Share this page
8 / 10
ya ɗan rage buɗewar hannayensa ya ce" Ina fata za'a duba maganar Dad, na barku lafiya." Daga nan ya miƙe ya juya a nutse ya ficewarsa a ɗakin ya barsu baki buɗe, ba ma kamar Dad da hankalinsa ya so tashi ya shiga tunanin to ko dai yaron nan bai bar aikin sojan nan na fitina ba? Ta ya yasan hakan? Bayan shi dai iya mahaifiyar su ne kaɗai tasan daga ina kuɗin ke shigowa sahihanin zance, sai kuma ƙannensa da suma yana tura musu saboda kar su ce an ware su. Daga nan asibiti ya nufa, a ƙofar asibitin ya aje motar sa ya ƙaraso wurin mai gadi, duk da ba zuwa yake ba idan babu dalili mai ƙarfi, amma dai ya san ko wanene Aswan, dan haka ya tarbe shi da girmamawa suka gaisa, gyara tsayuwar shi ya yi daga nan yana kallon mai gadin yace "Malami, kai ne a bakin aiki kwana huɗu da suka wuce?" Jinjina kai ya yi yace "E yallaɓai, ni ne kasancewar kwana bibbiyu ne muke yi ni da abokin aikina." Gyaɗa kai AA ya yi irin yawwa ɗin nan sannan yace "A ranar da dare, za ka iya tuna motar ujila nawa ce ta fita daga asibitin nan ko kuma ta shigo?" Shiru ya ɗan yi yana nazari kafin daga bisani yace "E to yallaɓai, gaskiya da dare dai ambulance biyu ta fita, ɗaya ana sallah isha'i ta fito ta dawo da majinyaci da suka yi haɗari, sai ɗayar kuma cikin dare sosai, dan ina gyangyaɗi ma ta yi oda na buɗe musu ƙofa suka fita." Jinjina kai AA ya yi yace "Ok, kuma wa ye yake tuƙa motar da ta fita tsakiyar dare?" Ba tare da wani ɗar ba ya bashi amsa da " *Mani* ne yallaɓai." Jiinjina kai ya sake yi tare da bashi hannu suka gaisa yace "Nagode sosai, zan tafi, sai anjima." Da gayya ya nuna masa zai tafi, sai kuma ya ɗan dakata yace "Ko Manin ya na ciki ne?" Da sauri ya amsa mishi da "E yallaɓai, dukansu ma zaka same su acan sashin su dake kusa da sashen tsananta kula." Sai kawai ya shiga ciki gadan gadan, hakan ya sa ba kowa ya san Aswan Aliyu Anza ya shigo asibitin ba, kai tsaye kuma can ɓangaren da zai samu Mani ya nufa kan shi tsaye. *_SAJEERAH_*🖊️ *Alhamdulillah.* 23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕 *WATA TAFIYA* 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕 _RUBUTAWA, TSARAWA_ *SAJIDA NIJAR* _TARE DA_ *SAMIRA HAROUNA* _VIVE LE NIGER_ 🇳🇪 *LITTAFIN KUƊI* _Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._ _*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._ _Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._ _'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._ _Bismillahir rahamanir-rahim_ *9* Cikin wata ƙatuwar rumfa ya samu drebobin har da dreban Dr. Hamat, sallama ya musu duk suka gaisa, kafin ya tambaye su "Dan Allah Mani fa?" Manin da kan shi ne ya amsa yana mai ƙarewa AA kallo, murɗaɗɗen jikin shi dake ɓoye cikin manyan kaya, shigar shi da fatar shi duk sun nuna ba ƙaramin mutum bane, kuma shi dai bai da wani laifi da yake aikatawa ko ya aikata da zai ji tsoron bayyana kan shi, dan haka ma ya miƙe ɗin suka keɓe kamar yadda AA ɗin ya buƙata. Ba ya son jan magana, dan haka kawai ya je ga gundarin magana ta hanyar faɗin "Malam Mani, kwana huɗu da suka wuce an tabbatar min kai ka ja motar ujila da aka fita da ita da dare daga asibitin nan, shine nake so naji me ye a cikin motar? Kuma ina ka kai