Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
jallabiyar da yake sallah da ita ya bude dirowar gadon ya dauko kudi kowacce ya bata ya ce, 67 IZGILI JAMILA MUHAMMED “Sai na neme ku kada wadda tai gigin zuwa idan ba na kirata ba, yana gama fadar haka ya ce, Ku fito suka fito sai ya bude kofar. Kudirat ta saki dariya ta ce, "Handsome kalle kafa babu pant ana ganinka a haka zaka je gurin Daddy." Cikin sauri ya kalli jikinsa ai kuwa ana ganin nasa kasan cewar rigar ruwan madara ce kuma tana da yauki mannewa mutum take da sauri ya fada dakin ya sako gajeran wando ya fito dai-dai nan ya sake jin karar wayar ya san mai kiran batare da ya dauki wayar ba ya bude kofar yana washe baki daddy ya ce, "Ai ni da badan maigadinka ya ce, kana nan ba kuma naga duk motocinka suna nan da cewa zan yi baka gidan ko kuma ba ka yi murnar gani na ba my son?" Hisham ya ce, "Na yi murna mana daddy.' 68 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daidai nan suka shigo cikin falon sosai Daddy ya kallu Kudurat da suke zaune a falon ya mai da kanshi ga Hisham din da yake tsaye da alamun tambaya a fuskarsa, Hisman ya ce, "Wadannan abokan aikinane wani aiki ne ya kawosu yanzu. Suka gaida daddy ya amsa musu fuska babu walwala su kai waje Hisman ya buɗe firij ya kawowa Daddy Ruwa da lemo yana kuma tambayar Mominsa. Daddy ya ce, "Tana lafiya.” Daddy ya gyara zama ya ce, “Wai ni shin Hisham sai yaushe za kai aure ne, ko yaushe akai maka magana daga kace wannan sai kace wan can kana ta faman zille-zille. Hisham ya ce, “Haba Daddy ni fa ba girma na yi ba, just 33 year ne fa ka ga da saura na. وو 69 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daddy ya ce, "Da sauranka fa tunda ba kai sittin ba,mana tunda shi ne dai-dai lokacin ka ko?" Hisham ya ɓata fuska tabbacin baya son fadan nan ya ce, "Please Daddy ka bar maganar nan daga zuwanka ko hutawa ba ka yi ba, me ake da aure, aure ai takura ne. " Daddy ya saki baki yana kallan dan nasa tun ba yau ba ya daɗe yanayin dana sanin tura ɗan nashi kasar mai jan kunne karatu, tun yana tatsitsinsa gaskiya ya cuci kansa wannan Abu yana damunsa ya rasa yadda zai yi bai isa yai masa faɗa akan duk abinda yake yi ba sai ya ce, shi dai ana san a takura masa, duk ya dauko dabi'unsu na lalata. Daddy da idanuwansa suka fara canja launi saboda ɓacin rai ya ce, "To wallahi bari in gaya maka in dai ba kai 70 IZGILI JAMILA MUHAMMED wani abu kan maganar aure ba daga nan zuwa karshen watan nan tuni zan yi wani abu a kai, kuma sai na baka mamaki.' " Yana gama fadar hakan ya mike dan yın Alwala dan ya ji masallacin kusa da gidan suna kiran sallah. Alhaji Mansir kwangila shi da Alhaji Umar mai akwai suna zaune a falon gidan Alhaji Umar din bayan gaishe-gaishe irin na abokanai, Alhaji mansir ya ce, "Gaskiya ina cikin damuwa.?' Alhaji Umar ya ce, "Ikon Allah Alhaji me ke damunka Alhaji Mansir ya furzar da huci mai zafi ya ce, "Akan yaran wajena Hisham ne, wallahi ina cikin ɓacin ran kaishi turai karatu banda karatu har da shedana da duk wata lalata ta turawa duk ya kwaso, to shi yasa nake IZGILI JAMILA MUHAMMED san in yi masa aure, tun lokacin