cikin shiga irin ta hausawan asali da hakan ya kara fito masa da suransa dakyau ga wani shadda sun saka a jiki faril sol sai maiko yake da yauki a jikinsu.
Har lokacin uwar tana zaune a falo fuska daure shima ganin hakan yasa ya dan gaida ita sama sama yasa kai ya fita bayan yayi mata sai sundawo.
Basu dawo gidan ba a yadda suka saba sai sun tafi sun kaiwa kakaninsu dake raye gaisuwan jumma,a muddin suna gari akace jumma,a tayi sun saba da hakan.
Sai dare suka dawo nan falo suka samesu lokacin Abbansu ya dawo daga tafiya shima suka zauna suna gaisawa dashi cikin fara,a yakewa dan nasa ba,a da fadin malami yau yaya kuma ?
Mamin ku tace ka dawo hasale kana masu cicika ba gaira ba dalili jin hakan yasa ya kawar da kansa gefe daya kafin kuma ya juyo yana kallon salma din .
Da sauri ya girgiza kai yana fadin mami na fada maki wani abu don Allah da muka shigo ta kallosa cikin takaici tana fadin koka fada fa aishi yajawa kansa koma meye.
My friend bani labari yaya akayi kallon Bashir din yayi yana matse dariyansa kafin Bashir din ya dauki filo yana jefa masa ganin hakan yasa ya cabe filon yana fadin ka jefeni to saina fada kuwa.
Yauwa fada muna mu tayashi fushin muma muji kowa ya taba min besty na baisan ba,a tabawa yallabai kakansa ba a zauna lafiya ?
Abba gamo fa yayi da aljana yau muna batun dawowa gida shirin jumma,a muka ganta tsaye a wajen motarta jin hakan yasa kowa dagowa yana fadin Aljana kuma ?
Yace a itace ta bashi tsoro Abba wallahi koni na firgice da farko nan mami din tace wai tsaya wasa ko gaskiya don Allah ?
Yace mami saura kiris in kawo maki shi gida shame shame aiyau saidai nima a tsorace din nake a lokacin nan ya kwashe komai ya fada masu daya faru dasu.
Sukace me zasuyi in ba dariya ba suma har uwar da da fuskanta ke a daure a lokacin take fadin kagani ko kaga abinda nake fadi ko.
Ni wanan tsarin sam bai mun ba wallahi mami Allah da farko na tsorata lokacin data dago wasu manyan idanuwa nata tana kallona dasu.
Sai dai dana tuna da labarin Alh da yace inda ake gane aljani a wurin kafa yasa nayi saurin kai idona akan kafanta na kalla naga shegiya kafarta sumul suke yasa ban razana ba.
Yallabai kajima sunan da suka nada masa ashe a school din mahaifin yace toba lectural bane sunan komai ai zakiji a garesa yanzu balle yadda suke ganinsa haka duk bat da kamasa sai sun zargi wani abu a kansa ai.
Z
[8/3, 9:18 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
0️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ya kasance Assabar yau tunda safe nayi wankan tsariki don ina fashin sallah dama ban dade da farawa a yan kwanakin nan don Allah ya rufa min asiri na fito cikin irin matan da basu saurin fara al,ada da wuri saboda banyi sauri fitar da nono ba da wuri.
Sumana ma,ana gashin kai yakan dameni don tsayinsa haka bakan damu Ammah data yanke min da farko tana yanke min din yakai sau biyu ranan Abbu ya tsaya ya haukace mata cikin gida kanwai tana bin ra,ayin yarinya kamar tana kafirtani.
Ba Allahne yaso ganina a hakan ba yai min wanan baiwan wasu na nema ni Allah ya ban kuma tana nuna masa rashin godiya.
Haka ya juyo kaina yayi min nasiha sosai mai kashe jiki tun ina yarinya nakuma rike wanan nasihan nasa a raina don yace a gobe kiyama sai wanan suman da aka yanke yayi shati,a damu akan Allah ya turosa bauta mun hanasa a duniya wanan ya kara firgitani.
Yasa a yanzuma da sumar yai min bala,in yawa ako yaushe saidai na dunkuleshi cikin wani tsohon ribon nawa na daure bakima sanin tsayinsa yadda nake tattarasa.
Shi kuma giran ido dole na barshi hakana don tsoron tabawan da nakeyi kamar yadda Abbu ya tsorata mu tun farko gaskiya Abbu dattijon arzikine mai mutunci kawaici halarci kai bansan ya zan suffanta maki shi ba don kare hakkin iyalinsa dama na makwabta da yan uwa.
