```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 99 to 100
Radau haka taji shelar daurin auran ta, a kunnen ta, wasu hawaye suka wanke Fuskar ta, ta rasa gane shin na farin ciki ne ko kuwa aka sin haka?, tabbas tasan tayi rashin wanda take so har abada, amman tasan Sadeeq ma ba daga baya ba, tashin hankalin ta shine idan Umma taji ya zata dauki abun, sai dai kuma tana farin ciki donta auri wanda yake matuk'ar son ta.
Umma kam mutuwar tsaye tayi, ko dai Kunnen ta ne beji mata daidai ba?, Auran Ahmad akeyi yau ba na Sadeeq ba, rud'ani ta shiga sosai, waya ta dauko ta soma kiran layin Daddy, baya amsawa ,haushi taji ta yi jifa da wayan,safa da marwa kawai takeyi duk ta rasa meke mata dad'i.
Bayan lafawar mutane, Daddy suka tara meeting din gaggawa wanda kowa ya halar ta, tun daga y'an gidan su Ahmad, Sadeeq kai harda na su Hanan.
Cikin nutsuwa take shigo wa, babbar lufaya ta yafa sai zuba kamshi take yi,gefan Umma ta zauna kanta na kallon k'asa ta gaishe su, amsa sukayi tare da saka mata albarka.
Sai lokacin Daddy yayi gyaran murya, aka bud'e taro da addu'a sannan yace "Nasan da yawa cikin ku, kuna dauke da tarin tambayoyi akan sabon Al'amarin da kuke ji yanzu, amman idan kuma kuka tuna komai Allah yana iyawa, to ba zai zama abun mamaki ba, kamar yacce kowa ya sani ansa aure da niyar Ahmad amman kuma Allah da ikon sa sai ya koma akan Sadeeq, ina so ku sani dama Allah ya nufa Hanan matar Sadeeq ce ba Ahmad ba, hakan ya faru ne ta dalilai, da azo a samu matsala gara kar a fara".
Nan Daddy ya fad'a masu komai ya faru da yacce akai auran ya koma kan Sadeeq, Alhmdllh kowa ya gamsu da baya nan sa.
"Ae ba wata matsala indai Hanan ta amince, don ni ita nafi ji, duka da Ahmad da Sadeeq duk yara na ne ,fata na Allah ya basu zaman lafiya "Umma ta fad'a.
Sosai Hajiya taji dad'in karar da Umma tawa yaron ta, wanda bata yi tunani ba, albarka tasa masu tare da yiwa Umma godiya.
"To Alhmdllh tun da kun fahimta, sai dai ina rokon ka Ahmad daka fitar da Mata, zaman ka haka nan bazai yiwu ba, karka bani kunya "Abbu ya fad'a (baban Sadeeq).
Sosai sukayi godiya, sannan aka tashi taron cike da so da kaunar juna, kamar Family d'aya, da yamma aka kai amarya dakin ta, washe gari akayi walima, Ahmad yasa Umma zata masa magana amman sai ta share shi,shima haka yaci gaba da rayuwarsa cikin jin dad'i .
B'angaren Amarya da Ango kuwa hankali kwance suke zaman lafiya, Sun fahimci juna, suna rayuwa cike da girmama juna.
A gurguje pls
After 6 year's
Yara ne maza masu matuk'ar kama da juna, ga shegen wayau, kamar yaran larabawa, komai nasu iri d'aya, ball suke halbawa a cikin makeken Gate din gidan, karar motar da suka ji ne yasa sukayi wurin motar da gudu suna "Appie oyoyo ",cikin sauri Faruq ya fita a motar ya rungumi yaran tare da d'agasu Sama yace "Oyoyo my twin's "kallonsu yayi sosai sannan yace "Anif waya saka ball?"
Kyakyawan yaron da aka Kira Anif wanda daka gansa kasan be cika hayaniya ba yace "Just ina gwadawa ne ".
Jansu yayi zuwa cikin gida, anan suka samu Mahmoud yana ta aekin game a system yanzu ya zama saurayi yana JS 2.
da gaggawa ta safko daga stairs tace "Mahmoud maza dakko mun Anif, Ball fa yake yi, yasan baya da lafiya kuma "
Sai lokacin ta lura da Faruq dake dauke da yaran, murmushi tayi tace "Appie sannu da zuwa, harka dawo? ".
kallonta kawai yake yi, tayi masa matuk'ar kyau, sanye take cikin dogon riga na material Pink colour Sosai kayan suka Karb'i jikinta ga daurin zara buhari datayi, sosai ta kara fari da kyau tayi d'as abun ta ga kibarta daidai kwanin sha'awa.