dana kama shi da giya a firji dinsa nake cikin damuwa shi yasa nake san yi masa aure kasan aure abu ne mai girma kuma yana gyara mutum to gaba daya daya na rasa yarinyar da zan zaɓa masa mai hankalin wadda zata juri halinsa ta dinga tuna masa idan taga yana abunda bai dace ba, to na yi tunanin na yi tunanin na kasa zaɓar masa to kawai sai sai nana tattara nabarwa Allah lamarinsa ya zaɓa masa mafi alkhairi na kuma dukufa da addu'a sosai. Wani ikon Allah banyi sati da fara tsaiwar daran nan ba na fara mafarkin wata yarinya, to amma banga fuskarta ba, tana sanye da dogon hijabi har kasa ta juya bayanta da yaro a hannunta to tun daga lokacin ya zama duk lokacin da na kwanta sai na yi mafarki, to kwanaki da 72 IZGILI JAMILA MUHAMMED na zo nan muna magana sai naga wata yarinya zata wuce Islamiyar." Alhaji Umar ya ce, Zawuya ke nan.?" Alhaji Mansir ya ce, “Ita, ya ci gaba da cewa "Wato ranar da na ganta sai naga nutsuwarta da hankalinta nasan ta fito daga gidan tarbiya shi ne nake san in tambayeka ko ka san 'yar inace tana saka nikaf." Alhaji Umar ya dan yi nazari ya ce, "Gaskiya ban san ta ba, sai dai akwai wani yarona kama sanshi dan Audu, to zan sa shi ya binciko mana in da take da kuma 'yar gidan waye." " Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan suka ci gaba da hirarsu akan harkokinsu da kuma hirar duniya. Cikin wulakanci ya kalli mai gidan ya daka masa wata gigitacciyar tsawa ya IZGILI JAMILA MUHAMMED ce; "Saboda tsabar baka san aikinka ba ko kuma dan ka koshi zaka nuna halin naku na talakawa, daga kunci abinci sai ku ɓollo da salo na rashin mutunci. Baba Audu babu abinda yake in banda makyarkyata yana durkushe yana bawa ubangidan nashi hakuri tamkar zugashi yake, sai faman tujara yake yi masa da tozarci, kala-kala, tsohon zai baka tausayi mutuka saboda a kalla ba a kasara ba zai yi jika da shi, sai wulakanci yake yi masa, irin na zafin naman nan. Hisham ya ci gaba da yarfa ruwan rashin mutunci yace, "Saboda tsabar ka isa tun jiya abaka dakardu ka bani dan. tsabar raini kaki bani har sai da mutumin yayo min waya saboda ya ji shiru, sam baka da niyar bani, saboda ka fara farfaɗowa daga cutar talauci, data kama ka, yanzu kana jin aljihunka da nauyi shi 74 IZGILI JAMILA MUHAMMED ne kake ganin dai-dai kake da kowa tsiyar talaka ke nan, a ɗaukeshi ranga ranga a taimake shi daya fara koshi kai zai farayiwa rashin mutunci, shi yasa ni da talaka babu wani tausayi, ban ɗauki talaka a bakin komai ba, face, kaskantaccen bawa, wanda zai min bauta in biya shi, a duniya babu wata rana da talaka yake da ita, bashi kuma da wani amfani daya wuce mai kudi ya bautar dashi domin shi bawansa ne.' " Shi dai Baba Audu in ban da ban hakuri babu abinda yake yi sai da ya ji ya ɗan tsagaita sannan ya fara bayaninsa ya ce, "Wallahi yallaɓai sanda mutumin nan ya kawo takardun nan ka fita kuma baka sake dawowa ba zuwa kuma sanda ka shigo na manta sai yanzu na tuna, ina shirin kawo maka sai kuma ga ka, amma 75 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan Allah dan Annabi ka yi hakuri hakan ba zata sake-faruwa ba, in sha Allahu.' " Cikin Izgilanci gami da