Share this page
2 / 8
Suka kori nana daga gidan ta dawo nan gidan mu da zama a wajen mu ta zauna inda Ammah ke faman dawai niya da ita da yarta sannu a hankali tafara sakewa tana rage damuwa har yar uwarta Ammah ta samu jin labarin abinda ya faru zuwansu saudiya da taki ta fadawa kowa da farko. A yadda tace da suka je can sana,a take sosai kashe rika suna samun kudi amma kudin ba nata bane na hjy ce. Don har hjy ta gina gida anan kano da iri kudin da take turowa a nan gida Nageria kuma ashe ita hjy din takan shigo nageria tayi abinda zatayi ta koma ba tare data je kauyensu ba. Ana cikin haka da girma ya soma ita nana hankali ya fara zuwa mata ta nemi da ta koma gida amma hjyn ta hana don takarrdun da komai nata na wajen hjyn . Dama kuma haka sukeyi da anje can ance sai su karbe takardun tafiyan ka sai kagama masu bauta ka gama wahala zasu fito maka dashi a lokacin kaima zaka fara neman kudi ka. Suna hakane har Allah ya hada ita nana din da wani balaraben mutum shi wanan da kike gani a jikin photon dai da shakuwa yai shakuwa a tsakanun su har ya nemi auren ita nana a wajen mutanen su nacan. Wanda ba tunanen komai hjy din da sauran shuga banin su suka taru suka aurawa nana wanan mutumin acan suka sha bukinsu batare da kowa na ita nana ya sani ba ana gida. Yadda ta fada muna zama sukayi na so da kauna dashi na fi sabi lilah har Allah ya kawo masu rabonki aka samu cikinki a lokacin. Wanan mijin nata tace yayi murna sosai da samun karuwankidon ya gwada mata gata iya gata kamar yadda Allah ya umurta a nunawa iyali. Har Allah ya sauketa lafiya suka radawa yarinya sunan nana Aeesha ma,ana Aishatu a nan dai wajen mu. Ya kula dasu yadda ya dace sosai ko bayan haihuwanki din kwatsan suna nan ta fara ganin canji a gurinsa na wasu dabiun da bata sanshi dasu ba daga baya ya fara nuna hattara da tsana daga ita har yar nata. Abinda nana bata sani ba shine ashe auren contragi yayi da ita nawani dan lokaci dama sai kuma aka samu akasin hakan rabo ya shiga tsakani a lokacin. Shi aiki ya kawoshi saudiya yayi wanan aurene don kaucewa zina kamar yadda sukeyi acan din wanan yasama ya zabi bakar fata yayi auren hakan da ita. A nasa shirin idan zai koma gida kasansu saiya sallami ita nana din sai kuma rabonki tsakaninsu ya shiga ciki wanan ne ya daga masa hankali a lokacin. Har ya fara nunawa nana da yarta wanan halin gashi kuma kasansu sun fara matsa masa lamba ya dawo gida hakana son har ya kara lokaci a can. Kwatsam nana ta wayi gari bashi sai takarda da kudi masu yawa daya barmata wanan ya dagawa nana hankali sosai a lokacin. Mutanen su nacan ta fara nema ta sanar masu da abindake faruwa kinsan halin mutane sunga wurin cin kudi sai suka fara karban kudi a hannun nana da sunan suna taimaka mata a lokacin a gano inda Abduljalil ya shiga. Dadewa dasu yasa nana din ta farga da abinda suke mata kudinsu kawai sukeci suna mata karya bayan haka ba wani taimakon da suke mata a lokacin sai karairayi na yau daban nagobe daban. Don haka ta daure bakin aljihunta ta tsuke wanan ya kawo sukai mata sheri ganin ga dukiyan da miji ya bar mata ya gudu ya koma kasansu sai sukai shawaran yi mata cune ga askar dinsu nacen. Don idan ta baro can din su koma su mallake komai nata wace tayi shekaru