suka faru , yadda yaga bata damu ba hakan yayi masa dad'i sosai , ya yi mata sallama ya fita ya koma wajen y'an d'aurin auren.
Toh a haka aka daura aure su inna Asabe baki har kunne yarinyarta ta samu mai kud'i , Wanda yake fita birni dama hakan tafi so ace yau d'iyarta tafi ta kowa sa'a a k'auyen , haka dai aka k'araci bikin anci an kuma sha biki kam sam barka amma fa Fatima tasha habaici wajen inna Asabe da k'awayenta har ma da zainabu da k'awayenta dare nayi aka kai amarya gidan mijinta da zummar sati d'aya zasu yi su tafi Lagos sai mu ce Allah ya bada zaman lafiya ya kad'e fitina amin .
Lokaci nata tafiya bayan anyi biki amarya su ka tf da mijinta Lagos , a haka lokaci ke ta tafiya , cike da k'alubalen rayuwa a yanzu shekara d'aya kenan da bikin zainabu da Ado , a yayin da Fatima take cikin tsaka mai wuya , cin zarafi ,kyara , habaici, duka , zagin cin mutunci, ba Wanda bata fuskanta ba daga mahaifiyar ta ta inna Asabe, ga wani cin zarafi da y'an k'auyen keyi mata , duk inda suka ganta zancensu d'aya tak'i aure , wasu ma har cewa sukeyi tana zaman karuwanci ne kawai ganin mahaifinta baya duniya , dama dai sauran maganganu barkatai , haka take d'auke kanta daga wad'annan habaice habaicen wani zubin inna Asabe da k'awayenta ne zasu taru a gidan su ci mata mutunci son ranta, ga aikatau iri iri bata hutawa , ita kuwa inna Asabe taci mai kyau tasha mai kyau ba abinda ya dame ta saboda y'arta tana aiko mata da abin duniya , Fatima kuwa sai tayi sa'a sannan ta samu abinci taci say d'aya a rana , kuma duk wannan halin tsananin da take ciki bata tab'a tarar kowa ta fad'a mishi ba , gashi samari yanzun basa zuwa wajenta mutane suka dinga tunanin ko shafar aljanu ce , ko kuma dan ta huce mizanin y'an matantaka a k'auyen , abinda basu sani ba inna Asabe ce tayi asirin da ba Wanda zaiji yana Sonta kaf garin , tun abin baya damun Fatima har ya dawo yana damunta , in ta zauna ba abinda take tunawa sai rayuwarta da mahaifinta da kuma labarin mahaifiyarta Wanda mahaifinta ya bata , sai dai taci kukanta babu mai rarrashinta, abin d'aya ta k'udurta a zuciyarta Wanda idan tana tunawa takan samu sa'ida a zuciyarta , shine yake sanyawa ta k'ara nutsuwa , na cewar bashakka ko ba dad'e ko ba jima zata nemo asalin dangin mahaifiyarta ,wannan yakan sanya taji dad'i sosai a ranta.
🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸
A yau Asabar tun safe ta tashi ta kama kiciniyar aiki sosai takeyin aiki sakamakon bak'in da zasuyi daga b'angaren inna Asabe d'an kanwar mahaifiyarta ne zaizo dan haka ta sanya Fatima yin aiki ganin shi a birni yake da zama kuma y'an birni lallab'a su akeyi, haka fatima ta zage sosai tanayin aiki , wajen k'arfe biyun rana bak'in suka sauka murna sosai inna Asabe tayi na ganin tare da d'ansa aka so mai suna Bilya , ko kad'an yaron baya da tarbiya komai kai tsaye yakeyi gashi sai ya had'u da sakalcen uban ai kuwa abu ya k'ara ta'azzara sosai , shaye shaye, Neman mata ba Wanda bayayi , kai ya kai mak'ura wajen aikata abinda bashi kenan ba, ganin d'an uwanta, cikin washe baki suka gaisa da juna tare da tambayar bayan saduwa, sunyi hira sosai , Fatima na jinsu tana d'akinta , inna Asabe ce ta kwala mata kira da sauri ta fito ta gaishesu , aifa tunda biliya ya d'ora idanunsa akan Fatima ya fara lasar baki kamar wani tsohon maye, inna Asabe ce ta umarci Fatima da ta kawo was bak'insu abinci haka ta dinga jigilar abinci tana kai musu , Shiva d'ari fita d'ari sai sun had'a ido da bilya , tun tana masa yakana har sai da ya k'ureta tako galla masa harara , ai sai yaga tafi d'azu kyau , sai da ta gama komai sannan ta juya ta nufi d'akinta ta barsu suna cigaba da hirarsu ta zumunci...........
