na faɗin "Sis Yusrah, ya ɗawainiya?"
Da fara'a ta amsa da "Alhamdulillah aunty Bilkisu, ya baby da maman ta?"
Amsa aunty Bilkisu ta bata da suna lafiya yayin da take nufa wajen gadon tana ɗaukar katin Zahra'u tana dubawa, da sauri kuma ta kalle su tace "Aunty Zahra'u, wai har yanzu ba'a bayar da sunan da za'a rubuta ba?"
Ƴar dariya Zahra'u tayi tace "Mama ki ji wai likita sai ta dinga kirana aunty? Bayan kuma ta girmeni fa."
Yusrah ma dariya tayi tace "Na sani tunda na gani rubuce a katin nan, amma ai yanzu ke uwa ce, Allah ya baki girman."
Dariya dai mutanen ɗakin suke yi, sai dattijuwar da tace ma Yusrah "Sunan ne wai har yanzu suke ta tunani, shi uban ne bai gama yankewa ba, a dole sai ya fara sanin ma'anar suna kafin ya saka."
Murmushi Yusrah ta yi da girmamawa tace "Ai hakan ma yana da kyau Mama, idan ba'a san ma'anar ba sai ayi kwaɓa."
Aje musu katin tayi tana cewa "To, nasan sai zuwa safe ko kuma idan Sakina ta hau aiki sai ta saka, ni yanzu gida zan wuce sai kuma gobe idan Allah ya kaimu."
Aunty Bilkisu ce ta miƙe ta nufi wajen kwanukan abinci da kayan ƙwalam tace "Gida zaki je Yusrah? Ina zuwa dan Allah."
Tana tsaye ta ga tana ta haɗa kayan arziƙi irin wanda ake ta kawo musu suma a asibitin wasu a leda wani a kwano mai kyau, saida ta gama ta miƙo mata tace "Yawwa Yusrah ga wannan ko, kema kya ɗan huta gajiya idan kin je gida..."
Girgiza kai Yusrah tayi tana cewa "A'a wallahi aunty Bilkisu, ki barshi ma nagode."
Nan fa kowa dake zaune ya sa baki kan sai ta karɓa tana a'a, har Intisar da ke nan har lokacin tace "Idan baki karɓa ba fa ba zan ƙara zuwa asibitin nan ba, haka ke ma dai?"
Da iya gaskiyar ta tace "Wallahi idan na karɓa Mamanmu faɗa take min, sai ta ce akan aikina duk abinda aka bani na karɓa kamar cin hanci ne, dan Allah ku bar shi."
Mama da taji tarbiyyar ta ta birgeta ne ta kalleta tace "Ƴata, ki karɓa, wannan abinci ne, baki san da shi ba aka ɗauka aka baki, idan kin je ki faɗawa Maman ki ni ɗaya mamar taki na ce ki karɓa ba komai."
Sam ba dan ta so ba ta sa hannu ta karɓa fuskar ta duk a kyaɓe kamar za ta yi kuka, juyawar da za ta yi kenan sai ga Bilal ya shigo hannun shi da wasu ledojin, Yusrah dai bata kalle shi ba ma dan ta jima da tsarguwa da yawon kallon da yake mata, musamman da ta fahimci mutanen masu kuɗi ne sosai, tana shirin raɓashi ta wuce sanda yake aje kayan hannun shi Intisar tace "Yawwa Bilal, me zai hana ka aje Yusrah gida? Dan garin akwai hadari sosai fa."
Da sauri Yusrah ta juyo kamar a tsorace tana cewa "A'a aunty Intisar, ba sai ya kaini ba, zan je da kaina, nagode sosai."
Nan ma dai takura ta suka so suyi, amma sai Mama ta ce su bar ta kar takurar ta yi yawa, haka ta musu sallama ta fita tana mai rasa yadda zatayi da kayan nan, dan ko ledar dake hannun ta nauyi ne da ita saboda jibga jibgan lemukan kwalaye da aunty Bilkisu ta saka mata a ciki.