mai yawa a cikinsu tasan hakan zai iya faruwa don hakane ko yaushe tana tafiya da dukiyanta a jikin ta da komai a cikin jikinta tace. Kwatsam kuwa rana daya sai gashi Askar din sun sallama mata akan suna tuhumarta ta hauro kasan ta kazamin hanya tazo nan tana aikata alfasha a kasansu. Wanan abin yayi sanadin da suka hada da ita da wasu da aka kama suka ingizo keyansu zuwa nan Najeriya shine ta nufo gida a lokacin kwatsam muka ganta. Kinji Nana duk abinda mutane ke fada a kanki cewa ke shegiyace baki da uba ba gaskiya bane kedin har halak ce kamar ko wani da a duniya illa akasin da aka samu naki kaddaran yazo a haka. Ya dago yana kallona zuwa lokacin hawaye ya gama bata min fuska don kuka nakeyi shafe shafe ya shiga lalashina a cikin tashin hankali yana fadin. Na dauka shekarun ki yakai na rugumar kaddara a yanzu yasa na yarda na fada maki asalinki da muke boye maki a yau ai nana da nasan ba zaki iya jure hakan ba da banyi gangancin baki wanan labarin ba a yanzu. Wanan kukan da kikeyi zai iya jawo hankalin makwabata su yi zaton ko wani mugun abin nayi maki gashi ni kadaine dagani saike a gidan nan yanzu. Jin hakan yasa ta tsagaita kukanta don gaskiya Abbun ya fada balle tumba ta aiko kan tazo gidan nasu kamar yadda uwarta Ammah ta fada. Tace anan zata kwana bata zuwa can din tuno hakan yasa ta mike zuwa dakin kwanta ta kwanta shima Abbu din bai kara cewa da ita komai ba a lokacin don zuciyarsa da ba dadi. Saboda tuno da abubuwan da suka faru a baya game da yarinyar yasan dole sai hakan ya faru dasu don tun suna boye mata dole wata rana zaizo da zasu fada mata gaskiya akan zancen ta. Haka kowan su ya kwanta da bacin rai ga Aeesha ba zancen barci a ranan haka ta kwana tana tunane akan mahaifanta dataji labarunsu a yanzu wanda abin ya tsaya mata a zuciya sosai. Sai tambayan kanta takeyi da meyasa ya rudi mahaifiyar ta har ta yarda da hakan yasan ba auren fissabillah yayi mata ba a lokacin. Da irin zancen nan ta kwana a zuciyanta idan tace tayi barci a wanan ranan karya ta fada yadda taga rana haka taga dare a wajenta dukko da dun,bin gajiyan dake jikinta ta nemeshi ta rasa a rana. Hakan yasa washegari ta tashi da wuri jin Abbu ya fita zuwa massalaci itama ta tashi tayi sallah bayan ta idarne ta fito ta hasa wuta don yin dumamen da zasu karya dashi. Koda ya dawo har kunu takai ga dama masu da dan guntun gumban da Ammah ta rage har ya saura zuwa wani lokaci Abbu ya dawo daga masallacin da tasbaha a hannunsa yana ja. Shimfida ta shiga ta dauko masa tayi mai a wajen da yake zama tare da dauko abun karyawan ta jera masa yadda Ammah dinta ke masa a kullun idan zai karya. Albarka da fatan alherin daya saba jero mata ya dinga saka mata duk da yasan a ranan hankalinta ba a kwance yake ba alama ya nuna tana cikin damuwa sosai a lokacin. Ta juya zata shiga dakinta taji muryanshi yana fadin nana zonan yaki yana nuna mata gefenshi da alaman tazo ta zauna zaiyi magana da ita lokacin. Kamar itama yasan da sauran zancen da take son tambayanshi a lokacin kasan zuciyanta ta dawo ta dan tsuguna a gefenshi don ta kasa zaman daidai yadda ta sabayi dashi a lokacin. Kafin yakai ga furta mata wani zance yaji ta jefo masa tambaya tana fadin Abbu dama nace yanzu ina ita wanan