Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
Gombe da ma kauyikansu sai dai mu ce, Allah ya ji kansa, halinsa na gari ya bishi, mutuwar Alhaji Bawa da shekara Alhaji Mansir ya tattaro ya dawo Kanon dabo mai mata mai mota mai dala da gworon dutse. saboda harkokinsa sun fi yawa a can kano da Abuja, a inda ya kera gidansa a Zoo road suka tare sai dai duk karshen wata yake zuwa Gombe domin duba hajiyar, sai da ya kaɗa ya raya ya ce, Hajya ta dawo amma ta tubure ta ce, babu inda zata saboda mutanan alhaji marigayi saboda duk wani abu da ake yi da babu 100 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda aka daina 'yan'yan ta maza sun tsaya mata musamman Alhaji mansir dan shi ne ya dauko kyauta irin ta mahaifinsa, da son talakawa mararshi, dan gaskiya yafi kannensa najib da Isma’il taimako dan su da Hajjo tai musu zancen duk wata ga abinda zasu kawo cewa su kai kai a bari wanda Baffa ya yi ya yi, ya isa, Allah ya bada lada. Batai mamakin jin irin wannan maganar daga bakinsu ba dan ta sansu ta san halinsu suna kyamatar talaka sun ce su da talaka ko a hanya, shi yasa kwandalarsu ba zasu bayar ba, dama da mahaifinsu yake yi ba asan ransu bane, dan dai ba yanda zasu yi ne, kuma saboda ba kudinsu bane, ko da yake shi najib sai da ya taɓa gayawa Hajjo gaskiya ta gayawa Baffa ya daina kashe musu kudi haka. 101 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta kalle shi da alamar tambaya ta ce, "Wana irin kudinku yake kashewa aikuwa babu kun ya babu tsoon Allah ya ce, Dukiyar Baffan nasu ai ta suce saboda haka gaskiya Baffa ya daina raban kudi da abinci ai sangarta su ake yi, su dinga zaman banza, zuciyarsu ta ida mutuwa, tunda suna da mai basu abinci har ma da nace fane, dan kada ta Allah ta kasance gadonsu ya zaru babu auki." Hajjo sai ta saka salati tana salallami fadi take oh ni Rahine yau naga. abinda ya ishe ni najib Allah ya shiryeka to ni dai ba za aji wannan maganar a bakina ba, idan ka matsu kai ka same shi sai kai masa maganar, shi yasa koda suka ce su ficikarsu bazasu bayar ba bata damu ba, ta gayawa Alhaji mansir ya ce, Dama bata yi musu magana ba. 102 IZGILI JAMILA MUHAMMED Hajjo kin san dai kome ye kike bukata zan yi miki su yarane daman niya dace in yi ko meye Hajjo ta ce, "Duk da haka kai ma ai zaka so su taimaka maka tunda abinda ai da yawa, kuma kamar yanda kudi suke zuwar maka suma haka kawai dai su haka Allah ya yosu in dai batu ne nasu bayar to fa ba za a ji bakinsu ba, saboda Allah rayuwa kuwa zata yiwu. a haka kana da shi ba zaka taimaki dan uwanka marasa shi ba. Alhaji Mansir ya ce, "Hajjo ki daina ganin laifinsu suna fa da iyali ga yara da wanne za su ji." Hajjo ta ce, "Da yake kai baka da iyalin ko haka dai ya dinga bata hakuri ya ce, tunda ya ce, zai iya zai iya dinne tunda mahaifinsu ya rasu, shi ya dauki nauyin yin sadakar da aka sabayi, duk safiya ana dama koko da kosan sadaka 103 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma kokon da sukarinsa bajau, da rana kuma ana yin wake da shinkafa da mai mutum sai