sa ban sake ta ba tun farko,me ya sa ban ja wa igiyar layi ba tun farko ?
Wayen nan tambayoyin sune yayi ta jefawa kan sa.Sai dai babu mai bashi amsar su.
Wani irin tausayin Nadiya da abun cikin ta ya taso masa hakan ya sa bai ma shiga ɗakin nata ba kamar an tsikare shi ya miƙe ya fice.
Ficewa yayi daga gidan bai zame ko ina ba sai inda gidan da abun tsafin na su yake da bokan na su da yake ɗaure musu.
Yana shiga ya tarar da Babu kowa a gurin sai jini dake a jiye a kusa da bokan.
Wanda ke zaune a ƙasan tiles ɗin ɗakin da ya zama kamar bola dan haɗaɗden ɗaki ne sai dai sun halaka shi da tarkacen tsafi.
" Tausayi a zuciyar ka,zaka lalalata komai,Zaku kunya ta kai da yan uwan ka,Kuɗin da ka tara namu zasu ƙone,Akwai alamar rushewa a tattare dakai,Ɗan buhun bura uba,Ungo Nan ka sha jinin ƙwarangwal,Tausayi ya bi ta kudu ka bi gabas Tanimuuuuuuu ".
Tanim dake cikin tashin hankali da sauri ya kafa bakin sa akan ƙwaryar da bokan na su ya miƙa masa wanda ke zaune a kusa da wata irin halitta jini ta ko ina jikin sa babu kyan gani ga dariyar da aka fara a hankali har tayi ƙara sosai ta ka raɗe ɗakin.
Tass ya shanye jinin sannan ya sauke ƙwaryar Dan ba wani abu bane a gare su shan jini ko shaye shayen su ya ɓace suna zuƙar na su,na kan su.
Yana gamawa bai ce masa ƙala ba haka shima sannan ya sanya bakin tissue ya goge bakin sa tare da yin gyatsa ta ƙoshi.
Dariyar ƙeta Ce ta ƙara fitowa kafin a kara furta " Ƙwarangwal taji daɗi babu kai babu Tausayi ko na uban ka ne,ka cigaba da zuba iskan cin ka mun ɗaure maka ".
Ana kai ƙarshen maganar ba,a ƙara cewa komai ba haka shima bokan dake zaune ya koma kamar babu rai jikin sa.
Wannan shine abun da ke zare musu duk wani tausayi shiya sa ko wajen Kwanciya baya Tausayin Nadiya,ko kaɗan haka yake komai kamar wani mugun azzalumi,Shanty ma haka take fama wanda ita bata ɗauke shi komai ba face ma ta saka shi a layin sa,ar ta, Dan irin mijin da take nema kenan.
Ganin haka ya sa Tanim ficewa da sauri yana fita bai zame ko ina ba sai gidan na sa inda Nadiya.
Yana shiga Kamar yadda yayi zato bata cikin falon,bai bi takan ta ba sai ya shige bedroom ɗin sa.Yana shiga ya faɗa toilet sai da ya ɗauki lokaci sannan ya fito bayan yayo brush da wanka Sannan ya fito.
Writer POV
Tanim dai bai san Qungiyar su na tare da wannan allon tsafin ba sai da ga bayan nan ya sani wanda kwata kwata bai wuce bayan bikin su da NADIYA ba,Duk kannin su suna ciki team ɗin na su sai dai bai sani ba sai da suka mishi tayi ya karɓa,shine abun da ya ƙara hargitsa shi sai ya zama na bayan neman mata harda homo ya kaɗa kan sa,inda duk wani iskancin na su suna ganin an ɗaure musu shi,ada ko sallah Tanim yana ɗan kwatantawa yanzu kuwa komai ya ƙara daƙushe masa,Komai na shi kamar ya ƙaru neman matan haka,maza ma,tafiyar shi Turai,da Shanty kuwa Allah ka ɗai ya san uwar da aka tsinana sai dai duka babu Alkhairii a ciki,duk da haka kuma shanty bata damu ba,dan wata rana a gaban ta ma yake gudanar da komai na sa,Da ƙaton sa,kuma mafi yawan karuwin nasa turawa ne,mace ce bata yarda ta gan shi da ita ba ko wace ce saboda yadda take jin kishin sa.✍️
***
Babatun Sallah bakomai ya faɗa kan gadon sa yana kwantawa bacci mai nauyi ya kwashe sa.
