Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
duk nasa ne , kuma daga tsatson da yafi so , ba shakka yasan Allah kad'ai zai sakawa Fatima amma ba dai shi ba. Tausayin yaranne ya kama shi, saboda rashin imani , lokacin fitowarsu duniya baiyi ba amma tsabar zalunci sai da aka sanya yaransa suka sha wahala, ya k'udurtawa ransa cewar wallahi kome ake ciki sai ya gano Wanda ya yiwa matarsa haka, kuma yaso kassara masa gudan jininsa. Tunawa yayi da Mummy hakan ya sanya yayi dialing number na ta , aikuwa bugu d'aya ta d'aya ta d'aga, cikin hanzari ya fara sanar da ita abinda ya faru kama daga dukan da akayi mata , zuwa haihuwar da tayi, sosai mummy ta firgita da jin labari , sunan asibitin ya fad'a mata sannan ya kashe wayar . A nan kusa da hospital d'in ya fita ya jibgo uwar siyayya , na kayan baby da wanda mamansu zata sanya, bayan kuma akwai a gida . Ko da ya dawo ya tarar har lokacin suna bacci , cikin kulawa so da k'auna ya k'arasa kusa da Fatima da ke kwance kamar matacciya, anyi mata dressing na wajen da su LAILA su ka dake ta, sanadiyar allurar baccin da likitoci suka mata ya sanya har a time d'in bata farka ba , domin ta samu hutu. D'aya bayan d'aya ya d'auki yaran hassan da husain, kasancewar nurses d'in sun gama banbanta masa su kowa an lik'a masa sunansa a saman hularsa, Hassan ya d'auka ya masa hud'uba da mahaifin Fatima wato Iliyas ,sannan ya d'auka Hussain ya masa shima kiran sallah da hud'uba ya sanya masa sunan mahaifinsa wato Muhammad, sannan ya jera mata su a kusa da ita . Hoton yaran ya fara d'auka , sannan yayi posting through WhatsApp, Facebook, Instagram, Twitter da sauransu, aikuwa kan kace me ana ta masa murna Allah ya raya , kiran mummy ce ta shigo wayarsa , hakan y sanya cikin Sauri ya d'aga , ta sanar masa da cewar tana parking space driver ya kawo ta, aikuwa koda ya k'arasa suna tsaye ya musu jagora har zuwa cikin d'akin da suke, sosai hajiya taji dad'in ganin yarinyar ta ta da jikokinta cikin k'oshin lafiya , d'aya bayan d'aya ta d'auka , a nan ya sanar da ita sunan da ya sanya musu , taji dad'i sosai . Kafin kace kwabo asibitin ya cika da y'an barka , kowa sai sam barka , cikin y'an barkan harda aunty Aisha da Halima k'awar Fatima sai tsiya su ke mata, ita dai Fatima sai murmushi take musu, tana tuna fuskar bak'uwar aunty Aisha, tabbas itace wadda a gabanta LAILA a wanchan karon ma ta illata rayuwarta , kenan a wannan karon ma ita ta kawo LAILA cikin gidan ta kenan , sosai ta shagalta da tunani, daga baya ta yanke hukuncin bazata sanar da kowa ba , zata ajiye abun a ranta, kawai ta barsu da Allah , saboda duk wani abu da ya faru da ita ba kowa ne ya janyo mata shi ba sai KISHIYAR UWA, amma ba yadda zata yi haka zata daure. LAILA Achan b'angare guda kuwa, LAILA ta cigaba da lallab'a Aliya akan cewar ba abinda zai faru, ta kwantar da hankalinta, ko yarinyar mutuwa tayi , ba wani abu tunda ba Wanda ya gansu sosai suka shagalta da hira, LAILA sosai tayi murna dan ganin cewar tasan ma Fatima k'arshe sai mutuwa saboda a yadda suka baro ta , kallon Aliya tayi had'i da cewar" kinga Aliya ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru inshaAllahu kinji ko, kuma nasan yarinyar nan shegiya mayya k'arshe ma dai sai kabari saboda ta jigata da