dai ya nemi ya ji, kuma ba sai almajirai ba ko waye in dai yake ko ya kai kwanansa, duk girmansa sai an take masa shi abinci, duk ranar juma;a ana can ja kalar girkin da safe ana yin kunun tsamiya da fanke, da rana kuma ana yin tuwon shinkafa da miyar taushe, kuma gaba daya Alhaji mansir ne yake komai hatta da 'yan aikin da suke wannan aiyukan shi yake biyansu, kwandala babu ta wani dan uwansa kuma duk karshen Iwata yake zuwa ya saurari talakawan da mahaifinsa yake taimaka musu, wasu bikin 'ya zai yi babu gaba ba baya. Wani matarsa ce ta haihu babu Ragon suna wau rusaune ya rutsa da su, da dai sauransu duk kuma wanda ya kawowa Alhaji Mansir matsalarsa to sha 104 IZGILI JAMILA MUHAMMED Allahu sai ya taimaka masa sai mutumin nan ya yi farin ciki ya saka masa albarka. Hisham ya yi Primary dinsa wata tsadaddiyar makaranta dake cikin birnin na Kano mai suna Attaufeek Iliman an tahafees yaro ranar da ya gama primary, to ranar aka masa bikin sauka to shi ma Hisham haka daga nan sai alhaji Mansir ya kai shi Germany gidan kanwar Hajiya Zalifan watan Nadiya da take aure a can suke zaune a can ita da mijinta sai dai basu haihu ba a can yai Secondry dinsa yai kuma jami'a. Hisham ya zaɓi ya gaji dadinsu watan dai yana san zama controctor aikuwa sai da ya zama Hisham tun yana Secondry dinsa ya fara Harka da 'yan mata kasancewar kyakkyawa gaskiya Allah yai masa halitta gaskiya Hisham ya gama haduwa Hundred percent to jinin .105 IZGILI JAMILA MUHAMMED larabawa fa, da kuma fulani ga kulawa dole a ga kyau dan usuli duk inda kake neman kyakyakyawa to kana samun Hisam sai a shafa fatiha, saboda kyau ne tsabarsa babu mide babu abinda yake kara masa kyau irin wadannan kyawawan idanuwansa masu firgita 'yan mata ko da yaushe zaka gan su a lumshe. Hisham dogone amma ba irin zankalkal din nan ba ne yana da dan jiki watan murjewajiki dan shi ba irin ramammun nan bane sanna kuma shi ba mai jiki ainun ba ne, fari ne tas irin farin larabawa kana ganin sa zaka san shi din balarabe ne ta yadda ga shin kansa yake akananɗe mai kuma azabar santsi da baki irin na larabawa. Yana da dogon hanci, bakinsa dan dai-dai mai fararan hakora tas, tamkar kankara, idanunsa a lumshe tamkar mai 106 IZGILI JAMILA MUHAMMED jin barci yana kassara dubun nan 'yan mata da wannan kallon na shi mai ratsa JINI DA JIJIYA. Hisham Mansir Kwangila ke nan miskili mai murdadɗan hali yana da tsare gira ba shi da fara'a tunda yake shi bai san so ba, bai taɓa yin shi ba kuma baya son yasan shi bare ya yi shi, duk 'yan matan dayake yi bai taɓa cewa yana san su ba sai dan shi suce suna son sa... Ya yi 'yan mata 'ya'yan manya wadanda ba zai iya kirga su ba shi din mane min mata ne na sosai amma ba ko wacce kuci ku bamu ba shi din sai kin kai kin doke kin haɗu koma ki na da abinda ya yi masa shi ne zai ce miki bukatarsa shi yasa matansu suke rububinsa suke kuma son sa. Hisham sai da yai shekara goma sha tara a duniya sannan ya samu kanwa mai 107 IZGILI JAMILA MUHAMMED a sarar sunan Hajjo kakarsu wato Rahina, ake kiranta da