Share this page
3 / 8
duk halinda yarinya ta shiga ku Allah yaba amanan rikonta ba wani ba. Yalon dake hannuna nake zumudin ci naji kamar ina taunar tsakuwane a bakina lokacin don yanayin dana shiga a lokacin. Saboda zargina ya zamo gaskiya duk abinda Ammah kewa kuka bai wuce zancene daya shifi mahaifiya ta wadda ta kawoni duniya ba a lokacin. Muryan Ammah ce ke fadin Aeesh me kikeyi a cikin daki daba zakizo ki dauki abincin ki ba sai yayi sanyi na fito jiki a sanyayye ina fadin na koshine Ammah. Dagowa tayi ta kalleni kafin tace har me kikaci kafin ta rufe baki nace yalo ta tabe baki tana fadin yalo abincine banda shirmen ki nidai dauko min kwanon can ki mikawa tabawa tsaraba. Kwanon data nuna min din na dauko nakawo gabanta ta bude ta diban masu lokacin na dauka zuwa gidan tabawa din dashi tunkan na shiga nake jiyo hayaniyarsu don haka sukesu da haniya kamar gidan dambe ko yaushe. Tana zaune tana raba abinci nayi sallama tare da gaida ita na mika mata ina fadin Ammah tace na kawo maki yan tsarabanta tace dazun nake jin ai ta dawo a wajen yaran nan. Juyewa tayi cikin wani kwarya dake gefenta tana fadin ai zan shigo yi mata sannu da safe ki gayar min da ita da dawowa na amsa da to na juya na fito kawai. Anan waje din na wuce su Abbu sunata hayaniyarsu ta maza akan siyasa kamar fada da yake akwai duhu a lokacin ban tsaya gaiyar dasu ba na shige gida ina mamakinsu. Ammah na daki lokacin don haka daga kofa na tsaya na fada mata nadawo da sakon ta bawa din na juya zuwa dakina. Kwanciya nayi don banda katabus a lokacin banda tunane da ba amsa da zuciyana ketayi akan zancen daya shafi mahaifiyata din. Wace fuskata yake min tsaye a hotonta dana gani wanda ban gajiya da kallo a ko yaushe ina faman ayyana abubuwa da yawa a zuciyana game da ita. Ina kwanciya naji Abbu ya shigo yana fadin kinga ikon Allah ko hadarine aka hada tako ina garin nan da alaman bana ruwan sama zaiyi saurin sauka garemu insha Allahu. Nima yanzu nake fadar haka a raina ai ganin yadda ko ina walkiya kawai ake sakewa sama makin ya shiga daki anan suka zauna suna hira a zatonsu nayi barci ko a lokacin. Tiryan tiryan Ammah din ke koro masa duk yadda sukayi acan din da abinda kowa ya fada akai sai faman fadin umm,umm ikon Allah dama shirinsu ke nan Abbu ke fadin. Kafin naji yace abinda nake so dake shine daga yau ki kawar da idonki acikin wanan zance don Allah ku bar masu suje suci in zasu iya in ba yau akwai gobe ai a wajen Allah. Kin ganni nan Ammah banson fitinan daya shafi gado ko kadan badai sun sayar da wajen ba to kuyi hakkuri kusa masu ido kuga ikon Allah ai inku matane suna ganin baku da yadda zakuyi akwai maza a cikin ku donshi dayyabu ba zai yarda ba haka kuma ba,a sab abinda gobe zai haifar ba ai ga bawa. Jikina ya kara sanyi da zancen su kamar ranan haka na kwana banyi barci ba duk iskan da akayi har aka gama ba ai ruwan sama ba idona biyu. Haka na shirya washegari na fita zuwa school kwana biyu sai rama ya shigeni na fara ramewa a tsaye don damuwa dana saka kaina. Saukin abin karama nake a lokacin amma ibada ya shigeni sosai a zuciyana haka nake fitowa a tsakar dare cikin sanda nakan fito nayi alwala in raba dare ina gaida Allah ina neman daukaka a wurin ubangiji. Yadda malaman