Please
Share
&
Comments
To be continue.........
INA K'ARA GODIYA GAREKU FRIENDS NAWA DA FAN'S NAWA ALLAH YA BAR ZUMUNCI .
Please ayi manage da wannan I'm so tired.
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad)🌸
Shafi na 1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹
🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹
🌸🌸
🌹
Bayan ta fito daga d'akin inna Asabe , d'akinta ta nufa cike da takaicin bilya wannan wanne irin mai shegen kallo Allah ya had'a ta da shi , tana murna Allah ya raba ta da Ado ashe hakarta bata kai ga cimma ruwa ba ga wani mai nacin kallo ta had'u dashi , a haka dai tayi ta maganganunta tana jan tsaki .
A chan d'akin inna Asabe kuwa bayan Fatima ta fita , bilya ne ya dubi inna Asabe yace " gwaggo wacece wannan dana gani a gidan nan, saboda ban tab'a ganinta a gidan nan ba ", kyab'e baki tayi sannan tace" Fatima mana y'ar kishiya ta da ta rasu " zabura yayi cike da jin dad'i " yauwa anzo wajen ya fad'a yana sosa kai ," baban shi ne ya dube shi , yace ya akayi ne d'an baba , ya fad'a ya sauraronshi," baba dama gaskiya ina sonta kuma so nakeyi na aureta ", tashin hankali Wanda ba'a sanya masa rana , ai inna Asabe ji tayi kamar zata mutu , kallon d'an uwan nata tayi taji me zai cewa d'an nasa " ah Masha Allahu ai hakan ma yayi lallai yayi kyau , ah abu a cikin gida " ita dai Asabe ta kasa cewa komai, shi kuwa bilya murna jin mahaifinsa ya amince , sosai suka yi hira har bayan la'asar kafin su fara shirin tafiya , ita dai Asabe abin duniya ya dame ta saboda tana tsammanin ta yi abin da ba mahalukin da zai so fatima amma ga wata sabuwa, ta aurar da d'iyarta ga d'an birni tana ganin ba wanda zai k'ara cewa yana sonta amma gashi mai kud'i daga birni ya zo yana sonta, sallama yayi mata tare da sanar da ita cewa lallai ta sanar da Fatima halin da ake ciki kuma ba dad'ewa za'ayi ba za'ayi bikin saboda tsananin son abin duniyarta ta kwantar da kai , ya sallameta da kud'i masu tsoka haka shima bilya ya bata najin dad'in cewar ta amince za'a bashi fatima, haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga k'auyen.
A cikin gida kuwa bayan inna Asabe ta shiga kasa zaune tayi ta kasa tsaye , ta saka wannan ta kwance wanchan , duk dai akan Fatima ne da batasan ta auri bilya saboda tasan suna da kud'i kuma batason ta shiga daula tana son tayi ta ganinta cikin tsanani, amma da ta tuna da waye bilya da irin halayensa ai sai ta godewa Allah dan ko ba komai Fatima zata k'unshi bak"'in ciki saboda auren mashayin giya da Neman mata bazai haifar mata da komai ba sai tashin hankali domin kuwa babu kwanciyar hankali , k'arshe ma dai ciwon zuciya ya kamata ta mutu , wannan tunanin da tayi ne ya bata k'warin guiwar tunkarar Fatima da zancen.
🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌸🌹
Da daddare bayan Fatima ta dawo daga tallan ta da ta saba , zuwa tayi ta iske Asabe a kishingid'e tana cin nama balagu da ta bayar da kud'i a siya mata wajen idi mai nama , duk kuwa a cikin kud'in da yayan nata ya bata ne , " inna sannu da gida , Fatima ta fad'a had'e da rusunawa tana mik'a mata kudin cinikin da tayi " karb'a tayi ta k'irga su tsab daga bisani ta tura su k'ark'ashin tabarmar da take kishingid'e, har zata tashi ta zaunar da ita sannan ta fara yi mata zancen bilya da duk abinda ya ke faruwa sannan ta k'ara da cewa " kuma wallahi auren nan kamar anyi shi angama, dan na yanke ranar auren nan da wata d'aya mai zuwa za'ayi shi", gaban Fatima ne ya fad'i sakamakon wannan magana da innar ta ta tayi , da to ta amsa sannan ta juya ta shiga d'akinta cike da tashin hankali.
🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸
A cikin d'aki kuwa safa da marwa ta Shiga yi , tana tunanin yadda zata b'ullowa da lamarin, a gaskiya kota halin ya ya ne bazata tab'a yadda da auren wannan mutumin ba , zatayi duk mai yiwuwa wajen gujewa aurensa to ta ina zata fara , tayi zurfi a cikin tunani ta tuna da aminiyarta ta yarinta hannatu , aikuwa ta yardarwa kanta cewar lallai zata samu mafita bisa ga hukuncin da ta yankewa kanta , tana ta tunani har chan dare sai daga baya bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.
🌸🌹🌸🌹🌸🌹🌸🌹
Da asuba ta farka da Sauri ta gama aikin gida tsaf , ta gama abin da zata fita dashi tallah , sallama ta yiwa inna Asabe bayan tayi aikinta tsab sannan ta fita talla, Alhamdulillah ta siyar da wuri dan haka ta wuce gidan hannatu domin samun mafita , da take itama hannatun tayi aure shekaru biyun baya da suka wuce , a tsakar gida ta tarar da ita suka rungume juna cike da murna , sosai sukayi murna na ganin juna, bayan sun gama murnarsu sanan Fatima ta fad'awa aminiyar ta ta abin da ya kawo ta , sosai hannatu ta girgiza da jin wannan maganar , ta dubi Fatima cike da kulawa tace " Fatima nasan kinyi hak'uri , a yanzu bazan baki shawarar ki zauna a aura mini mashayin giya da Neman mata ba , dan haka yanzu meye mafita, nan Fatima ta shaida mata Cesar tanason ta tafi neman dangin mahaifiyarta , hannatu ce ta k'arfafa mata guiwa na cewar hakan yayi indai tasan inda suke ta sanar da ita cewar mahaifinta kafin ya rasu ya sanar da ita garin mahaifiyarta ta , amma ita yanzu matsalarta guda rashin kud'i a hannunta , hannatu ta sanar da ita baza'a samu matsalar kud'i ba insha Allahu , haka su ka k'ark'are matsalar ta su haka ta tafi gida cikin farin ciki .
🌸🌹🌹🌸🌹🌹🌸🌹
Haka dai rayuwa tayi ta tafiya , cikin k'warin guiwa ga Fatima , na yarda ta samu damar zuwa Neman dangin mahaifiyarta , ko ba komai zata ga ko da hoton mahaifiyar ta ta , kuma ta sadu da sauran y'an uwa mahaifiyar ta ta, tana ta shirin barin garin , a yayin da inna Asabe a b'angarenta it a ma tana ta shirin biki ta sanarwa da kowa domin murnar da takeyi na cewar fatima zata shiga kabarinta ne , sosai fa takeyi shiri kamar ba bu abinda Yake ranta , bayan ta gama shawo kan y'an uwa malam iliya , da nuna musu alfanun yadda auren zai kasance , suka kuwa yarda da hakan har suke tunanin ma Asabe ai tayi hankali.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
A haka har satin biki ya shigo , yayin da fatima ta shirya tsaf da komai nata bayan ta karb'i kud'i wajen hannatu domin shiga mota yayin tafiyar ta wajen kakanninta.
Dangin ango sun kawo kud'in sadaki da kayan lefe , kaya sosai aka kawo duk da bak'in cikin da Asabe ke ji amma idan ta tuna yadda Fatima zata dawo sai taga ba komai bane ba , an fara biki yayin da Fatima take nuna musu ba abinda yake damunta .
A Daren ranar d'aurin aure mutane mata mata masu girki NATA aikinsu , Fatima CE ta lek'o ganin hankalin kowa yana ga aikinsa ya Sanya cikin sand'a ta juya ta d'auko duk wani kaya da zata buk'ata da kud'in da k'awarta ta bata , lallab'a ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba ta nufi k'ofar gida, tana tafiya kuwa ta had'u da mai mashin godiya tayi ga Allah duk da a lokacin bata kawo cewar zata samu abin hawa ba saboda dare yayi sosai , ta tsareshi had'i da fad'a masa tashar motocin garin zai kai ta , ya amince ta hau bayan sunyi cinki ta yarda , basu zame ko ina ba sai tasha , tana zuwa kuwa tayi sa'ar samun direban na k'ok'arin tashi Dama sauran mutum d'aya Duke jira aikuwa tanajin motar zariya ce da Sauri ta fad'a bayan ta sallami mai mashin d'in da ta hau , da take tafiyar ta dare ce babu wuya suka bita daga cikin k'auyen suka cilla babban titi , sai a sannan Fatima ta saki dogon numfashi samun nasara .......