Ummita, Hisham ko da ya kammala karatunsa bai dawo Nigeria ba, wani kamfanin zane zane ne suka dauke shi aiki sai da Alhaji Mansir ya yi da gaske sannan ya dawo gida amma duk da aka yadawo da ɗabi'ar nasara duniya ya koyi yadda ake daga kwalba mata kuma yanda suke sonsa duk inda ya shiga in dai da mata sai sun so shi dan Allah yai masa farin jini in dai ya shiga guri sai an so shi to kuma daman an ta shi garin ida suka dauki zina tamkar ado, kuma akai dacen shi din mai farin jinin matanne da kansu suke yi masa tallan kansu, burinsu dai da fatansu ya yarda dasu batare da ko kwandalarshi ba, su abin alfaharinsu ne kamarsa hadaɗden saurayi ya kwasa sai dai alhaji Mansir yai masa jan ido kuma an kammala ginin 108 IZGILI JAMILA MUHAMMED kamfaninsa na Abuja shi yasa ya matsu ya dawo domin ya kula da shi shi kuma alhaji Mansir din ya kula da na nan Kano din, ya kuma gaya masa ya siya masa fili a nan cikin garin Abujan idan yana da zanen gidan da yake sha'awa to ya turo masa ta computer sai Ai masa kafin ya dawo aikuwa har an kammala masa hohoho dan da shi gaskiya gida ya tsaru tamkar wani shugaban kasa. Gidan ya gama haduwa bada dadewa ba ya diro Nigera kasarmu ta gado, ya yinda ya kwashe tsayin shekaru ba ya kasar dan tunda ya gama primary ya tafi sau biyu kawai ya zo shi yasa yaga kasar ta canja masa, tamkar ba dan kasar ba, dan duk komai ya canza masa, ‘yan uwa ansha murnar dawowarsa, Ummita kanwarsa ma sai murnar dawowar yayanta take. 109. IZGILI JAMILA MUHAMMED Bayan ya huta yai raban tsaraba kowa aka bashi sai da yai wata biyu yana hutawa sannan ya tattara ya koma Abuja daman dawowarsa da sati akai kasaitacciyar walimar dawowarsa, tare da murnar bude kamfanin. An sha shagali an kar kudi tunda ya tare Abujan ya dada ci gaba da harka da matansa giya tamkar ruwan roba ya maida ta. Dan idan kuka ganta jejjere cikin firji dinsa ka dauka lemo ne. Gwani ne a harka da mata da kuma wiwi, sai taba da ita ma ya kware gurin shanta, to daga su baya karawa da komai duk wani rashin tarbiya da ya koyo ya kuma zubar da wanda iyayansa su kai masa; to bai daina sallah ba, kuma yana. yinta a kan lokaci, duk yanda ya kai da sheke a yarsa to da zarar lokacin sallah ya yi to zai watsar da koma mai yake, sai ya 110 IZGILI JAMILA MUHAMMED sauke farali, Hisham yana da mutukar tsafta ga ya shi kuma da tsantsani na jaraba. Ba ko wanne abinci yake ci ba, sai kina da maşifar tsafta shi a duk gidansu idan ba Momi ce tai masa abinci ba ba iya ci, da ba yacin girkin 'yan aikin gidansu, dan haka ba kowane restaurant yake cin abincinsu ba, sai irin kasaitattun nan, wanda sai manyan garin na Abuja, suke zuwa to irin su yake iya cin nasu, koma sai ya bada tsaftar gurin da ma'aikatansu zaka sha mamaki, mutuka yadda ya dauki al'adun turawa, da ɗabi'unsu to sai kuma bai dauki cimarsu ba gaba daya ma ba zai iya cin irin abincinsu ba, dan tunda yake bai taɓa ɗanɗana irin abincin nasu ba, kuma ya ɗauki tsawan shekaru goma sha tara zuwa a shirin a turai amma bai taɓa gigin dandanar cimarsu ba, don