tsinci kanta a ciki , babu abinda ya gigita mahaifiyar Fatima sai labarin rasuwar malam Iliya mahaifin Fatima, tayi kuma sosai , sai da aka bata baki da nasiha sannan ta hak'ura ta dangana, a nan suka tsayar da zasu yi sati a nan , zasu kuma su bar Fatima wayen mahaifiyarta ta yi wata , duk da Ahmad bai so watan ba amma yana ganin in yayi adalci gwara ya hak'ura , haka kuwa akayi sun gama kwanakinsu, suka bar Fatima kasancewar anyi hutu dama, sosai suka dinga zaga dangi da ita aka nuna mata duk wad'anda bata sani ba , anan take tabbatar da cewa ita d'in y'ar dangi ce.
A b'angaren LAILA kuwa rayuwa ta bud'e musu ita da Aareef su ke cin karensu babu babbaka, yanzu kam LAILA ta zama y'ar hannu ba inda bata zuwa, maza kowanne iri bi take yi , sai dai kawai mu mata addu'ar shiriya.
ZARIA
Sai da Fatima ta cika wata d'aya , sannan aka fara shirin komawarta bayan mahaifiyarta ta gyara ta sosai, domin Ahmad ya sanar mata bata tare a gidansa ba , ya fad'a mata duk yadda suka yi da Mummy, ta kira yayarta ta , ta rok'eta akan ta barwa d'anta matarsa, sosai ta mata magana ta yadda zata fuskanta, kuma ta amince da hakan , dama ita tunaninta a bari a samu dangin Fatima kuma an samu sannan dad'in dad'awa tayi hasashen akwai dangantaka da Fatima shiyasa, ko da aka sanarwa da Ahmad sosai yayi far in ciki, ya kuma shiga hidimar gyaran gidan da Fatima zata zauna kasancewar ba gida d'aya zasu zauna ba, hakan ne ya sanya Ahmad bai lura da halin da matarsa LAILA ke ciki ba , baya ma da lokacinta , harkar aikin gidan Fatima kawai yake yi.
A ranar da ta cika wata d'aya tun asubah ya kama hanyar Zaria , karfe shida a k'ofar gidan ta masa, sosai ya ga ta sauya masa, tayi kyau saboda gyaran da aka mata, bayan sun gaggaisa , ya sanarwa da gwaggon na sa abinda ya kawo shi , duk da ya shaida mata tun jiya, tana son zama da d'iyarta amma kuma aure ya raba su, ita kanta Fatima bata ji dad'i da zasu rabu ba , a haka aka zuba mata kayanta a mota, suka yi sallama da kakannin na ta da mahaifiyarta, tana kuka ta shiga motar shima ya shiga ya ta da ta , bayan ya musu sallama, su ka d'auki hanya sai Kaduna............
Please
Share
&
Comments
To be continue.................
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
SHAFI NA 39_40
KADUNA
Ko da suka k'arasa Kaduna, gidan Mummy kai tsaye su ka wuce, Fatima jin ta take yi a wata duniya ta dabam , ko a mafarki bata tab'a kawo Mummy a matsayin wadda suka had'a dangantaka da ita ba, har su ka Shiga gidan , bata sani ba sai da Ahmad ya d'an bubbuga jikin kujerar sannan tayi firgigit ta dawo daga tunani" sai ki fito in kingama tunanin ", yayi murmushi ita ma murmushin tayi sannan ta fita.
A falo su ka tarar da Mummy , mamaki ne ya kamata , lallai Ahmad yanzu sai da ya je ya d'auko ta, ai ita tama manta yau ne ranar dawowar fatiman kai yaran yanzu ma sai dai a barsu kawai, gaisheta su ka yi ta amsa , sannan ta tambayeta mutanen Zaria , nan su ka shiga hira,Mummy ce ta kalli Fatima , "am daughter ki gama shirinki goben Allah ya kaimu , zaki tare a gidanki dan haka ki gama shirya komai", da " toh , kawai ta amsa , a sanyaye sannan ta tashi "Mummy bacci zanyi ", " OK , je ki kwanta nima bari na shiga d'aki ", da toh ta amsa sannan ta nufi d'akinta , ita ma Mummy haka.