yawa, tana magana tana k'ok'arin bud'e status d'in da Ahmad ya d'auka , wani uban ihu da zunduma had'i da ashar ",Aliya dake zaune ta mik'e dama a firgice take saboda tsananin tsoro sai a yanzu take danasanin sanarwa da LAILA , dan batasan LAILA zata iya yin haka ba "," zo kiga", kallan fuskar wayar tayi jarirai ta gani twins duk maza, kuma kamar su d'aya da Ahmad, bata tsinke da al amarin ba sai da ta karanta comment d'in da yayi a k'asan yaran ,a tare su ka furta " mun shiga uku , dama bata mutu ba" ai a hanzarce Aliya ta had'a yanata yanata ta bar gidan cike da tsoro da tashin hankali, ta bar LAILA ita kad'ai tana zulumi , shikenan asirinsu ya tonu matukar yarinyar ta ta shi to ba makawa ita zata fara ambata , matuk'ar aka tambaye ta Wanda ya aikata mata wannan d'anyaen aikin. After 1 week Sosai Fatima ta warke sai abinda ba'a rasa ba , ranar aka sallame su , aka bar bikin sunan wani satin , yaso abar masa Fatima a gidanta amma fafur Mummy tak'i wai ita zata kula da yarinyarta da jikokinta , haka ya hak'ura badan ya so ba saboda yana buk'atar matarsa a kusa da shi amma ya k'yale, Halima kusan kullum tana gidan domin duba mai jego da yaranta , haka a b'angaren LAILA duk wannan abun da akeyi bata tab'a zuwa ganin jarirai ba , kuma ba Wanda yabi ta kanta , har da shi uban gayyar domin shi a yanzu ta lafiyar uwar yaransa yake yi. RANAR SUNA. Sosai Fatima ta samu lafiya , ranar suna yara aka rad'a musu sunansu da kowanne yaci , anyi bajinta iya bajinta , sa aka yanka da raguna kowanne yaro biyu, an ci an sha , an raba kayayyaki , mejego tayi kyau k'arshe, ina daga gefe ba sai na hango Queen nersmerh tawo da tawagar y'an moonlight writer's, su Mrs breaker ana ta k'alala idanu , an sha atamfar roba , su latifa sai bud'e idanu akeyi anaso a hango Ahmad , ni kuwa na b'uya saboda banaso su ganni , ballantana su saka ran zan samo musu abinci. Chan tawagar KISHIYAR UWA FANS su ma suka hallara, duk cikin su sis fareeda ce kawai sai sis humaira suka ci kwalliya , Dan haka na ja su gefe na zuba musu abinci , su kuwa su Queen na barsu da yunwa.🤪🤪. Toh Alhamdulillah, a haka taron suna ya watse bayan an raba gifts sosai, aka tashi , aka bar me jego da yaranta, Mummy na kula da su , sosai yaran suna wayo kai baa ce y'an wata bakwai bane ba, a haka suka cigaba da zama har sun kusa wata d'aya. A chan b'angare guda kusa , sosai Ahmad ya sanya anayi masa bincike, akan Wanda ya shigar masa gida a ranar da Fatima zata haihu, shaidar farko da aka samu a wajen mai gadin da ke kallon gidan Fatima ne, cewar LAILA ce da k'awarta ko da wannan magana ta isa ga kunnen Ahmad , ya razana sosai kuma yak'i gasgata hakan , amma yanzu ya gasgata, kuma abu kad'an yake jira ya sanya a kamo masa su , ko ya koma gida baya nuna mata damuwarsa , kuma har lokacin kowa al amarin gabansa yake yi , bai sanar da ita har a lokacin Fatima ta haihu ba, ita ma bata nuna masa ta sani ba , ganin anyi shiru da zancen ya sanya daga ita har k'awarta Aliya suka saki jiki, aka cigaba da harka da samarin bariki. A b'angaren Ahmad, tun Fatima na kwana ashirin ya matsu ta koma , tun baya fad'awa Mummy yana jin kunyarta har ya same ta ya sanar da ita , amma fir tak'i, ko da ya tuntub'i Fatima da maganar ta shaidawa Mummy tana son komawa, k'in