An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ƁOYAYYEN SIRRI by Hafsat Umar Amintacciyar Jajirtattu
official
by
HAFSAT UMAR
Amintacciyar Jajirtattu
( AMANAR SHIDORIA WRITER'S )
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*
*Zazzafan Littafin da suke ongoing na jaruman Shidoria*👇
```1. BUDURWAR ABBANMU Pretty Sk.```
```2. WASAN KADDARA
Asmeetah Writter.```
```3. DAGA RUGA NAKE
Mrs Awwal.```
```4. KURUCIYA
Fatima Bintu Hussain.```
```5.MABANBANTAN ZUKATA
Maryam Star.```
```6. ƘADDARAR MASOYA
Umulkhairy Hashim Abo.```
```7. GARWASHI
Hafiza Amanar Ameey Laylerh.```
```8. YARINTA
Amanar Ta Batulu.```
```9. BOYAYYEN SIRRI
Amanar Shidoria Writter.```
```10. DAGA BAYA
Sha'awanatu Farouk Diggi.```
GARGAƊI 🧏🧏
Wannan littafin mallakin mai shi ne , ban yarda wani ko wata ta sauya man labari ba, Ƙagaggaen labari ne, idan yayi dai dai da rayuwan wani akasi ne.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
Not edit
🅿️ 01
Iska mai sanyi ke kaɗawa a unguwar GRA cikin birnin Kano.
Gidan Alhaji Sulaiman ya haskaka da fitilu, amma a cikin gidan zuciya ɗaya ce kawai take cike da duhu, zuciyar Zarah.
Zarah ba yarinya bace mai yawan magana, tana da nutsuwa, amma idan ka kalle ta da kyau zaka ga akwai wani abu da take ɓoyewa .
Sirri ne mai nauyi da ya fi ƙarfin shekarunta.
A wannan daren ne aka shirya bikin ɗaurin aurenta da Aminu, ɗan attajirin abokin mahaifinta.
Kowa cikin gidan yana murna.
Amma ita fa?
Tana tsaye gaban madubi, hawaye na zuba a hankali.
Wayarta ta yi ƙara, saƙo ya shigo wayan, wani irin faɗuwa gaban Zarah yayi.
“Zarah, idan baki faɗi gaskiya yau ba, komai zai lalace. Haris”.
Hannunta ya fara rawa.
Haris…
Sunansa kaɗai ya isa ya sa zuciyarta bugawa da ƙarfi.
Shi ne soyayyar da ta ɓoye tsawon shekaru uku, soyayyar da mahaifinta bai taɓa amincewa da ita ba, amma ba soyayya ce kaɗai matsalar ba, akwai wani abu da ya faru shekaru da suka wuce…
Wani dare mai kama da wannan da ta ke cikin ƙunci .
Wani hatsari.
Wani alkawari.
Wani sirri da zai iya rusa mutuncin iyalinta gaba ɗaya.
“Zarah!” Muryar mahaifiyarta ta katse mata tunani. “Baƙi sun fara zuwa ki fito.”
Ta share hawaye tayi murmushi na dole ta amsa kiran da ake mata .
Amma zuciyarta na cewa:
Yau gaskiya za ta fito fili… ko kuma zan shiga ƙunci har ƙarshen rayuwa na .
A ƙofar gida kuwa , wata mota ne a fake a ƙofar gidan Alhaji Sulaiman, wani kyakkyawan saurayi ya fito shi ba fari ba kuma ba baƙi ba irin chocolate colour ɗinnan, ya fito cikin baƙin kaya, idonsa cike da ɓacin rai da damuwa , kana ganinsa kasan hankalin sa a tashe yake.
"Yau ba zai bar Zarah ta shiga rayuwar da ba ta so ba."
Sai dai bai san cewa sirrin da yake ƙoƙarin fallasawa zai cutar da shi fiye da kowa a cikin gidan ba.
Ƙarar kiɗa ta cika harabar gidan Alhaji Sulaiman baƙi na ta shigowa, ana gaishe-gaishe, ana ɗaukar hoto.
Zarah na zaune a kujerar amarya, cikin kaya masu sheƙi.
