Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
akan batun aurenta domin ita abinda ta dasawa zuciyarta shi ne Yusuf yana son ta, illa wasu kyale-kyale na matan jami'a da suka debe masa hankali wanda ta san ita da an jure an yi bikinsu, zata jure da duk wani abu da zai rinka yi mata na wulakanci, har Ubangiji ya dawo mata da hankalin sa, to bata samu goyon baya ba. Ta dubi wata 'yar karamar agogo da ke bisa tebir ta ce, "Lah Gwoggo tara ta yi, bari na je mu yi hira da Baba, akwai wasu adduo'e da na ke son dauka a hannun sa." Inna Tambai ta ce, "To Dije in ce dai gobe anan zamu sha yinin mu? ta ce "E, isha Allah zan zo." Ta shiga shagon da ke kusa da anguwarsu ta sayi dan littafi da biro saboda daukar addu'a wajen Baba Kado. Ta yi sa'a Baba Kadon na tsaye suna sallama da amininsa malan lliya. Ta durkusa ta gayas da Malan lliyasu, ya сe, "Wato Dije idan da ban zo ba sai ki koma ba za ki je gidana mu gaisa ba ko?" ta ce, "Haba Baba wace ni? Aniyata saі gobe zan zo, ai ko ban yi niyyar zuwa ba na san babu yadda za'ai Baba ya amince min har na koma ban je na gaisheku ba. Malan Illiyasu ya yi dariya ya ca "To ne yadda 22 Ta yi mashi sai da safe ta shige cikin gida. Su Ankudi da yaransu ana zaune a falo suna hira ta yi sallama ta shiga ta nemi waje ta zauna. Bayan kamar minti goma Malan Kado ya shiga gidan ya wuce kai tsaye dakinsa yasa baki ya kwallawa Dije kira, ta isa dakinsa ya mika mata wata kullin leda baka mai kulle da nama balangu ya ce, ta je ta ci. To amma ita Dije sai ta hada kan kannanta suka zauna suka ci gaba daya. To ire-iren wannan zumudin na Malan Kado suke haddasa tsana tsakanin Dije da su Ankudi. Bata gama cin naman ba Malan Kado ya sake kwalla mata kira, ta kakkabe hannunta, ta dauki litafi ta nufi inda Malan ya ke zaune wato a bakin kofar dakinsa, ta nemi kujera yar tsugunne ta zauna ta gefensa, suka shiga hirar makaranta, tana bayyana masa irin matsalolin da ta fuskanta amma yanzu ta shawo kan komi. Tace "Baba akwai wasu addu'oe da ka sha fada min cewa idan mutun ya shiga cikin rudani ko damuwa ya rinka karanta su insha Allah zai shawo kan abinda ya dame shi" ya ce "E kwarai kuwa akwai su, kala-kala, sai ki shirya na rinka fada maki kina rubutawa." A kalla ya tsara mata addu'oe kamar kala biyar sannan ta tambaye shi na tsari da na aljanu suma duk ya gaya mata. A zuciyar Dije bata cika amincewa da kowa ba baya ga mahaifinta domin a ganinta shi kadai zai iya rufa mata asiri idan ta yi abin neman rufin sirri, tana son ta ji labarin Yusuf don haka take ganin wajen Babanta ya dace ta ji wannan labarin ba tare da an yi tseguminta ba. Ta cije ta daure ta sadda kai kasa nuna alamun jin kunya ta ce, "Baba" ya amsa amma kuma sai ta yi shiru ta kasa magana, ya dago kai ya dube ta ya ce, "Menene Dije?" ta ce "Wai Baba kuna samun labarin Yusuf?" Malan Kado ya yi shiru a bisa dukkan alamu Dije ta lura bai ji dadin tambayar da ta yi ba don haka sai ta yi dana sanin yin tambayar, Sun dauki lokaci babu wanda ya yi ko wani motsi mai karfi, ko wanne da abinda ya ke raya ma ransa zuwa can Malan Kado ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi yadda 23 na ga kin murje na dauka kin manta da żan cen Yusufa, ban yi zaton har yanzu kina tuna shi ba Dije. Ki vi hakuri