u guys
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
💞⚜💞⚜💞⚜💞⚜💞⚜💞⚜💞⚜
*DAFIN SO*
STORY AND WRITING BY
*MARYAM ISMAIL*
{MAJI DA'DIN KAINUWA}
MARUBUCIYAR
SANADIN GATA
DALILIN SO
HANAN
YAUDARA KO BUTULCI
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
Fitattu sha biyar (15) 2020
Follow me on Facebook at
Maryam Ismail(maji dadin Kainuwa).
*page* 11 to 15
Tun a mota ya fara balbaleta da bala'i,"uban waye na ganki dashi acan tsaye?"
Shiru tayi a matsukar tsorace don ita kanta tasan bala'in Yaya Sulaiman yafi karfinta,wata Uwar tsawa daya daka mata saida tayi zumbur ta baro sit din motar tana kallonshi idanuwanata harsun kawo ruwa "ya ....ya shid'in ya kusa bigeni da...da mota ne"ta karashe maganar a matukar tsorace.
" shine kuma don tsabar iskanci zan tambayeki kimin banza,wallahi zan b'alb'allaki idan na kuma yi maki magana kikamun shiru"ya fad'a a hassale.
Bata kuma cewa komai ba ,don tasan donya tsaya ya jibgeta ba abu mai wahala bane ,Yaya Sulaiman beda hakuri ko kad'an shiyasa take matukar tsoranshi ,har Allah ,Allah take Yaya Sawam ya dawo daga tafiya koya koma kaita school.
Cikin wani tankameman gida sukayi parking ,fita tayi da sauri gudun karta kara had'asu ashe tabar Textbooks dinta a ciki.
"Ke ubanwa zai maki dakon wannan Yan iskan books din naki?" Ya jefo mata tambaya murya cunkushe.
"Kayi hakuri na manta ne"hannu na kyarma ta kwashesu ganin hararar da yake jefa mata yasa ta zunduma a guje cikin gida.
Kwafa yayi tare da Jan tsoki yayi waje abunsa.
(Nikam nace matar Sulaiman ta bani wallahi wannan jaraba haka).
Waro ido ta kumayi don ganin da gaske Yaya Sawam tage gani wani ihu ta saki ta ruga ta rungumesa tana fadin" Oyoyo Yaya Sawam dina,shine ka dawo baka fad'amun bako?".
Lallai nan nake ganin tsantsar kama domin babu abunda ya raba kamar Jannat da Sawam ,dondai yana namiji ne kawai,murmushi yayi tare da fad'in"lill baki girma har yanzu ba zaki daina rungumata ba,kinfa girma kuma kinsan ba kyau ko".
Turo d'an karamin bakinta tayi tana fad'in"to kaiba Yayana bane ba,kai komai baka so"
Shigowar Abba ya katse masu firan,ya shigo cikin Shiga ta alfarma murmushi bayyane akan kyakyawar fuskarshi ,kai tsaye tsakiyar Sawam da Jannat ya zauna yana shafa kanta tare da fad'in "a'a mutanan Lagos zuwa ba sanarwa sai kawai mu ganka"
"Abba sannu da fitowa,zuwan bazata ne kawai na gaji da hutun na dawo gida nima,nayi missing rigimar Lill"ya karashe maganar yana lekenta,itako tayi lamo jikin Abba batashi takeyi bama.
" ke kullun son jiki kamar Mage ,Abban ma saikin kwanta a jikinshi duk girmanki tashi maza kije ki cire Uniform dinki"Yaya Sagir ya fad'a dake zaune tun d'azu yana kallon yarintar da Janna ke saki.
"Idan bata kwanta jikin Abbanta ba,jikin wa zata kwanta Sagir" Abba ya bashi amsa.
