Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suke ciki wasu sun fita wasu kuwa ko shurawa basu yi ba wasu suna cikin wayen da suka ƙone saboda motar na ci da wuta sai aka rasa mafitar Fiddo su sai yan ƙalilan kafin ma motar ta yi butt gaba ɗaya. *** Zaune yake kusa da Dr Abida yayi tagumi kwana biyu har ya faɗa saboda ya san cewa ya cutar da Dr Abida matuƙa duk da ba yin kan sa ba ne aikin wacchan Azzalumar ce da yanzu ya ƙara tabbatar wa da kan sa ba da son ran sa ta shigo gidan sa ba.Tunanin zantukan ta da suka shiga kunnen sane suke ta ƙara hargitsa tunanin sa ya mutun musulmi zai aikata irin wannan ɓarna ribar me zai samu,wace makoma yake tanadar wa kan sa a gobe gaban ƙiyama mai zai faɗa Ubangijin sa da ya turo shi bauta masa,Tariyo zantukkan ya ƙara yi kamar yanzu suke shiga kunnen sa alokacin da ya shiga asibitin bayan an kawar da Jaruma,a lokacin an fara samun kan Jamcy ta fara farfaɗowa tana ta sabbatu kamar ta ɓaɓɓa. " Jaruma,Mata ta kar ki tafi ki bar Ni,Ke mata ta ce,Auren shine farin ciki na kasancewar mu tare Yafi mini komai dake duniyar nan,Dole sai mun cika burin mu,Sai mun lashi Zumar Shegen yaron nan Tanimu,sai nagana ma uwar sa azaba,Ni zata wulaƙanta ta cika gida da ya yan ta,ta hana mini haihuwa,sai na tarwatsa zuri'ar ta,yadda na raba ta da ɗan ta haka zan raba kan iyalan ta,Kuma sai na kashe Jazlan,Da shi da uban na sa har da uwar sa,Kuma yarinyar nan ƙanwar Nadiya sai na wulaƙan ta ta,Ni zata wulaƙanta dan taga na kwaɗaitu da ita,Jaruma Lokaci yayi da zamu ƙara sa Alhaji mu cigaba da rayuwar mu hhhhhhhhh boka Miyan ka akwai daɗi ,sun fi sugar garɗi,Daga yanzu sune kaɗai ruwan da zan iya sha ka aiko su ɗan duhu su kawo mini hhhhhh "..... Ta kai ƙarshen zancen tana gaɓɓatar Dariya. Alhaji Abdulkarim da Likitan da suka shigo kuwa turuss suka yi.Idanun sa sunyi jazir ya kasa ko iya ɗauke idanun sa akan ta gata dai ta dai duk ta nakkasa domin har an guntule ɗayan hannun.Fuskar ta ma duk ta chan za. Har ya juya zai fita ta ƙara furta " Ni nake yiwa Tanimu Safarar mata da qungiyar su ta gay nice mai ita Ni nake haɗa Alhaji da Alhaji Hajiya da Hajiya,Alhaji da yan mata,Hhh Yayi silar kashe muna boka dan haka sai mun sabauta rayuwar sa,shi da ɗan na sa ya tarwatsa muna aiki,ya saɓa dokar mu,Sai na hukunta shi,Sai na kwashe dukiyar Alhaji Abida bata isa ta ci ta ita kaɗai ba da ya yan ta,Sai dai ma ta ci ta lahira,Ni Jamcy Uwar tanɓele uwar yan harka,Uwar yan iska,sai na kai ƙarshen Duk wani jinin Abida,Yadda na kashe rayuwar ɗan a raye haka zan kashe Tata,Hhh sai na kashe ta,HHhH Ni na yi koyawa Tanimu shan taba,Ni na ƙara ɓata rayuwar sa ganin yadda ake sakan ta sa da gata,sai nayi amfani da hakan na ƙara dagula sa har Turai nake haɗa shi da mata fa babu club da bai sani ba a Turai inda yayi karatu kuma fa duk Ni nake tura sa,da aikin boka na,Sai ta kece da wata dariya kamar ta samu matsala kuma duk wannan abun idanun ta a rufe suke a zaton ta mafarki take yi. " Amma na faɗa Miki Jaruma Shegen da uwar sa ta dage duk da na saka masa ƙiyayyar ta haka itama na cire mata shi a zuciya,sai maganin ya bar cin sa sai kaɗan,Shi ya sa na dai na wahalar da kaina kan sa,sai gashi ɗan neman da kan sa yake kan sa,Maganin da na saka mai bita zai