a kauyenku Bakori?" Itama ta yi dariya tace, "Ke ko
meyasa ki kai min wannan tambayan?"`Yar Jos tace, "To
na ga kowa yace yana son ki ba kya yadda ya-zo gida ma
sai ki bata maganar, sannan na lura kin faye zurfin ciki shi
ne na yi tunani kila kina da wanda ki ke so, ba ku gama
shirye-shiryenku bane." Hadiza tace, "Bana son na karyata
ki amma ke saboda Allah duk wanda ke nuna suna so na
kin ga ya dace na aure su?" 'Yar Jos tace, "Me zai hana su
ba maza bane?" Hadiza tace, "To shikenan na amince da
ke anan mu bar wannan labarin amma bari na ba ki tarihin
aurena da wani dan kauye dan uwana."
Hadizan Bakori ta warware mayar Jos tarihin
rayiwarta har zuwa ranar da ta dawo gidansu.
Hadiza `yar Jos ta baro gadonta ta dawo gadon
Hadizan Bakori tace, "yanzu Hadiza wa'annan matan da
mu ke zuwa sune suke gana maki irin wannan wahalad? Ta
amsa "Wallahi kuwa yadda ki ka gan su a raine din nan sai
mugun abu da bakin wulakanci iri-iri."
`Yar Jos tace, "kai lalle akwai maza `yan garari`yan
iska a duniya yanzu shi wannan Yusuf duk irin kaunar da ya
rinka nuna maki amma shi ne a lokaci guda ya je ya yi maki
irin wannan cin mutuncin a gaban Inna Tambai mata mai
mutunci da ita? Wai ko dai tabin hankali ya same shi iyayen
ba su gane ba? Amma ni yanzu ina ganin mai kyau kamar
ki a fadin jami`armu? Kin san Allah wani lokaci har tunani
na ke yi na ce ko mutumin kauye zan aura domin ni sai na
ga mutanen kauye kun fi mu kyau". Hadizan Bakori ta cе,
341
"Ina son ki ko don seli ki mai suman."
Hadizan Jos tace Ya Ubangiji Allah ka hada ni da
wannan Yusuf sai na rama maki wulakancin da ya yi maki,
shi din me? Don Allah ba ki ji labarin inda ya ke yanzu ni ko
ne mabuta masa na zage shi tas, wai ke don Allah wace irin
zuciya gareki da har kika kyale shi, ai idan nice har gaban
Gwoggo Halima zan same shi na wanke shi tas."
Hadizan Bakori ta ce, "Wallahi ban kara jin labarinsa
ba. Tun tamba yar da na yi ma Babana a hutuna na farko da
na ba ki labari amma ran da mu ka je Bakori na hada ki da
inna Tambai ki sha labarin inda ya ke clomin ta sani sai dai
ina tabbatar maki idan don ni za ki yi nnasa tsiya don Allah
ki bari domin idan na yi haka ban gode wa Allah kenan ba
a bisa baiwar da ya yi min, lalle na san na shiga fitinu a
dalilin shakuwa da kaunar da na ke ma Yusuf, amma kuma
canjin rayiwar da na rinka samu a dalilin rashin aurensa sai
ta zamar min kwanciyar hankali da daukakar rayuwa."
"A gaskiya na san na so Yusuf amma na san ina kara
son shi ne saboda zan bar azabar gidanmu na sami yancin kaina to irin rayuwar da na samu a gidan mahaifiyata da ci gaban makaranta ta sai suka gusar min da Yusuf a raina, sai kuma Allah ya kara yi min wata daukaka ta basirata wadda a dalilin ta na zo wannan gida, kin ga na sami ci gaban rayiwa, domin rayuwa ma a wannan gida makaranta ce, yanzu dubi ko na'urorin da ke kicin idan ba dalilinBaba Isa ba yaushe zan zo nan har na san su? Ki tuna fa ki ga yadda gidan mahaifina yake to yau y shi na zo gidan da zan kwaba kek ko burodi cikin minti goma a injin sannan na gasa cikin yan mintoci, da sauran girke-girke, haka nan yau ni Hadiza Dije na iya tuka mota bayan mahaifina keke gare shi? Kin san Allah ba na jin haushin Yusuf da rashin aurena domin ko da zan sami irin wannan rayuwar a gidan
sa karshenta zan sha wuya can gaba, domin na lura namijin zara ne. Kin ga ran da ya sami dadin raina min wayau zai yi yace zai auro `yar duniya kamar shi su ci duniya yace ni yar kauye ce, domin sai yanzu na ke tsanar tsarin rayuwarsa cika son komi na `yan duniya ni kuma a lokacin rashin ye
35
wayau sai na rinka biye masa wai don kada ya kira ni
bakauya.