wulakanci ya karɓi takardun ya ce, "Kuma daga yau sai yau muddin haka ta kara faruwa to a bakin aikinka, sake kwatanta abinda ka yi, yana nufin ka koshi dai-dai kake da kowa. Dan haka yarage ruwanka, ka kiyaye, ko ka sake, aikatawa. Cikin takunsa na isa hade da kasaita ya bar wajen baba Audu ya dade tsugunne a inda ya barshi saboda tunda yake ba a taɓayi masa wulakanci da kaskanci irin na yau ba, sai kawai ya ji wani irin zazzafan hawaye suna zubo masa ace kamar wannan da yayi jika dashi a ce dan Allah ya yo shi talaka yana aikin a karkashinsa kan ya yi masa laifin da bai taka kara ya karya ba, zai zage 76 IZGILI JAMILA MUHAMMED haka, yana gaya masa irin wadannan maganganun. Ya mike daga durkuson da ya yi yana sharar kwalla cikin mutuwar jiki ya koma kan benci da yake kai dai-dai nan yaji sallama akansa ya dago da sauri yana amsawa Malam Saleh ne direban kamfanin ne ya zauna kusa dashi yana bashi baki ya ce, "Baba ka yi hakuri da abinda yallaɓai ya yi maka tunda Allah ya haɗamu zama dashi babu yadda zamu yi sai dai hakuri shi fa a duk duniya babu wulakantacce a gurinsa kamar talaka, babu wanda yake kyama yake tsangwama hade da kyara irin talaka, gani yake takalmin kafarshi yafi talaka, daraja, a gurinsa ka gan ni nan Baba yallaɓai ba jin kunyar na yi sa'an mahaifinsa baya iya cire hannu ya wanke min fuska da mari. T By lay mida on ideol 77 : IZGILI JAMILA MUHAMMED Baba Audu ya ce, "Me yai zafi malam Saleh?" Malam Saleh ya ce, "Ranar kaddara ce ta hau kaina ya aike ni ne to akan hanyata ne karfan nasara da bashi da tabbas sai kawai mota ta tsaya cak na yi na yi taki ta shi na rasa inda zansa raina dan yaja kunne na in yi sauri mutumin sauri yake zai bar kasar ne, gaba ɗaya hankalina ya gama ta shi kuskuran da na yi na rashin kiransa in gaya masa tun a lokacin kawai sai na fita ina ta 'yan dabaruna ga mi da ‘yan jogane-jogane na, na ma buɗe in jin motar ina ta jagwalgwalawata na bar wayata a cikin mota a she, shi mutumin da ya aike ni gurinsa yana tai masa waya ya ce, ban fa zo ba shi kuma zai yi missin din jirgin shi dan haka shi ya tafi, sai kuma wani lokacin, shi ne shima yallaɓai ya keta 78 IZGILI JAMILA MUHAMMED kiran wayata ina ni ban sani ba, danni ina waje ita wayar tana mota dan haka banji kiran da yake tayimin ba. Sai da akalla na yi kusan awa biyu da wasu 'yan mintoci sannan cikin ikon Allah sai ga shi ta tashi ai cikin sauri na rufeta saboda sai da ya gargade ni da lallai lallai in tabbatar duk yanda zan yi nan da minti arba'in in kasance a gurin, to gashi na kusanyin awa uku aikuwa wanda na je domin sa yama daɗe da tafiya cikin sanyi jiki naja motar na dawo na riga na sani nashi ga wani hali, yau sai Allah aikuwa tunda nai horn aka bude min na ganshi yana ta zirga-zirga tamkar mai nakuda na sanni kuma sai Allah, aikuwa ina tsayawa na fito na durkusa kafin ince wani abu sai jin wani shahararren mari na yi akan kuncina ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, 79 IZGILI JAMILA MUHAMMED ashe takardun wata kwangila ce zan karɓo masa da yake shirin shakar makudan kudade bana wasa ba, shi ke nan in ba wani ikon Allah ba ya rasa su. A