Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗin idanun sa basu daina hango mashi Kyakkyawar surar matar ta sa ba. Yana fitowa kuwa tsaff kuwa shima ya shirya cikin shigar pyjamas daga cikin wayen da Tanim ya ba shi ya shirya tsaff.Turaruka ya fesa sannan shima ya haye gadon. Ganin shi kan gadon ne ya sanya NAJIBA ɗan jin faɗuwar gaba daren na su na jiya na dawo wa akan tunanin ta.Runtse idanun ta tayi da ƙarfi jin da tayi ya janyo ta jikin sa ya haɗe da nasa duk da ƙaryar Baccin da tayi. Jamil kuwa dariya yayi kafin ya sauke Numfashi da ajiyar zuciya yana furta. " Ba abinda zan Miki ". Dan ya san afarke take she's just pretend. Numfashi NAJIBA ta sauke tana ɗan ƙara shigewa jikin sa dan taji daɗin kwanciyar akan jikin sa.Idanu ya fara rufewa itama haka inda take bacci ya kwashe ta.Sai dai shikam yallaɓai Jamil in muku ta Gariti.😅 Babu Alamar bacci a tattare dashi tun yana jin lamarin a matsayin ƙarami har ya zo ya wuce tunanin sa bashi da iko face bawa ruhin sa abinda yake so hakan ya sa ya fara aiwatar da komai a tsanake.Najiba da barci yayi wa nisa sosai kafin a hankali ta fara buɗe idanun ta duk da taji tsoro amma haka ta shanye abunta ta ƙyale shi ƙarshe ma ta fara bashi haɗin kai sai dai da zancen yayi Nisa ta fara neman nayi,amma masu iya magana kan ce idan baya ta wuce babu gyara mai sha ta riga ta sha.Dan haka dole ta miƙa wuya.A wannan daren ne Jamil ya ƙara angwancewa da Amaryar sa cikin so da ƙauna. A ɓangaren RALIYA kuwa tun asuba take kuka har bacci ɓarawo ya kwashe ta bayan ya yo mata wanka,Sannan suka yi sallah.Inda daƙyar ya samu ta sha magani bacci ya kwashe ta Dan kukan sangarta ta yi ta saki.Bawan Allah Ibrahim duk ya susuce sai yayi kamar ya kira Umma sai kunya ta hana shi domin bai san abinda zai ce mata ba,haka ma Yayyen sa.Hakan ya sa ya maida hankali yayi ta Rarrashin ta domin shi ba komai ya iya ba.Ganin ta tashi zaune ne dan bai lura da buɗe idanun ta ba hakan ya sa ya saki Murmushi yana furta. " My Halal " . " Kin ta shi " . Kai RALIYA ta gyaɗa masa tana ƙaƙalo ɗan murmushi mai cike da kunyar sa sannan ta yi masa ina kwana wadda bata samu damar yi masa ba saboda kukan da ta sha a ɗazun. Hannun ta yariƙo kafin ya shafa kan ta dake ta ɗauke da ƙananan kitso yar yar wanda ya kitsu sannan ya furta yana ƙawata fuskar shi da murmushi. " ALLAH yayi Miki Albarka,Allah ya cigaba da faranta miki My ya bamu ya yaya masu albarka,ina son ki Raliya ke ce duniya ta ta har abada,Farin cikin ki shine nawa RALIYA,ina roƙon ki ƙara kame wa daga dukkanin Abinda ba halal naki ba Nagode,Nagode Nagode ". Ya na kai ƙarshen zancen ya sakar mata Wani zazzzafan kiss a kan goshin ta wanda ya saka ta ɗan runtse idanun ta da ɗan ƙarfi cikin wani irin yanayi mara fassaruwa a gare ta.Idanun ta ne suka ciko da hawaye badan komai ba sai Dan farin ciki.Tana fatan soyayyar da Ibrahim yake mata ta ɗaure har abada,tana fatan samun Aljannar ta aƙarƙashin ƙafafun sa cikin sauƙi,Albarkar da ya saka mata kuwa wani irin zama tayi a zuciyar ta saboda ta ji daɗin ta sosai,domin abun farin ciki ne miji ya saka Miki albarka kamar yadda muke jin daɗi idan iyayen mu sunyi muna saka albarka to shima hakan ne domin kuwa Aljannar ki na ƙasan ƙafafun sa tun da ga haka kuma zaki fahimci nasarar ki ta biyu a duniya