yi wanka ya bayas
da faralin da ya hau kan shi. Sannan ya fiddo wani yadi mai
shara-shara dinkin doguwar riga da wando sun fiddo da
zatin Yusuf sosai ya bare turare sabo gadagal ya fesa.
Yana rike da tsarabar Fa'iza yayin da yake sakа
takalmansa, yace, "Amma dai Awal ha ka da kirki yanzu ko
rakiya ba za ka yi min ba?" Awal ya juya baya ya ki yadda
su hada ido da Yusuf yace, "Har yanzu dai ba ka gajiya da
son na yi maka bayani ko? Na sha ce maka irin gidansu
Fa'iza ba wajen zuwa na ba ne amma ka ki ka dains gayyata
ta. Ni ka ga tafiya ta ina da anguwar da zani zuwanka ne ya
tsayar da ni, sai in ce, sai mun dawo kenan".
Karfe biyar du minti tarə daidai na yamma,Yusuf yа
isa kofar gidansu Fa'iza, kamar kullum masu gadi da 'yen
barandan gida suna nan zaune a kofargidn kowanne na ta
hidimar gabansa. A yau Malan Inusa ne ke kishinge bisa
dogon benci da kur'ani dan izihi ashirin a hannunsa yana
tulawa, Yusuf ya nufi wajensa domin dama ya fi saukin kai
10
Malán Inusa ya mike zaune ya matsawa Yusuf waje
ya zauna, suka dade suna gaisawa tare da tambayarsa
labarin Kwara.
Yusuf yə uan kaskanta da murya yace, "Allah dai
yasa mutuniyar tawa na nan?" Malan Inusa ya dubi Yusuf
yace, "Wai Fa'iza?" Ya amsa "E ita" Yace "Tana nan amma
a yau gaskiya babu halin ganinta" Yusuf ya zaro ido yace,
"Malan Inusa me kuma ke faruwa in ce ko lafiyarta lau?"
Malan Inusa ya kara kallon Yusuf da kyau yace, "Wai kai in
ce ko redio baka da shi ne? In ba haka ba duk rugundumin
nan da aka sha cikin redio da talabijin ka ce wai baka da
labarı?" Yusut ya yi galala yace, "Ina da labari na tambayeka?"
Malan Inusa yace, "To an daura auren Fa'iza da dan
gwamnan iiharmu! Yau kimanin kwana shidda kenan, daurin
aure da ya amsa sunansa a kasar nan, don haka kai ma ka
san vabu hali ka yi magana da matar mutane".
Yusuf ya yi kokari ya yi ma Malan Inusa wasu 'yan tambayoyi amma ya san ba su da anfani, tun daga bakinsa
zuwa makogoronsa a bushe ya ke kar kat, duk iya dabararsa
ya yi amma ya kasa tashi, ya na jin Malan Inusa na wasu
maganganu masu kama da ban magana amma a gaskiya
yace bai iya tunawa ua ko daya.
Wannan itace rana ta farko da ya fara jin kunya da
cewa wai yana son Fa'iza da aure. Ya yi karfin hali ya daga
kai yana kallon mutanen da ke kai da komowa a kofar gidan
su Fa'iza, babu wanda ya damu da shi tamkar dama bakon
Malan Inusa ne ba wai na diyar gidan ba. Mota da mutun biyu a gidan baya direba na janye 'da su, suka iso gidansu Fa'iza, nan da nan kowa da kowa ya maida hankalinsa a
kan wa`annan baki hatta Malan Inusa ya mike ya nufi wajen
su, yayin da ya ke tafiya ne ya ke cema Yusuf "Ina jin ma yallabai ne Shehu angon Fa'iza".
*
Yusuf ya mike a hankali ya tari yana tanagal - tangal,
a haka ya rinka tafiya a kalla ya yi tafiyar awa biyu cif a
kasa, can hanyar Hanwa low coast ya mike ya sami wani
tsaunin dutse ya haye ya yi zaune.