Bilal da bai ji daɗin haka bane ya zauna yana turo baki, kallo ɗaya Mama ta mishi tace "Me ye kai kuma?"
Dariya Intisar tayi tace "Mama, autan ki fa shi daga ganin jar yarinyar nan kawai yake jin ya yi mata, sai wani rawar kai yake mana."
Murmushi Mama tayi tace "In kuwa hakane ai sai nace ba ka yi zaɓen tumun dare ba, dan da alama yarinyar ta samu tarbiyya."
Aunty Bilkisu ce ta amsa da "Gaskiya ne Mama, alamu ma sun nuna haka, ba kamar sauran likitoci ba da zaka ga suna da hawa kai."
Intisar ma cewa tayi "Gaskiya kam, tana da shiga rai, ga kuma nutsuwa da hankali, komai nata a sanyaye ba hayaniya."
Wani daɗi ne yake kashe Bilal daga zaune, mutum biyu ne dama a duniyar nan yake fatan samun amincewar su, Mama da aunty Bilkisu, saboda su kaɗai ne mata da ba ya iya bijirewa umarnin su, ya ɗauka ba lallai su kula da tarbiyyar ta ba idan ba yar gidan masu kuɗi bace, dan shi tunda ya ga wayar hannun ta ɗazu tana waya da ƙawar ta *Maryam*, wata ƙaramar Oppo ce kuma ba sabuwa ba, a kuma wannan zamanin ganin budurwa kamar Yusrah, iya jar fatar ta kaɗai ma ta isa sama mata babbar waya, uwa uba kuma kyau da ta haɗa da shi mai ɗaukar hankalin mai kallo, to amma Alhamdulillah tunda suka yarda da tarbiyyar ta, iya haka ma da suka mishi ya ishe shi.
*Yusrah* na fita kai tsaye hanyar fita ta nufa har ta isa bakin titi, ai kuwa kamar jiran ta ake abun ka ga yanayin marka, saukar ruwa kawai ta ji a jikin ta kuma ba wai yayyafi ba, ruwa ne da ɗan ƙarfin su suka sauka da ya saka mutane neman mafaka wasu kuma na ƙara gudun ababen hawa, cikin sa'a ta samu adaidaita sahu ba kowa ta tsayar da shi, tana faɗa masa inda ta nufa ya ruɓanya mata kuɗi saɓanin yadda take bayarwa, sanin dole dama za ta sha tsada saboda ruwan nan ya sa ta rage kaɗan, ba gardama ya ce ta shiga suka ɗauki hanya.
Basu wani jima ba suka isa, wajen ciro kuɗin ta bashi sai da ta shiga tunanin ya za ta yi gobe wajen zuwa asibiti? Dan su kenan gare ta kuɗin ta bashi, Baba ko Mama kuma bata da tabbacin ta samu wajen su, ko zata samu ma kunyar tambaya take ji, shiyasa take Allah Allah a mata albashin ta na farko ta kawo musu su yi buƙatun gida ko za ta ji daɗi a ranta ita ma cewa ta taimakawa iyayen ta.
Ana ta kiraye kirayen sallah ta shiga cikin gidan da sallama, da gudu kuma Safwan ya tarbeta yana ihun "Aunty Yussy ta sha kashin ruwa, mu muna gida zaune abun mu."
Kwanon hannun ta ya fara karɓa, ita kuma tana ta ƙoƙarin ɓoye jakar ta ko dan wayar ta dake ciki, dungure masa kai tayi tana dariya suka shiga ɗaki da gudu gudu dukan su, Hannah na tsaye bakin ƙofa tana kallon ruwa, Mama kuma na zaune kan kujerar katako da roba a gaban ta ta nan alwala a ciki dan kar ta jiƙa ledar ɗakin duk da kuwa ba sabuwa ɓace, Hannah ce ta fara ɗan musu suka wuce tana faɗin "Yussy me kika taho mana da shi haka har da kwanuka yau daga asibitin?"
