Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
" uhmmmm Mummy please anjima inason daughter ta ki ta rakani unguwa , ya fad'a yana kallon mummy don jin me zatace "," Ina zaku je banason ka koyawa yarinya ta yawo bazata je ba,", " please mummy ba dad'ewa zamu yi ba, da kai ta amsa alamar ta yarda sannan ya juya ya kalli Fatima dake zaune , "ki shirya bayan la'asar , kafin na dawo abinda yace kenan sannan ya juya fita ita ma ta tashi ta shigewarta d'aki domin cika umarnin yallab'ai, kuma malami a gare ta , wato Ahmad............ Please Share & Comments To be continue............. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 KU NA K'ARAMIN K'AIMI FAN'S, INA TARE DA KU NIMA, LUV U ALL 😍😍. SHAFI NA 29_30 Mummy kuwa, bi Fatima tayi da kallo , tare da wani k'ayataccen murmushi , irin na su na manya wadda ita kad'ai tasan ma'anarsa, sannan ta girgiza kai , ita ma ta mik'e ta shige cikin d'akinta. A b'angaren Fatima kuwa, tana shiga d'akinta wardrobe ta bud'e, tsayawa tayi tana duba kayan da zata sanya, rasa wanda zata saka tayi , saboda batasan inda za su je ba , sai da ta gama dube dubenta ,har ta mik'e zata kirawo mummy ta taya ta zab'ar kaya kawai sai ta hango wata marron color d'in doguwar rigar abaya , hakan ya sanya ta zaro ta , wadda taji stones kalar gold, sai siririn mayafinta, jaka da takalmi ta zab'o su ma kalar golden da agogo, sannan ta fad'a wanka , ko da ta fito sai da ta gama zafa lotion mai k'amshi sannan ta zura kayan ta yane kanta da mayafin rigar , takalmi ta zura sannan ta rataya jakar ta ta, ta feshe jikinta da turaren "Al' oud Al khalij", sannan ta nufi falon, tana fita yana shigo wa, da idanunsa masu rikitar da ita , a zuciyarsa ya furta masha Allahu , k'arar bud'e k'ofar d'akin Mummy ne ya dawo da shi daga duniyar da ya shiga , sannan ya k'arasa cikin d'akin ya zauna, " Mummy barka da fitowa , ya ce da ita ", sannan ya dubi Fatima wadda ta mak'e a jikin bango kamar zata shige " mu je ko , abinda ya furta kenan sannan ya yiwa Mummy sallama ya nufi hanyar waje" , ganin haka ya sanya Fatima ta bishi cikin hanzari, mummy ce ta musu a dawo lafiya , bayan ta sanarwa da Ahmad kar su kai dare, da toh ya amsa mata sannan ya k'arasa ficewa, ko da su ka k'arasa bakin motar da kanshi ya bud'e mata sannan ta shiga , shima ya zaga ya shiga su ka bar gida bayan gateman ya bud'e musu gate. A chan b'angaren LAILA kuwa, tana zaune a falonta ita da k'awarta Aliya fire, cike da jin haushi Aliya ta dubi k'awarta ta " ni wallahi kina bani haushi, ta ya ya kawai daga ce miki , kar kije sai ki zauna yayi ta juya ki , wallahi ni banga namijin da zai juyani kamar waina ba, ta k'arashe maganar cikin masifa", LAILA kuwa sai kallonta take yi yayin da maganganunta su na k'ara shigarta," kinga Aliya bari naje nayi wanka na shirya, ai wallahi baza'ayi babu ni ba, haka kawai jirani in zo mu tafi , LAILA ta fad'a had'e da mik'ewa tsaye tana k'ok'arin hawa up stair na gidan da toh Aliya ta bi ta sannan ta d'auko wayarta ta fara kiran