Don ko yanzuma din da na gama sallah ina zaune a daki na barbaza suman kaina don yasha iska ina son zuwa gidan maman Aimana don ita kadaice ke min kitso a unguwar idan na tashi kitse kaina randa naga dama don sai inyi wata ukku ban yarda an taba min kai ba tun amma na fadan haka insha duka da muzanci a school har suka gaji suka kyaleni don idan nayi kitso sai nayi ciwon kai sosai daga baya.
Amma yanzu da nakan danyi kalaba ya rage min ciwo yasa nake son zuwa gun maman Aimana ta kwashe min kan nawa din.
Duk hakan na cikin zumudin zuwa school a gareni yadda naga yan matan wajen acan acan dasu kowa na nuna banjintarta a wajen da baiwan da Allah yai mata.
Duk da ba hakan a raina har ga Allah amma ba zanso tsayi a muzance ba nima tunda nima yar adam ce kamar kowa .
Muryan Abbune nake ji daga dakinsu yana fadin da farko abinda na fara tsikaya shine nayi tunane mai yawa wallahi akan zancen nan Ammamatan .
Jeka ka dawon yarinyar nan yayi nisa da yawa donshine nayi tunane da in saida gidan nan in koma can kusa da makarantar nasu in samu dan fili ko dakuna biyune in saya.
To kinsan mutane sai banji sun taya gidan nan da amarshi ba gashi naga wani gida mai kyau an karasashi da dakuna hudu ke gida ga kitchen ga bayi ako wani daki koda na saida wanan din sai nayi ciko sosai zan sameshi amma gaskiya da zamu sameshi mun keta rainin sa,oin mu mun shigo zamani muma amma ina hannu bai kai ba.
Ammah naji tana fadin haba malam yanzu duk akan Aeesha ka hana zuciyarka shakat haka har kana zancen saida gida haba dai fissabilillah abin yayi yawa ai.
Yawa fa kikace Ammah yawa fa ko kin manta rayuwan mu a karkashin innuwar yarinyar nan ya takalla,ane ko kin manta wanan ma da muke ciki ta dalilinta muka sameshi ne ?
Ko so kike gobe kiyama mu tashi Allah yana tuhumarmu da kasa rike amanan daya bamu nata don ni nasan an haifo nanane saboda mu a yadda na yanke a zuciyana.
Don baki san hikimar ubangiji na zamanta a wajen mu ba a yanzu don me zamuyi sakaci da baiwan da amanan da ubangiji ya bamu kuma ?
Yau in bamu shayar da yarinyar nan dadi daga atzikinta ba sai yaushene zamuyi hakan a rayuwan mu idan mune yau bamune gobe fa Ammah.
Wani tausayi da kaunar Abbu na kara jin yana shiga min rayuwa da hakan yasa nakai kwance ba shiri nama manta da saurarensu don da nakeyi don dama ba komai nakeji ba sai wanda iska ya koro min.
Sai can har barci ya fara dibata naji muryanshi yana fadin nana ta kina inane Abbuki fa zai fita ko yau ba cin taliyar hausance.
Zubur na mike na fito ina kokarin saka hijjab nake gaidashi da kwana duk da tun safe mun gaisa amma ka,idanr in kara gaidashi don har ya saba da halina.
Abbu yau ba taliya nake so ba zan je kitsone kudin kitso za a bani na fada ina kai kaina kasa naji suna hada baki wajen fadin a,a,a yau din ?
Nayi murmushi nima da har gefen kumatuna yake dan lutsawa a hankali ya fara lalaban aljihunsa yana neman kudi kafin ya zaro yar dari biyar da dari biyu yana miko min yace wanan na kitso wanan kuma na taliya ai ina zai isa ko ?
A, malam kaida Aeesha dai sai Allah yanzu fa na gama tambayanka kayi mirsisi ka hana min amma ita yanzu fada daya ka dauko ka bata to Allah ya kara budi da nisan kwana angode sarkin da aikawa ya sani.
Yanzu kika gyara maganarki da sai ince ko kina kishinku na matane kuma kan yarki yanzu tunda kinga kin hanani karo maki abokiyar zama na hanu kuma.
Waceni aiko me kaiwa nanan taka yau nikaiwa don wacan nana din da aka rabamu da ita da karfi da yaji wananma ta samu gurbi a wajenka.
To bagashi ubangiji ya musaya muna ba da wanan da mukai hakkuri tace haka har ya soma tafiya yake fadin kinsan arzkkin da zamuci nan gaba gun yar nan tawa kuwa .