bayan ta Rabuwa da iyaye lafiya. Hawayen da yake share mata ne suka sanya ta jan Ajiyar zuciya tana ƙara jin sanyi acikin zuciyar ta.Da tsaida zancen zucin ta. Murmushi ta ƙara saki kamar yadda ta saki yana Binta da idanun sa sannan ya furta " Kuka Ba Agidan Khalillullah ba lalala ". Yayi zancen yana kallon ta. Dariya tayi kaɗan jin yadda ya fidda ƙal ƙala da gunn a zancen, haka shima dariyar yayi sannan ya ƙara furta. " Ya jikin naki ".? Kai ta sunnar ƙasa kafin ta gyaɗa masa kan ta cikin jin kunya domin ta san inda yake magana akai.. Kai ya jinjina shima ya na sauke Ajiyar zuciya kafin ya furta. "Bari na kawo Miki abin karin kumallo". Yana kai ƙarshen ya miƙe ya fice. Da idanu RALIYA ta bishi tana sakin murmushi. Da kuloli guda biyu da flask da cups guda biyu ya shigo akan tire da bire di a gefen hannun sa, anan tsakiyar ɗakin ya ajiye kafin ya ƙara komawa ya ɗauko mata kazar jiya da lemu da ruwa. Duka anan gaban ta ya ajiye bayan ya shimfiɗa carpet akan ledar da ke shimfiɗe da ɗakin. Taimaka mata yayi ta sauko ta kuskure bakin ta kasancewar tayi brush a ɗazu. Masar ƙwai ce da ƙosai sai kuma flask dake ɗauke da Haɗin shayi mai kauri wanda an riga ma an haɗa. Zuba mata yayi yana yankar mata biredin tare da saka mata Masar ƙwai da ƙosai aciki karɓa tayi,Inda ta fara saka wa cikin ta sai dai tafi shan tea ɗin dan yunwa take ji sosai wadda ta yo mata sallama ayanzu. Sai da ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya yi nasa shima Dan ya kasa yin sa breakfast ɗin.Ficewa yayi da kayan sannan ya taimaka mata ta ƙara yin wanka ta kimtsa tsaff ko ina sai tashin ƙamshi yake yi duk yadda Raliya ke nuna jin kunya haka Ibrahim ya rufe ido yana baje kolin salon tashi soyayyar da Amaryar sa Raliya yinin ranar kuwa raliya taga gata ta sha tarairaya kamar ƙwai dan komai in zata yi shi yake karɓewa yayi a cewar sa bata da ƙarfi a jikin ta,duk da kuwa jikin ta ya saki Sosai sai yar kunyar da ke ɗawainiya da ita. *** Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a kowanne ɓangaren sai dai duka ɓangaren guda biyu ba,a rasa wanda ke tattare da matsananciyar damuwa ba. Domin kuwa Yau sati Uku da Bikin su kuma a sati mai zuwa ne Tanim ya ɗibar wa Jamil wa,adin ajiye masa komai na sa da komawa bakin aiki kafin ya neme shi ya rasa.Tashin hankalin da Jamil yake ciki ya tsananta domin ayanzu Najiba ta na neman rasa kan shi, Dan a yan kwanakkin da suka gabata wata irin soyayya suke nuna wa junan su mai cike da ƙauna wanda har hakan ya kusan mantar da shi damuwar da ke tun karo shi,sai dai a yanzu komai ya chanza domin kuwa ta ko ina komai yana neman rikichaɓe masa wanda ke binshi bashi ma ya taso da zancen sa da sunan tuni.Gashi yar motar da yake ja ta daina aiki tana neman manyan kuɗaɗen da koshi kan shi ayanzu neman su yake yi aljihun shi yayi slow sauƙin ta ma suna da abincin da ya ɗan siya musu kafin su tashi barin gidan. A ɓangaren su NADIYA kuwa babu wani chanji ayanzu game da Tanin shigowa da yan matan sa cikin gidan ayanzu ya ƙaru wani lokacin sai dai ta ji hayaniyar fitar sa da karuwar sa.Kuma bata sanin shigowar sa domin tun da ta fahimci halin da ta jefa kan ta sai ta fara tsabbace kan ta gefe tana gujewa haɗuwar su dan ko ganin shi bata ƙaunar yi muradin ta a yanzu bai wuce a ce ta samu wani kaso