ki manta da zancen Yusufa in Allah ya yaırda, za ki sami miiin da ki ke so tankar yadda ki ke son Yusufa, domin a yadda na sami labari, yanzu ko mahaifiyairsa kuka take akan yarinyar da ya ke nema da aure, gaba daya an ce ya canza rayuwarsa. Ki yi hakuri Dije da Yusufa kamar yadda na yi hakuri akan shi domin nayi iya kar kokar na yaron nan yaki dawo wa gare ki, har kudi na rabawa malamai ayi mana rokon Allah akan Yusufa amma kin ji shiru, saboda haka na dangana na bar wa Allah zabi yasa hakan tafi alhairi." Kan Dije na sunkuye a kasa, kunya da bakin ciki suka baibayeta, tabbas Yusuf dan sha'awa ne, hankalinta ya yi matukar tashi, shin me ma ya kai ta ta yi zancen Yusuf hakan ta kara tsananta tausayinmahhaifinta a ranta, wai har rokon Allah ys bayes da kudı ayi akan Yusuf bayan ta san yana yi da kan shi, mya ko alhakin mahaifinta ba zai kama Yusuf ba? Nan da nan idanunta suka cika da kwalla amma ta jure tasa habar zaninta ta goge. Та се, "Ваba, ka yi hakuri. In Allah ya yarda daga yau zan fita daga zan cen Yusuf a zuciyata ba zan kara tunaninsa ba". Malan Kado bai ce komi ba baya ga ajiyar zuciya. Ta kwan ta a dakin Ankudi ta yi lamo hawaye suka ci gaba da zuba ta gefen kunnenta, har yanzu ita tana mamaki ne irin zantuttukan da Yusuf ya ke fada mata amma ace wai bai son ta? Wannan shi yafi daure mata kai. Da niyyar kwana bakwai Dije ta sauka garin Bakori amma bacin ran da zancen Yusuf ya saukar mata sai ta ji kwata-kwata ta tsani garin. Dan haka wanshekare da Malan Kado ya ce "Mata yaushe ne komawar ta ki Malunfashi?" ta ce;" Baba ai kwana uku zan yi" ya ce, "Na yi zaton za ki mana sati anan" ta ce "Baba akwai bikin diyar kanwar su Baba Isa da za'a yi a Katsina shi ne na kë son na bi yaya." Abu daya Dije ta cire wa Malan Kado kewar tsohuwar matarsa Amina wato da sassafe idan ta tashi ta yi sallah ta kan share gidan lungu-lungu har zuwa kewaye wato bandaki, 74 cikin kwana biyu gidan Malan Kado ya canza ya rinka tuna haka su kai rayiwa da Amina. Lokacin da zata koma Malan Kado yu sai mata kaji goma. Inna Tambai ta sai mata man gyada da kubewa, haka nan Malan lliyasu ya aiko mata da kayan miya da barkono, ta sauka gida da tsaraba rankatakab. KASHI NA BAKWAI Yaya Amina na gindin turmi tana kulkula daddawa zata zuba a miyar yayin da Dije ke share tsakargida inda yara suka ci abincin rana. Malan Rilwan ya yi sallama kai tsaye ya shigo gidan. Malan Rilwan kanine ga Malan Isa babban ma'aikaci ne a garin Jos, yana daya daga cikin wa'anda su ke taimakawa su Amina da Malan Isa. Matar Rilwan daya da 'ya'ya biyar itama Binta matar Rilwan, ma'aikaciyace to ire-iren su burge yaya Amina don haka take jin zafi ada da za'a hana Dije neman ilmi. Dije ta zube kasa ta gayas da Baba Rilwan ya rike kugu yana girgiza kai ya ce, "Yaya Amina ka da kice min mutuniyarmu ce wannan 'yar Bakori?" Amina cikin nuna alamin jin kunya ta dan yi murmushi tace "Kai Rilwanu baka da dama fa!" ya ce, "Wallahi da manaki, kin san ni rabo na da ganin ta, tunda ta zo hutun farko, kin ga min yarinya ta zama mace sosai, yanzu aji nawa take?" Dije ta yi dariya ta ce saura wata biyu mu gama, da mun koma jarabawar fita za mu yi. Rilwan ya ce, "Da kyau, haka ake so, ina fatan dai ana abin kirki." Anan ne fa zancen yayi ma Amina