tare babyn, "Alhmdllh "Dr Amina ta fada
"akwai saura fa "be idasa rufe bakinsa ba ta kuma wani yunkurin sai Baby ta kuma fad'owa, take komai na jikinta ya sake idanuwanta suka rufe ko numfashi batayi, nurses suka karbi yaran donsu gyarasu, ita kuma likitoci suka hau Kanta.
Da sauri Ammi ta iso wurin tace "yaya jikin nata "ji yakeyi kamar daya buda baki sai fashe da kuka, Ibtihal ce tayi karfin halin cewa "suna ciki, be fitoba tukun ".
Sai lokacin ya fito yace "Alhmdllh Allah ya sauketa lafiya, a bada kaya "Dr Salim ya fada.
Sosai Ibtihal ta Saki murmushi, Ammi ma tace "Alhmdllh ya Allah "
"itafa ya take Salim? "Faruq ya tambaya.
"muna Kanta dai "ya fada tare da karbar kayan hannun Ammi ya koma ciki.
wata mumunar faduwar gaba ta safkowa Faruq tsoro karara ya bayyana a fuskarsa kansa ya dora a kafadar Ammi hawaye suka ziraro masa, shafa kansa tayi alamar rarrashi.
Da kyar Dr Amina ta samu Jannat ta karba numfashin da take hura mata, ta soma numfashi, ajiyar zuciya ta soma saukewa, hamdala sukayi kafin aka soma shiryata.
"meye aka samu? "Dr ya tambaya.
"duka an samu Baby Boy's "Nurse ta basa ansa.
murmushi yayi ya karbi yaran an shiryasu cikin Blue kaya da suna matukar kama da juna, "ku canza mata dakin hutu a mata allura donta samu ta huta "yana fadin haka ya fito rike da yaran a Hannunsa,"nizan fara dauka Dr "Ibtihal ta fada ta karbi kyawawan yaran tana jin tsananin farin ciki a ranta da kaunarsu "Ammi kiga masu kyau, kodawa suke kama yaran kamar yaran larabawa ".
dafa Kafadar Faruq, Salim yayi yace "ka kwantar da hankalinka nanda mintoci zaka shiga ka ganta,tana shiryawa ne "nannauyar ajiyar zuciya ya sauke cike da jin dadi ya soma godiya ga Allah, sai lokacin ya karbi yaran ya tsura masu ido.
*ina masoya Jannat, yaufa ranar kuce, saiku fara shirin zuwa suna* ππ»ππ»πΉπΉ
Maji Dad'i βπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 91 to 92
Jin wata irin soyayyar yaran na ratsa shi yakeyi Sun masa matukar kyau saidai ya kasa gane dawa suke kama, ko kadan basa kama da Amira, jansa Ibtihal tayi zuwa dakin da aka kwantar da Jannat, kallonta yakeyi tayi masa wani irin fayau bacci takeyi ga drip a hannunta kusa da ita ya zauna yana sakin murmushi, "kallon ya isa haka, a barmun y'ata haka nan "Ammi ta fada.
Shafa keya yayi yana murmushi kasa kasa ya ajiye yaran inda take yabar dakin yana godewa Allah daya sauki Amira lafiya.
A hankali ta soma bude idanuwanta da har Sun canza kala don wahalar da tasha, Ammi ta kamata ta gyara mata zamanta, tea me kauri Ibtihal ta hada mata, saida Ammi tayi da gaske sannan ta shanyeshi tasha drugs dinta, lumshe idanuwanta tayi tanajin bugun zuciyarta na tsananta, tab'ota da akayi yasa ta bude idanuwanta tana kallon kyakyawar fuskar Faruq dauke da murmushi marar misaltuwa, zama yayi kusa da ita "ki tashi ga yaranmu kisa masu albarka kinji Momy na ".
Kawar da Kanta tayi gefe.