Please
Share
&comments
To be continue........
🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA , DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTUN LITTAFIN NAN , TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD, DA ALIHI DA SAHABBANSA MASU GIRMA.
BAYAN HAKA NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA D'AUKACIN Y'AN UWANA NA SABON RUWA'S FAMILY, LUV U ALL🥰🥰
AJUJI'S FAMILY KUMA HAR DA KU BAZAN MANTA DAKU BA , JINJINAR BAN GIRMA GAREKU ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI , AMIN🥰🥰
MAHAIFIYATA ALLAH YA JA DA RANKI , HAJIYA FATIMA TURAKI ADAM , LUV U MY MOM❣️❣️
KISHIYAR UWA FAN'S NA GAISHEKU SOSAI DA SOSAI.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹
🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹
🌸🌸
🌹
SHAFI NA 15-16
A haka sukayi tafiyar kusan awa d'aya da rabi kafin nan su isa cikin garin zaria, bayan an karb'i kud'in motarsu , kafin nan suka k'arasa garin zaria, bayan an Shiga cikin tasha a lokacin kusan k'arfe ukun dare , mutane suna ta sauka daga motar yayin da Fatima tana chan ta shiga duniyar tunani bata ma san an k'arasa cikin tashar ba , direban ne yana k'ok'arin juya motar domin komawa ya k'ara d'ebo wasu fasinjojin , juyawar da zaiyi ya hangota a zaune tana tunani , "baiwar Allah direban ya fad'a ya d'an dukan saman kujerar" firgigit ta farko daga duniyar tunanin , sai a lokacin ta farga da cewar lallai fa sun isa garin zariya , " ki sauka anzo fa , ya fad'a had'e da nuna mata wajen da sauran mutanen suka fita, tsimmokaran kayanta ta d'iba sannan ta sauka daga motar , tana k'ara rik'e kayan nata, shi kuma direban ya juya da motar ta sa bayan ya sauke dukkan fasinjojin, domin komawa , sai a lokacin Fatima ta fara tunanin ina zata shiga , waye ta sani a garin zaria ita yanzu ya ya zatayi , sai a sannan ta ji tsoro ya kama ta , ga dare ya yi gashi cikin tasha ne ga mutanen da suka zo da su duk kowa ya kama gabansa , gefe ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu kafin gari ya waye tasan nayi , mutane taga suna gilmawa kamar walk'iya , tsoro ne ya kama ta , d'ago kanta tayi aikuwa taga sun yi mata rumfa , irin yan iskan cikin tasha ne , wani gabjeje ne ya yi magana cikin kakkausar murya , yana mai nuni da ita ," ke me kikeyi a nan ya fad'a yana k'walalo idanu " kakkarwa jikinta ya fara yi , tsoro sosai ya shige ta , " magana ake yi miki ba , wani ya fad'a daga cikin wad'annan y'an mutane , " kaga rik'emin ita kawai kagani babban nasu ya fad'a , chafka d'aya daga cikinsu ya kaimata da sauri ta zille ta fara ihu ga babu mai taimako, gudu take yi suna bin ta a baya har suka fita daga cikin tashar suna bin ta a baya, sosai takeyi gudu har ta hau kan babban titin garin basu daina bin ta ba, ga babu mutane sosai kowacce mota kawai wuce was takeyi , a lokacin Fatima ta gaji lik'is tana neman fad'uwa , tsautsayi ya sanya tana k'ok'arin tsallaka titi mota ta d'ebo da gudu aikuwa ta kwasheta , k'arar da ta saka ne ya sanya wad'annan mutanen suka juya da gudu suka koma idan suka fito , da sauri mai motar ya fito daga cikin motar ya k'arasa inda ya ga yarinyar a kwance hasbunallahu ya furta ganinta da yayi cikin jini ko motsi bata yi , a cikin zuciyarsa ya fara tunanin to me ya fito da wannan yarinyar cikin wannan daren ganin tunanin bazai kai masa ba ya sanya ya d'auke ta da Sauri ya nufi cikin mota da sauri gashi dare yayi a haka ya tada motarsa ya figa da gudu kasancewar yana Sauri ne dan haka madadin ya kaita asibiti kawai sai ya wuce da ita cikin garin Kaduna ya bar zariya da ita kasancewar gaba ki d'aya ya gama rud'ewa .