k'awar ta su wadda ta gayyace su birthday, domin ta sanar da su LAILA zata samu damar zuwa, ita kuma LAILA ta k'arasa hayewa saman benen. A chan b'angaren su Fatima kuwa, sai da suka yi tafiyar kusan minti talatin ba tare da kowa ya cewa d'an uwansa komai ba, chan Fatima ta dubi yallab'ai da ke aikin tuk'i " uhmmm wai har yanzu ba'azo ba , ta fad'a kamar ba ita tayi maganar ba ", " siyar da ke zanyi abinda yace kenan , yana k'ok'arin shigar da motarsa cikin wani katafaren wajen shak'atawa, da idanu kawai take bin wajen ba dai tsaruwa kam , kamar rak'umin da akala haka take bin sa, har su ka k'arasa wajen wani taro daga gani na manyan masu kud'ine a d'aya daga cikin jerin kujerun su ka zauna, kujerar d'an uwansa tana kallonsa, anyi decoration na k'ayatarwa a wajen , abokan nan Ahmad wad'anda su ka zo taro bikin zagayowar ranar haihuwar matar d'aya daga cikin abokinsu mai suna Muhammad lawan, ko wanne yazo suna gaisawa da Ahmad, suka dinga yi mishi tsiyar wai ya k'ara aure bai fad'a musu ba shi dai kawai dariya abin yake ba shi , sannan ya sanar da su ai k'anwarsa ce, a haka su ka dinga hira sosai Fatima ta bi dad'in had'uwa da wad'annan mutane masu karamci . A chan b'angaren su LAILA kuwa, sosai su ka gama shiryawa, cikin wani hamshak'in leshi , mai tsananin kyau ta sanya , ta sha uban takalmi mai tsini ta sanya siririn mayafi, k'asa ta sauka ta tarar da Aliya na zaune, kod'ata ta farayi sannan ta shiga d'aukanta a photo , sosai tayi ma hotuna , sannan su ka shiga mota suka nufi wajen birthday partyn . Sai da su kai kusan minti talatin , sannan suka k'arasa wajen , parking d'in motar LAILA ta yi, sannan suka nufi k'ofar shiga, a chan b'angare d'aya suka zauna , su ka fara hira da k'awayensu, chan wadda ake yiwa birthday d'in mai suna Ramlat ta k'arasa wajen su LAILA, da fara'arta ta isa wajen gaisawa su ka yi , sannan ta umarci LAILA da ta taso su gaisa da mijinta , da kuma babban amininsa , cike da karairaya ta tashi su ka nufi wajen domin gaisawa. A b'angaren Mummy kuwa , shiru taji dan haka ta tashi ta shiga safa da marwa a falon , wayar ta ta d'auka ta shiga kiran Ahmad, amma me bai d'auka ba sosai hankalinta ya tashi , ta zauna ta shiga zaman jiran dawowarsu. A b'angaren LAILA kuwa, tun daga nesa ta hango abokin mijin k'awarta ta , wanda take wa kallon kamar mijinta Ahmad , amma kuma ai wannan tare da kyakykyawar yarinya balarabiya ta ganshi, ni kuwa nace toh su LAILA an fara tsufa kenan😝, tana k'arasawa tana ganin kamanin wannan mutumin yana k'ara yi mata kamanin mijinta, sai da ta k'arasa wajen suka gaisa da mijin Ramlat, Ahmad da ke zaune kawai ya kalli LAILA k'warai ba zargi yakeyi ba LAILA ce matarsa , kawai kafe ta yayi da idanu, yana kallon ikon Allah , yanzu wannan itace matar da yake aure marabarta da masu zaman Kansu kawai d'aurin igiyoyin aurensa da ke kanta, ita kuwa LAILA jin kamar ana kallonta ya sanya ta juya domin ganin wake kallonta, k'walalo idanunta tayi sannan ta zunduma wani uwar ashar tare da fad'in " me zan