primary, secondary ce dai bata amince ba, duk kuwa da cewar malaminsu na makaranta, malam Ahmad yayi gwagwarmayar ta cigaba, ganin irin hazakar da take da shi amma fafur ta k'iya , ganin haka ya hakura har ya koma garinsu Kaduna, dama bautar kasa yazo kuma ya gama ya koma ba tare da samun ya samu ya cika burinsa na ganin Fatima ta cigaba da makaranta ba .
A yanzu gashi mahaifinsu girma ya kamashi dan haka baya iya tab'uka komai , duk da, ada ma ba iya yin komai ballantana yanzu da ƙarfinsa ya ƙare duk da yana gudu da ƙyamar abun a zuciyar shi, ganin yadda ake yiwa d'iyarsa , a lokaci da dama ya kan so ya baiwa yarinyarsa labarin mahaifiyarta amma idan ya tashi faɗa mata sai ya kasa , a haka yake barin abin a ransa badan yana so ba, wani lokacin ya kan ji kamar ya yi kuka, idan ya tuna da mahaifiyar Fatima da irin zaman da sukayi lallai ba shakka Fatima ta dauki halin hakuri irin na mahaifiyarta.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(Asalin labari)
Shin wai wanene mallam iliyasu mahaifinsu Fatima ?
Malam iliyasu hafaffen garin kano ne, a ƙaramar hukumar wudil yankin darki , yana zaune tare da iyayensa da yayyensa da ƙannensa, mahaifinsa malam Bello matan sa uku , laraba da hansai da kuma Rabi kowacce su tana da yara laraba itace ta fari, tana da yara biyar kuma itace mahaifiyar su mallam Iliya , bayan haka yana da ƙanne, biyu mata biyu, maza biyu, Khadija , Lami, da kuma Habibu da sulaiman , a dakin hansai wadda itace ta biyu yaranta huɗu , Adam, Muhammad, da kuma Salamatu, Rabi yaranta biyu , Hannatu da kuma Hadiza waɗannan sune zuri'ar malam bello .
Mallam bello da iyalansa suna rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da tarbiyarsu, abin birgewa da sha'awa , yana kulawa da iyalansa yadda kowa kanyi sha'awar waɗannan iyalan . Hakama matan gidan suna da haɗin kai sosai kowacce duk da zaman kauye ne takan taimakawa ƴar uwarta, kuma suna taimakawa mijinsu .
Malam iliya shine babba cikin yaran malam bello, gaba ɗaya ragowar yaran gidan kannensa ne , yakan sanya kannensa su tafi makarantar allo, kasancewar a lokacin babu makarantar boko, ya taimakawa ƙannenansa sosai wajen iliminsu na muhammadiyya.
Sana'ar malam Bello noma idan ya girbe abinda ya shuka ya kai birni ya sayar , aikinsa noma da fatauci ta haka yake rike da iyalansa , lokacin da malam iliya ya kai mizanin samartaka sai ya sanya iliya akan harkar suna tafiya duk Inda yake harkar fataucinsa , in sun tafi sauran yaran maza sukan kula da harkar noma ta yadda zasu taimakawa mahaifinsu, lokacin da suka dawo gida fatauci Allah ya hadashi da Asabe wadda ta kasance yarinyace ƴar mace mahaifinta ya rasu tun tasa ƙarama dan haka ta tashi hannun mahaifiyarta babu kwaɓa , anyi gwagwarmaya kafin auren dan mahaifinsa bai so auren ba, amma ganin d'an nasa ya na ce yana sonta yasa ya barshi a haka akayi auren ba tare duk da ba kowa yaso auren ba amma a haka akayi auren ...........
Please🙏🏻
Share
&comments
To be continue.........
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸
(True life story)
🍁Daga alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Fatan alkhairi ga duk makaranta littafina , godiya ta musamman ga masu gyara min kura kurai na .
Jinjina gareki aunty nersmah da aunty dije, kuna namijin kokari wajen kuga littafina yayi daidai ba tareda samun matsala ba ina godiya sosai Allah ya bar kauna a tsakanin yan moonlight writer's association amin.
Luv u all my dear fan's🥰 wannan page din sadaukarwa ne gareku.