Amma zuciyarta? Tana bugawa kamar za ta fasa ƙirjinta.
Aminu ya zauna kusa da ita, ya matso ya ce cikin murmushi,
“Kin yi shiru tun ɗazu… ko kina jin tsoro ne?”
Ta ƙoƙarta ta yi murmushi. “A’a…”
Sai dai kafin ya ƙara magana
Ƙofar harabar ta buɗe da ƙarfi.
Kiɗan ya tsaya cak, idanu suka koma gefe guda.
Haris ne.
Sanye da baƙin kaya, fuska a ɗaure, idonsa cike da fushi da ɓacin rai.
“Zarah!” ya kirata da murya mai amo.
Wani sanyi ya ratsa jikinta.
Alhaji Sulaiman ya miƙe tsaye. “Waye kai? Me kake so a nan?”
Haris bai kalli kowa ba sai Zarah.
“Ki faɗa musu gaskiya yanzu.”
Hankalin kowa ya koma kan Zarah.
Aminu ya miƙe tsaye shima. “Wace gaskiya?”
Zarah ta ji numfashinta ya ƙi fita ta kalli mahaifinta… ta kalli mahaifiyarta… sannan ta kalli Haris.
“Haris,” ya ce da ƙarfi, “shekaru huɗu da suka wuce, ɗanku ya yi hatsarin mota wanda ya kashe wani mutum kun rufe maganar saboda kuna da kuɗi.”
Alhaji ya yi sauri ya ce
“Ƙarya ne!” ya faɗa da ƙarfi.
Haris ya ci gaba: “Mutumin da aka kashe… mahaifina ne.”
Wani abu ya taso tun daga zuciyar Zarah, ji take yi tamkar Allah ya ɗauki ranta yaw ta huta,
sirrin da take ɓoyewa tsawon lokaci ya fito fili.
Aminu ya juya ya kalli Zarah. “Kin san da wannan?”
Hawaye suka fara bin kuncin ta.
“Eh…” ta faɗa a hankali.
Hayaniya ta tashi.
Wasu na cewa a kira ‘yan sanda wasu na mamakin wannan lamari.
Iyalan biyu sun fara zargin juna, wannan ya kalli wannan,zasu fara rikici sai kuma suka ji
wata murya ta fito daga cikin taron.
“Ba gaskiyar nan kaɗai ba ce…”
Kowa ya juya.
Wani saurayi ne, ɗan uwan Zarah, fuska cike da tsoro.
“Ba ɗan Alhaji ne ya tuka motar ba a wancan dare…” ya ce da rawar murya.
“Ni ne.”
Shiru ya sauka a babban falan kamar ruwa ya cinye su.
Zarah ta ji ƙafafunta sun yi sanyi.
Haris ya tsaya cak.
Alhaji Sulaiman ya kalli ɗan nasa da mamaki.
“To… me ya sa aka ce ɗana ne?” Aminu ya tambaya cikin ruɗani.
Saurayin ya kalli ƙasa.
“Saboda ana son a kare ni… domin ni ne babban ɗan Alhaji Suleiman Idan aka kama ni mutuncin family namu zai taɓu .”
Zuciyoyin jama’a suka rikice.
Haris ya yi shiru na ɗan lokaci… sannan ya ce:
“To ina kuɗin da ake turo wa duk ƙarshen wata ?”
Zarah ta runtse ido domin ita ta san amsar.
Kuɗin bai taɓa isa hannun su ba.
Hayaniya na ci gaba da tashi a harabar gidan wasu na ihu, wasu na kuka, wasu na ɗaukar bidiyo.
Sai kuma
Ƙarar motar ‘yan sanda ta karaɗe unguwa.
Motoci biyu suka tsaya a bakin ƙofa jami’ai suka sauko cikin kaya shuɗi suka fito da sauri.
“kowa ya tsaya a inda yake!” wani jami’i ya yi magana da ƙarfi.
Shiru ya sauka tamkar babu kowa a gurin , kamar an tsayar da lokaci.
Zarah ta ji hannunta na rawa Haris ya tsaya a gefen ta , idonsa na bibiyar duk wanda ke cikin gidan.