Nana din take da kace itace mahaifiyata ? Ya dan murmusa a fuskanshi yana kada kai tare da kai loman tuwon da ya yanko a bakinsa yace Nana nan insha Allahu muna sa ran hakan saida tana can kasa mai tsarki don can ta koma. Duk da dai bada yardan mu tayi hakan ba don data kawo shawaran komawa can din daga baya bamu yarda mata da hakan ba sai ta shamace mu ta sulale ta koma ba tare da sanin bu don ba zata iya rayuwan nan ba don acan ta taso tayi rayuwanta da komai. Hankali ya so ya tashi bayan batanta saida na zaunar da ita Ammah nan na bata magana don tafiyanta ya nuna tabar muna amananki a hannun mu nida Ammah din don wayiyar gari mukayi muka nemeta muka rasa a lokacin. Sai ke kadai a dankin kwanan kwace da yar takardan da wasu tarkace cikin leda data bari a gefen ki na daukeki Ammah ta bude ledan kudine a cikinsa masu yawa sai sarkan gwal guda biyu a cikin wani leda daure. Ganin batarta zai iya jawo magana tun kan mutane su farga da hakan yasa nayi shawara da ita Ammah washegari nazo nan cikin kano na saya muna wanan gidan nan a wanan unguwar a cikin kudin. Nakoma can kauye ba wanda yasanda hakan saiji sukayi kawai munce munbar gari zuwa nan cikin kano da kowa nawa wanan yasa kikaga ko dayan mu zaije gida bamu yarda muje dake har yau din nan don gujewa abinda zuwan naki zai haifar a kauyen mu din. Gudu tayi ta barni ke nan a wajen ku itama na fada ina kallon fuskan Abbu din da alokacin shima ransa a bace yake da tuno da abubuwan da suka faru a baya. Cikin murmushin yake yace dani ba zance gudun tayi ba kuma zan iya cewa hakan don hankalinta nacan kan nema maki inda zataji labarin mahaifinki daya tafi ya barku da kuma makomar dukiyanku data baro a can a lokacin. Wanan nake zargin ya mayar da ita wacan kasan a lokacin don mun taba samun labarinta wurin wani mutumin garin mu inda har tabada sako garemu yace taji dadin ganinsa kuma shima din yace bai ganta a mugun kama ba lokacin. Kinga ke nan duk inda nana take tana cikin koshin lafiya haka kuma muna a ranta musanman ma ke din nan da a yanzu tasan kin girma kin kai munzalin hakan a girma. Ba abinda muke kullum sai adduan Allah ya karkato muna hankalinta zuwa gida ta dawo cikin yan uwa kamar kowa wanan shine fatan mu a yanzu. Ki godewa Allah nana da kika taso a cikin mutuncin daba duk ya zata samu hakan duk da muke ba mu muka haifeki ba Allah ya dora muna kaunarki a zukatan mu fiye da yayan da muka haifama a ciki mu a yanzu. Don ke din kin kasance ammace a wurin mu idan munyi maki rikon daba daidai ba ranan gobe kiyama Allah zai tambaye mu wanan a bainan jama,a. Na sani Abbu banda kamar ku a fadin duniyan nan koda kuwa yau uwata da ubana zasuce zasu dawo gareni basu kaiku girma da daukaka ba a idanuna. Masha Allah tunda har kin san wanan to ina son ki cire duk wata damuwa dake kasan zuciyarki game da iyayyenki a yanzu haka kuma ki daina kwankwanto koke wacece daga wanan ranan . Don kema ya ce kamar kowa da aka samu ta hanyar halak banson in kara ganin ki a cikin damuwa wanan kaddarankice da Allah ya zano maki tun farko. Abbu yayi min magana da zasu kwantar min da hankali da wanda zaisa kada inga laifin mahaifana da suka haifoni kuma suka kasa rikona a hannunsu don saba lamba. Da haka Abbu ya fita zuwa kasuwa