daga dukiyar shi ba,kuma tana samu ko ya sake ta ko bai sake ta gidan su zata koma.Duk da hakan kuwa da take yi Tanim a wasu lokuttan ya kan mata bazata dan wasu lokutattan takan buɗe ƙofa idan ta tabbatar ya fita.Sai yayi amfani da wannan damar yake rutsa ta kuma haka zai yi mata ta ƙarfi da tozarci ya fice duk kukan da take yi kuwa ko a jikin sa bare a tafin ƙafafun sa. A yanzu kuwa mutun ɗaya ce take jin daɗin ta ita ce Shanty wadda kusan kullum tana gidan wajen ta tana zuwa tun safe har dare sannan ta bar gidan. Tun abun na damun Najiba har ya kai ya daina damun ta sai take samu damar fitowa suyi fira tare a Babban falon. Kuma wannan shine silar da ya san ya Tanim daina shigo mata da yan mata cikin gidan wanda yake yi a wajen sa sai kuma idan ya tabbatar da Babu Shanty a cikin gidan wadda ya ƙwallafa rai akan ta itama kuma da yake itama shegiyar kan ta ce tana sane da shi tana jiran lokaci ne,tana jiran lokacin da zai kawo kan shi da kan shi,kuma tsaff ta fahimci irin zaman na su sai dai bata taɓa yi mata irin zancen ba. Yau ma zaune suke a cikin Falon bayan sun gama cin haɗaɗɗen girkin da me aikin ta tayi mata cikin wayen da Tanim ya zuba a gidan ganin gidan na neman lalacewa domin kuwa NAJIBA bata fitowa sai ta ta ga dama kuma tana fitowa take komawa ɗaki sai kuma lokacin da Shanty ta shigo gidan na su wanda bata san dalilin ta na yawan zuwa gidan ba har yanzu duk iya binciken ta. Nigerian Film suke kallo mai suna " PERFECT FRIENDSHIP " na Maurice sam suna yi suna taɓa fira wadda rabi ta duniya ce da kuma dariyar Films ɗin da kuma recommending wasu daga cikin Films ɗin Maurice ɗin. Takon tafiyar shi ta sa Kowannen su juyawa shi ɗin dai ne ya matse cikin riga da wando ya maƙala wasu irin sarƙoƙi a wuya kamar koda yaushe kamar ba ɗan musulmi ba ya tara gashi wanda akayi wa deying jaa.taka wa ya cigaba da yi cikin rangwaɗa.Shigar tashi kamar ba ɗan musulmi ba sai dai bazaka taɓa iya cewa shine mai aikata abubuwan da yake yi ba a fuska Salihi a zuciya fir'auna. Ƙamshin turaren sa ne ya ƙara susutar da Shanty inda ta kasa ɗauke idanun ta da ga kan sa jikin ta na wata irin tsuma ji take kamar ta je rungume sa ko zata rage abinda take ji a jikin ta da zuciyar ta.Domin kuwa Tanim irin mazajen da take so ne komai na sa a yadda take lissafa shi ne a cikin zuciyar ta da tunanin ta,Dalilin tarewar ta gidan na NADIYA kuwa shine tun lokacin da Nadiya ta bata sirrin mijin nata ta kwaɗaitu dashi wanda har ta ji zata iya yin komai akan sa rashin samun sa a gare ta babbar matsala ce yadda take ƙara jin sa a tunanin ta da zuciyar ta ita kan ta lamarin yana bata tsoro sai dai duka barikan ci ne yafi yawa Dan bata jin ta shirya Aure ayanzu da yan shekarun ta wanda a ƙalla zata yi shekara ishirin da shidda Dan duk ta girmewa su Najiba da Nadiya ƙawance ne kawai da babu ruwan shi da shekaru.Kamar dai Aure bature na cewa Age is just a number. Zaka ga mutun da number mai yawa babu hankali bare tunani mai kyau. Zaka ga mutun da numbers kaɗan sai dai Allah ya zuba Mishi hankali irin na manya. Haka abun yake. Kowa da yanayin da ubangiji yayi sa. Shekaru ba shine girma ba mutunci shine komai yana zubewa komai girman shekaru sun zube.