in har ya ce, IZGILI JAMILA MUHAMMED zai dandana to fa babu shakka sai ya tanadi gadon a Asibiti, saboda yasan sai ya kwanta ciwo dan shi a ganinsa babu babban abin kazanta irin abincinsu, dan shi ko gani ya yi suna wani jagulan girkin to fa ranar yini zai yi zuciyarsa na ta shi, sai ya yi amai, zai ji dadi. Shi a rayuwarshi babu abincin da zai ci ciki lafiya baka lafiya irin abincin mu na Nigeria. Aiko dole Anty Nadiya take yin irinsu tun bata saba ba har ta koya dan shi da kansa yake yi, tana ganin har ita ma ta iya take yi musu ai fa sai ta ga gaskiyar Hisham abincin Nigeria yafi na kowacce kasa dadi, a ido, zaka ganshi da tsafta hade da ban sha'awa, baki ga shi da dan karan dadi ranar da Hisham yai musu dan haka hohoho! Zo ka ga wawa su gurin Al Mubrak mijin Nadiya shi ma Balarabe ne 112 IZGILI JAMILA MUHAMMED aiki ne ya kawoshi Germany amma haifaffen Misra ne, danwaken fulawa ya yi musu, da man gyada ziryan da yajin da yasha magi ya yanyanka dafaffen kwai a ciki ai ji su tamkar kunnansu zai tsinke saboda dadi duk wata Momi take aiko musu da ka yayyakin amfani irin na Nageria har fulawa take aiko musu da ita su kuka, daddawa, karkashi, kuɓewa bushashshiya, zogale, wake, gyaɗa, man gyada, dakakken yaji, manja, kayan kamshi, man shanu, bushahhen kifi, ogun, ayodi, da dai sauran kayayyakin girki irin na Nigeria. Aikuwa Hisham ya zage ya danɗasa musu girkin da wata macen ma ba za ta yi test ɗn na shi ba, komai cikin tsafta Tentable gare shi kullum ga kalar girkin` da zai yi ya iya wainar fulawa, wadda baya gajiya da cinta, wake da shinkafa, IZGILI JAMILA MUHAMMED jallof din shinkafa ko taliya alkubus ma ya iya, arayuwa tuwo ne kawai bai iya ba, shi ma ba wai towanne bai san yanda ake ba ya san yanda ake yi tuka tukenne bai iya ba, duk sanda zai musu tuwo sai dai ya nunawa Nadiya ta tuka. To bata iya ba har ya koya musu, ita da Mijinta. Wai shi ma yana san ya iya saboda watarana ko idan Nadiyan bata da lafiya aikuwa tunda kowa ya iya shi ke nan idan daga Hisham ne ya riga dawowa makaranta sai ya girka musu abinci, idan Nadiya ce, sai ta yi dan ita ma karatu take anan jami'a da Hisham din yake, amma ba departement dinsu da ya ba, idan kuma mijin tane ya riga ta dawowa to shi zai musu abincin. Haka yai rayuwarsa cikin jin dadi gidan Anty shi tamkar kaninsu haka suka dauke shi ba dan ba shi yasa yake yadda IZGILI JAMILA MUHAMMED ya ke so, a kuma lokacin da yake so mahaifinsa ya shiga tashin hankali ne tun randa ya kama kwalaben giya burjik a dakinsa lokacin da ya dawo tun daga sannan yake san ya yi aure ko ya rage wani abun dan aure ni'ima gare shi yana sa arage duk wani iya shegen da ake yi tun daga lokacin yake tuntuɓarsa da zancen amma shi Hisham din ya share maganar a ganin sa me zai sa ya yi wani aure idan banda takurawa kai da saka wa kai tention to shi gara ya yi rayuwarsa a haka duk da ya san hakan da yake yi ba dai-dai bane, ga tarin zunubin da yake ta jibgawa kansa Zina ai babban laifi ne ko da yaushe idan wannan tunanin ya faɗo masa sai ya shiga