Ahmad su ka bari a falo , yana ganin Mummy ta shiga d'aki yayi zuruf , kamar wani b'arawo ya nufi d'akin Fatima, a hankali ya tura k'ofar d'akin , tana kwance tana niyyar yin bacci, da yake ta juya bata ji shigowarsa ba , jin an zauna a gefen gado , tayi tsammanin ma Mummy ce, sai da k'amshin turarensa ya buge ta, sannan tayi saurin juya wa," am yallab'ai , me kake buk'ata, ta fad'a tana k'ok'arin tashi , tunawa da tayi irin kayan da ke jikinta ya sanya ta koma ta kwanta", sai da ya gama k'are mata kallo sannan ya rab'a gefenta ya kwanta, cikin zaro idanu tace " amma fa yau Mummy tana nan ", " ai na sani ba wani abu nace zanyi ba, bacci zanyi " ya fad'a yana k'ok'arin janyo ta jikin shi ," dan Allah yallab'ai Mummy fa tana nan ", " kar ki dame ni " , abinda yace kenan ya rungume ta, ita dai sai rarraba idanu take yi har bacci ya d'auke su , ko da Mummy ta fito ganin baya nan tayi tsammanin ya tafi sashensa , sai ta koma d'aki ita ma domin ta d'an matse bacci.
A chan b'angare d'aya , LAILA na hanga a zaune tare da wani saurayi , hannunsu a sak'ale da juna, banji mai suke tattaunawa ba, naga dai sai dariya suke shekawa, wa'iyazubillah , kamar ba matar aure ba, " wallahi Aareef kana ji da ni, irin wannan kyauta haka " , cikin dariya shi ma yace " ai in dai zaki dinga sanya ni farin ciki ba abinda bazanyi miki ba, fatana mu kasance har abada", da k'yar su ka rabu da juna , na nufi gida, sai a yanzu take danasanin yin aure , ashe abinda su Aliya suke fad'a mata gaskiya ne , ba komai a cikin aure sai nadama , da ace a lokacin Aareef ta had'u da shi da aurenta tafi jin dad'i , a haka ta shiga gida har a lokacin bai dawo gida ba abinci taci sannan ta haura sama domin hutawa, wayar hannunta ce tayi k'ara , ganin mai kiran ya sanya tayi dariya had'i da d'agawa, " lallai matar nan kin samu duniya kin manta damu ko, aka fad'a daga chan b'angaren ," ah haba Aliya wallahi guy d'in da na had'u da shi ne ya k'ure k'arshe , amma ban manta da ke ba , so ya gida ", daga chan b'angaren Aliya ta amsa, nan su ka ci gaba da hira cikin nishad'i , ita kuma LAILA tana bawa Aliya labarin Aareef, bayan sunyi sallama , ta kishingid'a bacci kuwa yayi awon gaba da ita.
A b'angaren su Fatima kuwa sosai baccin ya musu dad'i musamman ma Ahmad yaji dad'in baccin sosai, sai k'arfe kusan biyu sannan suka tashi, Ahmad ne ya riga tashi dan haka da azama ya nufi k'ofar falo Allah ya taimake shi Mummy bata falo hakan ya sanya ya tafi part d'insa , domin yin sallah.
Ko da Fatima ta tashi , ganin baya nan ta ji dad'i , hakan ya sanya ta shiga toilet domin yin alwala.
Ko da tayi sallah , kasa fita falo tayi gani take yi kamar mummy tasan Ahmad a tare su ka yi bacci da ita , a chan falo ganin Mummy tayi har lokacin Fatima bata fito taci abinci ba , "am baba na duba min kaga daughter ta lafiya , naga har yanzu shiru, ko gajiyar ce har yanzu", tashi yayi ya nufi k'ofar d'akin Fatima, da sallama ya shiga cikin d'akin tana zaune a bakin gadon tana ganin shi tayi zumbur ta mik'e , " ki je inji Mummynki , domin naga yanzu kin k'wace min fada ta", murmushi tayi kawai tayi hanyar waje shima ya bita, ko da su ka gama con abincin , sai ya zauna su ka dasa hira shi da Mummy, ita dai Fatima bata samu su baki kasancewar akan tariyar tata ake yin maganar , ganin abun na su yayi yawa ya sanya ta shiga d'aki ta barsu, sai wajen bayan magriba sannan ya tafi gida .