Bai farka ba sai da aka gama kiraye kirayen Sallar la,asar sannan ya miƙe yana miƙewa ya faɗa toilet yana fitowa ya jera sallolin sa kamar wani salihin bawa ya daɗe zaune akan carpet kafin ya miƙe yana naɗe carpet ɗin ya faɗa ɗakin Nadiya.
Nadiya dake zaune akan gadon ta wadda bata daɗe da yin Sallah ba ta ɗaga kan ta ta dube shi,Sai dai kamar bata gane shi ba.
Mamakin wanda ke wurin ne ya sanya ta ɗan ƙara kallon sa,sai dai a kallo na biyu ta ƙara tabbatar da shi ɗin ne.
Hakan ya sa ta sauke kan ta ƙasa ba tara ƙara kallon shi ba,sai cigaba da pressing wayar ta ta.
Wata irin mahaukaciyar dariya ya kece da ita.
Yana dosar ta ita kuwa Nadiya duk yadda take jin faɗuwar gaba ta kasa motsawa ta Kara kallon shi.
Hawa kan gadon ya yi yana kallon ta bakin shi ɗauke da murmushi wanda ke nuna zallar ƙetar da ya shigo da ita.
Hancin sa ya fara bin jikin ta da shi yana shaƙar ƙamshin da ta burbuɗa a jikin ta yana yi yana zuƙar numfashi kamar wanda yake neman ra sa shi gaba ɗaya.
Ƙala Nadiya bata ce masa ba ko yin dogon motsi sai ma hannun ta da ya kasa iya taba wayar sai ma gefe da wayar ta faɗi A kusa da ita.
Sai da ya gama sunsinar ta sannan ya sauke dogon numfashi yana kafe ta da idanun sa da suka sauya masa lokaci ɗaya dan wata irin wutar ce ke ruruwar ma sa ta sha'awar ta,lokaci ɗaya.
" Cikin nan bazan karɓe shi ba,ban shirya zama Da yaya ba dan haka ki yi gaggawar zubar dashi kafin nayi na wa aikin ".
Shine furucin da ya ratsa Kunnuwan Nadiya wanda sune kuma sanadin buɗe idanun ta da suka sauya mata yanzu cikin tashin hankali haka ta watsa mishi wani irin mugun kallo wanda har sai da Tanim ta ɗan razana.
Hawaye ne suka wanke fuskar ta take wayen da bata san da fitowar su ba.
Bata san yaushe ya san da cikin na ta wanda ba wani sosai ya bayyana ba sai idan tana tsaye ne zaka ga ɗan tudun,Amma sai gashi taji kalmomin dake shirin hargitsa mata ƙwaƙwalwa,a kullum tana zullumin yadda zata fuskance shi da maganar tayi tunanin ya yi farin ciki da cikin na ta.Sai gashi taji a kasin haka.
Kallon fuskar ta yayi maimakon ta bashi tausayi sai ma sakin mahaukaciyar dariya da ya ƙara yi yana kallon cikin na ta kafin kuma cikin isgili ya matse cikin da iya ƙarfin sa.
Wata irin ƙara Nadiya ta sanya cikin zafin azaba saboda cikin ya fara tauri.
Bai bari ta ƙara sa rufe bakin nata ba ya ya zura nashi ciki cikin wata irin ƙeta yake bin ta da wani irin mugun kiss yana sauke numfashi.
Nadiya dake ta ƙoƙarin ƙwatar kan ta wadda ta samu ɗan ƙwarin jikin fizge kan ta, da mugun ta ya cije mata harshe da ƙarfi wasu hawaye ne suka ƙara silalo mata sai dai fahimtar dalilin samun wannan cizon hakan ya sa ta natsuwa ta daina ƙoƙarin ƙwatar ta kan ta.
Sai ruwan hawaye dake silalo mata domin duk wannan abun bai dame ta ba irin zancen cikin na ta wanda ta san duk abinda yake faɗa iya Gaskiyar sa ne yake zancen,komai zai iya aikatawa..
Tanim kuwa cigaba da kissing ɗin ta yayi yana lashe jinin da yake fita akan harshen ta da iya ƙarfin sa.Cigaba da jagwalgwala ta yayi kafin kamar an tsikare sa ya miƙe ya fice bai jima ba ya dawo dauke da kwalin hollandia.
Kamar kullum haka ya tuttula mata shi a jiki sannan ya bi da harshen sa wani gurin ma harda cizo yake haɗa mata.
Sai da ya gama suɗe ta tass sannan ya aiwatar da muradin sa.......