Alhaji Sulaiman ya matsa gaba. “Jami’i, wannan maganar ta iyali ce”
“Maganar kisa ba ta iyali ba ce,” jami’in ya katse shi.
Idanu suka koma kan saurayin da ya amsa laifi.
“Sunanka?” jami’in ya tambaya.
Ya haɗiye miyau. “Faisal…”
“Ka tabbatar kai ne ka tuƙa motar a ranar hatsarin?”
Kafin ya ba da amsa, wata murya ta fito daga bayan taron.
“Ƙarya yake yi!”
Kowa ya juya.
Wata tsohuwar mai aikin gidan ne.
“Na san wanda ya tuƙa motar a wancan dare na gani da idona!”
Zuciyar Zarah ta kusan tsayawa.
Haris ya matsa kusa.
“Waye?” jami’in ya tambaya.
Tsohuwar ta nuna yatsa.
Ba Faisal ba ne .
Ba Aminu ba ne .
Alhaji Sulaiman.
Wani sabon tashin hankali da yafi na farko.
“Ki rufe mana bakinki a gurin nan yanzu !” Alhaji Sulaiman ya ce cikin ihu.
Amma jami’in ya ce, “Ku kama shi.”
A cikin daƙiƙu, an sa masa sarƙi a hannu.
Zarah ta ji duniya na juyawa, wanda ta ɗauka a matsayin Mahaifinta… wanda take ɗauka tamkar ginshiƙi ne na mutunci da ƙimanta… kafin kowa ya Ankara Zarah ta faɗi ƙasa a sume.
Haris ya kalli Zarah, ba da fushi ba, da farin ciki,
“Wannan shi ne gaskiyar da nake son ta fito,” kafin ya ƙarasa magana ya ga Zarah kwance a ƙasa tamkar bata numfashi .
jami’in ya juya ya kalli Aminu,
“Kai ma za ka zo ofis domin bayar da bayani.”
Aminu ya tsaya kamar dutse.
Auren ya lalace, mutuncinsu ya rushe, Iyali sun shiga hannun doka
Sai kuma wani jami’i ya ciro wata takarda.
“Akwai bayanin cewa an fitar da kuɗi daga asusun Alhaji Sulaiman a ranar da hatsarin ya faru… amma iyalin mamacin basu karɓi wannan kuɗin ba.”
Sai lokacin idanu suka koma kan Haris da Zarah
domin ita ce ta yi aiki a bankin iyalinsu a lokacin .
Ganin Zarah bata numfashi yasa babban jami'i yace , a tada mota yanzu a wuce asibiti , nan take Haris wanda ya daɗe da fita daga hayyacin shi ya ɗauki Zarah kamar baby girl ya saka ta a mota sai asibitin
No edit
🅿️02
ZARGIN DA YA KARYA ZUCIYA
Bayan Zarah ta farfaɗo, ƴan sanda sun buƙaci ganinta domin wasu tambayoyi.
Ofishin ƴan sanda ya yi shiru fiye da yadda ake tsammani.
Zarah na zaune a gaban tebur, hannuwanta a haɗe, idonta sun yi ja saboda kuka, amma cikin idonta ba tsoro kaɗai ne a ciki ba, akwai wani abu da take ɓoyewa.
Jami’in bincike ya buɗe fayil.
“A ranar da hatsarin ya faru, an cire kuɗi miliyan goma daga asusun Alhaji Sulaiman, ke ce kika sa hannu a takardar fitar da kuɗin?."
Zarah ta runtse ido.
“Eh… ni ce.”
Haris da ke tsaye a gefe ya ji zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
“Amma…” ta ɗaga kai a hankali, “ba ni na karɓi kuɗin ba.”
“To wa ya karɓa?” jami’in ya tambaya.
Sai tayi shiru.
Haris ya matsa kusa da ita ya ce “Zarah, ki faɗi gaskiya, wannan ba lokacin ɓoye abu ba ne.”
Idanun Haris cike suke da tambayoyo ba zargi ba, amma akwai alamun rauni.