gani , Ahmad wannan wacece a tare da kai , ta fad'a tana nuna Fatima ", sosai tsoro ya kama Fatima tayi wuri wuri da idanu, aikuwa jin sannan zagin ya sanya mutane suka jiyo suna kallonsu, ganin haukan da LAILA keyi ya sanya Ahmad ya daka mata tsawa , " aikuwa tayi ta kuwwa tana zagi , tana kururuwa, " Fatima koma chan kije ki zauna, ya fad'a yana nuna mata wajen zama", ai LAILA tana ji ta zunduma ihu , " shegiya , matsiyaciya , tsohuwar karuwa , wai dama kina mak'ale da mijina ban sani ba", ta fad'a had'e da janyo Fatima , ta wanchakalar da ita a gefe , kafin Ahmad ya zo ta kwashe ta da wani gigitaccen mari, juyawa tayi ta d'auko wani kofin tangaran ta sauke mata shi a kai , k'arar da Fatima ta saki ne ya janyo hankalin mutane dama shi kansa Ahmad d'in , akwai cikin hanzari , ya k'araso wajen ya wanke LAILA da wani azababben mari , wanda sai da taga taurari, kuwwa ta sake saki tana k'ara lalubar Fatima dan ta k'ara yi mata wata illar , k'ara kifa mata mari yayi, ya warb'ar da ita gefe, ganin Fatima tana kwance kamar ba rai a jikinta , ga jini da ya dinga zuba , aikuwa da sauri ya k'arasa wajen ciccib'eta ya nufi mota yana haki , saka ta yayi a mota sannan ya shiga ya tada ya fita daga wajen biki gaba d'aya , ya nufi asibiti hankalinsa a tashe. B'angaren LAILA kuwa , zube wa tayi a k'asa ta hau rusar kuka, had'e da dana sanin zuwa wajen birthday d'in, Aliya ce ta kamata ta mik'e suka nufi mota , saboda tsabar tashin hankali, ita ta tuk'a motar , yayin da LAILA take ta kuka , su ka fice daga gurin bikin, suka nufi gidansu LAILA , bisa umarnin da LAILA ta bawa Aliyar............. Please Share & Comments To be continue.................. 🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 HHHHH WALLAHI KUNA BANI DARIYA , FAN'S DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, HHHHH ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI AMIN🤣 🤣😍 BAYAN HAKA YAU YADDA KUKA SANYANI JIN DAD'I , NIMA ZANYI MUKU TYPING SOSAI DA SOSAI, FATAN ZAKU YI ENJOINING SOSAI, LUV U ALL. NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN GA MASOYAN LITTAFINA NA KISHIYAR UWA SHAFI NA 31-32 Ko da su LAILA da Aliya suka isa k'ofar gidansu LAILAN, horn sosai LAILA ta shiga dannawa, gateman d'in da sauri ya k'araso ya shiga kiciniyar bud'e gate d'in, kasancewar tsohon ne, hakan ya sanya duk ya rikirkice ya kasa bud'e gate d'in, aikuwa da sauri ta k'araso cike da masifa" dallah malam kana ganin zamu shiga sai wani salo salo kake yi ka gaza bud'ewa mutane, ta fad'a idonta na kan tsohon " yi tayi kamar zata bangaje shi ta nufi cikin gidan tana k'wallawa Mummynta kira, tana kuma rusar kuka, Aliya fire kuwa tana cikin motar a zaune da k'yar Baba maigadi ya bud'e gate d'in ta shiga da motar sannan ya rufe , ta rufawa LAILA baya itama ta shiga cikin gidan. Chan d'aya b'angaren kuwa, hajiya tana zaune ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi tayi kiran duniya Ahmad baya d'aga wayarta, gashi har k'arfe takwas na dare