Shafi na 4️⃣
A haka akayi auren har amarya ta tare , kadahan kadaran ake zaune tsakanin Asabe da dangin malam iliya, babu wani jituwa a tsakaninsu , da yake ita kuma ba wani iya mu'amala tayi ba bata damu da su ba su ma basa zuwa inda take itama haka , a haka har akaci wata hud'u da aurensu a sannan ne ya ci gaba ta tafiye tafiyensa zuwa garuruwa , sai ya hutashshe da mahaifinsa akan ya zauna tunda shi ya kawo karfi sai ya dauki kaninsa su ka ci gaba da tafiya.
Abinda yake damun 'yan uwan malam iliya akan irin rashin mutuncin da matarsa Asabe keyi na bata ganin kowa da mutunci k'annensa basa zuwa gidan yayansu , duk kuwa da irin soyayyar da ta ke tsakaninsu dan shi Allah yayi shi mai so kyautatawa 'yan uwansa , amma kash sai Allah ya hada shi da mata marar sanin darajar mutane.
Har iya wannan tsawon lokacin Asabe ko batan wata bata tab'ayi ba hakan ne ya sanya ta kara bakin jini cikin dangin malam iliya , abinka ga k'auye sai surutai kala kala akan taki haihuwa , dan haka mahaifansa mata su ka fara mishi zancen ya kara aure , a sa'ilin da malam iliya yajewa da Asabe zancen nan kamar wadda zatayi hauka dan kishi , ta ci alwashin matukar dana raye babu shi babu kara aure , cin zarafi kuwa babu Wanda bai sha ba a wajen Asabe , ranar tayi yaji ta sanar da mahaifiyarta , abin ka ga gidan da babu tarbiyya haka mahaifiyar ta ta ta goya mata baya , kwananta d'aya a gidansu washe gari malam iliya yaje gidansu Asabe biko amma anan uwar ta ta ta sauke masa kwandon rashin mutunci da cin al washin ba za'a ayiwa yarinyarta kishiya ba indai tana raye kuwa , hakuri yayi ta bayarwa akan insha Allahu hakan bazata faru ba sannan ta yadda 'yar tata ta koma gidan amma sai da tayi ak'alla sati guda sannan ta koma.
Malam iliya zaune gaban mahaifinsa wanda ya sanya aka masa kiranshi , ya sunkuyar da kai kasa yana sauraron mahaifinsa cike da girmamawa , " kaji abinda na ce maka ba rigada na yanke hukunci na zab'a maka maryama 'yar gidan aminina malam kalla kuma umarni na baka ba shawara ba na yanke aurenka nan da saba'ar wata in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai ka sanar da mai dakinka" , "to" ya amsa cike da girmamawa saboda baya tab'a jayayya da mahaifinsa akan komai ma , amma shi kadai ya san halin da ya ke ciki game da zancen da mahaifinsa ya fada masa , yayi masa sallama tareda shiga cikin gidan domin gaisar da iyayenshi mata , sosai inna hansai ta mishi fada tareda kwadaitar dashi romon da ake samu yayin da aka samu zuri'ah , ta gama yi masa nasiha sannan yayi musu sallama tare da innar sa ya tafi gida cike da fargabar ta ya ya zai fadawa matar sa Asabe a haka ya yini ya kwana babu sukuni da walwala , har sai da Asabe ta gane tambayarsa tayi yace mata ba komai wucewa tayi ba tare da kulawa ba .
Washe gari da safe ya tashi da nufin sanar da mai dakin nashi, amma ya kasa , haka yayi ta ajiye da maganar har biki ya kusa saura sati biyu bai sanar da iya ba.