dadi domin ta san diyar ta mai kwazo ce, sai ta ce, "To Rilwanu ka tsaya ka shiga mana ka zauna" Ya shiga dakin Amina ya zauna bisa kujera. Amina ta dauko masa refot din Dije wanda duk take daukar na daya yana dubawa tare da yabawa, sai Dije ta yi sallama ta shigo dauke da tire mai kwalbar kunun zaki da kwalbar ruwa da kofi ya ce, "Yauwa Dije, kamar kin san ina tare da kishi, ina fata kin yi shirye-shiryen shiga jami`a 25 jami'a" Dije ta koma gefe guda ta tsugunna ta dan sadda kanta kasa, tana satar kallon Amina. Amina ta ce, "Jamia! Sakandiren ma da yaya aka yi? wannan uban nata an ya zai bari kenan? Rilwanu ya ce, "Haba Amina, ki yi kokari ki samu ya amince, insha Allah ni zan dauki nauyin komi nata, domin ni ma tawa Hadizar bana zata gama kin ga sai na hada su tare" Dije ta ce, "Don Allah yaya ki tambayi Baba na nan gidan ya bar ki mu je ki ga Babana. Wallahi in ke ki kai mäi magana zai amince ya ban ni na wuce jami'a." Rilwan ya ce, "Gaskiya Hadiza ta fada zan yi ma Yaya Isa magana ya bar ku ku je Bakorin idan Malan Kadon ya amince, shi kenan sai ku aika min inshe Allah zan shirya komi sai su rinka zuwa jami'ar Jos ita da Hadiza ta waje na. Kin ga ma babu dalilin zama a makaranta, sai su zauna a gida kullun direba ya kai su." Malan isa yayi murna kwarai da shawarar Rilwan domin shi ma yana alfahari da basirar Dije. Suna isa Bekori grdan inna Tambai suka sauka, bayan sun ci abinci aka ce Dije ta je ta kira Babanta. Maian Kado ya ga Dije múrna ta lullube shi, tun zuwan da ta yi kwanan baya bata sake zuwa ba, sai dai idan ya matsu da tunaninta ya tura Tambaya ta dubo ta. Bayan sun gaisa tace, "Baba tare mu ke da Yaya Amina tana can gidan Gwoggo Tambaya tace ka je ku gaisa". Malan Kado ya rinka washe baki yana tunanin lalle kila Dije ta sami miji tunda har Amina ta zo da kan ta. Yadda Malan Kado ya ga Amina mulmul da ita sannan tana nan shar da ita sai shi ya ji duk ya muzanta a gaban ta, domin duk tsufa da rashin koshin lafiya sun bayyana a tare da shi. Suka gaisa cikin rashin saki jiki ko wanne na jin nauyin dan uwanse sei inna Tambai tace, "To Malan wannan tafiyar taka ca Amina ta yi maka". Kan sa a sunkuye yace, "To yaya aka yi?" Tambaya tace, "Sha'anin karatun Dija ne, shi ne Rilwan kanin Maian Isa da ke aiki a Jos yaca, ilen ka amince zai gama da tashi diyar su shiga jami`a. Malan Kado ya yi sauri ya dago kai ya dubi Amina 26 sosai, duba na hakika yace, "Ban amince ba, ni a zato na ma ca ni ke zancen auren Dije ya kawo Amina amma sai a zo min da wata magana ta keta haddin Allah, ina laihin wanda ta yi? Allah ya anfana ya isa haka, ki dubi Dije yadda ta koma kusan kansu daya fa da Amina! Sannan ace wai taje jama'a kamar da namiji." Amina tace, "Malan ba ni aron hankalinka nan, ka taba jin inda aka ce aure ya hana neman ilmi ko ilmi ya hana aure? Wallahi tana cikin makarantar idan Allah ya kawo mijin na kirki sai ayi auren, amma yanzu na hanga ban ga wani tsayayye ba, Allah kadai ya san lokacin auren mutun, saboda haka tunda Ubangiji ya baiwa wannan diya taka basirą ka barta ta nemi ilminta ba' a san iyakar al'umar da za su anfana də ita ba, wallahi da yau bata san komi ba su Rilwanu ba za su matsa maka ba akan son ta ci gaba da karatu, mun yi maka alkawari a yau ta sami