"bakya son ganin twins Boy's din namu ko? "
A razane ta juyo "twin's" ta maimai tana kallon yaran dake hannunsa, take hawaye suka soma zubo mata, Hannunta na rawa ta Karbi yaran ta zura masu ido tana bin ko ina na jikinsu da kallo, komai Nasu na Ahmad ne harta y'an yatsunsu irin nasa ne bakinta na kyarma tace "like father like sons"rungumesu tayi ta fashe da kuka, "am sorry Ki daina kukan nan, kiyi Addu'a Allah ya raya maki su, ni kuma nayi maki alkawari bazasu taba kukan rashin mahaifi ba indai ina raye "
Da irin wannan maganganun ya kwantar mata da hankali, kwanansu d'aya aka sallamesu daga asibiti suka koma gida, tasha mamaki babu abunda bata iske ba tun daga bed din yaran da kayan sawa da duk wani abun da suke bukata, ita kanta saida ya cika mata akwati d'aya na kaya, rasa bakin godiya tayi har kwallan dadi saida tayi, Sosai Ammi ke kula da ita da yaranta.
Zaune take ta fito wanka, yaron na farko sai faman tsala kuka yakeyi, dayan kam ko yayi kuka muryarsa bata fita sosai beda kuzari sosai, kallonsu kawai takeyi tama rasa me zatayi masu, turo dakin yayi ya shigo da sauri ya tureta ya dauki yaran ya soma jijigasu, kafin ya fara basu fida, nono baya isarsu, saida sukayi shiru ya kalleta yace"yara da haihuwa kwana hudu shine zaki rika sakasu gaba suna kuka ko?, ki daina tun kafin mu bata ,wanne suna kikeso a masu huduba dashi? "ya jefo mata tambaya.
Dukar da kai k'asa tayi tana k'ara gyara towel din data rufe kanta dashi, sannan tace "Yaya ka zab'a masu duk d'aya ne. "
"no ki fad'a sunan da kike so, yanzu ke keda wannan hakkin".
Shiru tayi kamar tana nazari ,sannan tace "asawa Babban Umar Faruq(ARIF) karamin kuma Ahmad (ANIF).
Murmushi ne ya subuce masa yace "First Father and Second Father kenan, Allah ya raya su ".
Huduba ya masu sannan yace "Amira ina ganin kamar Anif baya da cikakkiyar lafiya, bayan suna zan kaisa a dubasa, Arif ya fishi kuzari da komai ma ".
Kai kawai ta gyada yayi murmushi ya mike yabar d'akin, kai tsaye d'akin Ammi yaje ya fad'a mata sunan da aka sakawa yara, tayi murna sosai sannan tayi masu addu'a.
Ranar suna ansha shagali, anyi komai cikin wadata da kwanciyar hankali, naira a aljihun Faruq kam ta koka, dan taro sosai Ammi tayi saidai muyi addu'ar Allah ya raya mata yaranta. Sosai ta murmuje tayi kyau abunta, bama zaka tab'a cewa ta haihu ba, duk rabin rainon yaran yana hannun Ibtihal ne da mai aekin daya samo mata,suna zamansu cikin jin dad'i,har gida Dr Salim ya turo Dr ya duba Anif nan yake fad'a masu Asthma ce yaron ke garesa da ciwon zuciya dole a kula dashi sosai, kada ana takura masa da kuma barinsa yana yawan kuka .
Tunda Faruq ya fad'a wa Amira hankalinta yayi mugun tashi, rungume yaron tayi ta fashe da kuka tace "kaci sunanka Ahmad Anif babu abunda ka baro na mahaifinka, ina fatan Allah ya tsare man Kai ya baka lafiya ".
Da kyar Faruq ya lallasheta yace zai nema masa magani ko a inane kada ta damu ciwo ba mutuwa bane,haka dai Sukaci gaba da rayuwa duk kularta ta maidata akan Anif sukayi shak'uwa sosai ko kad'an bataso yayi nisa da ita.
