Share this page
5 / 8
don tana business dinta tana samun kudi sosai yadda ta bashi labari har ya bukaci ya ganeni akace dashi ina islamiya. Bayan fitan Abbu gidan kawai ina bakin murhu ina hasa wuta naji Ammah ta saki wani irin kuka daya tayar min da hankali lokaci guda har bansan sanda na fada dakin ba a razane cikin tashin hankali. Wurin Ammah din dake durkushe ta zubawa wasu kaya idanu na nufa ina tambayanta a gigice da Ammah waya mutu meya faru anyi wani abune ? Duk lokaci daya nake wanan babatun cikin tashin hankali a gareta kafin idona yakai ga kayan dake gabanta a take zuciyana yayi wani irin ras ras a wajen . Hakan yasa nakai durkushe a hankali ina bin kayan da kallo da ido abinda ya fito bakina lokacin shine Nanace ko Ammah ? Wani irin kallo Ammah din ta watso min a lokacin sai kawai na mike na fice daga dakin lokaci guda cikin karfin hali na nufi wajen aikin dana soma naci gaba ba tare dana sake waigen dakin Ammah din ba kuma. Fitowanta cikin mamaki yayi daidai da shigowan Abbu gidan dauke da kayan cefanen daya sawo muna na dago da idanuna da sukai ja ina masa sannu ya amsa da fadin dama nasan haka Nana ina sauri da Allah Allah karkiyi talge kafin na karaso. Kayan da Ammah ta karba a hannunsa nabi da kallo da dan buhun daya nuna abincine a cikinsa daya aje gefe daya sai kuma na kawar da idona da sauri akan kayan na juya zuwa aikina ina jin Ammah na fadin malam zo nan ya bita zuwa daki. Abbu bai karasa shiga dakin ba Ammah din ke fadin yau naji abin mamaki a bakin yarinyar nan da sauri ya juya ya kalleni yaga ina gyaran wuta ya juyo gareta yana fadin meya faru kuma ? Tayi ajiyan zuciya mai nauyi ta sake kafin tace sunan uwarta naji ta ambato min a bakin ta kamar a mafalki fa malam da cewa Nana ko ? Dan murmushi yayi kafin yace kin dauka duk tsayin nan bata san komai bane ta sani tasan komai game da uwarta don har hotonta ta gani a dakin nan ai ranan. Kirji ta dafe tana fadin na shiga uku malam garin yaya haka ya faru yace ban san ya akayi ba amma ta gani ta kuma san komai zaune takai saman dan gadonsu na katako lokaci guda tana dafe kai. Wai meye hakan data sani tayi wanin abin asshane a gareki ki natsu kibi yarinyar nan a yadda ta bimu ban son tashin tashin da zai kawo bacin rai a yanzu kuma. Hakan bai sa Ammah shiru ba sai bayan sallah insha,i Abbu ya dawo daga sallah ya fita ta zauna a inda muke zama nan tasa min kira daga daki na amsa na fito zuwa gareta. Tana zaune a cikin damuwa har lokacin nafito ina fadin gani Ammah ta dago tana fadin barci zakiyi bakici abinci bane Aeesha ? Na koshi na fada a razane ta dago kai tana sauke min wani kallo tare da fadin me kikaci kika koshi dashi ba komai na fada ciki ciki a wani irin yanayi na damuwa. Waime ke damun rayuwankine haka kika sakawa kanki wanan damuwa haka to ki jini da kyau wallahi Allahma shedanane Aeesha dani da bawan Allah nan don bamu rageki da komai ba a rayuwan ki . Yau abinda bawan Allah nan ke dauka a kanki kodashi ya haifeki ya tsaya a nan amma kin bi kin damu kanki kin tsiro da wasu halaiya na daban a yanzu akan abinda bashi bane gareki. Yau dai nasan duk abinda wani zai fada maki a duniyan nan mukace dake ga gaskiya dole ki yarda da hakan a kanki don shine gaskiyan gareki. Don