Ga abinda ya rinka fadi: "Fa'iza ba ki cuce ni ba,
babu wanda ya ingiza ni cikin wannan wahalar sai ni kai na
Yusuf sai ko kaddara" Ya yi shiru sannan ya ci gaba, "To
wai minene laifin Fa'iza anan? Idan ma Allah ya isa na yi
mata lalle zata dawo kai na in ga bala'i, na rasa Fa'iza na
rasa rayiwata, ina son Fa'iza a yau na yadda Fa iza bata so
na. Why?"
Abinda Yusuf dai bai da labari shi ne, a lokacin da
mahaifin Fa`iza ya ce lokaci yayi su ba shi mijin da suka
zaba, babu tantama Ismail Fa'iza ta fiddo, anan take
mahaifinta yace, "Fa'iza idan dai ni zan ba ki shawara ki
dauka Isma'il ba mijin aure ba ne, domon na yi iya bincike
na banji gaskiyar sana'arsa ba, saboda haka idan aure za ki
yi na tsoron Allah, ki kiyayi Isma'il". Ana cikin haka ne, a
wata rana sun je filin jirgi rakiyar Baban su Allah ya dora
idon Shehu dan gwamna na wannan zamanin akan Fa'iza.
Alhaji Abba yayi binciken da musulunci ya kayyade
aure ya fada akan Shehu.
Yusuf ya yi kuka daga karshe yace, "A yau babu
Fa'iza, babu Dije tana can gidan wani mijin". Amma rashin
Dije alhairi ne domin ita ma ya san ba wani son shi take yi
ba, auren kawai take so ayi mata.
Ya duba agogon hannunsa karfe goma da rabi na
dare, ya mike ya nufi gidan su Awal, a kalla hankalinsa ya
dawo jikinsa ya fada a fili "THE GAME IS OVER!" Tafiya
yake har ya ga ji likis, gajiyar ta fara tambayarsa, ya rinka
jin kamar ya watsar da kayan da ke hannunsa wato dai
tsarabar Fa'iza amma kuma ya bai wa kan sa shawara gara
ya jure ya rike ya kai ma su Sarai kada asarar ta yi mai
yawa.
Ya isa gidansu Awal karfe daya saura na dare, abin
mamaki Awal na zaune a zaure yace "Awal lafiya baka
kwanta ba?" Ya ce "Ina zan kwanta na yi bako ya bace a
gari, don Allah ina ka je Yusuf?" yace "Bar ni kawa Awal ba
ni ruwan sanyl na sha."
Ya kawo masa ruwa har da damammar hura a kwano,
12
Yusuf ya sha nan da nan idanunsa suka kara kadawa su kai
jawur.
Yace, "Yanzu nan saboda Allah Awal ka san an daura
auren Fa'iza?" Awal yace, "kai yanzu din nan a yadda ka zo
kana ta faman rawar jiki ko na shekara ina fada ma an
daura wa Fa'iza aure yaushe za ka yadda da ni? To ai garama
dai da hakan ta faru, wallahi Yusuf baka jin magana haka
kawai da rana tsaka ka canza halayyarka, ni wallahi cikin
sha'anin nan mahaifiyarka kadai na fi jin tausayi, bayan irin
kuncin da ka saka ta na jama'ar gari sai kuma yadda ka
rinka mai da kan ka dan karya saboda Fa'iza. Shi ne, ka yi
ma Allah Subahanahu godiya da bai makareka da auren
Fa'iza ba, sannan ka roki mahaifiyar gafara a bisa karyace
- karyacen da ka rinka yi mata". Yusuf ya dafe kan shi
"Don Allah Awal zan sami panadol na sha kai na tamkar
ana fasa kwakwa". Awal ya mike ya bude wata jaka ya
mika masa panadol.