ranar na dandani bakin ciki bana wasa ba wallahi da ina da yadda zan yi da tun a lokacin zan baar aikin nan, to bani da wata hanyar neman kudi, ga kuma iyali, dan ba karamar wahala na sha ba kafin Allah ya datar dani, na samu wannan aikin dan haka dan Allah Baba ka yi hakuri kuma ka dinga kiyayewa abinda zai ja ya ci mutuncinka, tun da shi baya ganin mutunci da kima hade da darajar talaka ba. Baba ya ce, "Kada ka damu insha Allahu haka ba zata sake kasancewa ba, zan kiyaye, tunda abin babu mutunci sai kai ka alkinta girmanka dan kada a sake ci maka mutunci.' 95 80 IZGILI JAMILA MUHAMMED Malam Sale ya ce, "Wannan gaskiya ne dole ne ka dinga kiyaye abinda zai sa a wulakanta ka." ****** Dan audu ne yake ta faman korawa Alhaji Umar mai da akwai tare da abokin nasa labari. Fuskar alhaji Mansir ta cika da annuri ya godewa Allah tunda ya taimaka aka samu gidan dashi har ya shiga damuwa da yasa yaji shiru bai sake ganinta ba, kuma ya ji dadin yadda Dan Audu ya bincika ya gama cika shi haka nan Allah yasa ka masa kaunarta tun ganin daya ke ta mafarki yana yawan ganinsa yana zaune a wani dokar daji ya nata kuka shi kaɗai sai ya ganta ta zo tana bashi hakuri tana lallashinsa duk da baya ganin fuskarta wani sa in kuma sai ya ganshi yana cikin fain ciki yana ta yin mrmushin amma ita tana kuka shiya sa ta 81 IZGILI JAMILA MUHAMMED tsananta da addu'a ya kuma sa'a taya shi saukar karatu duk juma'a akan dai Allah ya tabbatar da Alkhairi idan ita ce, mafi alkhairi ya kuma kawo sauki ciki lamarin ya kade fitina dake cikin al'amarin. Dan Audu ganin irin tarin fara'ar dake fuskar alhajin yasa ya kara kaimi yana kara koro wasu kuskuren zancen duk dai akokarinsa na ganin Alhaji yaga kokarinsa aikinnasa. hade da kwazansa akan Aikuwa kwalliya ta biya kudin sabulu dan kuwa Alhaji ya yi masa kyauta ta mu samman ya yinda Alhaji ya ce, tukukaicin ka ka gobe ka jira zai a kawo maka mashin shi ne tukuicin binciko min gidansu, da ka yi ya kuma dantso kudin da bai tsaya kirgawa ba ya ce, "Wannan kuma kasha ruwa ka ji, ladan kyakkyawan labarin. 82 IZGILI JAMILA MUHAMMED Dan audu tamkar zai shiɗe saboda murna godiya yake gami da jero dogayan addu'o'in tamkar wani saban maroki, yana karkawa yayi durkoso a gabansa yana faman jinjina masa hannu tamkar yanda akewa sarakai. Alhaji Mansir ya ce, "To dan Audu sai gobe ke nan. " Ya ce, "To ya alhaj." Alhaji ya fita yana kwararowa ‘ya'yan har jikoki dama tattaɓa kunnan alhaji kasan zuciyarsa yana ta kakkabin halin kwarai irin na wannan alhajin shi sam ba matsolo bane tamkar uban gidan nasa, da bai ajiye komai ba sai shegiyar rowa ta bala'i duk yanda kake da shi babbar kyautarsa ita ce, ya bawa mutum gudar dubu ɗaya, to lallai wata dakwalar budurwa ko bazawara ya kawo masa labarinta to kuwa zai samu gudar dubu ko 83 1 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma yinin ya yi yana wahalta masa, to idan ba daya daga cikin wannan ba ne to tsakaninsa da kai dari biyu ne sai kuwa idan yasan kanai masa wata ranar ne. Zai iya baka dari biyar shi ba abin kunya bane ka zo neman taimako gurinsa amatsayinka na yaransa ko kuma dan uwansa ya tattakura