Sauke yaran yayi yace "eh Aunty na dawo ".
kama kunnen Anif tayi "Ahmad bana Hana ka Ball ba? "
"aushhh Aunty kad'an nayi, banyi gudu ba, am sorry to "Anif ya fad'a.
Janye yaron yayi yace "Amira aeko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, karki cirewa yaro na kunne ".
Dariya Mahmud yayi yace "Aunty muyi tafiyar mu, idan Appie yaga twin's ko kulamu baya sonyi".
Haka dai suke ta fira gwanin burgewa, kafin kowa ya kama gabansa.
******
da gudu ya fad'o masa ya fige tab din dake hannunsa, shiru yayi idonsa k'asa can kuma yace "Stop disturbing me pls, i hate that nonsense "
Zaro ido Arif yayi a fusa ce yace "u call me nonsense,am not i think u are "
wani uban naushi Anif yawa Arif a baya,yana d'agowa ya rama shima, jin hayaniyarsu yasa Jannat shigowa d'akin ,da sauri ta rike hannun Anif tace "what's that, bana hanaka dukan sa ba "
"Aunty he call me nonsense "Arif ya fad'a.
Cikin tsawa Anif yace "u did First, who ask u to come here"
"stop that, bana son wannan fad'an ranku zai b'aci yanzu kam ".
naushi Anif ya kaiwa chair din dake gabansa sai hawaye shar shar, bakin ciki ya dame sa an hanashi ya rama, barin d'akin kawai yayi don tsabar takaici.
ji tayi har cikin ranta bata ji dad'i ba, don gaskiya tana matukar son Anif kuma tasan baya da rigima zaku iya wuni a wuri be tanka kaba tasan Arif ya tsoka nesa, to amman bata da yarda zata yi.
"Arif ka daina tsoka nan sa, bana son kuna rigima ".
Bude baki yayi zaiyi magana da tsawa tace "keep quite boy".
Ta fita tabar masa dakin.
Majidad'iβπ»
stylish Star β¨
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 101 to 102
Tun da ya dawo gidan bega Anif ba, tun daga dakinsu yake kwallah masa Kira "Anif, Anif, my Son Why are you "shiru beji motsin kowa ba, da Jannat yaci karo, "ina Anif? "tambayar daya jefa mata kenan, kauda idonta tayi "bansan ina yake ba "ta bashi amsa a takaice, wani wawan kallo ya jefa mata "amman ae kinsan ba lafiya ne dashi ba, kuma kika barsa, bazaki iya neman sa ba "kwafa yayi, ya wuce bayan gidan, enterance na lambun gidan ya shiga, can ya hangosa mak'ale bayan flowers sai gyarman sanyi yake numfashinsa na fita a sassarke, da gudu ya isa Wurin sa yana jijigasa, idanuwansa harsun canza kala, daukarsa yayi da sauri ya fito zuwa compound na gidan driver din Ammi yake kwallahwa Kira, har riga rigan fitowa Ammi da Jannat, "lafiya Kake kwallah wannan kiran haka? ",turus tayi ganin Anif a Hannun sa "subuhanallah meya samu Ahmad din ","ki tambaye ta Ammi "ya kare maganar yana jefar Jannat da harare, Key ya fizge daga hannun Bala ya fad'a motar ya fizgeta da uban gudu, cikin gaggawa Gate man ya bude masa, shikam yayi gaba, "wai me yake faruwa ne Maryama?, meya samu yaron ne? "
Shiru tayi tana raba ido, "Ammi nima ban gansa tun dazu bafa "ta bata amsa.
"maza dauko mayafin ki da Key din mota ,mu bisa ",da gudu tayi daki ta dauko hijab, dakin Ammi ta shiga, Ibtisam ce kawai a dakin bata kulata dame take fad'a ba ta zari Key tayo waje, ita ke driving din kai tsaye asibitin su Dr Salim suka nufa, mintuna kad'an suka kaisu, a reception sukayi tambaya, aka basu amsa yana Emergency, tun daga nesa suka hango Faruq yana ta safa da marwa da sassarfa suka isa, "ya jikin sa? "Ammi ta tambaya, goge zufar kansa yayi "abunda nake jira kenan "ya bata amsa.