bayan ya ban dari yace insai taliyan hausa in sulala da rana inci komawa nayi daki naci gaba da tunanen duniya don har yanzu zuciyana ya kasa gaskanta labarin da Abbu ya ban game dani din ashe mutane sunyi gaakiya da suke dangantani da larabawa tabbas ni din yar balaraben asaline ashe . Jinin sune a jikina kamaninsune na kwaso nake ruwa dasu jinin su shiyafi karfi a jikina bisa ga na mahaifiyata wanan tunanen na wuni yi ni kadai a gida da haka har barci ya daukeni ban sani don idona dake da rankon barcin jiya da banyi ba. Koda ta falka karfe ukun rana ya gwauta a gagauce ta debo tuwa a randa ta shiga bayi ta watsa ruwa tafito tayi alwala zuwa sallah bayan ta idar wanan hoton dake gefenta ta kara jawowa ta zubawa matar jikin photon ido na dan lokaci tana nazarinta. Tabbas ko a cikin hoton rayuwa ya nuna tana cikin jin dadi da walwala a lokaci saboda yanayin da suka dauki photon ya nuna gidane hadade ko a dacan baya don akwai abubuwan more rayuwa a gidan da photon ya nuna. A fili take fadin don me zaki gudu ki barni cikin bakin ciki da takaici bayan kune sanadin zuwana duniya a haka ina kika shiga kika watsar dani haka kamar marainiya ? Idonta ta mayar kan wanan balaraben tun daga rawaninsa daya dan daura ga kai har zuwa fuskansa dake nuna tsawon dogon hancinsa zuwa dan gashin bakinsa kafinta mayar da idonta kan farar jallabiyan jikinsa tana runtse idanuwanta. Cikin jin kuna da wani irin tsanarsa a zuciyanta ba zan yafe maka ba ta furta a fili kayi sanadin zuwana duniya ta hanyar yaudara kuma ka wofintar dani a cikin duniya duk da kasan da ina raye a doron kasa. Hakana dinga sakin maganganu ni kadai a gidan kamar sabuwar mahaukaciya in na gaji in fashe da kuka inyi kuka saina gaji kuma in cigaba da magana. Har nagaji nayi barci a wurin saida almajiri yazo yana bara na falka sauran tuwon dana zubawa Abbu ya rage shina raba biyu na kirasa nabashi ya shiga jero min addua. Nan kofa na zauna bayan na debo ruwa a randa nake zauna na tasa abincin a gabana na kasaci da kyar nayi loma biyu naji tuwon bai wucewa hakan yasa na mike zuwa alwala nayi sallah. Haka na wuni ko wanka banyi ba a ranan sai zuwa yamma na dan samu zuciyana ya sake har na samu na dinga yan aiyukan daya dauke min hankali. Sauran garin tuwon daya rage na tuka muna don zai isa saboda daga bakina saina Abbu har miya na hada koda Abbu ya dawo da wasu kayan cefane yasanu ina kwasan tuwo. Tun daga kofa yake fadin nana ikon Allah a ina kika samo kayan girki na juyo ina fadin Abbu sannu da dawowa ya amsa da yauwa har lokacin da mamaki a fuskanshi. Ya sake maimaita min tambayan dayayi min da farko na bashi amsa da fadin Abbu sauran na jiyane daya rage na tuka muna. Allah yayi maki albarka nana ya fada nakanji dadi idan Abbu da Ammah suna min wanan adduan don duk sukai min nakanga fa,idan wanan abin ZAINAB IDRIS MAKAWA [7/23, 10:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 0️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kwanan Ammah uku ta dawo cikin bacin rai hankali tashe na gane hakan ne ga yanayinta duk da hakan bai hana ta hango yar rama da nayi ba. Keko Aeesha wanan rama fa ko bakya cin abincin ne bayan tafiyana lokaci daya duk kin zube haka meke damunki haka ko kinyi ciwone a