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Sai ana kiran sallar asubah sannan su ka k'arasa , asibitin cikin garin ya wuce da ita saboda yana da amini Dr Sadeeq, tun kafin su k'arasa ya sanar da shi halin da ake ciki, dan haka suna isa ya tarar da nurses suna jiran isowarsa ciki kuwa harda Dr Sadeeq din , da sauri aka d'orata akan gado aka shiga da ita cikin asibitin , shi kuwa mutumin da ya kad'eta kwata kwata ya rasa nutsuwarsa , ya kai ya kawo haka ya dinga yi " haba Ahmad kayi a hankali mana ko sai ka jawowa kanka wata matsalar , Dr sadeeq yayi furucin yana duban abokin nasa , " girgiza kai kawai Ahmad yayi saboda bayaso ya zama sanadiyar salwantar rayuwar wannan baiwar Allah , " bakasan me nake tsoro ba sadeeq , wlh ina cikin tashin hankali bansan me zanyi akai ba idan yarinyar nan ta rasa rayuwarta ta sanadiyya ta , Ahmad ya fad'a kamar zaiyi kuma , " d'aya daga cikin likitocin asibitin ne ya fito kasancewar Dr Sadeeq ya tsaya wajen abokin na sa domin kwantar masa da hankali ," a gaskiya yarinyar nan ta auna arzik'i amma mun samu ta farfad'o daga doguwar suman da tayi ,Dr Khalil ya fad'a yana duban Dr Sadeeq"," yawa Dr sannu da k'ok'ari min gode fa " , " ah ai babu komai ai maigida Ahmad ai namu ne Allah ya kiyaye gaba ", suka amsa da amin a tare , sai a lokacin ne Ahmad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya , Dr Sadeeq ne ya dubi Ahmad , " am abokina ya akayi ne al'amari irin wannan ya faru" a take Ahmad ya bawa Dr Sadeeq labarin yadda abin ya faru tun daga farko , sannan ya k'ara da cewar hasalima ina sauri ne saboda laila na sanarda ita cewar zan dawo a yau daga kano shiyasa ", " amma baka tsammanin iyayen ta zasu nemeta , Dr Sadeeq ya fad'a yana duban Ahmad ," nima haka make ta tunani amma komai ma in ta farka zamuji" daga haka suka cigaba da hirar abinda ya faru.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Sai da akay kiran sallah sannan suka tashi daga hirar suka nufi masallaci , domin yin sallah har suka dawo daga sallah Fatima bata farfad'o ba, dan haka Ahmad ya bar Fatima a hannun Dr Sadeeq ya nufi unguwarsu dake cikin wata GRA dake garin Kaduna.
🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹
Tangamemen gate mai kalar ruwan madara masu gadin gidan su ka bud'e , hancin motarsa ya danna cikin gidan, ma'aikatan gidan sai kai kayo sukeyi , masu ban ruwa suna ta bawa furanne ruwa , duk inda ya gifta masu aiki na ta gaida shi yana amsawa cike da fara'a akan fuskarsa duk kuwa da cewar a zuciyarsa ba haka bane ba saboda yana tunanin me zai tarar a cikin gidan uwa uba kuma Fatima dake gadon asibiti.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Shin wai meke faruwa ne a chan k'auyen Darki ne bayan Fatima ta baro 'yan biki da inna Asabe?
Ana ta aikin biki har safiya tayi , inna Asabe ta shiga cikin rububin mutane , hakan bai Sanya an farga da cewar amarya ta gudu ba har sai da hantsi ya fara fitowa ana ta shirye shiryen d'aurin aure ganin har wannan lokacin Fatima bata fito ba ya sanya inna Asabe ta aika Abu da ta kirawo mata Fatima domin ta shirya saboda an kusa fara d'aurin auren , a lokacin Abu nada juna biyu dan har ya fito sosai , lek'awa tayi cikin d'akin cike da gatsali " dalla chan ai saiki fito banza kin wani zo kin zauna a d'aki kin bar mutane , " shiru taji dan haka cike da bala'i ta chusa kai , wayam ta gani dan haka ta fito da gudu ta nufi d'akin inna Asabe..........