Asabe na zaune a tsakar gida aminiyarta ta shigo da gudu cike da alamar firgici a fuskarta , dubanta Asabe tayi cike da haushi ta ce " wai baraka yaushe zakiyi hankali ne wai ke ba kiga cikin da ke jikinki ba kika shigomin irin haka salon ki zo haihuwa ki mutu " dakatar da ita Baraka tayi ta hanyar cewa " yo ba gwarama mutuwa ba an san lokacin ka ne yayi akan wannan bala'in da ya ke shirin tunkararmu" " wanne bala'i kuma Allah ya tsaremu da shi "ta fada tana tura d'an kwalinta gaba har zuwa girarta , " ke Asabe da labari na zo miki naga alamar ke baki sa ni ba ko " ? Ta tambayeta ta jiran amsarta "dan Allah ki fadamin mana kina wani jan zancen" ta sake tura dan kwalinta gaba, "to wallahi mijinki yqna nan yana shirin k'ara aure" , "kan uban chan ba Ankara da garin da ta b'arar ba , ta zunduma wani uban ashariya ," haba biri yayi kama da mutum , shiyasa ya kasa sukuni a cikin gidan nan har ya tafi fataucin nan ashe ya san abin da su ke shiryawa shi da matsiyatan iyayan na shi ", lallai ya taro wa kansa bala'i wallahi ," a'a tsaya mana ai ba hargagi zakiyi ba " cewar baraka da ta ke sake neman wajen zama, " tsayawa zamuyi mu fitar da maganin matsalar da ta ke tunkaro mu", zaman 'yan bori tayi ta zuba uban tagumi hannuwa biyu biyu , " inajinki baraka" ta fada dana kallonta " me ki ke so ayi yanxu "? Ta tambayeta tana kallonta , " kinsqn babu yadda za'ayi nabar wata mata ta auri malam wallahi kina ganin bana haihuwa ta yaya zaayi na bar wata ta shigo ta haifawa malam iliya d'a musamman ma na miji ta yadda zata cinye dukiyarsa " " kinyi gaskiya kuwa aminiyata" yanzu kinaso a tsayar da maganar aurenko"? Ta tambayeta ," eh " ta bata amsa " to yanzu tashi zakiyi mu tafi chan kauyen lajawa akwai wani hatsabibin boka , sunanshi boka sha yanzu magani yanzu , amma ina fatan kinada kudi a hannunki "? Ta tambayeta tana kallonta ," eh da akwai wanda malam ya barmin da zai tafi ban tab'a komai ba ", " to tashi zakiyi mu tafi dan kinsan da zafi zafi akan daki karfe", " eh to bara na Shiga na dauko mayafina" ta shige daki a birkice domin dauko mayafi ,sannan su ka yi waje cikin hanzari.
Mata mu kula! Mu kula ,a kula! , kawaye sukan kawo cikas sosai a zaman aure , kar ki bari kawarki ta rudeki takaiki ta baroki akan tudun dana sani , sirrinki ki boyeshi karki sake ki bayyanawa kawarki halin da kike ciki da mijinki , zata sanyaki kiyi danasani a rayuwarki da rayuwar aurenki baki d'aya, daga k'arshe mijinki ya sakeki , in batada aure ta aure miki shi , Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu amin .
Basu k'arasa cikin dajin ba sai da sukayi tafiya sosai har rana ta fad'i kana suka karasa , dan har Asabe ta sare amma Baraka ta k'arfafa mata guiwa da kyar su ka karasa bayan bakar wahalar da su ka sha k'afafunsu sun kumbura sosai sun jigata , kana su ka karasa wajen , tunda su ka nufi wajen Asabe takejin iface iface namun daji kukan tsuntsaye da sauransu , a haka su ka karasa ," Ku shigo da baya" cewar boka sha yanzu , cikin wata gabjejiyar murya, da sauri suka juya har suna kokarin bige junansu , Baraka ta zunduma ashar ta yiwa Asabe da nunin itama tayi wannan itace sallamar Shiva wajen bokan , aikuwa itama tayi , sannan ya basu izinin zama , su ka zauna ,Asabe ta bud'e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shiru , zuwa kamar Minti biyar sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata, yayi nuni da wata kwarya sai ta taho da kanta ta zauna a mazauninta kan wata tararriyar kasa , yayi nuni da ruwan cikin kwaryar aikuwa yayi bakikkirin daga baya kuma ya koma fari, aikuwa ya shek'e da dariya" angama bukatarki ta biya za'a fasa auren nagama komai , yanzu maganar aure babu ita na Sanya kiyayya mai karfi tsakaninsu " Myrna sosai Asabe tayi najin an fasa auren malam iliya ,su ka yiwa boka sallama da zasu tafi ya bata maganin da zata zuba masa a abinci da Wanda zata zuba tayi wanka sai turaren da zata sanya Wanda idan har ya shak'a to zai manta da kowacce mace a duniya sai ita, sannan suka nufi hanyar gida a lokacin anyi sallar magariba sannan su ka karasa gida , sai da suka huts sannan Baraka ta nufi gidanta itama, da kudirin aikata abinda boka ya sanyata ta kwana , dan tana tsammanin dawowar malam a tsakankanin wannan lokacin , a haka tayi bacci tattare da mummunan k'udiri a ranta.