islamiyan mu sukr koyar damu a kullum wanan sai banyi wasa da hakan a rayuwana ba na rike hakan sosai a zuciyana duk da bansan amfani hakan ba gareni. Aeesha nayi firgigit ina dagowa dagawa tare da kallon Ammah din ina fadin na,am Ammah itama kallon mamaki take min a . . Keko me kike tunane haka har kira ukku bakiji ba lafiyan ki kalau kuwa yar nan tunfa dawowana naga sauyi a gareki kardai wani abu ya faru dake a bayana kika kasa fada min Ammah din ta fada. Cikin damuwa da kulawa take min maganan tare da maida hankalinta gareni lokaci guda nace cikin sauri Ammah wallahi ba komai daya faru dani bayan ki . To meke damunki haka yar uutana yaki zo nan ki fada min ta fada tana nunamin kusa da inda take zaune a lokacin. Hakan yasa na karasa ina sakin hawaye nace Ammah a cikin muryan kuka sai kuma na kasa karasa maganan dana so fada saboda tuna gatgadin da Abbu yai min kafin ya ban tarihina din a ranan. Hankalinta ne ya tashi gashi kuma ina fadin ba komai saina fake da fadin mafalki kawai dai nakeyi akan wata mata. Mata kuma na gyada mata kai wace irin matace haka kuwa nashiga uku ni Ammah nidai inba manya bace ta sa min ke gaba haka ? Bari malam ya shigo ya bamu hayaki ayi insha Allahu inkin tirara ba zaki daina ganin ko wace muguwa ba cikin mafalkin da yardan ubangiji. Haka kawai ban damu da dan kowa ba balle wata muguwa tasa min ya a gaba don hassada da bakin ciki kurwanki kurrr wallahi. Sai ta jawoni tana shafan kaina tare da tambayana kanki dai bai ciwo ko na girgiza kai alamam a,a gareta. Nayi kukana ma,isha a saman jikinta kafin na tashi na fara aiyukana nagida don kada ta kara jefa kanta cikin firgici. Da Abbu ya dawone take fada mashi shidai murmushi yayi ya dauko hayakin ya bata ta tukaka min ina ji ina gani ba yadda na iya da Ammah don nina jawa kaina hakan a lokacin. Abbune ya zaunar dani yana min fada akan na natsu na cire tunanen komai a raina a yanzu in dai mayar da hankalina ga karatu in samu inci jerabawana yayi min alkawarin ina gamawa insha Allahu gaba zai kaini in karo karatu gaba da secondary da yar gidan malam iro ke zuwa. Wanan magana da mukayi da Abbu ya karfafa min gwiwa yasa har nasake na koma normal na watsar da zancen Nana a zuciyana ban mason in tuno da inada wata mahaifiya bayan Ammah. ZAINAB IDRIS MAKAWA [7/25, 9:54 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 0️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Duk wanan abindake faruwa azaton Ammah Aeesha bata sanda zancen uwarta ba duk ko da hannunka mai sanda da Aeesha din ta dinga munawa uwar nata amma. Hakan yasa dauke kai da zancen wata nana can a yanzu ta mayar da hankine kawai kan karatun da Abbu ya kwadaita mama zata gaba da secondary ta karo ilimi. Dama ta dade tana burjn hakan a ranta sai gashi yanzu Abbu da bakinsa ya kwadaitawa Aeesha din karatun a yanzu duk da ita yarinyar tasan abin yafi karfin Abbu din a yanzu. Don karatu ba wurin zuwan dan tallaka bane ba irinsune ke zuwa karatun boko ba don na diyan masu hali da fada,aji acikin kasa. Ance kwadayi mabudon wahala donko na kwadaita da zancen wanan karatun dashi nake kwana nake tashi tunda Abbu ya fada da bakinsa nasan da wuya bai cika min wanan alkawarin ba. Manya sunci da alkawari ga yaro gara kayiwa