Suka yi shiru na dan lokaci can Hadizan Jos tace,
"Kai! Ni kam Allah ya hada ni da Yusuf na fada masa
magana domin wanda Allah ya ba mata mai hali irin na ki
ya gama mallakar komi a rayuwa amma don tsageranci irin
nasa zai ma Baba Kado haka, a gaskiya Hadiza akwai
yarinyar da Babanta ke son ta kamar ki?"
Hadizan Bakori ta kyalkyale da dariya tace,`Kin ji
sokoncin naki ba, ba ga ki ba da Baba Rilwan ba?" "Yar Jos
tace, "Wai ba kya jin yadda ake kwafdata da zagi wani
lokacin?" Hadiza tace, "Ai ba kya ji ne kamar wata yar
bebi, kyan ki Dr. Sani ya nemi bulala, idan mun kai mashi
ke". Ta kyaikyale da dariya tace "Sai ya nemi bulala biyu
kenan."
*
Abba Abba ya hakura ya sakawa Hadiza Abdulkadir
ko a ranar da suke sallamar ban kwana, wato a rannan zai
koma Bauchi mahaifarsa ya kammala jami'ar Jos. Suna
tsaye ya dafe hannunsa jikin dalbejiya yayin da ita kuma
Hadizan ta mikar da dogon hannunta tana tsinko ganyen
dalbejiya, ya yi gyaran murya, yace, "Hadiza na ji sakonki
wajen Hadizan Jos amma ni ban dangana ba ina tabbatas
maki wata ran sai kin yi da nasanin kin amincewa da ni,
amma dai ga adireshina nan da nambar talfon din gidanmu
ina saurarenki ako dayaushe, zan yi zaman jiranki ko nan da
shekara nawa ne, har zuwa ranar da ki ka janye sarautar
haranta ta soyayya a tsakaninmu". Ta yi murmushi tace,
"Ni kam na fi daukar kauna ta yanuwantaka da
mahimmanci fiye da kaunar soyayya wadda ke karewa balle
a zamanin nan namu mai cike da rudin kwadayi."
Abba yace, "Kwadayi kamar yaya?" Tace "E mana
yanzu za ka kulla soyayya da mutun dan lokaci kadan zaı
iya barinka a dalilin ya ga wadda ta fi ka, kyau, ko ta fi ka
kudi da dai sauransu duk me ke kawo haka in ba kwadai
ba?
Abba yace, "Haka ne amma ni ina daukar wannen
36
dama can ba soyayya bace ta gaskiya ta riya ce, amma
kuma wani lokacin skwai fa kaddara".
KASHI NA TARA
A kullun dai su Hadiza suka ziyarci mahaifinta a Bakori
ba shi da wata magana irin ta, "Wai Dije yaushe za ai aure
ner" Ta kance, "Wallahi Baba da zarar na sami mijin zan
kawo maka shi da kai na ni kai na ina son na yi auren
saboda danmiwar da na lura kana nunawa haka nan kuma
ganin yanzu ni ce babba a gidan nan". To irin wa'annan
kalaman na Dije ta samu ta danne zuciyar Malan Kado daga
zancen aurenta sai ya rinka tausaya mata yana ganin kamar
da gaske bata sami mijin ba ne, ya yi alkawari a ransa zai
daina damunta da magana ya shiga yawaita yi mata addu'a.
A babban bankin C.B.N Rilwan ya samarwa Hadiza
da Hadiza aikin hidimar kasa na Kaduna. Suka zauna a
gidan Baba Garba cikin Anguwan Sarki shi ma Baba Garba
kani ne wajen su Rilwan yana aiki a matatar mai.
Bai fi wata uku ba kacal su kammala hidimar kasa a
wani lokaci sun je Jos hutun kwana uku da yamma Mama
Binta ta duba firij din ta na kicin ta ga bata da kayan salad
sai ta kwallawa su Hadiza kira. Hadizan Bakori ce ta fito a
guje tace,`Ga ni mama'. Mama tace, `Ina daya Hadizan?"
