Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
na shi shiryeshiryen. Saboda haka da aka je kai kayan sa rana har da akwati shidda na lehe. Nan da nan Bakori ta diba diyar Baka Kado lehenta. rabin dozin,yan kari kuma suce dozin. Wannan zance ko ina ne a garin Rakori da Malunfashi む anobal STAA DA Dnuol lla at d stes eb saaoda TSyniKASHI NA GOMA SHA BIYU anntum anag met ey венс аg ay ab lsa sad syitaS Hadiza na zaure suna kallon wasan Samanja a talabijin sai ga kaininta mai bi mata dan wajen Yayaı Amina ya isko ta Keduna, nan talke Hadiza ta san babu lafiya ko kumas akan zancen suren ta ne, ta zare ido tace, "Saminualafiya,lullec me yasfanu, to Yayasceabaalafiya?" Ya sadda kai yace, yaw "lafiyarta lau, Alhaji Kado ne dai/babu lafiya yana asibitin Funtua kwance Bney em iria lusY anitods an emuk sd sindA Hadiza ta yi luu bisa kujera sai hawaye rau rau, "me studA ya same shi Saminu?5Yace, "An ce wai kewayar gona yaddiisl je sai dai aka maido shi gida barin jikinsa ya shanye." ed em irla Karfe shidda na yamma Hadiza da Saminu sun iso gud asibitin Funtua, hankalinta ya kara tashi yadda ta ga bakin Alhaji Kado ya jirkice tayi kuka ta yi kuka har sai da ta san vavix kuka ba zai mata maganin komi ba sannan ta hakura. Tana erda nan zauna tare da su Malan Iliyasu can wajen karfe tara nalauek dare sai ga suInna Tambai, anan suka dawo da wani sabon kukan.stnores s вnenлu ly usb st awuat ly et aslulleo isa Inna Tambai ta lallashi Dije suka tafi Bakori ta kwanaA a can amma asuba na yi ta dawo Funtua gani take ta yisogal kamar zarta iske ya mutus sy syhams haао ву вyhsb ly вy ise Misalin karfe daya da rabi na rana Armiru ya iso yace mata ya yi waya ne Kaduna matar Baba Garba ta ke sanar 00 61 masa garabinda ya faru shi ma daga Abuja ya ke. Tace, "Wallahi ciwon Baba kuma ya tashi". Amiru ya ce, "Dama yayi masa kárfi haka?" Tace, E' yace, "Amma Hadiza ya dace mu kai shi wata asibitin da tafi.wannan". Tace, "in dai law sbud cayill 57 82 on samu ne na fi son A.B.U. Zariya". Yace, "A to barı mu ja mu ga likitan wannan asibitin ko?" Suka jora zuwa ofishin likita suka yi masa bayanin bukatarsu ya dauko katin Alhaji Kado ya duba sannan ya rubuta takarda wadda za'a kai can A.B.U. Zariya. Ya debe su a motorsa sai Zariya sai da ya tabbatas an duba Alhaji an bashi gado sun shiga yi masa abinda ya dace, sannan yace Hadiza ta zo ya kai ta G.R.A gidan abokinsa da safe sun kawo ta shi kuma ya wuce Kaduna. Kimanin kwana biyar haka Amiru ya rinka jele hanyar Zariya har sai da ya ga sirikinsa ya fara gane mutane, sanna kuma kullun zai ga Hadiza ta rungume shi tana ba shi abinci. Sai hankalin Amiru ya kwanta ya ci gaba da harkan kasunwancinsa. Da zai tafi Lagos sai ya bar wa Hadiza cellular din sa ya ce "idan akwai wata damuwa ki yi min waya, da zarar na sauka Lagos zan sanar da ke lambar wayan daki na, haka nan ga ta ofis din mu na Kano da Abuja ga kuma na abokina Yusuf shi ma yana