Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Izgili SARAUTA JAMILAH MUHD, AHMED (Mrs Bashir Salisu the Door) IZGILI JAMILA MUHAMMED HAKKIN MALLAKA Jamila mohd ahmed SHEKARAR BUGU 2014 GODIVA Ga Allah S.WA) ya bani ikon yin wannan rubutu, salati mara adadi ga shugaban halitta annabin mohmed (S.AW) GARGADI Ba'a yarda wani ko wata ya sauya wannan littafi ta wata siga ba, ko daukar wani abu a ciki ba tare da izinin mai littafin ba, a kiyayc Ban yi wannan littafi dan cin zarafin wani, ko wata ba, kagaggen labari nc, da na rubutu shi dan nishaɗantar da masu karatu, ba dan cinzan ko tuno asirin wani ba, dan haka IZGILI JAMILA MUHAMMED IZGILI C ikin mutukar nutsuwa take takunta wanda yawancin samari da mutane suke ganin yangance da ita amma kuma ba haka bane haka Allah yayota, ita bata sanin sanda take yin yangar haka tafiyarta take, dan ita a rayuwa bata iya sauri ba, komai nata cikin nutsuwa take yinsa gami da wata irin rausaya tamkar bishiya kuma natural ne daga Allah amma bayin kanta bane, dan ita bata sanin sanda take yi, sai dai ta ji kawayenta suna fadar wai ta ci ka yanga komai zata yi a yangance take yinsa duk sanda suka fadi haka sai dai ta yi dariya dan ta san idan zata kwana dubu tana gaya musu ita bata san yadda ake yin yangar ba bare ta yi, baza su yarda ba, dan haka take rabuwa da su, 5 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan ta san haka take ba wata yangar da take yi. Tun da ta taho ya kura mata ido kur ko kiftawa ba ya yi gaba daya hankalinsa baya kan abokin nasa da yake ta faman rattabo masa bayani ina shi kuwa hankalinsa ya yi gaba bai ma san me yake ba, gaba ɗaya yarinyar ta gama burgeshi. Nutsuwarta da shigarta sun burgeshi. Sanye take da dogon hijabi ruwan toka har kasa da duk alamu hijabin Islamiya ne dan tun ɗazu yake ganin 'yan mata masu kalar Hijabin su na wucewa sai dai ita har da nikabi a fuskarta kuma hijabinta har kasa ne saɓanin na wadanda ya ga ni, wata dai-dai gwiwa ne wasu ma dai dai cinya shi dai tun dazu daya fara ganinsu suna wucewa bai ga mai hijabi kamar nata ba saboda ita har wajen idan sahu yazo mata. IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta wuce ta gefensu idanunsa kyam akanta suna yi mata rakiya. Alhaji Umar mai akwai da yakewa abokin nasa baya ni. Ya ji ya yi shiru ya dan kalli inda yake sai ya kula gaba daya hankalinsa da nutsuwarsa suna wani gurin can, basa kansa. Ya lura ya kurawa guri daya ido ya kalli inda yaga yana kalla bai ga komai ba sai kawai mutane da ya ga suna zirga zirgarsu yawancinsu duk 'yan Islamiya ne da suke ta tururuwarwar tafiya zuwa gidajen iyayen su. Ya dan taɓa kafaɗarsa gami da kiran sunansa. Alhaji Mansir dan kimanin shekaru saba'in da biyar, ya yi firgigit ya juyo gare shi tamkar wanda ya ta shi daga barci ya ce, “Am! Alhaji Umar me kake cewa ne?" 7 IZGILI JAMILA MUHAMMED Alhaji Umar ya ce, "Ina hankalinka ya tafi ne?" Alhaji Mansir ya ce, "Na dan tafi wani tunani." Alhaji Umar ya ci gaba da yi masa baya ni ya ce, “Mun yi dai dashi Nan da sati hudu zai turo mana da cikwan kudin dan wallahi sai da nai masa jan idanu, in shi yana takamar dan zamani ne to ni nashekaran jiya ne, dan na ga jiya naga yau, kuma sai dana jaddda masa in har lokacin yayi na ji babu labari to wallahi kotu zan maka shege dan baka ga yadda ya dinga bani hakuri ba da ya ga na je masa ba sauki yana ta makyarkyata da ya ji zancan Kotu yana bada hakuri nan na taho na barshi. ". Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan ni zan tafi yadda mu kai da Alha ji Auwal game da aikin titunan nan zan ma waya.' " IZGILI JAMILA MUHAMMED Alhaji Umar mai Akwai ya ce, "To babu damuwa," Su kai Musabaha. Alha ji Mansir ya shiga dankararriyar motarsa ya tafi. Zaune take atsakar gidansu tana tankaɗan dawar tuwan dare Innarsu Kuwa tana daga can gefe tana kaɗa miyar Kuka, kuma suna ɗan taɓa hira mahaifinsu ne Malam Usuman ya yi Sallama gaba ɗaya suka amsa masa ya shigo hannunsa rike da dan autan Innarsu ɗaya Hannun kuwa bakar leda ce yake rike da ita Inna Lariya ta saki Kadin miyar da take yi ta shimfida masa wata sabuwar tabarma da take jingine gefe guda tana masa sannu da zuwa Hadiya da sauri ta karɓi ledar da take hannunsa ita ma ta nai masa sannu da zuwan Inna ta dauko kofin silbar dake ajiye a gefe guda 9 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda aka ci ka shi da sassanyar ruwan Tulunta ta a jiyewa maigidan tana karai masa sannu. Ya sha ruwan sosai sanyinsa ya ratsashi sannan yayi hamdala ya dire kofin shima ya nai mata sannu da gida. Aliyu dan Autan Inna yana daga gefe sai murmushi yake faman dukawa gaba daya ji yake tamkar an sakashi a gidan Aljanna saboda dadi ya san tunda yaga Abbansu da leda yasan yau da cin kayan dadi, shi yasa ji yake tamkar zai sume saboda murna, shi ma zai nunawa su Abdul Abokinsa kayan dadin da Abbansa ya siyo musu ko sa dainai masa gorin babbansa baya siyo musu tsarabar kasuwa kullum, Abdul sai ya yi masa dariya saboda shi Abdul din babansu ko da yaushe ya dawo daga kasuwa sai ya siyo musu kayan dadi su lemo, ayaba, . 10 IZGILI . JAMILA MUHAMMED abarba, Kwai, dafaffe, Biskit, youghort, wata rana har da gasheshen nama ko Kaza kuma ko babansu bai dawo da wuri ba to da sassafe sai Abdul ya ajiye ya nuna masa dan haka shi ma yau tunda Abbansu ya siyo musu tsarabar kasuwa to shi ma ba zai ci ba sai ya ajiye da safe ya nunawa Abdul ya dai nai masa dariya yana cewa babansu baya yo musu tsaraba idan zai dawo daga kasuwa, kalubalenku iyayan yara gaskiya da yawa iyayen yara abinda muke bama kyautawa yadda zamu dinga bawa yaranmu abu suna fita da shi suna nunawa yaran makota ko kuma yaran abokan zaman mu idan gidan haya ne ta yadda zaki ga an bawa yaro abu ya fita da shi cikin yaran gidansu yana ci a irin haka ana samun matsala babba, saboda wani yaran zai ‘yan musu wani kuwa sai dai ya ɗagawa sauran 11 IZGILI JAMILA MUHAMMED yaran hankali suna gani yana ci ba zai ba su ba, haka za ki ga yara suna rusa kuka duk su dagawa iyayen su mata hankali dole sai an basu irin abinda wane yake ci kun san yaro da gasa wata uwarma zaka ga ita ke tura yaranta waje cikin yara ya ci abin sai ka ga ta dauki abu ta ba shi sai ta maza je ka gurinsu wane ku yi