ya fito da naira hamsin ya ce, a sai wa yara garin rogo (kwaki) Duk unguwar Koki babu wanda bai sanshi ba, koda karamin yaro ne, ka tambaye shi gidan Alhaji Umar mai akwai to zai nuna maka sai fa in mai shan nono ne. Kowa yasanshi saboda tsabar son kudinsa da matsolancinsa uwa uba kin talaka ya ce, talaka ba shi da wani alfanu a gurin mai akwai. (Wato mai kudi) face, hidim ta masa shi kuma ya biya shi shi ne IZGILI JAMILA MUHAMMED kawai amfanin talaka a gurin mai akwai, alhaji Umar mai akwai ya yi mutukar tsanar talaka gani yake tamkar shi mutumin shi ya ɗorawa kansa talauci ba Allah ba, Alhaji Umar mai akwai shaharar ran mai auri saki ne gaba ɗaya kudinsa suna tafiya ne aa gurin aure aurensa mutane da dama sun ce auran dandano yake ga shi kuma baya san 'ya'yan abin Allah sai ya yo shi daga cikin masu rabon samun 'ya'ya, ko ya ya taɓa mace, sai ta samu rabo da shi kuma abinda yake ba kanta masa ke nan. Shi fa gani yake a duk duniya babu babbar matsalar irin zama da mace ɗaya yasha yiwa abokansa fada idan yana jin suna fadin matarsu daya ta ishe su ya kance ba kuda hankali ba kusan ciwon kanku ba, in banda rashin sanin me duniya take ciki, ya za ka zauna da mace, 85 IZGILI JAMILA MUHAMMED daya sai kace jaraba aini ko mata huɗu ba zan iya zubewa ba in yi shekara dasu batare da na yi can ji ba, ai gara adinga yi ana sabuntawa, aikuwa Alhaji Umar mai akwai ya auri mata kusan ashirin da uku, a kun dade da shi kina iya masa so sai shi ne zai barki ki yi shekara, to daga nan zai ɗaga miki jan kati idan ciki ne dake zai ce ya bar miki abinda yake cikinki duniya da lahira kada ki kuskura ki doso shi da wata matsala ta dan zai kuma yi miki ba, razanar ranku daga ke har yaran in dai kika kuskura kika danganta shi da wata matsala ta yaran zai kuma gaya miki zai fara rufawa yaran asiri, dan kada ai masa gorin ko yaran shege ne zai kuma gaya miki yana nan a amaṭsayinsa na ubansa, sai dai fa baya so idan ke kina so ya bar miki shi ke ka ɗai idan kema ba kya so to ga gidan marayu nan kina iya IZGILI JAMILA MUHAMMED sadashi da can, idan kuwa ke din irin barebarin nance, to uku ya yi yawa zai ce waje road shi din bai dauki mace a bakin komai ba face, ruwan kashe gobara, shi yasa baya daukan raini, ko wulakanci daga gurin kowa ce irin mace ba, da zaki kawo masa shakiyancin banza zai gaya miki ke din ba wata tsiya bace, agurinsa, dan idan ya so ana fita da kayanki ana shigo da na wata dan cewarsa mata sun yi yawa, tamkar ledar pure water ne, ga sunan burjik, duk inda ka zaga birni da kauye, dan haka shi a gurinsa, canja mace a gurinsa tamkar canja rigar jikinsa ne, duk sanda ya bukaci yasha iska zai canza ki da wadda ya ke so, shi yasa” yake mutukar ganin bakin abokin nasa, ganin tun wani shuɗadɗen zamani yake fama da mata daya Aisha, wallahi ba zai iya ba, sai wani ciwon ya shige shi, saboda 87 7 IZGILI JAMILA MUHAMMED bakin ciki da takaicin kaɗaici,, kullum babu wani canji sai kace masifa. Alhaji Umar ya karkatar da kai, yana kallon Abokin nasa ya ce, "Alhaji Wai duk murnar wannan maganar ne, yasa kake wannan rawar jikin hade da wannan batun kudi, tamkar wani