aiki ne a Abuja sannan ga ta mahaifina!" Hadiza ta bude ido ta се, "lah ba na iya yi ma Baba waya," ya ce, "haba Hadiza ashe, shi ma ba Babanki ba ne, in dai ki na cikin damuwa, ki buga mashi." Ta raka shi har gindin mota, tana yi masa Allah ya kiyaye, hanya, ya ce, "kin tabbata dai wa'annan kudin sun ishe ku?" ta ce, "Haba Amiru sai kace wadda zata sai rai, yaushe zamu kashe wa'annan kudade." Tana zaune kusa da Babanta tana bashi ruwan lemo sai cellular ta yi tsuwa, ta dauka ta yi kunnenta a zatonta ko Amiru ne, sai ta je an ce, "Ina Amiru" ta ce, "ya je Legos?" aka ce, "wa ke magana?" ta ce "matarsa ce Hadiza" sai ya yi dariya ya ce, "Ran amariya ya dade, idan ya bugo ace ina san magana da shi abokinsa ne Yusuf daga Abuja;" ta ce "zan sanar da shi, sai anjima." Alhaji Kado ya rinka badardarawa maganarsa guragura wai menene kuma wannan? Hadiza ta yi mai bayani. Ya bude baki numa alamun yana mamaki. ita da su Malam Iliyasu suka rinka yi mai dariya.. 58 Ana ta murna sauki na ta samuwa, daga Legos Amiru ya yi mata waya ya ce, "yau dai sauran kwana ashinrin da biyar bikinmu. Ubangiji Allah ya ba Baba lafiya don mi ji dadin shagali." Hadiza ta ce, "amin" ya ce, "ki gaida min Baba, sai na zo gobe." Da azuhur bayan su Malam lliya sun yi mai alwala sun kawo dutse ya yi sallah. Kafin ya kwanta, sai shakuwa har idonsa na kafewa. Nan da nan Hadiza ta ruga kiran likita, suna isowa tana rike da hannun likita. Likita na duba Alhaji Kado, amma i.na, babu Abdulkadir, ya amsa kiran sarki Allah. Hadiza ta yi waya dakin Amiru amma shiru ba'a dauka ba, ta yi ofis din su nan ma ana ta surutu bisa layin, kwatsam idonta ya fada bisa lambar Yusuf. Ta na yi bugu daya, Yusuf din ne ya dauka, ta ce, "don Allah ka nemi Amiru ka sanar da shi sirikinşa ya rasu yanzu a nan Zariya." Kafin Yusuf ya yi wata tambaya, ta kife layi. Tana sharan hawaye a fice zuwa bakin titi, ta nęmo masu motar haya wadda zata dauki gawar Alhaji Kado. Kafin mangarib har an kai shi makwancinsa, ya bar su Hadiza da juyayin rashinsa da sauran rigingimun duniya wa'anda ba su karewa sai in irin wannan ta afku. Ana sallar mangarib, yaya Amina da mijinta suka iso amma ita anan zata zauna har sai an yi sadakar uku. Kashegari Hadiza da Inna Tambai suka gyara dakin marigayi Kado suka shinfida dardumarsa inda za su rinka zama kenan. Ita da yaya Amina da Inna Tambai da mutanen da suka zo masu ta'aziyá, koda yake inna Tambai bata ga ta zama ba domin Hadiza ta bayas da kudi an yanka rago sannan an sawa buhun shinkafa ta ce a dafa saboda zuwan baki na nesa. Aiko misalin sha biyun rana sai ga motoci biyu ta maza da mata daga Kano iyayen Amiru. Inna Tambai ta yi murna da shawarar Hadiza da suka gyara dakin marigayi da ina za su saka wa'annan kosasun mutane? domin dakin su Ankudi, zaman shi sai ka daure. lyayen Amiru har da daron sinasir da daron waina 59 da na shinkafa suka zo suka ce a baiwa jama'a sadaka, sannan kuma