Ta glass din wurin Jannat ta hango yaron ta likitoci a kansa harda abun tai makon numfashi ,tuni hawaye suka wanke mata fuska yaron da take masifar so kamar ranta, shine yake wahala haka saboda saka cin ta, tuni ta rude tana karanto ko wacce irin addu'a tazo mata, ganin ya yunkuro kamar zai dai na numfashi, bata san ta Saki kara ba, tana bubbuga Glass din kofar shiga take nema, da sauri Faruq ya rike ta "oya keep quite, bana son shirme anan ","Appie kaga yana wahala fa, mutuwa zaiyi ya barni, idan ya mutu zan bisa Allah, kace ya tsaya don Allah karya barni bazan kuma bari a b'ata masa rai ba ".
"shhhhhii nace kiyi shiru ba, kina mayar dake gida ",shiru ta hadiye kukan dake taho mata zaunar da Ita yayi, Ammi tazo tana bata baki da hakuri, Dr Salim na fitowa duka Suka mike suna jiran mezai fad'a, "karku damu Asthma dinsa ce ta tashi, da alama ya zauna wuri me sanyi, ko kuma an bata masa rai, dole sai kun kiyaye wannan fa, yanzu komai yayi daidai zaku iya tafiya "takarda yaba Faruq "a nemi wannan drugs din friend ".
"OK insha Allah, thank u, sai mun hadu "
Ammi ta karbi driving motar ta tayi gaba, shikam yana front site, sai Jannat a baya ga Anif a cinyar ta Yana bacci, shafa kansa take tana hawaye da tunanuka iri iri har Suka iso gida, da gudu Arif ya fito yana kallon Anif dake hannun Faruq har dakinsu aka kwantar dashi a bed, kansa Arif ya shafa Yana kallon Faruq "Appie meya same sa please"ya kare maganar yana marairaice fuska kamar zaiyi kuka, "Asthma dinsa ya tashi, but he is getting better karka damu ".gyada kai yayi yace "Allah ya basa lafiya ",duk wunin ranar Arif anan ya wuni sai da Faruq yayi da gaske sannan yaci abinci kadan, beyi daidai ba har sai da yaga Anif ya tashi, kuma Alhmdllh ya tashi da sauki, bude idon sa na farko shima Arif ya tambaya a tare sukaci abinci sannan yasha Drugs dinsa suka fara kallo. Sosai Jannat tayi farin ciki da ganinsu haka, taji dadi sosai tana godewa Allah.
7days latter
Kowa gidan sai shirin tafiya biki akeyi Abuja, sosai hankalin ta yake tashe, dondai bata son yiwa Ammi Gardama da bata je ba, duka Sun gama shirya komai a mota, sai tafiya motan farko Ammi, Ibtisam da Mahmoud, sai Arif wanda duk inda Ammi tasa kafan ta yana biye da ita, Bala driver ya dukasu sukayi gaba, sai dayan Motan Ibtihal da Anif a baya, ganin harsu Ammi Sun tafi Jannat bata fito ba yasa Faruq komawa don dubo ta, tsaye ya ganta tayi shiru, "Amira ya kira sunan ta "dagowa tayi tana raurau da idon ta, juya mata kai yayi ya kama duka hannu wanta biyu suna fuskantar juna "bana hanaki tunani ba, Amira ki yarda dani babu abunda zai sameki ina tare da ke, ki tsai da hankalinki zuwa Abuja bashi zaisa ki rika tuna baya ba, ki fuskanci gaba yaci ace yanzu farin ciki zakiyi kodon rayuwar yaranki kinsan suna bukatarki, ki daure kinji, insha Allah komai zaiyi daidai ".
Gyada masa kai tayi tana share hawaye, mikewa tayi, batace komai ba tabi bayansa, front sit ta shiga nan Suka dauki hanyar Abuja.
Majidad'iβπ»
stylish starβ¨
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 103 to 104
Sadaukarwa ga Real majidadi fan's group
Tunda Suka doshi hanya ta kasa sukuni, hankalin ta duk inda yake ya gama tashi, rayuwar da tayi baya ne kawai ke dawo mata, fad'uwar gaba kam ba'a maganan sa, duk wannan abun da takeyi Faruq yana lura da ita, ya rasa me yasa ta tayar da hankalin har haka, juyowan da zaiyi ne suka had'a Ido, hawayen da yaga suna shirin safkowa ne yasa ya girgiza mata kai, itakam batayi aune ba taji hawayen na gangarowa akan kyakyawar fuskar ta.