Yar Bakori tace, "Tana wanka, kin san Dr.Sani ya yi waya
daga Legos yace ga shi nan zuwa". Mama ta yi murmushi
tace, "Shiririta ni dauki makullin karamar mota ki yi sauri ki
sawo min kayan salad da alayyahu don Allah maza ki kawo min."
Hadizan Bakori ta fito sanye cikin kyakyawar shiga
ta yane kanta da wani gyale na zamani ta fito tana sulbi ta
nufi inda ake aje motoci, ta shiga ta tayas. Maigadi ya dage
mata koía ta fita da sauri.
Daga can gefe su Rilwan ne da abokansa suke hira,
a cikinsu har da babban bako Mai Martaba Hakimin wani
gari ne a can cikin jihar Katsina, shi ma kusa ne a gwamnatin tarayya amma samun sarauta da tara dinbin dukiya ya sa
37
ya yi sallama da siki ya rungumi sarautar da yan kanfanonin
da ya kafa. Wannan mutun shine yallabai Mamud, idonsa
fes akan Hadizan Bakori, ya tambayi Rilwan "shin wai ina
ku ka sami waccan yarinyar ne dazun na ganta ta gitta ita
da Hadizan gidan nan yanzu kuma ta fita da motar gidan?"
Rilwan yayi dariya ya bashi cikakken bayanin Hadiza,
yallaba Mamud yace, `Idan haka ne ko ina son ta zan ko
aure ta'. Rilwan ya kara dariya yace, "Sarkin hadama kana
nufin ka yi mata uku?" Yace, "shi ne me, ba basarake na ke
ba?"
Rilwan yace "Na yi zaton sarautar`yan boko a ke".
Mamud yace, " Yan bokon yanzuai ba sa anfani da
turancinsu wajen tara mata, sai`yan bokon da waton na
zamanin 1960". Rilwan yace, "To ni sai na ce Allah ya
bada sa'a ai ba na hana yallabai diya ta ba."
Can muna iya kiran lokacin karfe tara saura`yan
mintoci na dare dn karamin yaron Mama Binta yayi sallama
dakin su Hadiza yace, "Anti Hadiza Baba yace ki yanka
lemo ki kai falon baki". Ta mike da sauri ta yi abinda aka
umurceta.
Ta yi sallama ta shiga sai Yallabai Mamud kadai zaune
a falon, zata aje a bisa tebir yace "Kawo min nan gaba na,
ke ce Hadizan Bakori?" Ta dube shi a tsakiyar fuskarsa
tace, "E ni ce, a kira Hadizan Jos ne?" Ya kyaikyale da
dariya yace "Amma fa wannan lakani na ku da ban sha'awa
ya ke, sai dai Hadizan Bakori na ke son magana da ita".
Hadiza tace, To' ta nemi waje ta zauna.
Ya shiga tambayarta labarin yadda a kai ta zo jami`ar
Jos ta bashi bayani, sannan ya nemi jin labarin iyayenta
duk ta gaya masa, ya dan fito daga cikin kujerar ya tsura
mata ido yace, "Hadiza a yau na ganki na kuma yaba da
abinda na gani don haka ina gayyatanki da ki zama ivalina?"
Tamkar ruwa ya ci Hadiza ita ko me yasa rayuwa ke latsa ta
ne irin haka? Ita dai ta san ba kowa bace illa talaka likis
wadda bata a bakin komi gidan. Ubanta na son ta yi aure
fiye da zaton dan adam ko don ta farantawa Baba Kado rai
to amma me yasa take cin karo da mazan da bata so?
38
Tabbas babu abin ki wajen Mamud sai dai kawai ba irin
rayuwar da ta ke son samu bane a gidansa domin tuni ta
sha jin labarin gidan sa wajen Hadizan Jos.
Gidan Mamud babu abinda bai mallakawa wa` annan
mata na shi guda biyu ba, to amma babu zaman lafiya;
bala'in kishi suke yi tamkar su halaka junansu, ashahadu a
wuyansu an ce akwai dan amaryar da ya rasu ana kyautata
zaton uwargidan ta kasheshi don kada ya girma ya gaji
Mamud.