A chan gidan su malam iliya kuwa anata shirye shiryen biki saboda wannan bikin na so ne , ana wannan yanayin malam iliya ya dawo saga fatauci , lokacin da ya je gidansa da yaga Asabe bata nuna masa wata alama ta nuni da cewa tasan zancen hakan ya saka ya ji dadi kuma yayi mamaki bisa ga yadda yasan qauye da gutsuru tsoma , amma yaga sab'anin haka, hakan ya sanyashi ya tafi gidansu domin gaida mahaifins. Tana fita Asabe ta yi shirinta tsaf da magungunan da bokq sha yanzu ya bata ta zauna zaman jiran malam ya dawo daga gidansu ..............
Please🙏🏻
Share
&comments.
To be continue........
Luv u all my fan's🥰🥰😍
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
(True life story).
🍁Daga alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina matuk'ar godiya gare ku masoyana , saboda nuna kulawarku ga littafina mai suna Kishiyar uwa , a gaskiya na rubuta shi ne badan komai ba sai don tunanin da nayi wannan shi ne abin da yake damun al'umma , idan mata taga an bar mata 'ya'yan abokiyar zamanta idan har basa shiri da ita to fa su ma yaran nata sun Shiga uku , dan Allah mata mu kiyaye wannan hakkin lallai sai Allah ya tambayemu a kanshi , ki sanya a cikin ranki idan da yaranki ake yiwa haka ya ya zakiji a cikin ranki , Allah yasa mu gyara amin.
Ina ganin comments naku gaskiya ina jin dadi , kuma ku ma burgeni , insha Allahu bazan baku kunya ba
Comments🥰
Maman Ammar
Kishiyar uwa🌹💞nicely sis Allah ykara basira ina matukar jin dadinsa wlh 🥰🥰
~phareeeda
Allah sarki Fatima zakisani kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭
Duk naga comments ina godiya.
Shafi na5️⃣
Ko da malam Iliya ya k'arasa gidansu ya tarar ana ta shirye-shiryen biki , wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaida shi amsawa yayi kana ya mishi maganar "angama komai da ake buƙata yanzu abinda ake jira shi ne saboda su na so su kai kayan aure da sadaki, saboda auren ya kusa, amsawa yayi da to , kana yayi godiya, ya yi masa sallama ya shiga cikin gidan wajen iyayen sa mata , nan ma ya tarar suna ta shiri sosai , ya gaida su ya mu su alkhairi, ya tsaya sai da su ka ga ma komai na harkar kai kayan auren, da sadaki sannan ya nufi hanyar gidansa.
A can gida kuwa Asabe ta gama har had'a komai da tasan boka sha yanzu ya ba ta, dan haka a halin da ake ciki malam Iliya kawai ta ke jira ya dawo gida, tayi wanka da magani ta shafa turaren da sauran kayan amfanin da ya bata za ta sanya masa a abinci.
Da sallama ya shiga a bakin sa , amsawa tayi cike da kwarkwasa , ƙamshin turaren da boka ya bata shi ya shak'a ai kuwa ta ke yaji kanshi yana juyawa , wanka ta jashi yayi, a hakan dai ta bashi wannan abinci ya ci , kana ya fada mata kanshi na yin ciwo zai kwanta rakashi tayi har sai da ta tabbatar da ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin ta, fita tayi daga gidan domin sanar da k'awarta halin da ake ciki.
Har bayan magariba bai tashi ba har Asabe ta dawo daga gidan Baraka , sannan ya tashi daga baccin , zuciyarsa yaji ta b'aci gaba ɗaya yaji auren da ake shirin yi masa ya fita a ransa , yaji ya tsani yarinyar gabaki ɗayanta, haka ya kwanta ransa na b'aci, ko da gari ya waye mahaifinsa ya kirashi bai je ba , har aka kwana uku bai je ba , kai auren ya taho dangin sa nata harkokin biki amma shi banda shi, dan haka mahaifinsa ranshi ya b'aci yayi niyyar zuwa har gida ya same shi.