"oh no, meye na kukan kuma?, please kiyi hakuri ".
Runtse idanuwan ta tayi da karfi, gaban ta na tsananin fad'uwa "Yaya inajin kamar zan mutu da tsoro, gaba na yana faduwa".
Kallon Jannat ya Kama yi, a karo na barka tai"ki fara karan ta addu'a, bana son wannan damuwar ".
A hankali ta soma Karan ta duk addu'ar da yazo gaban ta, ba wani jimawa bacci ya dauke ta, ajiyar zuciya ya sauke, zuciyar sa cike da tunani iri iri. Sai da ya rage a motar shi kadai ke bayi bacci ba, tunda suka fara tafiya sallah kawai ke tsayar dasu ,cikin dare suka iso Abuja, firgigit ta bude idanuwan ta, jin sanyayyar iskar dake ratsa ta,tun da tabar garin su yaune rana na farko data tako garin, tsawan shekara 8 da watanni kenan, wani irin farin ciki taji ya shige ta lokacin data tuno da Ammin ta, da y'an uwan ta, tunani take yi duk runtsi baza ta yarda tabar garin ba, ba tare da taga mahaifiyar ta ba, har suka iso gidan da zasu je tunanin da take yi kenan, kuma daga nan babu nisa zuwa unguwarsu ,a mutun ce aka tarbe su duk da dare ne, sannan aka kaisu dakin da kowa zai zauna ita da Ibtihal da yaran ta dakin su daya, tsab Ibtihal ta hade ido tace baza ta zauna daki daya dasu ba, dakin Khadija ta zauna dama aminiyar ta ce, don kusan halin su daya, wanka sukayi suka shirin bacci,kafin kowa ya kwan ta, amman bacci ya gagari idon Jannat har asuba sai bayan tayi sallah, sannan ta kwan ta.
*********
"waike Madina na rasa ina kika ebo wannan mugun warin jikin da kike yi, duk kinbi Kin ribe, ga zubar da ruwan ciwo a kafa, wallahi duk kin lalata mun gida da wari "Inna take fad'a wanda yanzu har tsufa ya soma kama ta, duk da ita ma ba isashshiyar lafiya ya ishe ta ba.
"wai ke dukwa ya jefani a wannan halin halakan in ba keba, ni fa yanzu ba tsoranki nake ba, gara ma ki rabu dani ki fita a harka na, ni ban tab'a ganin Uwa irin ki ba".
Kanne ido Inna tayi ta soma balbalo masifa "Kaji shegiya da bata maida ragon suna, yo ni me ake da haihu irin taki, munafuka harni kike cewa wacce irin uwa ce?,tsinanniya, ga yaron shege kin kawo mun a gida, da ci daku zanji ko da tsabar warin da kikeyi? ".
Tab'e baki Madina tayi "Oho maki dai, dama tun yaushe na gama lalacewa kuma dukta silarki"hawaye ne ya gangaro kan fuskar ta, taci gaba da cewa "nan kika turani na rabu da Aminiya ta, duk alkhairin da tayi mun amman na zalunce ta, na raba ta da kowa nata, shin kina tunanin ko hakkin baiwar Allah zai barmu ne? ".
Shiru tayi ganin yarinyar data shigo da gudu a gidan tana kwallah kiran "Umma, Umma na "kara sowa tayi tare da dukawa gaban Madinat, duk da Cewa tasan Lamrat nada k'ananun Shekaru ta san ta da masifar wayau, kafin ta gama tunanin ta tace "Umma yauma kina yin kuka ne? "ta jefa mata tambaya.
"ba kuka nake ba Lamrat, ido na yanamun ciwo ne "
"sannu Umma na, zakiji sauki kinji, idan na girma na zama likita zan duba maki, kinga na dawo islamiyar bara na biya maki abunda na koya "nan ta soma karatu, rungume ta Madina tayi tana kokarin fashewa da kuka, tana kara jin tsananin kaunar y'ar tata, tana burin ta warke kodon y'arta ta samu rayuwa mai kyau da inganci, bata so tayi irin rayuwar da tayi.