Yusrah dai kayan jikin ta ta fara ragewa tana ma Mama sannu da gida, ita ma da fara'a ta amsa mata da "Yawwa Yusrah, ruwa sun dake ki ko?"
Tana cire baby hijab ɗin ta tace "Wallahi kuwa Mama, kamar a kasa na taho."
Alwala Mama ta ci gaba da yi ba ta ko kalli kayan nan da ta shigo da su ba, ita ma Yusrah ba ta kula ba sai ma shigewa ɗaki dan ta canza kayan jikin ta, kafin ta fito Hannah ta buɗa kwanon dan ganin ko menene? Ba wai dan kwaɗayi ko ɗaukar hankali ba, dan Safwan bai isa ya yi haka ba musamman a gaban Mamansu, dan haka shima ledar yana ajiyewa ya fara shirin alwala.
Mama na ganin abinda ke cikin kwanon ta kawar da kai, saida ta gama alwalar ta tsaf ta miƙe tsaye ta yi addu'ar ta bayan kammala alwala _"Ashhadu an la'ilaha illalah, wahadahu la sharikallah, wa ashhadu anna Muhammadan abduhu wa Rasulillahu, Allahuma-j'alni minattawabina, waj-alni minal-mutaɗɗahirin."_
Tana saka hijabi Yusrah ta fito, lokacin ne ta jefeta da wani kallo mai tattare da harara cike da tuhuma ta nuna mata kayan dake gefe a taƙaice tace "Daga ina wannan?"
Yusrah ba ta tsammaci wannan tambayar Maman za ta mata ba, dan haka ta ɗan sosa kan ta cike da alamun rashin gaskiya tace "Mamanmu, wallahi wasu mutanen ƙwarai ne a asibiti da ƴar su ta haihu, zan taho gida shine suka ban wannan."
Kausasa kallonta ta sake yi gare ta tace "A matsayin me kenan?"
Da dariya Hannah da ba'a tambaye ta ba tace "A matsayin kyauta ko?"
Kallon ta duk sukayi sai Maman da ta haɗe fuska ta nunata da yatsa tace "Kar na kuma jin bakin ki."
A sanyaye Hannah tace "Kuyi haƙuri."
Saida gaban Yusrah ya faɗi da Maman ta maida duban ta gare ta, da sauri tace "Mamanmu, wallahi ba yadda ban yi da su ba nace a'a, amma sai tsohuwa ta ce na karɓa ai abinci ne, sannan idan na zo na faɗa miki wai ita tasa na karɓa ba dan ina so ba, wallahi ko Mamanmu."
"Wace tsohuwa?" Maman ta jefa mata tambaya, da sauri Yusrah tace "Maman mijin wacce ta haihu ce."
Cikin faɗa Maman tace "Amma ai ni na hanaki karɓan wannan, Yusrah so kike ki fara cin haramun kuma ki kawo mana mu ci, na sha gaya miki duk wani da zai baki kyauta in dai akan aikin ki ne to baki cancanceta ba, ko ban faɗa miki ba? Yanzu shi wannan abun cin ban san a wane mataki zan ajiye shi ba, amma bana so kowa ya taɓa komai a ciki har sai Babanku ya shigo, idan ya yarje a taɓa kwa anfana da shi, idan bai yarda ba dole a fitar min da su daga gidana, kin fahimta?"
A nutse ta jinjina kai tace" E." Wucewa Maman tayi ta bar ta dole ita ma ta ja jiki a sanyaye duk tana jin ba daɗi, ganin Hannah tayi alwala a robar da Mama ta yi ya sa ita ma ta yi anan, sallayar da Hannah ta shinfiɗa ita ma ta tsaya anan suka kabbara sallah tare sai Safwan a gefen su.
Har sallah isha'i Baba bai shigo ba saboda har lokacin ruwa ake kuma ba yayyafi ba, ganin haka ya sa Hannah kallon Mamansu tace "Mamanmu, ko dai ruwa sun hana Babanmu shigowa gida? Gashi har an fara sallah isha'i."