Yusuf yana jin Awal na ta sharara bacci yayin da shi
komi ya yi mai zafi daga zuciyarsa har kwakwalwar kan sa,
ya rinka jin shin a duniya akwai wanda ya taba shiga kunci
irin na shi? domin shi dai yanzu bai ga kamar Fa'iza ba a
duniya son ta ya ke, son da bai iya misiltawa dan adam
yayin da ya san shi da Fa'iza har abada, to wannan kalmar
ce ke wahalad da shi.
Da safe ya dibarwa Awal tsarabar da ya yi ma
mutanen gidansu. Awal yayi godiya ya dubi Yusuf yace,
"Ka tabbata za ka iya tafiya Bakorin nan ko dai mu je na
raka ka asibiti, ka ko ga yadda yanayin jikinka ya canza?"
Yusuf yace, "Babu komi zan lallaba, ai gida za ni" Awal
ya ce, "Shi kenan mu je na raka ka tasha."
Ya isa gida, Salmanu na zaune cikin shagonsu, wasu
yara na sayen Omo da magi mai tauraro, ya hango Yusuf
na sauka bisa dan acaba da wani dan acaban ya labto kayan Yusuf nan da nan Salmanu ya sallami yara ya nufi wajen Yusuf, yana yi masa barka da`zuwa tare da amsan kaya yana shiga da su cikin gida. Rabon da Yusuf ya ga fara'ar Gwoggo Halima tun zamanin yana neman Dije sai
13
ko yau tamkar zata kama shi ta rungume.
Ya sami tabarma ya kishingida da ganinsa ba sai ka
tambaya ba ka san yana tattare da matsaloli Gwoggo ta
kama aje masa abinci a gabansa amma ban da ruwa babu
abinda ya taba.
Ya fara tambayar jama'ar gida kamar kannansa da su
Malan aka tabbatas masa kowa lafiya. Gwoggo tana
murmushi tace, "Sai kuma mu ka ga Fa'iza da wani ana
hidimar daurin aure ba da kai ba?" Yusuf ya lumshe ido
kamar bai ji abinda ta ce ba, zuwa can yace "Wallahi kuwa".
Ya mike ya nufi dakinsa yace ma gwoggo a cikin ledojin
nan a duba akwai busasshen kifi a dauke a gyara kada ya
lalace.
Kwana biyu da dawowar Yusuf duk ya fita
kamannunsa domin mugun zazzabi da damuwa ta sakar
masa, tun Gwoggo Halima nayi masa dariya ta dawo abu
ya dame ta. Aka diba aka ce kila maleria din sa ce ta dawo
likita yace, sam ya auna jinin babu maleria, to ai fa sai
gwoggo da malan Tukur suka shiga neman masa maganin
gargajiya, kamar na shawara da basir saboda irin sambatun
da aka ji yana yi a hankali Malan Tukur ya lura duk ciwon
da ake tunanin yana damun Yusufa ba su ne ba, sai kawai
ya koma rokon Allah wanda a kullun yana rubutawa Yusufa
Bissimillah kafa dari babu daya sannan addu'ar (Ya Hayyu
Ya Kayyum bi Rahamatika Astagfirillah) ta zamanto abin
ambaton Yusuf a kodayaushe, cikin ikon Allah wannan su
ne sanadiyar warkewar Yusuf tas, ya murje ya roki gafarar
mahaifiyarsa.
Yusuf ya fid do takardunsa ya shiga neman alkı lunyulungu kamar karamar hukuma da ma'aikatar karamar
hukuma da maʼaikatar ilmi ko za'a dauke shi malamin
makaranta, har dai gidan redio Katsina ya leka amma shiru
ka ke ji.
Babu dare babu rana ya rungume Malan Tukur tamkar
yadda zai rungume mahaifinsa a kullun yana ta dibar karatu
da nasihohi da dabarun zaman duniya, idan har baya tare
da Malan to yana shagon Falanke tela yana hira.