*ABUJA*
sukuku ta shigo gidan da k'atuwar jakkar kayanta fuska a kunbure, "yau na shiga ukku ni Goggo meya sameki Madina ?",ta karashe maganar tana sakin roban Hannunta garin tuwon da zasu tuk'a ya b'are a k'asa.
kuka ta fashe dashi tazo ta rungumeta, sai lokacin Malam dake alwala ya juyo ya kallesu takaici ne ya kamasa ya girgiza kai yana k'ara godewa Allah daya natsar masa da Faty harya aurar da ita, itama Madina a kullun fatan shiriya yake mata, mikewa yayi yabar gidan dama masallaci zai tafi.
zaunar da ita Goggo tayi ta bata ruwa a randa, saida tasha sosai sannan ta soma ajiyar zuciya, "ke bansan iskanci tunda kin huta sai ki fad'amun meke faruwa kuma"Goggo ta fad'a a masife.
"Goggo Ashman aure zaiyi, Alhaji Mado ya koreni, Goggo na shiga ukku duk wasu wanda suke tare dani yau Sun gujeni Sun juyamun baya ya zanyi da raina ".
Salati Goggo ta Saki tana tafa hannu "shi Atman yake ko ubanwa dan yana kwallon shege tantiri shine zaice aure zaiyi, to wallahi be isa ba, duka zanyi maganinsu y'an iska kawai ki share hawayenki, ina nan baki ba kuka".haka taita sababinta, ita dai Madinat wanka tayi ta hadiyi magani donduk dukan da Ashman ya mata yasa jikinta yayi tsami, baccin wahala ta farayi.
*******
sanye yake cikin Farin Kaya yadi yayi matukar kyau ga Hula dara ya murza a kansa ga agogon Gucci daure a tsintsiyar Hannunsa, takalmi yan soke ne kafarsa sai fitar da sihirtaccen kamshi yakeyi, parlo ya fito beko tanka kowa ba ya zura kai zai fice, muryar Umma yaji tace "kai zo nan ka duba wannan kayan ".ji yayi zuciyarsa na neman fashewa badon yaso ba haka yazo yana bin tarin kayan su biscuits da alawa da kallo an cika wuri dasu, "kayan saka bikinka da Hanan ne, kuma baza'a saka da nisa ba,saika fara shiri ".
Kai Kawai ya gyad'a bece komai ba ya tashi ya fita, gidan gonar Sadiq yaje yana neman hutawa da zafin da zuciyarsa ke masa anan ya samu Sadiq ,shima be kulasa ba yaci gaba da harkar gabansa, Sadiq kam be wani ji babu dadi ba,don yanzu mishkilancin Ahmad yafi na ko yaushe baya magana ko kad'an aeki ma sai yaga dama yake zuwa.
******
A yaune duban al-umma suka shaida auran Ashman da Mubaraka akan sadaki nera dubu hamsin, ango yasha wanka saidai yak'en dole yakeyi ji yakeyi kamar a mafarki, be bari anyi shagali ba haka akayi bikin shalin alin gara amarya tayi Mothers day, da yamma haka aka kaita gidan auranta wanda iyayenta suka narka dukiya a ciki, amarya sai murna yau burinta ya cika ta auri Ashman da take so tun yarinta, kuma tayi alkawarin zama dashi ta ko wanne hali.
*Maji Dad'i* βπ»
πππππππππππ
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 93 to 94
*ina bada hakuri da jina shiru, kunsan rayuwar abubuwa basu Karewa,a kara hakuri my real fans*
Zaune yake ya rike babbar riga a hannu ya zame hularsa baya shiru kawai yayi yana jin fadan da iyayen nasa ke masa,kwatakwata hankalinsa ba wurinsu yake ba, shidai kawai yaji Adnan ya tab'ashi alamar ya tashi su tafi, murya ciki ciki ya musu sai da safe, Sannan Suka fita.
"Ango kasha kamshi, kaga Angon Mubaraka".abunda Adnan ke fad'a kenan.
"wallahi zanci Uwarka, Shege kawai, ae duk da Hannunka aka mun wannan iskancin".
"Munahiki kana so kana kaiwa kasuwa, aure dai dole kayi ".da dariya k'asa k'asa ya figi Mota suka bar wurin.