bayana take tambaya cikin damuwa ? Lafiyata kalau Ammah kawaidai kila kewanki ne yasani rama nake gani tafi can ja,ira saboda tafiyan kwana biyu ki zube haka ? Kodai malam ne baya kawo abinci ki dafa maku ta tambaya cikin nuna kulawanta a gareni nace abinci kan har sai mun ture ai. Gefenta na karasa isowa na zauna ina fadin da alama dai a gajiye kike Ammah ko in fita in nemo maki wani abu kici ta kalloni tana kako murmushin dole a fuskanta tana fadin dadina dake Aeesha tausayin da jinkai. Yanzu har kin fahinci damuwa a fuskana to kwantar da hankalinki gajiyace kinsan hanyar namu bakyaune dashi. Ina maman gwarzo don naga tare suka tafi ai da ita take fadin tun acan kowa ya shiga motar garinsu don tafiyan zai zama wahala idan tace sai ta biyo ta nan kuma. Nidai ban matsa mata ba naci gaba da aiyukana da nasan nice zanyi idan tana gida har lokacin Amma din tana zaune a inda take . Har lokacin Ammah na zaune a inda na barta cikin damu saida aikai kiran sallah la,asar na kawo mata ruwa a cikin buta a nan inda take din don tayi alwala ta samu ta mike ta zagaya ban dakin ta dawo tayi alwala ta shiga daki. Nima shinaje nayi bayan na idarne na fito a hankali nake jin sautin kukan Ammah din yana tashi daga dakinta na dan dade tsaye a cikin damuwa kafin na yunkura na shiga dakin tana ganina tayi saurin share hawayen dake fuskanta tana saita kanta. Don kada in gane halin da take ciki a lokacin da wayauna dole in gane ko ace ni karamace yau naga uwata tana kuka haka dole in shiga halin damuwa da tashin hankali. Balle a shekarun da nake lokacin ya kamata in fahinci wani abu yana damun Ammah din a lokacin kuma koma meye ba karamin abu bane wanan. Zubewa nayi akan gwiwana ina fadin Amma saboda nice kike kuka ko nice bacin ranki a yanzu na sani sani itama ta sani don tasan haka zai faru ta gudu ta barku dani kuna kumsan bakin cikin da ba laifin ku bane ya kawosa. Wani irin kallon mamaki Amma din ke mun a lokacin don bata taba zato ko tsamanin jin makamancin hakan a bakina ba don bata taba tsamanin har zansan ba ita ta haifeni ba. Ga irin nata hikimar fada sosai ta hauni dashi tana fadin wani zancen banzane haka nazo ina mata in tashi in bata wuri tunda bansan meke damunta ba in barta da abinda ke samun zuciyar ta. Simi simi na mike nima ina sharab kwala zuciyana a cunkushe ji nake dama na mutu in huta da wanan bakin ciki da nake gani a rayuwata tun ina kankanuwa dani haka . Itama Ammah din fitowa tayi tana fadin in bata aikin in wuce islamiya kada in makara hakan yasa na bi umurninta na shirya na nufi islamiya. Mai karatu da zaki hadu da ire iren mu diyan watsin kano da ake haifowa a saudiya a watso nan gida Africa a jibgemu zakiji labarin dayafi nawa daci a kunnen ki Don saikai da hakan ya shafa kasa abinda kake fuskanta daga gida da kuma wajen jama,an gari don kiri kira za a nuna maka rashin gata ko wani cin fuska a bainan jama,a. Haka na nufo makaranta na samu hat an soma karatu ka,idane ga duk wanda ya makara irin hakan a hukuntashi a kwaini da tsoron bulala duk da ba wani bulala bane mai yawa biyune zuwa ukku. Saidai nayi sa,a ina isowa malamin namu ke fadin yau ya akayi kika makara nan na marairaice ina fadin mahaifiyatace bata gari natsaya aiki na makara. Karyana