14
Falanke tela kamar yadda su Yusuta kan krasa
sunansa na gaskiya Sha'aibu, aminin Yusuf ne tun suna
yara, illa dai kawai Falanke bai yi ilmin zamani ba kamar su
Yusufa. Falanke mutun ne mai ban dariya ga barkwanci
don haka tunda ya fara sana'ar dinkin keke a kullun shagonsa
cike ya ke da samari ana hira ana ban dariya yanzu haka
Yusuf sai ya kai karfe dayan dare a shagon Falanke suna
hirarsu, wani zubin har Yusuf ya amshi maballi ya rinka
taimaka masu.
Kamar kullun yau jumma'a da la'asar sakaliya Yusuf
ya shiga shagon Falanke sai yace, "Falanke za ni gidan
Malan Tukur akwai wata addu'a da na ke koyo ina son na
gama daukar ta a yau ko za mu tare ne, daga can sai na
raka ka Funtua sayen zaren dinki?", Falanke yace "Wannan
zance na ka Yusuf shine abin yi, daman yau kuiyar dinkin
nan na ke yi".
Suna zaune gaban Malan Tukur yana baiwa Yusuf
karatu, duk sha'awa ta kama Falanke, ya rinka raya ma
zucıyarsa lalle shi ma zai dawo daukar karatu wannan
dunıyar shirme ce kawai.
Mota irin ta daga wane sai su wane ke iya shigar ta
a kasar nan ta danno kai ta shigo zuwa kofar gidan Malan
Tukur, gaba daya su Yusuf suka raja'a wajen kallon wannan
galleliyar motar tamkar gajimari.
Direban ya fito da sauri ya bude mai motar mota.
mota. Alhaji Yahaya ya fito cikin kyakyawar shiga kai kace domin shi aka kera wannan mota.
Yusuf da Falanke suka rusuna suka gayas da Alhaji Yahaya yayin da Malan Tukur ya mike suka shiga dakin
zaure shi da Alhaji Yahaya domin su gana, kimanin shekara
goma sha takwas kenan Alhaji Yahaya na zuwa wajan Malan
akan wasu bukatansa na duniya. Alhaji Yahaya babban ma'aikaci a Abuja, haifaffan garin Katsina ne, kusan Alhaji Yahaya na daya daga cikin manyan ma'aikatan da Katsina
ke takama da su a matsayin`ya yanta.
Sun jima suna zantawa da Malan aka bukatar da ta
15
kawo shi. Malan yace, "Kamar kullunı hana son ka ji komi
Insha Allah za mu kai kukanmu wajjen Ubangiji, abinda kuma
duk ya zartas mu dauka shi ne mafi alhairi a pare mu".
Alhaji Yahaya ya yi murmushi zuciyarsa ta yi mai dadi don
haka ya ke zuwa wajen Malan domin malan mutun ne mai
dayanta Allah.
Malan Tukur yace "Alhaji akwai wani taimako da na
ke nema a wejenka ina fatan za'a taimaka min idan har an
ga abin bai fi karfinku ba". Alhaji yace "Haba Malan kа
fada mana". Malan yace "yaro gare ni ga shi nan waje ya
kammalo karatunsa na jami'a amma mun nemi aiki mun
rasa, shi ne zaka taimaka ka samar masa aiki". Alhaji yace
"A kira shi Malan"; Malan ya kwallawa Yusuf kira.
Alhaji yace, "Ina takardan imakarantar taka?" Yusuf
gabansa ya fara bal bal, duk farin ciki ya mamaye shi tabbas
ya san batun aikin sa ne kuma babu abinda zai hana irin su
Alhaji samar masa.
Yace "Ranka shi dade su na nan". Ya dubi Malan ya
ce "Baba suna cikin takardun ka na zaure bari na je na
kawo" nan da nan Yusuf ya milka takardu hannunsa na
rawa.