Har cikin gida ya rakashi kafin ya baro gidan, Kai tsaye gidan ya shiga babu alamar akwai mutum a gidan d'akinsa ya shiga yayi wanka, ya fito daure da towel, tsaye yayi cak yana kallonta da mugun mamaki, a harzuk'e yace "Ubanwa ya kawoki d'akin nan? "
Kyarma ta somayi tana raba ido don ta tsorata sosai, "ina jin tsoro ne Yaya "ta k'are maganar tana hawaye.
Dafe Kai yayi "dallah ki rufe mun baki malama, ansan kina tsoron aka maki auran? ".
Had'iye kukan tayi dana kyarma, don gani take kamar jibgarta zaiyi, k'asa ta zame tana raba ido.
Banza yayi da ita ya karaso cikin d'akin ya shirya, kafin ya haye Bed ya bata baya. Itama anan ta zame tana bacci sai da Asuba ya tasheta shikam ya wuce masallaci.
******
"kaji Iskanci zagayen uwar me kakewa mutane? ",Sadeeq ya tambayeshi.
"ka fiye damuna Sadeeq, don Allah ka rabu dani "yana fadin haka ya kuma juya kanshi dake matuk'ar sara masa, duk abun duniya ya masa yawa akai.
"solution fa kake so Ahmad, in baka fad'amun damuwarka ba, wa zaka fad'a wa ".
"a Gida ne aka kawo kayan saka biki na da wannan Yarinyar ".
Jin wani abu Sadeeq yayi har cikin ransa, donko ya dad'e da soyayyar Hanan a zuciyarsa, ya kasa furtawa ne don ganin wanda akeso a aura mata .
"kaga akwai mafita,matso kaji ".
A kunne ya masa rad'a,murmushi Ahmad yayi yana kallonsa tare da girgiza kai sannan yace "shikenan bara mu gwada sa'a".
*******
"waini na rasa meke damunki, wanne irin ciwo ne haka Madinat, ina kika kwaso shi, alamu ya nuna kamar kina da ciki, yaushe rabon da kiyi al'ada?".
"Goggo na dad'e "ta bata amsa tana goge baki dukta galabaita ta gama kwarara amai .
"amman akwai sakarar yarinya, shine kuma kikayi shiru, so kikeyi ki jawo mun sheri, aeko maza ki shirya asibiti zamu yanzu ".
hijab kawai Goggo tasa ta, tasanya Madi gaba suka je Asibiti, gwajin farko aka gano tana da ciki wata biyu, salati Goggo ta Saki cikin tashin hankali tace "likita a zubar dashi yanzu nan ".
"bazai yiwuba inko aka zubar dashi zata rasa ranta don bata da cikakkiyar lafiya, sai dai kuyi hakuri kuga abunda Allah zaiyi ".
"na mutu wallahi bazan zubarba, haka kawai na kashe kaina, wallahi nafi son raina akan komai, kinga tafiyata ni, yo kaina farau bare naji kunya " .da sababi Madinat tabar asibitin ba arzik'i Goggo ta biyota sai fad'a sukeyi a hanya.
******
Da sallama ya shiga gidan ,cike da farin ciki Umma ta tarbeshi suna gaisawa sannan tace "ina abokin naka, aeni yau nasan fushi yake dani "
Sallama Ahmad yayi beko kulasu ba ya wuce d'akin Granny.
Maji Dad'iβπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 95 to 96
"ka gani ko, sai fushi yakeyi dani, bayan gata nake so na masa ".
"to Ummu sai hakuri ae, insha Allah zai daina"ya bata amsa.
"shidai ya sani amman dole yayi aure ae, kuma badai wannan me kama da aljannun ba Allah".
Murmushi kawai yayi, yana tunanin wacce irin kiyayyah ce tsakaninta da Jannat.
"bari na gaishe da Granny "ya fad'a tare da mikewa.
Da Sallama ya shiga dakin Granny "y'ar tsohuwa matsamun na zauna kusa da amaryata".
"haba rabani da yaudara irin taka, kazo yau kamun wayau".
"haba yaufa dake nake auren,har toshin kaza zan kawo maki na amarci "ya Kare maganar yana zama kusa da ita.