Yallabai yace, "Ba ki ban amsa ba Hadiza". Ta dawo
daga tunanin rayuwar gidansa ta ce, "Ka ba ni lokaci zan yi
tunani". Yace, "Ban dai yi maki ba kenan, kila na yi ma ki
tsufa?" Ta yi mai wal da 'yan kyawawan hakoranta ta сe,
"Lah wallahi babu zancen tsufa, ka san komi yana son a yi
nazari". Sai ya ji Hadiza ta kara shiga mai cikin rai, wannan
fara'ar da ta yi tabbas tana son shi sai ya ce ya amince.
Mama Binta tace "To Hadizan Bakori ya kamata dai
ki kwantarwa da mahaifinki rai inda duk ake son samun
miji yallabai Mamud ya kai miji sai dai kuma idan akwai
wani kudirin a ranki". Hadiza ta ce, "A gaskiya Mama ina
ni, ina fitinar matansa wallahi ban iya wa". Mama Binta ta
'sha mur tace, "Kina nufin shi ma watsa maganar ta shi za
ki yi? Karyarki ta sha karya in don maganar matansa na yi
mai wannan maganar ya ce ba gida daya zai aje ku ba, su
suna can inda suke a Katsina amma fa ba za ki yi aiki ba."
Yar Bakori ta daure rai ta shiga tunanin abinda zai je
ya komo a kanta, ita kan gaskiya ba za ta cuci kanta ba ta
auri gidan da ake bala'i kiri-kiri, yadda duk Mama Binta ta uya Hadiza ta ki amincewa, domin a san ran Mama Binta
ayi bikinsu gaba daya nan da wata uku idan sun kammala hidimar kasa.
Kashegarin da su Hadiza za su koma Kaduna tare da
Mamud a kai tafiyar motar su Mamud na gaba ta su Hadiza
na baya har su ka isa gidan Baba Garba.
Mamud ya kebe Hadizan Bakori yana ci gaba da kokarin shigar da kansa amma abisa dukkan alamu bai samu
fuskarta ba, ya kawo kudi dubu ashirin ya bata, da farko 39
an ta ki amsa amma sai ta yi tunanin don ta raba shi da
wa'annan kudi har wani abu ne a wajensa? Sai ta amsa ta
yi godiya.
Ko sisi bata taba ba ta adana a banki ma`ajiyar
kudinta. A wannan dare kwana sukai zance daya na Mamud
Hadiza da Hadiza.
Bayan sati daya Mamud ya sake dawo wa Kadina
wajen Hadiza har ya shaida mata idan zai koma Katsina zai
biya ta Bakori ya gaida Malan Kado Sannan ya shiga
Malunfashi ya gaisa da su yaya Amina. Hadiza dai bata ce
masa komi ba domin a ganinta ta kai matsayin a bar ta ta
zabin mijin aurenta da kan ta, saboda ta wuce zamanin
auren dole.
A ranar da yaje Bakori tamkar an yi ma Malan Kado
gafara kowa ya gan shi ya san yana cikin murna, domin
Allah ya kawo masa mijin Dije miji kuma na fada aji ako ina
cikin fadin kasar nan, lalle Allah na amsar addu`o` in bayinsa
in dai sun roke shi, wai yau kamar Dijen da ake muzantawa
gidan sa itace babban mutun irin Yallabai Mamud ke
tsananin so da aure? Baba Kado ya je masallaci ya yi nafila
raka'a biyu yana ma Ubangiji godiya.
a
A Malunfashi ma gidan Yaya Amina bayan tafiyar su
yallabai Mamud, maigidanta Malan Isa ya shigo suka zauna
a daki suka zubawa kudin da ya ba su ido, Amina tace,
"Yanzu Malan duk fadin jihar nan ta mu wanene bai da
labarin wannan mutumi da kyawawan halayensa?" Malan
Isa yace "Ke maganar jaharmu kadai ki ke yi, gaba daya
kasar za ki ce, a gaskiya wannan yarinya ba karamar sa`a
gare ta ba a rayuwa sai kawai ki shirya ki je can Jos din ki
ji yadda aka tsayar da ranar bikin waccan Hadizan sai a zo
aje Bakori a samu a daidaita ayi masu biki rana daya kamar
yadda shi Alhaji Mamud din ya bukata".