Alhaji Yahaya ya duba takardun Yusuf da kyau ya
kada kai yace, "Bapu komi Malan ai yaron ya yi abinda ko
wacce ma'ikata ke so, zan iya samar masa aiki a ko ina,
amma ba dole ne sai aikin gwamnati ba ko na kamfani ne
masu zaman kan su zan samar masa".
Yusuf ya karkatar da kai cikin murmushi yace, "Godiya
nake ranka shi dade".
Alhaji ya fid do katinsa mai adireshinsa na gida da na
ofis ya baiwa Yusuf yace ka same ni Abuja ran talata mai
zuwa.
Yusuf ya fito shi da Falanke suna ta murna da zumudi,
Falanke yace, "Don Allah Yusuf idan Abuja aka aje ka nima
ka yi min hanya na koma can da zama an ce sana'ar dinki
tafi ci a can". Yusuf yace, "Insha Allah na yi maka alkawari."
A ranar litinin da daddare kwana a kai Gwoggo Halima
da Malan Tukur na yi ma Yusuf huduba suna cewa, "Don
16
Allah Maitama kada ka kuskura shaidan ya rinjayi zuciyarka
ka canza akidarka domin yanzu za ka tsincí kan ka ne a
wani matsayi na daban. Haka nan ko wane mataki Ubangiji
ya kai ka, ka tabbata kana girmama na gaba da kai, sannan
ban da danne hakkin na kasa da kai ban da danne hakkin
al'umma ka tabbata akwai ranar da za ka tsaya gaban Sarki
Allah ka yi bayanin yadda ka gudanar da al'amuranka.”
Magana ta karshe itace "Don Allah Maitama idan ka
sami aiki, sannan ka mallaki mahallinka to ka zo gida ka
duba mata 'yar mutunci ka aura domin darajar da namiji
bata cika sai da iyali."
A nan ne fa Yusuf ya yi sunkui da kai, an ya zai iya
mallakar mace a duniya? Kwata-kwata ya dawo rakiyar
mata, domin kamar shi wai Fa'iza bata son shi to menene
abin mannewa sai wata ta so shi? Shima a ra'ayinsa ya
sallama kaunar ko wacce irin diya mace a duniya.
Karfe goma sha biyu na rana ya isa ofishin Alhaji
Yahaya, zuciyarsa ta raunana ganin irin tsananin tsaron da
ake yi akan Alhaji Yahaya, arizikinsa daya ya nuna katin Alhajin sannan aka bar shi ya shiga.
Aikin ya samu na wani shaharararren kanfanin 'yan
kasa da hadin gwiwar nasara jar fata. Mamaki ya kama Yusuf bai taba zaton zai iya samun hanyar wani ba wanda
ke aiki a wannan kanfanin amma yau albarkacin Malan Tukur
ga shi an dauke shi aiki a kanfanin.
Wasa-wasa wata daya juriyar aikin Yusuf yasa manyamanyan daraktoci na kanfanin sun san da Yusuf sani ko ba
na wasa ba, irin sanin da ya jawo Yusuf jikinsu, domin ko tsakar dare Yusuf na tare da su ana gudanar da aiki, wanda ba ko wanne ma'aiki zai iya ba, wannan ta ba su damar fara fita da Yusuf kasashen waje.
A ranar wata asabat da yamma direban kanfaninsu Yusuf na janye da shi a motar kanfani sai ya ga abokinsa
Amiru cikin wata galleliyar motarsa, ya umurci direba da cewa ya tsayar da Amiru.
Amiru ya fito a lokaci guda Yusuf ya fito daga gidan baya. Amiru yace, "Kai mutumin daga ina! Yaya na gan ka
17
haka kamar bakon wani baindiye?" Yusuf ya kama kafadar
Amiru ya janye shi gefe daya yace, "Ai ni bana sai hamdala.