abun cikin ta?" Duk da bai san komai ba, amma yadda ya tambaye shi ɗin sai gaban shi ya shiga faɗuwa, a daddafe yace" Yallaɓai ban san komai ba, ban san me ye a cikin motar ba nima." Ɗan duƙar da kai AA ya yi, a sakanni kuma ya ɗago fuskar shi a kausashe ya kalli Mani da yanayin da babu wasa ko fara'a a ciki yace" Kar ka min ƙarya Mani, hakan zai hassalani gaskiya, ka faɗa min me ka ɗauka kuma ina ka kai abinda ka ɗauka? Masaniya gareni mai ƙarfi shiyasa har na zo nan." Cike da tabbaci Mani yace" Wallahi yallaɓai ban san ko menene a ciki ba, abinda zan iya cewa kawai bayan ma an kusa gama loda kwalayen ne aka tadoni dan har na fara bacci, ina zuwa makullin motar aka ban aka faɗa min asibitin da zan kaita, iya abinda na sani kenan." Wani kallo ya masa kamar harare yace" Su wa suka ɗora kayan a wannan lokacin?" Da inda inda yace" E to, biyun dai ba ma ma'aikata bane a asibitin nan, sai kuma dreban oga (kawu Hamat)." Da mamaki AA ya dube shi yace" Ba ma'aikata bane? Su waye kenan?" A hankali Mani yace" Gaskiya ba ma'aikata bane, sai dai lokaci lokaci sukan zo nan wajen oga, musamman ma ranar juma, kusan duk juma'a ma tare da su muke zaman nan, jefi-jefi yakan kira ɗaya daga cikin su ya aika." Hannu AA yasa yana murza goshin shi tare da jinjina kai a ranshi yana ayyana" Dreban oga? Sani kenan?" A ɗan dubarance ya karkata dan ya kalli Sanin, amma ikon Allah sai ya kama shi yana kallon su irin kallon ƙurilla na son gano ko jin me ake tattaunawa, bai yarda ya ƙarasa juyawar ba kawai ya basar yana wani irin shegen murmushin gefen laɓɓa. Cikin tsareshi da idanun da da yasan yadda yake ji da yake masa kallon nan yace" Me ye a cikin kwalayen?" Girgiza kai ya yi da rashin tabbaci yace" Gaskiya yallaɓai ban sani ba, amma dai bana raba ɗayan biyu cewa kwalayen magunguna ne." Taɓe baki AA ya yi yana kawar da dubansa gare shi yace" Dama kuma ka saba ɗaukar magunguna zuwa wasu asibitocin?" Jinjina kai ya yi yace" E akan yi hakan, tunda idan aka yi odar kayan aiki ko magunguna muna zuwa mu ɗauko, wani lokacin kuma Pharmacie asibitin nan takan siyarwa da wasu asibitocin kaya, saboda ko shakka babu asibitin nan ita ce ta farko wajen ajiye kayan aiki da magani." Wani shaƙiyin kallo AA ya mishi yana ɗaga gira sama yace" Wace asibiti ka kai motar?" Ba tare da shakku ba yace" Asibitin koyarwa ta Alhaji Saddi Ja." Cikin jinjina kai AA ya ɗan shiga juyawa yana ambatar" Saddi Ja?" Abokin mahaifin shi ne, to me kenan hakan yake nufi? Mota cike da kuɗi, an kaita asibitin abokin mahaifin shi? Ya salam! Ƙwarai wani lokacin ya kan ji kamar ya dakatar da abinda ya fara, saboda idan ya ji wani sai ya dinga jin abu kamar tsoron inda binciken nan zai kai shi, sai kuma ya ƙwarara kan shi tare da ba wa kanshi ƙarfin guiwar ci gaba. Kallonshi ya yi yace "To amma da ka kai motar ba gaban ka aka sauke kayan ba? Sannan ka juyo da motar?" Da tsanaki Mani yace "Abun ma da ya ɗan ban mamaki kenan, dan oga cewa ya yi na kai motar na baro acan da safe za'a ɗauko, abinda bai taɓa faruwa ba kuma sai a ranar." Shiru AA ya yi yana nazarin abinda Mani ya faɗa masa, kafin daga bisani ya mishi sallama tare da godiya ya fice a asibitin ba tare da kawun shi ya san ya zo ba, Sani kuma zai