***
Kuka take kamar ranta zai fita bayan komai ya wakana tsakanin su,bayan ya gama cin zarafin ta.Idanun ta sunyi luhu luhu luhu kamar da su, ga jikin ta yayi laƙwas ko ɗaga shi ta kasa yi.
Bata san cewa Tanim yayi tafiya ba Amma ta so ace bai dawo gidan ba bayan tsawon kwanakkin da ya share baya gidan.
Maganganun da ya jera mata akan cikin sunfi komai ɗaga mata hankali,ya zata zubar da cikin da ta ƙwallafa rai akan sa,ta sanya buri akan sa,wanda har yanzu bata da wani tabbas akan burin na ta,tuno kalmomin na sa da yake furta wa...
_" Bana son wannan cikin,ki ɗauke shi amatsayin cikin Shege ne kika yi a waje,ban haɗa komai dashi ba,idan zaki cire shi kafin ya bayyana ki cire shi hakan shine samun maslaha a gare ki,A gobe goben nan kije ki cire shi idan ba haka uƙuba da azaba zasu dawwama a gare ki,hutun da kike samu da kuɗin da kike kallo zasu rinjaye ki,Zan ajiye Miki kuɗin da zasu kai har inda zaki samu mai cire wannan banzan cikin da kike kira nawa "._
Kuka ne ya kubce mata bayan tuno da kalmomin da suke ƙara ratsa zuciyar ta da gangar jikin ta suke shiga cikin zuciyar ta suna samun gurin zama.
Wayar ta ta janyo da niyyar kiran wayar Najiba sai dai ta kasa yin hakan sai ma kukan da ya ci ƙarfin ta.
Jefar da wayar ta yi kan gadon sannan ta miƙe a hankali ta faɗa toilet bayan gama cin kukan na ta da ya kasa samun control.
Tana fitowa wankan ta kabbara Sallah raka'a huɗu tayi ta isha ta sallame sannnan tayi shafa'i da wutiri tayi Addu,oi tana yi tana kuka har dai kukan ya kai ga rinjayar ta,haɗe kai da gwiwa tayi tana rusar kukan.
Tana cikin wannan kukan bacci ya kwashe ta mai nauyi.
Bata farka ba sai guraren Asuba haka ta miƙe jikin ta duk babu daɗi ta faɗa toilet ta ɗauro Alwallah tayi Sallah sannan ta sake yin wani wankan.
Tsaff ta shirya cikin atamfa wadda ya sha ɗinkin bubu da zane plain kayan sun Amshe ta sosai,tayi ɗaurin nan mai rufe kai gaba ɗaya wanda ake sake jelar shi a kan wuya.Sai dai da ka kalli fuskar ta zaka san tayi kuka bana wasa ba kuma tana cikin damuwa.Tana zama tunannin maganar sa ya dawo mata inda take hawaye suka wanke fuskar Nadiya.
Ɗan muskutawa tayi daga bakin gadon tana sauke a jiyar zuciya baccin safe taso tayi sai dai ta kasa saboda yadda ta matsu safiya ta idasa waye wa ga kuma Damuwar da take ciki wadda har take jin ciwon kan ta na neman tashi wanda ya ɗan shafa mata lafiya kwana biyu.
Wazata faɗa ma Damuwar ta,wazata faɗa ma yadda take ji a cikin zuciyar ta,Mahaifiya ta. Ta furta a hankali abayyane murya a karye.Kai ta girgiza da sauri hawaye na ƙara wanke mata fuska,ko gidan ta hana ta zuwa.Bare ta taje chan ta Share mata hawaye,a duk lokacin da ta je sai ta azalzale ta kar mutan unguwa su zata sako ta a kayi ta daina zuwa gidan gaba ɗaya sai zata dawo wanka.Hakan ya sa gaba ɗaya Nadiya ta daina zuwa gidan.Gashi ko awaya ta kira ta magana ɗaya ce ta ƙara kame ƙafar mai gidan su ci arziki da kyau,bata ko bari ta ji ko NAJIBA'r na da wata matsala,amma haka zata saka ta da zancen cin dukiyar Tanimu ,Bayan sun gama gaisawa shiya sa ko kiran ta kasa yi mata yanzu,Itama haka sai da ta sami cikin nan ne ta gan ta bayan taje ganin ta a sibiti da kuma gidan sai kuma ɗan yawan kiran taji ya jikan ta yake,Bama ta ta ta take yi ba.Tuno hakan ne ya san ya hawaye ƙara wanke mata fuska inda ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Duk yadda yar uwar ta ta so tayi amfani da kisisina ta ya mace ta kasa saboda Tanim ba natsatsatse bane,yadda take gani ya riga yayi Nisa,yo Ina ma ta gan shi bare ta fara aiwatar da aikin ta,koda ta aiwatar bata tunanin ya shiryu ya daina abubuwan da yake yi,koda ya shiryu ta san abu ɗaya ne zai masa wahalar dainawa saboda yadda ɗabi'ar ke shiga jikin masu aikata ta tana da wuya mutun ya sauya ba tare da ya ɗirki maganunnuka ba wayen da har yanzu babu tabbacin sahihancin su,duk da Ance suna cire tsutsar jarabar dake cin jikin masu aikata ɗabi'ar.