ta shin hankalin irin laifukan da yake aikatawa, ya yi ta tuba gurin Allah amma ya kasa hana zuciyarsa aikatawa, saboda shi din baya iya ' IZGILI JAMILA MUHAMMED daurewa ko ya ce ya daina da zarar wata daga cikin 'yan matan nasa ta zo to fa shi ke nan zai koma ruwa, saboda tsabar sansa da 'yan mata suke yi ba shi yake kiransu ba su suke zuwa har inda yake kuma sai ya ga mai musu wulakanci saboda shi din IZGILANCI halinshi ne, ko dan jinin sarauta yana yawo a jininsa ne, yasa yake da shariya, da tsare gida, duk yanda kuke da shi karya ne ka ga dariyarsa shi sam baya dariya sai dai murmushi, shi ma mai gani daga Momy dinsa sai Daddy dinsa sai fa idan ya yaba da ke. Farkon haduwarku ba zai ce kin masa ba, ko yai miki magana sai dai ya dan yi miki murmushi, to har ku rabu da shi ma, ba zaki kara ganin ya yi miki ba, shi kuma duk yanda kika kai da nacinki yawan lokacin da za ku yi ke da shi wata ɗaya ne, da ga nan kuma sai wata, saboda 424116 IZGILI JAMILA MUHAMMED yan matan su suke nuna masa kaunarsa su suke kamar su ne namijin shi kuma shi ne macen shi yasa yake ja musu aji yake yi musu yadda yaga dama saboda su suke binsa ba shi yake binsu ba. Tir da wannan zamanin da 'yan mata suke ganin cinye wace waye wace dan kin buɗa baki kin cewa saurayi kina san shi wannan ba ɗabi'ar kamun kai bane, wai mai yasa mata muke wulakanta darajar mu, muke banzartar da kimar mu mace fa daraja gareta shi yasa Hisham bai ɗauki mace wata tsiya ba, saboda ya cam fasu duk matan waka suke basu da kintsi, saboda bai taɓa haduwa da ta garin ta kirki ba, wadda duk kyansa duk kuɗinsa haka duk ajinsa kuma duk mukaminsa karya yake ta bishi sai dai shi ya bita ko da kuwa shi ne shugaban kasa, dan har yau har gobe akwai na gari na kirki a IZGILL JAMILA MUHAMMED cikin 'yan matan masu kuma kima da daraja, sannan kuma da yawa a duniya shi din ne bai taba dacan haduwa da ta kirkin ba yanzu watansa tara ke nan da dawowa Nigeria. Sanda ya dawo da sati biyu suka 'koma saban gidan da Alhaji Mansir din ya tamfatsa a sultan road a ciki ma a kai bude saban kasaitacciyar walimar kamfanin na Abuja da kuma murna dawowar ɗan lelan Alhaji wanda Alhajin ya sangarta shi ya taɓarashi, su ka kuma barshi yake yadda ya ga dama ba kuma tare da sun tsawatar masa ba. AN DAWO LABARI Hadiya ce sun kuye bakin murhu tana faman hura wuta taki ta kama kasan cewar icen ɗanye ne saboda yana yi na damina ta ɗago da idanuwanta da suka yi jajir saboda a tsabar hayaki tana amsawa 118 IZGILI JAMILA MUHAMMED yaron da ya shigo sallamar da ya yi, yaron ya ce, “Wai wani Awaje ya ce, na sallama da Malam Usman.?' Ta ce "Kace yana zuwa. Ta mike daga durkson da ta yi tana karkade jikin ta ta yi sallama kofar ɗakin. Innar ta su, in da baban nasu yake kishingide yana sauraren gidan radio kano suna gabatar da zaɓan yamma Inna kuma bata nan ta tafi dubiya, amma ta san tana hanya tunda yamma ta yi, duk da dai bata wani jima da tafiya ba, dan sai bayan sallar la'asar sannan ta tafi. Malam Usman yasa hannu ya rage radio yana amsa mata