miji za'a daura mata aure. Ka yi tunani ana son taimaka mata ne a bisa baiwar da Allah ya yi mata". Malan yayí jigum, can yace, "Haka ne Amina, yadda na ke jin zafin Dije kema na san haka kike jin zafin ta, na tabbata ba za ki so ta da halaka ba, tunda kin ga akwai alhari idan mun bar ta ta je neman ilmin shikenan a dai shaidawa Rilwan din wannan yarinya amana ce fa a hannunsu". Amina ta yi dariya tace, "Dan wannan Malan kada ka ji komi ka rinka sawa ranka tamkara gaban ka take ko a gabana, kar kaji komi wallahi." Dije da mahaifiyarta Amina suka koma Malunfashi cike da murna da zakwadin an amince masu zuwa jami'a don haka ko da Dije ta kare hutunta ta koma makaranta bata tsaya bata lokacin ta ba ta kama karatu fiye da yadda ta saba. A ranar da suka aje biro wato sun gama jarabawar karshe a makarantan 'yan mata ta garin Malunfashi a rannan Dije bata kara kwana ba sai dakin Yaya Amina. Wanshekare Amina ta ce ta shirya ta je ta yo sallama da mahaifinta Malan Kado domin a yadda Rilwan ya ce ran asabat zai zo ya tafi da ita za su fara kwas din konfuta na 07 wata uku kafin jarabawarsu ta fito. Dadi ya kara lullube Dije. Kwananta daya a Bakori ta dawo Malunfashi ta shiga shirin tafiya Jos. Mahaifiyarta Amina ta ce, "Ina so ki kara natsuwa bisa wadda ke gare ki, wannan gida da za ki wata rayiwa ce ba irin ta mu ba, rayuwa ce irin wadda sun mallaki komi na rayuwa, ta fannin abin duniya to kada ki ga an sakar maki komi, ki nemi wuce gona da iri. Ki iya da talaucinki haka nan ki tuna karatu za ki yi ki dawo wajenmu masu talauci, ki kama kan ki ban da kananan maganganu, sánnah ki yarda da Allah a komi na al'amarinki, yarda da Allah zai kai ki matsayin da ba ki zata ba, ki mallaki abinda ba ki taba mafarkin mallaka ba. KASHI NA TAKWAS Hadiza Abdulkadir ta bude sabon babin rayuwa mai cike da al'ajabi a birnin Jos. Gidan Rilwan gida ne irin na`yan bokon zamani duk abin jin dadin dan adam ya tanadar masu shi a gidan. Lokacin da Dije ta isa gidan tun a harabar gidan gaban ta ya rinka faduwa bal-bal, suna shiga falon hatta kafarta rawa take, ta nemi kasa bisa kafet ta yi zaune. Rilwan yace, "ki zauna bisa kujera mana". Amma ina! tamkar Dije bata ji shi ba ita dai gabanta kawai ke faduwa, bata taba ganin gida irin wannan ba. Dakunan bacci a bisa bene, don haka Rilwan ya haye zuwa dakin baccinsa yayin da iyalin gidan su ka san dawo war sa nan da nan suka zo falo gaida Dije. Babbar 'yar itace Hadiza ta mikawa Dije hannu tace, "Sannu da zuwa ni sunana Hadiza Rilwan". Dije ta ce "nima suna na Dije Kado". Hadiza ta yi dariya tace "sunan mu daya kenan" Mama Binta itama ta iso cike da fara'a tacе, "A'a sunanki Hadiza kinji daga yau kada ki sake kiran kan ki Dije Kado sai dai Hadiza Abdulkadir shi ne ainihin sunanki." 28 Hadiza Abdulkadir dai har yanzu tsokar cinyoyinta rawa suke yi a firgice ta ke, har Hadiza ta dauko jakarta ta ce ta zo su je dakinta inda zai zama dakinsu su biyu. Ganin yadda aka kayatar masu da dakin ya kara bugun kirjin Hadiza, komi ya kara rikice mata a zamanin da Hadiza ta shigar da Dije kewaye don ta yi wanka ta rasa yadda zata bullowa wajen wanka balle inda zata tsugunna don fitsari dole ta nemi alfarmar Hadiza don ta koyar da ita. To haka Hadiza ta rinka fuskantar irin wa'annan