Ko da ya isa gida , bai bi takan LAILA ba ya nufi d'akinsa , kasancewar yayi sallah a masallacin gidan Mummy , ana shirin yin isha'i , ya nufi masallaci, ana idarwa ya dawo ,a d'aki ya zauna , aiki yayi sosai sannan ya kwanta , da farin cikin gobe ya war haka yana tare da Fatima a gida d'aya , ji yayi kamar ya janyo goben, a haka dai ya lallab'a yayi bacci cikin nishad'i.
A b'angaren LAILA ko da ta ga bai shigo ba, kuma taga dawowarsa hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba kasancewar tana charting da wani sabon saurayi da suka had'u a Instagram, sosai guy d'in ya tafi da imaninta, soyayya suke zubawa , kamar ba matar aure ba, a yanzu ma da shi suke chart, ko da yake sauran ma bata rabu da su ba , sai misalin karfe d'aya sannan ta kwanta bayan sunyi sallama..............
Please
Share
&
Comments
To be continue..........
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
SHAFI NA 41__42
Washe gari , tun asubah ya tashi , kasancewar akwai aikin da ba'a k'arasa ba a gidan Fatima, kuma ya bar masu aiki , zasu yi aikin kwana, da hanzari ya shirya, k'arfe bakwai daidai ya fita daga gidan bayan ya sanarwa da LAILA cewar zaiyi tafiya, kafin ya dawo ta shirya masa kayansa a jaka,da murnarta ta amsa har sai da yayi mamaki, kasancewar in dai zaiyi tafiya ta dinga k'orafi kenan , yana fita daga gidan ta shiga falo , had'i da lalubar number Aareef , kasancewar ya shaida mata lallai su had'u a yau , dan haka ko da ya d'aga da murnarta ta sanar masa shima yayi farin ciki, sannan ya fad'a mata inda zasu had'u.
A chan b'angare guda bayan ya k'arasa gidan ya tarar da komai ya kammala , saboda ya makara a office ya sanya bai biya gidan mummy ba sai dai ya sanar da ita amgama aikin, saboda ta shaida masa cewar za'a so jere, bayan ya gama sanar mata ne ya wuce office.
A chan gidan mummy kuwa, daga ita sai mahaifiyar Fatima sai kuma aminiyarta , wato hajiya sadiya, kasancewar ta sanar da su dalilin auren d'an nata ya sanya su ma suka yadda da hakan , sannan suka sanya albarka, su da kansu suka yiwa yarinyar ta su jere na gani na fad'a, komai masha Allahu, sai san barka, wannan kenan.
Fatima a zaune a d'aki, yayin da Halima k'awarta tana ta aikin lallashi, " kinga Fatima ki nutsu ki k'watarwa kanki y'anci, kinga dai yadda yanzu rayuwa take , wallahi da ni na samu ya Ahmad da wallahi yaga yadda ake tarairaya, , dan wallahi ko ita LAILAN zata yi mamaki , ki rik'e mijinki hannu biyu biyu , kinji na fad'a miki " , cikin sheshshek'ar kuka Fatima tace " Halima bazaki gane ba ina tsoron LAILA wallahi , saboda irin matan nan ne masu mugun kishi akan mijinta ba abinda bazata yi ba walllahi", " shi yasa na fad'a miki ki jajirce tunda yanzu matsayinku d'aya da ita , a da dai ke ba kowa bace ba amma a yanzu gaji y'ar uwa a gare shi kuma mata , ki sanyawa kanki salama", sosai ta mata nasiha yadda jikin Fatima yayi sanyi sosai ta yaddarwa kanta cewar zata iya , sai da ta ga ta saki jikinta sannan ta kira mai k'unshin da zata mata , dama an gyara mata kai dan haka aka fara yi mata k'unshin.
Sai k'arfe biyar sannan ya samu damar barin office, gida kai tsaye ya nufa, ko da ya k'arasa tarba ta musamman ya samu daga LAILA , yayi mamaki sosai amma haka ya biye mata , ya kammala komai , yadda a b'angaren LAILA ta matsu da tafiyar Ahmad haka shi ma ya matsu da ya tafi , har bakin mota ta raka shi , sai da ta tabbatar ya bar gidan sannan ta juya ciki domin fara shiri, cike da murnarta, hmmmmn LAILA kenan.