sallamar ta durkusata ce, "Abbu ana sallama da kai'a waje." Ya ce, "Wa ye.?" Ta ce, "Ni ma ban sani ba." Ya dauki hularsa dake ajiye a gefensa yana kokarin sawa ya ce, "To 119 IZGILI JAMILA MUHAMMED 'yar gidan Abbunta maza je ki ci gaba da aikinki." wata Ta saki wata dariya mai ban sha'awa ta tafi ta ci gaba da aiyukanta shi ma Abbun fitowa ya yi dan ya ga mai sallamar yana fitowa yaga tsadaddiyar mota ta dallare masa idanu, saboda kyau sabunta tai shurum a kofar gidan nasa, tana hutawarta daga gefe kuma wasu kasaitattun Alhazawan birni ne tsaye a jikinsu sanye da dakakkun danyin shaddodi, sai zabga daddadan kamshin turare suke irin nasu na manya, ya dan ja turjiya ya tsaya turus, yana tunanin ina mai sallamar yake dan shi ko kusa bai yi tunanin wadannan hamshakan mutanan sune masu sallamar ba dan ya san shi dai shehu Usman mai faci duk cikin mutanan daya sani yake kuma har 120 IZGILL JAMILA MUHAMMED kar dasu ba shi da irin wadannan balle har yai tunanin su ne suke sallamar... Sallamar ya ji an yi masa yai saurin dawowa daga tunanin da yake yi, ya amsa sallamar shi ma cikin sakin fuskar tamkar dai suma da suke ta sakar masa, murmushin. Shi dai shiru ya yi yana kallonsu daya ne ya farayin magana ya ce, "Mu ne muke sallama." Ya ce, “To madalla Alhaji Yakubu babban na hannu daman Alhaji Mansir dinne dai har yanzu yake maganar ya cc, "Daman Mun zo gurin ka ne da wata muhimmiyar magana wadda take bukatar zama dan ni din ba gwanin tsaiwa banc. Ya fadi hakan yana dariya, wadda ta bayyanar da hakorin farin gwal din da yake bakinsa. Malam Usman ya kalli rugujajjen kofar gidan nasa mai dauke da jarkasa 121 IZGILI JAMILA MUHAMMED tumumu irin jajur din nan ya kai dubansa gurgurarriyar kofar shiga gidan ta katako mai barazanar rusowa. Ya dan saci kallonsu dubi irin danyun shaddojin dake jikinsu yanzu haka zasu dansu a cikin jarkasar nan wata zuciyar ta ce, to ya za'a ayi ai sun kallo yadda gurin yake kuma a hakan suke san su zauna. Ya dubi Alhaji Yakubu ya ce, "To bara in kawo abin zama. " Suka ce babu damuwa ya juya da sauri çikin gidan ya same ni ina kwasar tuwon dare ya ce. "Hadiya maza shiga daki ki dauko sabuwar tabarmar ledar nan cikin girmamawa ta ce, "To" Ta dauko da sauri ya ce, "Yauwa ki zubo ruwan sha ki kawowa baki." Ta amsa cikin girmamawa ta saurin karasa kwashe tuwan ta dauko saɓanin 122 IZGILI JAMILA MUHAMMED kwanon sha sabo fil ta sake ɗauraye shi ta tuttulo ruwan tulun Innar mai dan karen sanyi ga shi ruwan dadi. Farin fenti jikin kwanon shan sun tai maka gurin fito da farin ruwan gami da tsaftar sa tamkar irin ruwan da suka saba amfani da shi, ta shiga ɗaki ta ɗauko zumbulelen Hijab dinta da nikaf ta saka ta ɗauki ruwan ta yi soro inda take jiyo maganarsu duk da dai ba sosai ake jiyo maganar ba ta yi sallama cikin siririyar murya ta durukusa har kasa ta gaishe su Alhaji Mansir da yake cike da fara'a gami da wani matsanancin farin ciki ganinta a zuciyarsa fadi yake tarbiya da dadi gami da biyayya da sanin girman na gaba sai gurin diyan talakawa dubi dai irin yadda zube gwiwa bibbiyu saɓanin 'ya'yan masu dà shi, wadda wata ma ko kallan arziki abokanan babban nata basu isheta. 