ga buhun suga da buhun shinkafa, suka ce daga mahaifin Amiru shi ma yana nan zuwa gobe, sannan Amiru ya ce, ayi masu gaisuwa kamin dare yana nan zuwa yau. Inna Tambai ta yi hanzarin sauke abinci sannan ta zubawa bakin Kano. Sai da suka yi Sallah sannan suka kara bada hakuri suka Kano, suna yabon Hadiza akan lalle Amiru zai mori mata ga kyau ga addini sannan ga natsuwa. Tsakanin ta da kowanne bako ya shigo gaisuwa a natse cikin mutunci sai ta juya bisa karatu wani dan karamin kur'ani da ta ssyo a Madina. Idan har ta yi magana mai tsawo, to da Inna Tambai ne, ko ana bukatar wani abu. Rasuwar Baba Kado ta kama alhamis ne, saboda haka a lokacin da Yusuf ya sanar wa Amiru a waya yana shaida masa Hadiza ta yi waya tana sanar da shi mutuwar Babanta, gaba dayansu mutuwar ta bugi zukatansu, domin a gaskiya Yusuf, koda bai san kowacece Hadizan ba, ya tausaya mata a bisa yanayin sautin muryarta, sai ta dawo mai da tunanin ta shi mutuwan mahaifin, tabbas babu abinda ya fi mutuwa ciwo, radadinta a zuci duk yadda dan adam yaso ya bayyana bai iyawa, sai dai ran da a kai ma ka, sai ka ji abinda kowa yaji. Saboda haka, sai Yusuf ya rinka ba Amiru hakuri har ya ce, "ina fatan zaka shigo jirgin Abuja don mu raka ka Malunfashi wajen ta'aziya;" Amiru na so ya ce masa "ai a Bakori ne" amma sam maganar ta kasa fita bakinsa saboka juyayin tsohon Hadiza sai dai kawai yace; "To ina nan zuwa." Falanke ma da ya ji tafiya ce wajen kauyensu sai ya ce, "yallabai zan biku", suka ce "Bissimillah!" A ranar jumma'a suka baro Abuja. A motar Amiru su uku ne da Yusuf da wani direban kanfaninsu sai wata galleliyar motar Yusuf da ya shigo da ita kwanan nan daga Hong-Kong su Falanke ne da wani abokin su da direban Yusuf. Sun iso Zariya ne Amiru ke cewa ina fatan ka zuba komi da komi a sabon gidanka na Bakori dòmin ina ganin 60 anan zan zauna har sai an yi sadakar bakwai, kasan mahaifin Hadiza mutumin Bakori ne." Yusuf ya juyo ya dube shi ya ce, "amma ce min ka yi yar Kaduna ce, iyayenta ne a Malunfashi;" Amiru ya ce, "kai labarin Hadiza na da tsawo. Ainihin mahaifinta ma dan Bakori ne, uwarta ina jin aure ne ya kai ta Malunfashi koko yar malunfashin ce, shi ne ban gane ba, idan de mun je gidan, kila kai ka gane tunda dan gari ne." Shi ma kan shi Yusuf sai labarin ya dan rikice masa ko me yasa, oho! Suna isowa Bakori gidan Yusuf yana a bakin hanya ya ce, "ga fa gida Amiru mu tsaya mu aje kayanmu tukun?" Amiru ya ce, "haba mu dai fara isa gidansu Hadiza, ka san kuwa ban san wannan shi ne gidan ka ba? domin kwanan baya mun zo nan Bakori da Hadiza har ta ke cewa, kai amma gidan nan ya birge ni, na ce mata, ai dole ya baki sha'awa domin irin wannan gidan a kauye?" Yusuf da Amiru su kai dariya. Me kuma zai faru, kwatancen da Amiru ke yi ta inda suke bi duk hanyar gidan Malam Kado ce, har aka isa kofar gidan.Yusuf ya amince gidan Baba Kado ne, ya dora kan shi cikin tafukan hannunsa, nan da nan