Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bar su dai suna ta kalle kalle lungu da saƙo tare da bin kowa na gurin da mugun kallo. Ɗai daga cikin su ce wadda kamar ta fi su tsaurin ido ta furta a yatsine. " Wai dama nan gidan matsiyatan ne ai gwanda kusan na yi, Maganar Auren Nadiya da Sayyid yake ko uban wa babu ta,mun soke ta,Babu zancen,Mai za'a yi da ɗan gidan Talaka talakan ma malamin islamiyya da basu iya komai ba sai zaman Aji da tara gemu,kunga yarinya zubin masu kuɗi,duk dangin ku, shine zaku nace har dake tsohuwar banza algunguma " Takai ƙarshen zancen tana nuna mahaifiyar ta Sayyid da take da tabbacin itace Tsohuwar Angon. Cigaba da magana ta yi " to bari kuji wannan saƙon na uwar Amarya ne,dan haka tun wuri ki kira ki tsaida yaron ki dan idan ba haka ba rayuwar shi zata Shiga galari,Zai kai kan shi ga halaka,gwara ma tun wuri ku janye batun ku dan mun fi ƙarfin ku,har abada babu mu babu haɗi da Jinin talaka,wannan saƙon Uwar Amarya ne,kuma wannan baku ga komai ba idan har ya kasance baki dakatar da hakan ba ". Mtswwa wadda ke zuba rashin mutuncin taja tsaki dai dai tana kai ayar zancen nata. Sai dai basu ko kai da fita ba suka ji timm ba kowa bace kuwa ta faɗi face Mahaifiyar Ya Sayyid kasancewar tana da Bp inda ta ke ya motsa har yayi Sanadin kai ta ƙasa.Wani abun mamaki kuma mutanen nan har suka gama masifar su babu wanda ya iya tanka musu kamar duka an rufe bakunan su. Haka suka yi kan ta ganin abun ba na lafiya bane dole aka kwasa akayi asibiti da ita.A lokacin ne kuma aka kira mahaifin Ya Sayyid ɗin aka sanar dashi abinda ke faruwa wanda ta sa dole suka bar gurin suka bar masallacin gaba ɗayan su suka yi asibiti daga chan kuma jin abinda ke faruwa Ya'yan na su ya zartar da hukunci kasancewar shi mai zuciya dan ta motsa sosai. Duk yadda ya Sayyid abun ke son taɓa zuciyar shi ya ƙi bashi dama kasancewar duk abinda suka faɗa an zayyane masa zuciyar sa ta sosu matuƙa lamarin ya tayar masa da hankali zuciyar shi har wani irin rawa take yi na ɓacin rai ta gefe ɗaya kuma wata irin ƙaunar Nadiya ce ke ƙara taso masa kamar ana ƙara masa gishiri bai taɓa tunanin son da yake mata ya kai haka ba sai yanzu da yake ganin ya rasa ta har abada Dan shi kan shi bazai taɓa komawa ba da sunan neman Auren ta har abada duk soyayyar da yake ji kan ta zai haƙura ya bawa zuciyar shi natsuwa,Wani irin hawaye ya share masu ɗimi wayen da bai san lokacin da suka fito masa daga tsayen da yake cikin ɗakin na sa bayan dukkanin abokanan sa sun gama masa jaje. wayar sa ya janyo ya danna kira da numban da yayi saving da Nady wanda sai da ya gama ƙare mata kallo domin shi ya san cewa a yanzu ba ya da hurumin kiran ta kasancewar ya samu labarin An ɗaura ma ta Aure da Tanim wanda ya ƙara tabbatar masa da komai shiryayye ne anyi shirin wulaƙan ta sa ne sai dai ya san cewa iyayen maza basu da sani kan lamarin.Numfashi ya sauke yana ƙara kafe wayar ta sa da idanun sa.Bugu biyu ba,a ɗaga ba sai a kira na uku sannan a ɗaga kiran cikin yar hargowar dake tashi. " Hello ". Wadda ta ɗauki wayar ɗai daga cikin ƙawayen Amarya ta furta. " Ina mai wayar,?Idan tana kusa ki bata ". Ya furta a tsanake fahimtar ba Muryar ta ba ce. Kallon wayar tayi ganin numban babu save kafin kuma ta mere baki ta ta tashi ta na matsawa inda Nadiya take zaune wadda ke cikin