Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌸🌹kishyar uwa 🌹🌸 (True life story). 🍁🌸Daga alk'alamin nussad🌸 MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION πŸŒ™πŸŒ™πŸŒŸβœοΈ https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ πŸŒŸπŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒŸ π‘Šπ‘’ π‘Žπ‘Ÿπ‘’ 𝑑𝒉𝑒 π‘šπ‘œπ‘œπ‘›π‘™π‘–π‘”π’‰π‘‘ π‘€π‘Ÿπ‘–π‘‘π‘’π‘Ÿπ‘  𝑀𝑒 π‘π‘Žπ‘› π‘ π’‰π‘Žπ‘˜π‘’ π‘œπ‘“π‘“ π‘’π‘£π‘’π‘Ÿπ‘¦π‘‘π’‰π‘–π‘›π‘” π‘Žπ‘  𝑀𝑒 π‘€π‘Ÿπ‘–π‘‘π‘’; π‘œπ‘’π‘Ÿ π‘ π‘œπ‘Ÿπ‘Ÿπ‘œπ‘€π‘  π‘‘π‘–π‘ π‘Žπ‘π‘π‘’π‘Žπ‘Ÿ, π‘œπ‘’π‘Ÿ π‘π‘œπ‘’π‘Ÿπ‘Žπ‘”π‘’ 𝑖𝑠 π‘Ÿπ‘’π‘π‘œπ‘Ÿπ‘›. π‘Šπ‘’ π‘€π‘Ÿπ‘–π‘‘π‘’ π‘‘π‘œ π‘‘π‘–π‘ π‘π‘œπ‘£π‘’π‘Ÿ π‘€π’‰π‘Žπ‘‘ 𝑀𝑒 π‘˜π‘›π‘œπ‘€.π‘Šπ‘’ π‘Žπ‘Ÿπ‘’ π‘Žπ‘™π‘™ π‘Žπ‘π‘π‘Ÿπ‘’π‘›π‘‘π‘–π‘π‘’π‘  𝑖𝑛 π‘Ž π‘π‘Ÿπ‘Žπ‘“π‘‘ π‘€π’‰π‘’π‘Ÿπ‘’ π‘›π‘œ π‘œπ‘›π‘’ π‘’π‘£π‘’π‘Ÿ π‘π‘’π‘π‘œπ‘šπ‘’π‘  π‘Ž π‘šπ‘Žπ‘ π‘‘π‘’π‘Ÿ.. π‘‚π‘’π‘Ÿ π‘Žπ‘‘π‘£π‘–π‘π‘’ π‘‘π‘œ 𝑑𝒉𝑒 π‘¦π‘œπ‘’π‘›π‘”π‘ π‘‘π‘Žπ‘Ÿπ‘  𝑖𝑠 π‘Œπ‘œπ‘’ π‘ π’‰π‘œπ‘’π‘™π‘‘ π‘€π‘Ÿπ‘–π‘‘π‘’ π‘π‘’π‘π‘Žπ‘’π‘ π‘’ π‘¦π‘œπ‘’ π‘™π‘œπ‘£π‘’ 𝑑𝒉𝑒 π‘ π’‰π‘Žπ‘π‘’ π‘œπ‘“ π‘ π‘‘π‘œπ‘Ÿπ‘–π‘’π‘  π‘Žπ‘›π‘‘ 𝑠𝑒𝑛𝑑𝑒𝑛𝑐𝑒𝑠 π‘Žπ‘›π‘‘ 𝑑𝒉𝑒 π‘π‘Ÿπ‘’π‘Žπ‘‘π‘–π‘œπ‘› π‘œπ‘“ π‘‘π‘–π‘“π‘“π‘’π‘Ÿπ‘’π‘›π‘‘ π‘€π‘œπ‘Ÿπ‘‘π‘  π‘œπ‘› π‘Ž π‘π‘Žπ‘”π‘’. π‘Šπ‘Ÿπ‘–π‘‘π‘–π‘›π‘” π‘π‘œπ‘šπ‘’π‘  π‘“π‘Ÿπ‘œπ‘š π‘Ÿπ‘’π‘Žπ‘‘π‘–π‘›π‘”, π‘Žπ‘›π‘‘ π‘Ÿπ‘’π‘Žπ‘‘π‘–π‘›π‘” 𝑖𝑠 𝑑𝒉𝑒 𝑓𝑖𝑛𝑒𝑠𝑑 π‘‘π‘’π‘Žπ‘π’‰π‘’π‘Ÿ π‘œπ‘“ π’‰π‘œπ‘€ π‘‘π‘œ π‘€π‘Ÿπ‘–π‘‘π‘’. π‘†π‘œ 𝐿𝑒𝑑 𝑑𝒉𝑒 π‘€π‘œπ‘Ÿπ‘™π‘‘ π‘π‘’π‘Ÿπ‘› π‘‘π’‰π‘Ÿπ‘œπ‘’π‘”π’‰ π‘¦π‘œπ‘’. π‘‡π’‰π‘Ÿπ‘œπ‘€ 𝑑𝒉𝑒 π‘π‘Ÿπ‘–π‘ π‘š 𝑙𝑖𝑔𝒉𝑑, π‘‘π’‰π‘Ÿπ‘œπ‘’π‘”π’‰ π‘Ž 𝑝𝑒𝑛, π‘œπ‘› π‘Ž π‘π‘Žπ‘π‘’π‘Ÿ . YA ALLAH, YA RAHMAN, YA KAREEM, YA ZULJALALI WAL IKRAM, ALLAH YA SHIGE MANA GABA. بِسم Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… ~~~~~~~πŸ’žπŸ’ž~~~~~~~ Da sunan Allah mai rahama mai jin kai , mai jin kai . Salati ya tabbata ga sugabanmu annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu girma. Wannan littafin badan wata ko wani na kirkireshi ba nayi ne domin mutane masu irin halin in sunji su gyara , Allah ya bamu ikon gyarawa amin. Sadaukarwa ga iyayena , da kuma duk makaranta littafina. Shafi na 1️⃣ Tafe take akan hanya kana ganinta kasan hankalinta baya tattare da ita , saurin da takeyi ya wuce misali , kai in ka hangota daga nesa tsammani ma zakayi mahaukaciya ce , yarinyace wadda bazata wuce shekaru goma zuwa sha daya ba, a kofar wani gida naga ta tsaya nima kuwa na nemi guri na tsaya dan ganin abinda zai faru , kokari takeyi ta shiga gidan tana kuma ja da baya , ta dauki tsawon mintuna goma kafin daga bisani ta tura kofar gidan da sallama ta shiga , cikin sanda ta shiga a hankali da sallama a bakinta, kitchen naga ta nufa da ajiye abinda ta siya tana kokari fita daga kitchen din juyawar da zatayi sukayi karo da juna, goshinta ta dafe sbd tsabar buguwarda tayi duk wannan abin da akeyi sai yanzu nqga fuskar wannan yarinyar mashaAllahu kawai na ambata saboda