Amiru na sami aiki daya da daya anan Abuja, yanzu kai a
ina ka ke ne?" Amiru ya ce, "Ba ni Kano ba ni Legos amma
na fi zama nan Abuja. Ni ke tafiyar da yawancin kasuwancin
mahaifinmu ina fatan za ka zo gidana mu zauna anan Abuja".
Yusuf yace "Ai ni ma sun ba ni gida yanzu haka har na
dauko wannan uban rigimar don ya debe min kewa wato
Falanke tela, yana nan na manna mai daki daga jikin gidana
ya fara dinki, a kullum shagon baka rasa jama'a ana
sokonci."
Amiru yayi dariya ya се, "Ка сe kai gidanka gidan
hira ne, inda su Falanke su ke ai wajen raha ne, Insha Allah
nan zan mayas gidan hira ta, yau din nan ina nan zuwa."
KASHI NA SHIDDA
Bayan shekara shidda da rabuwar Dije da Yusufa,
bari mu ji yadda Dije ta samu shekara shidda a gidan
mahaifiyarta Amina.
To Amina dai bata da wata diya mace baya ga Dije
domin kimanin maza biyar cif ta haifa a gidan Malan Isa,
to dawowar Dije hannunta wannan sai ta bata wata dama
ta nunawa Dije gatanci da so na kasancewarta diya mace
tilo a gare ta, duk wata 'yar atanfar zamani ko yadin zamani
wanda bai fi karfinta ba za'a ganshi a gindin Dije, yayin da
ita kuma Dije ta mayas da zancen káratun'ta ne kadai matsala
a rayiwarta. Farkon jarabawarta ta zo na bakwai, amma a
fannin lissafi itace ta zo na daya, domin Dije na ganin beken
wa`anda ke cewa lissafi na da wuya ita a ganinta duk
rashin natsuwa ne, a ranar da malaminsu ke yaba mata
cewa tana daya daga cikin 'ya'ya matan da ya taba gani
wadda ta iya lissafi, nan ne tunanin Yusuf ya bijiro mata a
dakin Inna Tambai yana koyar da ita wasu darussa, amma
da suka zo kan lissafi, sai ya lura ta na so ta kure shi domin
shi ma ba gwanin ba ne wajen lissafi, ya ce, "Da mamaki
yadda ki ka iya lissafi haka har kin so ki kima" Ta yi
18
zarce
murmushi tace, "Ba haka ba ne abinda ke faruwa mutane
ne sun yi ma lissafi mummunar fahinta, har ya zamanto
wani ma bai taba tsayawa ya koya sai kawai yace, "Bana
yin lissafi shegen wuya ne da shi". Yusuf ya yi kasake
maganan Dije ta yanke shi, domin ya san akwai abokansa
da dama wa'anda ba su shiga aji lokacin darasin lissafi
zamanin yana sakandire wai su ba su ganewa.
Tace, "Ni ko ka ga duk aiki babu wanda na ke fahinta
irin lissafi". Yusuf yace, "ko ba ki fadi min ba ni na- san haka, sai dai na ba wani labari. Ina alfahari da samun mace
mai natsuwa da fahintar abinda ba kowa ne ke iya fahinta
ba."
Suka hada ido ita da shi suka yi murmushi. Nan da
nan Dije ta yi ajiyar zuciya ashe duk karya Yusuf ke mata,
ba haka take ba a zuciyarsa? Abinda ya fi daurewa Dije kai shi ne me yasa tun farko Yusuf bai muzanta halittarta ba
sai daga karshe? Ita dai ta san akwai wani abu da Allah ke nufi akan ta da Yusuf amma dalilin Yusuf ba dalili ba ne.
Sai da Dije ta sami watana bakwai cif a Malunfashi
bata je Bakori ba, a wannan hutun ganin ita ta zo na daya
a makaranta sannan kuma ta shiga aji biyar a lokacin saura
wata tara ta kammala karatun sakandire. Yaya Amina kamar yadda`ya`yanta ke kiranta itama Dijen Yaya take kiranta
sai ta umurce ta akan ta shirya ta je ta gano mahaifinta da
su Gwoggo Tambaya.