123 IZGILI JAMILA MUHAMMED Masu tarbiyar cikinsu ne zasu gaishe su daga tsaye, ko kuma a ce, sannunku. Daddadar muryarta mai cike da nutsuwa ce ta katse masa zancen zucin da yake yi, ta ce, “Ga ruwa." Alhaji Yakubu ya suri kwanan da ta ajiye sanyin ruwan da ya ratsa kwannan ya ratsa tafin hannunsa yayi saurin bude murfin, ruwan garai-garai gwanin kyau ya sha sanyin ruwan ya kwaranya a tumbinsa yai hamdala Alhaji Mansir ma ya sha su kai godiya ga Allah. Alhaji Yakubu ya gyara murya ya fara da gabatar da kansa ya ce "Ni suna na Alhaji Yakubu Galadanci, ni haifaffen garin nanne a galadanci iyayena suke amman ni ina zauna ne a Alu Aɓenue sai kuma abokina kuma aminina shi kuma sunansa Alhaji Mansir kwangila haifaffin 124 IZGILI JAMILA MUHAMMED garin Gombe ne amma anan garin shi yake yana zauna ne a Sultan Road kuma shi ne wanda yai dalilin zuwannmu nan.” " Malam Usman ya ce, "TO madalla Allah dai yasa lafiya .?" Alhaji Yakubu ya kuma sakin dariya ya ce, "Lafiya kalau, alhaji Daman dai yaga 'ya wajenka ne ya yaba da hankalinta da nutsuwa gami da tarbiya irin ta gidan nan shi ne ya yiwa dansa kamu, in dai babu wanda akaiwa * alkawarito yaran gurinsa yana son ta. " Malam Usman ya ja shiru na lokaci mai tsaho sai can ya ce, "To Alhaji hakikanin gaskiya ban yi mata miji ba, kasancewar ban bata damar sauraran samari ba, saboda karatu, take duk da dai ta kusa gamawa dan saura wata uku ne kurum ya rage ta gama, to amma wani hanzari ba gudu ba, kamar na so na ji 125 IZGILI JAMILA MUHAMMED kace shi Alhajin ne yayaba da ita ba shi yaron bane, ya ganta, ya ga yana son ta ba. Alhaji Yakubu ya cc, “Haka nace to mu din mu na yi ne kamar yanda shari'ar ta tsara gurin neman aure kuma muna bin yadda addini ya tanadar cewar idan zaku aurar da 'yar ku, hakkin iyaye ne su nemawa ‘yarsu miji na gari haka ma mijin suna iya zaɓa masa mata ta gari shi yasa muka zo da karfinmu saboda tarbiya irin ta gidanka mu kai kwaɗayin hada zuri'a da kai." Malam Usman ya sauke ajiyar zuciya, Gaskiya ya gamsu da duk wani bayani da kuka yi kuma shi ma zai so hada zuri'a da su dan ya fahinci su din dattawan kwarai ne, kuma ya gane su din ba daya suke da sauran ,masu kudin wannan zamani ba, da karan gidansu yafi ye musu talaka sau dubu, basu talaka mutum ba, ba wai dan kuɗinsu ba sai dan kamala da mutuncin da suka nuna ko 126 IZGILI JAMILA MUHAMMED kusa ko alama bai ga wani wulakanci ko tsantsanin da suka nuna masa ba tun zuwansu lallai ku a cikin masu kudin su din daban suke ya cc, su dan ba shi lokaci zai tuntuɓi mahaifyar yarinya ko da wanda ita yarinya take so suka cc to babu damuwa kamar yaushe yake ganin zasu dawo dan su ji yadda ake ciki ya ce idan Allah ya yarda nan da kwan uku suna iya dawowa su kai masa godiya ya ce, Ai babu komai ya rako su har kofar gida gurin motarsu ya nayi musu fatan alkhairi da addu'ar sauka lafiya.