🤌 Ido ɗaya Tanim da rabin hankalin sa ke kan ta tun shigowar sa ya ƙyafta mata irin na neman magana na yan bariki aiko da sauri ta sauke wani irin Gwauron numfashi tana Lumshe idanu tare da shigewa cikin kujarar kamar wata ƙadangaruwa. Nadiya da ta ɗauke kanta kan shi tana taɓe baki ta kai duban ta kan Shanty da ke a zaune idanu a lumshe sai tayi kamar ma bata san da shigowar Tanim ɗin ba sai hakan ya yi mata daɗi itama bata ce mata ƙala ba sai ta mai da hankalin ta kan Tv dan a tunanin ta ko bacci take son yi. Tanim kuwa cikin Rashin damuwa ya shigewar sa ɗakin sa bata re da yayiwa Nadiya ko Shanty magana ba sai dai ta ƙasan ido yake bin Nadiya da mugun kallon ƙurilla domin kwana biyu yayi neman hanyar da zai gan ta bai gan ta ba.Tun daren da ya samu ya shiga da zai fita ya jefe ta da kalamai mara sa daɗi inda ya tabbatar mata da zargin ta akan dalilin Auren ta,sannan kar ta saka ran zancen saki zai shigo ciki babu wannan maganar a yanzu,kuma ko wane irin lokaci ya so zuwa wurin ta zai zo yana bata lokaci ne kawai.Har da sanar da ita shi ba ita yake so ba ƙanwar ta RALIYA mai kamun kai ba irin ta ba ballagaza mara tarbiyya,ita kawai ya saye ta ne dan kashe ƙishin sa,Sannan kar tayi tunanin kuɗin da take nema da burin samu a gidan sa ta same su,domin yana sane da kuɗin sa take so ba shi ba.Haka yayi ta jefa mata mugayen kalamai marasa daɗi wanda har da zargi ya ke neman maƙala mata shida yake abun sa bata taɓa saka ido ba sai shi,Hakan ya tabbatar mata da tabbas ba son ta yake ba tun asali zancen yar uwar ta ya zama gaskiya domin kuwa ita kaɗai ta san halin da take shiga a duk ranar da Tanim yaje mata dan shi mutun ne mai jarabar tsiya haka Halittarsa take wanda hakan yayi saurin jefa shi ga halaka tun yana da ƙananan shekaru a ƙasan Turai har yanzu da ya dawo gida Nigeria. A Ranar kuwa NADIYA ta ci kuka duk da ta shaida ba son shi take yi ba saboda yadda yan matan sa da yake shigowa dasu lamarin su ya daina ɓata mata rai sai dai tana jin zafi matuƙa ba rayuwar da ya jefa kan sa ga kuma sabuwar ɗabi'ar da ta fuskan ci yana yi ta shaye shaye wadda sai ayanzu ta san da ita.Duka wannan matsalolin babu wanda ta taɓa sanarwar ta barwa cikin ta har mahaifiyar ta ta kasa faɗawa bata san dalili ba sai dai idan abun ya dame ta ta sha kukan ta ita kaɗai,wasu lokuttan tana ɗan ɗaukar Alqur'ani ta duba tayi addu,a wasu lokuttan kuwa kan ta sai ya rufe daga kukan sai bacci ya kwashe ta,wanda ibadar ma ba duka ake cika ta ba.Zuwan Shanty ya fara kawo mata natsuwa acikin gidan.✍️ Wata sabuwa Shanty 🚶 Daga Alƙalamin ✍️ Fa'eehbg Like,share, comments,vote pls 🙏 Ƙarin bayani. 08069059746 Idan akwai shawara ko comments ƙofa a buɗe take. Zan ƙara faɗa muku labarin a channel ɗita yake tafiya.in kina son farkon labarin Kiyi following ɗina sai ki mun magana na baki farkon labarin.✍️Link a sama. https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko._*☝️ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ P.19 *_TAURARI HUƊU_*⭐⭐⭐⭐ *_# Fa'eeh Bg_* *_# Shanty_* *_# Tanim_* A ɓangaren Tanim yana shigewa ɗaki ya sauke ajiyar zuciya kasancewar wata irin buƙata ce ta ta so masa bata kowa ba ku a face ta son kasancewa da Shanty.Kan makeken gadon na sa ya haye yana rufe idanun sa da suka sauya lokaci ɗaya bayan haɗa idanun da suka yi da Shanty ɗin. A gogon hannun sa ya duba da kyau yana sakin numfashi kafin