farin ciki bakin ta har kunne Ansha ado kamar ka sace su ka gudu an sha make up.Farin cikin ta cikar Wani buri na ta da ya cika daga cikin burikkan ta na farko ta zama matar mai kuɗi surukar mai kuɗi da sauran burikkan na ta da Allah ne kaɗai masanin su. Shiru tayi tana kallon ƙawar Tata da ta kara mata wayar tana furta " Ban san kowa ye ba numban babu suna ".Ganin Nadiya ta ɗan mata alamar wane ne. Mere baki tayi tana juya idanun ta kafin ta furta. " Ɗan wahala ne zaki ce mini ".Ta furta inda Takai ƙarshen zancen tana sakin Murmushi domin ta san an kai ƙarshen game ɗin. Ya Sayyid dake sauraren ta kuwa Idanun sa ya runtse da ɗan ƙarfi cikin abubuwa biyu da suka mintsini zuciyar sa da suka sanya jikin sa wani irin yin sanyi wanda duka wayen nan zantukkan sun tabbatar masa da bashi da wani matsugunni a zuciyar ta,kasancewar a cikin kunnen sa komai ya shiga. Numfashi ya sauke yana jin zuciyar sa na masa wani irin zafi kafin ya furta. '' NADIYA ".! Jin tana furta " Idan zaka yi magana kayi magana, Nasan dai ka zauna Islamiyya idan ma baka zauna ba ka saurara A redio,Maganata da kai ma Haramun ne yawwa saboda ayanzu ni mallakin wani ce ta sa ta har abada,ta shi shi kaɗai ". " NADIYA ".! ya ƙara ambatar sunan nata jin bata amsa masa ba sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya a hankali jin ta amsa masa ciki ciki.Inda ta amsa tana yatsine yatsine tare da juya idanun ta kamar yana gaban ta.Daga ƙasa kuma tana jan guntun tsaki wanda ya sauka cikin kunnen sa. " Na yarda Komai muƙaddari ne daga lillahi,Ni na san dama chan ke ba rabo na bace,Amma ki sani duk wata zaluntar da kuka mini Na yafe Miki sai dai abu ɗaya bazan iya yafe Miki ba NADIYA shine,Zagar mini mahaifiya da kuka yi, Bazan ce dole sai kun bata haƙuri ba.Dan bana buƙatar hakan.NADIYA Allah ya gani naso ki ne saboda Allah,Na Ƙauna ce ki saboda Allah tun kafin ki kai wannan girman a yanzu kuma na san kin san da hakan,kuma ki sani har yanzu babu abinda ya ragu daga ciki.Ina son ki,ina son ki NADIYA,ina Miki fatan Alheri Allah ya baki farin ciki mai ɗaurewa a cikin gidan ki na gode da karɓa kira na da kika yi,sannan ƙofa a buɗe take a duk lokacin da kike neman neman taimako na zan Miki in Sha ALLAH,sai wata rana. ". Yana gama zancen na sa ya kashe wayar ta sa tare da goge numban ta gaba daya daga wayar sa.Da duk wani abu da ya shafe ta yana jin zuciyar sa na masa babu daɗi kamar ya saka kuka. Jiki a mace ta zuba ma wayar idanu wadda ta zaro yanzu kasancewar jin shirun da tayi.Jikin ta ne yayi sanyi ƙalau sai dai kasancewar tana cikin wani irin farin ciki sai ta hana hakan yin tasiri a gare ta sai ma hararar wayar da ta cigaba da yi tana jan tsaki tare yin yan Dan gale dangale inda ta samu kan ta da yin saving numba ta sa ƙalau wanda bata san ma ta aika ta hakan ba sai da ta ga ta ta saka a icloud storage nata sannan ta ga abinda tayi da sauri kuma ta goge wadda ke kan simcard ɗin.Saboda haka kawai zancen sa na ƙarshe ya ɗan yi tasiri sosai a gare ta.Tsakin da ya fi na farko tare da miƙawa ƙawar Tata wayar.Inda aka Cigaba da tsokanar ta kamar yadda ƙawayen ke yi musu. Dukkanin su a gidan Hajiya Samira Suka yi taron na su.Raliya Kaɗai ce tayi nata a nan maƙwabtan su. A ɓangaren NAJIBA itama ta sha ado kamar Nadiya dan kwalliyar su bata da banbanci sai dai ta ɓangaren