tsananin kyau da yarinyar ke da shi , matar da sukaci karo naga ta finciki yarinyar zuwa waje , au ke yanzu dan ubanki na aikeki tun dazu amma sai yanzu kika ga damar kawomin aiken , magana take shirin yi amma ta dakatar da ita ta hanyar wanka mata mari sai da bakina ya fashe, kara ta saka saboda azabar da tasha , inna wallahi ba dadewa nayi ba gurin ghalin ne akwai layi in ina bashi kudin baya amsa sai da wani mutum yazo sannan ya mika masa ya bani sakon, rufamin bqki shegiya waya tambayeki , nace miki ki fadamin dalili , labilen dakin aka daga yarinyace da bazata gaza shekarun wannan yarinyar ba itama ta fito tana mika alamun daga bacci ta tashi , inna ina abincina tana magana tana yatsina fuska ni yunwa ma ta fito dani , kallonta tayi tace zo nan yar lelen inna da baba , bara na baki ki sayo alala gidan talatuwa ki ci saboda wannan shegiyar ta sa ke yin halin nata, ta kalleta mai mugun halin tsiya kawai. Daga kofar gidan naji anayin sallama alamar zaa shigo , wani dattijo ne naga ya shiga gidan tana tura keke da fartanya akan kafadarshi da alama daga gona ya dawo, haba asabe naji ya ambata yaya tun daga waje nakejin sautin muryarki menene ya faru ya tambaya cike da yunwar ta amsa masa tambayarsa , kaganta nan tun dazu na aiketa amma sai yanzu ta dawo , kallonsa ya juya gurin yarinyar nan ta farko yace Fatima garin yaya kina dade batun kinsan ina gab da dawowa daga gona kuma da yunwa zan dawo , wallah baba akwai layi a gurin sai dana dade sannan ya bani na taho gida, toh a daina tafiya ana dadewa kinji ko toh tace tare da tashi daga wajen saboda tana da aikin da take da shi masu yawa, Alhamdulillah duk da kankantar shekarunta amma aiki ko babba sai haka , ita kuwa wachchan bqta da aiki sai bacci ,girki ta daura sannan ta kama wanke kwanika , cikin kankanin lokaci ta gaba komai tsaf ba tareda wani jan dogon lokaci ba, sallama tayi kofar dakin amsawa babanta yy kamin ya bata izinin shiga ta durkusa kasa sannan tace inna ba gama aiki toh ta amsa mata ba tareda ta kalleta ba kije ki dauko hijjabi zan aikeki toh tace tana kokarin tashi mahaifin nasu ya tsayarda ita ta hanyar fadar kinci abinci aa ta bashi amsa je ki ci sai ki tafi aiken, haba malam tayaya zance zan aiketa amma ka goya mata bayan kar taje don bani na haifeta ba ta fada ta hanyar fashewa da kuka, haba asabe yarinyar nan bataci abinci ba , bazai yiwu yarinyar ta zauna ba abinci ba batun kuma da akwai, ke tashi kinji kije ki ci abinci sai ki tafi toh tace hade da tashi ta fita . Toh bayan ta gama ne aka bata aiken da zatayi , ta tafi , a hanya ta gamu da yar ajinmu rahane , lah Fatima dama kina nan mallam Ahmad yana ta tambayarki kwana biyu bakyason zuwa makaranta , wlh ba haka bane ba yanzu ma inna ta aikeni gidan baraka aminiyarta inayin sauri sai min hadu wajen tallah da dare , toh sukayi sallama ta tafi. Tana zuwa kofar gidan ado