fad'a tayi , hakan ya hassala shi , domin yana buk'atar matarsa a kusa da shi da yaransa, sai ya d'auke musu wuta ya daina zuwa, ya maida kansa gun tabbatar da zarginsa akan LAILA, ya k'yale su , domin yanaso yaga iya gudun ruwan Mummy da Fatima. AFTER 2 WEEKS. A lokacin komai ya kammala na bincike , LAILA na zaune a falo tana shan ice cream aka k'wankwasa k'ofa , cikin gadara ta tashi ta isa wajen k'ofar tana tambayar ways , shiru aka mata , cikin fusata ta bud'e me zata gani y'an sanda , sun kusa bakwai maza sai mata mutum biyu , basu yi wata wata ba suka damk'i hannunta bayan sun bata shedar kamawa, sannan aka cilla ta bayan mota sai police station , ko da su ka k'arasa, tana ta so ta musu taurin kai aikuwa , ta sha jibga koni na tausaya mata 😩, DPO ne ya kira wayar Ahmad , ya shaida masa da cewar an kama LAILA tana hannunsu a halin yanzu aikuwa , yana wajen aiki amma haka ya tattara kayan aiki ya nufi office d'in y'an sanda. Ko da ya k'arasa sosai LAILA tayi mamaki, da jin cewar wai Ahmda ya sanya a kamata , to me tayi abinda ta fara tambayar kanta kenan , amma sai ta dake, ko da aka fara fad'a mata abinda ya fara ai daskarewa tayi , bata gama dawo wa daga cikin duniyar da ta shiga ba, taji saukar takarda fara a hannunta , bud'ewa ya bata umarnin tayi , aikuwa tana bud'ewa ta zunduma ihu , " Ahmad ni zaka yiwa haka , ni zaka saka sakin ma na wulak'anci har uku ", " shi ne abinda ya kamata da a yi miki, domin dama na gaji bazan iya zama da wadda zata ga bayan iyalina ba , dama na gaji da halinki, dan haka kije na sauwak'e miki , kuka sosai ta shiga rairawa , anan Ahmad ya tafi ya barta bayan ya shaidawa DPO akan itama k'awar LAILAN a kamo ta , sannan ya juya ya tafi yabar LAILA a hannun y'an sanda, ya kuma shaida musu cewar da an gama zasu wuce kotu.............. INA GODIYA SOSAI DA NUNA K'AUNARKU GARE NI , KWANA BIYU KUNJINI SHIRU, BUSY NAKE SOSAI , FATAN ZAKU YI ENJOINING NA WANNAN PAGE D'IN , LUV U FAN'S😍😍😍😍 Please Share & Comments To be continue............. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 47__48 Bayan ya tafi, y'an sanda biyu maza d'aya mace, suka jefa LAILA a cikin mota domin nuna musu gidan Aliya su cika umarnin DPO. Ko da suka k'arasa a lokacin Aliya na tsakar gida tana rufe d'aki kasancewar ta samu labarin an kama LAILA ya sanya ta yi sauri had'a kayanta tana k'ok'arin barin garin, ko da ta ga LAILA tare da y'an sanda , tuni hantar cikinta ta kad'a , zawo mai k'arfi ya kamata , amma basu barta tayi ba su ka jefa su a mota aka nufi office, a wannan lokacin sai da suka ci dukan tsiya , sun ma fita a hayyacinsu , sannan aka rabu da su, duk wannan al'amarin da yake faruwa , mahaifan LAILA basu sani ba haka ma Mummy bata sani ba , ya kyale su sai sun gama girbar abinda su ka shuka sannan zai saka a mik'a su kotu, saboda mutuk'ar Mummy ta sa ni shirinsa ya wargatse kwata kwata , haka ma iyayensu , hakan ya sanya yayi shiru da bakinsa. A chan b'angaren Fatima kuwa, daga ita har yaranta suna samun kulawa sosai a gurin Mummy, kuma suna kwana na talatin da biyar , hakan ya sanya ta shawarci Ahmad akan cewar Fatima tana yin arba'in za su tafi k'auye domin ganin gida tare da shaida musu al'amuran da su ka faru , sosai ya yarda da hakan shi ma addu'arsa