Wani tuk'uk'in bak'in cikine ya turnike zuciyar Sulaiman yana ganin duk sakalcin Jannat dasa hannun Abba yarinya na SS3 bata daina kwanciya akanshi ba.mikewa yayi fuuuu hakan kuwa yayi daidai da fitowar Innata "au don rashin Arziki Sule bigeni zakayi,yaro sai bak'ar zuciya kamar ba misulmi ba ina dalilin wannan bak'in halin baka".
Wata Uwar harara ya watsa mata yace" inna tureki meye a ciki ni bani wuri Kafin kijiki a k'asa kur'an"yana zuwa nan yayi gaba abunsa sai surhwa bala'i yake.
"Sai dai ka ture Ubanka Abdullahi gashinan,d'an banza marar mutunci dakai"
Dariya Sawam ke dannewa amma saida ta fito har dukewa yakeyi don tsabar dariya.
Take kam Inna ta juyo kanshi "kaji wani marar mutuncin ko,yaushe ma ka dawo d'an banza mai Jan kunne d'aya bayan d'aya zanci mutuncinku nasan tsiyar dazan kulla maku Yan banza".
Tsalle Sawam ya daka tare da rungume Innata yace" I love u Innata".
"Kaga aekinku kenan,maza zauna Ku barta ta huta " Abba ya fad'a.
"A'a banni dasu duka zan iya dasu wallahi" Innata ta fad'a tana zama.
"Innata sannu da fitowa,bari na sauya kaya Nazo muci abinci kinji". Jannat ta fad'a tana mikewa.
" to y'ar Albarka jeki kinji"
Maida kallonta tayi ga Sagir "tokai ina Uwar taku kuma,da baka iya tankawa mutane don bakin hali".
Murmushi kawai yayi yace " tana d'aki innata".
************
Zaune yake daga shi sai 3 quarter da singlet cikin kayataccen parlonshi Wanda yaji kayan more rayuwa ko d'akin wata macen Albarka ,laptop ce gabanshi sai danne danne yakeyi Dr Ahmad(Sorry a baya nace Ahmad business ya karanta,mistake ne Dr ne ya karanci Medicine da fatan zaku fahimcenu) kenan,hankalinshi kwance idanuwansa sanye da siririn farin gilashi irinna likitoci.
Ko Sallama batayi ba haka ta banko d'akin ta shigo tana kare masa kallo dason ya tanka mata,banza yayi da ita don haka tazo kusa dashi ta zauna tana fad'in "yo aekin banza,waikai Amadu ubanmi ka dauki kanka,ko ubanka Dana haifa innazo wuri shi yake fara yimin magana".
Dafe kai yayi alamar y'ar tsohuwar nan ta fara takura mashi gaskiya,amma bece komai ba.
" au shirun zaka kuma yimin,nace ae maka aure duk wannan iskancin zaka barshi ne ae".
Hannu ta zura k'asan Table din da yake zaune ta janyo plate din abinci lafiyayye jolluf rice ne sai rabin kaza da koslow amma duka lomanshi batafi biyu ba ya ajiye,"yauwa na samu abun kamaka bari na kaiwa Hauwa'u(Ummi)wannan tasan wahakar banza takeyi bacin abincin kakeyi ba"tana zuwa nan ta mike.
Saurin riko hannunta yayi cikin sanyayyar murya yace"Granny please mana".
"Ja iri,yo uban menene hilis(please)kuma kasan nace ka daina man wannan shegen yaranyen da bana fahimtar komai a ciki,sakeni kuma dole nakai mata kamaji" tana zuwa nan ta fige hanunta ta fice daga part din tana sababi ta nufi part finsu.
Yatsanshi biyu ya saka yana murza goshinshi kamar mai luliya wani abu,lips dinshi ya datsa sosai kamar zai fasa,tare da furzar da iska daga bakinshi Wanda hakan ya zame masa d'abi'a,mikewa yayi cike da kasaita ya nufi part din Ummi.
"Aeke wahala kawai kikeyi dama kin daina kaiwa wancan mishkilin banzan yaron abinci,dondai zubarwa yake koya tusa gaba yaita kallo,yanzu kiji wannan don Allah don besan darajar abincin ba" Granny ta karashe maganar tana zama.