ba zamu fada maki abinda zai dawo ya cutawa rayuwanki ba daga baya muma ya cutar damu don muke tare dake ako wani lokaci. Kuka na dan farayi naji ta sake min tsaya tana fadin ba kuka na zaunar dake nan ki mun ba kiranki nayi inji waya fada maki wani labari a game damu ko ke ? Kaina girgiza mata a lokaci alaman ba komai a rayuwana saidai ina mai jin wani iri kasan zuciyana kamar in kashe kaina don bakin ciki. Nake ji a lokacin abinda yasani dagowa shine muryan Ammah din dake fadin duk da kin kasa tambayana labarin da kikewa bakin cikin kike wanan rama to ni nan nasan kin sani. Saidai ina kwankwanton a inda kikaji wanan labarin shine ya daure min kai a yanzu ba wani abuba so nike insan me aka fada maki game da mahaifiyar ki ? Da alaman tsoro a fuskana na dago ina kallonta sai kuma na dukar da kai ina tunane tsokin takaici naji taja tana fadin. Ga kayan can da taba wani bawan Allah tare da kudade masu yawa ya kawo maki har damu don haka sai ki tashi ki duba idan zaki iya don naga kin sakawa zuciyar ki abinda bashi ba a yanzu. Kaina girgiza nace ko tsinke bana so Ammah abawa wanda duk ya dace nagode ai bankai karshe ba naji saukan hannun Ammah a fuskana saida naje tangal tangal daga zaunen da nake don zafi. Fada ta fara tana fadin ni zaki kawowa diban albarka Aeesha sakaiyar da zaki min ke nan a yanzu ace na hinjiraki ban maki rikon gaskiya na tsakani da Allah ba. Idan Nana da mahaifinki sun maki laifi da farko idan kin kula yanzu ita Nana kokarin take ta burgeki ai taga ta wanke maki zuciyar ki. Ina laifinta ga hakan tunda duk wani abu donko take turoshi a garemu saboda rayuwanki ya inganta ai kada ki dauke mu bamu san abinda mukeyi ba mana. Ko duniya Nana ta mallaka a yanzu wanan bai tsone min ido ko in kalla balle raina ya biya da ace aikin banza takeyi a can mutumin nan saida ya rantse muna kamar yadda itama ta rantse masa da aure ta daura a can din bayan ta koma saudiyan. Don haka ki shiga taitaoyin ki dani kafin ranki ya baci kada ki dauko min wani surfa banza ki dagwala min lissafi dashi yanzu kuma. Sautin kukanane ya karu a lokacin akan nace ban karban kayan da Nana ta turo muna Ammah ke min wanan fadan da baida tushe haka har duka abinda bata taba min a rayuwana ba tunda na tashi. Gyaran muryan Abbu alaman zai shigo gidan a lokacin yana sanar muna hakan baisa na rage sautin kukan da nakeyi ba wiwi ina jan majina ta hanci don zuciya daya kawo min. Tundaga kofan gida yake fadin wai yayane meke faruwa hakane wai daga Ammah har ni ba wanda yai masa magana a lokacin. Sai ya cigaba da fadin tambaya fa nakeyi anyi shiru meya kawo haka kuma yanzu Ammamatan ya juya kanta ya kureta da ido yana son jin amsa . Haba malam kamar Aeesha zata zauna tana gardama dani yau don wani ya rutsata ya fada mata maganan daba shiba ta dauka tana kokarin rainawa mutane wayau. Juyawa yayi gareni saida ya kare min kallo a cikin tausayi yace haba Ammah kibi yarinyar nan sannu mana don Allah yau ko me tayi tayisane akan kurciya da dacin rai. Don ko an tabata dole tayi hakan ina hakkurin ki ya shiga da zaki biyewa yarinya kuna saida hali a cikin shiya muryan kukanta har waje na tsinkayoshi. Ai dole in biye mata malam da wani yarinyar nan ke son inji a yanzu da nata iya