babba shimai fahinta ko hakan bai yuyu ba yasan kayi niya Allah ne bai bada ikon cikawa ba. Amma shi yaro har ya girma yana rike da wanan alkawarin a zuciyarsa bai taba mantawa da wanan alkawarin a rayuwansa. WANI GIDAN KUMA Matar gidance a zaune takewa wata mace baka maidan jiki kitso sana,ar wanan mace ke nan a wuni zata kitsewa matan unguwarsu kai a dan bata kudin da zai rufawa rayuwansu asiri a kulum. Kitsone da ake kira da kitson hannu na gargajiya na kasan hausa ko ince namu na yan Africa da yawancin matakeyi a kansu. Ita wanan mai kitson tas zata tsuncewa mutum kai ko waya ga kanka saiya tambayeka a ina akai maka wanan kitson wanan yasa take samun kasuwan sana,anta na kitson saboda matane na manya da yan kwalisa da suka amsa sunan su a gari suke zuwa irin wanan kitson duk daba banbanta kudin kitsonta takeyi ba amma don jin dadin kitson zasu iya daukan kudi mai yawa su bata duk da hakan bata fasa yiwa masu karamin karfi kitson ba a daidai kudinsu suma. Don kina matar wani idan kinzo kin samu koda yarinyace karama akan layi wanan ba zaisa taci maki layinki ba na kitson saidai ki tsaya akan layinki har azo kanki. Mace ta daban ita dukko da yawan surutu da akansan masu kitso dashi amma ita wanan kamar hakan sa,an kitson tane don idan ta kama kai bata taba magana. Saidai su yan kitson su yi ta hiransu suna zuba ana gulma wacan da waccan koda ba a san mutum ba don daukanwa kai nauyi za a zauna a tofa miyau baki a zance. Amma maman Aimana tana zaune gum da bakinta tana faman kwashe masu kawunansu tas in an gama a dunkule dan alherin da aka riko mata a mika mata a asirce. Yauma dai matane yan kwalisa sunkai bakwai akan layi gidan ya kaure da hirarakinsu daga can wata daga cikin matan ke fadin ke,,,, Sukai juyo suna kallonta take fadin yanzu naga wata ya a karshen layin nan saida gabana ya fadi don kyauwonta. Wata take tambaya halan wacece tace nima dai ban sani ba nan ta barni ina kallo zakice balarabiyace kai duk yadda akayi dai tana da hadi dasu saidai abinda ya daure min kai shine shiganta irin namu na hausawane zani da riga da dan kwali. Kila yar buzayece dai inji wata wata kuma ta karba da fadin kema ai kin sani ai duk zancen nan da sukeyi maman Aimana ta gane wa suke nufi amma batayi magana ba a lokacin. Aeesha cefa kila ta gani Aimana dage tsaye a kofan dakinsu ta fada matar ta dago tana fadin kin ganeta ke nan tace a unguwar nan suke aida zama. Yar buzayece ko sai lokacin uwar ta dago tayiwa yar kallo daya hakan yasa taja bakinta tayi shiru don kallon warning din da uwar ta jefa mata a lokacin. Duk da wasunsu sun gane hakan amma basuyi shiru ba don wace ta fara maganan take fadin gaskiya duk da ina mace saida na tsaya kallon wanan yatinyar yau. Wata kila yar wani mai kudine irin matan da mazan mu kan je niger su auro din nan tazo ta haifa mashisu haka dama abinda mazan mu keso ke nan ai. Gidan kitso ance gidan rakwato gidan tsincen mata anan zakiji labarin auren mijin ki ko ko zancen tarihin kishiyarki dama duk wani tarihin makiyin ki indai a gidan kitsone. Daya bayan daya take kitsewa matan kansu suna tafiya har akai ta karshe ita mai yawan zuba din nan ta kwashe mata kai tas tana sauri don ka,ida kitsonta karfe biyar zuwa biyar da rabi. Zata