Wata kyakyawar mata na gani zatakai kimanin shekara 45 amma jikinta be nunaba yacce Kasan y'ar shekara 30,haka take tasha gayu da wani d'anyan less kwalakwalan dake jikinta da yanayin ta zaisa ka gane cewa tabbas Hutu da dukiya sun jiku a jikinta,daka ganta zaka hango tsantsar kamarta da Ahmad ,bako musu zaka gane ita ta haifeshi,Hajiya Hauwa'u kenan .
Sake da baki haka tabi plat din hannun Granny da kallo sannan ta maida kallonta ga Ahmad dake shigo yanzu,"Mama kinyi kokari da kika gano haka ,Ahmad bayajin magana Mama bansan meyasa bayacin abinci ba".
"Kema kinji ki da wani batu marar dalili ina yaro zai samu natsuwa bayan kinsan beda aure gashi da shegiyar kwakwa duk yabi ya zuke sai bak'in rai,wallahi mata zan samo mashi kuma dole ka aura " Granny ta karashe magnarta tana jefawa Ahmad mugun kallo.
Tsaki yaja "ke dallah bar wurinnan,anawa mutane magana kin zura idanu kamar na mayu" Ahmad ya fad'awa Saratu da taketa faman matsawa Ummi k'afa.
"Mugun banza Amadu abunda ka iya kenan" cewar Granny.
"Wai ke ba Sunana Amadu ba,u have to stop calling with that nonsense name" ya karashe maganar a has sale.
"To sannu Ubale,wato ubana kenan,ance Amadu kuma al-qur'an ka kuma zagina saina rama ni kake cewa citap(Wai Stop hhhhh),ja'irin yaro da Hauwa kake, silili kasau din banza mai kama da zabayyana mumunan banza" Ta karashe maganar tana nunashi da hannu tare da tab'e baki.
Wata uwar tsuka ya saki tare da zama kusa Ummi.
Karab Granny tace"tsaka ma da tayi Allah tsine mata yayi balle kai kayan banza".
Daukan plat din abincin Ummi tayi tana murmushi itakam tanason zaman Granny da Ahmad diramarsu na birgeta saidai ba ikon dariya."oya maza ka bud'emin bakinka tunda haka ka zab'a".
Kumbure fuska yayi tare da turo baki sannan ya bude kadan,Ummi ta saka masa spoon a baki,tauna abincin yake kamar yanacin magani dakyar yake hadiyewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihar raju'una ni Salame,wannan bankad'a har INA,ki tusa gardin Allah ta'ala kina bashi abinci kai hauwa bakiji dadi ba wallahi,ni kunga tafiyata kada kusa zuciyata ta fashe". Tana zuwa nan ta mike tare da wucewa hanyar d'akinta,da harara Ahmad ya rakata harta b'acewa ganinsa.
Da k'ar yaci quarter din abincin shima saida yaga ran Ummi ya soma b'aci yanaci yana yarfa hannu kamar wani Baby,shikam a duniya cin abinci shine babban abunda ke takura rayuwarsa.
*********
Bako Sallama ta banko kyauran gidansu ta shigo tana huci,saman katifar Goggo ta jefar da Jakar makarantarta tana fad'in" aekin banza wai meyasa kullun itace sama dani,kullun saita samu abu kafin ni"Madinat ta karashe maganarta tana huci.
"Saboda kinsa sanya,kin yarda kin zama y'ar kore kin nuna rashin wayo" Goggo ta fad'a Wanda shigowarta d'akin kenan ta tsinkayi zancan Madinat.
Murmushi Faty tayi dake zaune gefansu tana duba littafi"Haba Goggo ba haka ya kamata ki mata ba,kamata yayi ki nuna mata mahimmancin Jannat a wurinta tasan sun banbanta,ya kamata ta mayar mata da alkhairi kamar yadda ta taimaketa lokacin da take bukatar taimako ,amma saiki biye mata".