yayi, zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, hakan ya sanya ta kissima abubuwa da yawa a ranta, shed'an ya dinga yi mata wasi wasi a cikin zuciyarta, gashi ta kuma yi ta d'auka wayarta, i zuwa yanzu ta kira Ahmad ya kai sau kusan ashirin, amma still baya d'agawa, sake kira ta yi a karo na gaba , shi ma baa d'aga ba hakan ya sanya ta nemi guri ta zauna ta zubawa ikon Allah idanu , tana kuma jiran dawowarsu a koda yaushe. A b'angaren su Fatima kuwa, da gudu ya dinga tafiya kamar zai tashi sama, gani yake yi kamar ma yarinyar bata numfashi, hakan ya sanya ya k'ara k'aimi a tafiyar ta sa , yayin da hannunsa ke sak'ale a cikin na ta, ji yake yi Kamar ya zunduma ihu, amma ba shakka ya na kukan zuci , ya zaiyi idan aka ce yarinyar nan ta rasu, ina zai sanya rayuwarsa yaji sanyi lallai bazai yafe wa kansa ba, lallai idan har yarinyar nan ta rasa ranta ta dalilin LAILA wallahi sai yayi shari'a da ita , ko da duk abinda ya mallaka zai k'are ne ,a haka ya dinga tunani har ya k'arasa cikin asibitin, wanda da taimakon Allah ne kawai ya kai shi , nan wani asibiti mafi kusa ya kai ta saboda yana ganin idan har ya kai ta asibitin su Dr Sadiq lallai kafin ya k'arasa zata rasa ranta, ko da suka k'arasa , ganin irin ciwon da ta ji , jini duk ya b'ata mata jini, ya sanya likitocin suka ji tsoro, suka k'i karb'arta , sai da y'an sanda, hakan ya sanya ba shiri ya je police station mafi kusa da asibitin ya taho da y'an sanda guda biyu , suka yi cike cike sannan likitocin suka shiga da ita domin ganin ta hayyacinta, shi kuma ya nemi guri ya zauna, ya had'e kai da gwiwa yana sauraron hukuncin doctor d'in. Tun daga tsakiyar falon ta fara kiranta, cikin k'araji, Mummy! Mummy!Mummy!, haka ta dinga k'walla mata kira, cikin sassarfa ta k'araso, " ke me ya faru na ganku haka, ta fad'a tana duba LAILA, wadda ta fad'a jikinta , fashewa tayi da kuka kamar hakan ya k'ara tayarda hankalin Mummyn ta ta, ganin ba zata ce komai ba ya sanya ta juyata kalli Aliya" Aliya lafiya kuka shigo a hanrgitse , ta tambaya tana jiran amsarta, " k'arasawa Aliya fire ta yi ta fara zayyanewa Mummy k'arya da gaskiya, wani uban ashar da Mummy ta yi sai da LAILA ta d'ago da sauri ta kalle ta, cike da hargagi ta ke fad'in " lallai Ahmad ya cika cikakken marar mutunci, yanzu amma ke kina cikin wannan halin baki sanar da mu ba , wallahi ba abinda zai sanya ya dakeki ya zauna lafiya , sai munyi k'ararsa kotu , da k'yar su Aliya suka rarrashe ta, ta hak'ura , bayan tasha al washin sanar da mahaifin LAILA in ya dawo daga, tafiyar da yayi ita kuwa LAILA ta k'udurta a ranta sai ta ga bayan Fatima ko ta halin yaya ne ,Mummy ce ta kwantar mata da hankali, kasancewar tace mata zata d'auki mataki akan Ahmad dama kanta ita Fatiman , hakan ya sanya LAILA ta ji sanyi a ranta , da kuma ta tuna yanzu fa tana gida zata ci karenta babu babbaka, ni kuwa na ce sai ki taci ai bazai wuce tafiya yawo ba ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏😚, sai da suka kwantar mata da hankali , sannan suka tsunduma hirar