Please
Share
&
Comments
To be continue........
🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹
🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA MASOYA LITTAFIN KISHIYAR UWA.
SHAFI NA 17_18
D'akin Inna Asabe ta nufa ko sallama babu," ! Inna , ta kwad'a mata kira da k'arfi , juyawa Asabe ta yi ," ke lafiya" , ta tambaya ta mik'ewa tsaye, " inna fa Fatiman ba ta nan fa" wani ihu inna Asabe ta zuba , tana duban mutanen d'akin da su ka zuba mata idanu, Abu fa kamar wasa k'aramar magana ta zama babba , tun kafin mutanen wajen y'an d'aurin aure su hallara ake nemanta duk inda aka san za'a ganta an nemeta amma shiru , nan fa aka ba za ma ko Allah zai sanya a ganta , amma shiru , lokacin da iyayen ango su ka zo aka Sanar da su , sosai hankalin ango ya tashi na b'atan amarya Fatima , aka yi nema aka gaji hakan ya sanya aka hak'ura da d'aurin auren aka ba ri sai an ganta tukunna , zancen fa ya cika k'auyen Darki na cewa Fatima ta gudu, wad'ansu na cewar dama bariki ta ke yi shi ya sanya zaman k'auyen ba zai yi mata ba dole ta shiga duniya , haka dai aka hak'ura duk da cewar y'an uwan marigayi malam Iliya sun koka na rashin Fatima amma suka hak'ura, wannan kenan.
KADUNA STATE
Lokacin da Ahmad ya isa k'ofar falon , thumb print ya danna , aikuwa a take k'ofar ta bud'e , shiga yayi da sallama , masha Allahu wani tangamemen falo ya bayyana , ga sanyi Ac da ya gauraye wajen , a d'aya daga cikin kujerun d'akin , wayar shi ya d'aga ya k'ira daga chan aka d'aga "haba habibty gani fa na dawo ina falon k'asa , kuma wallahi na gaji ," daga chan b'angaren aka yi magana , ban san me a kace ba na ga ya b'ata fuska , ya kashe wayar , kai shi ya zai yi wajen ba dad'i cikin gida ma haka , "Allah ka duba lamari na, ya fad'a yana duba k'afar bene , wata mata ce take saukowa daga ganinta kasan hutu ya ratsa ta akalla ba za ta wuce Ashirin da bakwai ba a duniya , sosai tayi kyau ba k'arya , ba ta da tsayi sosai amma fara ce , anyi mata kitson attach ya zubo har kafad'a , daga ganinta kasan idanunta sun bud'e da duniya, ' LAILA ' kenan uwargida wajen Ahmad , " haba Laila kina sa ne da cewar jiya mu ka yi zan dawo ai kya kirani ki ji me ya tsayar da ni amma kika yi ignoring nawa, kamar ba mijinki ba haba Laila, ya fad'a yana dubanta ", tab'e bakinta tayi " haba my luv ka san dai nima banda time ko saboda ka ga nima na fita aiki , " kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya rasa meyasa kwata kwata LAILA bata damu dashi ba yana matsayin mijinta , ganin ba za ta tambayeshi meya faru ba ya sanya ya fara fad'a mata abin da ya faru da shi , "uhmmm Allah ya kiyaye" kawai ta ce sannan ta juya ta fita a d'akin , girgiza kanshi yayi sannan ya tashi ya shiga band'aki , wanka yayi sannan ya shirya yana fitowa falo wayar shi tayi k'ara dubawa yayi ya ga Dr Sadeeq ne ya kira dan haka ya d'aga cikin hanzari , sallama yayi , aka amsa tachan d'aya b'angaren ," ok to gani nan zuwa , kawai ya fad'a ya nufi saman d'akin LAILA , ya na bud'a d'akin ya hango ta akan bed tana charting, sallama yayi mata bata amsa ba , kawai ta d'aga mishi kai , juya wa yayi ya fita had'e da girgiza kansa , harabar gidan ya nufa sanye da yadi d'an Abba kalar sky blue da hula zanna bak'a , da sauri direba ya taso, girgiza masa kansa yayi alamar ba tare zaku fita ba hakan ya sanya ya koma kan bencin baba