"Ke dallah wawiya Samara marar ilimi wacce ta gado bak'in hali irinna ubanta,kai wannan yarinya da asibiti na haifeki zance an canzamin ne,idan ba zaki bamu goyon baya ba kul na kuma jin bakinki ,me mugun baki kawai.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karashe*
*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
Pls
Vote
Comment and
Share
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇
🍇🌹🍇🌹🍇🌹
🍇🌹🍇🌹🍇
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇🌹
*DAFIN SO*
Story and written by
MARYAM ISMA'IL
*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* ✍🏻
*FITATTU SHA BIYAR (15) 2020*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
SANADIN GATA
YAUDARA KO BUTULCI
HANAN
DALILIN SO
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
AND NOW
*DAFIN SO*
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇🌹
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Page 16 to 20
"Dama aeke kullun duk abunda zanyi banyi daidai ba,keda baki da zuciya da kishin y'an uwanki haka zaki k'are cikin bak'in talauci,ni karki kuma shiga harkata wallahi" Madina ta fad'a tana nunawa Fati yatsa.
Girgiza kai kawai Fatima tayi tare da fita daga cikin d'akin yayinda zuciyarta ke mata wani irin kuna bawai kuma don kalaman da Madinat ta fad'a mata ba a'a ta sabayin fiye da hakan ma,kawai sai don tana guje masu dana sani da zasu iyayi ko wanne lokaci.
"Mtswww wannan yarinya da ke kaidai na Haifa da bak'in ciki ya kashe ni wallahi"
Juyo da kallonta tayi kan Madina tare da fad'i "ke matsoman nan kiji ".
Matsowa Madinat tayi tare da kanga Kunnenta jikin bakin Goggo,wata shewa ta dauka da ita donjin abunda Goggon ta fad'i " kai Goggo na,ur d best wallahi".
Sosai Goggo ta shiga farin ciki ganin yarda ta sauya y'ar tata daga damuwa zuwa farin ciki,sosai takejin nishad'i don farin cikinta na tafiya ne tare dana Madinat.
"Goggo yanzu zan fita,amma bazan jimaba zan dawo".
" To ,Allah yah tsare kinji y'ar albarka"Goggo ta fad'a tana mikewa
Shigowar Baba yasa ta daure fuska don dama jiranshi takeyi,ko zama beyi ba ta soma sababi"Allah wadaran mutum ya kashe zuciyarsa ka zauna ko wanne namijin arzik'i na tashi ya nema amma banda kai Malam sai faman rik'on carbi,sai kace shi zamuci,ka tanka ace ka fiye bala'i bayan kuma janka akai ,nayi dana sanin wannan auran kaddarar da iyayena sukayimin".
"Allah ubangiji ya shiryeki ,ke kullun cikin b'ata kike" Baba ya fad'a yana barin gidan gaba d'aya ma.
"Yo akwai Wanda ya kaika shiga b'ata da rashin sanin ciwan kai,ke maza shirya ki kawoman abun d'an tab'awa a baki tunda me Allah yasa baki kashe zuciyarki ba.
Madinat kam wucewa tayi ta sake wanka tare da tsukewa tayi gaba abunta.
*************
Kwance yake akan makeken gadonsa ,karan sigari ne hannunsa yana busawa cikin kwanciyar hanali,ya kwalar wine nan a gabansa yana sha,ya fita cikin hayacinshi kagare yake yabar Hotel din zaman jiran Jannat kawai yakeyi,mikewa yayi yana tangad'i ya fito daga d'akin da yake duk abunda ya tari gabanshi kwallo yakeyi dashi cikin b'acin rai.
" kai wanene wancan nike gani kamar Ashman,yau Allah ya nunamin shi,kasan cutar mai gida akayi aka bashi award wallahi bashi yaci ba"samarin dake zaune suke fad'a.