sutura kowa lifaya ya saka sai dai da Ban daban wanda kuma aka kawai sai ta samu kan ta da faɗuwar gaba shi yasa ta koma gefe duk yadda ƙawayen na su ke tsokanar ta,sai ta kasa yin wani dogon motsi sai dai kawai ta yi guntun Murmushi tana bin su da idanu ga wani irin son ganin mahaifiyar ta da take ji yana taso mata tana son ta rungume ta ta mata kuka ta share mata hawaye.Wani irin rawa zuciyar ta ke yi kamar ta yi kuwwa kowa ya jita. Ta samu salamar abinda take ji. Ina dangin Angwaye,Jamil,Tanim, Ibrahim ?Ku fito muje ɗaukar Amare Nidai Ina gefen Tanim na NADIYA.😂😂💃💃💃💃💃mu zamu je bikon Nadiyar mu tare da team ɗina.💃💃 WASAN YANZU AKA FARA.✍️ Daga Alƙalamin✍️ Fa'eehbg ✌️ 08069059746👇 Ƙarin bayani. https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ P.14 Bayan taron ɗaurin Aure ya watse kuwa bayan kowa ya watse ne sai a lokacin Malam Abdul basiɗ dake jin kan sa na sara masa tun bayan gama ɗaurin Auren Ya ɗan rufe idanun sa da suka yi masa wani irin Nauyi. Malam Rabu'u kuwa shima dake kallon sa bai iya cewa komai ba haka ma su Malam Adamu da suke cike da jimami basu san ya'a kayi komai ya wakana ba da yardar su ba.Sai dai mai aukuwa ta auku. A hankali ya ɗan buɗe idanun sa da suka ɗan sauya ya furta a hankali " Allah ya basu zama lafiya,Tabbas bamu da iko sai abinda Ubangiji yayi,kuma hakan ne dai dai,Allah Mungode maka ". Amin su malam Rabu'u da su Malam Amiru suka amsa cikin Tausayin sa domin kowa ya san yadda suka samu labarin halayen Tanim ɗin ko wane uba mai hankali da mutunci bazai iya Aurawa yar sa miji irin Tanim ba. A ɓangaren Jamil kuwa fuskar sa yau kamar gonar Auduga haka yake ta wasar baki tare da ƙara godewa ubangidan na sa da ya shige masa gaba akan komai dudda da rancen kuɗi shine wanda yayi masa da duk wata hidima.Haka ya kasance cikin farin ciki A lokacin irin na sabon ango mai cike da shauƙi a ransa da muradi na kasancewar sa da anar son sa. A ɓangaren mahaifiyar ya Sayyid ta farfaɗo inda take ta saka mahaifin sa ɗaura masa Aure da wata yarinya nan yar maƙotan su,yarinyar kirki.yar Matashiyar ta Dan kaɗan Raliya zata girme mata bare ma akai ga su Nadiya,duk da ba wata tserewa a tsakanin su. Hidimar bikin ta cigaba da kan ka ma anan gidan suma basu fasa komai ba.Haka hidimar ta cigaba da tafiya yadda ya kamata.Haka itama Raliya take gudanar da nata hidimar tare da kawayen ta tasha a do itama gwargwado idan ka ganta baka isa ka kushe ta ba duk da kayan su Najiba sunfi tsada da kyau Amma sai ta yi wani irin sharr da ita kasancewar babu make up a tattare da ita sai ainahin kyawun da Allah ya zuba mata. Bayan shuɗewar wasu awanni... Ta kowa ne gefe ana ta shirin kai amare gidajen na su inda dan gin Tanim duk da yadda suke ta sakin magana haka suka karɓi Nadiya da malam Rabi'u da Adamu suka kaita.Sai wasu daga cikin ƙawayen Hajiya Samira dana Mama Hafsatu.Wanda kuma zuwan su ya ɗan sai ma Nadiya girma Dan duk da habaice habaicen na su da suke yi kamar abun dole sun koma yin ƙus ƙus ganin fuskokin su Hajiya Samira da ƙawayen ta babu wasa. Kowa ya jinjina ma irin daular da Nadiya ta shiga duk da kowa ya ɗan fahimci kamar dangin mijin basu wani karɓe ta ba.Ganin yadda gidan yake cinjim da da manyan motoci gashi wani irin gida na alfarma na masu idon nera. Nadiya ta sha kuka idanun ta sunyi jazir musamman A.lokacin da