bokin al'ammura amma cikin kwana bakwai ta fahinci komi. Suka fara zuwa kos din konfuta na wata uku, inda anan kuma kullun suka dawo gida Hadizan Bakori ke kara yi ma Hadizan Jos bayani (yadda mama Binta ke kiransu kenan har sauran jama'ar gida suka dauka yadda za'a rinka banbanta su). Daga Hadizan Bakorin har Hadizan Jos babu wadda ta fito da sakamako mara kyau a lokacin da wata ukun su ya cika a makarantar koyon konfuta, saboda haka ne ma Baba Rilwan ya yi sha'awa ya sawo masu konfuta ya aje cikin gidansa har suka rika koyar da kananan kannensu. A daidai wannan lokacin ne kuma WAEC ta sakar masu sakamakon jarabawarsu. To Hadizan Jos mákarantar gwamnatin tarayya ta Bauchi ta yi don haka Baba Rilwan ya bada mota suka tafi Bauchi amso sakamakon jarabawa. Lokacin da za su shiga ofishin malamin da sakamakon ke hannunsa Hadizan Jos ta rike Hadizan Bakori gam-gam tace, "Wallahi Hadiza gabana tamkar ana luguden uku, uku, na tsorata kada fa na fadi jarabawar nan!" Hadiza tacе, "Haba don Allah ki rika addu`a Insha Allah za ki ci ne". Hadizan Jos tace "Masifar Baba kadai ma ta ishe ni". Ta ce "Babu komi za'ai nasara." Suka saki juna, Hadizan Jos ta murda kofa zata shiga ta juyo suka kara dubar juna ita da 'yar Bakori sukai murmushi tare da dagawa juna hannu, Hadizan Bakori ta ce, "Ina nan ina maki addu`a." Minti uku, minti biyar, har zuwa minti ashirin Hadizan 29 Jos bata fito ba, sai 'yar Bakori ta fara tsorata, tayi uagumi har tana hardewa wajen adclu'a, zuwa can ta fito ta fada kan Hadizan Bakori tana fadin taya ni murna Hadizaı, tare da mika mata takardar. Hadiza tana dubawa tare da cewa "Eye! Hadizan ba 7 Credit. Credit a lissafi, Credit a turan,ci ai kuma jarabawa ta hadu Allah ya maida mu clanshinki." Baba Rilwan ya yaba yace, "To abinda za`a yi gobe sai ku je Malunfashi ku amso ta Hadiza idan ta ci ku zo na shirya maku gagarimin bikin taya murna." Hadizan Bakori gabanta ya fadi ras wato tana cikin hatsari kenan tace, "Baba idan ban ci ba fa?" Yace, "sai ki sake daukar wata jarabawar har sai kin ci." Ai ko rannan 'yan Bakori ba ai bacci ba kwana ta yi cikin zullumi. Sun zuba ado na atanpa iri daya wadda Mama Binta ta dinka masu. Suna isa Malunfashi Hadizan Bakori tace a wuce zuwa makaranta kafin aje gida, Hadizan Jos tace, "Haba ba kya bari mu je gida ko ruwa mu sha?" `Yar Bakori ta galla mata harara tace, "Tafdjam! Ko kin san jiya kvvanan zullumi na yi, shi ne ba kya tausaya min? Ai duk na kosa na ga abinda na shuka ko hankalina ya natsu." Suna isa suka ci karo da malaminsu yace, "Ina taya ki murna Dije domin gaba daya jihar Katsina ke ce ki ka zo na daya a kyaun sakamakon jarabawa". Hadiza ta dubi Hadizarı Jos ta kwantar da kanta bisa kafadar `yar Jos tace "Na gode Allah da ya fid da ni wannan shedarar siradin." Lokacin da suke bude mota suna fita a kofar gidan Malan Isa, kowanne Hadiza ta koma mashi kamar bakuwa don tsarin kyau a cikin gida ma Yaya Amina na ta wangale baki ganin yadda diyarta ta canza wata uku kacal. Abinci kawai suka ci sukace zasu wuce Baba Rilwan yace kada su kwana kuma suna son tsayawa Bakori su gaisa da Baba Kado. Cikin kwana bakwai aka gama shirye-shiryen karatun su Hadiza suka kama karatu a jami'ar Jos; Hadizan Jos na 30 karanta fannim Public