Yana k'arasawa bakin gidan, yayi horn mai gadi ya bud'e masa, ya shiga , a lokacin su Mummy sun gama jere sun tafi gida, tsayawa yayi ya jera kayansa a wardrobe sosai tsarin gidan ya burge shi , yana gamawa ya nufi gidan Mummy sakamakon kiranshi da tayi akan cewar yaje ya d'auki matarsa ,aikuwa cikin hanzari ya nufi gidan Mummy, uhmmmm sarakan azarb'ab'i kenan.
Ko da ya k'arasa a lokacin angama shirya ta , ba wani dad'ewa yayi ba , mummy tace su tashi su tafi dare ya fara yi , anan fa aka ga abu domin fafur Fatima ta tubure ba inda zata je, koni sai da na mata k'walla , haka ma mummy da k'yar aka lallab'ata ta shiga motar su ka fice daga gidan.
Ko a hanya ma , kukan ta cigaba da yi , yana sauraronta, duk da yana jin kukan har cikin ransa amma haka ya k'yale ta , a hanya ya tsaya ya siya gasashshiya kaza , da fresh milk sannan su ka nufi gidan .
A chan b'angare guda kuwa, LAILA , kwance akan gadon hotel d'in da Aareef ya kama musu, " wallahi baby kanaji da ni irin sannan garab'asa haka, ta fad'a tana duban Aareef da ke fito wa daga cikin toilet da alama daga wanka ya fito" ai baby kad'an ma kikq gani indai ni ne", murmushi tayi, sannan ta tashi ta fad'a jikinshi daga suka cigaba da aikata abinda su ka zo , wa'iyazubillah.
Ko da su ka k'arasa gidan , da kanshi ya mata jagora har cikin gidan, tana lullub'e da mayafi sai k'amshi take yi , a d'aya daga cikin kujerun ya mata masauki, sannan ya nufi cikin kicin da plate ya fito a hannunsa, ya shiga zuzzuba musu, sai da ya gama sannan ya mata umarni da ta sauka su ci tsabar yunwa ce ta sanyata dole ta sauka su ka fara ci duk da a takure take jin ta, bayan sun gama ya nuna mata d'akinta yace ta shiga tayi alwala , bayan ta gama su ka yi sallah , sannan akayi shirin bacci, toh nima daga nan na janyo k'afafuna na fice daga d'akin baki d'aya, saboda kar ace min nayi gulma, wata k'ara da Fatima ta saki ne ya haddasa ni ba shiri na fice daga gidan a miliyan, don tsabar abin tausayi.
Asubah ta gari amarya da Ango.
Ko da na koma lokacin komai ya wakana, Ahmad zaune a gefen gado yana aikin lallashi , ni kuwa nace tunda ka aikata kuwa sai kayi aikin lallashi , komai shi ya mata , sannan ya barta , tayi wankan tsarki, ya shimfid'a mata darduma , ya jasu sallah, albarka kuwa Fatima ta sha ta gurin Ahmad, gani yake duk duniya yafi ko wanne namiji dace , ya kurbu zumar Fatima daidai gwargwado.
Ko da gari ya waye a lokacin Fatima , zazzabi ya rife ta , Ahmad na zaune yana jinya , yaji ana k'wank'wasa k'ofa a hankali ya mik'e saboda kar Fatima ta farka daga baccin wahalar da take yi , yana zuwa ya ga mai gadin Mummy ne ya bashi basket d'in abincin sannan ya juya ya tafi , shi kuma ya koma cikin falo.
Sai k'arfe goma sannan ta tashi a lokacin ya sata tayi brush ya zuba musu abinci , kunun tsamiya ne sai k'osai sai farfesun layan cikin , da lallashi ya dinga bata , yayin da kunya duk ta addabeta , a haka su kayi kalaci , sannan ya bata magani su ka koma bacci.
A chan b'angare d'aya LAILA sai Washe gari ta koma gida , tare da kyautar da Aareef ya mata , aikuwa suna cikin sallama, da Aareef Allah ya jefo da Dr sadeeq , kasancewar ya kira number Ahmad , baya shiga saboda ko shi kansa bai San yayi auren ba , LAILA da ke tsaye bata lura da shi ba dan haka su ka gama duk abinda zasu yi sannan ta shiga gida , da matukar mamaki a fuskarshi ya juya da mota ya bar k'ofar gidan...........
Please
Share
&
Comments
To be continue............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸
( True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
SHAFI NA 43__44
Toh haka dai Ahmad ya kwashe kwana bakwai a gidan Fatima, suna kwasar amarci da soyayya, tun Fatima najin kunya har ta saba , ta sake tare da taimakon k'awarta Halima, sosai take wayar mata da kai, aikuwa tayi amfani da shawararta ta, sai da ya kammala kwanakinsa, sannan ya koma gidan LAILA badan ya so ba.