Da wata ranar talata lokacin saura kwana biyu a ɗaura auren mahaifin nasa yayi dirar mikiya a gidan, faɗa ya rufe shi dashi, sosai shi kuwa ko a jikin shi ,sai ma duban mahaifin na sa da yayi yace masa shi ya fasa auren daskarewa mahaifin nasa yayi abinda bai taba ji ba , juyawa yayi ba tare da yace komai ba ya tafi gida cike da damuwa, ko da ya sanar da matan nashi sosai su ka ɗauki zafi akan haka, amma da yayi musu bayanin yadda zasu fi ganewa su san ba laifin sa ba ne ba, sai su ka daina hargagin da su ke yi , a haka aka bawa iyayen yarinya hakuri abin ka ga k'auye gari fa ya ɗauka aka yi ta ƙananan maganganu, daga baya komai ya lafa, ita kuwa data ga haka sai ta saki jikinta tayi ta iya shegen ta abin ta , ta kuma mai da zuwa wajen boka sha yanzu kamar masallaci, mahaifinsa ya nema masa ak'alla yara sunyi biyar tana wargaza auren daga baya mahaifinsa ya hakura ya zubawa sarautar Allah idanu, yayin da tsanar Asabe ta dawo sabuwa a zuk'atan matan gida da yaransu .
Yanzu shekarar malam Iliya goma da aure , batun gwagwarmayar da ya sha , a harkar sana'arsa da rayuwar auren sa da Asabe Alhamdulillah, komai ya kankama ya samu rufin asiri sosai , babban abinda ke damunsa shi ne rashin haihuwa domin a wannan cikin shekarun aminyar Asabe Baraka ta haihu namiji aka sanyawa d'an nata sunan mahaifinta wato Adamu, a wannan shekarun mahaifin malam Iliya ya sanya ana tayiwa d'ansa addu'ah akan Allah ya dawo masa da d'ansa daga Sharrin matarsa Asabe, Allah kuwa ya amsa addu'arsa da ya dade yanayi.
A garin yawon fatauci, wata rana malam Iliya fatauci ya kaishi zariya , bayan ya gama komai yana shirin dawowa gida a nan Allah ya haɗa shi da mahaifiyar Fatima wadda ake kira da maimunatu ta kasance haifaffiyar garin zariya ce , sosai ya yaba da hankalinta , bai yi mata magana ya bita gidansu ya tambayi izinin neman aure mahaifinta ya amince , amma ya faɗa masa shi fataucine ya kawo shi zariya , shi haifaffen garin kano ne, ya kuma tambaya akan in ya tashi dawowa, magabatan sa zasu zo nema masa aurenta , a haka suka rabu badan junansu sun so ba , ko da ya fad'awa mahaifinsa yayi murna sosai ya faɗawa matansa amma yayi gargadi mai kyau akan kar wanda ya fitar da zancen, haka kuwa aka yi aka ɓoye maganar har sai da biki ya rage y'an kwanaki, amma Asabe bata da labari.
Alhamdulillah lallai rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya , domin kuwa a ranar jumaah ne aka daura auren malam Iliya da maimunatu mahaifiyar Fatima , mace mai hakuri da kawaici , mahaifin malam Iliya shi yayi komai na auren. Sai ranar da aka daura auren sannan Asabe taji , ranar ansha bala'i domin kuwa gidansu malam Iliya ta tafi ta dinga yi musu hauka amma ba wanda ya kulata ta k'arashe rashin mutuncin ta tayi gida kamar mahaukaciya, ta koma a ranar , ko da ta koma gidan bai kulata ba ta ƙarasq wulakancinta ta hakura .
Dare nayi 'yan kawo amarya suka kawota aka a jiye ta a ɗakinta suka mata fad'a sosai , aka ce a kirawo Asabe domin a musu fada amma ta aika musu sak'onnin zagi ba arziki su ka tattara yanasu yanasu su ka yi waje cike da Allah wadai akan halin Asabe , aka bar amarya a cikin gidan mijinta .
Sai muce Allah ya bada zaman lafiya , ya kauda fitinar Asabe amin.
Godiya mai tarin yawa a gareku yayata y'ar uwata wato Usaina musa saleh bisa ga gudummawarki gareni Allah ya taimakeki a aikinki ya bada sa'a amin.
Godiya a gareku yan moonlight writer's association Allah ya k'ara had'a kawunan mu amin ya taimakemu amin , ina godiya sosai.
Please🙏🏻
Share
&comments
To be continue........
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina k'ara godiya ga Allah subahanahu wata'ala da ya kara bani damar ci gaba da littafina na kishiyar uwa, kuma ina godewa mahaifana da y'an uwana da suka jajirce wajen ganin na ci gaba da rubutu na , haka ma fan's nawa ina kara godiya.