"Kuma da alama a bige yake"cikin hanzari suka mike da gudu sukayo inda yake,suka fara angazarshi,kanshi ya bugu da bangon wurin,hakan kuwa yayi daidai da shigowar Jannat hotel din,k'ara ta saki ta isa wurin da gudu tama jijjigashi tare da kiran sunanshi.
" ke cika kibar wurin nan tun Karin kema mu kwalbe dake,bakuga shigarta ba"d'aya daga cikinsu ya fad'a.
Sai yanzu suke karewa shigarta kallo,sanye take cikin wando jeans blue colour sai top white colour,hills ne black kafarta,yayibda top din keda pattern din black a jiki,siririn blue din Vail ta yane yalwataccen gashin kanta dashi,sai jikar goyon dake a bayanta,Wanda hakan ya zame mata al-ada shine shigarta ko yaushe.
Saurin mikewa tayi tare da bude jikara ta Ciro katon ba'ar Riga da nikaf ta sanya.
Cikin Mamaki samarin nan suke binta da kallo,baki na rawa suka furta"Secret super star"a tare.
Ganin suna kokarin janyo mutane Kansu don sun fad'i sunan da karfi tasa tayi saurin cire Nikaf din tana nuna masu alamar suyi shiru.
"Don Allah ko zamu samu sa hannunki?".
" why note,but pls Ku taimakamun mu maidashi d'aki"ta kare maganar tana nuna Ashman.
Ba b'ata lokaci suka kwasheshi tare da maidashi dakinshi suka shimfidesa a bed tare da lillibeshi,hannu ta sanya masu suka fita suna mata fatan alkhairi.
Wani farin ciki takeji a zucitarta yana ratsa ko ina a jikinta,tana matukar son taga tayi suna,kamar ko yaushe rife jikinta tayi ta rataya jitarta ta saita laptop ta soma rero sabuwar wak'ar da zata Dora a pages dinta,ba jimawa ta saketa,kafin kace me tuni an fara comments da likes.
Wani irin murmushine ya subuce mata ,da wani irin jin dadi da yake ratsa jikinta,burinta kenan a duniya taga tayi suna ta fannin wak'a kuma Alhmdllh ko yanzu burinta ya cika don't tana ganin masoya saidai fargabarta d'aya da masoyanta keso ta fito ta bayyana kanta a duniya kowa ya Santa.
Ba ita tabar wurinba said a taga Ashman ya daidaita sannan ta barshi yana bacci ta koma Gida.
Cike da fargaba take taka step din shiga main parlo na gidan da tsananin fad'uwar gaba ba komai yaja wannan ba said ganin motar Yaya Sulaiman a gida kuma ta tabbatar yau saita Allah"Assalamu alaikum "shine kawai abunda ta iya furtawa ta shiga cikin parlo tsaye tayi cak ganin mugun kallon da Sulaiman yake jifarta dashi da tuhumar daga ina kike" ke zonan daga gidan ubanwa kike?"ya jefo mata tambayar data rud'ata,jiki sanyaye taje gabanshi ta duka,d'aga idanuwanta tayi Wanda harsun fara canza kala don tsabar tsoro ta kalli tabkekiyar plasma din dake mak'ale jikin parlon dakin ,shirin mawak'a akeyi amma duka wurin wak'arta kawai ta bije dakin ga pictures dinta lillike fuska rufe a wurin sai sharhi ake akan ta fito ta bayyana kanta,juyo da kallonta tayi gareshi"Yaya kayi haku....."bata idasa ba taji saukar kyawawan Maruka har biyu a Jere,wani razanannan zafi da zugi suka ziyarci kuncinta tuni shatin hannunsa suka fito a kumatunta,hawayene sukaci faba da zarya akan kyakyawar fuskarta data kade tayi jajir.