Zarah ta kalle shi, wannan shi ne mutumin da ta ke ƙauna tsawon shekaru, amma idan ta faɗi gaskiya, wataƙila za ta lalata komai, sai dai bata da zaɓi.
“Na ba wa wani amanar kuɗin,” ta faɗa a hankali.
“Waye?” jami’in ya tambaya.
Ta haɗiye miyau.
“Faisal.”
Haris ya juya da sauri. “Faisal? Amma shi ya ce bai san komai ba!”
“Saboda na roƙe shi ya yi shiru!”
Zarah ta fashe da kuka. “Na yi hakan ne domin na kare mahaifina.”
Ofishin ya yi tsit.
Ta ci gaba da magana cikin rawar murya
“Bayan hatsarin… mahaifina ya zo wurina cikin dare, ya ce in fitar da kuɗin, za a kai wa iyalin mamacin domin a sasanta, amma da na ba Faisal kuɗin bai kai su ba.”
Haris ya ji kamar ana zuba masa wuta a zuciyarsa.
“To me ya sa baki gaya min ba?” ya tambaya cikin rauni.
Hawayenta suka ƙaru. “Saboda ni ce dalilin, soyayyar mu kaɗai dalili ne, ba don soyayyata da kai ba, da mahaifina bai shiga wannan tashin hankalin ba.”
Haris ya yi shiru yana tunani , wato goyon bayan mahaifinta takeyi har yanzu, bata ma ganin abinda yayi.
Zuciyarsa na faɗa masa gaskiya take amma kuma… mahaifinsa ya mutu, iyalan sa sun sha wahala.
Jami’in ya ce, “Za a sake kamo Faisal domin ƙarin bincike.”
Aka fito da Zarah daga ɗakin bincike.
Haris ya tsaya shi kaɗai yana tunani soyayya a gefe guda, adalci a gefe guda, idan ya tsaya mata, mutane za su ce ya manta da mutuwar mahaifinsa,
idan ya juya mata baya zai rasa ta har abada, sai ya runtse ido,
sai ya furta a hankali, “Ba zan bari ki faɗi ke kaɗai ba… amma dole ne gaskiya ta fito gaba ɗaya.”
Hausawa sunce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya , ranar shiga kotu ya zagayo.
Kotun ta cika maƙil, ƴan jarida, ƴan uwa, maƙwabta kowa na son jin yadda labarin hatsarin da aka ɓoye shekaru huɗu zai ƙare.
Zaransa ɗaure da sarƙa, Faisal ma yana nan, fuska babu annuri.
Alƙali yah na zaune a kujerar masu ƙara idonta a ƙasa, Alhaji Sulaiman a gefe guda, hannu
shigo.
Kowa ya miƙe, bayan zaman alƙali kowa ya koma ya zauna.
An fara shari’a.
An karanta tuhume-tuhume, ɓoye gaskiya, hana isar da kuɗin diyya, da kuma karkatar da bincike,lauyan gwamnati ya miƙe.
“Wannan iyali sun yi ƙoƙarin sayen gaskiya da kuɗi,” ya faɗa da ƙarfi. “Sun ɓoye mutuwar mutum tsawon shekaru.!"
Sai kuma aka kira lauyan kare wanda ake zargi, kowa ya maida hankalin shi a ƙofa, sai aka buɗe ƙofa.
Haris ne.
Sanye da baƙin suit, fuskan sa ba yabo ba fallasa.
Zarah ta ɗaga kai da mamaki.
“Ni ne lauyan da ke kare Zarah Sulaiman,” ya faɗa cikin murya mai natsuwa.
Duk kotu ta yi shiru.
Lauyan gwamnati ya kalle shi da mamaki,“Kai ɗan mamacin ne.”
Haris ya amsa cikin ƙarfi
“Eh, amma adalci ba ya nufin ramuwar gayya, adalci yana nufin gaskiya.”
Zuciyar Zarah ta cika da wani irin farin ciki ba wai kawai ya tsaya mata ba ne, ya zaɓi gaskiya sama da fushi.
An kira Zarah ta ba da shaida, ta faɗi komai wanda ta sani, yanda aka umarce ta ta fitar da kuɗi, da yanda ta ba Faisal amanar su.