shegen da takeyi yanzu ko da wanda muke fama dashi kan rashin yar uwarmu. Duk yadda take ji mumafa muna jinsa a yanzu aiko inga dubaiya ban cancaci hakan a gareta ba a yanzu me muka rage yarinyat nan dashi don Allah malam a yanzu ? Umm,ummm Ammamatan ki duba lamarin nan ki auna shekaru ba daya bafa yau ace kaine hakan ya rutsa dakai ko babban kanka ke ya zakaji abin don Allah. Shi yaro a sannu ake fahintar dashi ya gane bada garaje ba irin hakan ya juyo gareni yana fadin ke nana rufe min bakin ki a yanzu idan kina son muyi magana a tsanake dake ko kuma in fasa hakan inyi fushi nima in baki baya in fita a zanceb in barki da Ammamata din kuyi tayi. Jin abinda Abbu din ya fada yasa na sassauta kukan nawa sannu a hankali yana ganin hakan ya juya ya fice daga gidan ban jima ba na mike na shige daki na barta a wajen cikin bina da kallo. Ya dan jima bai shigo ba sai can naji shigowansa yana rufe gida kafin kuma naji muryansa a kofana yana kwala ma sunana kira da ke nana fito ki karba nan . Jin hakan yasa na fito daga dakin ya bini da kallo kafin yace ungu jeki randa ki debi ruwa ki daureye fuska da baki kizo ki zauna kici. Na koshi na fada a sanyayye wani tsawa ya buga min da yasa na nufi sashen randan ruwab namu da sauri ina diban ruwan . Zama yayi saman shimfidan da yayi a tsakat gida kodana dawo gefensa ya nuna min yana fadin zauna nan a kusa dani . Ba mussu nakai zaune kamar yadda yace din ya miko min leda da tun kan in bude nasan meye a cikin ledan don kamshin dake fita a cikin takardan ga kuma nutrients milk mai sanyi har guda biyu. Bayan na karbane ya fara kwalawa Ammah kira itama ta fito ya mika mata ledan yana fadin karbi bude muna nan ya mika mata itama zama tayi cikin damuwa tana bude ledan daya miko mata din a lokacin. Dan juyowa yayi yana sauke min kallo tare da fadin bissimillah mana Nana nakine wanan gani nayi yau rayukanku sun baci bakuci abinci ba zaku kwana da yunwa daga karshe hakan ya zamo maku matsala. Maza ki bude ki somaci kikuma saurari abinda zan fada a yanzu ina son kowa ya bani kunnuwansa ya saurari abinda zan fada a yanzu wurin nan. Don zancene da zanyi a matsayina na uba kuma maigida a gidansa don haka kai tsaye umurni zanba ko wani ku a nan ko kuma doka a gidana don haka ina son kowan ku ya ban hankalinsa yanzu ya saurareni. Ke Nana dake zan fara don haka ina son ki saurara kiji abinda zan fada a yanzu a kanki don a yanzu kece wace kika saura da wanan zance kuma idan kinyi hakan ba laifi bane don kinyi a wajen kowa. Ko ita uwarki gata zaune bacin raine da damuwa ya saka tayi maki wanan boren a yanzu amma ba don taso hakan a gareki ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA [8/1, 9:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND MAMAN BIBO KAYAN MATA 08068871330 KOKO ROAD SOKOTO JA YA FADO,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 0️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nana na dauka ilimin ki da wayaun ki tare da tarbiyan ki zai saki natsuwa ki fahinci gabar da muke son dora rayuwan ki a yanzu ? Sai gashi kuma na hango ba hakaba a wajen ki don nayi zaton yadda ake zuzuta ilimin da kwazo a yanzu zaisa ki hango matakin da muke shirin doraki. Idan kinyi tunane da babu dan dana taba