Dadin hakan Ammah taji har ta kasa boye farin cikinta tace Allah dai yaja nisan kwana ya nuna muna lokaci lafiya muka amsa da amin.
Tsaye yake a bakin window dakin ya kurwa haraban gidan nasu ido yana nazari kafin ya taka zuwa tako daya yana sake labulen tagan don ganin motar data doso gidan a lokacin.
Dan guntun tsuki yaja ya juya ya nufi bandaki ya dauki lokaci a ciki kafin ya fito a natse yake komai nasa kamar baiso har karfe taran safe yakai wai a hakan sammako yake sonyi zuwa aikin dashi kadai yasan abinda zai kaisa a yau din.
Kusan duk weekend hakan yakanyi yaje gun aikin nasu yakan jima a office dinshi da mahaifinsa yasa aka tsara masa komai najin dadi ba wanda govenment ta bayar ba kawai.
Ko office din daga can bayane inda ba wani hayaniyan mutane da yawa wajen don haka ba kowa bane mai zuwa wajen sai yan tsirarun mutane don ba kowa ma yasan da office din nasa ba a wajen.
Kamshinsa yasa duk suka juyo lokaci guda suna kallonsa tare da fara gaidashi da kwana yan kanninsa sukeyi kafin bakuwar nasu tace wai dama Bashir na gidan nan ?
Yana nan hjy Kura mami ta fada a dan dakile ya juyo yana fadin ina kwana bai jira amsanta ba ya fice mami na fadin ina zaka baka ko karya ba yake fadin na makara mami ana jirana a office.
Yasa kai ya fice uwar tana fadin salman din fa ganin baiko juyo ba yasata jan guntun tsuki tana fadin wanan halinsa sai a barshi yaro da kafiyan tsiya haka ?
Ki barsa hjy Hindu halin ubannasa ya kwaso kinsan fa jinin nan nasu na sarauta dole yana yawo a jikinsu ko mu mata wani lokaci ai kinga yadda muke dai balle n su ?x,,d7z
rj Salman din daya fitobb ed4e7se7sns7 737 ja cikin sauri saidai ganinsuf, ,,4j 7 a falon yasa yaja b tsw2asss#*#2aya yana gaidasu da kwana kafins mami tace dasmmd.i,ix.x.4id.hi kays 7u tafikkr55gr kar ya wuce daivk kasan halinsa dai.
Ai ina jin ya tafi ma mami zan sameshi na dan makarane yau salman din ya fada to ka zauna ka karya mana tunda ya fita no mami bari dai in samesa ya fada.
Ke husna hada masu breakfast din su tafi dashi can cikin basket da sauri wace aka ambata da husnah din ta mike don hada masu yadda mami din ta fada tayi.
Shi kuma salman din ya koma ya dauko key din motarsa daya baro a dakinshi kodaya fito ya samu yarinyar ta gama hada komai a basket zai dauka yaran sukace bari mukai maka yaya suka dauka suka bi bayansa.
Bayan sun saka mai a bayan mota nan Azima ta marairaice tana fadin ya salman ka sawo muna tsaraban hanya don Allah.
Ya saba da hakan indai ba tare da yayan nasu zai fita ba zasu labe susa ya sawo masu tsaraban hanya shine irin masara gassa ko dafafe yalo mangoro agwalama duk dai abin yayi a lokacin ko rake tunda ba samun sukeyi ba kuma suna da sha,awansu tunda ba,a sayowa gidan shi kuma sai ya kwaso masu shi da yawa har sai ya lalace an zubar.
Nayi sa,a mace daya na samu a gidan duk da uban sammakon dana bugo itama din saura biyu a karasa mata zakice uban sammako ta bugowa maman Aimana din.
Bayan mun gaisane da ita take fadin Aeeshace ina an aikokine ko na girgiza kai tare da neman waje nakai zaune ina fadin kitso nazo mama.
Cikin mamaki take fadin yau wace rana Aeesha yaushe rabonki da kanki ya samu kitso yau anga dama ke nan dai ?
Murmushi kawai nayi mata take fadin ina maman Aeesha nace tana gaidake lekowa Aimana tayi tana fadin Aeesha ce a gidan hakan yasa na mike zuwa dakinsu din kamar ba nice tazo gidan mu ranan nayi banza da ita ba a namu gidan .
Duk dai muna haduwa ai kullum islamiya dasu zan iya cewa dasu kawai ma nayi sabo akaf unguwarmu din a yanzu.
A cikin zance nake fada mata ranan monday zan fara shiga school daukan karatu aiko tayi zubur zuwa wajen maman nata tana fadin gashi har Aeesha an gama mata komai zata fara shiga makaranta ranan monday ita shekara biyu ke nan tana zaune gida zuwa lokacin sun karasa kitson uwar na tukewa matar kai .