iyayen Maza ke musu Nasiha da Addu,a Babu ma kamar Nasihar mahaifin ta dan mahaifiyar ta bata yi mata ko Addu,ar ba ko huɗuba sai faman matsar ƙwalla da take yi na rabuwa da tilon yar ta. Haka sukayi mata sallama suka wuce kasancewar itama Najiba su zasu wuce gidan na ta yanzu,wanda Malam Abdul basiɗ ya kai ta da kan shi.Wanda kuma suna da tabbacin Mama Hasiya bata bada yar ta haka ba.Haka kuwa akayi koda suka tafi sun isko wasu daga cikin maƙotan su da kuma abokanan arziki haka itama suka yi ta santin gidan nata kasancewar dukkanin su mazajen na su sun ce sun yafe kayan ɗaki Raliya kaɗai akayiwa Wanda duk da haka Mama Hasiya bata yarda ba sai da ta bata wasu kuloli haka masu kyau kusan guda biyar wayen da ta saye dan ta. Haka suka fita gidan da santin sa suna yiwaa Amare fatan Zaman lafiya. Haka aka watse aka bar Najiba na ta kuka babu abunda ke dawo mata arai face huɗubar mahaifiyar ta wanda kuka ya ci ƙarfin ta ya hanata ƙara sa sauraren huɗubar sai yanzu ne kuma komai ke dawo mata sabo tana ƙara jin tausayin mahaifiyar ta ta da kuma yar uwar ta da ta haɗa su guri ɗaya ta musu Nasiha mai ratsa zuciya wanda ita kan ta Mama Hasiya tana Dannewa ne kawai, kai daga ninta kasan Karfin hali ne take yi,rabuwa da ya ya biyu ai ba wasa ba duk da ba wani mugun wuri bane guri ne na ibada Amma akwai kewa musamman su da ke da wata irin shaƙuwa da mahaifiyar ta su kamar yadda itama Nadiya take da Tata. A ɓangaren Raliya ma wasu daga cikin dangin su na Jigawa su ka rakata bayan Malam Amiru yayi mata rakiya da kuma malam Abdul basiɗ da ya kaita da kanshi har ɗakin ta bayan gama yi mata huɗubar. Sun kai ta ɗan madaidaicin gidan ta dai dai gwargwado na talaka gida ne madaidaicin wanda ya ke ɗauke da daɓe da filasta mai tsari shi yasa ko ina ya ke ta ɗan fidda haske kasancewar ya kunna mata Ingin da ya aro ga wani abokin su.Dan asamu haske a wannan ranar. Raliya taci kuka sosai kamar yadda Najiba ta sha kuka dan zan iya cewa nata yafi karfi ma saboda da ƙyar aka ɓangare ta jikin ta mahaifiyar ta aka fita da ita dan atafau cewa tayi ta fasa Auren abarta gurin Ummar ta sai da akayi da ƙyar sannan aka fito da ita kafin a ka damƙata ga malam Amiru suka mata huɗubar sannan suka fice da ita daga gidan gaba ɗaya.Haka kuwa dangin Ibrahim suka karɓe ta cikin mutunci da girmama juna. Kamar yadda aka watse aka bar yan uwan ta hakan ce ta kasance da ida ita itama cikin abinda bai fi mintina biyar ba gidan ya koma tsiff sai kukan injin da ke iske mata.Hawaye ta share masu zafi kafin ta ƙara shigewa akan ɗan madaidaicin gadon nata ga wani irin tsoro na shigar ta haka kawai sai kuma kewar mahaifiyar ta da tafara ɗawainiya da ita da ta yar uwar ta, tana cikin wannan tunanin taji zance ƙasa ƙasa tare da muryar maza haka sai dai da alama ba da yawa suke ba. Ibrahim ne ya shigo fuskar shi kamar farin alkuki ya ƙara yin haske sai murmushi da fuskar ke fitarwa na farin ciki.Bayan yin sallamar sa wadda ta amsa masa ciki ciki saboda Muryar ta data fara disashewa ya furta " Ki sauko muje falo ". Babu musu kuwa ta fara ƙoƙarin saukowa tana sauko ya riƙe hannun ta suka fice tare. Jin hannun ta ana shi sai da ya ɗan daburtar da ita sai dai tana tuna huɗubar mahaifiyar ta sai ta samu kan ta da yin laƙwas dan so tayi ta janye dan wata irin Kunya ke kama ta haka kawai da Tsoro. Tun zaman su gurin take jin muryoyin da take zaton abokan sa ne suke tsokanar ta Ibrahim na kare ta sai dai ko kan ta bata ɗaga ba bare cire mayafin haka suka yi musu nasiha sannan suka yi musu Addu,ar zaman lafiya kafin suka ajiye masa ledar da suka shigo da ita wadda ke shaƙe da kayan this thing.