dawo kan shi, amma yadda ya ga yana kallon su yasan ya fahimci wani abun ne, dan haka ba yanzu zai ritsa shi ba, sai lokacin da yake bille-billen neman tsere masa, sai ya take wutsiyar sa ya hana guduwa, duk wanda suka ganshi ba su san wanene shi ba idan ba dreban kawu Hamat ba, hakan ma ya sa AA na fita ya miƙe da sauri daga shayin da suke zugawa zasu sha yace yana zuwa. Bai zame ko ina ba sai ofoshin Dr. Hamat, kai tsaye ya shiga duk da babu mai yi masa wannan shigar ƙawarar, amma ko da ya ga Sani ne yasan akwai abinda ya zo mishi da shi, hakan yasa ranshi bai ɓace ba sai ma gyara zama da ya yi yace "Sani, me ya faru ka shigo min haka?" Ba tare da ya zauna ba dan bai da wannan hurumin yace "Oga, akwai matsala fa." Da sauri ya ɗora hannayen shi kan makeken table ɗin shi cikin harshen Sanin wato zabarmanci yace "Wace irin matsala kuma?" Shi ma a harshen nashi da ya fi iyawa yace "Oga, Chairman na gani fa a asibitin nan, kula yana magana da Mani dreba." Da ɗumbin mamaki kawu Hamat yace "Akan me suka tattauna?" Girgiza kai ya yi yace "Ban sani ba yallaɓai, sai dai hirar su ta ɗauki a ƙalla minti ɗaya ko biyu, ina tsoro fa oga." Da jin haushi kawu Hamat yace "Tsoron me? Kawai daga ganin su suna tattaunawa sai ka ce kana jin tsoro?" Da wata irin gurguwar hausa Sani yace "Oga, kasan chairman rigimammen soja ne, ina tsoron shi fa gaskiya, ba ya da kirki ko kaɗan idan aka shiga harkan shi." Da wani malalacin kallo kawu Hamat ɗin yace "Ka shiga harkan tashi ne kai?" Girgiza kai ya yi alamar a'a, dan haka kawu Hamat ya gyara zamanshi cikin lumtsumemiyar kujerar shi yace "Je ka kawai, ka rage tsoron nan kar kasa ma ya zarge ka." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan oga." Jiki a sanyaye ya fita a ofishin sam bai ji nutsuwa ta saukar masa ba, saida ya tabbatar ya rufe masa ofishin sannan ya ƙara ɗagowa daga kujerar da mugun sauri yana rarako idanu yace "Aswan a asibitin nan? Kuma tare da Mani dreba?" Babu zufa a goshin shi, amma saida ya kai hannu saman goshin ya shafa sannan ya ɗauki wayar tangaraho da niyyar kira ya ce a turo masa Mani yanzu yanzu... *Amma* shigowar Yusrah ta dakatar da shi daga hakan wacce ta ƙwanƙwasa tare da yin sallama, a ƙage da jin an takura masa yace "Wa ye? Shigo?" A nutse ta murɗa abin buɗewar ta shiga kanta tsaye, a tausashe ta furta" Barka da warhaka Docter." Wayar da ya taɓa ba ajiyewa ya yi ba dan kuwa ya zama wajibi ya ga Mani direba, hakan ya sa da ɗan yanayin gaggawa ya amsa ta da yawwa. Da kula ta ce" Dama wata mai naƙuda ce aka kawo, cikin ikon Allah har ta haihu shine nace bari in shigo in sanar maka." Sai da ya ɗan yi tsam dan ya gane me take nufi, sannan ya ƙanƙance idanuwansa kamar dai bai gane ɗin ba yace" Me kike nufi?" Yusrah ta ce " Eh da ta zo ne muka amshi haihuwar har ta haihu shine na shigo in sanar maka dan a yi dukkan abinda ya yi saura." Da mugun ɓacin rai ya ce" Kika amshi haihuwar dai! Ke kina da hankali kuwa? Ko me kike taƙama da shi? A kan wani dalili zaki amshi haihuwa a asibitina kai tsaye ba tare da an sanar min ba? Wannan wani irin hauka ne? Ke a wa? Wacece ke? Daga ke har kwalin da kika mallaka na zama likitar banza ne a wajena, saboda wani dalili zaki take min