zai shine,Bin maza Kinga kuwa Banzan ya hau layi Shegen gari da daban boka ya hana ba yadda nake kwaɗayin sa ai da na ɗa... .... '' Alhaji Abdulkarim bai tsaya sauraren jin ƙarashen abinda zata furta ba " Ya juya hankali ta she a hasale idanun sa har rufewa suke yi,Da ƙyar iya damƙawa Dr kuɗi masu yawa yana faɗin kuyi yadda zaku yi da ita.Ya bar asibitin a masifar da ta shiga kunnen sa wadda bai taɓa ji ba ko saurare.Allah ne ya kai shi gida lafiya. Da shigar sa ƙaton Falon Dr Abida ya faɗi da taimakon Tanim da ya fara farfaɗowa a ka daura shi kan gado tabashi taimakon gaggawa har ya fara samun sauƙi.Dukkanin ya yan sa hankalin su matuƙar tashe yake Dan haka suke kasancewa gidan kullum ganin sa dan abinda yake iya kawo masa hayewar jini ba ƙarami bane Dan Dr.Abida ta na yawan duba shi babu komai a tare da shi tun ba yanzu ba.... Numfashi ya sauke jikin shi na ƙara yin sanyi yanzu shi kunyar Matar sa ma yake ji na farko ya ɓata mata tarbiyyar ɗaa saboda so da ya ke yi masa mai tsanani ,sannan ya cutar da shi bai bashi tarbiyya ba,bai bashi ilmin addini ba, sai zallan Gata da ya nuna masa fiye da sauran ya yan wanda da ace ba ciki ɗaya. Suka fito ba da an samu rarrabuwar kai.Wanda koda ciki ɗayan zai iya da sa ma yan uwan ƙiyayyar sa. Hawaye ne yaji sun silalo masa akan kwarmin idon sa tuno maganin da ya gani a ɗakin Tanim ɗin ɗazu da ya ji yana son ganin sa sai yaje ɗakin ya same shi yana bacci ga tarin drugs nan gefen side drower an sha an ajiye da ruwa a gora. Hankalin sa matuƙar tashe ya baro ɗakin yana kaico da Halin Jamila da ta jefa dubbanin mutane a ciki.Lallai kaidin mace Masifa ne,ko da yaushe sharrin su abin mamaki ne zaka yi mamakin yadda suke da banzar ɗab'ia kamar ba su ba.Wata idan aka ce maka tana iya aikata wani abun zaka rantse ƙarya ne ba dai ita ba,zaka ganta natsatssa.Mafi yawan mata kishin su ne ke azabtar da rawuyar su yake basu damar yin zalunci. Allah ya shiryar dake Jamila idan kina da rabon shiriya ya faɗa a ƙarshe a cikin zuciyar ta sa " Bazan taɓa yafe Miki ba har duniya ta naɗe har gaban abadan '' Ya faɗa a bayyane a hankali kamar mai ciwon tsoron magana. Dr.Abida da ta zuba tagumi abun duniya ya dame ta ,Dan har yanzu Nadiya ta hana Tanim ya ga ɗan sa hakan ya sa ya ƙara zabgewa ya rame ga ciwo na cin sa hankali kamar bai shan magani.Sai dai sauƙin ta ɗaya warin da jikin sa ke yi ya ragu ba kamar kullum shi ya sa kusan kullum falon da nan sashen gaba ɗaya kusan kwalbar turare aka ƙararwa,cikin ikon Allah da addu,a da ta haɗa da Tata da ta manyan malamai ya rage dan ta fahimci wannan wata jarabwar ce ko ɗai daga cikin sakamakon sa na abun da ya aikata a baya.Sai kuma Ga Alhaji Abdulkarim ya dawo mata mutuntimi tayi tambaya haka ma ya yan sa kasa faɗa musu komai,sai dai idan Damuwar ta tasar masa sai Bpn ya ƙara ɗagewa sama yau kusan sati haka yake zaune gida babu fita kuma sai yayi shiru abun na damun ta. " Alhaji ".!! Ta furta masa a sanyaye sannan ta cigaba da magana '' ba zaka faɗa mini abinda ke faruwa ba wai,kullum Bp sai ƙara hayewa yake yi,Ni da ya yan ka ka sanya mu cikin wata damuwa bayan wadda muke ciki ". Ɗan kallon ta yayi kafin ya sauke numfashi ya ce " faɗin bai da amfani ne Abida,Amma in lokacin sanin yayi zaki sani ". Bata wani ji daɗin maganar sa dan ta so taji mene ne Damuwar ta sa. Jin amsar sa sai Bata sake cewa komai ba. Ganin hakan ya san cewa ta ji bata ji daɗin amsar da ya bata ba kuma ya san gaskiya ce muddin ya faɗa mata nata jinin sai yafi nashi hayewa dan babu komai cikin abun da zai faɗa mata face Zallar tashin hankali . Hannayen ta ya riƙo a hankali kafin ya kai ƙasa kan guiwoyin sa idanun sa cike da hawaye.Cikin matuƙar tashin hankali Dr Abida ta fara waige waige kar Saheeba ko Tanim su faɗo ko wani daban.Hakan ya sa take ƙoƙarin ɗago shi shima idanun sa cike da hawaye,sai dai ta kasa ƙarfi ba ɗaya. Kalmar da ya furta ta neman gafara ce ta sage mata guiwoyin ta hawayen ta na saukowa na tsoro da tashin hankali. Yadda ta ke haɗa shi da Allah ne ya tashi hakan ya sa ya ta shi ya zauna a kusa da ita jin ta ce ta yafe masa ganin bai da niyyar tashi ɗin. "Ashe kece mai gaskiya nine a dubu Abida, Ki yafe mini Nasan na Miki lafukka iri iri amma ni nasan da ba da son raina nake yi ba,ki yi hakuri na san an cutar da Tanim,musamman Ni na cutar da shi matuƙa ina jin cewa ina ma ana dawo da baya dana dawo da ita na gyara abun da na ɓata da hannu na,domin na san nine silar wargaza komai,yau gashi an wayi gari Tanim na ɗauke da mugunyar cutar ƙanjamau sakamakon Abunda ya aikata duk da bashi kaɗai ya tura kan sa ba na yi kaico da rayuwar da na saka ɗana a ciki,me ya sa ban nema masa ilmin Islama ba ya zama babban malami,me ya sa bai samu tarbiyya ta ƙwarai a guna ba,na san kinyi ƙoƙarin iyar wa ki,Kuma Allah ya saka Miki da Alkhairi ya baki ikon cinye jarabawar ki,ya bamu ikon riƙo da ƙaddarar mu,Shima kuma Allah ya bashi Lafiya ya ba shi ikon yin riƙo da ta shi ƙaddadarar ". Haka yayi ta mata nasiha bata re da ta san inda ya nufa ba duk da ta yi mamakin yadda ya san Tanim na ɗauke da cutar H I V wadda babu wanda ya san da ita daga ita sai Tanim ɗin sai Saheeba,sai kuma wayen da suka yi gwajin. Sai da ya gama take tambayar sa inda ya san maganar Nan ya sanar mata komai sai dai har yanzu bai faɗa mata abun da ya ke ƙara sanya shi damuwa ba. Abun ka da mata miji nan suka fara taɓa yar firar rayuwa cikin tausayin tilon ɗan su Namiji da ya haɗu mummunar ƙaddara .Da jarabawar Rayuwa.Ta ɓangare ɗaya har yanzu hankalin ta bai kwanta ba,ta san akwai abun da yake ɓoye mata. Ƙarar wayar sace ta sanya shi ɗaga kiran sai dai cikin tashin hankali yake sauraren abinda ake faɗa. Miƙewa yayi da sauri yana furta " Ku shirya keda Saheba Da Tanim zamu fita ". Da sauri ta kira Tanim ɗin da ke ɗaki abin duniya ya sha masa kai tunani kamar zai tafi da rayuwar sa. Haka ya fito duk ya faɗa daga Ni kasan damuwa da ciwo na cin sa.Mota ɗaya suka fita da ita irin Babbar Motar nan Prado mai seat na kusan goma direct Asibitin da aka kwantar da Jamcy ya ce driven ya nufa da su...✍️ Matuƙar razana page ɗin nan ya saka Ni wallahi.Ba dan komai ba sai dan tuna masu irin wannan halayyar akwai dubbanin su cikin wannan duniyar,duk wani laifi da Allah ya hana irin wannan suna aikata abin su a doron ƙasa babu tsoron Allah babu, imani duniyar kaɗai aka saka gaba,duniyar mai muni babu tunanin mutuwa.😭 Hasbunallahu wa ni'imal wakil.Allah ka sa mu dace,ka cigaba da rayar damu cikin Cikakken imanin mu da wankakkar zuciya.