Da la'asar ta sauka garin Bakori ta sha lullubi da bakin gyale yayin da take daure da wata atanpa 'yar Japan
mai tsantsa ruwan bula da baki, an dinka riga da zani da kallabi na atanpar, takalmanta sukol ta yi shar da ita, 'yan matanci da kuriciya ke ta fita jikinta kai kace sarauniyar 'yan mata ce ta wannan zamanin. A kafadar ta tana rataye da wata bakan jaka mai cin kimanin zani da riga kaman kala shidda. Tana ta wuce jama'ar da ta sani suka santa
amma abin mamakin Dije kowanne ya kan dauke mata kai
nuna alamar bai gane ta ba.
Dai.dai kwanar shiga lungun gidansu ta ci karo da Shafa mai kosai dauke da kwaryar wakenta zata nika injin. 19
Dije cikin fara'a tace, "Sannu mai kosai". Shafa ta kara
dafe kwaryar wakenta, tana ma Diya kallon tsoro tace,
"Yawwa sannu 'yan mata daga ina ki ke yarinya?" Dije ta yi
dariya tace, "Mai kosai ni ce Dije diyar Baba Kado fa!" Mai
kosai ta bude baki tace, "Iko ya tabbata wajen Sarki Allah.
Yanzu Dije ke ce kika murje haka? Kai duniya idan mutun
bai mutu ba bai gama kallon abin al'ajabi ba, ke ko Dije ina
kike aure haka?" Dije ta yi dariya tace, "Mai kosai ban yi
aure ba, ina hannun innata ina makaranta."
Mai kosai ta tsaya galala tana mamakin canzawar
Dije yayin da Dijen ta shige ta bar ta nan tsaye cikin mamaki.
Malan Kado na kishingide bisa tabarma a kofar gidansa, ya
dawo kasuwar Dayi ya gaji likis, yana ta kallace-kallacen
yaran anguwa, sai ya hangi galleliyar budurwa ta nufo
gidansa, zuciyarsa ta bashi ko Dije ce, amma wata zuciyar
ta rinka raya masa yaushe Dije ta kai girman wannan
budurwar da wayewarta? Illa kawai murmushinta da irin
kallon ta sun kamanta masa irin na Dije.
Ya mike ya zauna sosai ta iso gare shi ta ce, "Sannu
da hutawa Baba". Ya ce, "Ni fa na ce wannan Dije ce amma
canzawar da ki ka yi gaba daya ta hana na amincewa
zuciyata, keDije! Ke ce haka?" Tana cike da dariya tace,
"Nice Baba".
Ta durkusa bakin zaure ta fara gaishe shi yayin da ya
rinka amsawa baki bude, ya ce, "Ban taba zaton za ki yi
girma kamar jikin mahaifiyarki ba! Masha Allah tubarkallah,
Sannu da hanya, ya su Aminar da kannanki?" Ta amsa
"lafiya lau. Baba sunce duk suna gaidaku."
Yace "Shiga cikin gida ni ma gani nan shigowa". Tа
mike ta shiga. Ta cimma su Sabura da Ankudi ana nan
kamar yadda ta bar su, babu cikakkar tsabta kamar yaya
Amina. Ta yi ma Allah godiya da ya raba ta da rayiwa irin ta
su Ankudi, babu tsabta babu kamun kai balle uwa uba kula
da ibadar Allah, amma wajen yaya Amina dole ne ka'ida
wankan nan ayi shi sau biyu a rana, sallah da zuwa Islamiya
kuwa da ladan ya yi kiran sallah ne, kowa ya nemi butar
alwala, sannan babu hali karami ya raina na gaban shi,
20
idan bako ya yi sallama ya shigo gaba daya yaran gidan
za` a tarbe shi da sannu da zuwa a kuma gaishe shi, sannan
a ba shi guri ba'a zama inda manya suke. Tabbas Dije ta
sami kanta cikin canji kala-kala wanda ta ji dadin hakan.