"ji munahinci, yarinya tun cikin tsumma an kwarkware ta, ni wallahi ki nemo uban ta ki mai data gidansu na gaji da gorin mako ta akan y'ar shege ".
bata kuma kula ta ba, ta kama y'ar ta ta dingisa kafa tabar tsakar gidan.
*******
Kwance yake rufda ciki a saman Chair, rike da hannun kyakyawar yarinya ta fito ,zata kai kamar shekara hudu, daka gan ta, kaga sak mahaifin ta, da sallama mubaraka ta iso parlon, ba tare daya juyo ba ya amsa mata, shafa karamin cikin dake jikin ta tayi tace "Abban Jannat ".be juyo ba sai da yaji Jannat ta fara magana cikin kwarancin ta, da sauri ya juyo tare da rungumar yarinyar yana mata dariya "Abba" haka kawai take maimai tawa.
"tunda kun man tani a tsaye, to ni zan tafi kitchen "
Sai lokacin ya kalle ta fuska sake yace "a fito lafiya "
******
tunda safiya yayi suke faman hidimar shirin bikin su, daga filawa suke, an masu zane mai kyau ga kitso mai kyau, Amarya Aisha gani daya tawa Jannat taji jininsu ya hadu sosai suke shiri kamar sunyi shekaru tare da yamma kamu don haka suka tafi wurin makeup.
Majidadiβπ»
stylish star β¨
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 103 to 104
Not edited
Daga gidan makeup suka wuce wurin kamun, cancadi sosai Janna tayi kyau Cikin shigarta ta ango tasha makeup bazaka taba cewa ta aje yara har biyu ba, anan suka hadu dasu Arif shigarsu iri daya da faruq, tun daga nesa ya kure ta da ido, ba k'aramin kyau tayi masa ba,a hankali take takawa har zuwa in da yake, Shagwab'e fuska tayi Kamar zatayi kuka tace "ni Yaya karkasa na fadi, sai kallo na kakeyi ".
Murmushi yayi yace "ba dole na kalli mata na ba".
"Aunty kinyi kyau sosai"Twins suka hada baki.
Dukawa tayi ta basu pac a koshi tace "thank u Babies"
Wuri yayi wuri sai cashewa ake yi, figan agogon Arif, Anif yayi ya ruga da gudu, zagaye wurin suka shiga yi, baya baya Arif ya soma yi ji yayi ya fada jikin mutum ,juyowar da zaiyi, Arif ya rikesa shima, yace "thank God na kamaka yanzu ,oya bani da sauri "
"can't u see na bige Uncle? "abunda Anif ya fada kenan.
Zaro ido Arif yayi ya duka yana goge kafan wanda suka bige yace "am very sorry Uncle, be gani bane ".
Murmushi yayi ya duka tare da janyo yaran jikin sa, sosai suka burgesa lokaci daya yaji kaunar yaran na shigar sa, "OK don't worry, what's ur name guys? "
Murmushi sukayi Anif yace "am Faruq Umar Faruq ana Kira na Arif, sai twins bro na Ahmad Umar faruq muna kiransa Anif, and urs uncle ".
"am Sulaiman Abdullahi nice to meet u "hannu ya basu Suka gaisa yace "ina parents dinku ne ?"
"munzo nan da Appie dinmu ne sai Auntynmu Ammi na gida, u know we live in Adamawa "
Zaro ido Sulaiman yayi yace "Adamawa me kukazo yi nan to? "
"this is d first time mukazo nan fa, Aunty dinmu akewa biki, kai kuma waka sani anan ?"Anif ya masa tambaya.
"Ango din is my childhood friend ".
Shiru yayi yana kallon ta da mamaki Sosai fuskar sa ganin wacce ta rike yaran, kwata kwata hankalin ta baya kansa, yaran ta rike kwarai tace "don't try that again twin's, stop going out without telling Aunty ok"ta fada idon ta kansu.