kakabe gidanta tas ta tsabtace ko ina yadda gashin kan matan kitsonta ba zai takura masu a girkinsu ba ko wani abinci. Wanan aikin Aimanace yanzu data girma ta saba da hakan don a cikkn hakan ta taso bisaga irin tarbiyan da uwar nata ta dorata a kai ke nan a kullum. Saboda ga kitso rufin asarinsu yake fitowa inda uwar ke samu tana masu yan lalurorinsu harma dana gida wani lokacin duba ga rashin karfin mijin da Allah bai hore masa ba sai dai shima bai zauna haka ba don yana da sana,ar yinsa da yake daukan nauyin iyalinsa dashi. Saida suka kare aiyunkansu yara sin zauna cin abinci maman ta fito daga daki tana fadin Aima ashe ba nahanki zuwa inda matan nan ke taruwa ba. Ban hanaki tsoma masu baki a zancen da zasuyi ba a cikin gidan nan ko kinga sa,ankine a cikinsu ? So kike kija min magana kin ganinan neman kudi da bukatansu ya kawosu wurinan da badon haka ba ba zaki gansu gidan nan ba donsu duka ba sa,oin yin mu bane kin sani. Donshi nake kama baki akoda yaushe kan ko wani irin zance da zasuyi a cikin gidan nan daga yau nayi maki kashe din karshe akan irin hakan. Kan yarinyar yana duke bata dago ba muryan uban ne daya shigo yake fadin meya faru yake jin muryan ta hakane don ita ta kasance mace da bata da son hayaniya dama. Dan dagowa tayi tana kallonsa tace ba komai sannu da zuwa ya amsa yana kallon inda yaran nasa suke zaune. Kafin ya shige daki juyawa tayi itama ta shiga dakin ta sameshi kaya yake kokarin sauyawa a lokacin saboda dare da yayi yake fadin kince ba komai kuma naji kina jawa aimana kunne ai ? Bata jine nayi warning dinta kan matan dake zuwa gidan nan kitso tabar shiga lamarinsu amma batajin hakan idan suna zancensu wani lokacin zakaji ta tsoma baki ita karama da ita ina ita ina shiga zancen manya don Allah ? Yace hakan ba kyau gaskiya ki dinga tsawata mata tundai irin matan nan da yanzu suka gane zuwa gidan nan ko ba a fada ba yan duniyane nima nayi tsoron hakan gaskiya. Amma da nayi tunanen halinki sai naga in dai kece ba za a samu matsalan komai ba kuma Allah ya kara karewa din ku dai bi komai a sannu. Tunda baku san inda suke fitowa ba haka kada azo watarana ace ai gidan nan wani jidali ya faru a dalilin zuwa kitso nan kinga sai anbi a sannu komai. Ya gama shirinsa ya fito waje inda tayi masa shimfida ya zauna yana magana da yaransa dake gefensa a zaune kafin ya mayar da hankalinsa kan yaran abincinsa. Yana budewa yaga tuwon shimkafa tayi lafiyayyen miya ya dago ya dan dubeta yana fadin yau ciniki yayi kyau ke nan haka banga abinda na kawo anyisa ba ? Nasan zakayi magana ai tukwicin kitso aka kawo min yakai kwano shida ko bakwai koma yafi hakan har da kudin kayan miya ta hada min wata hjy ce dattijuwa haka nayiwa kitson kullum tanawa Aimana ba,a tana kiranta da sarakuwar ta. To Allah ya saka mata da alherinsa shimkafa haka mai uban yawa har kwano shidda mama Aimana zatayi magana taji yaran sun kaure da fada a tsakaninsu. Wanan yasa ta dakatar da zancen dataso ta furta ta mike zuwa wajen yaran dake fada kan kashi tana raba masu gardama a lokacin. Ba komai sukewa fada ba dan kashin miyan data saka masune bakai nasu hudu ba wajen ta rabo shine dalilin wanan fada ta juya zuwa wajen telen miya ta dauko mai dan girma ta mikawa Aimana din