ta ci karo da shi a rayuwarta ta tsanin wannan bawan Allah kwata kwata baya burgeta duk kuwa da tururuwar da yam matan garin ke masa, duk da ita yarinya ce amma takan banbance abu mai kyau da zai amfaneta da marar kyau , ah Fatima ya fada yana washe baki naam ta amsa tana kokarin shiga gidan , aa dakata mana , aikena inna tayi kuma ina sauri ne , au wai asabe ya tambayeta gaba tayi bata bashi amsa ba , da sallama a bakinta ta shiga matar ba zaune akan tabarma inna ina wuni lafiya ta amsa , sannan ta bata sakon da aka ce ta kawo batun ta gama dubawa ne sannan ta mai da mata ragowar ki kai mata kice na zaba , zamuyi magana, toh tace sannan ta tafi gida . Tana shiga ta kai mata sakon, toh ki huta ga kayan tallah chan na hada miki, toh tace sannan ta fita. Da magariba bayan an fita a masallaci ta fita da gyadarta zuwa dandali inda samari da yam mata ke haduwa , kawarta ta dazu ta karaso ah Fatima har kin karaso , eh ta bata amsa , wlh kina kokari gaskiya, yanzu abinda zaayi muyi sauri mu sayar mu koma gida saboda kinga garin na damuna ne ,eh haka ne , mashaAllahu sunyi ciniki dan haka kafin a tashi suka tafi gida , kawartace ta fara shiga gida , sannan ta wuce daf da zata shiga yayi saurin shan gabanta tsaya mana tun daga nesa nake kiranki baki juyo ba danAllah Ado ina so na shiga gida inna na jirana , ai da saninta nazo wajenki dan nazo tace bakya nan kina dandali, eh ta amsa masa, amma yanzu zan shiga gida sai da safe saurin janyo mata hannu yayi kara ta saki sannan ta gartsa masa cizo ta shiga gida , kudin tallan ta bata sannan ta ci abinci ta shiga dakin mahaifiyarta wanda ya ratattake saboda asabe ta hana a gyara shi, kwanciya tayi a kan tabarmar kabar dake dakin , tunani ta fada yi shin ina zata ga dangin mahaifiyarta batasan mahaifiyarta ba gashi mahaifinta har yau bai fada maka tayaya akayi mahaifiyarta ta gujeta ba , hawayene ya zubo mata sakamakon tuna irin rayuwar da take ciki shin yaushe zata fita daga rayuwar da take ciki ita dai tun iya tashinta a haka ta taso ta ganta cikin wahala , Allah ya mata magani kawai a haka bacci mai nauyi na gajiya ya kwasheta ta niyyar tashi da wuri saboda tana da niyyar zuwa makaranta kota halin kaka ne , shiyaga take da niyyar yin aikinta da wuri ta gama a haka har asubah tayi ta tashi saboda ta saba tashi ta yi aiki sosai ta kammala kamin ta gama komai tayi sallama da mahaifinta tayi hanyar makaranta. *PleaseπŸ™πŸ½* *Share* *Comments* To be continue 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸 (True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸. πŸŒŸπŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒŸ *πŸŒ™βœ¨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATIONπŸŒ™βœ¨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… ~~~~~~~πŸ’žπŸ’ž~~~~~~~ Godiya ga Allah subahanahu wata'ala , da ya bani damar ci gaba da rubutun littafina