ya karbu don cewa yayi ban sanki da halin makara ba don baki da wasa shige ki shiga ciki har da dan rusunnina ina godiya na shige da sauri cikin ajin na jona tare da sauran yan uwa akaci gaba da karatu dani. Koda muka taso na iso gida na samu har Abbu ya dawo yana waje yana yan gyare gyren wurin da suke zama karba naje yi da sauri yace barshi nana shige ciki ki huta kinji. Ammah na tsakar gida tana kawar da kaya nayi sallama idona kyam a kanta ina karewa yanayinta kallo tare da gaida ita da kallo. Cikin sakin fuska kamar ba ita na bari cikin wancan yanayin na damuwa ba tace Aeesha kin dawo ke nan ya hanya na amsa da lafiya Ammah . Ki dauko ledan can ki bude akwai dan tsaraba dana sayo maki a hanya da sauri na karasa ina fadin to mama na karasa wajen ledan. Na jawo ledan na kawo gabanta tace bude ki diba mai isan ki kije kici na duka na fara bude ledan da dan saurina ledan yalo na fara cirowa cikin murna da ganin yalo don ina son cin yalo arayuwata naci gaba da tona ledan nan ma naci karo ayya soyayya da gyada suya ruwa ko wani kuli daya na dauka sai yalo guda ukku. Na tura ledan agaban Ammah ta dago ta kalli hannuna kafinta maida kallonta ga ledan tana fadin kara mana donki na sayo kinsan malam in yayi ya debe yalo kawai a ciki. Nace Ammah bari inci wanan in Abbu ya dawo ya diba sai inzo in kara anjima batayi magana ba kai ta kawar daga gareni kawai Abbu bai shigo gida ba saida yazo daukan abincinsa. Bayan ya shigo din ina jinsa yana fadin ni zancen nan ya daure min kai mutane yanzu basu da tsoron Allah a zukatansu kiri kiri ku dannewa mutane hakkinsu saboda wani dalili naku can dabana addinini ba sai zalla son kai. Naji Ammah tace ka barsu kawai ai inba nan akwai can zasu bamu inda basu dashi hakki dai kowa yasan namune don muna da iko a acikinsa. Ba wanan bane damuwana ba malam yadda suke muna bugun kadanya baki dayan mu damu muka kashe mahaifin mu saboda bakin cikin dakin mu har mahafin mu ya mutu ai. Wanan ba hujja bane Amamatan koda hakan gaskiyane kuna da hakki akan dukiyasa ai abu daine son kai da rashin imani yaiwa mutane katutu a zukata yanzu. Idan ita nana bata kusa ku baku kusane ko ance kada aba diya mata hakkinsune ? Dama nasan komai dadewa sai irin hakan ya faru don mutane yanzu kiris suke jira su samu dama saisu fake a nan su zallunce ka don zalunci yanzu ya bar birni ya koma ga mutanen kauye garama na birni suna jin wa,azi yanzu daidaikune marasa imani kowa yana tsaye yana neman na kansa. Nana dai komai daren dadewa muddin tana raye zata dawo kasan nan wata rana dole ko su fito da dukiyan nan kamar kada ya fadi hakan naji Ammah din na fadin. Kaiya malam da zata dawo gida aida yanzu ta dawo din haka dai ta zabawa kanta rayuwan nisa damu naji yana fadin kaiya nakan rabaki da irin wanan zance Ammah . Idan haka ta zabawa kanta me zakice ga wa yanda sukayi sanadiyar fitanta gida tun tana kankanuwanta ko shima duk har lokacin abinda ta zabawa kanta ke nan a rayuwa. Sam banganin laifinta har gobe a idona don yarinyar nan ba itace ta jefa kanta cikin wanan halin ba kiyi tunanen hakan ko wani lokaci abin saidai istigifar kawai za a yi don shiya dace kawai yanzu. Gareku iyayye masu tura diya aikatau kada kuce baku da kamishon

Chapter 2 of 8