🤲🤲 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Like share,Vote, react, comments pls. Masu neman ƙarin bayani Kuyi magana da ñumban da ke ƙasa. 08069059746 Saƙo kawai pls ban da kira.🙏🙏🙏 Saƙon soyayya💔💔 ga duk wani masoyi nawa na kusa da na nesa.Ina ƙaunar ku🥰🥰 kamar yadda kuke yin tawa.Allah ya bar min ku ya cigaba da arzutta ku ku cigaba da sayen littafaina na kuɗi tsofaffi da masu zuwa🤲🤲.🤭🧘😜 *FA'EEH BG CE🤙*✍️✍️✍️ *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.39 A ɓangaren Jamcy kuwa yau tun da safiyar Allah ta waye ta ƙara hargitse wa domin kuwa sabuwar hauka ta fara,saboda jikin ta da yake ta faman ƙaiƙayi ga Shi duk ta ɓata gadon da bayan gida saboda yadda jiya zuwa ta kasa riƙe sa.Duk yadda ake son taimakon ta abu ya gagara ƙafarta da ta ƙarasa ruɓewa kuwa an yanke a daren jiya sai ya zamo tana jan ƙafa ɗaya.Ga wata azababbiyar ƙishirwa na damun ta amma duk ruwan da suka bata bata iya shan su,Sai sunan Boka Hatsabibi take faɗi tana kuwwa wadda ke nuna alamar hauka ta kama ta gashi sai zayyane laifukkan ta take yia fili.Duk da qari da warin da ke wurin haka jama'a suka zagaye gurin suna alawadai da ita cikin tausayin ta da ya gushe musu.Ganin abun nata bana wasa bane ganin yadda take wani irin kuka kamar ta fara kukan kare saboda lokaci ɗaya kukan ya sauya,Ga idanun ta sun birkice hakan ya sa Likitota suka yanke shawarar kiran Alhaji Abdulkarim da suka yi magana dashi kusan sau uku tun kai ta asibitin saboda yadda yake ta fama da kansa a gida shima.Duk wani taimako da zasu bata iya yin su abu sai gaba yake yi dan haka cikin gaggawa suka kira sa a waya suna sanar dashi.. **Duk da mamakin su na wanda akawo asibitin dake mamaye da su basu bayyanar ba ko tambayar sa har suka shiga cikin asibitin bayan driver ya sauke su a cikin ƙatuwar asibitin. Tun kafin su isa ƙofar ɗakin suke jin wani irin kuka kamar na kare ga wari ta ko ina sannan ga jama'a sun taru gurin kamar ana raba kuɗi suna magana ƙasa ƙasa wanda bai wuce ɗebe mata albarka da tsine mata ba. Kasancewar ya san komai dan haka ya ratsa jama'ar yana saka nosemask da yace kowanne su ya zaro a cikin motar domin ya san ɗakin bai shaƙuwa. Isowar sa dai dai ƙofar ɗakin dake wangale kaɗan ya ƙara jin kalaman da suka tarwatsa masa ƙwaƙwalwa akwanan baya wanda har sai da yayi jinya,sai gashi yau tana ƙara maimaita su dalla dalla tana yi tana kuka irin na kare sanannn ta ɗan yi shiru sai ta koma ambatar Saliva na Hatsabibi take so ta sha ƙishirwa take ji,tana faɗin a bata su, kuma sune kawai maganin ta,ga idanun ta ajuye amma baki ya ƙi mutuwa jikin ta sai kakkarwa yake yi a haka take kukan kuma idanun a kafe Sannan take faɗin komai dalla dalla,har wanda bata faɗa ba ranar,Domin har da niyyar da tayi ta saka ma Jazlan guba ta faɗa kuma yadda take zancen da alama ko yanzu ta samu chance zata aiwatar da ƙudurin ta. Masifar da tafi ƙarfin kunnuwanta ce ta sanya ta yanke jiki ta faɗi ƙasa kafin ma Sahiba ta taro ta zuwa jikin ta.Cikin kuka haka Sahiba ke ambatar Sunan Dr Abida da wani irin tashin hankalin da sai yau ta gan sa kuma ta jishi domin ko a tarihi bata ji irin sa ba,Shi kuwa Tanim shock ya tsinci kan sa mai matuƙar girma domin dasƙarewa jinin sa yayi na wucin gadi komai na