doka?" A ɗan tsorace da yanayinsa ta ja baya kaɗan dan kamar zai shaƙota haka yake masifantarta, murya a sanyaye sosai dan kare kanta ta ce" Ka yi haƙuri Docter ba take dokar ka na yi ba, da aka kawota tuni kai ya bado shi yasa kawai na shige da ita ɗakin haihuwar." "ki min shiru, ki min shiru nace, ko da ace ɗan na yawo a ƙasa aka zo asibitin nan kar ki kuma min haka, kin fahimta?" ya katseta rai ɓace, kai ta sadda jiki a sanyaye ta ce" Ka yi haƙuri in sha Allah ba za'a kuma ba." Rai ɓace ya koreta, ta juya ta fita a sanyaye tana tafiya daidai da nufowar wata kyakyawar matashiya da za ta girmi Yusrah a ƙalla da shekaru huɗu ko biyar ma, fara tas da ita cikin lafaya mai kyau da tsada, tare take da Bilal dukkansu bakunan su a washe saboda farin cikin haihuwar Zahra'u. Tunda suka tunkarota Bilal ke kallonta yana ma matashiyar raɗa da cewa " *Aunty Intisar*, kinga likitar nan? Dan Allah bata dace dani ba? Dan Allah ki mata magana ki ji nutsuwa, wallahi yarinyar ta haɗu." Kallon shi tayi da murmushi tace "Uhumm?" Gyaɗa kai ya yi yace "Allah da gaske nake, ki yi wani abu auntyna." Ƙarasowar su da sukayi ya sa Intisar kallon Yusrah dake jiki sanyaye kamar za ta yi kuka ita tun kallo ɗaya da ta musu ba ta sake ba tace "Sannu sister?" Da sauri Yusrah ta kalle ta, da ƙyar ta ƙaƙaro murmushi tace "Yawwa, sannun ku?" Bilal dake ta kallonta da fara'a ya amsa da "Yawwa likita, ya aikin?" Kafin ta ce wani abu Intisar tace "Sister Docter yana ciki ne?" Jinjina kai tayi tace "E yana ciki." Murmushi Intisar tayi da ya sake bayyana kyawunta tace "Nagode." Kallon Bilal tayi ta masa alama da suje, tuni Yusrah ta raɓasu ta wuce sai Bilal da ya bita da kallo sannan ya kalli Intisar yace "Aunty ya haka kuma? Sai ki barta ta tafi baki faɗa mata ba?" Ɗan hararan shi tayi tace "Kuma haka ake yi aka gaya maka? Kai tsaye sai na ce mata kana son ta? Ka kwantar da hankalin ka, a asibitin nan muka ganta, zan samo maka bayanan ta har na gidan su ma." Tana ƙwanƙwasa ofishin saida ya ja dogon tsaki saboda ya aika kira ne kenan an ɗaga aka sake katse sa, aje wayar ya yi yace" Shigo?" Ganin Intisar da Bilal a bayan ta yasa shi dole ya ƙirƙiro murmushi a fuskar shi yana gyara zaman shi da faɗin" Lalala! My lovely daugther, ke ce a asibitin namu?" Da fara'a sosai suka ƙarasa suka shiga gaishe gaishe, kafin take cewa" Ai aunty Zahra'u matar Yaya Marwan ce ta haihu nan ba jimawa, na ma haɗu da likitar da ta karɓi haihuwar, ita ta sanar da ni kuna ciki, shiyasa na zo na gaishe ku." Da mamaki ya kalleta yace" Dan Allah, ki ce wacce ake faɗa min ta haihu yanzu matar Marwan ce?" " E wallahi uncle." Ta faɗa da fara'a, jinjina kai ya yi ya ɗauki waya yana cewa" Ban sani ba, amma bari na kira nurse Yusrah na sanar da ita ta ci gaba da kulawa da su har zuwa safe da za'a sallame su." Murmushi kawai ta yi bata hana shi ba har saida suka ji ya yi umarni da a turo masa nurse Yusrah yanzu, ci gaba sukayi da tattaunawa har saida Yusrah ta yi sallama ta shigo da tunanin ko me zai faru kuma yanzu? Amma tun daga ganin fuskar shi yana ta dariya shi da su Intisar ya bayyana mata cewa ko dai ƴar sa ko ƴar uwa, duk da babu kama ta fuska akwai ta jini ga kuma suffa, gaishe su tayi da barka da