Share this page
3 / 9
na tabbata bazatayi wani abu marar kyauba ,don Allah ka tausashi zuciyarka akan y'ar uwarka ka daina mata mugun duka" Daddy ya fad'a. A fusace Sulaiman ya mike yana harara Inna yace"gaki gata nan ina jiye maku lokacin da zaku gane cewa wannan ba gata kuke nuna mata ba lokacin da nadama bata da amfani gareku ,ninan Sulaiman na cire hannuna akan lamarin Jannat komai taga dama tayi wallahi na gama bi ta kanku". "Eh kuma a fito da matar Aure nanda sati d'aya gwauran banza dakai" Inna ke fad'a. "Aure kam zanyi kodon na nisanta da ganin abunda kukeyi,ki zuba ruwa k'asa kisha gobe za'a saka bikina,kuma ki fita harkata salan na kawo matata kice zakimin iyayi " yana zuwa nan ya fice a zuciye,Sagir na kiranshi amma ko waigowa beyiba yabar gidan. Haka suka watse daga parlon kowa da abunda yake sakawa aranshi,Momy kam tasan halin Sulaiman da bakar zuciya tasan ko za'a mutu ya fita daga sabgar Jannat kenan ko me zatayi bazai tsawatar dinba,kuma tasan yanzu tarbiyar Jannat nadab da rushewa saboda illar gatan data samu. Har sunyi shirin kwanciya amma bacci Sam ya kauracewa idonta Batayi niyar shiga maganar ba amma yanzu kam ta kasa hakura balle data biyo ta d'akin Jannat taji babu abunda takeyi illah waya da saurayi. "Wai meke damunki kin kasa sukuni ko barci ya gagareki Momy" Daddy ya fada yana zama kusa da ita. Murmushi takaici tayi tace"Daddy yanzu kana nufin kace bakasan meke damuna ba,be kamata ace kayi abunda zai raba kan yaranka ba ka nuna fifiko da soyayyar Jannat karara a fili,Daddy gaba ake dubawa,ko da fad'a zakayiwa Sulaiman be daceba ace kayishi akan Idon Jannat ba". "An tab'a d'an so ko Momyn Sulaiman,nasan kina matukar son Sulaiman saidai ni kuma bazan zuba ido ya nemi kashemin tawa y'ar son ba,komai Maryam tayi a sanar dani zanyi hukunci da kaina,amma Ku barta tayi abunda takeso ,da kuke maganar shigar da takeyi duka shekarunta nawa, meye abun sha'awa a jikinta ga wani ,please mubar wannan maganan Ku daina takurawa Mamata". Hawayen takaici ne suka zubowa Momy tasa hannu ta share tace" eh inason Sulaiman saidai ban nuna banvanci a tsakanin yara na ba,kuma ban hanashi tarbiyyah me kyau ba,wallahi Daddy ina guje maka ranar dana sani ranar nadamarku". Mikewa Daddy yayi yana sababi kada tayiwa y'arsa mugun vaki,gashi zata fara weac wai addu'a take buk'ata gaba d'aya dakinma ya bar mata. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karashe *ALK'ALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Please Vote Comments And share πŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡ πŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉ πŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡ πŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉ *DAFIN SO* Story and written by MARYAM ISMA'IL *MAJI DA'DIN KAINUWA CE* ✍🏻 *FITATTU SHA BIYAR (15) 2020* *LITTAFAN MARUBUCIYAR* SANADIN GATA YAUDARA KO BUTULCI HANAN DALILIN SO ASALI NA TABON 'DA NAMIJI ADDINI NA SO 'DAYA AND NOW *DAFIN SO* πŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉπŸ‡πŸŒΉ *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ Page 26 to 30 Rushewa da kukan bak'in ciki Momy ta kumayi ta rasa wannan wanne irin gata ne,fatan ta dai Allah ya shirya mata Jannat ,in ta samu akasin hakan batasan ya zatayi ba kuma. Washe gari tun safe