wasa ko kuma fita tsakar gida gurin su wane ka ci mana, to gaskiya irin haka babu dadi ke dan asan kuna cin abu sai kin tura yaro dan a gani alhalin yana dagawa yaran mutane hankali. Akwai matan da suke cewa yaransu kada ka cinye duka mana ka rage da safe ka nu̟nawą su wane, da dai ire-iren haka, gaskiya mata mu daina irin wannan idan ke kuna da halin cin abu bai ka mata ki dinga turo yaranki suna dagawa wanda 12 i IZGILI JAMILA MUHAMMED kika san basu da halin wannan abin dan Allah mata mu daina Allah ka iya mana. Inna Lariya ta juyo tana kallon Malam din fuskarta fal da farin ciki ta ce, "Malam yau dai da alamar dawa Tai nama.? Tun da na ganka da leda.' " Shi ma murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Yau kam Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai godiya." Ta ce, "Gaskiya kuwa, ba ka ga auta ba ma baki yaki rufuwa yarasa inda zai sa ransa saboda murna sai wata dariya yake ɓangalawa gaba daya su kai dariya har da Hadiya wadda take kaɗe zaninta ta matsar da garin tana cewa. "Abbu Kalli irin zaman ma da yai ." har da tankwashe kaafu.' Suka kuma yin dariya. Malam Usman ya ce, “Bari dai in bude tsarabar nan in raba kowa ya dauka 13 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan naga dattijo na ya kagara kowa ya ci ko ba haka ba." Ya ce, "Hakanne Abbu su ka kuma yin dariya." " Malam Usman ya kalli Hadiya ya ce, "Zo ki dauka ki wanke. Ta ce, "To" Cikin nutsuwarta ta dauki ledar daya tureta gefe ta dauko wata 'yar madaidaiciyar roba ta juye abin dake ciki mangwaro nene lafiyayyo lafiyayyo masu kyau manya manya. Ta wanke su tas sannan ta kawowa Innarsu dan ta san ita zata raba dai dai nan Bintu tai sallama ta shigo mallam ya kalleta ya juyo da kallonsa ga Innar da take raban Mangwaron ya ce. "Wai shin Lariya bansa dokar fitar yaran nan waje ba, In dai fitar ta wuce cikin wuce wannan lokacin. 14 IZGILI JAMILA MUHAMMED Cikin tsananin ladabin Innar har da dan dukawarta daga kan kujera ‘yar tsugunne da take kai ta ce, "Ka fada.?" Ya ce, "To to raina ni a kafara yi da zance bana san abu ayi sanin kanki ne babu abinda natsana irin a dinga barin yara mata suna kaiwa magriba a waje, har nake kafa miki misali da cewar ko aike ne in har magriba ta sawo jiki to ki dinga hakura har na dawo ni sai in je, shi ma dattijo sai da nai masa faɗa, da har na same shi a waje yana wasa ke kuma babu ruwanki da kisa ayi kiransa ya dawo gida tun da yamma ta yi ko.?" Inna Lariya cikin ladabi gami da kwantar da harshe ta ce, “Ka yi hakuri Malam dan Allah Allah ya huci zuciyarka wallahi dole ce ta sa na aiketa kuma bama ta da lafiya ba, gidan babansu na aiketa dan dazu Iya Saude ta aiko min 15 IZGILI JAMILA MUHAMMED idan nadaka garafuni in bata to nai duban duniyar nan ban gan shiba sai bayan ɗan aiken ya tafi sannan na ganshi dan sai da na caje ɗakina sosai to shi ne da suka ta so Islamiya na ce tai maza ta dawo amma dan Allah ka yi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba, ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Allah yasa." Ta yi saurin cewa "Amin" Tai wa Abbu Sannu da zuwa sannan ta mika