Share this page
8 / 8
kamar wace akaiwa wahayin wani alheri. Dan murmushi nayi ina fadin banson in fara da makarane Ammah gyara muryan da Abbu yayi yasa ta kauce mashi a hanya ta dan karasa fitowa wajen. Ya dan kalloni yana fadin kin shirya ke nan nanata zakiko iya shiga yau ko a bari sai gobe tunda jikin naki bai karasa warware ba. Da sauri nake fadin zan iya Abbu insha Allah shike nan aikin kare zance ya fada tare da fadin muje nayiwa sale dan gidan wazan magana zai kaiki har school din naku inyaso sai ki dawo da kanki garin dawowa don iya kaikine kawai mukai magana dashi. Na juyo don inyiwa Ammah sallama na samu ta rike haba tana kallona don cikin tufafin da Abbu ya dinko min ne na saka kuma kayan sun min daidai kamar an aunani matsala dai wrapper tayi min da atamfan yasa nake dan hardewa tunda ban saba sakashi ba. A kofansu muka hangoshi yana goge babur din nasa har can muka taka Abbu na gaba ina biye dashi a bayanshi muka kai ya dago yana gaida Abbu din. Kafin naji Abbu yace to gata nan sale don Allah ka tabbatar da ka kaita har ciki don Allah ya amsa da to baba insha Allahu. Daga bayan baba na dan leko ina masa ina wuni ya amsa min cikin fara,a tare da fadin yau za,a fara shiga ke nan nace ehh Abbu yana tsaye kofan gidan nasu saida yaga tashin mu ya juya zuwa gida. Yana mai min adduan fatan alheri da neman kariya daga Allah shiko nan Sale sai yan faman gyare gyare yakeyi a cikin motansa kafin yace yi hakkuri fa kinsan ban gama gugabane kuka fito kada baba yaga na dan tsaya nawa gashi tsaye na amsa da babu komai Allah dai ya kaimu lafiya. Cikin yardan Allah muka shiga lafiya har inda madakatar mu yake nan ya fita yana dan waige waige har ya hango wanda yake nema a wajen ya yafitoshi tare da kiran sunarsa ya juyo. Ya iso inda muke yace dama nasan zuwa yanzu kafito don Allah wanan kanwatace unguwar mu daya ina son in nuna maka itane idan tana neman wani taimako. Kai sale kanwarka ina wanan ai da ganinta yar haure ce saidai da yake ka gyara zancen ka fadi gaskiya zan yarda to yaya zan karasa da itane yace kaima ka sani ai yana zaro yan canji ya bashi yace barshi kawai mu samu ciko mu karasa ciki. Jeki kanwa ga mota can ki shiga ya nuna min motarshi din don akwai tazara daga inda sale ya ajeni zuwa cikin haraban school din don bako wani mai mashin ake bari ya shiga ba har ciki ba. Da yake safiyane saiga wasu mutum uku sunzo tare nan muka garzaya zuwa cikin school din dasu har kofan science department ya kaini ya aje zan fita yake fadin to kanwa ko zan anshi lambarkine idan kun tashi inji ? Banda waya na bashi amsa kai tsaye a zatonsa gatse nayi masa don budurwa kamata za ace banda waya hakan yaba sauran daliban dariya sai lokacin nasan na kwafsa ma son dariyan da sukayi din. Ya juya yana fadin to idan kin fito anyi dace na shigo na karasa dake waje ai ina nan ko yaushe sai yamma nake barin nan din. Godiya nayi mai na juya nacigaba da tafiya gabana sai faduwa yakeyi a lokacin kai tsaye na kusa kai ajin yan tsirarun dalibaine zaune maza da mata don lokacin ba a gama registration ba. Kuma gashi safiyane ba a taru ba hakan yasa na danyi siririyar sallama ina rabon ido mm a hango gefen wani taga can baya ba kowa na nufi can na zauna a takure. Ni ba waya ba balle in kalla kuma ni ba littafai ba balle nace zan danyi karatu a lokacin hakan yasa na duka kawai kamar mai tunane. Ina a haka naji ajin yayi wani tsit lokaci guda da sauri na dago kai dan ganin meye yake faruwa wanda nagani a gaban aji tsayene ya sa gabana faduwa lokaci guda. Yana saye cikin suith din maza dark blue tayi masa kyau sosai ko wancan ranan a cikin irinsu na gansa saidai wancan bakakene suna da kuma bambanci da wanan. Lalai ya tabbata magana Ammah ya fito ashe shi din malamine dama a wajen da farko