da bataba da farko. Mijin na zaune yanaci gaba da cin abincinsa saidai hankalinsa na wajensu har lokacin kafin matar nasa ta dawo inda yake tana fadin. Naso in dan debawa Ammah koda kwano dayane daga cikin shikafan nan akai masu suma su dan sa albarka yace hakan yana da kyau shine zama tare ai. Ya fada yana taunan kashi don yasan koda matarshi taba aminiyar nata kuma uwar dakinta dan abinda ta samu batayi aikin banza ba. Don Ammah mutumiyar kirkice a wajensu dan zaman su tare zakace yar uwarsuce ta jini don abinsu a yanzu ya koma kamar zumunci a tsakaninsu. Don ko haihuwa tayi Ammah na tsaye da ita sai tayi arba,in zata zauna gidanta taga ta samu lafiya da karfi hankalin Ammah ke kwanciya hakan yasa itama Rakiya din ta dauki Ammah din tankar yar uwarta na jini a cikin unguwa duk kuma sanadiyar zaman unguwane kawai ya hadasu. Zan iya cewa dasu kawai suka yarda suke hurda na cancan a tsakaninsu har suna iya fadawa juna damuwansu wani lokacin wanan ke nan. Aeeshace take sauri don aiken da Ammah din tayi mata tana saurine don gudun fadan mahaifiyar nata don tasan aiken yana da muhinmanci. Duk kayan data jawo bai fita gareta don zama tsuman da kayan sukayi ko kuma suyi mata kadan sub dage mata a yanzu sakamakon girman da jikinta ya kara a yanzu. Sai wani bakin rigane wanda Ammah din tayi ta faman boyo shekara da shekaru sai yanzu kuma ta mannawa Aeesha din a yanzu don takai munzalin amfani da rigab a yanzu. Saidai tana jawoshi ta tsaya ta kurawa rigan ido na dan lokaci kamar tana tunane akai kafin zuciyarta ya bata amsa da kwarai tabbas sune din. Rigace wanda taga matar da Abbu ya ambata da nana kuma wai itace mahaifiyarta wace ta kawota duniya ta watsar da ita ta bata a cikin tsana da kyama a yanzu. Zakice matarce tsaye a gabanta a lokacin takewa kallon tsana da bakin ciki a zuciyarta lokacin wani hanzari tayi tana wurgar da rigan dake hannunta din tana cika tana batsewa tare da jera tunane a zuciyarta. Juyawa tayi bayan ta dauki rigan ta nufi kofan fita daga dakinta a lokacin saidai tana fitowa daga dakin tana jin muryan Aimana dake sallama tana shigowa gidan nasu a lokacin. Wanan yasa ta dagata daga yunkurin zuwa dakin mahaifiyar nata ja tayi ta tsaya dole tana amsa sallaman duk da zuciyarta ba dadi a lokacin tana fadin Anty Aimana kece. Ehh Aeesha ina Ammah tana dakinta ta fada sanin su ba bakin gidan nasu bane sun saba shiga dakunan nasu yasa ta fada masu haka kai tsaye. Tana tsaye da wanan rigan a hannnunta har lokacin bata koma dakinta ba taji Ammah na fadin Aeesha ina kikene wai dauko min kwano daga nan waje. Hakan yasa ta yada rigan a kofanta ta nufi inda roban yake ta dauka tana nufar dakin mahaifiyar nata a lokacin. Tana shiga dakin idonta ya sauka saman shikafan gwaunatin dake cikin roban da sukazo dashi din mikawa Ammah roban tayi ta karba ta juya ta fita daga dakin ba tare data tsaya nuna wani damuwa da abindake wakana a dakin ba. Miskilanci da izza da isa irin na Aeesha yana damun amma sin yarinyar duk yadda tayi ta rage wanan halin sai ya zamanto kamar tana kara ingizatane a lokacin yadda take haka ta saka hijjab dinta saman kayan ta fita zuwa aiken nata a lokacin. Sai bayan tafiyan yaran Ammah ta fito rakasu ta dawo ta hango wanan rigar