bai wuce ya kalla wadda ta wahalar da matarsa ba , Allah kad'ai yasan hukuncin da zai d'auka akanta , ko da aka sanarwa da Fatima sosai tayi farin ciki dad'in dad'awa ta taji da mamanta za'aje , wannan kenan. A chan chaji office kuwa, su LAILA sun sauya kamanni sosai baka gane su Ba, musamman ita LAILAN wadda hutu ya ratsa fatarta , abin gwanin ban tausayi , Ahmad da kansa ya ga ya dace akan cewar ya sanar da mahaifinsu, ko ba komai ai yanzu sun gasu, wayar mahaifin LAILA ya kira ya sanar da shi , aikuwa cikin tashin hankali ya nufi office d'in , haka ma mahaifin Aliya , sosai ransu ya b'aci musamman baban LAILA a ganinsa wai an tozarta y'arsa , ganin hargagin da su ke yi masa a kai yana k'ok'arin haddasa masa ciwon kai ya sanya ya bar office d'in, ko da ya sanar da Mummy bata ji dad'i ba amma , kuma hakan da yayi shi ne daidai , ta yi addu'ar Allah ya k'ara kiyayewa. To da k'yar da sud'in goshi aka samu Ahmad ya hak'ura , akan kai su LAILA kotu , sai da aka kai ruwa rana , tin Fatima batasan me ya faru ba har ta sani , ta shaida masa ita kam ta yafe , ya k'yale su , wannan dalilin ya sanya ya k'yalesu . Ranar da suka cika kwana arba'in aka d'auki hanyar kano , da Mummy ,Ahmad, da maman Fatima , da ita kanta Fatima sai y'an biyu , ko da suka k'arasa garin da k'yar Fatima ta gane gidan na su , saboda ya tsufa ya lalace , babu duk wani kayan more rayuwa kamar da, tun daga tsayawar su mutane suka fara lek'owa , mata ta Katanga , su na ganin ikon Allah , d'aya bayan d'aya su ka dinga fitowa daga cikin motar , abin mamaki ya bani wa jama'ah ganin bak'in turawa suna shiga gidan Asabe , to ko laifi tayi , a nan tsaye mutane suna kallo su ka shigewarsu. Tsakar gida su ka tarar da wata tsohuwa ga tulin yara a gabanta , kuma da alama ba tsufan shekaru ba ne ba , kawai halin rayuwa ne , kallonsu ta shiga yi , domin ba wanda ta gane a cikinsu , daga cikin d'akin su ka jiyo maganar wata tsohuwa , " yanzu ke zainabu a haka zamu dinga zama da yunwa, ko fita bazaki yi ki barato mana abinci ba, ta fad'a tana shirin fitowa "," wallahi inna kinsan Ba bayarwa mutane zasu yi ba ,kawai mu zuba idanu mu gani, lah inna na manta kinga bak'i muka yi ", da sauri ta fito daga d'akin tana lalubar bango , Fatima da ke tsaye daskarewa tayi ganin wadda aka kira zainabu , kenan Abu ce ta koma haka, toh ina mijin na ta , duban ta ta kai ga inna Asabe innalillahi ta furta ganin yadda kamannin ta su ka sauya, ga makanta, oh rayuwa kenan duk gudunka iya ka abinda Allah ya sanya zaka tsaya toh fa anan zaka tsaya . Sosai Asabe ta shiga rud'ani jin Fatima ce ta zo har da miji da kuma yara, ai abun bai bata tsoro ba sai da taji mahaifiyar Fatima tayi mata bayanin ko ita wacece , sosai kuka ya kufce mata , " nayi nadama marar amfani , Fatima ki yafemin nasan na k'untatawa rayuwarki da yawa , amma ki yafe ni , komai da kika ga ya faru da ke nice sila, ta juya ga mahaifiyar Fatima, wadda imani ya k'ara cika zuciyarta ganin wai Asabe ce a wannan bigiren , nan ta shaida mata cewar ba komai ta yafe mata, shi kansa Ahmad Wanda ya k'udurci yi mata wulak'anci ai sai ya nemi bakin yi ya rasa. Kafin kace me gida ya cika da y'an uwa, Allah sarki har da baba Muhammadu, har kuka yayi, kuma yaji dad'in ganin Fatima da mahaifiyar Fatima, kowa mamaki ya kama shi ganin ashe dama Maimunatu bata rasu ba, sai da su ka sarara sannan , Fatima ta sulale ta nufi gidan rahina, sosai suka yi murnar ganin juna , sosai su ka yi hira sannan ta mata alkhairi , ta raka ta har bakin zaure , su ka gaisa da Ahmad sannan suka wuce........... Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 49__50 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ 'KARSHE💃🏻💃🏻 Bayan sun koma ne, baba Asabe ke zaiya ne musu duk abin da ya faru, har da abin da ya faru da zainabu , tace" yaron nan ashe ba d'an arziki bane ba , ashe da ake cewa ya samu aiki a kudu , ba aikin Allah da Annabi ne ya kai shi ba, bayan aikin da yake yi , harda neman mata, watan su d'aya ta fara fuskantar k'alubale a rayuwar aurenta, da abun yayi tsamari , haka zai shawo kayan mayensa, ya shigo ya mata dukan tsiya , ya kawo mata yan mata karuwai , da k'yar tayi haihuwa d'aya a haka sai da ta Haifa masa wad'annan yaran , ba abinci , kullum sai duka , da k'yar bayan haihuwar jaririn nan ta samu Allah ya sanya ya sake ta , gashi ba kud'in mota , haka nan mak'wafciyarta ta bata kud'i da wadanda tayi aikatau ta had'a ta nufo gida, shi yana chan yana shek'e rayuwarsa a chan, ta fad'a tana matsar hawayen namada ", da k'yar su ka lallab'ata tayi shiru, sosai su ka jajanta mata, a ranar suka koma Kaduna da zama, amma kafin su tafi sai da su ka ajiye musu alkhairai da dama , sannan Fatima ta bada kwangilar a gyara gidan na su , ta bawa baba muhammadu jari , sosai tayi rabon bajinta wa dangin na ta , ana murna da komai su ka tafi duk da sun so su kwana amma mummy tace zata zo na musamman ta kwana, sannan su ka koma Kaduna. A chan b'angare d'aya , bayan an saki LAILA da Aliya , sosai ta shiga harka da samari , ta had'u da wani saurayi , sosai rayuwarsu su ke yi, bai fada mata yana da cuta mai karya garkuwar jiki ba , sosai su ke mu'amalarsu , bata tashi farga da cewar ta kamu ba sai da ciwo matsananci ya taje wajen likita gwajin farko aka tabbatar mata da cewar ta kamu da HIV , kamar zata yi hauka su ka dawo da mummynta gida , rayuwa duk ta sauya mata , gashi mahaifinta yanzu karayar arziki ta same shi , haka dai ta k'arasa jinyar cutar ta tana karb'ar maganin gwamnati a asibiti. Fatima ta koma gidan ta , soyayya mai tsabta su ke zuba wa, kullum tana godewa Allah da ya sauya mata rayuwarta zuwa mai kyau, a yanzu ta gama karatunta tayi jarabawar k'arshe su na jiran sakamako , saboda kamfanin Ahmad da yake k'asar waje yana buk'atar cigaba ya sanya yayi tunanin cewar gwara su tafi da iyalinshi chan , domin ita ma ta cigaba da karatunta a fannin Medicine. A b'angare d'aya soyayya mai k'arfi ta ginu tsakanin doctor Sadeeq da Halima k'awar Fatima tun lokacin da ya ganta a sunan y'an biyu ya rikice mata, a yanzu dai an Sanya ranar aure sai dai fatan Allah ya sanya ayi da mu Amin. Bayan komai ya kammala , su ka fara shirin tafiya kasancewar komai , ya yi kyau game da result na Fatima , hakan ya Sanya ana i gobe zasu tafi su ka shawarci junansu akan su kai ziyara asibiti, su bada taimako aikuwa , sunyi abinda ya dace , suna k'ok'arin fita daga asibitin Fatima taji ana kiran sunanta, da sauri ta juya , wata ta gani mai kama da LAILA sai dai wannan bata kai LAILA komai ba saboda a