hutawa tana kallon shi dan jin me zai ce mata? Ba kunya, ba tsoron Allah ya kalleta yace "Nurse Yusrah, wannan da kike gani ƴata ce, wacce kika karɓi haihuwar ta kuma matar Yayan mijin ta ce, dan haka ki kula da su sosai da duk abinda suke so har zuwa safe, idan kika zo aiki gobe sai ki zo ki sanar da ni kafin mu sallame su, kin gane?" Da sauri ta jinjina kai tace" To Docter." Har ta juya ya sake cewa" Sannan..." Juyowa tayi tana duban shi yace" Kin yi ƙoƙari sosai wajen karɓan haihuwar nan, dama kuma abinda yasa kenan na ɗauke ki stage anan, ƙwazon ki da hazaƙar ki, ki je nima yanzu zan je na sake duba uwar da ƴar dan na ƙara tabbatar da lafiyar su." Mamaki hana Yusrah magana ya yi, kawai ta juya jiki a saɓule tana magana da kanta da cewa _" To da ba waɗanda ya sani bane ba fa?"_ Saida ta fita Intisar ta kalle shi tace" Uncle stage na ji ka ce? Na ɗauka ai sabuwar ma'aikaciya ce." Murmushi ya yi kawai yace" Tana da ƙwazo ne yarinyar, ai kema kin gani, ita ɗaya ta karɓi haihuwar." Jinjina kai tayi tace" Gaskiya kam." Daga haka suka ɗan taɓa hira sannan suka miƙe, tare suka fito ya je har ɗakin mai haihuwar ya gaisa da maman su Bilal sannan ya ƙara duba su, wasu sababbin magunguna ya rubuta ya ba Bilal ya ce sun fi waccen da Yusrah ta rubuta kyau da inganci sannan ya koma ofishin shi. *AA ANZA* Ya yi niyya ne mai sunan niyya, hakan ya janyo daga asibitin nan asibitin koyarwa ta Saddi Ja ya nufa, sai dai tun daga cikin mota ya saƙala bavet (facemask) dan tuni mai gadin ya yo kan shi yana so ya shaida wanene kafin ya buɗe masa ƙofar. A hankali ya zuge glass ɗin motar zuwa ƙasa, mai gadin na leƙowa yace "Barka da rana yallaɓai?" A tausashe tamkar wani ɗan sarki ya amsa da "Barka." Mai gadin ne ya sake cewa "Yallaɓai ciki za ka shiga ne? Ko wani ake nema?" Wani nauyayyan kallo ya bishi da shi yace "Ko kai na gani ma ba damuwa, ina so na san wani abu ne..." Saida ya ɗauke kai daga kan mai gadin sannan yace "Za ka iya shigowa ciki muyi magana." Shiru mai gadin ya yi yana kallon shi da tunanin ya zai raina masa hankali haka? A wannan zamanin? To amma kuma shi? Wannan tunanin da ya tsaya yi ya sa AA sake kallon shi a tausashe yace "Ba damuwa, za ka iya shigowa, ba abin da zan maka." Dariyar da bai san da zuwanta bane ta kubce mishi, buɗe motar ya yi ya shiga yana riƙe dariyar shi, wacce ba komai ya sa ta zo mishi ba sai duba da yadda yake da yadda AA yake, ko riƙe shi AA ya yi fa tam ba zai iya kubcewa ba, in dai ba ko yana fama da ragonta na rashin ƙwarin jiki da hutu kan sa ƴaƴan masu abun suke tasowa ciki ba, amma jikin AA ma ai bai nuna haka ba. A ɗarare ya zauna yana kallon AA ɗin da shi kuma yake kallon gefe guda, cikin sanyin murya yace "Wani abu nake so na sani, kai kaɗai nasan za ka iya bani amsar daidai, saboda na san duk wani abu da zai shiga ko ya fita ta ƙofar, to da sanin ka ne, hakane?" Da gamsuwar bayanin AA ɗin yace "Hakane yallaɓai, dan ni kaɗai ne mai gadi a wannan makarantar, kuma anan nake rayuwata, iyalina ma suna ciki." A daƙile AA yace "Da kyau, kwana huɗu da suka gabata motar ujila ta asibitin Anza clinik ta shigo nan cikin dare, zan iya sanin a wane ɗakin ajiya aka sauke kayan cikin ta?" Da mamaki mai gadin ya kalle