Sai kuma Haris ya miƙe
“Mai girma alƙali,” ya ce, “ba Zarah ta haddasa hatsarin ba, ba ita ta ɓoye kuɗin ba, ta aikata kuskure, eh , amma kuskuren biyayya ne ga mahaifi, ba niyyar cutarwa ba.”
Kotu tayi shiru kowa da abinda yake saƙa ma zuciyarsa.
Sai lauya ya kira Faisal.
Ya kasa ɓoye gaskiya, ya amsa cewa ya karɓi kuɗin, ya yi amfani da su domin biyan basussuka da kasuwancin da ya fara.
Wani hargitsi ya sake tashi a kotu.
Alhaji Sulaiman ya sunkuyar da kai, Alƙali ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce,
“Wannan shari’a an ɗaga zuwa mako mai zuwa domin yanke hukunci.”
Bayan an watse, Zarah ta tsaya gaban Haris.
“Me ya sa ka yi haka?” ta tambaya cikin rawar murya.
Haris ya kalleta.
“Saboda idan na bar ki, zan zama kamar su na zaɓi gaskiya amma ba na nufin zuciyata ba ta ji rauni ba.”
Hawaye suka sauka a fuskarta.
“Shin za ka iya yafe mana?”
Ya yi shiru, “zan iya gwadawa… amma sai bayan gaskiya ta bayyana.”
Bayan mako guda yaw an dawo kotu domin yanke hukunci, kotun ta sake ciko kamar da.
Zarah ta shigo tare da mahaifiyarta, Haris na gefe guda, kana kallan fuskan sa kasan yana cikin damuwa da tunani mai zurfi, Faisal yana gefe ya sunkuyar da kai.
Kotun ta sake cika kamar kullum, sai aka shigo da Alhaji Sulaiman kallo ɗaya zaka yi masa kasan yana cikin nadama, duk ya zama wani iri kamar mutumin da yayi shekaru a kulle cikin cell.
Alƙali ya shigo, aka miƙe,bayan ya zauna kuma kowa ya koma ya zauna.
Kafin ya fara magana ƙofar kotu ta buɗe wani dattijo ne, sanye da farin babbar riga. Fuska cike da tsoro da damuwa.
“Mai girma alƙali!” ya faɗa da ƙarfi, “Ina roƙon a dakatar da hukunci, akwai wani gaskiya wanda babu wanda ya sani sai Alhaji Sulaiman.”
Sai aka fara hayaniya.
Alƙali ya ɗaga hannu yace “Waye kai?”
“Sunana Malam Bashir, tsohon abokin marigayi.”
Haris ya ɗaga kai da sauri, Malam Bashir ya juya ya kalli Haris, idanunsa cike da tausayawa, “Ɗana gaskiya ba kamar yadda kake tunani take ba.”
Zuciyar Haris ta buga da ƙarfi, Malam Bashir ya juya ga kotu.
“A ranar hatsarin mahaifin Haris ba kawai ya mutu ba ne ya san wani sirri game da Alhaji Sulaiman kafin hatsarin.”
Kowa yayi shiru.
“Wane sirri?” alƙali ya tambaya.
Dattijon ya ɗaga murya
“Alhaji Sulaiman da marigayi sun kasance abokan hulɗar kasuwanci, amma kwanaki kafin hatsarin, sun yi rikici mai tsanani saboda wata takarda ta mallakar fili.”
Idanu suka koma kan Alhaji Sulaiman.
Malam Bashir ya ci gaba
“Marigayin ya gano cewa an sauya wasu takardu ba bisa ƙa’ida ba kuma ya yi niyyar kai ƙara.”
Zuciyar Zarah ta kusan tsayawa da jin wannan sabon al'amari.
Haris ya ji wani abu tun daga zuriyar sa har tsakiyan kansa.
“Shin kana nufin ba hatsari bane shiryayye shiri ne?” lauyan gwamnati ya tambaya.
Malam Bashir ya ce cikin sanyi,
“Ba wai nace an shirya hatsarin bane amma ina cewa ba hatsari ne kawai ba, akwai rikici mai zurfi a baya.”