Amina ta sadda kai tace, "Ai ni Malan tsakanina da
zuri arku bani da kalmar godiya sai addu`ar fatan alhairi
kawai, duk abinda za ai ma yaro sanadiyar arziki sun yi ma
wannan yarinya ko `ya`yan da muka haifa da kai iyakar
dai zumunci kenan." Ya ce, "Wannan duk ba wanı abu bane
40
mu dai fatanmu Allah ya daidaita Dije da wannan bawan
Allah yasa itace sanadiyar zaman lafiyar gidansa domin na
san aminin Rilwan ne ba tun yau ba."
Amina bata tsaida ranar tafiya Jos ba tana ta yan
kintse-kin tsenta a tsanake, yayin da hankalin yallabai Mamud
ya jirkita ya dimauce bai ganin kyan wata diya mace face
Hadiza a kullun yana bisa hanyar Kaduna yana kuma dankara
mata iyayen kudi ita kam Hadiza tana adanawa a banki.
Suna kammala hidimar kasa shugabansu na wajen
aiki yayi mata alkawarin sun dauke ta aiki, saboda haka
wannan ya fi komi farinciki wajen Hadiza domin tana tunanin
yadda zarmanta zai kasance a Malunfashi kafin ta sami aiki
domin tana ganin bata iya zama Jos babu Hadizan Jos
kuma Mama Binta na so ta auri Mamud.
Suna isa Jos komi ya kacame na shirye-shiryen bikin
Hadizan Jos da Dr. Sani inda zai aje ta Abuja wato inda ya
ke zaune kenan da kanfaninsa.
Kusan a wannan lokacin kowa ya azazzalawa `yar
Bakori ganin ta sami miji mai son ta.
Yaya Amina ta iso, sai da ta turke Hadiza a gaban
Mama Binta sannan ta ji wannan danyen labari wai bata
son Mamud, kafin Hadiza ta ankara har idanun Amina sun
juye tamkar an watsa mata barkono tace, "Tafdijam! Ai ba
ki isa ba dan ubanki, tun yaushe na ke jin labari kina samun
samari kina basarwa, to wannan kam tunda ya nuna kauna
babu abinda zai sa a fasa."
Hadiza ta bata rai ta dan muskuta tace, "Ni wallahi
Yaya bana aurensa, tunda na ce bana iya rayuwar iyalan
sa, ban ga dalilin da zai sa ku tada hankalinku ba."
Amina ta harzuka zuciya ta zo mata wuya, ta ce, "To
sai ki fada mana wanda kike so tunda mu ba mu isa ba."
Tace, "Ni a yanzu ba ni da kowa a dai kara min lokaci."
Hadizan Jos na zaune can gefe daya ta yi tagumi
tana jin badakalar da ke faruwa akan Hadizan Bakori, ita
kanta ta dan tsani Hadizan Bakori anan domin bata son
taurin kai iri wannan, tunda tace babu tsana tsakaninta da
Mamud me zai hana ta hakura da yadda iyayen ta ke so?
41
ita kuma wadda ake abun don kanta ta kakure ta na,
ts shakar kuka. Mama Binta tace, `A gaskiya Hadiza ki baiwa kan ki shawara wannan ba zancen bata rai ba ne har
ayi kuka, zancen gaskiya ne randa ka rasa mai fada maka
gaskiya ka shiga uku, ki jure kawai ayi maku bikinku
hankulanmu su kwanta, ba kya tausayin tsohonki? Wallahi
Mamud yace da suka je gaishe shi kamar ya hade su don
murna, amma kuma ace duk ke kadai ki watsa farin cikin
kowa?'
Wasu hawayen suka taho a guje da ta ji an anbato
Malan Kado, tasa hannu ta goge ta murje hancinta ta ce,
*Insha Allah zan yi masa bayani zai fahinceni." Amina ta ja
tsaki tace, "Zancen banza me ke gareki wanda za ki fadi
mashi, to ko wannan dan iskan yaro Yusufa ki ke zaman
jira?" Hadiza ta yi war da idanu bakinta a bude, itama `yar
Jos ta bude bakin suna mamakin maganar Yaya Amina.
Yaya Amina ta cigaba da cewa, "Idan shi kike kunata kina
da wahala, domin uwar da ta haifeshi ma ance yanzu kuka
take da shi, saboda ya yi kudi don kudi amma yana can ya
budewa kadangarun bariki kunne, iyakar su da shi ya aiko
masu da kudi amma shi yana can yana shagalinsa, yanzu
wannan ne abin saurare?"