shi, yayin da AA ya yi murmushin mugunta, da gangan ai yake mishi tambaya kamar na yasan komai dan ya ji me zai ce, amma sai mai gadin yace" Clinik Anza? Yallaɓai kana nufin motar da ta zo nan kusan ƙarfe biyun dare?" A yangance ya amsa mishi da" Ita nake nufi." Sai kawai ya yi murmushi yace" Ayya, yallaɓai ai motar da ta zo a wajen ajiye motoci kawai Mani ya ajiye ta ya fito, ya bani makullin ya ce an ce za'a zo da safe a ɗauka idan an gama sauke kayan, to kuma yana bada baya bai fi minti talatin ba sai ga wani ya zo ya ɗauki motar." Lokacin sosai AA ya kalle shi, duk da fuskar shi rufe take da fuske (facemask), amma daga yadda naman gaban goshin shi ya tattare ya nuna ya shiga mamaki ne yace" Aka ɗauke ta kuma? Tun a daren ka ke nufi?" Gyaɗa kai ya yi yace" Tabbas yallaɓai wannan motar ba ta kwana nan ba, hasalima ba ta yi awa ɗaya cikakka ba aka fitar da ita." Da ƙaguwa yace" To wa ya ɗauke ta? Kuma ina aka kai ta?" Girgiza kai AA ya yi yace" Gaskiya yallaɓai ban sani ba, wanda ya zo ya ɗauke ta ban taɓa ganin shi ba ma, ya dai gaya min shine aka turo ɗauka ni kuma na bashi makullin." Duka AA ya kaiwa sitiyari ya furta" Shiitttt!" Tsaki yayi yana kawar da kai ya yi shiru, ranshi ya ɓace sosai, ta yadda ya ji kamar ba zai iya jurar wannan rainin wayon ba, to wai wa ma yake da hannu a cikin wannan abun ne? Ya akayi kuma suka iya ɓadda sawu haka kamar ana bibiyar su ko sun san za'a bibiye su? Da kaushin muryar dake nuna hassalar shi ya kalli mai gadin yace "Shikenan nagode, sai anjima." Da sauri mai gadi ya buɗe motar shima yana godiya ya rufo masa ƙofar sa, tayar da motar ya yi ya juya akalar ta zuwa gida yana jan tsaki kala kala da mita a ran shi, ko abinci bai ci ba ya fito wannan aikin sa kai ɗin, gashi ana ta wani yawo da shi kamar ƙwallo, kuma ba zai yarda ya fara aikata abinda zai karya doka ba, dan a yarjejeniyar su da Chef akwai kiyaye hakan a gare shi da ya zama wajibi, ba dan haka ba da Sani da yake ganin kamar ya san abubuwa dayawa zai ɗauko ya yi ta jibga har sai ya faɗa masa komai... Amma kuma ƙwarewar sa yake so ya nuna ta wannan ɓangaren, dan haka zai je gida ya huta ya samu nutsuwa, zai sake komawa wajen Mani dreba ya tambaya ko an dawo da motar? Idan an dawo da ita wa ya kawota to? Ya san ai ba zai rasa samun wata makamar ba anan ma. *_SAJEERAH_*🖊️ *Alhamdulillah.* 23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕 *WATA TAFIYA* 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕 _RUBUTAWA, TSARAWA_ *SAJIDA NIJAR* _TARE DA_ *SAMIRA HAROUNA* _VIVE LE NIGER_ 🇳🇪 *LITTAFIN KUƊI* _Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._ _*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._ _Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._ _'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._ _Bismillahir rahamanir-rahim_ *10* Haka Yusrah ta ci gaba da kulawa da mutanen nan da bata san komai akan su ba har sanda ƙarfe 06:00 ta yi sannan ta fara shirin tafiya gida, bayan ta gama kimtsawa saida ta zagayen duk waɗanda ya kamata ta duba kafin ta tafi, daga ƙarshe ɗakin da Zahra'u take ta nufa dake su suna vip, da sallama ta shiga ɗakin kuma duk suka amsa mata da fara'a har Aunty Bilkisu

Chapter 8 of 10