suka shiga hidiman had'a kayan bikin Sulaiman komai a ranar suka kaishi har akwati sannan aka tsaida ranar aure nanda sati biyu. (🀣🀣sulen inna za'a angwance sai murna nake,dikda yayiwa gidan yaji). Zaune suke a main parlo fira kwai sukeyi yayinda Sagir keta fama da Imam yaronsa ya hanashi sakat gashi so yake ya fita. Cikin natsuwa ta soma safkowa daga stairs din gidan zuwa parlor kowa da kallo ya bita ,sai lokacin nima na soma kallonta,sanye take da black jeans sai pink top mai irin budaden wuyan nan ,gashin kanta tubke tsakiyar kanta sai wata hadaddiyar hula black colour, hills ne sosai kafanta bakake sai zaran dauresu pink shima yayinda fuskarta ke dauke da lite makeup ba kad'anba tayi kyau sai wata jakar goyon bak'a data Goya ,har gabansu ta safko tace"Momy zanje na dawo yanzu kinji". "Yanzu Janna haka zaki fita,kalli shape din jikinki,wai meke damunki ne,kuma gidan ubanwa ma zakine" Momy ta fad'a. Turo d'an karamun bakin ta tayi tana bin Momy da kallo murya cunkushe tace"bakinsan mun fara lesson a scul ba". "Yanzu kuma mai shigar nan tayi ,ga wannan yarinyar cikin kayan dana bata jiyane meye aibunsu ae sun rude ko ina kuma a mota za'a kaita ko,jeki Mamana" Abba ya fad'a. Rungumar Abban tayi"I love u Daddy so much". "Love u too,Allah ya tsare hanya" ya fad'a yana shafa kanta Hanyar fita ta nufa sora kad'an ta fad'awa Sulaiman dake shigiwa gidan,a matuk'ar tsorace taja baya tana hak'i murya na rawa take fadin"Yaya am sorry pls" "Mtswwwww" yabi ta gefanta ya wuce .aeki da gudu ta sheka waje, driver yaja motar suka wuce School,don Sawam ya fita. Momy kam dakewa tayi bata kuma kallon Daddy ba don bak'in cikin yayi mata yawa. Cike da ladabi Sulaiman ya gaeshesu suka amsa,yayinda Sadiya matar Sagir ta gaeshesa,ya amsa cike da fara'a,yasa hannu ya dauki Imam yana fadin"oh my sweet boy". "Eh aefa yaranka sun bani da yarayen banza na yahudawa dolema su koya ,kai ammafa ka burgeni da zakayi auran nan ko kaima kaga kwanka a duniya my tab'a Musa albarka". Waro ido yayi" ki tab'a yatonwa ki koya masa sa ido,wallahi badai d'ana ba kyaji dashi dai,aeki ganinsa ma bakyayi kinma ji"ya Kare maganar yana mikewa. Kallon baka da hankali Inna ta masa tare da sakin baki tana tunanin iya ina rashin kunyar Sulaiman ta tsaya,takin Momy ya wuce a ciki ya sameta da sallama ya karasa gabanta ya duka tare da dora duka hannayensa biyu saman cinyarta muryarshi na rawa yace"Momy na meye damuwanki duk kika canza haka". Murya na cracking ga hawaye cike idonta tace"Sulaiman,Jannat"sai kuam tayi shiru. "Na rokeki Momy na kada kiyi mata kuka,kiyi mata addu'a ki jure,komai Jannat zatayi kinsan dasa hannun Daddy,amma don Allah kada kiyi mata kuka Momy,shiriyarta muke buk'ata" ya fad'a yana goge wa Momy idonta. Murmushi tayi tana k'arajin soyayyar d'an nata a ranta"Allah yayi maka albarka ,kayi ma y'ar uwarka addu'a kaji". "To Momy ni damuwarkice bana so,kuma ba fushi nike da itaba kawaidai harkarta ne bazan kuma shigaba" ya k'arashe maganan yana had'e ido kamar tana gabansa. ******* Kwance yake rubda ciki akan makeken Bed dinsa,da kingansa zakisan cewa tunani kawai yakeyi yayinda zara zaran lashes dinsa suka kara kawata fuskarsa kasancewar idanuwanshi suna a lumshe,kamar an muntsinesa ya tashi da sauri tare da safko legs dinsa kasan bed din hannuwansu duk biyu