"Ke yanzu Jannat wannan rayuwa?,kina zubar mana da mutunci yanzu wani ya ganki a hanya miye banbancinki da masu tafita Church, baki da aeki sai shigar kafurai har ki zagaye garinnan bakijin komai,anya kuwa kina da cikakken hankali" ya karashe maganar yana zare belt din wandonsa.
"Lafiyanta qlau Sulaiman,iskanci ne,nayi nayi tabarsa kayannan tak'i,amma laifin Abbanku ne tunda ko jiya saida ya siya mata wasu wallahi duk abunda Janna ta zama laifinsa ne ,so aeba hauka vane" Momy ta karashe maganar tana zabga mata uwar harara.
A bazata saidai jin saukar Belt rayi kota ko ina tuni ta rude ta rasa wurin sosai ihu kawai take saki tare da neman agaji,a guje Sawam ya fito "Yaya don Allah kayi mata hakuri".
" barnan kona had'a dakai wallahi"ya vashi amsa a hassale
"Wayyo Allah na ni Maryama na shiga ukku na lalace,Sule mai kake shirin yiwa takwarar tawa ,mugu azzalumi ka bigi Aysha gata nan tana kallonka karka kuma bugunta mugu mai kama da kumurci" Inna take fad'a da kuka wewewe.
A rude Momy ta nufota"inna don Allah kiyi hakuri ".
Tsaida kukan tayi cak tana bin Momy da mugun kallo" yau kaji munahinci Anya Aysha kinason ganin annabi kuwa,yarinya Ku daura mata karan tsana komai tayi ba daidai ba,ki zuba ido wannan gardin banzan yaita zabgarta,wallahi bari Audun ya dawo zaki Sani"
"Nifa kada ki kara cemin gardi wallahi"
"Sule nace ubanka ,yo kai menene inba gardin ba mai lasisi kuwa,ko nima dukana zakayi hatsabibin marar kunya,mai bak'ar zuciya"
Bude baki yayi zaiyi magana Hannu Momy ta d'aga masa,a dole ya hadiye maganarshi tare dajan tsuka yana jefawa Inna harara.
"Kai Sawa (Sawam),maza kama ta mu tafi".
Jannat kam kuka kawai take ruzga haka sawam ya kamata suka tafi d'akin Inna ,ta had'a mata ruwan wanka tanata sababi da masifa.
***********
Kallon idon yarinyar yakeyi kuri dason tuno tabbasa ya tab'a ganin mai wannan idon da irin kallonnan tuni ya Lula duniyar tunani.
" aekin kenan kallon wad'annan mararsa aekinyin maza sauyamun tasha bazan iya jurar ganin wannan rashin tarbiyarba yarinya Karama ta bata rayuwarta ae banga amfanin boye kanta da takeyi ba gara ta fito ta ida saida kyawunta ga mazan waje"Umma ta karashe maganar Rana zama
"Um um humm ae da yake ke Uwar data haifesace ya canza,Niko ae ko kallo ban isheshiba saidai ya tareni da wancan mugun kallon nasa yana tsotsar baki irin na y'an iska" Granny ta fad'a tana bankawa Ahmad harara.
Shima hararar ya bita dashi ya kuma tsareta da idanuwansa.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
Pls
Vote
Comments
And share
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇
🍇🌹🍇🌹🍇🌹
🍇🌹🍇🌹🍇
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇🌹
*DAFIN SO*
Story and written by
MARYAM ISMA'IL
*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* ✍🏻
*FITATTU SHA BIYAR (15) 2020*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
SANADIN GATA
YAUDARA KO BUTULCI
HANAN
DALILIN SO
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
AND NOW
*DAFIN SO*
🍇🌹🍇🌹🍇🌹🍇🌹
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Page 21 to 25
"Kaini masha Allah, kurwata kur wallahi ,ka wani tsareni da mayun idanuwan nan naka mararsa fasali da Kyan gani" Granny ta karashe maganan tana bankawa Ahmad harara
Remote ya dauka tare da sauyawa Umma tashan ,sannan ya juyo da kallonsa ga Granny "waike ina ruwanki da harkana,mata kin matso ga kabari amma bala'in sa'ido bazai barki ki zauna lafiya ba,you're disturbing me fa Granny".