Tunda tazo Wurin idonsa yake kanta ba karamin farin ciki ya shiga ba, don kallon farko ya gane Jannat, a hankali ya furta "Maryama "
Sai lokacin ta ga mutum a wurin kallon farko ta dago da sauri tare da ja baya, Hawaye ne suka silalo a fuskarta ,kara rike Hannuwan yaran ta tayi ta juya da sauri ta nufi Faruq dake tahowa farfajiyar wurin, wanda shima yaran yake nema, da sauri Sulaiman ya fizgo ta kafin ta fada jikin sa Faruq yayi saurin shiga tsaka nin su ta fada a kirjin sa ,kankame sa tayi ta rushe da kuka da kyarma jikin ta ko ina rawa yakeyi, a rude yake tambayar ta meke damun ta, amman ta kasa magana sai kallon Sulaiman da takeyi, juyowa yayi da kallon sa ga Sulaiman yace "bawan Allah me yake faruwa ne ".
wani kallo Sulaiman ya jefa masa yace "waye kai?, meye hadin ka da ita? "
Zaro ido Faruq yayi yace "haba malam ya ina tambayarka naga kasa ta kuka Sannan kamun wani banzan tambaya wanda bashi da amfani ,naga wancan yafi mahimmanci da mu sani, before mu fara sanin su waye mu ".
Kallonsa ya maida ga Jannat yace "Amira will u stop that nonsense and explain everything to me ganin kamar ransu ya soma baci su duka, kuma tasan halinsu duka da bakar zuciya yasa tace "he is Yaya Sulaiman ,my blood brother ".
Sai lokacin sunan y'an gidansu ya fado masa, kafin ya gama tunani yaji muryar Sulaiman yace "ina kika tafi?, sai kiyi fushi da gida ?shekara nawa, u mean wannan yaran shine abunda kika haifa?kizo muje gida yanzu ".
girgiza kai tayi ta kuma matse hannuwan yaran ta tana girgiza kai, "bazanje gida ba, Abba zai tsine mun ne, bazan koma ba, Abba baya so na "da gudu taja yaran ta tayi wajen wurin, da sauri Faruq yaje yaja motarsa yabi bayan ta ,a Titi ya samesa, gaban ta ya tare yasa yaran a mota sannan itama ya saka ta ya soma Driver seat yaja motar a guje da Mota Sulaiman ya rufa masu baya har yaga gidan da suka shiga, sannan ya Kama hanyar gida ganin babu nisa a tsaka ninsu.
"kinga ki daina kukan nan, kina dagawa yaranki hankali kijibi yadda suka koma gashi munzo gidan biki a haka zaki shiga da kuka?,share hawayen fuskar ta tayi ta balle murfin mota ta fice dakinsu ta wuce ta zube a bad tana jin zuciyarta kamar zata fito dan tsananin zugi da zafi, da yaran ya shigo rike a hannunsa kai tsaye dakin da Ammi take ya nufa.
(kuyi hakuri da errors, nayi gocewan k'ashi ne a hannu, da kyar nayi wannan ma, banyi editing ba)
Majidadi βπ»
stylish starβ¨
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
ππππππππ
*DAFIN SO*
ππππππππ
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 105 to 106
"A'a y'an bikin ne harkun dawo? "Ammi ta tambaye sa, "eh Ammi mun dawo, sannu da hutawa "
Kallon yaran ta yi wanda ta lura duk babu sukuni a tare dasu, janyo hannuwan su ta yi tace "Twin's din Ammi, waya tab'aku kuma? ".
"ba Aunty bace take ta kuka, daga ta had'u da wani Uncle "
Rungume yaran tayi tace "Ayyah am sorry, zata daina ku zo ku kwanta zanje na ganta yanzu "mai da kallon ta tayi ga Faruq tace "ka jira ni a parlo "kai kawai ya gyada mata ya fita tare da janyo Door din dakin. Yaran ta yi wa wanka ta saka masu kayan bacci, sai da ta tabbatar da bacci ya dauke su kafin ta dawo parlo, zaune ta same sa yana pressing phone dinsa, a chair ta zauna tare da rage sautin TV din dake ta aeki a parlon, wayan ya aje ya tattara duka hankalin sa gare ta, "waye Maryama ta had'u dashi? "tambayar data masa kenan, sai da ya nisa sannan yace "her Brother Sulaiman,shine abun ya tashi hankalin ta, kuma shi yana so ya tafi da ita gida ne ".
Shiru Ammi tayi tana nazari sannan tace "lallai al-amari babba, amman kuma hakan na da amfani kafin mu koma gida ya kama ta a dai dai ta komai, nikam kuma ina tunanin rabuwa da Y'ata, ban shirya rabuwa da ita ba ".murmushi Faruq yayi yace "amman ae kin shirya zama da ita a matsayin suruka ko? "ya mata tambaya yana sunne kai k'asa.
Murmushi Ammi tayi tace