ban fahintar me yake fada saida na kwantar da hankalina na fara gane bayani yakeyi wai zaiyi test idan ya gama. Don turancinsa zaki rantse da baturen gaskiyane shi yadda yake kara harshen shi a lokacin don hakane idan baka natsu ba baka iya fahintar shi. Kalon kalo naga daliban sun fara a tsakaninsu don ban gane me hakan ke nufi ba yasa ban wani damuwa ba abunda da dai na sani zan rubuta ai in mika mai. Yawancin abinda akai muna ne a secondry ya maimaita muna kafin ya fara rubutu da dan sauri sauri lokaci guda nida ko pepper banda na fara tunane sai gashi ya raba muna pepper's da kanshi . Har answer wanda zamu rubuta fasahan mu tunda na duka ina karatu question pepper din ban dago ba sai da zan fara rubutu na tsaya dauko biro dina ba tare da wani fargaba ba na duka na fara rubutu yana tsaye kyam yana rabon idonsa ga kowan mu a gaban aji fuska murtuk a lokacin. Badai nice ta dayan kaiwa ba amma zan iya cewa ina cikin na farko da muka mika kowa kuma ya mika zai fita wajene kai tsaye. Fita nayi na samu sauran wa yanda suka fara fitowa din na samu can dan nisa dasu na tsaya ina bin ko ina da kallo don dai ni sabon shiga ce zance ga komai. Allah ya rufa min asiri yawancin abinda ya tambayemu na dan sansu don yawan bitan littatafai da nakeyi nawa textbook hakan ne ya taimaka min. Nan nake jin halaiyansa wajen su daga inda nake zaune din kamar ban tare dasu sunan malamin dai yakai ukku ko hudu shine malam bash ko malam dan kwalisa ko bakin bature mai wuyar sha,ani duk dai naji sunan ne a dan tsayin da nayi a nan a takure nake zaune naji kamshin turarensa ya daki hancina ashe shine ya fito zai tafi hakan yasa na dago kai in kallesa caraf idon mu ya sarke dana juna nayi saurin sauke kaina kasa da sauri. Har yazo da dan saurinsa ya shige wani lungu nan kan ranan yasha zagi kowa da abinda yake fadi a kansa lokacin son sun fahinci makyatacine shi daga zuwa sai test haka don Allah ? In turanci yake ji ko wani abu meyasa ya buge ga koyarwa yana abu kamar wani boss can wata mace ta fada a bayana. Shigowan wani malamin yasa aka nutsu don daukan darasi lissafine tsatsanta bayan na wacan da muka buga don haka koda muka fito kaina ya gama daurewa a lokacin. Don yanzu nasan na shiga karatu wanda bana secondry ba balle primary don haka na dawo gida a matukat gajiya sai da dan huta na mike na fito taya Ammah aikin gidan har zuwa lokacin da Abbu ya dawo daga kasuwa. Ranan zaune yayi ina bashi labarin abinda ya faru a school din yake fasin dama karatu sai an dake Nanata Allah yasa kina da himma da kwazo kan hakan saiki kara maida hankali sosai don Allah. Matsalan da yanzu naga Abbu yana fuskanta shine na yawan cacan kudin abun hauwa da yake min inda har ya fara korafin hakan naji. Ba wai Abbu ya nuna ya gaji da hakan bane a kaina neman mafita dai yakeyi yadda abin zaizo masa da saukin Allah saboda yana korafin wurin yayi nisa damu sosai don ma wanan dan abokin nasa ya tausaya masa ya dan rage masa kudi yadda sukai ciniki. Allah yasa ina zaune a wajen da yake magana ba kasafai nake yawan tsoma masu baki ba bansan ya akayi ba ranan nayi subul da baka ina fadin Abbu ka fitar da sarkokin nan mana ka cika kudin gidan da kayi magana kwanaki. Kafin in rufe baki naji Ammah na fadin ji mun yarinya akan karatun naki za a sa sarka a kasuwa aje sayen gida dashi ? Kai naga Abbu ya dan girgiza kafin yace da ita mayar da yukanki kube Ammamatan nima ba zanyi hakan ba ai don nasan abinda nake yi karatu kuma yarki ta fara ke nan sai ta zamo wani abu a rayuwanta insha Allah hakan nake fata ko bayan raina. Nauyi da kunyar abinda Ammah tayi taji ta koma fadin ni malam aiba nace wani abu bane kada dai ita nana din ta dawo kuma babu kayanta an batar dasu kaga hakan ba zataji dadi ba ta bamu amana munci ke