" kwal ubanka Madu ,ni kake cewa tabin(disturbing), yaro ka zauna ka zageni tsab to wallahi baka isaba ,muna fiki kawai ki ganshi sululu amma ya dage da zagin wacce ta haifi ubanshi kuma kana kirana wani Grandi can don mugunta,to ba yafewa zanyi ba".
Harga Allah maganan da yayi da farko tasa ya gaji sosai donshi ba dabi'arshi bace dogon magana ba,saidai Granny na damunshi tana zame masa ciwan kai ga gulmar tsiya"kada ma ki yafe d'in"ya bata amsa.
Sallamar Alhaji Aliyu shiya bata damar bata ansa kafin ta ansa sallama saida ta nunashi da yatsa"wannan ko Madu gashi nan ya shigo toda Ali kake tsohwan marar kunya".
Shikam Alh Aliyu dariyace keson kwace mashi don tabbas yasan halin nasu ne suke bugawa,cikin sauri Ahmad ya karbi jikar Baban basa yana fadin"you're welcome Abee".
"Thanks my Son".
" welcome back Abee"Umma ma ta fad'a tana d'an risinawa.
Saida ya zauna k'asa kusa da Granny sannan ya amsa mata ,kafin ya juya kallonsa ga Granny "Mama sannu da gida".
" nikam ina ganin masifa gidannan,yo bakuso inji kuna zageni ko to da kuka kai k'arata ga Alin dukana zaiyi ko Yaya,kuita wani shegen yaraye da babu dalili ,kawai kuyi mashi haye gaskiya bakuji dadi ba,kai Amadu kalli Ubanka a k'asa koshi biyayya yake min ballantana kai na baya dana rena, wannan yaro anya bak'in halinka zai bari ka samu mai sanka ko".ta karashe maganan tana rike haba.
A rayuwa babu abunda Ahmad ya tsana sama da surutu sosai yake takura nashi, kanshi ne ya soma alamar ciwo mikewa yayi tare da nufan part dinshi kad'an ya juyo yace"wannan d'in haihuwarshi kikayi ae"ya karashe shigewa part dinsa yana saluting dinta.
"Ka k'amewa Hauwa ,d'an banza nasan maganinka gidannan,badai baka da kunya ba".
Umma da Abee kyau dariya ke cinsu ba halinyi,yanzu Abu ya dawo kansu,dole suka gumtse.
" yauwa Aliyu sai yanzu na samu damar ansa gaisuwarka,sannu da dawowa,maza tashi kuje kaci abinci ko ka huta,Hauwa tashi ki kula da mijinki nima bacci zanje nad'anyi kafin na shiryawa Mishkili tsiya sai yasan yayi dani".
Da"to "suka amsa tare da mikewa sukayi part dinsu itama wurinta ta wuce tare da kushin kid'awa tana lumshe ido.
Tsaye yake cikin toilet yayinda ruwan shower ke zuba bisa jikinsa,gashin kanshi yayi luf gwanin burgewa,kyawawan idanuwansa a lumshe ga zarazaran eyelashes da suka kara k'awa fuskar tashi,towel ya dauro ya kuma rike d'aya yana tsane ruwan dake kanshi,kwata kwata ya rasa meke damunsa motsi kad'an ita yake gani duk Inda ya juya ta kasa v'acewa tunaninsa,kyakyawan murmushinta kawai yake gani,tuni zuciyarsa ta soma azalzalarsa akan son sanin wacece wannan yarinyar kuma mai yasa ya damu da ita,So ne zuciyarsa ta vasa amsa," kai no,bashi baneba"yaba kansa Amsa da sauri,yanke shawarar ya kira Sadeeq ya tambayesa ya So yake,wayarsa ya dauka tare da dannawa Sadeeq kira.