wato kishiyar uwa . Ina matukar godiya a gareku masoya na musamman na cikin group nawa na what's app da kuke ta nuna kulawarku ga rubutu na nagode . Ina matukar godiya ga mahaifana da 'yan uwana da suka goya min baya wajen karfafa min gwiwa wajen yin rubutu na , na gode. Shafi na 2️⃣ Bayan ta isa makaranta a lokacin karfe takwas na safe , dan haka tana Shiga ajinsu ta nufa , da sallama a bakinta kana ta samu wajen zama ta zauna saboda a lokacin malaminsu bai karaso ba . Sunyi kamar zaman mintuna biyar sai ga malaminsu na English ya shiga , bada bata lokaci ba ya shiga yi musu darasi, ya dauki tsawon mintuna kana daga bisani yayi tambayoyi aka bashi amsa ya gama abinda zaiyi ya fita. A haka aka fita break. Alhamdulillahi kowanne malami ya samu damar shiga ajinsu a haka har lokacin tashinsu yayi sun kammala darasin ranar dan haka kowa ya kama hanyar gidansu . Tana shiga da sallama a bakinta bayan tayi bankwana da kawarta rahane akan cewa sai sun hadu gurin tallah . Tana shiga dakinta ta wuce sakamakon rashin jin motsin kowa da tayi wannan ya tabbatar mata daga inna asabe har y'ar lelen tata basa nan dama tasan mahaifinta bayanan yana wajen aikinsa a gona, kayan makaranta ta cire sannan ta hau aikin gida sakamakon anyi kacha kacha da gidan kuma tasan babu mai gyarawa sai ita ta gama sharar tsakar gidan tana shirin yin wanke wanke kwanika taji sallamar mahaifinta alamar ya dawo daga gona , " Baba sannu da dawo wa ta fada tana shirin karbar fatanyar a hannunsa"a'a gidan ba kowane ya tambaya yana sauraron amsar da zata bashi " eh Baba ba kowa , kada kansa yayi sannan ya shige dakinsa ita kuma ta ci gaba da aikinta. Sai bayan sallar magariba ana shirin yin ishsha'i sannan asabe ta dawo ita da Abu diyarta fagajam fagajam suka shiga gidan ko sallama babu a bakin daya daga cikinsu , a lkcn Fatima har ta dauka tallarta ta fita . " inna ki duba mana abinci mana na kwaso yunwa Abu ce mai maganar cike da raini tana murguda baki alamar 'ya'yan da aka shagwaba aka lalata basu ganin Kimar kowa , " ah bari na duba in shegiyar yarinyar asabe tayi wannan furuci tana niyyar tashi tana dubawa ta tarar har ta gama abincin dan haka suka ci ba ko tunanin yin sallah saboda magariba ma a hanya ta isko su. Achan dandali kuwa bayan ta karasa ta tarar da kawarta rahane har ta rigata zuwa " Fatima yau kinjima baki fito ba nayi tsammanin ma bazaki fita ba yau , zare idanuwanta tayi alamar mamaki sannan race " chab wallahi aiki na tsaya yi ne shine na dade ban fita amma ina gamawa na fita na samu gidan namu ne ba kowa to na gama aikin ina jiran su dawo ba Wanda ya dawo shiyasa na fita kawai da yake nasan inda kayan tallar suke, suna zaune suna hira har sukayi cinikin gyadarsu sosai kana suka taba wasannin su na yara suka nufi gida. Rahane ta fara isa gida kafin nan Fatima ta nufi gida kamar kullum Ado ta gani a kofar gidansu " tsaki tayi ta wuce zata shiga gidansu da sauri ya sha gabanta cike da kare mata kallo kana yace " ke wai bakya ganin mutane ne sai kiyi wani fuska ki shige dan kinga an damu dake ya tambayeta ya kallonta "da ni nace ka damu dani ne ta fada cike da k'osawar ya barta ta shiga gida naji bake kikace ba amma kinsan ba wadda nike nunawa soyayya irinki ko kinsan dai 'yammatan garin nan suna kawo Kansu inyi soyayya dasu ko ," toh naji " ta fada tana kokarin shiga gida don ita a rayuwarta ta tsani zancen soyayya gani takeyi kamar dan iskane Wanda ke cewa yana sonta , duk kuwa da dama mutane samarin kauyen na kawo mata hari duk da yarintarta amma tana gocewa , maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi " zanyi mawa innata maganar , jitayi kamar ta sanya ihu saboda razana ita fa ta tsani wannan mutumin , baki ce komai ba ya fada ya na kallonta , shigewa gida tayi tare da banko kofar gidansu ta barshi a tsaye yana kallon kofar gidan tare da cewa lallai zanyi maganinki ta karfi tunda bakisan lallashi ba ya fada a cikin zuciyarshi a yayin da yake shirin barin kofar gidan. Wannan kenan Da sallama a bakinta ta shiga , a tsakar gidan ta tarar da mutanen gidan barka da dare ta musu kana ta mikawa inna asabe kudin warta tayi kana ta kirgasu sai da taga sun cika cif sannan ta saki fuska" tashi kije ga ragowar abinci Chan ki ci toh tace sannan ta tashi ta nufi wajen abincin. Mahaifin Fatima Wanda tunda ta shiga baice uffam ba ya juya ya kalli yarinyar tasa cikeda tausayi a ransa ya na fadi lallai hakkin yarinyar nan bazai taba bari na ba ina so na fada gaskiyar labarin mahaifiyarta amma ina tunanin wata rana zata iya guduna zuwa ga mahaifiyarta , a cikin ransa yake wannan maganar sa'ilin da yake jin k'unar azabtar ta 'yarsa da akeyi yarasa gane kansa sai yayi niyyar yin magana sai ya kasa amma ya barwa Allah komai. "Uhmm ni kuwa asabe dazu da rana na dawo bakya nan ina akaje ne , au shaf fa na sha'afa wallahi yar gidan yaya habu na kan tudu aka saka ranarta shine mukaje , oh ni asabe malam kai bakaga abin arziki ba ai mu dai mun sha kallo inayiwa Abu fatan samun haka , karkada kanshi kawai yayi lallai mata ba'a musu ita nata kawai ta sani Allah ya kyauta. Anan inason naja hankalin mata wadanda ke zaune ya yaran kishiyoyinsu 'ya'ya na kowane babu Wanda kasan zai yi maka rana a rayuwa , amma wadansu matan ba wadanda suke ababen soyuwa a garesu sai yaransu kawai banda su kowa ma hotone , musamman in baa zaman lafiya da mahaifiyar yaron ko yarinya, Ku tuna su fa basu da laifi ko kadan hasali ma basu san yaya akayi gabarku ta kullu ba, mata mu kula amanar Allah ce in ka ci tabbas zata ci ka fatan zamu gyara ,Allah ya bamu ikon gyarawa amin summa amin. Bayan ta gama cin abincin ta tattare kwanikan da akaci abincin dasu a dare nan ta wankesu , a lokacin data gama ba kowa duk an shiga daki dan haka itama