yasa tare da dafe kansa yanajin zuciyarsa na masa zafi,ji yakeyi yau in be ganta ba besan yazai kasance bama. Turo kofar dakin Ummu tayi ta shigo da sallama bakinta,zuba masa ido tayi ganin bemasa ta shigo ba,ajiye plate din hannunta tayi akan k'aramun table din dake kusa da ita isa wurinsa tare da zama tace"Son what's ur problem at all ka canza bansan meke damunka ba kuma,ni mahaifiyarka Ce kana da wacce ta fini da zaka fad'awa damuwarka". Sai lokacin ya d'ago idanuwansa dahar sun fara canza launi ya kurawa Ummu Ido murya sanyaye yace"just pray for me Ummu". Ji tayi itakam wannan hali na Ahmad ya fara isarta duk ya ida juyewa dama can gashi da murd'ad'an hali ballantana yanzu kuma,plate din abincin ta jayo tana bud'ewa,white rice Ce sai stew da namu a ciki,saurin kauda kanshi yayi yana yatsine fuska. "Oya look at me Ahmad Kasan Allah u must eat today,kai kullun babu abunda ke baka wahala sama da cin abinci ,tona fara gajiya" Ummu ta fad'a tana mika masa plate din ta hade rai. Badon yasoba ya k'arba'a ya fara jujuya Spoon cikin abinci da hankali yake sakashi bakinshi yana taunawa kamar me cin magani,da kyar yaci spoon 5 ya shagwabe fuska yace "Ummu na Please".ruwa ta mika masa a glass cup yad'an kurb'a kadan yana kallon agogon dake manne cikin d'akin zunbur ya mike yace" I have to go Ummu,let me fresh up". Batace mishi komaiba ta dauki plate din abincin tabar dakin,shikam wanka yayai ba'a dauki lokaci ba ya ahirya ciki. K'ananun kaya yayi maaifar kyau sai zuba kamshi yake,inka Kalli Ahmad bashi da maraba da larabawa inhar ba magana yayi ba,key din mota ya dauka ya fito waje yana duba Mobile phone nashi,tsaye yayi cak ganin Granny gabanshi ta zuba mashi ido,zaro daradaran idanuwansa yayi tare da dafe kai da hannunsa yace"chaii another problem woo". "Au iyar shegen yakai nan Amadu ni kake kira hirablam(problem), babu abubda ka iya daga wanka sai a canza kaya abi wannan inuwa ta kare a dawo gidan uwa,k'aton banza ba aure". Hade fuska yayi lokaci d'aya yana hararta yace" fitarmun a hanya,baza'ayi auranba"yana zuwa nan ya rab'a ta gefanta ya wuce.aekam da Sauri ta juyo tana fadin"kawa hauwa rashin kunya,fitsararre kawai zaka dawo ka sameni nasan maganinka ae"tana zuwa nan ta wuce tana sababi. Shikam motarsa ya Shiva ya kama hanyar makarantar su Jannat. ******** "Kaga Honey nanfa school nazo,zasu iya ganewa innasha wani abu, ka bari inmun tashi zan iskeka gida" Jannat ta fad'a fuska Kwabe. Harararta Ashman yayi tare da juya mata baya yace"just live me,dama ae nasan ba sona kikeba ur just pretending ". Kamar zatayi kuka ta fad'a jikin tana fad'in" am very sorry Dear"ta karbi kwalbar hannunshi ta kada kai bata ajeba saita ta shanye wine din tas ta y'arda kwalbar.murmushin gefan baki yayi nacin nasara ya samu ya fiddota a motar yace ta jira ya dawo,da gudu gudu Madinat tazo ta shige motar sukabar wurin makarantar.lokaci kad'an wine din ta soma aeki jikin Jannat tuni ta fara gani dishi dishi ta soma waiwaye da neman tsallakar titi. Kallonta kwai yakeyi fuskarsa cike da damuwa ya had'e kai da sitiyarin mortar yana nanata "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un" ganin da gaske mota tayo kanta yasa ya fito da Sauri ya fizgota ta fad'o jikinshi ,kallonta kawai yake don be tab'a zaton ganin haka daga gareta ba,surutai kawai