duniya. ASIBITI Sai da likitocin da nurses d'in suka kwashe wajen awa d'aya da rabi akan Fatima , sannan ta farfad'o da wani matsanancin ciwon kai, sakamakon kofin da LAILA ta buga mata a tsakiyar kanta, sai da suka gama yi mata duk abinda ya dace kama daga wanke ciwo, suka d'inke mata wajen, lokacin da suka gama , su ka mata allurar bacci sannan suka fita, Ahmad da ke zaune, yayi zurfi a cikin tunani, wanda doctor na ta yi masa magana amma ya zurfafa sosai a cikin tunanin irin hukuncin da zai d'auka akan LAILA , tunanin da ya fad'o ma sa a rai ne ya sanya yayi murmushi Wanda ya fi kuka ciwo , toh fa fan's d'in yallab'ai gare ku, dan Allah Ku bincika mana me yake shirin k'ullawa😁😁, sai da likitan ya data shi sannan firgigit ya juya " doctor ya jikin na ta, ta samu sauk'i ko ya ya, ya yiwa likitan tambaya biyu a lokaci guda", " Alhamdulillah, tana lafiya, ta farfad'o zaka iya shiga domin ganin ta, amma dai ta samu bacci ya d'auke ta sakamakon allurar baccin da muka yi mata, Allah ya k'ara kiyaye wa", da amin ya amsa, sannan ya juya ya shiga d'akin da sallama a bakinsa, a kujerar da ke cikin d'akin ya janyo had'e da zama kusa da gadon, tana kwance , fuskarta tayi fayau da ita, hannunta ya kama ya murza a hankali , " Fatima ni ne sanadin fad'awarki a cikin wannan halin , ta ya ya zan iya yafewa kaina , a dalilina a karon farko kika kusan rasa rayuwarki, yanzu a dalilin mata ta, marar kan gado gaki cikin wani halin mai wuyar sha'ani, Fatima inaso rayuwarki ta zamato abar sha'awa ga kowa ta yadda duk wwanda ya kalleki bazai miki kallon k'ask'anci ba amma na gaza samar miki da farin cikin , ni wanne irin mutum ne wane iri ne ni, kuka ne yaci k'arfinsa bai ida k'arasawa ba, tashi yayi da ya tuna da cewar wayarsa na waje cikin motarsa, kuma bai sanarwa da Mummy halin da ake ciki ba , waje ya fita ya nufi motarsa , ko da ya d'auki wayar missed calls ya ganin rututu , yana duba wa ya ga Mummy ce, da hanzari ya d'auka dan yabi kiran sai ga wani kiran ya shigo , d'aga wa yayi had'i fad'in " Mummy LAILA ce , LAILA ce Mummy , fashewa yayi da kuka hakan ya razana hajia Amina ba kad'an ba" saurara Ahmad kamin bayani yadda zan fahimta, mai ya samu LAILAN, ta tambaya cike da zumud'in jin meke faruwa" , tsagaitawa yayi da kukan sannan ya zayyane mata duk abubuwan da su ka faru , salati Mummy ta sa ka sannan ta tambaye shi asibitin da suke , ya fad'a mata ta ce gata nan zuwa, da toh ya amsa ma ta sannan ya koma cikin asibitin. A b'angaren LAILA kuwa , ko da daddynta ya dawo , Mummynta ta sanar da shi , sosai ransa ya b'aci ita ma da yake uwar tsohuwar banza ce sai da ta k'ara da ta ta k'aryar bayan ta y'ay'an na ta, sosai ya yarda akan cewar LAILA ta zauna a gida , da shi a nashi ra'ayin ma Ahmad ya sakar masa yarinyarsa, ta yaya zaace yarinyar bata da ikon wata yawa a gidan aurenta said ya saka mata takunkumi, ganin LAILA ba ta yarda da cewar a sake ta ba ya sanya suka hak'ur, amma da sharad'in sai yaje da kansa shi Ahmad d'in sun ja masa kunne akan