A haka dai zaman na su ya kasance cikin walwala, da soyayya, yayin da a b'angare d'aya kuma zaman LAILA da Ahmad, ba'a cewa komai, ita dai ta maida hankalinta ga samarinta yayin da a b'angare d'aya, shi kuma Ahmad yake samun wannan damar in kwanan Fatima ya zagayo, a haka su ka koma makaranta, taci gaba da karatunta, bayan ya shaidawa principal d'in makarantar akan cewar zata yi jarabawar gama secondary a aji biyun senior
Hankalin Fatima ya kwanta , sai Sam barka , suna wata na hud'u da aure Allah ya a zurta , zo kuga murna lokacin da Dr ya sanar musu da wannan sakamakon , wanda a wannan lokacin suna daf da fara jarabawa,sosai ya shiga kula da Fatima cikin so da k'aunar juna , tarairaya ba wadda bata gani, ita kanta idan ta zauna godewa Allah kawai take yi , dan ganin Allah ya sauya mata rayuwarta ta da , da jin dad'i , rayuwarta dai abar sam barka da kwatance.
A b'angare d'aya kuma, Mummy tawa Ahmad magana akan cewar tunda yanzu rayuwar Fatima ta sauya, kamata yayi ya kai ta k'auye domin ziyartar y'an uwanta , a kuma shaida musu duk al amarin da suka faru, sosai ya gamsu da haka, ko da ya koma ya sanarwa da Fatima abinda Mummy tace,tayi murna sosai, ya sanar mata da cewar ana gama jarabawarsu, za su tafi , harda mahaifiyarta.
Fatima a zaune a falo, yayin da cikinta a lokacin ya kai wata bakwai,sallama taji anyi hakan ya sanya ta mik'e da k'yar ta nufi bakin k'ofa kasancewar tayi nauyi, da fara'arta ta bud'e k'ofa," ah aunty Aisha barka da zuwa, wallahi tun d'azu nike jiranki ,ta fad'a tana kallon mak'ofciyar ta ta , wadda suka shigo ita da wata bak'uwa, " ke dai bari Fatima wallahi Aliya ce ta tsayar da ni, kinganta nan k'awata ce sai dai ita bata ji ko kad'an," harara r wasa Aliya ta jefawa Aisha, da sannan Fatima ta matsa musu suka wuce, zuwa cikin falon, da hanzari Fatima ta wuce, domin kawo musu ruwa, Aliya ce ta dubi Aisha cikin mamaki bayan ta yi nuni da hannunta zuwa cikin wani photo,wanda Ahmad ya rungume Fatima aka musu photo, sunyi bala'in kyau sosai kamar ka sace su ," Aisha wannan fa waye, ta tambaya cike da mamaki, " lah ai mijinta ne " , cike da mamaki Aliya ta kalle ta, miji kuma ," girgiza kai tayi sannan tayi shiru, ita kad'ai ta san me take k'issimawa a ranta, Ahmad mijin LAILA shine ya zama mijin wannan yarinyar gashi ma ta lura akwai rabo a jikinta, a hanzarce ta sha ruwan da ta k'agauta ta fita ta sanarwa da LAILA halin da ake ciki, ko da suka gama bata koma gidan Aisha ba ta wuce gidan LAILA.