Hakan yasa matar ta dago ta kalloni da sauri take fadin maman Aima wanan yar bahaushiyace kuwa maman Aimana tace hjy bagata kina jin muna hausa ba da ita.
Tubarkhallah masha Allah ta fada bayan ta mike na zauna ina fadin kalaba mama din tace ai dama na sani kitson ki bai wuce wanan ke ta dora da fadin manya ko kanana ?
Da sauri nace manya mama ina tuke hijjab din kaina dama shi kadai na saka a kaina ba hula ko dan kwali tunda kan a banye yake min.
Nan matan ta sake kaiwa zaune tana faman zuzuta kan nawa da ace ta sani da bata zauna din ba don ni abinda na tsana a rayuwana ke nan.
Haka kuma ga zafi da nake ji har nakan kamawa mama din hannu don zafi wani lokaci sam banson abinda zai taba min rayuwata don haka nake akoda yaushe .
Dan abu kadan zai tabeni yanzunne jikina zai ja a gurin da abin ya dan tabani donshine ko yaushe zaki saamu dakina tas don hakan yakan ban wahala.
Shigowar wata da suke da ssanaiya da matar farko yasa gaba dayansu suka tsaya sharfi akan nawa kafin su gaji dayan tayi sallama ta wuce ya saura macen dakebi mun ta rage a gidan.
Ina Allah Allah in tashi saiga wasu har mutum biyu sun shigo a lokacin da kyat na samu mama ta tsaya kama min kan na fito na barsu ko sallama bamu samuyi dai Aimana ba a lokacin.
Ban shiga gida ba na biya gidan da ake murda taliya a unguwarmu na sayo na nufo gida da kyat na gama sulala taliyan nawa saidai bankai ga ciba dole na kwanta don kaina dake min ciwo.
Ammah data zaci nagama bataji nayi magana ba ta dauka don ta kishingidane lokacin ina zaton barci takeyi ta fito tana fadin kin gamane Aeesha ?
Taji shiru hakan yasa ta nufi wajen da ta hago tukuyar aje na sauke na aje budewa tayi taga ban taba ba yana yadda na dafashi aje.
Hakan ya bata mamaki ta taka zuwa kofana tana magana sai ranta ya bata ina bayi kila kamar zata tafi ta dan leka hangoni tayi a kwance nayi rub da ciki kwance din.
Salati ta soma tana fadin yau ga tsiya ki gama abinci makin ki zauna kici sai ki dawo daki ki kwanta kuma don shashanci.
Ke Aeesha fa ta ambaci sunana da dan karfi hakan yasa na dago na dan kalleta da idanuwana da suka kade sukai jawur a lokacin.
Subbahanallahi badai kitson bane yaja maki ciwon kai kuma yanzu kasa magana nayi sai kai dana kada mata kawai.
Ikon Allah ta fada hankali tashe ta koma ta shiga dakinta sauran magani ta dauko min kwara biyu na panadol daya rage ta debo ruwa a randa ta tsureni saida taga na shanye ta juya tana fadin .
Daga ciran kaya sai ya zamo kari ni tunda nagane hakan na daina damuwa da zancen kitsonki Aeesha ayi mace ace ba gyara ni na taba ganin hakan inba gareki ba ?
Allah sarki duhun kai da jahilci ya hana Ammah ta gane cewa har yanzu jikina da nasu halittansa akwai bambamci sai take ganin hakan kamar wani surface kawai jikina keyi don ko nan din akwai ai wace bakace amma hakan yana faruwa dasu sai ya kasance mace bata son abinda zai taba lafiyan kanta din.
Shan maganin a sannu kan ya fara lafa min jin yadda Ammah ta matsa min ne kan in tashi inci abinci yasa na dan fito na tsankwara zuwa dakina ina dan loma biyu bakina ba dadi don haka na koma na kwanta.
Koda salman ya shigo office din kai ya dago ya dan kallesa sau daya yaci gaba da aikin da yakeyi ba tare da yai mashi magana ba.
Basket din abincin da ya shigo dashi ya aje a gefe yana kallon wanda ke tsaye gabanshi a lokacin kafin yaji ya furta mai zaka iya tafiya amma ka maida hankali sosai don Allah ga aikinka .
Don kasan mutumin nan ya iya takon saka sosai da mutane ta yadda zai bat da kamanshi yayi aikinsa ba tare da an gane hakan ba yace yes sir ya sara mashi ya fita.