iya sanin Fatima LAILA ta kere mata da yawa, " baki ganeni ba ko Fatima , LAILA ta fad'a tana k'arewa Fatima kallo dama shi uban gayyar wato Ahmad , Wanda ya rumgume Al hassan a kafad'arshi , yayin Al hussain yana kafad'ar Fatima , bayani sosai tayi musu sannan su ka gane , aikuwa Ahmad yayi saurin jan Fatima domin ya tsani ganin LAILA a rayuwarsa , Fatima ce ta bashi hak'uri su tsaya su fuskance ta, LAILA hak'uri ta shiga bawa Ahmad dama Fatima , ta fad'a masa duk abinda ta masa, kama daga samun cikinta har zubar da shi da ta dinga yi, sosai yaji bakin cikin abun amma daya tuna da yadda LAILA take sai ya godewa Allah da ya sanya jininsa bai fito ta tsatsonta ba , sannan ta nemi yafiyarsa, yace shi ba komai, haka ma Fatima , ta zayyane musu abinda ke damunta sosai su ka jajanta mata, su ka mata al' kairi sannan suka barta tana zubar da k'walla na abinda ta yiwa rayuwarta , da tuni yanzu ita ke da wad'annan zuk'a zuk'an yaran, haka tana ji tana gani su ka tafi su ka barta . Ana i gobe zasu tafi suka je suka yiwa Mummy sallama, dama sun je zaria sun yiwa maman Fatima sallama , da dare suka gama shirya kayansu tsab , tare da na yaransu. Washe gari da misalin k'arfe takwas na safe jirginsu ya d'aga sai England, a babban birnin London suka sauka , sosai rayuwarsu ta sauya , Fatima ta fara karatunta a babbar jami'ar k'asar, sosai shi ma Ahmad ya mai da hankalinsa kan aikinsa da kuma iyalansa , rayuwarsu gwanin ban sha'awa. Bayan wani dogon lokaci, wata mata na hanga tana ta fama da yara , " Mummy wallahi bani ne ba Al Hussain ne , wallahi ba ni na dake ta ba ,duk su ka fad'a a k'ok'arin su na kare kansu ", " to naji Fatima ta fad'a," zo nan habibty ki fad'amin waye ya dake ki, Ahmad da ke tsaye ya tambayi y'ar yarinyar wadda take ta zumb'ura baki gaba, haba Nusy ta fad'amin kinji " ," Daddy ba yaya Al Hussain ne ya dake ni ba ", " ah lallai zan gamu da shi , bari kiga , ya fara k'ok'arin tashi ya kamo su , k'ara su ka saka , suka rungume Fatima , ita ma ta rungume su , yana zuwa da Nusaiba a hannunsa aikuwa ya had'e su gabaki d'ayansu yana dariya , tare da basu sumbata kowannensu a kumatu , yana mai jin dad'i da Allah ya azurta shi da iyali masu aminci. TAMMAT BI HAMDULLAH ANAN NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN " KISHIYAR UWA ", KUMA INA FATAN KUNJI DAD'INSA KUMA ZAKU YI AMFANI DA ABINDA KUKA JI MAI KYAU SANNAN KU WATSAR DA WAD'ANDA BA SU DA KYAU . INA GODIYA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, DA WAD'ANDA SUKE YIMIN EDITING NA BOOK D'IN NAN. INA GODIYA GA Y'AN KISHIYAR UWA FAN'S, ALLAH YA K'ARA MANA ZUMUNCI AMIN. JINJINAR BAN GIRMA GA SIS HUMAIRA DA SIS FAREEDA , KUNYI RAWAR GANI SOSAI ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI AMIN. NA SADAUKAR DA LITTAFINA GABAKI D'AYANSA GA , MAHAIFINA DA MAHAIFIYATA , ALLAH YA K'ARA MUKU NISAN KWANA MAI ALBARKA AMIN INA GODIYA SAI MUN SAKE HAD'UWA CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA MAI SUNA " BAK'AR GABA" INA FATAN KAMAR YADDA KUKA BI WANNAN SHI MA WANCHAN A SANNU ZAKU BISHI DOMIN JIN SAK'ON DA YA ZO MUKU DA SHI . TA KU HAR KULLUM NUSAIBA MUSA SALEH SABON RUWA (NUSSAD) PLEASE SHARE AND COMMENTS 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download

Chapter 10 of 11