y'arsu, uhmmmm ayi dai mu ganu in tusa zata hura wuta😙🤨. A chan b'angaren Mummy kuwa sai da ta gama kammala komai da zaa buk'ata a asibitin kama daga kayan sanyawar Fatima abinda duk tasan d'iyar ta ta zata bukata, sai da ta d'aukar ma ta sannan ta shiga mota direba ya ja su ka nufi asibitin . ASIBITI Ko da su Mummy su ka k'arasa , a harabar asibitin su ka tsaya, waya ta masa , sanan ya zo ya tafi da su d'akin da Fatima take, sai da Mummy tayi kusan awa biyu sannan Fatima ta farka, da addu'ah a bakinta, fara tariyo abubuwan da suka faru tayi , k'wallace ya shiga zubo mata a kumatu , duk ta sanadin KISHIYAR UWA rayuwa ta take tangal tangal , duk da ina tunanin na samu hutu na gudo daga azabarta ashe ba haka bane ba , muryar Mummy da ta ji ne ya sanya ta saurin goge hawayen fuskarta ta k'ak'alo murmushin da yafi kuka ciwo , " sannu kinji daughter, Allah ya k'ara sauk'i , Allah ya baki lafiya ," da amin kawai ta amsa , ta koma ta lumshe idanunta , sai wajen sha biyu sannan Mummy ta sanarwa da Ahmad ya tafi gida ita zata kwana da Fatima , da yaso yayi musu amma kuma , sai ya kyale, ya shiga mota ya nufi gida. Mummy ce ta taimakawa Fatima tayi shirin bacci , sannan ita ma tayi , Fatima da tuni bacci ya d'auke ta , mummy ta tsaya kallonta lallai yarinyar tana cikin jarabawar rayuwa, kuma Allah kad'ai zai fitar da ita , k'ura mata idanunta tayi, Allah ya sanya hasashen da take yi akan Fatima ya kasance gaskiya ne amin, toh fa mummy ya ya dai wanne hasashe kuma🧐, ganin baccin Fatima yayi nisa ya sanya ita ma mummy ta nemi wajen kwanciya. 1:30am Har a lokacin ya gaza runtsawa , tunani fal ya cika NASA k'wak'walwa da zuciya, wallahi ba shakka sai LAILA ta game kurenta shi kad'ai yasan ko wanne hukuncin ya tanadar mata, zata gane tayi kuskure babba a rayuwart, sai wajen k'arfe uku na dare sannan bacci b'arawo ya sace shi , da zumud'in ganin gari ya waye, domin sanar da Mummy shawarar da ya yanke akan al amari. Washe gari ya so ya d'an makara dan sai 6: 15 am ya tashi a bacci, da sauri ya tashi yayi dallah , saboda makarar da yayi , bayan yayi wanka ya shirya , sannan ya nufi asibitin . Ko da ya k'arasa , takwas tayi , yana shiga bayan sun gaisa da Mummy , Fatima ta gaida shi ya amsa cike da murmushi a fuskarsa, sannan ya mata ya jiki ta amsa da sauk'i , ya juya hankalinsa gaba ki d'aya wajen mahaifiyar ta sa," hajiya, ya kira sunanta , kasancewar indai zai yi mata maganar da take da muhimmacine haka yake kiranta, amsawa tayi sannan ya kamo hannunta " inason a d'auramin aure da Fatima kuwa ba tare da kowa ya sani ba , zaro idanu Fatima tayi haka ma Mummy, sannan ta ce............. Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 FANS DAN ALLAH KUYI MIN HAK'URI, BISA GA JINA SHIRU NA KWANA BIYU , WANNAN DALILIN YA SAMO ASALI NE SABODA INA BUSY , AMMA INSHA ALLAHU NA DAWO DA K'WARINA , LUV U ALL MY FAN'S😍😍. SHAFI NA 33_34. Mummy ce ta kalle shi had'i da fad'ar" lafiyarka kuwa Ahmad , wannan wacce iriyar magana kazomin da ita ne wai , ta fad'a tana kallonsa da son jin dalili", sunkuyar da kansa yayi k'asa ya kasa cewa komai , ganin haka ya sanya mummy sassauta murya saboda ta gane fushi yayi," haba son ta yaya za'ayi wannan d'anyen aiki baka ga abinda ya faru ba da matarka da daughter, son Fatima yarinya ce, bazata iya kishi da LAILA, kuma ko ba haka ba Fatima makaranta take zuwa , yanzu ta soma karatunta kana ganin in aka katse ta anyi mata adalci, tambaya tana jiran ya bata amsa"," Mummy ni dai kawai hakan nake so kuma bana San a d'auki lokaci mai tsawo nan da wani satin in Allah ya kaimu ya kama ranar juma'ah kenan", mummy ce ta dube shi , har cikin ransa da gaske yake ya sanya ta saukar da murya naji NA amince , amma da sharad'i za'ayi bikin amma nan da wata d'aya tunda ka matsu ayi a hakan", Fatima dake zaune jin abinda mummy ta fad'a sai da cikinta ya bada wata k'ara k'uuuuuuu , shikenan za'a kasheta da ranta ya zatayi kenan , kamata yayi ace tun kafin ayi auren nan ta samu ta fece, duk da son da mummy take mata ya kamata ace ta barta ko ba dan komai ba sai son tasan halin LAILA, a yanzu ma da ta gansu a tare ta fara sabauta mata rayuwa ballantana kuma ace ta auri mijinta ai shikenan kuma sai dai ta kai ta lafiya, tana cikin tunanin nan taji Mummy na kiran sunanta , cikin sanyin murya ta amsa. " ina fatan hukuncin da muka yanke yayi miki,mummy ta fad'a tana kallon Fatima da son jin me zata fad'a", Fatima tsintar kanta tayi da amincewa Mummy ba tare da ta San ta amince ba , murmushi mummy tayi , a gaskiya har cikin ranta ta aminta da Fatima , kuma tasan zata yiwa yaran d'anta tarbiyya, shi kuwa Ahmad da ke zaune sosai ya shagalta da kallon Fatima, sosai yarinyar take burgeshi, shi kad'ai sai kaga yana murmushi , mummy ce ta taimaka mata ta yi wanka ta gyara jikinta sosai a gurin cin abinci ne ta so tayi gardama , amma da Ahmad ya had'e fuska ya koma yallab'ai na asali, sai ta amsa ta fara ci sai da taji kamar zatayi amai sannan ta jijjiga kanta hakan ya sanya mummy ta k'yaleta, ganin da mummy tayi kamar Fatima na jin bacci ya sanya ta taimaka mata ta gyara kwanciyarta ba dad'ewa kuwa baccin ya kwasheta , su kuma suka ci gaba da tattaunawar bikin, nan Ahmad ya shaidawa hajiya ai LAILA tana gidansu , sosai ta nuna b'acin ranta akan haka , tace ya je ya taho da matarsa, ya fad'a mata bai ma San ta tafi ba jiya ne bai ganta a gida ba da ya koma , amma zai je ya dawo da ita, ya kuma sanarwa da hajiya Dan Allah ayi komai cikin sirri, wannan kenan. A chan b'angaren LAILA kuwa , sun barbaje a falo ita da k'awayenta duniya ta koma mata sabuwa, ba abinda yake damunta, duk inda taga damar zuwa babu mai hana ta , hakan ya sanya take cin karenta babu babbaka, wata wadda suke kira da woman leader ce ta dubi LAILA a yatsine" wallah babbar hajiya kina bani mamaki , kamar ba LAILA ba, y'ar k'walisa, ki tsaya namiji yana b'ata miki rai, in nice ai wallahi sai na barshi , ko da shine autan maza"," ki kyaleta abinda nakeso ta gane kenan amma tak'i ta fuskanta , Aliya fire

Chapter 7 of 11