Kotun ta sake rikicewa.
Haris ya juya ya kalli Alhaji Sulaiman.
“Shin mahaifina ba hatsari yayi ba , daman kashe shi kayi?” ya tambaya cikin murya mai rauni.
Alhaji Sulaiman ya yi shiru, sai hawaye suka sauko masa.
“Na yi kuskure” ya faɗa cikin ƙasa da murya, “Amma ban taɓa tunanin zai mutu ba.”
Zarah ta ji duniya yana juyawa fiye da kima, idan wannan ne gaskiya to ya soyayyarta da Haris ta kasance, tabbas akwai wani abun kenan?.
Alƙali ya buga tebur,
“za a buɗe sabon bincike game da wannan zargi, wannan shari’a ba za ta tsaya a nan ba domin sai anyi bincike mai zurfi.”
Bayan an watse, Haris ya fita daga kotu ba tare da ya kalli Zarah ba, sai ta biyo shi da gudu,
“Haris!” ya tsaya,
“Idan mahaifina ya cutar da naka ba zan taɓa yafewa kaina ba,” ta faɗa cikin kuka.
Haris ya juya a hankali,
“ba ke kika yi ba,” ya ce cikin sanyi, “Amma yanzu dole ne in gano ko mutuwar mahaifina hatsari ne ko wani abu fiye da haka.”
Idanunsa sun cika da wani sabon ƙuduri.
Ba kawai kare soyayya bane a gabansa.
Akwai bincike akan mutuwar mahaifin shi.
🅿️03
Daren ya yi duhu sosai , zukata da yawa na cikin ruɗani da tashin hankali.
Haris na zaune a ɗakinsa, tsofaffin takardu da fayiloli a shimfiɗe a gabansa.
Hoton mahaifinsa na gefen tebur yana kallonsa kamar yana neman adalci.
Maganar Malam Bashir na yawo a kansa
“Ba hatsari ne kawai ba…”
Haris ya fara da duba tsoffin takardun kasuwanci tsakanin mahaifinsa da Alhaji Sulaiman.
Akwai takardar mallakar wani fili a gefen gari, fili mai daraja sosai, amma wani abu da ya ja hankalinsa, sanya hannu guda biyu daban-daban a takarda ɗaya, alamu ya nuna anyi kwaikwayon sanya hannu amman idan ka lura akwai banbanci, ɗaya na mahaifinsa, na biyu ba daidai yake ba.
“Karye ne” ya furta a hankali.
Washegari ya je ofishin rajistar filaye, da ƙyar ya samu kwafin asalin takardar, a nan ne zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
Asalin takardar ya nuna cewa filin mallakin mahaifinsa ne gaba ɗaya, amma kwafin da ke hannun Alhaji ya nuna rabon kashi 50–50.
An sauya bayanai da komai na filin amman yanzu ya samu hujja da zai yi amfani da shi a kotu, sai ya kama hanyar zuwa gida .
Akan hanyarsa ya lura da wata mota tana binsa, ya ƙara sauri, motar ta ƙara sauri, zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi, ya juya cikin wata ƙaramar hanya motar ta bi shi ba zato ba tsammani motar ta rufe masa hanya.
Wasu maza biyu suka fito.
“Ka daina binciken da kake yi idan ba haka ba zaka je inda mahaifinka yaje,” ɗaya daga cikinsu ya faɗa cikin ƙasa da murya.
Haris ya tsaya yana kallan su.
“Ko me zai faru sai gaskiya ta fito,” ya amsa.
Ɗaya daga cikinsu ya matso kusa da Haris yace ,
“Ba ka san abin da kake shiga ba, wannan ya fi rikicin da iyayen ka sukayi a baya hatsari , fatan ka fahimta.”
Sun bar shi da barazana mai cike da ruɗani, kenan akwai wani bayan Alhaji Sulaiman.
Haris ya tsaya a wurin na ɗan lokaci, zuciyarsa na bugawa.
A gefe guda.