nan. Din wa take turo wanan kayan a nan yanzu ina dai don yarinyar nance amfanin karatunta baifi na ajiyan sarkokin nan ba ashe Ammah? Tayi shiru hakan yasa na mike tsam na koma daki sarka dai guda ukkune banga dalilin aje wanan kayan ba ga bukatansu ya taso mutumin nan yana iya kokarinsa wajen ganin ya ban kula da karfinsa da abinda Allah ya hore masa amma kamar Ammah bata duban hakan ita. Irin wanan tunanen na kwana dashi a raina da safe da Abbu zai fita rakani na dauko maganan inda na kara bashi shawara yace zai duba insha Allahu. Don sam baison kan abin duniya ya samu matsala da uwayena Allah zai bashi mafita insha Allahu duk da hakan ban dadara ba na daiyi shirune a lokacin. Bayan na dawo kuma na kara tuntuban Ammah kan zancen sai cewa da tayi dani ta gane ina son hadata da mijintane da yar uwarta. Nakan zauna inyi mamakin irin tsoron da Ammah ke ji akan nana wani lokaci Abbu dai bai taba kayansu ba kuma bansam yadda akayi ya samu kudi ya saida gidan nan da muke ciki ya cika ba duk a cikin dan kakanin lokaci. Sai ji nake ana fadin wai zamu tashi daga unguwar nan da muke ciki hakan yasa muka kara matsa kusa da unguwar yan uwansu Abbu don zan iya cewa a unguwa dayama muke yanzu dasu. Abbu sam bai iya mikani daya daga cikin gidajen yan uwansa in zauna yace don yan uwansane shiya san halaiyan kowa da ace ni yarsane ta cikinsa da zai iya yin hakan gareni. Da dai wasu dalilai daya barwa kansa sani ya sayar da gidan nasa muka koma sabon wuri amma Ammah kance wai akan dalilin karatuna da baida amfani karatun mace da yake ragage gareta tunda aure zatayi. Sai gashi dawowan mu nan sabon wajen a yanzu Ammah din tafi kowa jin dadin hakan saboda sana,anta takeyi sosai a unguwar kuma ya karbu don tana saida kayan miya. Tana dahon taliya tunda safe kuma tayi na rana haka na marance yara harda manya suna shigowa sosai saye sai ya kasance kamar mun shigo da sa,anmune cikin unguwar. Karatuna yanzu kuma yana cigaba sosai don kaina a kullum kara budewa yakeyi don banda wasa haka nake raba dare ina karatu sosai don kare mutuncina. Nan yan uwa suka fara dan kus kus akan dawowan mu nan din don sunyi mamakin yadda za ace Abbune ya sayi wanan gidan da kudinsa wai kullum yana yawo akan keke. Shi dai Abbu din yakayi murmushi kawai idan suna zancen a gabanshi don ba huruminsu bane da dole sai ya zauna ya fada masu illa iyaka shidai ya barwa Allah sani don baiwane daga Allah hakan gareshi. Cikin haka mukai hutu makaranta don dama koda naje an danyi nisa ga karatu lokacin don hakane nayi dan watani muka samu hutu. Sai lokacin na fara tunanen wani makaranta zan jona islamiya don ci gaban karatuna a lokacin akwai gidan wani tsohon mai kudi dake da wani babban islamiya can nacewa Abbu ina son a kaini naci gaba. Inda Abbu yaji dadi sosai da wanan shawaran tawa baiyi sanyi a gwiwa ba ya kaini saidai irin kalubalin dana samu a wacan unguwar shina samu a nan din na yawan kallon da nake sha gun mutane balle a yanzu dana zamo yar matshiyar budurwa. Ko a jami,a hakan nake samun wanan matsalan dasu wasuma a gabana zasu dinga gulmana saukin abin banda abokiya ko wani kungiya ni kadai nake karatuna da komai . Gashi ko wani malami yayi aiki zan haye don maida kai da nakeyi har sauran yan uwan karatuna suka fara zargi waiko dai suna banine wani malamin mu dan dattijone ranan da yai muna aiki na samu yace bai yarda ba saina fito na wanke kaina gareshi . Haka na fito din nayi solving a gaban kowa tun daga wanan ranan suka daina zargina ga malamai na samu saukin hakan garesu. ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/14, 10:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,, JA YA FADO,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 2️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8