sa ya ɗauke hankalin sa bai dawo kan sa ba sai da yaji Sahiba na ambatar sunan mahaifiyar sa da ya ke kallo a matsayin sanyin idaniyar sa da farin cikin da yayi masa saura a rayuwar sa ta yanzu. Numfashi ya sauke mai zafi idanun sa na cikewa da hawaye bakin sa ya kasa iya furta komai.Babu wanda yabi ta kan Jamcy da bata san wanda ke kan ta ba domin ta yi nisa ayanzu wanda bata jin kira a yanayin da take ciki,kuma babu abinda ta fasa kira daga sunan boka da ƙarin sunan Jaruma tare da zayyane laifukkan ta da yin kukan kare mara daɗin sauraro. Cikin sauri ya tallabi Dr Abida ya fice da ita inda aka bata gado kafin aka fara bata taimakon gaggawa. Shiko Alhaji Abdulkarim a gaban sa ta tafi tana kukan kare tare da kiran sunan boka da na Jaruma,duk yadda yayi ƙoƙarin Sanya mata kalma a baki ta kasa riƙawa sai sunan Boka Hatsabibi take kira da kukan karen da ta tafi dashi.Duk ƙarfin halin sa sai da ya zubar da hawaye domin irin wannan tafiyar ita ake kira anyi zuwan Zomo duniya.Anci kasuwa babu riba,sai ma tarin bashi da ta kwasarwa kan ta mara kyau domin kuwa shirka bashi ce hukuncin ta bamai sauƙi bane da saurin yafiya domin kuwa Ubangiji ka haɗa da wanin sa,tare da zubar da jinaina da sunan cimma wani buri,wanda hakan Babbar illa ce,Kuma Babban Laifi ne, ga rayuwar masu aikata hakan,ba zasu gane ba kuwa sai ranar haɗuwar su da Ubangiji. Haka ya rufo ɗakin inda da ƙyar nurses suka shiga suka yi mata last office suka rufe suka fito a gaggauce domin ɗakin kamar an ƙara manna masa wani irin wari babu daɗin shaƙa fiye da wanda take yi a farko.Kashin da tayi kuwa cikin abunta aka rufe ta.Wanda sai bayan ɗauke ta ward servant zasu yi gyaran gurin gyara mai kyau da wanke sa. Haka shima Alhaji aka duba sa dan take jinin sa ya ƙara hayewa. Bayan Farfaɗowar Dr Abida dake ta kuka tana Allah wadai da Wannan rayuwa ta Jamcy musamman da ta ji ance ta rasu a yadda ta bar ta.Tayi kuka kamar ba zata daina ba tsoron duniyar ya ƙara shigar ta.Ace kan abun duniya ta kai kanta ga irin wannan halaka mutum na wa ta cutar a wannan sabgar mutun nawa ta jefa a halaka.Wani irin Tausayin Tanim ne da ke gefen ta yayi shiru suko idanun sa sunyi jazir da su shima yaci kuka har ya gaji haka ma Alhaji Abdulkarim da bai daɗe da samun kan sa ba ya yi shiru kowa da abun da yake lissafawa cikin jimami.Kasancewar Sahiba ta sanar da Sauran yan uwan su sai ga su sun cika asibiti kowa da zuri'ar sa sun shiga tashin hankali matuƙa dan kowaccen su sai da ta koka haka suka saka mahaifiyar su gaba suna bata haƙuri tare da Rarrashin ta da bata baki.Dan take jikin ta ya ɗume ya fara kakkarwa kafin sun ankara ta ƙara sumewa dole aka fara bata taimakon gaggawa domin Bp ɗin ta ya ƙara hayewa babu abun da yake ƙara tayar mata da hankali irin jin harda mu'amala da maza ɗanta yayi,wanda bata taɓa sani duk binciken ta,wanda take ta gano bakin zaren irin yadda idanun Nadiya suka bushe da dalilin ƙin faɗa ma iyayen ta komai ashe wannan ne dalili hakan ne ya ƙara kai ta ƙasa cikin wani sabon baƙin ciki da ya rufe ta domin ta san iya cuta Jamcy ta cuce su ta gama da rayuwar ɗan ta.Har ya su gaba ɗaya. Sanin da Alhaji Abdulkarim yayi cewa bata da Kowa anan kusa Dan ko dangin ta bata bari ya sani ba har yanzu hakan ya sa