bari yai zurfin ilimi a gidan nan kamar yadda ke muka barki a yanzu kina samun ilimi shin azaton ki yanzu nayi hakan ne saboda ban haifeki ba ko me ? Da sauri na dago kai ina kallonsa cikin hawaye ina girgirza kaina a gareshi da nufin ba hakan bane yace kamar hakane Nana a ganina. Bari kiji dalili a yanzu na hango ilimin nan shine tsanin takawa a duniya shine matakalan cinma burin rayuwa ga dan adam yanzu. Inkai manomine sai da ilimin nan na zamani yake bunkasa haka in kai malamine saida ilimi kake samun cigaba a rayuwa ke komai yanzu da zakayi hatta kasuwanci yau ya koma idan baka da ilimi hakan bai bunkasa yadda ya kamata ga bawa. Hakan yasa nayi amfani da wanan daman na ke kokarin ganin mun inganta rayuwanki don gabarki ki samu makoma mai kyau a cikin rayuwa. Alhamdullahi kuma donke din yarinyace mai natsuwa yare da tarbiya yasa muke maki hangen hakan a kanki a yanzu don ba zanso mu tauyeki ba mu durkusheki nan gaba ba zaki fahinci mun maki rikon tsakani da Allah ba. Amma da ilimin nan na zamani zaki fahinci komai a rayuwa a yadda muke fata haka kuma keda kanki zaki warware ma rayuwanki dana iyayyen ki hukunci in muna da rai da lafiya. Idona na runtse cikin dacin rai daga inda nake zaune ina maijin yadda zuciyana yake tafarfasa lokaci guda don ambatosu da yayi a zancensa. Ya dora da fadin to don hakane nake son in baki dama daman da ban taba ba wani yaro ba a gidan nan don ki samu ilimi mai inganci da zaki taka kafarki dashi har hakan ya zamo maki bangon dafawa a rayuwan don akwai rai akwai mutuwa ga bawa in mune yau ba mune gobe ba a duniyan nan. Amma fa duk wanan dole saina saka daga wanan arzikin da ita mahaifiyarki take turo muna hakan zai yuyu don ke shedace banda halin wanan hasashen da nake maki a yanzu. Don haka zancen ace kince ba zakiyi amfani da dukiyar da mahaifiyarki ta turo ba baiko taso a garemu ba yanzu wajen ki nana. Don koda rantsuwa nayi a wajen ban kaffara ta turo munane don inganta rayuwanki a gaba don ba Ammamatan bane kadai ta bari ai nan najeriya suna da yawa meyasa bata turawa sauran yan uwa kudina idan sun mata yawa ne kike gani. Don haka banso ki zalunci kanki da kanki nana in ma wani abu kike tunane a yadda nasan Nana Asma,u sai naga ya girgiza kai ya kare da fadin nana tafi wayau da dabara a duk wajen nan. Don tasan inda ta fito tasan darajan iyayyenta dana yan uwa ba zata bari wani abin asha ya shigo rayuwanta ba a can wanan yasa ina cikin wa yanda suka yarda da abindata fada dari bisa dari da wanan kaddaran rabonki ya gittamata a lokacin. Nasan ko waye nana a lokacin don a wajen mu ta fara zama kafin a kulla karbanta daga hannun mu abawa hajiya Naito rikon da ya zamo sanadin komai a yanzu daga baya kuma kowa ya dare ya koma gefe yana gulman hakan. Ki godewa Allah Nana kina cikin gatanki da rufin asiri akwai dubunki da hakan ya rutsa dasu nana basu san kowa nasu ba a duniya sunan nan suna walagigi da tangaririya a cikin duniya. Ke ko uwarki tayi maki gata bata barki ba sai da ta tabbatar da ta barki a hannun yar uwarta daba zaki taba kukan tanshita a kusa dake ba. Don haka in dai har na isa dake ina kuma da kima a idanunki daga yau din nan na kawar da zancen Nana As,mau a gareki har zuwa dawowanta haka kuma duk