A tausashe Maman dake kan sallaya ta amsa da "Ba shakka, wataƙila kuma suna tattaunawa ne kan ramin can na baya dake neman ruftawa da gidajen mutane, ya faɗa min za'a yi taro na duka unguwa dan a shawo kan matsalar, tunda an je gurin gwamnatin amma shiru ba wani taimako daga gare su."
Safwan ne ya kalli Maman yace" Mamanmu, ni dai na fi so Babanmu ya fara gyara mana ɗakunanmu, saura kaɗan fa su faɗo man..."
A tsawace cikin tashin hankali Maman ta katse shi da" Kai! Rufe min bakin ka."
Shiru ɗakin ya ɗauka kafin daga bisani Maman tace" Ka daina faɗin haka *Yayan su*, ba kyau ka ji? Ka yi ta wa Babanka addu'a ya samu kuɗi ya gyara, amma ka daina cewa zai faɗo."
Jinjina kai ya yi alamar to, a hankali Maman ta miƙe jiki a sanyaye ko sallah isha'i bata kabbara ba ta shiga ɗakin ta, sun ɗauka wani abun za ta yi ko ta ɗauko, amma suka ga shiru ba ta fito ba tsawon lokaci, duk da sun damu da haka musamman ma Yusrah da take tunanin kar dai Maman kuka ta shiga ta yi akan ginin nasu da kullum lalacewar sa ke daɗa yik yawa? Dan ta taɓa ganin haka daga gare ta.
Har sukayi sallah bayan sun idar Yusrah ta kalli Hannah tace "Aunty Hannah, ko za ki duba Mamanmu ki gani, ko motsi babu a ɗakin."
Girgiza kai Hannah tayi tace "Mu barta Yussy, wani abun sai ka keɓanta ka ke samun damar fito da shi daga ran ka, imma a suffar magana, ko a suffar kuka."
Shiru Yusrah ta yi tana kallon ƙofar ɗakin Maman da labule ne kawai ya rufe ƙofar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tace "Hakane, Allah ya mana maganin dukkan matsalolinmu."
"Ameen." Hannah ta faɗa, wayar Hannah dake kan sallaya ce ta yi ƙara, Yusrah na ganin sunan da ya fito ta kalle ta da murmushi tace "Aunty Hannah kwana biyu ban ga Yaya *Jamil* y zo zance ba?"
Ɗaukar wayar tayi tana miƙewa tsaye tace "Kin manta Babanmu ba ya son yawan zancen? Ai shiyasa ko ya ce zai zo nake hanawa, amma dai mun yi magana yanzu akan duk juma'a zai zo."
Murmushi Yusrah ta yi tana bin ta da kallo har ta shige ɗakin su ita ma, daga ita sai Safwan aka bari, ba wani abu da take yi a wayar ta da za ta ce bari ta ɗauko ta duba, idan ta yi ƙara za ta ji, rabon da ta hau yanar gizo kuma saboda rashin isashen data har ta manta, kira ma ba wasu mutanen ne ke kiran ta ba idan ka cire Baba idan bata gidan ko shi baya nan yana so zai yi magana da Maman su, sai ƙawar ta Maryam kawai, bayan haka kuma sai irin samarin nan da zasu samu lambar ka baka san ta ya suka samu ba, ita kuma bata kula irin waɗannan dan gwara ka tarbe ta ka ce ta baka ya fi mata daɗi.
Sannu sannu ruwan suka fara ragewa zuwa yayyafi, suna nan zaune ita da Safwan har ta tambaye shi "Ba'a yi girki ba?"