ALLAH ya kare mu da ga faɗawa munanan ƙaddarori.
Ka raba mu da aikata Zina, luwaɗi maɗigo gamsar da kai.🤲🤲🤲🤲
Allah ka nisan ta mu da faɗawa wayen nan manyan kaba'irori.🤲🤲
A ɓangaren Tanim kuwa yana fita kowan ka baiyi ba ya fice daga gidan gaba ɗaya bayan ya ajiye ma Nadiya kuɗin da ya faɗa.Bai zame ko ina ba sai gidan shanty a chan ma sai da suka yagalgala juna sannan bacci ya kwashe su nan.
'''''''''''''
A gaban idanun ta safiya ta waye hakan ya sa da sauri ta miƙe mayafi ta ɗauka da jaka sai wayar ta,kasancewar ta tana da yan kuɗaɗe a hannun ta hakan ya sa bayan fitowar ta bata bi takan kuɗin da ya ce zai ajiye mata ba.Bata tsaya neman driver ba duk yadda suke da tulin motoci a garage ɗin,motocin kuma ba ƙanana ba.
Ficewa tayi daga gidan mai gadi na ɗaga mata hannu,wanda ke cikin ɗan mamakin fitar Tata,ga shi kuma ya ga ta ki neman driver bare a kira mata shi.Itama hannu ta ɗaga masa cikin ɗan sakin fuska saboda dattijo ne mutumin tana ganin girman sa sosai tana jin shi kamar su malam Rabu'u.
Tana sakar mishi fuska su gaisa cikin mutun ta juna.
Tana fita ta tare napep tana faɗa masa inda zai kai ta ta faɗa ciki.
A daidai wata private hospital ta tsaya tana biyan mai napep ɗin ta faɗa cikin asibitin.kasancewar private ce babu cunkuso hakan ya sa bata tsaya jira ba ta shiga ɗakin ganin likita.Cikin sa,a kuma ta samu likita mace a gurin yar dattijuwar.
Murmushi likitar tayi bayan gama sauraren ta sannan ta dube ta da kyau ta san cewa akwai yarinta kan Nadiya saboda bata wani tsaya duba zancen na ta ba kawai ta furta.
Ɗan kallon ta Nadiya tayi kafin tayi ƙasa da kan ta,cikin jin nauyin matar da ya same ta haka kawai.
" Ina son Aɓoye mini ciki na kar ya fito kowa ya gan sa har na haife shi "Wadda tayi furucin bayan faɗa mata cikakken sunan ta,sai dai ta kasa faɗar sunan Mijin ta a matsayin Na Tanim sai ta bada sunan ya Sayyid.
" Haihuwar fari ce halan? ".
Cikin son tabbatar da zancen Nadiya da ta furta
Matar ta furta cikin sakin murmushi.
Kai Nadiya ta gyaɗa mata cikin ƙara yin ƙasa da kan ta.
Kai Likitar ta jinjina kafin ta ƙara furta.
" Waya ce Miki ana ɓoye ciki a Asibitin,Likita baya iya ɓoye ciki, Dan hana ganin girman sa,sai dai mu cire ciki,kuma mu Bama irin wannan a aikin a cikin wannan a asibitin ,idan ma kunyar surukan ki kike ji,ki kwantar da hankalin ki,kowa ya san menene silar cikin,kuma Baga re ki farau ba ya ta,and kuma Bana Shege bane,so you have to relax kinji,ki bari cikin ki ya fita kowa ya gan sa ya san kin girma kema kin kusa zama uwa,ko bakya son a riƙa kiran ki da Umma ".?
Ta kai ƙarshen zancen tana sakin ɗan guntun Murmushi dake nuna sakewar ta ga Nadiya ɗin.Duk da furucin ta na ƙarshe ya tayar mata da wani irin Miki da take ta riƙewa tsawon shekaru.Sai dai bazaka iya gane hakan ba.