yakeyi barkatai,hakan yasa a dole ya sakata Mota ya rufe ya zagayo driver sit yaja motar yabar wurin School din. Maji dadi ✍🏻 *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *DAFIN SO* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ Story and writing by *maryam ismail* *Maji Dad'in kainuwa ce* ✍🏻 *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 79 to 80 Tunda wuri aka sallamesu, Maryam bata gama tsinkewa da mamaki ba saida suka iso gate din tank'ameman gidan, lallai ya hadu iya haduwa, haka suka shiga cikin gidan, mai aekin gidan suka kwashe kayan da suka dawo dasu a parlo suka samu Amma, zuwa tayi zata duk'a da sauri Amma ta riketa, tace "haba takwarata kinyi nauyi, ki daina dukawa kinji ". Zaunar da ita tayi a chair, sannan ta maida kallonta ga Ibtisam tace "maza kije kisa su Lami a gyara dakin dake kusa da naku, kar nazo naga ba daidai ba". Sunburar baki tayi, ta mike tana jefawa Maryam mugun kallo, karo sukaci da Mahmoud "kai dallah ka rika kallon gabanka idiot kawai "tasa hannu ta tureshi ,da sauri Ibtihal ta rikeshi ta jefa mata mugun kallo tace "banza me mugun hali ". Baki ta bude zatayi magana turus ta tsaya ganin Faruq ya harde hannuwa a kirji yana kallonsu, da gudu ta zuba tabar parlon. "oyoyo Appie"Mahmud ya fada tare da rungume Faruq, Mississippi yayi shima ya daga yaron sama cike da kaunar yaron, a kafada ya sabashi suka karaso parlon ya zauna a chair kallon Maryam yayi yace "kinga gidanmu, da fatan zaki rike amana, kada ki damu da yarinyar can, ba zamanta kike ba, an hada maki komai na bukata abunda babu kiwa Amma magana "be jira amsarta ba ya mike tare da Mahmoud suka wuce part dinshi sai zuba surutu yake masa. Godiya sosai tayiwa Amma kafin suka wuce sama, sosai dakin da aka bata ya burgeta ko a gidansu sai haka babu abunda babu har kayan sawa duk an zuba mata, girke girke akeyi a gidan kowa ka gani cike da farin ciki, "Ibtihal baki zakuyi a gidanne? " Dariya Ibtihal tayi tace "our king Zai dawo, wato Daddynmu "ta bata amsa. "Allah ya dawo dashi lafiya ". "Ameen sister". Da misalin karfe 4pm motoci ne reras suke shigowa kota ina sojojine ke baje, Faruq na hango sanye cikin kakin sojoji yayi matukar kyau da hanzari ya budewa General Al'ameen mota tare da sara masa, kowa sai kamewa yakeyi haka ko wanne soja a wurin yakeyi, cikin izza ya fito kamarsa da Faruq harta b'aci saidai shi shekaru Sun ja gaba yayi suka take masa baya har kofar da zata sadaka da cikin gidan, Faruq kawai ya bisa ciki, duka yan gidan suna a parlo da gudu Mahmud ya rugo tare da sara masu sannan ya rungume kakan nasa, shima dagashi yayi sama yana kara jin kaunar jikansa na ratsashi, haka Ibtihal da Ibtisam suka runmume Mahaifin nasu suna cike da tsantsar murna suna masa sannu, itama Amma sannu kawai take masa a chair suka zauna murna kawai sukeyi. Duk abunnan da sukeyi akan idon Maryam dake lekensu ta window tuni fuskarta ta cike shaf da hawaye wani irin kewar ahalinta takeji lokuta da dama wanda tayi da mahaifinta take tunawa dukawa tayi kasa a hankali take furta "kun cuceni kun rabani da farin ciki na, ya Allah ka kawoman dauki " "a gidan nan fa ba'a Kuka"ya fada yana karasowa cikin dakin har gabanta ya duka nesa da ita kadan. Saurin dagowa tayi tana dubansa tare da goge hawaye tace "Yaya Faruq" Kureta yayi da ido sannan yace "meya Saki kuka?, meya hanaki fitowa tarbar Abbanki? "duka ya jefa mata wannan tambayar. A hankali ta dago daga takuren da take ta nuna kayan jikinshi a tsorace tace "pls ka canza kaya, ina tsoron wannan". Murmushin sa me wuyar gani ya subuce masa yace "gashi kina gidan sojoji, kice kina tsoron soja, wasa kike ko". Matsowa yayi kadan da sauri ta hade kanta da gado zuciyarta na bugawa, gani yayi da gaske tana tsoro yasa yaja da baya yace "kije Amma na kira ",ganin ya juya zai fita yasa ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito, Ibtisam ce kawai a palon kusa da ita tazo tace "Ibtihal ina Amma "ganin irin kallon da take mata yasa ta gane Ibtisam ce mikewa tayi a fusace tace "nayi maki kama da wannan wacce batasan ciwan kanta ba?, karki kuma kuskuren zuwa kusa dani, inba haka ba zaki raina kanki"tsaki taja tare da tureta cikin sauri Faruq ya riketa ta fada a jikinsa, idanuwanta ta rumtse tana sauraran tajita kasa don ta sadakas, jinta a jikin mutum yasa ta bude idanuwanta dahar Sun soma canza launi tana kare masa kallo yacce ya murtuke fuska, itakam Ibtisam tuni ta soma rawar tsoro tana zare ido, kallonsu Ibtihal ta somayi tana murmushin mugunta tanawa Ibtisam gwalo, sosai Faruq da Maryam suka birgeta ta fara ayyana abubuwa da dama a ranta.janye Maryam yayi daga jikinsa ya zabgawa Ibtisam mari gigicewa tayi ta kwarara uban ihu, kallonta kawai yayi ta hadiye kukan "ke wacce irin Jakka ce, baki ganin yarda take?, ranar karshe a yau dazan kuma ganin ko kallon banza Kin mata, apologize now". wani irin tukukin bakin ciki ya taso mata hawaye share share a fuska baki na gyarma tace "am sorry"da gudu tayi stairs tana kuka wewe wata irin tsanar Maryam ke dawo mata. "oya Ibtihal ki kaita dakin Amma"juyawa yayi yabar wurin. zaro ido Ibtihal tayi tace "kai ashe yasan na fito " Kama hannun Maryam tayi suka wuce dakin Amma da sallama suka shiga dakin, da murmushi Daddy ya ansa sallamar tasu yace "barka da zuwa y'ata Maryama takwarar uwar gida ". Mamaki ya kama Maryam ya akai yasan sunanta kodai har sunyi magana da Amma, itama da murmushin ta karasa har kasa ta duka cike da kunya tace "Daddy na sameka lafiya, sannu da dawowa ". "yauwa Maryama ya karfin jiki? ". "Alhmdllh Daddy " "to inaso ki Saki jikinki kinji, nan ki daukeshi kamar gidan mahaifinki, na daukeki kamarsu Ibtihal, dan Allah karnaji karna gani,Allah ya saukeki lafiya kinji " da Ameen suka amsa sannan sukabar dakin tana cike da jin dadi da ganin karamci irin na wannan ahalin. Maji Dad'i✍🏻 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *DAFIN SO* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ Story and writing by *Maryam Ismail* *MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻 facebook Maryam ismail(maji dadi) Inster maryam maji dad'i Page 81 to 82 After some days. Tsaye yake jikin mirrow yayi wanka cikin suit Navy colour sai inner fara sosai kayan suka karbi jikinshi, sai fitar da sihirtaccen kamshi yakeyi hannunsa sakace yake da agogon gucci sai sheki takeyi Black colour ga shoe dinshi Black, daidai lokacin ya gama gyara yalwataccen sumarshi sannan ya juyo masha Allah shine abunda na iya fad'a sosai Ahmad ya kara kyau dukda kallo d'aya zaki iya gano ramar da yayi sosai,jakar laptop dinshi ya dauka da car Key dinsa yabar dakin, cikin izza da mulki yake