Wani harara Ahmad ya jefa masa yace "dallah malam ka zauna kayi abunda ya kawo ka".
"D'an nema da yake ta ciyoka ko, taimakonka zanyi idan kuma ka matsamun wallahi zan tafiyata"Sadeeq ya fada.
Magana sosai sukayi da Granny kuma Alhmdllh ta fahimcesu, sannan tace kada su damu zatayi abunda ya dace insha Allah. Da farin ciki Ahmad yabar dakin, yaji dadi sosai hankalinsa kwance a ranar,sosai ya sake ranar har mamaki Umma takeyi,a ranar aka saka bikin nan da sati ukku, komai Umma ta soma shirin biki, ko wanne bangare na amarya da ango shirin biki sukeyi, cikin ikon Allah Granny ta fahimtar da Daddy abunda suka tattauna da yaran kuma ya fahimta yayi na'am dashi.
*********
Sosai tayi abinci ta gyara ko ina fes, wanka tayi tasha kwalliya cikin atamfarta mai calar Blue sosai ta Karbi jikinta tayi masifar kyau, be dawo gidanba sai wurin 10 kai tsaye dakinsa ya shiga yayi wanka, ya fito yana goge kai da karamin towel, knocking yakeji "come in"ya fada yana murza mai a jikinsa.
Tun kafin ta shigo kamshin turarenta ya bide dakin, taku takeyi cikin nutsuwa harta iso kusa dashi ta duka har k'asa tace "ina kwana ",gabanta na dukan ukku ukku tana Tsoron amsar da zata samu dauriya kawai tayi ta shigo,ba kamar data ganshi da towel.
Tsab ya gama karantar yanayin da take ciki, kawar dakai gefe yayi yace "lafiya".
Murya na rawa ta kuma cewa "your break fast is ready Sir".
"nace kiyi girki da ni ne?, ko kuwa nace zan rika cin jagwalwalonki? ".
Tuni idonta ya kawo ruwa tace"kayi hakuri, gani nayi ya dace nayi, tunda zamanka nakeyi ".
"Owk kije ina zuwa naga ko zan iya daurewa naci ".
Murmushi tayi k'asa k'asa don harga Allah taji dadin amsawar da yayi, don ba haka tayi tsammani ba,mikewa tayi tana tafiya, da kallo ya bita ko ina na jikinta rawa yakeyi, donko mubaraka itama ba baya ba wurin kyau.
A gaggauce ya shirya cikin k'ananun kaya don fita zaiyi, sai zuba k'amshi yakeyi ya fito, zaune take a parlo da sauri ta mike ta karbi wayoyinsa da Key din motarsa ta bisa baya zuwa dinning, tunda ta bude girkin, kamshinsa ya bide wurin chips ne da farfesun y'an ciki sai ruwan lipton da yaji kayan kamshi, yana yatsine fuska yake cin abincin kamar yana tauna magani(π€£π€£anji dadi anata fuskewa kafin mubaraka ta halbo jirgin mutum).be wani ci sosai ba ya mike ya karbi kayansa tana masa Allah ya tsare bece komai ba ya fice abunsa. Tashi tayi ta soma tattare wurin.Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar masu, tun yana d'an shareta harya fara kulata wani lokacin har fira suke d'anyi, don mubaraka ba daga baya ba.
**********
"me kake tunani Abban Sulaiman "Momy ta fada.
murmushi yayi yace "ina tunanin rayuwa ne, Momyn Jannat ".
da sauri Momy ta dago tana kallon Abba wanda rabon da taji ya Kira sunan Jannat tun ranar daya koreta, wani sanyin dad'i taji a ranta ganin koya sauko ne.
janyota yayi zuwa jikinsa yace "kina mamaki ne Umman Jannat? "
gyad'a kai kawai tayi tana murmushin itama.
"ba abun mamaki bane, dama can sharrin zuciya ne, yanzu kam ina rokon Allah ya nuna mani y'ata kodon na gyara kuskuren dana aekata".