Tun daga bakin falo take k'wallawa LAILA kira, a hanzarce LAILA ta sauko daga upstair, " haba Aliya ta yaya zaki shigo kina min ihu bayan kinsan ina chan ina hutawa ta"," dallah chan wanne irin hutu , kina hutu amma mijinki yana chan shima yana hutawa " ," bangane ba, ta fad'a tana zare idanu"," toh ki sani cewar mijinki ya k'ara aure ba tare da kinsani ba ", wata uwar ashariya ta doka " ni za'ayi was hauka lallai ma amma ta yaya aka yi kika san cewar Ahmad yayi aure kin tunanin zaiyi aure ba tare da cewar ya fad'a min ba ta fad'a cikin k'araji "," yau da idanuna ma na kalla matar Ahmad harda tsohon ciki "," tsohon ciki fa kika ce tabbas kuwa," , " Aliya rakani in ganewa idanuna domin dai na tabbatar da cewar kina min wasa ne ko kuma gaskiya kike fad'a min , cikin hanzari da tashin hankali ta nufi sama domin daukar mayafinta, sai da ta sauko sannan Aliya ta ja ta , suka nufi mota , Allah Allah LAILA take yi su isa aikuwa ko da suka k'arasa sunyi sa'a mai gadi ya jagaya masallaci , aikuwa cikin hanzari suka shiga , sallama Fatima taji ya sanya ta fito bak'uwar d'azu ta gani , gabanta ne ya fad'i ganin wadda suke tare, " aunty LAILA , ta furta da k'arfi ", LAILA ce ta zare idanu wa take shirin gani kamar wannan mayyar yarinyar nan , aikuwa d'aga idanun da zata yi taci karo da hoton Fatima tare da Ahmad, wani uban hanzari ta daka gami da finciko Fatima , wallahi sai na kashe yarinyar nan , hankali na zai huta, jibgarta ta shiga yi tun Fatima na kuka harsai da ta suma sannan suka k'yaleta , aikuwa jini ya b'alle mata ganin haka ya sanya suka yi shirin ficewa daga gidan.
Ahmad wanda tun yana zaune a office , yaji gabanshi yana fad'uwa, hakan ya sanya ya baro wajen aiki ya nufi gidan Fatima , a bakin gate ya tsaya yana horn, shirin da yaji ya sanya ya fita daga motar ya nufi cikin gida , tin daga k'ofar d'akin ya fara sallama , shirun da yaji ya sanya ya shiga ciki, a kwance ya hango ta , da Sauri ya k'arasa inda take kwance, jijjigata ya fara yi , d'aga ta da yayi ne ya kalli jini na kwance a k'asa , cikin zare idanu, ya shiga girgiza ta yana kiran sunanta," Fatima ki tashi, ki tashi karki mutu , karki mutu bazan iya rayuwa in babu ke ba , ganin haka bazai kai ba ya sanya ya d'auke ta ya nufi mota cikin hanzari ya ta da mota ya nufi asibiti da ita.
Su LAILA kuwa b'oyewa suka yi ganin motar Ahmad ta nufo cikin layin, sai da suka bari ya wuce sannan suka wuce , ta k'yar su ka k'arasa gida suna maida numfashi , bayan sun huta Aliya ta dubi LAILA , "amma kina ganin yarinyar nan bazata fallasamu ba kuwa, ni fa inajin tsoro wallahi ,", " ke ni fa bai dame ni ba Allah yasa ma ta mutu kowa ma ya huta ," " amma kuma idan Ahmad ya sani fa, Aliya ta fad'a ,"," wallahi ko a jikina, ki barmin komai a hannuna , haka dai su ka cigaba da maimaita abinda ya faru, yayin da LAILA zuciyarta fari fes akan abinda ya faru .
A hanzarce ya k'arasa asibitin ,a lokacin Fatima ta jigata , tsananin wahala ya sanya ta farka daga sumar da tayi , suna k'arasawa aka shigar da ita d'akin emergency, ko da likitocin su ka duba , suka gane cewar nak'uda ta kama ta, nan da nan aka shiga bata taimako dan ganin ta samu ta haife abinda ke cikinta, Ahmad da ke safa da marwa , zancen zuci kawai yake yi , lallai duk wanda ya jawa matarsa wannan iftila'in wallahi bazai rabu da duk wanda yayi sanadiyyar fad'awar Fatima cikin wannan yanayin har ya sanyata nak'udar dole, a hanzarce likitan ya fito gami da cewar congratulations, bayan ya mik'a masa hannu " matarka ta haifi yara har guda biyu ma'ana twins , cikin tsananin farin ciki ya ma rasa meke masa dad'i , yama manta da damuwar da yake ciki , ko likitan bai jira ya gama magana ba ya nufi cikin d'akin...............
Please
Share
&
Comments
To be continue............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
SHAFI NA 45__46
INA BALA'IN YINKU FAN'S, SADAUKARWA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, TARE DA KISHIYAR UWA FAN'S, 😍😍😍😍👌🏻💃🏻
A firgice ya bud'e k'ofar d'akin, a lokacin nurses sun gama gyara ta da babies d'in tsayawa yayi yana k'are musu kallo, yaran kamar ba bakwai ni ba , ganin su yake kamar a mafarki wai ace wannan