wanda bai san ciwon su ba, akan wata can diyan talaka, irin wannan kyautar ko ka manta abinda dan Audu ya fada ne, ubanta ba kowa bane, face, talaka, a cikin talakawan ma na karshe a gun talauci ko baka ji sosai bane cewa ya yi ubanta fa faci yake yi, aini cewa nake daga jin baya nin Dan Audu ko duban mai rin kamaninta ba zaka sake yi ba, a matsayin Hisham na dan mai kudi wayayye, kyakkyawa me zai da wata Diyan talaka duk ‘ya'yan manyan masu sukuni karasa wadda zata zama sirikarka, matar danka, sai wata IZGILI JAMILA MUHAMMED ‘yar mai faci, kai wannan abu da bakin ciki yake, ina garin gami mai kuɗi da talaka, da har za kai sha'awar hada zuri'arka da ta shi.' " Alhaji Mansir Kwangila ya ce, "Wai ni shin Alhaji Umar mai ka ɗauki talaka ne, kaskantantacce, wulakantacce, kuma mara 'yanci, wanda duk sanda mai akwai (Mai kudi) ya mula yasha iska zai ciwa zarafi, ciwa zarafi, ya tozarta shi dan kawai Allah ya yishi mai shi, shi kuma ya yo shi mara shi, to ba haka bane, talaka mutum ne, tamkar kai, kuma ba'a bin wulakantawa bane saboda dinbin daraja da martabar da Allah yai wa bayinsa ‘yan adam Allah da kansa yake faɗa a cikin alkur'aninsa mai tsarki WALAKADI KARRAMNA BANI ADAM!!! Hakika ubangiji ya daraja ya girmama ɗan adam sai kai dan kawai Allah ya huwace maka 89% IZGILI JAMILA MUHAMMED za ka wulakanta mutum talaka, waya sani ma ko mutumin da kake wulakantawar ya fika a gurin Allah dan haka wallahi wallahi banga dalilin da zan kyamace talaka ba, wai dan kawai ni me shi ne, shi kuma mara shi, to haka Allah. ya nufin ya ganshi, kuma ba zan taɓa kin saba, wai dan yana faci, faci ai sana'ace, a gurin kane da ka raina shi har kake kiransa da al'amarin duniya ba yadda ka zata bane. Dan kana ganin kana da kudi to dare daya idan Allah yai nufin nuna ikonsa da buwayarsa. sai ya mai da shi kai da kake kiran koma ya fika sunan kaskantacce kuma kaskantattace matsayinka kake kiran kai kuma kadawo kamarsa, ko da yake ba za kai jarumtakar da ya yi ba, tunda ance ya daɗe a nan anguwar amma baka san shi ba, kaga hakan yana nufin ya iya da talaucinsa, tunda bai taba takowa kofar IZGILI JAMILA MUHAMMED gidanka da sunan maulaba, ka ga hakan yana nuni da cewar shi din mai jajircewane, da kuma tsayawa iya matsayin da Allah ya ajiye shi, kuma bai yi bakin ciki da yadda Allah ya yoshi marashi ba, bare ya dinga binbinin a gurin masu akwai ba suna wulakanta shi, kafin su dan watsa masa ‘yartsaba su nai masa dagawa, suna hura hanci ka ga kuwa akwai tarbiya a irin wannan gidan, sakamako 'ya'yanmu da muke barinsu babu tarbiya dan haka in dai ni Mansir ni ne mahaifin Hisham to fa bashi da wata matar aure idan ba 'yar gidan mai faci ba. Alhaji Umar ya tsurawa abokin nashi ido an ya kuwa kansa kalau, kai anya kuwa ko da yake daman yasan halinsa in dai akan talaka ne, yo mutumin da zai zauna gurin mai gadi suna hira, idan ka ganshi da ma aikatan gidansa 91 IZGILI JAMILA MUHAMMED yana kwasar dariya tamkar ba mai gidansu ba sai ka ga har wani share musu bakin yake tamkar ba mai kuɗi ba, shi yaga zai iya, shi yasa fa ko dariya baya iya yi a gidansa, dan kar wata ta yi gigin raina shi, in kaga