🥰😍 ina ganin comments kuma inajin dadi sosai wallahi.
Sadaukarwa ga duk makaranta littafin nan tare da y'an moonlight writer's association, Allah ya k'ara hada kawunanmu amin y Allah .
Shafi na 6️⃣
Aka bar amarya gidan mijinta , da dare yayi sosai abokanan ango suka rakoshi , amma fafur Asabe ta k'ek'asa k'asa ta hanasu shiga gidan, ban yadda suka iya haka suka koma , suka yiwa malam Iliya fatan alkhairi shi ma yayi musu sallama sannan suka tafi , shi kuma ya shiga cikin gida aikuwa yana shiga ta ce da wa Allah ya had'ani in ba dakai ba ta shiga yi masa ruwan bala'i amma yayi mata banza wannan ya k'ara kular da ita sosai , ya juya zai tafi tayi sauri ta rik'e masa wuyan rigarsa ta baya , a fusace ya juyo ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta wanda saboda tsabar razana da mamaki sai da ta zube k'asa , ni kuma da nake tsaye ina kallon abinda ke faruwa dariya nayi a hankali saboda kar masifar ta dawo kaina, amma ke ma Asabe in banda tsaurin ido ta yaya zaki rikewa sabon ango wuyan riga ki hanashi shiga d'akin amaryarsa abinda yafi haka ma zaki gani🥴 , saboda duk rashin mutuncinta bata tab'a rik'e masa riga ba da sunan rashin kunya sai yau , tana a zaune kafin ta dawo hayyacinta har ya shige d'akin amaryarsa Maimunatu sai rufe k'ofarsa taji garam aikuwa da sauri ta zabura kafin ta k'arasa har ya sanya sakata , sai dai muce asha amarci lafiya malam Iliya😍. Asabe kuwa kwana tayi tana hauka a tsakar gidan in ta gaji ta zauna in suka motsa mata tayi ta buga musu k'ofa haka ta kwana bata runtsa ba tsabar masifa.
Washe gari da safe kuwa suna fitowa suka ganta a zaune a tsakar gidan rana d'aya duk ta lalace , saboda masifar kishi , aikuwa tana ganin sun fito haka ta nufi maimunatu da itace sauri yayi ya kareta tare da watsawa Asabe mari ni kuma abin nema ya samu matar direba ta haifi mota ina kallon ta ina mata gwalo amma bata ganni ba ta juyo kenan b'arina ni kuma na fece🚴🏻♀️ a miliyan, a ranar haka ta hanasu sakat a gidan ya zamana ko ina maimunatu zata shiga sai dai malam ya rakata , a haka ta dinga rayuwa har malam ya koma da sana'arsa wato fatauci , aikuwa gida ya zamar mata kamar birsin dam ma iyayen malam da k'annensa suna sonta shi ne abin ya zame mata da sauk'i .
A lokacin da suka cika wata biyar da aure Allah ya azurta maimunatu da samun ciki zo kuga murna gurin malam Iliya , rana samun kulawa sosai , tunda Asabe taji maimunatu na da ciki shikenan fa hankalinta ya tashi abinda take ta gudu gashi ya faru , da sauri ta garzaya gidan aminiyarta baraka , a tsakar gida ta zube had'e da dafe kai " na shiga uku ni Asabe Baraka tawa ta k'are a gidan malam " ta fad'a cike da tashin hankali " nutsu kiyimin bayani" cewar Baraka wadda ke yiwa Ado wanka a lokacin yana da shekaru takwas da haihuwa," wai wachchan matsiyaciyarce keda ciki " a razane Baraka ta dubeta da gaske kikeyi mun shiga uku , to yanzu menene abin yi "? Ta tambayeta " to ai nima shi nake nema shiyasa na zo gurinki " bara na gama shirya Ado " ta ce tana kokarin tashi" to kawai Baraka tace domin kuwa hankalinta ba'a jikinta yake ba , rana gama shirya shi ta barshi a gida suka dauki hanyar wajen boka , sunyi masa bayani a cikin bayanin kuwa har da son haihuwar da Asabe ta ke son tayi yace musu zai fara ba ta haihuwar kafin nan , aikuwa a take ya sanya aljani ya shiga jikinta a take a wajen ta samu ciki sannan yayi mata alk'awarin sawa malam kiyayyar maimunatu da abinda ta haifa godiya sukayi masa sosai suka tafi gida .
Bayan kamar wata biyu da samun