ya miƙe ya zare kayan jikin sa ya faɗa toilet wanka ya ɗauro,yana fitowa kuwa yayi shirin sa sannan ya fice dan yana jin ya kasa jure wa,kuma No way kasancewar Nadiya na kusa bare ya shiga ɗakin sa da Shanty,duk da ba tsoron ta yake yi ba. A ɓangaren Shanty kuwa yanzu take maganar tafiya gida,suna cikin maganar sai gashi ya zo ya ratsa su ya fice yana bin ta da kallon ƙasa ƙasa ɗan daburcewa tayi wanda har Nadiya sai da ta zuba mata idanu kafin ta wayen ce dan shanty ba dai ba riki ba.Sallama tayi mata tana amsa fake call sannan ta bar gidan cikin sauri.Nadiya kuwa duk da ta san ba lokacin da take tafiya gida ba ne hakan bai dame ta ba sai ma miƙewa da tayi itama tana shigewa bedroom ɗin ta Dan bacci take ji sama sama duk da bayan la,asar ne,duk da bacciin na sauya mutun da ga yanayi mai kyau zuwa mara kyau.Sai dai kuma su ma Likitota sun ce abu ne mai kyau bayan na ƙarfe uku shima yana ƙara wa ƙwaƙwalwa lafiya da kwanciyar hankali kuma yana taimaka ma zuciya.. Annabi ma yayi gargaɗi da wanda mun san akwai hikimar haka nan.Barin sa shine dai alkhairi. Tana shiga ta kulle ƙofar da key take kuwa nan bacci ya kwashe ta mai daɗi bacci mai cike da mafarkai bayan ta haye gadon na su. Nadiya kuwa tana fita compound na gidan ta kama hanyar barin gidan baki ɗaya duk da ta haɗa idanu da Tanin da ke bin ta da wani irin shu'umin kallo.Ficewa tayi ta yar ƙaramar ƙofa shima bai dakatar da ita ba har sai da ya fice daga gidan gaba ɗaya bayan an wangale masa ƙaton gate ɗin gidan. Shan gaban ta yayi domin ta kasa taron abun hawa shi take jira ya fito taga ko zata dace domin yau bata zo da motar ta ba,dan itama ɗiyar wani Shege ce mai faɗa aji ta jiƙu da kuɗi,shine ma dalilin ƙara liƙe mata da Nadiya tayi bayan fara ƙawancen na su wanda Suka ɗinke waje ɗaya har da Najiba. Ɗan ya tsine fuskar ta tayi da ke ta glowing saboda ɗan hasken ranar da ta Haska ta da Asalin gyaran da take samu. Wani Shegen murmushi tanim ya saki kafin cikin Sadda kai ƙasa irin na bada girma ya furta. " Hajiya ki shigo Mu wuce kar a ganmu " . Ɗan waige waige Shanty tayi sannan ta zagaya ta faɗa gaban motar cikin amincewa umurnin zuciyar ta domin idan bata yi hankali ba zata rasa damar ta wannan shine dalilin da ya sa ta kasa yi masa dogon jan aji tsoron ta kar a janye ta,ya damar ga wuce mata har abada. Figar motar yayi da gudu suna barin Unguwar da ta ke ko ina tsiit saboda zaman ta ta masu kuɗi domin babu talaka a cikin unguwar sai yan kaɗan idan ma akwai. Suna hawa kan titi ya dube ta da kyau yana sakin Shegen murmushi kafin a hankali ya furta. " Ina fatan ba Matsayin mijin ƙawar ki,ki ka ɗauke Ni ba a yanzu,zaki ɗauke Ni amatsayin a bokin kasuwan ci". Shanty da ke sauraren sa cikin ɗan basarwa ta ta ce. " Ban fahimce ka "? Wani banzan murmushi ya ƙara saki irin na su na yan bariki kafin ya ƙara furta " OHK ina nufin zamu zamu yi kasuwanci dake ".Inda ya kai ƙarshen zancen yana sakin wata irin dariya ta shaƙiyanci. Shanty dake sauraren sa ko a jikin ta sai ma share zancen na sa da tayi kafin ta ga damar furta. " Wane irin kasuwan ci kenan ".? Tsare ta da idanu yayi kafin ya karkace baki ya yi murmushi irin na bugaggu sannan A hankali ya ɗaura hannun sa ɗaya akan albarkatun ƙirjin ta da suka buntsulo a cikin rigar a tamfar dake a sake kamar