ta wuce nata dakin dan kwanciya bacci aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita . Wata mata ta hanga chan kan wani tsauni mai Nisan gaske matar ta juya mata baya , matar tana ta kiran sunanta Fatima! Fatima! Ta na ta kiranta tana so ta kama ta amma ina ita kuwa sai kasan wannan tsauni takeyi gangarawa takeyi tana k'walla ihun Neman agaji a haka ta farka daga bacci tana ihu , salati tayi tare da addu'ar tashi a bacci tana lekawa taga har ta makara dan haka tayi sallah ta soma aikace aikace kamar yadda ta saba , da yake ranar asabar ce ba makaranta sai karfe goma zata tafi makarantar allo wadda da kyar asabe ta yarda akan zataje da taso da safe ta rink'a yi mata tallar kosai amma hakan bai samu ba. Wannan lokacin data samu hakan ya bata damar yin aiki sosai . Har ta gama ba Wanda ya fito da haka ta tsaya tana jiran fitowar masu gidan tare da addu'ar Allah yasa su fito da wuri dan ta samu damar zuwa makaranta........................... PleaseπŸ™πŸ» Share & Comments. To be continue....... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 ( True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸. πŸŒŸπŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒŸ *πŸŒ™βœ¨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATIONπŸŒ™βœ¨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… ~~~~~~~πŸ’žπŸ’ž~~~~~~~ Ina godiya da shawarwarinku , ga yadda zan tafiyar da littafina, musamman makaranta littafina da 'yan uwa da abokanan arziki. Ina ganin yawan comments naku, ina jin dadi kuma insha Allahu nima bazan baku kunya ba. Sadaukarwa ga iyayena da 'yan uwana da abokanan arziki , luv u allπŸ₯° Wannan page din nakine sadaukarwa gare ki 'yar uwata Zainab, Allah y kawo miji na gari amin. Shafi na3️⃣ Tana nan tsaye har karfe tara tayi kafin nan mutanen gidan suka tashi , da hanzarinta ta isa ga mahaifinta "Baba ina kwana" , taceβ€œ lfy qlu , har kin gama aikin naki ", β€œeh na gama da shi" β€œtoh Allah ya miki Albarka ", β€œamin" tace da shi , sai a sannan Asabe ta fito tsakar gidan , " Inna ina kwana", β€œlafiya "ta amsa a yamutse, β€œshin kin gama aikin naki ", tace β€œeh na gama", β€œtoh yau ba maganar zuwa makaranta, rafi zaki tafi Ι—ebo ruwa, ga kayan Abu chan zaki wanke saboda sun yi datti", kusan fashewa tayi da kuka saboda ta shirya akan cewa za ta je makaranta saboda ta kwana biyu bata samu damar zuwa ba , " toh" ta amsa mata, sannan ta juya ta nufi inda kayan ruwan suke, bokiti ta Ι—auka ta nufi hanyar kofar gida, β€œkafin ki dawo zan zube miki kayan a nan ", β€œto" tace sannan ta juya ta nufi kofar gida cike da Ι—acin rai . A hanya ta tsaya ta ci kukanta, ta Ζ™oshi, sannan tayi gaba , tana tunanin rayuwarta a nan gaba duk da ita yarinyace amma tana iya sanin masoyinta da maΖ™iyinta , ta Ι—ebo ruwa sosai har ta cika gidan dukka , kana ta fara wanke kayan , bata gama ba har sai