Bugu d'aya ya dauka tare da fad'in"Angon Granny sha mamaki".
"Mtswww banfa son iskanci ,mu had'u Royal nan da 1hrs".
Murmushi Sadeeq yayi shi wannan iko na Ahmad na bashi mamaki " ina wani abu kad'an".
B'ata fuska ya kumayi"to ka kwana kanayi,kasan bans son jira"yana fad'in haka ya kashe wayarshi tare da cillar da phone din a bed.
Murmushi kawai Sadeeq yayi ya mike tare da fara shiri.
Zaune yake cikin hadadden wurin hutawar yana duban tsadaddiyar Rolex din agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayi kusan 5mins kenan tsaki ya kuma saki lokaci na barkatai donharya kufulu.
"Am very sorry friend, but am here" Sadeeq ya karashe maganan yana zama a chair din dake fuskantar ta Ahmad.
Murya can cikin makoshi yace"yazan gane inason wani".
Wani shu'umin murmushi Sadeeq ya saki yana kuma bin Ahmad da kallo sannan yace"As how".
Tamke fuska Ahmad ya kuma yi yace"will u answer me or I shall go,ina da abunyi".
"Kullun bazaka canzaba uban y'an zuciya,alamomin so suna farawa ne ta hanyar tausayi,nuna kulawarka akan Wanda kakeso kullun kana son kasancewa tare da shi,wannan ma ya isheka ka gane halin da kake ciki Ahmad".
D'an zaro dara daran kyawawan idanuwansa yayi tare da fad'in" u mean am in luv with her,kai it can't be possible Friend "ya fad'a yana mai dora yatsun hannunsa akan goshinsa tare da cije cute pink lips dinsa kamar zai huda.
" Allah na gode maka yau Granny ta zub ruwa k'asa Tasha ,Allah yasa Hanan ka fara so yarinyarnan na sonka amma kaita ja mata aji,shegen kaya.
Wata Uwar harara ya shiga jefawa Sadeeq din "karka kuma wannan kuskuren na had'ani da that stupid girl guy", mikewa yayi ko sallma basuyi ba ya shige motarshi ,had'a kanshi yayi da sitiyarin mota yanajin bugun zuciyarshi na k'aruwa ,shi kanshi yasan zuciyarshi nada rauni bata da karfin daukar abu,ba komai take iya jurewa ba sakamakon tunda aka haifeshi yake tare da matsanancin ciwan zuciya,ji yayi koda so d'aya tak yana kuma son ganin wannan yarinyar data hargitsa dukkan wani tunaninsa tabbas indai haka so yake to yanayiwa yarinyar so mai tsanani Wanda yakejin bazai iya rayuwa babu itaba,ganin Sadeeq ya nufo motar yasa ya tada mota yana d'aga masa hannu.
" Allah ya shiryamun kai Ahmad u will never change kullun iskancinka k'ara gaba yakeyi"shima motarsa ya Shiga ya tada ya nufi harkokin gabansa.
*************
"Audu ae gwara aka dawo,dama zaman jiran ka dawo daga tafiya nike wallai"Inna ta fad'a fuska daure ita a dole ranta bace yake.
" meya farune innata?"Daddy ya tambaya.
"Meye ma be faruba,shin dama daka haifi Maryam ka d'anka tarbiyarta ga Sule ne koko,k'aton banza dashi ya damki y'ar ficiciyar yarinya ya dunga jibga ".
" wai Inna me kike nufi ne,kina ganin ae yarce ta fita da irin dadewar da tayi shin cikunku wani ya damu da ina take zuwa ko me take aekatawa y'a mace face haba Inna karki rika kasa fahimtar me nake fad'a"Sulaiman ya karashe magana a tsawace.
"Dakata Sulaiman ,Nina Haifi Jannat kuma nasan tarbiyar y'ata nasan me zatayi da kuma abunda bazatayi ba