ledar da Iya ta aikota ta kawowa Innarta su Innar ta bude taga curin fura ne da kuma nono mai kyau ta ɗaure ta kalli Malam ta ce, "Yau shi kenan ba za a ci irin tuwan nawa ba dan ga shi nan iya tayi maka haji da Umra." Malam Usman ya saki dariya ya ce, "Lallai kuwa yau tuwanki ko kallo bai ishe ni ba dan haka yi maza ki dama min 16 " * IZGILI JAMILA MUHAMMED kafin in dawo daga masallaci dan ga kira nan a na yi." Yana gama maganar ya karɓi butar da Hadiya ta miko masa ya fara alwala su ma gaba daya suka mike dan bada farali Aliyu auta ne yai zaune yaki ta shi. Inna ta ce, "Ya dai dattijo.?' Ya ce, "Inna mangwaro." Nan tai dariya ta ce, "Kayi sallar mana tukunna ko kaga nace su dauka kai kuma na hanaka.” " Ya mike da sauri damin yabi Abbansu masallaci dan in dai bai je ba zai iya cewa kada a bashi mangwaron tun da bai bi jam'i ba. **** Yau ma kamar ganin da yai mata kwanakin baya sai dai yau tana rungume da alkur'ani ta zo ta wuce ta gabansa cikin nutsuwar nan tata ya rakata da idanu 17 IZGILI JAMILA MUHAMMED tana dan yin yanga baya ya ji samarin da suke kofar gidan da yake makoftaka da gidan Alhaji Umar mai akwai daya saurayin ya san shi dangi tane ɗaya ne bai sani ba, ɗaya saurayin ya ce, "Gata nan fa mutuniyar taka." Kanti ya juya baya. Bashi ya saki dariya ya ce, "Wallahi Allah ya suturu bakui in ji kishiyar mai dorina ina zan iya." Kanti ya juya baya "Ai ba zan iya koyaushe dan cinikin da nayi akasuwa su kare akantin nan mutane ba. Nura ya ce, "Yanzu ina jin ta daina tunda yai mata illa." 29 Bashi ya ce, "Ta daina me? Kallo kafarta ka gani mana malam tamkar ta turawa saboda tsahar mankanti fuskarce dai dai ta ga ji da man shi yasa ta lalace take rufeta yarinya sai shegen jiji da kai 18 IZGILI JAMILA MUHAMMED ke da fuska ta riga tai dameji har kece me wani ɗagawa mutane kai." Su ka sake dariya suka tafa Alhaji Mansir ya ce, "To me ye ma'anar Kanti. Ya juya baya sun santa ne ko̟ ku ma dai ita ma bata da nutsuwa tamkar su, dan kallo daya za kai musu ka san su din kwararrun 'yan duniya ne, haka zuciyar Alhaji mansir ta dinga masa tambayoyi barkatai wanda ba shi da amsar su, dai dai nan Alhaji Umar mai Akwai ya fito hannunsa dauke da wasu takardu ya karaso inda Alhaji mansir yake tsaye jikin motarsa, ya mika masa hannu gami da cewa “Ga_su_nan ka duba su, jibi jibin nan nake son tafiya Kaduna akan aikin makarantun nan. " Ya ce, "Insha Allahu zan yi kokarin ganin na gama su jibin su kai sallama ya shiga motarsa ya tafi. 19 IZGILI JAMILA MUHAMMED BAYAN SATI UKU Hadiya ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta kai dubanta ga Jana data ke ta faman baza powder Hadiya ta ce, "Dan Allah Jana kibar saka powder nan haka kin ga yamma ta yi kada Abbu ya dawo ya tarar bamu dawo ba gobe ba zai sake barina fita ba." Jana ta dan dauke idonta daga kallon Mirrow ta ce, "Dan Allah kada ki takuramin ki barni in yi kwalliyata cikin nutsuwa dan na sanki da shegiyar hayyata in ke bakya abu sai ki hana masu yi suyi." Hadiya ta ce, "Yanzu duk wannan baza eye shadow da wannan jam bakin da kika gabza ba ki yi minti sha biyar kina yi