da Aeesha din ta jefar a wajen cikin mamaki Ammah ta karasa wajen rigar tana dauka. Bin rigan tayi tana tuno da abubuwa da dama dasuka faru a sanadiyar wanan rigar da yar nata ta yasar a kasa a yanzu rigace mai dibin tarihi a wajen su don ya zamo rigace dake tuna masu da abubuwa da dama dasuka faru a baya. Da wanan rigan yar uwarsu ta baiyana a garesu cikin kunci da bacin rai rugume da kaddaran rayuwanta Aeesha da suke kyautata zaton da yau ba Aeesha a raye da yanzu suna rayuwa da yar uwarsu a cikin sallama. A hankali ta duka tana daukan riga a kasa tare da furta kayya wanan yar da ace kinsan mahinmancin wanan rigan a gareki Aeesha ba zaki taba gangancin yada rigan nan a kasa ba a yanzu. Bayan daukan rigan a cikin karfin hali sannu a hankali takai rigan a hancinta tana sunsuna don tabbatar da shakan abinda take sonji a hancinta lokacin. Kamar ta kadu don yadda tayi saurin cire rigan a hancinta cikin sauri bayan shakarsa da tayi na dan lokaci. Ba komai yasata hakan ba saijin har wanan tsawon lokacin wanan rigan yana kamshin yar uwarta da ta bata tsawon shekaru da dama. Wanan kamshin Nana ta dawo masu dashi tanayi wanan kamshin ita kanta yarta keyi wanda kamshine na daban wanan turare yakeyi kamshine da banda wajen yar uwar nasu a lokacin basu taba jin wanan kamshin ba sai kanta. Hawayene suka taru mata a idanunta lokaci guda don tuno da yar uwar nata tare kuma da irin bakin ciki da takaicin da dawowanta garesu ya kumsa masu a zuciya wanda har yau ya kasance tana girbansa ita a zuciyarta [7/30, 11:00 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND MAMAN BIBO KAYAN MATA 08068871330 KOKO ROAD SOKOTO JA YA FADO,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 0️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Murmushin takaici ta sauke ta kara kame rigan a jikinta kamar hakan zaisa ta jin saukin abinda ke kunar zjciyar ta tunane ta fada na dan lokaci akan hakan. Lokacin nashigo da sallamata idonane ya sauka akan rigan dake rike a hannunta rugume kamar mai tunane a lokacin. Cikin karfin hali idona akanta nake fadin Ammah na dawo tace ingaidake ta gode kaita dago ta sauke min kallo da idanunta da suka kada sukai ja a lokaci guda ba yadda na barta ba da zan fita. Na juya zan shiga daki naji muryanta tana fadin Aeesha yaki zo nan hakan yasa na juyo na dawo inda take rigan dake hannunta ta jefo min kafin na karaso gareta tana fadin. Kinsan daraja da muhinmancin wanan rigan a wajen mu kuwa da kika watsar dashi a nan wajen kanki daya kuwa idan baki sani ba yau ki sani wanan riga da kike gani darajarta tana da yawa a garemu. Saidana dan kara kallon rigan da take kokarin miko min na mika hannu na karba a hannunta makin na nufi dakina dashi saina nufi dakinta dashi a lokacin. Bina Ammah din tayi da kallo cikin mamaki tana fadin ina zaki dashi cikin sanyin jiki na juyo ina fadin dakin ki zan mayat don ni ban komai da kayanta. Galala tayi tana kallona a cikin mamaki kafin tace itawa ke nan banyi magana ba kawai nasa kai na fada dakin na aje rigan na fito. Har lokacin sai faman kallon mamaki take min don yadda na daure fuskana akan zance ba kuma iya fuska ba gaba daya raina a bace yake don zancen rigan nan data dauko min din a lokacin.

Chapter 3 of 8