Kai kaɗai ya girgiza mata shima bayan ya juya ya kalli ƙofar ɗakin Mama, doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin to idan dai ba'a yi girki ba, to tabbas rashin kuɗi ne ya kawo haka, wataƙila ma shiyasa Baba ya jima bai shigo ba, kenan ya za ta yi gobe wajen tafiya asibiti? Dafe goshi ta yi tana ci gaba da tunanin abun yi, kwatsam suka ji sallamar Baba, da sauri Safwan ya miƙe ya fita ita ma saida ta tashi, haka ma Hannah sai da ta yi sallama da Jamil ta fito duk suka tarbi Baban, ledar hannun shi ya ba wa Safwan suka shigo ɗakin, Yusrah dai cike da tausayi ta zuba mishi idanu saboda kayan shi a jiƙe suke sosai, tuni ƙwalla suka cika mata idanu saboda tausayin mahaifin nasu da kullum burin ta taga tana taimaka mishi, ba ya da namiji babba sai su mata.
Hannah ma da kulawa tace "Babanmu yau kun jima, ruwa suka hanaku fitowa?"
Murmushi ya yi duk ya shafa kawunan su yana cire hular shi, cikin taushin murya yace "Ruwa ne suka hanani Hannah, ina Mamanku?"
Safwan ne ya yi gaggawar amsawa da "Suna ɗaki."
Jinjina kai ya yi tare da nufa ɗakin yana cewa "Bari na cire wannan kayan, ma sha Allah yau mun sha ruwa."
Yana daf da shigewa ya juyo ya kalli Yusrah da bayan gaisuwa ba ta ce komai ba yace "Yussy kina lafiya?"
Jinjina kai ta fara yi alamar e kafin tace "Lafiya lau Babanmu."
Murmushi ya sakar mata mai ma'anoni da dama, da sosai yake hango tsagwaron tausayin su a idanun ta dake shirin sakata kuka, shiyasa ma bai tsaya wajen su sosai ba dan kar ta fashe masa da kuka.
Baba na shiga ɗaki ya tsaya turus, amma dan kar yaran su ji me ke faruwa sai ya ƙarasa a tsanake kusa da maman dake zaune kan gado yana kallon ta hankalin shi yana sake tashi matuƙa saboda tunanin me take ma kuka?
Da kulawa sosai yace "Ƙanwata, lafiya? Me aka yi kike kuka haka? Yaran ne suka miki wani abu? Ko jikin naki ne?"
Share hawayen ta fara yi tana sauke ajiyar zuciya da cewa "Ka yi haƙuri Yayana, ashe ka shigo? Ka yi haƙuri dan Allah na ɗaga maka hankali, ba komai wallahi."
Sai kuma ta gyara zama dan ta basar da zancen tace "To ya tattaunawar ta ku? An samu wata matsaya ne?"
Ƙura mata idanu ya yi yace "Baki bani amsar tambayata, me aka yi kike kuka?"
Shiru tayi tare da sadda kan ta ƙasa, ta ɗan ɗauki sakanni a haka kafin ta ɗago a hankali tace "Yaya, na ce ko zamu koma ɗakin yara, su sai su dawo nan ɗakin namu, gaskiya hankalina ba'a kwance yake ba game da lamarin ɗakin nasu, tsoro nake jiye musu wallahi."
Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu har ta gama sannan yace "Ƙanwata, yanzu a ganin ki ɗakin namu ya fi nasu aminci ne?"
Ɗaga kai tayi tana ƙarewa kowace kusurwar ɗakin kallo, gaskiya ba wata maraba bace, gini dai ne na laka sai shafe shi da aka yi da simitin, shima dake abun ya ɗauki shekaru duk simitin ya kwaye wasu wuraren sai tsagwaron lakar a fili, ganin ba wani bambamci ya sa ta feso iska daga bakin ta tana kallon shi tace "To ya zanyi? Hankalina ne a tashe kullum, musamman ma idan suna cikin ɗakin sai naji na gagara nutsuwa."
Hannunta ya riƙe cike da tausasawa yace "Ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe, kar ki manta saboda nayi gyaran gidan nan na shawarta da ƴan uwana suka kuma yarda akan zamu siyar da filinmu ɗaya da ya rage mana na gado dan nayi wannan gyara, kuma in sha Allah ina saka ran fara aikin gidan nan a sati na gaba da zamu shiga, kinga kafin bikin Hannah ya tashi gidanmu ya zama sabo, ko ba haka?"