abinda ta turo da sunan naki ki dauka kiyi amfani dashi Aeesha. Ke kuma Ammamatan daga yau din nan bason a kara tayar da zancen nan don Allah har hakan yaba wani daman shigowa ya dauki sirin da muke faman dannewa shekara da shekuru a zukatan mu. Akwai sarka guda biyu da nana ta bari a lokacin suna wajen mu har yanzu mun masu boyon da ba mahalunki da zaisan dashi a gidan nan bayan mu. Don haka zan fito dashi a yanzu akai kasuwa a auna a tabbatar da kudinsa albashin in yaso idan sayarwa zamuyi sai a sayar a fara shirin karatunki da kudin ni nawa shawaran ke nan a yanzu . Sai naji Ammah ta nisa a hankali tana fadin to amma malam sai naga zancen karatun nan nidai gaskiya bai kwanta min kawai a sayar ta fito da miji anyi mata aure kawai shiyafi a daina wanan zance ko zata samu natsuwa itama. Dan murmushi Abbu ya sauke tare da fadin kaiya ana baki kina roko amma na fahinci kina ganin wanan shawaran nawa baiyi ba akan yarki ke nan ko ? Yata kuma yau malam to Allah ya baka hakkuri in abin har yakai can amma ni bada wata manufa ai na fadi hakan ba don kace inda mai magana yayine yasa na tofa nima. Kayi hakkuri bana rainawa tsarinka bane a yanzu gaskiya don nasan kafimu tunane ai dagani har ita kawai dai ina ganin auren kamar shine mafita a yanzu. Ammah ina son karatu don Allah na fada cikin sanyin murya don jikina ya gama mutuwa a lokacin da zantukan Abbu din dayakeyi akaina don a kainane zance ita Ammah nata mai saukine ai. Nice dai bawan Allah keson ingatawa rayuwana a wanan zaman kuma iya abinda ya rage ke nan suyi min a yanzu din har incinwa burukana na duniya a yanzu. Yadda yace hakan ya faru don washegari da safe yai kirana da kansa ya mika min tulin kayan da nake gani kamar wani shara a lokacin a hannuna ya kuma kara min nasiha akan rayuwa. Don gaskiya Abbu ya fada ba wanda ya isa ya kaucewa kaddaransa sai in Allah yaso hakan ga bawa haka kuma ko wace kaddara tana da wata manufa ga bawa Allah kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan. Yadda nakai kayan daki na watsa ban dago na sake waiyayansu ba duk da zuciyata tayi laushi a lokacin amma nake ganin kayan wani mugun abu a gabana. Don haka zan iya cewa ban bude ko leda daya na duba inga yaya kayan suke bama balle insan kallarsu kayane kuma masu yawa da zasukai kala goma ko fiye da hakan ajiye. Saidai kamshinsu daya ciki min dakin don kamshi sukeyi irin na turaren yan nahiyar can ta larabawa hakan ya fara sa kaina yana dan sarawa a lokacin. A hankali har na kai kwance ban fadawa kowa banjin dadin jikina ba a gidan sai Abbune da zai fita yake kwala min kiran da nazo nagani . Wanan yasa na taso a dunkule cikin hijjab din islamiyata ina dan kaduwa na nufoshi a hankali ya fara walwale min sarkankokin a gabana inda nake tsugune yana fadin. Kinga wanan biyun tun barin nana kasan nan data tafi ta barmu dake suke boye a hannuna wanan kuma sune ta aiko daga bayan nan. Saidai gun Alh sani zani dasu don akwai shagon sarkoki a kusa da shagonsa su auna su fada muna nauyi su in yaso sai mu in dawo asan abinyi dasu din kamar yadda na fada a jiya. Kai kawai na dukar tunda nayiwa sarkokin kallo guda ban sake dago kai na kallesu ba kuma saida na amsa masa dakai kawai hakan yasa ya dago don ya kalleni