ba, ai ban miki magana ba, to sanin ki da nayi naga ko kin gama fentefenten naki ba gama kwalliyar bace dan sai ki kara 20 IZGILI JAMILA MUHAMMED PROSTY wani minti sha biyar din kawai kina kallon madubi kina kara baza powder ja na ta ajiye sosan da take shafa powder ta kara gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta ta ce, "To da zaki ishe ni da Ina ta shafa powder ca nake ke ma kin shafa ko ke naki ba sai ni zaki hurawa wuta.' " baki gaAnty Meena ta shigo tana fadin ita ai shafawar masu hankali ta yi ba irin taki ba da sai a kusan karar da ita ashafawa daya, ke in dai zakiyi kwalliya sai ki shafa powder wajen sau goma. " Jana ta cuno baki tana kunkuni ita kuwa Hadiya dariya take mota ta ɗauki Hijabinta ta saka gami da ɗaura nikaf dinta ta ce, "To fi'ili madi ai sai mu tafi ko?' Jana ta kalleta wani takaicinta ya kamata tace dan Allah dubeta haka kawai kisa kanki a Uku ki dinga yawo cikin 21 IZGILI JAMILA MUHAMMED wannen zirmemen Hijah ki wani rufe fuska ke ba matar Liman ba zafi duk ya damc ki, dan Allah dubeki duba kayan dake jikin ki Hadiya tai saurin daga Nikaf dinta tana kallon Jana ta ce "Mc kayan nawa su ka yi.?" Jana ta ce, "Riga da siket ne ajikinki sun yi miki bala'in kyau sun yi cif-cif a jikinki tamkar ajikinki a ka dinka su saboda kyan da kayan su kai miki amma zaki kassara rayuwarki ki rufewa mutane, to ba a haka bane zaka samu mai son ka wanda zai ganka ya ga ka yi masa amma ke kullum zurum-zurum cikin hijab har da su nikaf shi yasa har yanzu baki da saurayi ko daya, to yaushe mutum zai ce yana sanki alhalin bai ga abinda yai masa a jikinki ba bare ya ce, yana son ki. Ta cije gefen danyatsanta ta ce, "Wayyo Allah garin dadina nesa in ji 22 IZGILI JAMILA MUHAMMED Angulu da ta lefa masai ai wallahi da ni Allah ya bawa farin ki gashinki, dirinki idanunki muryarki, wallahi ba karamin yaki zan yi ba don sai na saka samari runtsċ ido sai na daga musu ganye da duk wankan da nai sai na sumar da samari warwas Allah yai miki kira ba ta Allah Sarki ba ya yi miki halitta ba wadda miji zai ce shiga daka na yi ba, Amma kina cutar da masu sanki ni na tabbatar ko sau daya kika cire Hijab din nan da wannan Nikaf din na tabbatar sai kin saka maza karo." Anty Meena ta kaiwa bakin Jana duka ta ce, "To taki yin yadda kike so ke ganin fito da tsiraici waje shine wayewa to wallahi ba wayewa bace, sai ci baya wanne namijin ne kin gama tallar Nono da kugu awaje zai kwashe ki sai kace mara mafadi to bara in baki misali ke ce 23 IZGILI JAMILA MUHAMMED kika ga a titi ana sai da cincin ga wani abude kura da iska duk sun koɗashi ga kuma wani a cikin glass a rufe sai mai cincin zai baki nawajen nan wanda saboda kura da ta badeshi har ya fara canja kamannin shi, "Ai na san babu ta yanda za'ayi ki yarda ya baki wannanAlhalin kina ganin yarda yake sai dai ki ce na rufen nan kike so, saboda yafi mutunci to haka ma maza suke kallan duk wata mace mai bayyanar da jikinta mazan titi suna gani haka suke kallanta tamkar wannan buɗaddan cincin din da dattin duniya ya gama badeshi.. Hattara dai mata masu irin wannan hali masu gani cinyewarke