dauka dole akwai wata hanya bayan wannan, dole ya nemawa kansa mafita daga Tarkon Umaimah. End of free page Domin jin yanda zata kaya tsakanin Umaimah da Khalil Ku hanzarta biyan 500 dinku zuwa Asusun 8142548705 Opay Maryam Farouk Seku tura shedar biyan zuwa ga 07061838488 Yanzu ma aka fara wasan, Littafin Halin kishi yazo muku da sabon salo tareda tabo jigon da yake jijjiga mata a halin yanzu, ina me baku tabbacin bazakuyi nadamar bibiyar labarin Umaimah ba, kudai ku hanzarta biyan kudin karatun ku se naji ku πŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎ PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA πŸ‘‡πŸ» 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *(NADAMAR UMAIMAH)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* πŸ™ŒπŸΌπŸ™ŒπŸΌ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9