Tunda ya ambaci sati na gaba wata nutsuwa ta sauko mata, dan haka tayi murmushi tace" To Allah ya yarda Yayana, Allah ya tabbatar mana da alkairi, Allah ya baka iko akan wannan niyya ta ka."
Murmushi ya yi tare da miƙewa yana cire rigar shi yana faɗin" *Ƙanwar Abdul-Hameed* rigima, kawai sai kiyi ta kuka har da ƙoƙarin canza min ɗakina da na saba kwana a ciki? Hmmmm!"
Dariya tayi cike da jin kunya ta miƙe ita ma tana ɗaukar kayan da ya cire tana kakkaɓe su ta sagala a hannu dan ta shanya su tace" To me ba gashi kuma *Yayan Habiba* ya sakata dariya a bayan kukan ba?"
Dariya duk sukayi kafin ya ce mata" Yau ma dai sai kun haɗa da haƙuri ƙanwata, garin kwaki na nan da kayan haɗin shi wajen Safwan, ko iya yaran su gyara sai ku ci."
Da tausasawa tace" An gode Baban Safwan, Allah ya ƙara buɗi mai alkairi."
Har za ta fita daga ɗakin, sai kuma ta dakata take faɗa masa Yusrah ta zo da abinci, shiru ya yi na kusan daƙiƙa sha biyar tana tsaye tana jiran ta ji me zai ce, kafin ya kalle ta yace" Ku zuba mana mu ci, ubangiji ne ya ciyar damu daga gare su, sai dai ki sake faɗa mata bana so ta buɗe hanyar karɓan komi aka bata a wurin aikinta, wata rana za ta karɓi haram ta ci."
Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace" In sha Allah, zan ƙasa nusar da ita, ka yi haƙuri ba za ta sake ba."
Murmushi ya yi yace" Allah ya muku albarka."
"Ameen ya Allah." Ta faɗa tana fita daga ɗakin, akan kujerun ƙarfe dake falon ta shanya kayan kafin ta umarci Yusrah da ta karɓi garin ta gyara, ba ɓata lokaci ta shiga gyaran nashi musamman ma da ya zamana tana jin yunwa, saida suka gama gyarawa ta aje gaban Maman, ta ɗiba a faranti sannan ta basu sauran, ɗaki ta shiga ta kai wa Baban, jim kaɗan suka fito tare, kujera ta gyara mishi ya zauna ya karɓi farantin ya aje ya ce yaran su matso da nasu, haɗewa sukayi gaba ɗaya suka saka hannun su suna ci a nutse.
Saida suka cinye Baban ya kalli Maman yace "To yanzu a zuba mana wanda Yussy ta kawo ko."
Ba gardama ta tashi da kan ta ta ɗauko kwanon da leda, cikin kwanon da suka ci garin ta juye ashe miyar da ba komai a ciki sai zallar naman zabi da dankalin turawa yawa ne da shi, duk da abu ne da za su iya cewa daga sallah sai sallah suke samu, sai kuma ranar da ubangiji ya yi buɗi gare su suke iya samun nama a abincin su, dan mahaifin su kayan miya ne yake siyarwa a kasuwa, wasu lokuta ga kayan miya a gidan amma babu abun dafawa, ma'ana shinkafa, gero ko masara bare kuma ayi maganar makka. Amma haka daga yaran har iyayen ba wani wanda ya dinga haɗama ko zumuɗin zai ci, haka suka dinga jefa hannayen su bayan na iyayen su suna ci a nutse har suka cinye shi ma tass tunda miya ce babu mahaɗin ta, garin kuma dama ba kowa ne ya ƙoshi ba.
Ledar ma lemuka ne masu rai da lafiya da kuma kayan marmari a ciki, su ma Alhamdulillah haka suka sha har suka ragawa gobe, bayan hakane Baban ya yi hamdala sannan ya kalli Yusrah yace "Yusrah, nasan maman ki ta faɗa miki ba ta ji daɗin karɓan kayan nan ba? Kar kiga na ci, nayi duba ne da wasu abubuwa, amma dai ki kiyaye kin ji, mutumci ya zama shi ne sama da komai a wurin aikin ki, kin gane?"