nan to wallahi ci baya ne ba cinyewa bane bar ganin a nayi miki layi a gidan ku dan kina irin wannan shigar to ina mai tabbatar miki duk cikin masu zuwą gun naki babu 24 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda yake zuwa da zummar aure sai dai da niyar wata bukata ta shi, kuma da bukatarsa tabiya ba zai kara ko kallon inda kike ba to talla ki kai shi kuma ya taya kika sallama to kin ga kuwa taya zai kai ki gidansa harki zama uwar ‘ya'yansa, ke ma kin san (Impossible) Jana ta dauki ɗan yalolon mayafinta daya dace da atamfar jikinta da akaiwa dinkin riga da siket sun kamata dan-dam ta dauko post dinta ita ma kalar kayanta. Ta ce, "Sai mu tafi Sayyada." Anty Meena ta ce, “Ko baki faɗa ba mutane zasu fada su ce ita din Sayyada ce ke ko kunyar jerowa da ita baki ji ba, ita ta yi shigarta ta kirki mutum duk na cinsa ba zai ga ko ina nata ba, amma ke dubeki dan Allah wallahi Jana ki yiwa kanki faɗa, ki yi koyi da Hadiya ki dinga komai na ki da nutsuwa." 25 e. 2 IZGILI JAMILA MUHAMMED Jana ta figi ledar da Anty Meena ta shigo musu da ita, turaren wuta ne da Humra da take siyar da su ta basu turaren wutar ta kaiwa Iya mahaifiyarsu da kuma Inna mahaifiyar Hadiya Humrar ta suce ta basu sannan ta mikawa Hadiya dari biyu ta ce su hau adaidaita sahu. Hadiya ta ce, "Wallahi ki barshi Anty muna da kudin Mota." Anty Menna ta dan zare mata ido ta ce, "Karбi mana ai na san kuna da kudin motar na baku.” Hadiya kasancewarta mai da'a kuma ba a ai musu tarbiyar jayayya dana gaba, yasa ta karɓa tai mata godiya ta rakota har soro. A kokafar suka ga Jana ta cuge tana ta faman kumbure-kumbure. Anty Meena ta ce, "Ku gaishesu." Hadiya ta ce, "Za su ji." 26 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta gangara inda Jana take suka jera zuwa titi Anty Meena yayar Jana ce uwa daya uba daya ita cc a biyu a gidansu tana aure a Yalwa bata taɓa haihuwa ba. Jana suna tsaye abakin titin,suna jiran adai-daita sahu kasancewar duk wanda ya taho zaka same shi da mutane saboda yamma ta yi tun daga nesa ya hangota ya ganeta ita ce zuciyarshi ta gaya masa ya tsura musu ido yau ma dai irin shigar da ya ganta da ita ce sai dai wannan ba hijabin Islamiyar bane shi wannan kalarsa maron ne kalar flat din takalminta ne kuma sanye take da Nikaf dinta babu abinda kake gani sai kafarta kasancewar Hijabin dogo ne sosai. Idonsa ya kai ga wadda take kusa da ita ya kalleta yaga irin shigar da ta yi gaskiya ya yaba da nutsuwarta da hankalinta yana. kallo sai tsaida abin hawa 27 IZGILI JAMILA MUHAMMED suke amma ba su samu ba ya wuce ta gabansu yana ci gaba da fadin kamun kanta to shi dai duk ganin da yake yi mata cikin nutsuwa yake ganinta bai ma taɓa ganin fuskarta bato me yasa ya ji wannan samarin suna fada mata wani suna wai kanti ya juya baya mai hakan ke nufi? Wata zuciyar ta ce, masa kawai dan sunga ba kalarsu bace shi yasa suke jin haushinta har suke Igaya mata wani suna haka ya dinga tunani harya isa gida. ** . Hadiya tana sharar tsakar gida ta ji sallamar babbar kawarta tata Jana. Jana kawar Hadiya ce tun suna yara sun yi mutukar shakuwa ta