dariyarsa, to yana majalisar su ta masu akwai ne." ****** " Shin wanene alhaji Mansir kwangila Alhaji Mansir Asalinsa dan garin Gombe ne mahaifinsa mai suna Alhaji Bawa, shahararren mai arziki ne sannane a cikin garin na Gombe, kai bama nan kadai ba, har da sauran garuruwan da ke cikin Nigeria ya shahara sosai dan kasuwa ne babu irin kasuwanci da ba ya taɓawa, ya kan sari Auduga ya sarrafa tata a kamfaninsa yana fita da ita kasashen duniya, idan ya ta shi dawowa shi kuma sai ya saro shinkafa da wasu kayayyakin 92 IZGILI JAMILA MUHAMMED da muke bukata buka, sannan yana da kamfanin Tumaturin gwangwani sannan yana da wani kamfani amma hadin gwiwa ne, a jafan da suke kera takalma masu shegen kyau, matar Alhaji Bawa, daya mai suna Rahina, ana kiranta da Hajjo Allah ya albarkace su da ‘ya'ya bakwai uku maza hudu. Mata ta farko mace ce mai suna Binta da ake kiranta Batulu, sai na biyu mai suna Mansir, daga mansir sai Barira sannan Hindu, sai najib, sai Safiya, da kuma dan autansu, Isma'il gaba dayansu, sun ta so cikin kulawa hade da tarbiya irinta addinin musulunci sam Alhaji Bawa shi da Hajjo basu saki yaran sun sangartasu ba, wai dan kasancewar mahaifinsu, wani ne, sun basu tarbiya ta gari dan gaba ɗayansu, sai da kowa ya sauke sun yi karatunsu na boko amma 93 IZGILI JAMILA MUHAMMED matan iyakar su secondry ake yi musu aure Inna Batulu anan Gombe take aure bata taɓa haihuwa ba. . Safiya Bauci take da yaranta Hindu Abuja ita ma dana ta yaran Barira ma anan Gomben take dan ita basu da nisa da gidan iyayan nasu maza ne ya ce, su yi karatu, duk anan gida Nigeria dan bai yarda ya tura dansa wata uwa duniya da sunan karatu ba, kuma garin da suka daurewa sheɗana da duk wata lalata kugu wanne karatun waɗannan makiya Allah zasu koyawa yaran da suke son musulmi ne su da a duk duniya basu da abokin gabar da ya wuce, musulmi, to wanne karatu zasu koya masa ban da su wayar masa kai, ya san ilimin lalata ni wallahi wannan abin yana damu na rashin sanin. ciwon kanmu, Nigeria wani bature ko ka taɓa ganin ya kawo dansa Nigeria ya ce, 94 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya yi karatu, sai mu da bama kishin kasar mu zamu ringa jidar ‘ya'yanmu tamkar gyada muna kaiwa makiyanmu masu burin ganin sun karmu sun rusa mu, su zamu bawa yaranmu. Ai wannan damar suke samu su koyawa yaranmu duk wata sheɗana, sai sun gama lalata musu tarbiya sannnan zasu turo mana su dan su zame mana annoba, su buwaye mu, dan haka Alhaji Bawa yana daya daga cikin mutane masu kyamatar tura yaransu karatu waje, gaba dayansu mazan sun yi karatun su ne a nan gida Nigeria. Alhaji Mansir ya yi karatun sane a Jima'ar A.B'U A.B'U Zariya inda ya yi karatunsa akan kasuwanci wato Business. Mansir ya dade bai yi aure ba, dan har sai da dan Auta Isma'il ya fara haɓaka Alhaji Mansir ya haɗu da Zalifa ne a Misra 95 : IZGILL JAMILA MUHAMMED lokacin ya ji kan wasu harkoki da suka kai shi Zalifa balarabiya ce, gaba da baya mahaifinta shi ne Wazirin Sarkin na Misra. Mansir ya haɗu da Zalifa ne ta sanadiyar 'ya'yanta wanda Allah ya haɗa su anan garin Kamfanin Babanta ya je, domin gogewa da sanin makamar