taka stairs din har zuwa kasa, tun kafin ya iso Hanan ta tsura masa manya manyan idanuwanta don sosai ya mata kyau, wani mugun kallo ya wurga mata ba shiri ta juya fuskarta,maganar Umma ce ta dawo dashi daga kallon da yake mata, ba tare daya d'ago ba yace "Good morning " Bata ansa ba tace "maza taso yau dole kaci abinci, kakoga yacce ka koma kamar ba Ahmad dina ba ". Sai lokacin ya kalleta ya mike zuwa kusa da ita ,zama kawai yayi bece da ita komai ba yana kallon yacce take cika plate da chip's ga farfesun y'an ciki ga Tea ta hada a mug duka ta tura a gabansa, zaro kyawawan idanuwansa yayi alamar ya tsorata da ganin duk wannan abincin a cikinsa akeso ya shige. "ka tsaya kallo, karnaji bakinka a wurin naga babu komai a table din "ta fada fuska daure. Bece komai ba ya soma shan Tea din a hankali beko sha rabi ba ya ajiye ya soma kai loman farko na chip's a bakinsa a hankali ya soma taunawa kamar mecin magani ya hadiye da kyar, kwabe fuska yayi yana kallon Umma, kauda kai kawai tayi a lokacinne Daddy ya soma kiranta mikewa tayi tabar parlon, kamar jira yake ya dauki kayanshi ya yayi waje da sauri daidai bakin kofa yaci karo da Granny baya yayi ya dafe kai, "innalillahi ni Grandy Madu saurin me kakeyi haka zaka hankadeni eyi uban ukku "(sunan da ta kuma saka masa kenan wai za'a haifamai yan ukkun dabai sani ba. "please kibarni na wuce"ya fada, kafin tayi wani yunkuri ya fice ta gefanta da sauri ya shige mota yabar gidan, "uban y'an ukku"abunda ya fada kenan dukan sitiyari ,yanzu idan da gaske Jannat ta haifa masa yara ukku ya zaiyi ya gane yaransa,yanzu ko tana ina?, wake kula da hakkin daya kamata ace shiya kula dashi, lallai bazai taba yafewa kanshi ba inhar wani abu ya sameta ji yayi zuciyarsa ta tsananta bugu ga wani zafi da take masa dakyar ya idasa tuka kanshi zuwa asibitin ,beko ansa gaisuwar da ake masa harya isa office dinsa ya zauna kansa ya hada da table yana numfashi sama sama da alamun Asthma dishi zata tashi ga zuciyarsa da yakeji kamar ya fasa kirjinsa ya fiddota, jin soyayyar Jannat yakeyi tana kara ratsashi duk wani Second, tuni idanuwansa sukayi jajir ya soma fita hayyacinsa, "hlo Guy harka iso kenan"turus Sadeeq yayi yana kallon ikon Allah, da sauri ya karasa ya dagosa yana jijjigasa, allurar da ake masa ta jijiya ya dauko ya masa duk ACn dake office din amman zufa yakeyi, a hankali numfashinsa ya soma daidaita, a bed din dakin ya dorasa ya masa allurar bacci kodon zuciyarsa ta huta da tunani saida ya tabbatar komai yayi daidai sannan ya fita yaja kofar yana tunanin yaushe abokinsa zai fita daga wannan kaddarar data samesa tabbas Jannat itace farin cikin abokinsa dole duk inda take ya nemota kodon ceton rayuwar abokinsa bazai iya jurar rashinsa ba. ************ hawayen idonsa ya goge yace "Hajiya don Allah ki taimake ni wallahi bazan iya yin aure ba a yanzu, Jannat ita kadaice macen da zuciyata keso kuma ta aminta da ita ". "Ashman ka rufemun baki na riga na gama magana, aure ba fashi kasan Kana sonta ka gujeta, na riga na gama magana ".Hajiya ta fada a tsawace. Wasu hawayen bakin ciki da takaici suka zubo masa yace "kina so ki rasani ko?, to zan mutu na barki, amman inaso ki sani Hajiya Madinat ba matar aure bace, idan kuma kika matsa na aureta zan gudu na barki har abada, komai ya faru ita ta janyo ae ". "idan