- Suna karayin musabaha, Bintu ita da dan Auta Aliyu suka dawo daga Tahfiz, suka durkusa har kasa suna gaishe su, suka amsa cikin fara'a gami da jin dadin yadda aka karramasu. Alhaji Yakubu ya fito da kuɗi a aljihunsa har sun mike ya kira su, suka farasa gabansa sosai suka kuma durkosawa ya mifa musu sababbin ‘yan dubu dubun da 127 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya kirgo guda goma ya mika musu yaran tamkar ashim film suka wani zabura a tare gami da mikewa har suna hada baki gurin cewar A'a mun gude su kai hanyar shiga gida Alhaji Yakubu ya juyo da kallansa ga Malam Usman ya ce, "Haba Alhaji ya za kai min haka yanzu ba zaka sa baki su karɓa ba, ni fa na niya ba wai rokona su ka yi ba, cewa nake ka karanta babu mai mai da hannun kyauta sai shadani, hakan yana da kyau hana yaro amsar Abubuwa a hannun mutane. Amma fa idan bai san su ba in dai mutum ya san yaro ka ba shi abu bai karɓa ba, sai ka ji babu dadi duk da yake karбar ma ko da yaron ya san yanda ya ba shi to hakan ma koyan kwadayi ne, cewa nake a iya zaman da mu ka dan yi yanzu da kai ka yarda damu din masoyanka ne, tunda har muna son hada zuri'a da kai nan ba da dadewa ba, insha Allahu, ai ina ganin mun zama daya ko ba haka banc.?" 128 IZGILI JAMILA MUHAMMED Malan Usman ya cc, "Hakkun amman ina ganin Alhaji kudin nan sun yi yawa." Alhaji Yakubu ya ce "Ba wani yawa da su ka yi in dai ka dauke mu da zuciya daya, kuma 'yan uwa ka ɗaukcmu." Malam Usuman ya cc, "Wallahi da zuciya daya na dauke ku. " Alhaji Yakubu ya ce, "To In dai haka ne to ka sa su su karɓa tun da ni ma babansu ne. 99 Malam Usman ya yi murmushi kawai ya juya zuwa soran gidan inda yai kiransu ya dawo gurin su Alhajin yana karayi musu godiya su kuma suka ce babu komai sune da godiya. Bintu ita da Aliyu suka durkusa suka ce, "Abbu gamu ya nuna su Alhaji ya ce, "Alhaji ne yake kiranku.' Suka karasa gurinsu ya mika musu kudin ya ce, "Abbunku ya ce, ku karɓa.' " 129 IZGILI JAMILA MUHAMMED Suka juyo suna kallon Abbun nasu. Malam Usnam ya ce, "Ku yi musu godiya." Ai fa yara suka dinga zararo godiya sai da Alhaji Mansir ya ce, "ya isa ku je gida ku sayi Buskit.' " Suka ta shi cikin nutsuwa suka shige gida babu wata harguwa irinta sauran yara, komai cikin nutsuwa suke yinsa nan dai suka sake sallama sannan suka ja motar suka tafi, da alkawarin za su dawo nan da kwana ukun. ****** Da daddare bayan sun gama cin tuwon dare sun baje suna shan iska suna kuma hira Malam Usman yai gyaran murya ya ce, "Lafiya baki tambaye ni in da dan autanki ya samu kudi ba.?" Inna ta yi dariya ta ce, "Malam ke nan ai tunda Hadiya ta bani kudin ta ce su Binta ne suka cc ka yi baki shi ne bakin suka basu 130 JAMILA MUHAMMED na san za kai min bayani, idan ka mustu to gajen hakurin na me ye, da zan tambayeka." Malam Usman ya yi dariya ya cc, “Ai daman tsokanarki na yi ni da na san halinki na rashin bindiddigi da san jin kwakwaf ai gaba daya suka saki dariya har da Bintu da take kwance barci ya fara di banta. Hadiya ta ce, zuciyarta gaskiya ina san iyayena akwai su da barkwanci sai

Chapter 4 of 5