Sai dai ganin hawayen fuskar Nadiya da ta ji kalmar cikin Shege wadda ta tayar mata da mikin maganganun Tanim loka ci ɗaya ga wani irin tsoro da ya shige ta.
Wani irin kuka ne ya taso mata wanda ta kasa riƙewa lokaci ɗaya.
" Subhanallahi me ya faru Nadiya,daga magana sai kuka ".
Shine abun da Dr. Abida Abubakar take furtawa.
Da ƙyar ta samu ta rarrashi Nadiya tayi shiru.
Sallama Nadiya tayi mata dan ta kasa faɗa mata abin da ke damun ta kai tsaye kuma ta kasa yanke hukuncin zubar da cikin kamar yadda Tanim ya furta mata.
Haka Dr Abida ta yi sallama da ita cikin tausayi ta Dan ta san baƙaramin abu ne ya saka ta kuka haka ba,dabadan ta faɗa mata tana da Aure ba ai da sai tace Cikin bana hanyar Sunna bane,Sai dai har sunan mijin na ta ta sani.
Haka ta kasa ta koma ta zauna cikin Tausayin Nadiya da bata wani san ta ba sai yanzu wanda lokaci ɗaya taji ta shiga ranta tana jin ta kamar "ya yan cikin ta.Duk da kasancewar ta cewar tana da Yayan itama amma sai taji tana son ƙarin Nadiya a cikin zuri'ar ta,ta zamo cikin ta bakwai a cikin ya yan ta mata.
Tunanin da ya taso mata ne ya sa ta miƙewa zuwa zagayen patient tana sauke Ajiyar zuciya.
NADIYA kuwa tana fita gidan ta koma sai dai har ya kai bakin gate taji ta kasa shiga sai ta ƙara tarar napep ta shiga. Rijiyar lemu ta bashi amsa bayan tambayar ta ina zai sauke ta jin tayi shiru ga hawaye na tsiyayar mata Wayen da take ta ƙoƙarin dakatarwa domin bata son shiga haka ta ta yarwa yar uwar ta da hankali da Iyayen ta maza da ta san da su zata fara cin karo a ƙofar gidan.
Sun ɗan yi tafiya kaɗan sannan ya sauke ta a daidai ƙofar gidan nasu da kwatancen da tayi masa.
Kuɗin sa ta ciro ta bashi kafin ta fito tana masa godiya
Har ƙasa ta duƙa ta gayar da iyayen na su wayen da ke zaune suna shan hantsi da ya fito hankalin su kwance suna ɗan taɓa fira.
Tun dosowar ta gurin suke bin ta da idanu har ta kai ƙasa.
Kallon ta suke cikin wani irin mamaki da tausayin ta da ya dirar masu lokaci,Mamaki kuwa na son kashe su dan har su malam Adamu dake gurin yau ta gayar sai farin ciki ya kama su Nadiyar su ta da ce ta dawo Dan haka suka tashi da tarbiyyar su kafin duniya ta buɗe musu ido su rungume ta da iya ƙarfin su.Sai dai kuma farin cikin na su ragagge ne kasancewar ganin yadda fuskar ta tayi jaaa abunka da farar mace Dan duk ta fisu haske saboda fatar mahaifiyar ta ta kwaso Dan jawur haka fatar Mama Hafsatu take.
Har ta shige bayan sun amsa mata basu daina bin ta da idanun su ba ɓacewa ganin su ne ya sanya su sauke numfashi mai nau yi kamar wayen da wani nauyi ya taushewa zuciya zukatan su cike da tsoro dan yadda duk ta haɗa idanu da su ne tana ƙoƙarin ɓoye kukan da ke taso mata sai hankalin su ya ƙara tashi,sai hakan ya tabbatar musu da akwai Babbar Matsala...
Hmmm Allah NADIYA duk ta kashe mini jiki😂😥😩
Tausayi take bani.😥
Idan zan saka yadda nake Tausayin ta sai na cika shafi.🤦🥺
Jama'a wace ce wannan likitar Kuma?
Kamar tana da Tata matsalar itama?
Muje zuwa dai zamu ji komai in sha ALLAH.
💋Daga Alƙalamin✍️fa'eeh bg💋
ALLAH KA JIƘAN MAGABATAN MU.🤲
ALLAH KA SA MUYI KYAKKYAWAN ƘARSHE.🤲
Ƙarin bayani,ko bada shawara ga maruciya.
*08069059746*
Chat only.