Zarah na zaune a ɗakinta, tana jin tsoro, sai taji saukan saƙo daga lambar da ba ta sani ba
“Ki gaya wa Haris ya tsaya da binciken da yakeyi , idan ba haka ba, zai rasa abin da ya fi so.”
Hannunta ya fara rawa, ta san Haris ba zai tsaya ba, amma idan ta gaya masa wannan saƙo zai ƙara shiga cikin haɗari.
Ta ɗauki waya ta kira shi.
“Haris… don Allah ka daina binciken da kake yi.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci sai yace,
“Sun fara tsoratar da ke ko?” ya tambaya cikin sanyi murya.
Hawayenta suka zubo.
“Ba na son rasa ka.”
Yayi shiru na ɗan lokaci.
Sai ya ce a hankali.
“Idan na tsaya yanzu zan rayu da tambaya har abada, amma zan yi komai a hankali na yi miki alkawari.”
Bayan kwana uku da barazanar da akayi ma Haris da Zarah.
Haris ya fita cikin dare, daren ya yi tsit, iska mai sanyi na kaɗawa, tituna sun yi shiru.
Haris na kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya gana da wani tsohon ma’aikacin ofishin rajista wanda ya yi masa alƙawarin ba shi ƙarin bayani.
Zuciyarsa na cike da tunani, sai wayarsa ta yi ƙara, Zarah ce, sai ya ɗaga.
“Haris… ina jin tsoro,” muryarta na rawa.
“Kina gida?” ya tambaya cikin damuwa.
“Eh… amma ina jin kamar ana kallona.”
Kafin ya amsa, sai yaji ƙarar birki a gabansa.
Wata mota ta tsaya a gabansa ta toshe masa hanya.
Zuciyarsa ta buga da ƙarfi, sai aka buɗe ƙofa suka fito, wasu mutane uku ne duk sun rufe fuskokinsu .
“Haris Sani,” ɗaya ya kira sunansa cikin sanyi murya, “Mun gargaɗe ka amman kaƙi ko.”
Haris ya riƙe wayarsa da ƙarfi, “Zarah,” ya faɗa cikin gaggawa, “ki kulle ƙofa ki kira ‘ƴan sanda.”
“Me ke faruwa?” ta yi ihu a waya.
Amma kafin ya amsa ɗaya daga cikin mutanen ya ture shi da ƙarfi, wayarsa ta faɗi ƙasa.
An yi ɗan fafatawa tsakanin su da Haris, ya yi ƙoƙarin kare kansa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi amman ya jure.
“Ka tsaya da wannan binciken!” wani ya faɗa cikin tsawa.
“Ba zan tsaya ba!” Haris ya amsa da ƙarfi.
Sai wani ya bugi ƙafarsa da ƙarfi ya faɗi ƙasa numfashinsa ya yi nauyi.
“Wannan gargaɗi ne na ƙarshe,” ɗaya daga cikinsu ya raɗa mai a kunni. "
Suka bar shi a kan titi suka tafi.
A ɓangaren Zarah kuwa.
Ta ji layi ya katse, ta sake kira ba a ɗaga ba, zuciyarta ta shiga wani irin bugawa da ƙarfi.
Ta kira ƴan sanda, ta ɗauki hijabi ta fita daga gida ba tare da sanin inda za ta dosa ba, sai dai ta san zuciyarta na gaya mata wani abu ya faru.
Mintuna kaɗan bayan haka, an aka samu Haris a kan titi, ya samu raunuka amma yana numfashi.
An kai shi asibiti, Zarah ta iso cikin kuka, idonta cike da tsoro, ta tsaya a bakin gadon da aka kwantar da shi tana kallan yanayin fuskar sa ta nuna wahala, amma idanunsa sun buɗe a hankali, ya kalleta yace
“Bansan neman gaskiya yana da wahala ba.” ya furta cikin sanyin murya.
Hawaye sai gudu yakeyi akan fuskanta.
“Wannan ya wuce duk inda muke tunani Haris, ga dukkan alamu akwai wani mai iko a cikin wannan lamari, mu barsu kawai.”
Haris ya ɗan yi murmushi mai rauni.
“To mu ma za mu zama masu