anan ya fahinci yanayin da nake ciki lokacin. Da sauri yake furta subbahanallahi meke damun ki haka nanata nan hankalin Ammah dake kokarin kauda kayansu gefe daya ya dawo gareni. Tasowa tayi tana tamba jikina ta juya wurin Abbu tana fadin jikin gaba daya ya gashe kamar garwashin wuta kina ciwo Aeesh ba zaki fada kika kokarin halaka kanki haka ba gaira ba dalili saboda mugun abunda kikasawa zuciyar ki. Hannu Abbu ya daga mata ya mike da sauri yana fadin tashi muje chemist haka na daure naje chemist din tare dashi akai min allurori masu karfi na maleria tare da magani muka dawo gida lokacin idona ya gaba rufewa sai barci ya daukeni. Duk suna zaune sun tsureni da idanuwansu ganin na samu barci mai nauyi yasa Abbu fitowa daga dakin yanawa Ammah hannu da alaman ta biyushi. Batayi sanya ba ta mike ta biyoshi din zuwa wajen cikin tausa murya ya soma magana da fadin Ammamatan meyasa baki amfani da hankalinki ? Wani kallo ta watso masa yace kwarai ko so kike yarinyar nan ta bijere muna a yadda muka santa a baya ? Yanzun ne tafi bukatanki yanzunne kema zaki nuna mata kauna da kulawan ki a gareta don ga baki daya a yanzu bakin mu take gani a wanan gabar. Dole sai kin kara janta a ciki sosai fiyema da da can baya ki nuna mata itama yace kamar kowa tunda tana damu a duniya koba nana a kusa balle mahaifinta damuma ba mu sanshi ba. Wanan abin naki zai kara saka yarinyar a wani mugun yanayi da ba zamuso ba ki kwatanta a gareki yau ke haka ya sama a duniya ya zakiji zuciyar ki a lokacin da kika sanda haka ?. Nan dai ya lurar da ita halin da nake ciki kuma ta gane gaskiya Abbu ke fada hakan yada dana falko naga sauyi sosai a gun Ammah din duk da bada wani manufa take min hakan duk cikin tsawatawan su na manya ne a lokacin. A hankali na yaye hijjab din dana rufu dashi har kai ina kai dubana ga Ammah din dake zaune a gefena tana yankan kubewa. Sannu tayi min tana fadin sannu Aeesha kin falka ya jikin naki na dan juya dara daran idanuwana kafin in koma lumshesu ina fadin da sauki Ammah. Kokarin mikewa nakeyi zaune naga ta tashi da sauri tana kamani tare da fadin ina zaki da kyat na bude baki ina fadin bayi a takaice. Zaki iya ko in kamaki ta fada cikin kulawa nace cikin karfin hali zan iya Ammah na mike na fita kodana fito na samu ta fito daga dakin ta dauki tsintsiya a hannunta. Alwala na duka na dauro don duban yanayi da nayi ya nuna min an dade da sallah axahar a lokacin hakan yasa cikin karfin hali na daura alwala. Nazo nayi sallolina don tun ina alwala aka kira sallah la,asar duk da yau sauri saurine amma dai nasan lokaci tane yayi don basu muke bi sallah ba a gidan sai hudu daidai muke la,asar. Na dade a zaune ina mika kukana ga sarki Allah wanda yafi kowa sanin dumbin damuwan tattare dani a zuciya wanda ba kowa zai fahinci hakan ba sai wanda kaddaransa yazo daya da nawa din. Don ace baka da uba kasan hakan da girmaka ba karamin tashin hankali bane a wajen mutum saidai Allah ya kyauta kawai. A inda nayi sallah nakai kwance a hankali ina bin dan dakin nawa da ba komai na rayuwa a cikinsa sai dan tsohon katifana da akaiwa cikon ragga gefe daya kuma dan tarkacen ghana most go din kayanane a ciki wanda idan ya lalace nakan fadawa Abbu ya sayo min wani

Chapter 5 of 8