Jinjina kai tayi tace "Na gane Babanmu, in sha Allah ba zan sake karɓan komai ba daga yau, kuma wallahi dan Mamansu ta yi magana ne ma na karɓa."
Jinjina kai kawai ya yi, da haka suka taɓa hira kamar yadda suka saba kafin dare ya ƙara yi suka shiga ɗakin su suka kwanta, sai dai Yusrah tun bacci bai ɗauketa ba aka sake ɓarkewa da wasu ruwan, tun tana juye juye har baccin ya ɗauke ta ita ma.
*AA ANZA*
A nutse yake haurawa sama, bayansa ƙannensa ne ke biye da shi dan kowace da maganar da take so su yi da shi, a nutse ya nemi izinin shiga ɗakin mahaifiyarsa, jim kaɗan ta bashi dama ta hanyar furta" Bismillah Rohi."
Domin ta tabbata shine, baya taɓa zuwa ya kwanta ba tare da ya zo ya yi masu bankwana ba, haka kuma yanayin doka ƙofar ma tasa ce, a hankali ya shiga da sallama a bakinsa ya sauke mata murmushi yana idasawa daf da ita a tausashe ya zauna ya furta" Barka da dare Anna."
Murmushi ta yi itama a hankali ta ce" Barka kadai yaro, ya gajiya?"
Kai ya girgiza a nutse ya ce" Babu."
Murmushi ta yi ta kalli ƴan matanta da ido ta masu alamun lafiya?Kowace ta yi tsuru suka kasa bata amsa, hakan ya sa ta dube shi ta ce" Ni wai, ina kake zuwa ne? Ya ya kuma maganar tafiyar yaran nan? Ka ce za ka yi bincike akan makarantar da suka zaɓada kan ka."
Ɗagowa ya yi ya dubeta, sannan ya dube su, kai ya girgiza ya ce" Su yi haƙuri da tafiyar har a kwana biyu."
Su da kansu da suka ji ya dasa aya haka basu tsaya jiran wani bayanin ba suka fita daga ɗakin dan sun san nacewa a kan lamarin ba zai kaisu ga ci ba face ma ɓacin rai da zai biyo baya.
Suna fita Anna ta dube shi fuskarta a ɗaure ta ce" Aswan, me yasa kake so a kullum ringa yi maka surutu a kan abinda ya shafi Goggonku? Wannan da kake gani idan ka raina ta mu ka raina, tana da damar ta yi maka faɗa in ta yi ra'ayi, ka kula bana son ina ganin kana yi mata abubuwan nan da kake yi mata ka ji?"
Kai ya gyaɗa da kula sosai ya ce" Ki yi haƙuri Anna, za'a kiyaye."
Anna ta yi murmushi, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya miƙe ya yi mata sai da safe, dama ya gama da mahaifinsa tuni, dan haka yana fitowa ya kama hanyar sauka dan nufar nasa gidan, a saman matakala ta biyu suka haɗe da Goggonsu ita da Abrar, Abrar ɗin ɗauke da kular abinci jikinta sanye da doguwar riga ta bi jikinta masha Allah ta yi mata ɗass.
Tunda ta ganshi ta haɗe rai sosai, dan kuwa haushin sa take ji sosai kan abinda ya yi yau, Abrar kuwa sai ma ta so manta kanta a tsayen da take domin cak ta ja ta tsaya fuskarta ta yalwata da murmushi ta duƙa sosai murya a shaƙe ta ce "Barka da dare Yaya AA."
A saman leɓensa ya furta" Barka."
Barka ɗin da ya bada a jimulce daga ita har babarta sannan ya raɓe ya ƙarasa sauka ya fice gaba ɗaya daga falon, ba wai ya raina Goggo Tidin bane, hasalima shi mai girmama wanda yasan yana gaba da shi ne, kawai dai ta dinga yin