ka fasa Ashman meka nema ka rasa, toma wai dole tayi maka akan duk shawarar data baka, kaika lalatata don haka aure ba fashi " "ae ki tambayeta bani na fara b'ata ta ba, kuma yanzu haka ba wurina take ba, tana da wasu mazan a waje, laifi ne na aekata a rashin sani, kuma kullun ina rokon Allah ya yafeman, kuma duk inda Jannat take zan bita koda zan rasa komai nawa ina son In gyara abunda na bata ". be jira me zatace ba yabar parlon yanajin tsabar takaici da tsanar Madinat a ransa beko kula Adnan dake masa magana ba ya shige daki. Maji dad'i ✍🏻 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* *____________________________________* *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼* *πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *DAFIN SO* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ Story and writing by *Maryam Ismail* *MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻 facebook Maryam ismail(maji dadi) Inster maryam maji dad'i Page 81 to 82 After some days. Tsaye yake jikin mirrow yayi wanka cikin suit Navy colour sai inner fara sosai kayan suka karbi jikinshi, sai fitar da sihirtaccen kamshi yakeyi hannunsa sakace yake da agogon gucci sai sheki takeyi Black colour ga shoe dinshi Black, daidai lokacin ya gama gyara yalwataccen sumarshi sannan ya juyo masha Allah shine abunda na iya fad'a sosai Ahmad ya kara kyau dukda kallo d'aya zaki iya gano ramar da yayi sosai,jakar laptop dinshi ya dauka da car Key dinsa yabar dakin, cikin izza da mulki yake taka stairs din har zuwa kasa, tun kafin ya iso Hanan ta tsura masa manya manyan idanuwanta don sosai ya mata kyau, wani mugun kallo ya wurga mata ba shiri ta juya fuskarta,maganar Umma ce ta dawo dashi daga kallon da yake mata, ba tare daya d'ago ba yace "Good morning " Bata ansa ba tace "maza taso yau dole kaci abinci, kakoga yacce ka koma kamar ba Ahmad dina ba ". Sai lokacin ya kalleta ya mike zuwa kusa da ita ,zama kawai yayi bece da ita komai ba yana kallon yacce take cika plate da chip's ga farfesun y'an ciki ga Tea ta hada a mug duka ta tura a gabansa, zaro kyawawan idanuwansa yayi alamar ya tsorata da ganin duk wannan abincin a cikinsa akeso ya shige. "ka tsaya kallo, karnaji bakinka a wurin naga babu komai a table din "ta fada fuska daure. Bece komai ba ya soma shan Tea din a hankali beko sha rabi ba ya ajiye ya soma kai loman farko na chip's a bakinsa a hankali ya soma taunawa kamar mecin magani ya hadiye da kyar, kwabe fuska yayi yana kallon Umma, kauda kai kawai tayi a lokacinne Daddy ya soma kiranta mikewa tayi tabar parlon, kamar jira yake ya dauki kayanshi ya yayi waje da sauri daidai bakin kofa yaci karo da Granny baya yayi ya dafe kai, "innalillahi ni Grandy Madu saurin me kakeyi haka zaka hankadeni eyi uban ukku "(sunan da ta kuma saka masa kenan wai za'a haifamai yan ukkun dabai sani ba. "please kibarni na wuce"ya fada, kafin tayi wani yunkuri ya fice ta gefanta da sauri ya shige mota yabar gidan, "uban y'an ukku"abunda ya fada kenan dukan sitiyari ,yanzu idan da gaske Jannat ta haifa masa yara ukku ya zaiyi ya gane yaransa,yanzu ko tana ina?, wake kula da hakkin daya kamata ace shiya kula dashi, lallai bazai taba yafewa kanshi ba inhar wani abu ya sameta ji yayi zuciyarsa ta tsananta bugu ga wani zafi da take masa dakyar

Chapter 3 of 9