Hawayen dad'i ne suka zubowa Momy ta d'aga hannu tana godewa Allah daya nuna mata wannan rana, sosai suka sha soyayyah ranar ran Momy Fes.
"uban me kuma kake leke, shege me siffar aljannu "Inna ta fada tana fitowa daga part dinta.
"karki kuma cemun shege tunda kinsan Ubana, part dinki na lek'ane ne, wallahi zamu koma da"Sulaiman ya bata amsa.
Harara Inna ta watsa masa tace "wallahi Sulaimanu ina raga maka ne saboda wancan matar daka dake dauke da tsohon ciki da tuni nasa anyi waje da kai kaima ".
"aeko ke da kinga inda zaki, donni kinsan ba'a wannan dani, tsohuwa kin kusa mutuwa amman ki hayyaci kowa wallahi nayi maganinki"barin wurin yayi yanajin in yana wurin ba hakuri zaiyi ba.
"kuma nace Shege, munahiki Allah wannan yaron indai yana gidannan wataran kasheni zaiyi "tanayi tana matse kwallah.
dariya Sawam ya fashe dashi yace "dama shine maganinki ae, inkin raina kowa shi Zai saita maki sahu ae, kema saiki tab'o wanda ya fiki ".
"kaini naga jaraba, shegun yara duk Sun gado bak'in hali irinna Uwarku, nidai banga ranarku ba, Duka zansa ya koremun ku daga gidan ".
"kanki akeji dai, kinga tafiyata "nan ya barta tana sababi.
bari mu leka Adamawa
Majidad'iβπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 97 to 98
"kinsan Allah zan Kira Yaya Faruq, ki tashi ki kama yara sai zuba kuka sukeyi, kin tsaya kallonsu ".
"ni bansan me suke soba, nidai na gaji wallahi abada su "Jannat ta kare magabar tana raurau da ido hawaye ya cika taf a idonta.
"mtswww aekin banza, ubanwa ya haifesu da za'a badasu, kin wani damu mutane, to ki daukesu ku tafi gidan ubansu idan akwaishi "Ibtisam ta fad'a.
Uwar harare Ibtihal ta jefa mata tace "ke baki daina shiga abunda babu ruwanki ko?, wai harsai yaushe zakiyi hankali ".
"dallah malama rufemun baki, ko ciwan kanki baki sani ba kawai kin zama y'ar raino ,to karya nayi inda uban a tafi wurinsa mana, kuma wallahi idan kika kara cemun bana da hankali sai munyi bala'i dake ",zura shoe dinta tayi tabar dakin tana sababi.
Itakam Jannat hawaye yaki k'afewa daga fuskarta, ashe bata huta da wahala ba, ashe gori bazai kare mata ba, lallai Uba daraja ne ga yaransa sai yanzu take kara jin ciwan abunda Ashman da Madinat suka mata, bata tabbatar Sun gama tarwatsa mata rayuwa ba sai yanzu,dafa kan yaranta tayi hawayenta suka zuba akan fuskarsu tace "mahaifinku na sanku, yana kuma kaunarku kaddara ce ta rabaku kuma ina fatan ko bayan raina ta sake had'aku ".
Zuru yaran sukayi mata, wanda sunyi wayau sosai gasu bulbul abunsu kwanin sha'awa, sai halba kafafu suke suna gwaranci, jin tausayin yara na ratsata tayi, dafa kafad'arta Ibtihal tayi tace "Aunty Amira don Allah kiyi hakuri, kinsan halin Ibtisam ba wani abu sabo, insha Allah zata daina ".
Murmushin takaici Jannat tayi tace "karki damu, tana da gaskiya da gidan Ubansu suke wazai goranta masu, gara ta rika tunasarmun da inda nake kona san abunyi, ni ban riketa a raiba".
Da gudu Mahmoud ya shigo dakin ya fada a bayan Amira ya rungumeta "Aunty Momy na dawo"abunda ya fada kenan.
Share hawayenta tayi kafin ta juyo don tasan halin Mahmoud da shegen wayau ga surutu, "Oyoyo yaron Aunty sannu da zuwa, ya School din? ".