Sai lokacin salman din yakai zaune yana fadin good morning bai damu da amsawanshi ba yace a zuba breakfast ne yana dan kallonshi.
Kasa yaga yakai yana dan kwantar da kansa saman hannayesa da yayi makari kamar filo dasu don yaji taushi alokacin.
Ganin yadda ya kwanta yasa ya dan zuba masa ido kadan kafin yace dashi akwai matsalane yana mai kafeshi da idanuwansa.
Hannu ya karkada masa kafin ya gane nufinsa ya mike tsaye yana shirin fita jin dan uwan nasa yaja tsuki yana dagowa yasa ya dan juyo garesa yana fadin ka zauna kayi break din ka niba yanzu ba kasani.
Barin dawo akwai abinda zanyi a waje yanzun nan bai iya amsa mashi ba don kansa dake damunsa da ciwo ya kara kaiwa kwance din yadda yake da farko din.
Salman din yana fita yabi wani dogon corridor dake wajen da yake weekend ne yasa ba mutane da yawa a cikin school din .
Dan nisa kadan ya zauna yana fuskantar wani waje kafin can da sauri ya tura hannunsa a cikin alhijihunsa ya ciro wayansa kiran iPhone yana daukan wani photo ya mayar da wayan a aljihunsa.
Yakai wani lokaci a zaune wajen kafin ya mike ya bar wajen bai koma office din dan uwan nasa ba kai tsaye ya nufi cikin haraban makaranta tafiya ya danyi mai nisa zuwa wani lungu yayi abinda zaiyi a can ya juyo koda ya dawo har lokacin dan uwan nasa na a yadda ya barshi dan barci ya samu a lokacin da har yai mai nisa kadan jin an shigo masa office din yasa ya dago ksi yana kallon maishi.
Nan salman din ke fadin lafiya dai ko ya nuna masa kansa alamun shike damunsa dan shiru a lokacin hakan yasa ya zauna yana fadin ko zamu gidane don ina ganin ai kamar mun gama da yau.
Saida ya dago da kyau ya tsurawa dan uwan nasa ido kafin yace dashi akwai wani abinda ka samu ne a yau yace ba za a rasa ba amma sai nan gaba kadan zakaji komai.
Bai yarda da shirmen dan uwan nasa ba a yanzu don hakane ya kawar da kansa gefe daya kawai donshi baya son ma ya sako shi a zancen aikinsa ya dai fi barinsa a matsayin yaronsa kawai anan din.
Basu jima ba ya mike don tafiya gida har yakai kofa ya juyo yana fadin kazo da mota ke nan yace ehh ko dai na kaika gidane sai in dawo in dauki motar tawa.
No muje dai kawai ya fada dan haka daga shi har dan uwan ba wanda yaci abincin saida ya kai get yaba wanan yaron nasa ya karba yana godiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/3, 9:28 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
1️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Murna yaran suka soma hanin tarin raken daya kwaso masu shi a zatonshima zasuce basa son rake din sai gashi suna zanga masa godiya.
Yake tambayan su ko Bashir ya shigo don baiga motarshi a waje ba kuma yana gabanshi don shi ya tsaya yayi dan tsaye tsaye hanya.
Ya dawo dayan ta fada part din nasu ya nufa kai tsaye duk da kofan yana rufe a lokacin hakan bai hanasa shiga ba ya murda kofan ya hangoshi kwance haka yasa ya juya shima tare da mamakin dan uwar nasa.
Sai lokacin ya tuna da bai karya ba fa nan ya fito neman abinda zaici yayi sa,a sun gama abincin rana shiya zauna yaci ya koshi fita ya sakeyi .
Don shi ba irin dan uwarsa bane da kullum daga wajen aiki sai gida yana da abokai da yake yawan hurda dasu a cikin gari.
Wasa wasa har washegari ina fama da ciwon kai dole zuwa yamma na gyagije don kada Ammah tace banda lafiya ba inda zanje washe gari don na fahinci ita karatun ma bai kwanta mata a rai ba.
Dole cikin dakiya na samu jikin ya dan kara warware mun washe gari ko Abbu na dukan kofana na fito waje da sauri nayi haraman sallah.
Bayan na idar na hau murhu don banson bari Ammah da aiki da yawa don haka nice nayi muna abin karyawan safe.
Karfe bakwai saura har na shirya kamar yadda aka sanar min kuma yana a jikin timetable din da na saya ina tsaye kofan Abbu ina fadin Ammah na shirya.
Jin hakan yasa ta fito tana fadin yanzu yar kan bokon nan kike rawan jiki haka don Allah