Admin,yayin da Hadizan Bakori ke karanta fannin Account. A farkon shekarar karatunsu direba ke kai su daga bisani Mama Binta da kanta ta rinka koya masu motar har suka kware suka rinka kai kan su makaranta, idan an tashi su dawo gida. Yadda duk ake son diya mace ta kile to Hadizan Bakori ta kai karshen kilewa, an goge an cakare har an koma bayan cakarewar an cake, abin nufi anan Hadiza ta zama macen shiga gaban kowacce irin kasaitattar mota ko kuma muce ta shiga dan tsuntsun nasara mai shawagi. Hadiza Abdulkadir sanbaleliyar mace, doguwa mai kyan tsayi, akwai ta da shafaffar mara, cikin ta ya dame daf don haka ya fid do da tudun mazaunanta a sarari damewar cikinta ya kara sawa kirar nononta su fito das. Abinda ke jan'ra'ayin jama'a da nacin kallon fuskar hadiza Bakori shi ne, `yan kananan hakora masu kyalli da daukar hankali yayin da suka yi daidai da `yan kananan labbanta, labban da akodayaushe suke walkiya. Hancin Hadiza dan guntu ne ya yi tsari da`yan kumatunta, 'yan gwibi-gwibi idanuwan Hadiza ko sune abin sha'awa a irin kallon Hadiza tamkar an watsa taurari don walkiya, mawuyaci ne Hadiza ta dubi mutun da kwayar idonta bata saukar maka da sha'awa ba, domin akwai baiwar kwarjini na musamman da Allah ya yi ma Hadiza cikin taurarin lelonta wannan kenan, akwai ta, da sambala-sambalan yatsu don haka ne ma a kullun idan tana latsa lambonin konfuta Hadizan Jos ta kan ce mata "kai Hadiza Allah ya yi maki baiwar yatsu na gari tamkar an halitta maki su ne don ki rinka watsa su a bisa konfuta." A cikin makarantarsu, Hadizan Bakori bata da kawa ko saurayi baya ga Hadizan Jos sai ko Abba Abba. Shi ko Abba Abba irin karatu daya suke yi da Hadizan Bakori sai dai ya na gabanta da shekara daya, saboda haka, a kullun suna tare suna bitar karatunsu. Ita kam Hadiza a yadda ta dauki Abba Abba abokinta, wani mutun mai natsuwa wanda ya san abinda ya kawo 31 shi amma shi abinda ke zuciyar Abba Abba son Hadizan Bakori yakes, so kuma wanda ya ke kyautata zaton zai kai su ga aure, domin shi a duniya bai ga abinda Hadiza zata yi ba bai birge shi ba, komi na jikinta sha'awa ya ke ba shi, ya yi kokarin ya furta ma Hadizan amma ta ki bashi fuskar hakan, har lokacin fitar shi ta zo. A wata rana yaje ajin su Hadizan Jos ya nemı ganinta, tace, "Yaya dai lafiya ko Abba?" Yace, "Babu wani abu Hadiza ina son mu yi wata 'yar magana ne da ke". Tace "To mu je mu zauna". Suka jera suna tafiya har zuwa wajen da aka tanada don dalibai idan suna son zama su huta, ya dan jima yana mata `yan kame-kame daga karshe dai ya yane rigar kunya yace, "`Yar Jos tsakanina da ku yanzu mun zama tamkar `yan uwa domin haka ma wasu ke dauka a cikin makarantar nan ganin ba ku kula kowa sai ni. To a gaskiya ni aski ya zo gaban goshi domin`yan kwanaki ya rage min na kammala karatuna kamar yadda kika sani, to amma wani abu ke damu na sai dai an hana ni na amayas da shi". Ya yi siru anan. Hadizan Jos tace, "Waye ya hana ka ka amayas?" Ya ce "Wanda abin ya shafa"; Tace, "Wa ke nan?" Yace, "А gaskiya son Hadizan Bakori na ke, so kuma irin na wanda zai tabbata ga aure amma ta ki ba ni hanya na fada mata shi ne na ke son ki taimaka min." Ta yi murmushi tace, "Haba kamar ba namiji ba, me zai hana ka nunawa Hadiza bukatarka a zahiri ai ina ganin kun yi shakuwar da ba za ka iya rufe mata komi ba". Yace, "Haka ne Hadiza, wallahi wayon tsiya ne da ita yadda duk na so na sako batun soyayya sai ta ki kamar wadda soyayya ta wahalad!" `Yar Jos ta yi dariya tace, "Shirmen Hadiza ne kawai wadda bata da lokacin samari yaushe har soyayya zata wahtalad, ka ban ni da ita zan yi mata magana komi kenan zan sanar da kai."