😋 Suna fita kuwa bayan ya raka su ya dawo bayan rufe gidan murmushi yayi ganin tana nan inda ya ajiye ta da a lama bata ko motsa ba bare ta nuna alamar tashi sai hakan ya ƙara Mishi ganin wata irin ƙimar ta ya ƙara fahimtar cewa yayi mata domin ya san bazata taɓa tsallake umurnin sa ko ta taɓa wani abu na sa da sunan wofintar wa ba.Haka ya riƙo hannun ta suka kama hanyar bedroom ɗin ta bayan ya rufe ƙofar ta Falon da kashe haske. Suna shiga ya zaunar da ita kan gadon yana yaye mayafin ta a hankali tare da zuba mata idanu yana sakin murmushi tare da furta " Amincin Allah ya Tabbata a gare ki Mar atussaliha,gimbiya ta,Ya Al arusa,Mai kyawun asali,yau dai gaki a gidan Jarumin ki Ibrahim ". Murmushin da bata yi niyyar yi ba ta sauke tana ɗago kan ta tana zuba masa idanun ta masu haske da suka rikiɗa saboda kukan da tayi, saboda taji daɗin Kirarin da yayi mata ta kuma tabbatar da irin ƙaunar da yake mata wadda take ƙara gode ma Ubangiji na samun kamar shi duk da basu zauna ɗin ba kowa ya ga yanayin rayuwar kowa take ta zaman takewa duk da Kowannen su nada hope na samun rayuwar farin ciki ga ɗan uwan sa. Shima murmushin yayi sai kuma tausayin ta da ya ƙara dabaibaye shi ganin yadda idanun ta suka kumbura. " Kuka ki kayi har haka MY RALIYA " . Ya furta yana ɓata fuskar sa ganin wasu hawayen sun silalo mata akan kyakkyawar fuskar ta.Mayafin ya zare mata kafin ya miƙar da ita tsaye da taimakon sa suka shiga ɗan madaidaicin toilet na su dake a cikin ɗakin sai dai na wanka ne kawai a ciki na bahaya yana atsakar gidan.Haka kuwa suka yo alwallah raka 'a biyu sukayi kasancewar dukkanin su sun gabatar da sallah Isha.Duk wani abu da ake yi a daren farko dare mai ɗimbin tarihi da albarka a wurin matan da basu zubar da mutuncin su ba suka kawo shi a gidan mutun ci.Ibrahim ya gabatar.Wani irin farin ciki ne ke kama zuciyar sa da ya tuna yadda take amsa masa tambayoyin sa.Haka ya tattare kayan da ya ciyar da ita bayan gama Adduoin na su.Hawa kan gadon tayi da ya bata umurni kasancewar ta ƙi cire kayan da ya ce ta cire ta samu ta sha iska saboda leshin irin mai nauyi ne duk da lokacin sanyi ne ta na buƙatar rage kayan tayi wanka sai dai ta ƙi,brush kaɗai tayi, ganin zai matsa mata da dole sai tayi wankan sai ta saka mashi kuka dole haka ya saka mata ido ganin tabbas a tsorace take dashi.Wanka ya faɗa shima inda bai wani daɗe ba ya fito ya shirya tsaff cikin kayan kwanan shi.Gadon ya hau yana zuba mata idanun sa tare da sakin murmushi ganin kamar ma.tayi nisa a bacciin nata A hankali ya furta " Komai wayon Amarya sai mun sha manshanun ta yawwa ".Ya na kai ƙarshen zancen ya ƙara sakin murmushi kafin ya gyara mata kwanciyar ta yana tofe su da Addu,a tare da lulluɓa mata blanket inda ahankali ya shige jikin ta ya janyo ta jikin sa sai bacci ya kwashe sa shima mai daɗi.Raliya kuwa kasancewar a gajiye take hakan ya sa bata motsa ba da alama bata ma san abinda ke faruwa ba. Asuba ta gari. Amarya Raliya tamu🥱 A ɓangaren Jamil kuwa su Gariti ne da wasu daga cikin