Hadizan Jos daga can gefe tace "A'a Yaya ku
daina wannan maganar ko ni na isa shaida Hadiza bata
jiran Yusuf."
Amina tace "To ta fadi mana uban da take jira yaya
zata mai da mutane wawaye?"
To iyakar fada na iyaye Amina da, Mama Binta sun yi
ma Hadiza amma zuciyar Hadiza ko gezau.
Tsana da kananan maganganu babu wanda Hadiza
bata samu ba a lokacin bikin Hadizan Jos, kowanne ya
tsinci kansa cikin jin dadi a zamanin bikin amma ban da
yar Bakori. Wani karin bacin rai ma shi ne a lokacin bikin
kusan Mamud anan ya tare yana lallashin Hadiza wanda
har ya sa Rilwan ma ya tsoma baki ya rinka lallashin Hadiza
wannan shi ya kara tayas da ran Amina. Wai Dijen da ba
kowan kowa ba za'a zauna ana lallashi bayan da can an ba 42
wani yaro mara kwabo yace bai so amma a yau tana yi ma
mai hannu da shuni yanga. Bayan ta koma Malunfashi Amina
ta shirya ta je Bakori gidan Inna Tambai ta sa mijin Inna
Tambai ya nemo mata Malan Kado ta sanar da shi halin da
Dije ta ke, shi kan shi bai ji dadin labarin ba, hankalinsa da
na Tambaya ya tashi suna al`ajabin me ya sami wannan
yarinva. Tambaya tace, "Malan ko dai tun farkon yarinyar
nan su Ankudi sun yi mata asiri ne abin fa da ban tsoro,
yanzu idan ka tara`yan mata dari akwai mai kyan diyarmu
Dije! amma ace wai bata yi aure ba har yanzu kai Malan da
sake."
Amina tace, "kada ku zargi kowa isgilanci ne irin na
dan yau, ai ni yanzu wannan yarinyar har tsoro take ba ni,
na yi fadan na yi amma ko gezau, sai shegen kukan tsiya?"
Malan Kado yace, "yanzu yaushe zata zo nan Bakori?" Tace,
"Na ji tana cewa dai zata zo cikin satin nan idan ta sami
hutun kwana biyu ka san ta fara aiki anan Kaduna inda tayi
hidimar kasa sun dauketa aiki."
Malan Kado yace, "Wa'annan mutane suna fa da
mutunci sun kama ta sun rungume ai bai dace ayi masu
haka ba." Tambaya da Amina suka ce, "Sabo fa da Allah!"
Yace, "Ku ban ni da ita zata zo ta same ni in Allah ya yarda
karshen watan nan za'a daura masu aure."
Ta sha ado da wata doguwar riga mai kamar alkyabba
ta yane kanta da gyale mahadin rigar kai da ka ganta ka
san girman jami` a ne, domin ilimi ne ke bugun kyau yayin
da kyau ya gogu da jin dadin rayuwar gidan masu da shi,
kai da ganin launin fatar`yan yatsunta ka san sun murzu
da shafar mai mai gyara launin fata."
Tana rataye da`yar jaka a kafada yayin da dandako
ya ke gabanta dauke da akwati don karami na zamani, ta doshi gidan Inna Tambai, Hadiza Abdulkadir kenan. Suna shiga gidan Inna ta amshi akwatinta ta balle jaka ta mikawa
yaro naira goma sabuwa fil. Inna Tambai tace, "Eye ka ga fa mutanen banki!"
Sai da mangariba Baba Kado ya iso wajen bakuwar
tashi suka hadu shi da Inna Tambai inda suka shiga ba nan 43
su ke fita ba, ita dai kanta a sunkuye lalle bata da mafita
sai wajen Allah domin wanda take sa ran samun jin sanyi
shi ma bayan su ya ke.