idanunsa suka yi jajur sai kwalla shar, da ya tabbatar dai Baba Kado ne ya rasu. Mutuwar ta bugi Yusuf tamakar yadda ta bugi Hadiza domin har ga Allah Yusuf yana son Malam Kado kamar yadda Kado ke son Yusuf. Su Malam Tukur ne da Malam Iliyasu da sauran dattawan gari ke zaune a zaure, suka zauna suna juyayi. Malam Tukur ya ce, "Yusufa ashe ka ji mutuwar?" Yusuf ya ce, “E to". Sai kawai ya kara fashewa da kuka da ya tuno yau shekara daya kenan rabban sa da zuwa wajen Baba Kado suka mike za su shiga cikin gida, a bisa hanya ne Amiru ke cewa, "ashe ka ga ne Baban?" Yusuf ya ce, "Wallahi Amiru, ina son tsohon nan tamkar mahaifina." Suna shiga dakin da Inna Tambai ta ja su, wato inda Hadiza ta ke, anan ne kuma Yusuf ya kara zubewa da ya sha wani mamakin da ya ga Hadiza. Itama Hadiza ta dubi Yusuf ta juya ta maida kallonta 6.1 akan Amiru sannan ta sadda kai hawaye shar suka rinka fita. Koma mai Hadiza ta canza, babu tantama yasan wannan Dijensa ce, itace Amiru zai aura, lalle wannan abu da daure kai. To amma abin mamaki daya ne anan, me yasa ako yaushe yazo Bakori mahaifiyar sa Gwoggo Halima ta ke damunsa da fadan ya yi aure, bayan ta san Hadiza na nan bata yi aure ba amma ta ki gaya masa? Ya kawad da wannan tunanin ya daga kai ya dubi Dije tabbas itace. Mutuwar Baba Kado ta dawo ma da Yusuf da mutuwar mahaifinsa danya. Hadiza ta daga kai tace, "Amiru kana nan ko har sai lahadi idan an yi sadakar uku?" Ya dube ta yace, "ina nan ma har sai an yi sadakar bakwai, saboda ina ma da masauki gidan wannan abokin nawa da na ke gaya ma ki Yusuf." 62 DANDANO DAGA LITTAFI NA UKU Bayan an yi sadakar uku ta marigayi Alhaji Kado ran lahadi kenan, Amiru na can gidan su Hadiza sai ya dawo gidan Yusuf don ya dan kwanta yà huta, me zai faru? Yusuf ne a dakin da ya zauna ne Amiru yayi masauki duk ya yi dai dai da kayan Amiru, ga hotunan Hadiza nan kaca-kacă, sannan yana ta bincike masa takardu. Amiru ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, yayin da Yusuf ya yi kasake na rashin gaskiya. Na lokaci mai tsawo sannan ya ce," Amma Yusuf ka ba ni kunya, me za ka nema wanda ba za kà iya tambaya ta ba? Tabbas na san dai bai shige al'amuran Hadizan ka ke neme ba, kana zaton zan rubuta wayar matata ne a takardu ko adireshin gidansu? Niko wane irin dakiki ne da ba zan iya harda cewa ba a ka? idan su ka ke nema ba ni biro na rubuta maka.Kana tsammamin Hadiza wawa ce kamar kai da har zata iya saurarenka! Ka tuna fa kai ne ka ce baka aurenta don rashin fasali har dakin innarta? amma ka ba ni kunya kai ba amini ba ne maci amana ne." Yusuf ya daga mai hannu ya ce, "Dakata dan Allah Malam, maganar fa ta isa, sai ka ga ya min waye baya kuskure? Na yi kuskure kuma na gane kure na, duk abinda za ka yi sai ka yi dan zan koma neman Dije kuma Insha Allah ni ne mijin Dije ba dai kai ba, komi ka ke takama wallahi akan Dije na shirya..." 63 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6