da rana ta fito, sannan ta gama a wahalce , tana gamawa ta nufi dakin Asabe, " inna na gama" tace da ita, "to kije ki daura girki ", β€œinna wallahi banci abinci ba ", β€œka ji min shegiyar yarinya yo dan baki ci abinci ba sai me, ai aiki yanzu ma kika fara shi , sai kin gama aiki tsaf, sannan ki duba idan 'yar lele ta rage abincin ", to ta juya idanunta cike da hawaye , sai da ta kammala abincin nan tsaf sannan ta zuba musu ka'ida ne daman sai sun gama cin abinci sun rage kafin ta ci dan haka sai ta jira suka gama sannan ta dauki sauran taci a lokacin ta galabaita sosai, tana jan jiki ta shiga Ι—aki, zaunawa tayi, sannan ta soma cin abincin cike da kewar mahaifiyarta, duk kuwa da bata santa ba ta ya ya zata iya cigaba da fuskantar wannan rayuwar mai cike da tsanani da dana sani "Allah ka kawomin dauki amin" taΖ™arasa haΙ—e da share hawayenta da suka gangaro mata kuncinta , tana wannan zaman har bacci ya kwasheta . Tana cikin bacci nan taji an kwara mata , a razane ta farka, "au ke yanzu dan ubanki maimakon ki zo kiyi abin da za ki yi, kin san ki na da aiki shine kika zauna , shegiya mai mugun hali , tashi shegiya kawai" Asabe tayi furucin da bokitin ruwa a hannunta, "to inna zan fito ", β€œau jiran ki zan yi ki fito dan ubanki" ta tambayeta tana kokarin fincikota hade da kai mata duka, β€œinna dan Allah kiyi haΖ™uri wallahi na gaji" , β€œau ni ki ke cewa kin gaji, lallai wuyanki yayi kauri yau zaki gane kurenki a gidannan fito" , ta fada tana Ζ™oΖ™arin shiga daki , dukanta ta shiga yi ba ji ba gani, sai da ta tabbatar bazata iya moruwa ba, duk jikinta ta fasa mata shi "kuma ki tashi kije ki yayo itacen da zakiyi girkin dare tunda yau mallam IIlyan bai dawo ba" tana nufin mahaifinsu su Fatima , da Ƙyar ta tashi da rarrafe ta dauki yagaggen mayafimta ta fita domin yo itace a daji bata dawo daga itacen ba sai chan yamma a lokacin ta gaji sosai, amma haka ta daure ta daura girkin bayan ga Abu a zaune tana faman barar gyad'a tana zubawa a baki . A haka rayuwar Fatima ta cigaba da tafiya, cike da tsanani, da tsauri, da azabtuwa, har suka kai shekaru goma sha biyar ita da Abu a lokacin ne maΖ™erin budurci ya fara Ζ™era su , Fatima ta fito a matsayin kyakykyawar budurwa son kowa, to a sannan ne fa samarin kauye suka Ζ™ara yimata chaaaa a kanta ciki kuwa har da Ado wanda har yanzu yake kan bakansa na soyayya da ita , domin har ya sanar da mahaifiyarsa domin ta sanar da inna Asabe. Duk da wannan kyawun nata daya bayyana, amma hakan bai hana tsantsar wahalar da take ciki , ta bayyana akan kyakykyawar fatarta ba. A wannan shekarun abubuwa sun faru na daΙ—i, da akasin haka, ciki kuwa har gama makarantar Fatima, ta firamare wadda da Ζ™yar hakan ta samu, bayan gwagwarmayar da aka sha da inna Asabe akan harkar makarantar , a yanxu cikin ikon Allah komai ya zama tarihi game da makarantarta ta

Chapter 1 of 11