Tace, "Baba ka duba matsala ta don Allah da kyau
wallahi wallahi na yi kokari na ga zan iya auren wannan
mutumin ko don saboda kai ma amma na ka sa, dalilina
daya ne Baba shi ne iyalen sa." Ta fayyace masa labarin
irin zaman matan Mamud kaf sannan ta kara da cewa, "to
Baba wai shin ko ya aje ni gidana daban ai dai zaman matar
shi na ke wata ran dole ne mu hadu kuma idan mutun mai
mugun abu ne ai ko ba gida daya kuke ba sai ya sami
hanyar da zai tsangwameka, ni kam Baba na sha wuya a
zamanin kuriciyata bana son na kara fuskantar irin wannan
matsalar ko kuma dan da zan haifa. A gidan Mamud fa har
dan amaryar ake zargin uwargidan ta baiwa guba yaci ya
mutu sabada masifar kishi yanzu Baba ina mu ina irin
wannan rayuwar? Ka yi hakuri Baba.insha Allah aurena ya
kusa domin ina ji a jikina."
Malan Kado ya dubi Tambai yace, "idan haka ne ke ai
Dije tafi mu gaskiya." Tambaya ta ce lalle mu bamu san
tarihin gidansa ba, ina fa dalili za mu kai yarinya cikin fitina
balle kishinmu na mata yanzu suna jin ya aje ta gidanta
daban za su dirar mata."
Malan Kado ya aiki Inna tambai Malunfashi akan ta
baiwa Amina hakuri a kyale zancen Mamud, ita ko Hadiza
ta koma fagen aikin ta a kaduna tana zaune abinta cikin jin
dadi a gidan Baba Garba a kullun kwanan duniya sun kashe
fiye da awa suna hira da Hadiza daga Abuja maganar dai
kenan "Wallahi yar Bakori ki yi aure ashe babu abinda ya fi
aure dadi idan ka sami masu halin kirki kamar irin su Dr.
Sani." To irin wannan labarin na `yar Jos ya kan tayas da
hankalin Hadiza har ta ji kamar ta yi ma Abba Abba waya
akan ya zo su yi aure amma kuma babu sha`awa wadda
zata haifar masu da jin dadi auren." Yau ma laraba aiki ya
kacame masu don haka bata sami dawowa gida ba sai gab
da sallar mangariba, me zai faru ta cimma a falo, ita da
Baba Garba da matar Baba Garba tace, Lah! Yaya sannu
44
da zuwa saukar yaushe?' Kallo ma bata ishi Amina ba balle
ta tsinka mata, ta gayas da su Garba da matarsa, sannan
ta subuls jakarte daga kafada tare da takardun da ke
hannunta ta shige daki ta aje ta fada kewaye ta yi alwala ta
fito ta vi sallar mangariba sannan ta koma falo ta nemi
gefen kalet ta zauna tare da hade kafafunta.
Amina ta juya a fusace ta dubetta ta ce "Munafukar
banza munafukar wofi, kin je kin shiryawa ubanki karyar
da ki ka saba, shi kuma don rashin tunani ya hau kai, to
Allah ya ba ku sa`a tunda ba mu da mutunci ba mu da
daraja a idónku ai ban ga anfanin zamanki ba anan, domin
Rilwan da Isa da Garba duk daya ne sai ki koma can gidan
ubanki ki karaci sakarcin ki." Nan da nan Garba ya dakatar
da ita yace, "Haba! Haba!! Yaya Amina menene na gorin
gida? Mu mun fid da tsammanin Hadiza ta rike `ya yanmu,
idan ta rike kanınanta ai mu ta yi mawa, ban ji dadin wannan
magana taki bia, don Allah idan rai ya baci a san abinda ya
dace a fadi."
Duk wannan bai sa Amina ta saurara da bala'i ba
haka nan sam bata amince da zamanta ba, sai dai ta koma
can Bakori har sai da Garba ya yi ma Rilwan waya yayi ma
Amina fada sannan ta dan sausauta amma da sharadin
kada Hadiza ta sake zuwa wajenta a Malunfashi.
Hadiza ta yi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita ta
kwana tana rokon Amina amma kemerme Amina ta ki janye
hushin ta.
A kodayaushe tana kokarin rubuta mata wasiku na
neman gafara amma dai babu amsa. A wata jumma'a ta
shirya taje ta yi kwana biyu a Malunfashi, babu dai maganar
arziki a tsakaninsu sai dai akwai banbanci tunda ta gaisheta
ta amsa. Lokacin da zata koma Kaduna ta shirya tsab,
kkarsierita maza suka daukar mata kavanta ta durkusa gaban Amina tace, "Don Allah don