`Yar Jos bata nemi yi ma `yar Bakori zancen Abba Abba ba sai da daddare bayan sun kulle kofa sun yi shirin bacci Hadizan Jos ta ki kashe lantarki, saiyar Bakori ta juyo ta dube ta tace, "Yaya ki ka zauna ba ki kashe mana, wuta ba, na yi zaton mun kare hirar yau 32 bacci za mu yi?"`Yar Jos tace, "Haka ne yau magana ce gare ni ina son mu yi zancen aure, ba kullun maganar karatu ba sai kace da karatu zamu lahira". Hadizan Bakori ta kyalkyale da dariya ta ce "Baki da lafiva Hadiza, da wa za ki maganar auren? Ba dai ni ba mara miji Ki bari in kin sami`yar uwarki mai samari sai ku yi".` Yar Jos tace, "Insha Allah ba kya kara ganina da saurayi ko ki ji na dauki wayar wani sai ta wanda zan aura, a gaskiya na yanke shawara na tsaida miji".`Yar Bakori tace, "Wai Dr. Sani?" Ta ce, "Insha Allah shi zan aura”. Yar Bakori tace, Yanzu me sunan ba kya tsoron matarsa?" `Yar Jos tace "Ban ga abin tsoro ba wajen mace `yar uwata, auren mai mata ba wani abu ba ne illa mu `yan zamani da mu ke neman mu canfa abun, ki tuna fa addininnu da al'adarmu sun amince mana da aje mace hudu matsawar zaka iya baiwa kowacce hakkinta. To sanin kan ki ne Dr. Sani a shirye ya ke ya mallaka min gidana kaman yadda zai mallakawa uwargidansa na ta, to sai kuma me? Tana aikin asibiti yayin da shi kuma ya ke aiki a kamfaninsa na kashin kan shi, ni ma yace a kanfaninsa zan yi aiki idan na gama. karatu." Hadizan Bakori ta yi ajiyar zuciya tace, "Ke shikenan kun gama tsara rayiwarku?" Tace, "E saura ta ki, tunda kina tsoron kishiya ga saurayi ya aiko ni gareki". `Yar Bakori tace, `Wanene?' Hadiza tace, `Abba Abba'. Hadizan Bakori ta yi dariya tace, "Ya sha gas, wai me ke damun Abba ne? Mutumin da na dauka tamkar dan uwana shi ne zai wani bullo da zancen so? To a gaskiya ban amshi tayinsa ba". Yar Jos tace, "idan ki ka yi haka ba ki kyauta min ba haka nan ba ki kyauta ma Abba ba". Hadiza tace, "To sai na cuce shi don na gyara masa rai? Kin san Allah mai sunan kada ya wahalad domin ni kam ban taba jin daidai da rana daya ba ina yi masa irin sha'awar nan ta saurayi da budurwa ko har na kai ga sha'awar ace yau ga shi a matsayin mijina, a kullun mu ke tare da shi na kan tsinci kai na ina tare da wani haramiyana, wato kaman kanih mahaifina ko yayana wanda mu ke uwa daya ko uba daya to ki kamanta kan ki a 33 irin haka, yaya za ai har soyayya ta aure ta shiga tsakaninku? Bana jin zan iya soyayya da Abba don haka kice ya yi hakuri mu kasance a matsayin `yan uwa ko a ina nake kuma ko wa na aura Insha Allah zai zama na daya abokin shawarata." Hadizan Jos ta yi shiru tana tunani, tabbas `yar Bakori ta yanke hukunci game da Abba babu saurany wani sa rai domin tace kamar haramiyarta take ganinsa, `yar Jos a hankali tace, `Na tambayeki tsakani ga Allah?" tace, "Insha Allah na yi alkawarin gaya maki gaskiya." Tace, "Wai akwai wanda kuka yi alkawarin aure da shi ne

Chapter 3 of 6