ya ja Tanim dake ta kukan zuci yanzu aka saka musu ita a ambulance suka wuce da ita akayi mata abinda ya dace na mamaci sannan yan ɗai ɗai kun mutane suka sallace ta aka kaita makwancin ta daga ita sai abin da ta aikata anan duniya,ayyukan ta na ƙwarai su zasu ƙwace ta daga musubu,da azabar ƙabari kafin tsayuwar Alkiyama a yi mata hisabi dai dai da laifukkan ta.. Allah ya sa mudace,Allah ya bamu ikon aikata mai kyau,Allah kabamu ikon tunawa da lafirar mu a koda yaushe,ba mu saka duniya gaba ba.Allah ka bamu duniya mai kyau da Lafira mai kyau.Ka sa mu cikin Samu Samu.🤲🤲 *** A sibitin suka dawo direct zuwa lokacin itama Dr Abida ta farfaɗo idanun ta daƙyar ma suke buɗewa dan kuka kam ta cisa duk ta tuna kalaman da Jamcy ke faɗa sai taji kamar numfashi bai isar ta ma saboda tashin hankali,domin ta san musiba ce babbba fara irin wannan mummunan ɗabia domin barin ta ba abune mai samuwa cikin sauri ba,amma ta san cewa tun da har akwai asiri a ciki in Sha ALLAH ya daina kamar yadda take hasashe ,saboda yadda ya ke ɓance duk tsawon lokacin nan acikin ɗakin sa,Tana fatan shi kenan Allah ya ye masa. Bayan shigowar Alhaji Abdulkarim ne ya ƙara yi mata nasiha irin wadda yayi mata a ɗazu wadda ta ankarar da ita dalilin da ya sa yayi mata ashe shima abinda yaji kenan ya shiga wannan mugun tashin hankali da ya so taɓa lafiyar jikin sa dan yadda Bp ya sako shi gaba zai iya samun Stroke na ɓarin jiki a take saboda ba a ɗaukar lokaci bai tashi ba maganin yake sha banza. Zuba masa ido tayi ganin yadda ya rakuɓe gefe kamar Maraya duk wani gayu babu sa yanzu kan na sa ya saka anyi masa aski na tal kwabo domin ba,a bar masa komai ba sai walƙiya yake yi.Haka ma duk wata sarƙa ko yan kunne da yake mannawa ya cire su baya tare da duk wani abu da zai sa ya fito ba a asalin musulmi ba,Ya kai komai gefe ya ajiye domin ya riga ya sallama wa rayuwa ya san cewa tashi ta zo ƙarshe dan haka komai ya fice masa arai a yanzu idan ba maganin sa na HIV ba babu wata ƙwaya da yake iya ɗauka ko ta pcm ce dan ko su sai ta tuna masa yake shan su. Ya fito sa tayi da hannu.Kamar jira yake yi kuwa ya taso jikin sa a mace.Zaunar da shi tayi kusa da ita tare da ɗaura kan sa akan kafaɗar ta,tana ɗan shafa Bayan sa a hankali zuwa ƙeyar sa.Sai a lokacin ne kuka wanda yake kuka ya amsa kan sa ya zo masa take kuwa ya fara raira abun sa na dukkanin abun da ya tsane masa tun rayuwar sa ta baya abubuwan da ya aikata har iZuwa yanzu da yake girban abun sa bai wani damu da abun da Jamcy ta faɗa ba duk da yasan shima Wani lokacin bada son ran shi yake yi ba,Babu abun da bai dawo kan sa ba har zaman su da Nadiya yadda ya cuta mata.Kukan sa ne ya ƙara yin ƙarfi tuna yanzu yana da ɗa a duniya amma baida iko da shi ya san dole ta hana masa shi saboda kaitsaye ya nuna bai son cikin kuma ana naƙudar sa ya bata red card Mafi muni a gadon naƙuda kamar abun gudu. Jikin sa ne ya fara jijjiga kasancewar ta kasa Rarrashin sa haka ma kowa ya san cewa kukan rahama ne a gare sa hakan ya sa suka zura masa ido.Sai dai ganin yadda jikin sa ya fara jijjiga hakan ya sa hankali tashe har mahaifin sa da yan uwan sa mata suke rigangan yin kan sa kafin dai ayi wani abu idanun sa sun fara Lumshewa saboda tashin hankali da

Chapter 36 of 39