yadda babu wadda za tai kwana biyu batare da ta nemi 'yar uwarta ba duk da babu ta yanda za ai su hadu batare da sun kafsa ba anan dai na yi musu da maganar Malam bahaushe da 28 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya ce, sai hali yazo daya ake abota to waɗannan aminan junan su sam ba haka bane dan ko wace da inda ta dosa inda hakan halaiyace inda Jana ta kasance mai san gayu da kece raini tana da rawar kai mutuka ga saurin fushi amma bata da wuyar saukowa. Tana da kirki bata kuma da kyashi ko hassada ita in dai dan uwanta ya samu to ji take tamkar ita ta samu sannan bata da rufi duk abinda ya dameta kai tsaye zata gayawa babbar aminiyarta bban abinda yasa suke samun matsala da kawartata shine ita dai Jana Allah ya yo ta mai san saka kananun dinkuna ce kuma idan tasa ba zata sami mayafi mai yalwa ta rufe jikinta ba, sai dai irin na 'yammatan zamani ita tana jin bakin ciki ganin yadda kullum Hadiya take faman jibgawa jikinta dogayan hijab har da su 29 IZGILI JAMILA MUHAMMED nikaf, sai kace a zamanin jahiliya ga dai kyau dan asali kyau zalla amma bashi da amfani tunda kullum ana rufcwa masu so basu gani ba bare su yi sha'awa yayinda Hadiya tata kasance kasance. marasan magana sannan bata san raini ko wulakancin sam bata da saurin fushi amma kuma bata da wuyar saukowa tana da shagaɓa mutuka da sangarta in dai a gaban Abbunta ne da Innarta tana da tausayi ita abu kankani sai ya sata kuka shi yasa Jana take ce mata mai arhar hawaye, ita abu kaɗan sai ya sata kuka. Ta dago da sauri tana dariya Jana ta kalleta ta dauke kanta ta karasa gefen tabarman dake shinfide suna gaisawa da Inna Hadiya tana sharar tana dariya dan ta san lefinta ta san kuma shi yasa Jana ta zo tana karasa sharar ta wanke hannuwanta 30 IZGILI JAMILA MUHAMMED. ta karaso kusa da ita tana fadin "Kawata ya dai.?" Tana dauke kanta Hadiya ta guntse dariyar da ta cika mata ciki ta ce, "To ta so mu shiga ciki sai ingaya miki uzurina da abinda yasa ban aiko miki da wuri ba." Jana ta bita ɗakinsu ta zauna kan 'yar yalolowar katifar Hadiya wadda saboda sidewa ta dawo tamkar tabarma, ta kalleta ta ce, "Uhm Ina jinki faɗa min dalilin da yasa da kika san ba zaki je ba me yasa baki aiko min da wuri ba.?" Hadiya ta zauna kusa da ita ta ce, "Ai ya kawata ni ma ba haka na so ba na san Bilkisu Ibrahim ba zata ji dadi ba, babu daya daga cikin mu daya je." Jana ta harareta ta ce, "Waya ja? Idan bake ba da kika san ba za ki je waliman nan ba tunda wuri ba sai ki aikomin ba in sami abokin tafiya kawai 31 IZGILI JAMILA MUHAMMED sai dana shirya ina ta jiranki sannan zaki wani ce min Inna bata nan, shi yasa ni ma Faina ya ɓaci kawai nace to nima na fasa zuwa. " Hadiya ta ce, "Haba sister me yasa kika fasa ai Amiru ɗazu ya gayamin dana ce ya je ya gaya miki ki bani kayan walimar ya ce ke ma ba ki je ba. Jana tana faɗin ‘yar rainin hankali bayan sai da kika bari duk 'yan tafiyar sụn tafi sannan kika wani aikomin ai na ji haushinki sai kuma daga baya na ji daɗima da bamu je ba. Hadiya ta ce, "Saboda me? Yanda kika kwallafa ranki akan walimar nan. " Jana ta

Chapter 1 of 5