Su Ankudi da Sabura da yaransu ko wanne ya yi wal
da ido yana kallon Dije, Duk da kishi ya turnikesu amma
babu mai kuzarin iya cin zarafinta kamar da, a dole kowacce
a dakale ta ce "Maraba da Dije". Ta ce "yauwa sannunku
gwoggo mun same ku lafiya?" Suka ce, "lafiya lau". Ta
sami kujera 'yan tsugunne ta zauna, me Ankudi ta gani,
oho, ta debo ruwa a kwano ta mika wa Dije. Dije ta amsa
cikin fara'a tana sha sannan Ankudin ta sake cewa, "zai fi
kyau ki shiga da jakarki zuwa dakina ko na Sabura bai dace
ki aje a tsakar gida ba."
Wannan ma ya kara baiwa Dije mamaki ta mike ta
shigar da jakarta hatta gyalenta ma sai ta aje ta fito ta
zauna ta na kiran kannanta.
Bayan ta yi sallar issha'i taci tuwo tace, "Baba zani
gidan Gwoggo Tambaya na gaisheta" Ya ce "To, kice ina
gaisheta, amma fa kada ki kwana a can ki dawo nan gida".
Ta ce "Lah Baba yanzu zan dawo ai nima ina son mu yi hira
da kai". Ya yi murmushi dadi ya lullube shi domin yau ji ya
ke duniyar ta yi masa tas, a dalilin ganin Dije, yana son Dije
son da ya ke jin zai iya bada fansar ransa akan ya kubutas
da ran Dije.
Haka itama Dije tana son Amina innarta sannan tana
jin dadin zama da ita, ko yanayin canjin jikin Dije ka duba
ka san tana jin dadin zama da uwarta, amma abin mamaki
son da Dije ke ma Malan Kado cikin kashi goma kashi biyu
zata iya baiwa uwarta Amina, tana son Babanta fiye da
son da ta ke ma uwarta, yayin da ita Amina tafi son Dije a
duk cikin 'ya'yanta.
Dije ta yi sallama "Salamu Alaikum". Inna Tambai ta
amsa sallamar Dije sannan Dijen tasa hannu ta yane labulen
dakin su kai ido nudu da Inna. Inna ta fid do ido ta sa
hannu ta dafe habar baki tace, "D-I-J-E!" Dije ta fada cikin
dakin da sauri ta zube kan tabarma ta dora hannayenta
21
Inna Tambai tana kyalkyatar dariya. Inna tace, "Wani iko sai
Allah! Yau ke ce ki ka canza kamanni haka? cikin dan
kankanin lokaci. Kai Allah dai ya saka mana tsakaninmu da
su Ankudi, duk sune suka tsangwameki suka hana ki yin
abin kirki. Yaya su Amina da kannanki?" Dije ta ce "Lafiya
lau. Ta ce, dan Aliah na ce tana gaisheki kuma wai kun
kyauta tunda kika kai ni baki sake zuwa ta." Inna ta yi
dariya ta ce, "Wallahi ba haka ba ne, kullun kina raina Dije,
idan na yunkura zani sai ki ga wata hidimar ta danne ni;
kuma, Malan ya sami kimanin wata uku yana fama da
zazzabi akai-akai." Dije ta ce, "Allah sarki, ba mu sani ba,
amma dai ya warware ko Gwoggo? ta ce "E ya wartsake
sarai Dije."
Sun sami fiye da awa daya suna hirar yaushe gama
amma zuciyar Dije batai mata dadi ba, dòmin bata yi mata
zancen da take son ji ba, wato ita dai ranta na ga Yusuf,
abinda take so ta ji daga bakin Inna labarin Yusuf ko ya
dawo