Abokanan sa suka raka shi suna cike da Mamakin inda ya samu tangamemen gida haka kamar ba a Nigeria ba.Ga wasu tanƙama tanƙaman motoci parkey a a ma'ajiyar su.Komai dai gwanin burgewa.Sunyi mamaki matuƙa sai dai bai wani ɗaɗa su ba kasancewar sun san yadda yake son yarin yar wanda kuma duk da hakan babu wanda ya san yayi Aure A cikin dangin sa dan suna da tabbacin da mahaifin sa ya sani ba zai bashi goyon bayan irin wannan rayuwar ba rayuwar tozarci da kunya. Haka suka yi musu sallama suma bayan sun musu Addu'a tare da ajiye musu ledojin da suka shigo dasu. Jamil da ke ta ƙara faɗaɗa Murmushin sa ya saki Ajiyar zuciya yana bin ta da kallo daga zaunen da take ta ɗan ɗage mayafin na ta tana ɗan duban falon da ya ƙawatu da ado na musamman ya ƙawatu da abubuwa mafi tsada da take gani a Films ko a gidajen ƙawayen su masu kuɗi,Sai gata cikin ikon ALLAH itama.ta zamo a cikin irin gidajen Ajiyar zuciya ta sauke na samun cikar burin ta da ɓoyewar Asirin ta da take ta ɓoyo gudun ya guje mata.Hawayen ta kuwa ta ke suka ƙafe.A hankali ta saki murmushi wanda ya sauka dai dai a fuskar Jamil dake bin ko ina da kallo kamar yadda take yi.Sai dai A hankali ya sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya wani irin Tausayin ta na ƙara mamaye zuciyar sa raunin sa na son taso wa lokaci ɗaya dan Najiba itace raunin sa yana tsoron ranar da komai zai buɗe masa duk da shike da wuƙa da Nama a hannun sa. Ɗan murmushi ya ƙaƙalo kamar yadda ta saki nata yana Matsowa kusa da ita kafin ya miƙar da ita tsaye suka kama hanyar bedroom ɗin nata da yake da haske tarr kamar rana sai ko ina yake ta walƙiya kamar wata Aljannar duniya domin shima bedroom ɗin ta haɗu iya haɗuwa yana ɗauke da ƙaton gado da madubi da su shurack bags hanger,sip da sauran kayan ƙawata bedroom irin na masu Naira. Mayafin nata ya zare mata kafin a ya bata umurnin zuwa yin Alwallah inda ya fice. Ɗakin dake kusa da nata kaɗan ya shiga sai dai bai fi mintina huɗu ba ya dawo zuwa lokacin ta fito har ta maida mayafin ta.Hannun ta ya riƙo ba tare da ya furta mata komai ba sai a ɗayan ɗakin ya tsayar da ita kan carpet.Satar kallon shi take yi a hankali tana sakin murmushin farin ciki yau gata ga Jamil ɗin ta a rumfa ɗaya.A haka tana ji ya tayar musu da sallah Isha ya fara jan su kamar kuwa ya san itama bata yi ta ba sannan suka yi raka'a biyu ta ƙara raya daren na su mai ɗimbin tarihi. Itama ma dai gwargwado ta ɗan iya amsa wasu tambayoyin da yayi mata dan shima yana da ilmin sa gwargwado saboda mahaifin sa malamin addini ne shima har makarantar Almajirai suke da ita guda a ƙofar gidan nasu. Ledojin da ya shigo dasu anan ɗin ne ya janyo ya bubbuɗa tare da baje su anan gaban su. suya ce ta banƙararrun kaji da ke ta tashin ƙamshi sunji gashi na musamman.Duk da Najiba sunyi alkawarin Zasu ci su ƙoshi tare da ɗaukar shawarar ƙawayen su da suka ce musu har ƙashi su cinye,yanzu an bar kawaicin naman kazar daren farko,sai ta ji bata kwaɗayin kazar ko kaɗan sai ma wani irin tsoro ne da ya shige ta lokaci ɗaya.A jiyar zuciya ta sauke a hankali tana bin shi da kallo wanda shiko ko a jikin sa sai ma fara yagar kazar da yayi yana saka mata abaki inda take karɓa da ƙyar duk da nauyin da take ji na sa wanda ke saukar mata a yanzu.Haka ya saka ta ciyar dashi a ƙarshe dai suka ciyar da juna

Chapter 10 of 39