aiki, domin ya fada har kar Kwangila to wata rana ne shi ya yanta Alhaji bashir ya gaiyace, shi cin abinci gidansa to sai Akai sa'a Zalifan ta je gidan yayan nata ita da kanwarta Nadiya, tun daga sannan soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu ansha fama kafin kasancewarsu matsayin ma'aurata, saboda iyayanta basa son tai musu nisa dagewarta ce, tasa iyayen suka hakura suka aura mata wanda take so batare da ɓata lokaci ba aka sha biki amarya ta tare a Nigeriya a 96 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma a garin ‘iyayan mijinta watan Gombe da farko iyayansa da yan uwansa duk suna son ta amma daga baya duk sai suka canja canja mata su ka bi suka tsangwameta ta kuma rasa dalili sai daga baya ta gane kan rashin haihuwar da bata yi bane, a zuciyarta tai mamaki shekara uku ne kawai da auran su shi ne har ake gwada mata tsana irin wannan ta shiga tsananin damuwa ta yadda dangin miji suke tsangwamarta suka mai da ita mujiya a cikinsu, duk ta bi ta rame, sai hanci da manyan idanuwanta da suka karayin manya idanuwanta da suka karayin waje, gaskiya Zalifa kyakkyawa ce dan ko cikin larabawan ma ita din mai kyau ce, amma duk irin abinda suke mata bata taɓa gayawa mijinta ba sai dai ko yaushe ya nai mata korafin ramar da take yi, ta yi yawa, to dole ne ta rame babu 97 IZGILI JAMILA MUHAMMED 'yan uwa akusa dangin mijin da take san su zama 'yan uwanta sun tsaneta basa son ta idan ta je inda suke suna kyararta ai dole ta shiga wani yanayi to abin Allah shekararsu biyar da aure Allah ya bawa zalifa ciki wai murna a gurin Mansir da Zalifa ba'a magana har ma da dangin nasa da suke kinta sai duk suka saki aka shiga tarairayarta, shi Alhaji mansir Bawa ya yi mutukar murna da Allah ya nufeshi da ganin jika, daga Mansir da yake Mansir yaro ne mai hankali da biyayya ga taimakon marasa karfi. Akwana a tashi har Allah ya sauki Zalifa lafiya ta haifi danta namiji wowowo fadin kyau ɓata baki ne vare. daka ganshi kasan jinin larabawa ne, saboda tsantsar kyaunsa duk wanda ya zo barka sai ya tafi da zancen yaron nan, Hmm! Zo ka ga bakin Alhaji Mansir yaki ng IZGILI JAMILA MUHAMMED rufawa sai Hidima yake ya kawo wannan ya kawo wancan dangin Zalifa ma ba a barsu a baya ba, ana igobe suna suma suka diro nigeria dauke da kwaryakwaryar kayan arziki dan danginta sun zo da dama, dan jirgi sukutum kakan yaro mahaifin Zalifa watan Wazirin Sarki Misra ya dira duk mai bukatar zuwa Nigeria. To fa ga jirgi nan a kai ka a dawo da kai, haka akai taron suna lafiya a ka gama lafiya Jariri ya ci suna Hisham. Hisham ya ta shi yaro mai-nutsuwa gami da hankali amma fa miskili ne na gasken gaske shekararsa biyu a duniya Allah ya yiwa kakansa Alhaji Bawa rasuwa, rasuwar da ta girgiza duk wani mutum daya kwana ya ta shi a cikin garin na Gombe jama'a sun ji mutuwar mutum na mutane irin Alhaji Bawa, mai kirki 99 IZGILI JAMILA MUHAMMED mai taimakon bayin Allah mai hidima a gurin jadda kalmar Allah. Ayyukan da yake gami da taimakon da yake sai dai Allah ya biya shi Islamiyyoyi da masallatai fanfuna burtsatse babu wanda yasan adadin da ya yi a cikin birnin na

Chapter 3 of 5