ba ɗinkin yar Musulmai ba. Shafawa ya cigaba da yi da hannun sa ɗaya,a hankali yana lumshe idanun sa hannun sa yake ƙoƙarin turawa a ciki sai dai dakatawa yayi ganin yana neman losing control na shi domin hannun ma ya ƙi shiga saboda yadda rigar ta matse ta sosai.Gashi suna kan hanya kar su faɗa ma wata motar. Driving ya cigaba da yi yana sauke numfashi yana driving a slow kamar wanda ƙwai ya fashewa. Ita kam Shanty da idanun ta ke rufe kasancewar ta fara enjoying yanayin na su sai bata hana shi ba dama abun da ta daɗe tana mafarki ne yau gashi yana faruwa da gaske.Idanun ta ta buɗe tana bin titi da kallo kafin ta ɗan saci kallon Tanim dake driving bata son ya ga wallen ta wuri. Shi ya sa ta kame.Shi ko Tanin dake driving juyowa yai ya kafe ta da jajayen Idanun sa da suka ƙanƙance lokaci ɗaya kafin ya kece da wata mahaukaciyar dariya.Sai da ya gaji dan kan sa. Sannan ya furta. " Common Jor Bana son pretending Malama,na san kin san kasuwancin da nake magana a kai,I see how you enjoyed it " " And Na san abun da kike buƙata kenan tun farkon zuwan ki gidan nan,ina lura da yadda kike bina da kallo har dai daga baya na fahimci kema yar hannu ce,so babu wani maganar kunya,I know babu tan ta ma babu kunyar ". Yana kai ƙarshen zancen ya kece da wata mahaukaciyar dariya wadda tafi ta ɗazu. Shanty dai bata iya furta masa komai ba duk da ta na jin sa sai ma share shi da tayi kamar bata san zancen da yake yi ba sai dai kasan ranta taji daɗi saboda komai ya zo mata a sauƙaƙe,duk da taji Haushin kira mata Mara kunya da yayi. Sai da suka yi yar tafiya mai ɗan tsayi ba tare da ɗaya ya ce ƙala ba sai ma volume na waƙa da suka cika motar dashi. " A ina zan Ajiye ki gida ko,A Hotel "?. Ya furta yana ƙara wa idanun sa girma da sunka ƙara yin wani irin jaaa na jarabar dake tattare da shi mai cike da azaba a gobe a ƙiyama. Kyaɓe baki Shanty tayi kafin ta furta. " Me ka tana dar mini a cikin hotel ɗin da kake ta azarɓaɓi haka? ". Shanty tayi furucin cikin halin ko a jikin ta.Tana zuba masa idanun ta da suka sauya itama irin na jarababbun matan nan. Yar ƙaramar dariya yayi sannan ya furta mata. " kina son gani ". Kai ta gyaɗa masa tana wani juya idanun ta kafin a hankali ta sauke wata irin ajiyar zuciya burin ta zai cika domin ta ƙwallafawa ranta Tanim ta san cewa yafi fiye da yadda ƙawar ta ke bata labari Dan haka ta dauki Alwashin ko ta yaya sai ta samu shiga rayuwar sa ta ɗanɗana zumar shi kafin ta cigaba da bin rayuwar sa har lokacin da ta ji zata samu cikar duka burin ta akan sa.Zancen ƙawar ta ma baya gabanta tafi son ta bar ta cikin gidan ita da kan ta ta kori kan ta domin ta san barikan cin ta bazai taɓa barin ta zama a gidan ba. Har suka isa ƙalon City king Hotel babu wanda ya furtawa ɗan uwan sa ƙala face Kowannen su na sarrafa zance shi kaɗai a cikin zuciyar sa. Farin ciki Tanim yake ji kamar ya faɗawa mutanen gari domin yau take sallah a gare sa babu a bun da yake hasasowa a cikin idanun sa yadda surar Shanty zata kasance,a lokacin ya ƙara tabbatar da yadda yake kwaɗaice da ita sai dai yayi farin ciki sosai samun ta ta hanya mai sauƙi ba kamar ƙawar ta ba da ta sanya masa taurin kai har ya kai ga rashin zaɓi dole sai na Auren ta,duk da ya ga Yar hannu ce ya ɗan yi Mamakin yadda ta bada kai da

Chapter 14 of 39