Hannuwansa duk biyu yasa ya tallafi fuskarta "Aunty waya Saki kuka na halbeshi da bindigar Daddy ?".kamar daga sama taji tambayar tasa.
"Habibi Idona yakemun ciwo nefa"ta basa amsa.
Da gudu ya fita a dakin, part din Faruq ya shiga yana hak'i baya parlo Kai tsaye Bedroom ya fada yana maida numfashi.
Juyowa Faruq yayi ya jingina da mirrow yana kallon Mahmoud yace "ba sallah yaron Aunty? ".
"Oh am sorry Abban twins, Aunty na tana ciwan idone fa, sai ruwa yakeyi ".Mahmoud ya basa amsa ,be jira me Faruq zece ba ya Kama hannunsa suka fito, har dakin Jannat ya kaisa lokacin Iftihal ta fita, zaunar dashi yayi a bed yace "Daddy ka tambayeta ka bata magani, bara naje na canza kaya kafin Ammi na ta fito da gudu yabar masu dakin.
"me yake damun ki ne ?".
Kamar daga Sama taji tambayar tasa.
Basarwa tayi tace "ba wannan yaran bane sai wahala suke bani ba "ta kare maganar yata kwabe fuska.
murmushi kawai yayi don tsab ya gane ba abunda yasa ta kuka kenan ba, sharewa kawai yayi yace "to Maman biyu ae sai hakuri,kuma kinga Anif ae baya da rigima, rigima saidai takwara na ".
Murmushin ta mai kyau tayi har hakoranta suka bayyana "kilama gado yayi, kaima kawa Ammi rigima ".
Sosai ta birgesa da irin farin cikin da yaga tana yi, yunkurawa yayi zai mata dundu.
"Allah Yaya na daina fad'a, bakayi rigima ba "ta kare maganar tare da rumtse idanuwanta sosai ta soma kyarma.
"matsoraciya "ya fada ya kwashe yaran yabar mata dakin.
*********
Shirin biki ya kankama babu abunda Ummu da Mama (Maman Hanan) basu gama ba, amarya sai shan gyara takeyi, har wani Shek'i takeyi,lefe na gani na fad'a Umma ta hadawa y'ar tata akwati goma.
B'angaren Ango suma babu abunda basayi harta kayan sakawa komai iri d'aya Sadeeq da Ahmad sukayi, saidai a bikin ya hana hidimar komai daurin aure kawai za'ayi sai walima, Umma ce ta had'a walima daren aure,yaune ya kama ranar walima, an shirya komai tsab, Manya manyan Malamai Umma ta gayyata, amarya tasha kyau cikin purple lifaya da wani d'anyan leshi shima purple ga zanan lalle ansha ga kitso tayi matukar kyau sosai, Wa'azi sosai Malamai sukayi akan aure da biyayyah ga miji, Amarya tasha kuka sosai Wa'azi ya ratsata, tasha kyaututuka daga y'an uwa.
Ranar daurin aure
yaune ya kama ranar daure, kofar gidan Alhaji Aliyu ya cika d'an kam da d'an Adam abokai na kusa dana nesa, sai kayi da gaske kake gane wanda kake nema, maroka sai aekinsu sukeyi.
Can kusa da liman na hango taurarun wato Ahmad da Sadeeq komai nasu iri daya harta agogo sunsha kwalliya cikin wata d'anyar shadda Ash colour sai Hula da takalma bakake sai fitar da wani sihirtaccen kamshi sukeyi suna kyalli.
shelar dana jiyo ne ta tashi hankali, yasa na kara kutsawa don tabbatar da abunda kunne na yaji mun, tabbas haka ne An daura auran Zainab Kabir (Hanan) da Sadeeq Nasir akan sadaki naira dubu d'ari.
mikewa sukayi fara'a fal fuskar su, suna gaisawa da jama'a,ana masu murna, bani kadai na shiga rudani ba har mutane da yawa a wurin.
Tofa Reader's kunji wata sabuwa.
Majidad'iβπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*