*_Typing_*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*TAFIYAR TAURARI HUƊU*_
⭐⭐⭐⭐
_*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_
_*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_
*Taurarin marubuta huɗu masu aiki da hazaka,da zallar ilmin Adabi*
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.28
Da sallama ta shiga gidan sai dai kasancewar ba kowa tsakar gidan hakan ya hana ta samun Amsa Sallamar ta wadda ta yi ta sama sama.
Direct ɗakin Mama Hafsatu ta nufa da sallama ta faɗa ciki.
Mama Hafsatu dake zaune kan taburma tana ɗan sauraren Radio ne ta tsayar da shi tana zuba mata idanu kamar mai son fahimtar wani abu.
Nadiya kuwa bata kula kallon da take bin ta dashi ba fahimtar ko na mene sai ma ƙoƙarin zama da take yi a kusa da ita tana sauke Ajiyar zuciya.
Tana zama ne ta gayar da mahaifiyar ta ta cikin ɗan sake fuska sai dai bata samu karɓa gaisuwar Tata ba sai ma zancen da ta jefo mata wanda ya sanya hawayen da Nadiya ke riƙewa silalowa a take.
" Me ya sa bakya ji Nadiya,nace kibar zuwa gidan nan,ba kya ji ke baki san gulmar yan unguwar nan ba ne,yanzu za,a fara tallata kin dawo gida an sako ki kamar yadda aka saki Najiba ".
Hawayen ta share masu zafi sai dai bata iya furta komai ba,sai zura mata idanu da tayi Cikin wani mamaki Jin tana furta " Ki tashi ki koma.gida ko ma,mene ne matsalar zai wuce,bana son ki muna baƙin ciki da cin arzikin mu ,sannan ki kula min da jikana,kar ki yi muna asara gurin sakarcin ki ".
Murmushin da ya fi kuka ciwo ne ya suɓuce ma Nadiya jikin ta yayi sanyi domin ganin ta ke yi kamar mahaifiyar ta yanzu ta daina son ta kwata kwata yanzu ta zo Dan ta samu Rarrashi baƙin cikin da ta kwaso ya rage mata ta ƙara daɓa mata wani Miki.
Wani irin Tausayin kan ta ne ya ƙara kama ta wanda ya sanya take hawaye wanke mata fuska,ganin ko tambayar me yake faruwa taka sa, samu bare ta samu Nasiha bayan jin ba,a sin zubar hawayen na ta.
Ta fara ƙoƙarin yin magana sai dai kuka ya ci ƙarfin ta hakan ya sa mama Hafsatu miƙewa ta shige ɗaki ta laɓe bakin labule tana leƙo ta kaɗan.
Sai dai ganin yadda Nadiya ke kuka kamar wadda ranta zai fita haakan ya sanyaya mata jiki ta fito tana zama a kusa da ita tana rarrashin ta tana furta.
" Haba ɗiyar Albarka ,Kukan ya isa haka,idan faɗa ku kayi kiyi haƙuri kinji,ba komai bane ki koma ɗakin mijin ki,Idan An zo haihuwa ba sai ki daɗe gida ba, Dan Nasan kewa ta ce kika yi yar Albarka ".Takai ƙarshen zancen tana sakin murmushi.
Nadiya kuwa kamar ana ƙara mata giyar kukan ta har yi take yi kamar zata shiɗe.Haka take kukan tana janyo numfashi da ƙyar saboda yadda wasu maganganun masu ƙuna suka ƙara ratsa Kunnuwan ta suna zuwa direct ga zuciyar ta da take mata wani irin mugun zafi.
Sai da tayi mai isar ta sannan ta sauke A jiyar zuciya tana raba jikin ta da na mahaifiyar ta.
Mama Hafsatu ma jiki a sanyaye take duban ta ta san lamarin Babba ne Sai dai ba zata taɓa yarda su kubce ma damar su ba dan haka ba za ma tabar ta ta faɗi a bunda take son faɗi ba zata Rarrashe ta a hakan.Numfashi ta sauke tana tsayar da zancen zucin na ta,Kafin ta furta.
" Kiyi haƙuri Nadiya,ki kai kukan ki ga Ubangiji,komai zai wuce zaku shirya,kuma,bana son jin wani labari ya biyo baya kin ji ko ".
Mama Hafsatu ta furta kai tsaye,cikin Rashin nuna damuwar ta a fili.
Nadiya bata iya cewa komai ba Sai kai da ta girgiza ma mahaifiyar ta da har yanzu take jin kamar ta daina son
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 39