waje."
Dije ta sauko a hankali kamar mutumiyar kirki , sai raba ido take yi da dai ya kasa haƙuri tace " Baffa wannan gidan yana da kyau kamar ni, Allah ni dai ban zan zauna bayan koma Gwadabawa ba har abada, gaskiya ƴan birni suna jin daɗi."
.Malam Zailani bai tsaya sauraren Dije ba ya fara sauke kaya, Mero kuwa tana tsaye da ɗan cikinta, har suka kammala Dije na kalla kalle.
Bayan sun kammala Muzaffar ya nuna masu ɗakin da ya zaɓa, ɗaki biyu ne ciki da falo sai bayi, sosai suka yi farin ciki da wannan sauyi suka ƙara yi ma Allah godiya.
Alhaji Abubakar ne ya fito ya kama hanyan parking space, yana isowa ya ga su Malam Zailani har sun iso sannu da zuwa ya yi musu sannan ya faɗa musu yana uziri idan ya dawo zasu yi magana ya shiga mota ya kama hanyan Company.
Yana isowa Company, office ɗin shi ya shiga , yana zama Yusuf yana shigowa, su kayi musabaha sai ya zauna ya fara yi mai bayani.
Yusuf pa " Oga wannan lokacin mun samu riba sosai gaskiya, ma'aikata kuma babu Matsala, sai dai akwai maƙiya da yawa, kuma akwai wanda zai zo ya rusa mu , sai dai bamu san da wani fuska zai zo mana ba , we have to be very serious Sir."
Alhaji Abubakar " Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah, Maƙiya kuma Allah kaɗai yasan yanda zai yi da su karka damu , daman iya kan maganan kenan ko dai akwai wani?."
Yusuf pa " babu komai Sir ."
Alhaji Abubakar " yanzu zan koma gida in sha Allah, akwai abu mai muhimmanci da zanyi."
Kusan tare suka miƙe, suka kama hanyan lipter , bayan sun sauko ƙasa sai ya nufi parking space, kafin ya ƙarasa kusa da motan boom💥 ya tashi da motan , ga ba ɗaya iskan boom ɗin ya buge shi ya faɗi ƙasa , ma'aikata ne suka zo a guje ssuka tayar da shi , bai samu rauni ba.
Kowa ya jijjiga da ganin wannan al'amari, cikin minti kaɗan ƴan sanda suka iso gurin, Barrister Joseph Abraham, ya sauko ya tsaya yana ƙare komai da kallo, sosai ya yi bincike amman babu abinda ya samu.
Alhaji Abubakar yana gefe yana tunanin abinda ya faru yanzu , waye me neman rayuwar sa, kenan iyalina suna cikin haɗari , lokacin ya ƙara tsorata.
Barrister Joseph " hope u a fine, Sir can we talk now?."
Alhaji Abubakar " I'm fine Barrister, I can't talk now , I'm sorry, we can talk tomorrow by 4:00pm in my house ok ."
Yusuf ne ya fito da sauri domin ya ji hayaniya sosai , abinda idon shi ya gani ya bashi mamaki boom 💥 a motan Oga, gaskiya wannan lamarin abun tsiro ne.
Alhaji Abubakar ya ce ya ɗauko mota ya kaishi gida yanzu , Barrister Joseph ya ce dole sai an haɗa shi da jami'ai , amman yaƙi yarda , a haka dole aka ƙyale shi.
Bayan sun kamo hanya Yusuf ya ce " Sir what does that mean, can u imagine, tayaya zasu yi tunanin kasheka zai zo musu da sauƙi, it can be possible."
Alhaji Abubakar " Yusuf kenan kai dai ka tayani da addu'a , in sha Allah ba dai mutum ba sai sai Allah , Amman tayaya aka sanya min boom a mota , da ga gida fa nike sai Company."
Horn ya yi mai gadi ya buɗe mai get, parking space ya nufa , bayan ya yi parking sai ya fito ya buɗe ma Alhaji ƙofa shima ya fito.
Baiga kowa a harabar gidan ba, sallama ya yi ma Yusuf shi kuma ya shiga falo da sallama a bakin shi.
Hajiya Maryam ne zaune a ƙasan carpet , jin sallama tasan mai gidan ne ya shigo sai ta amsa , amman abinda ta gani yasa ta zaro ido , ganin yanayin Alhaji kaɗai ya isa ya isar mata da saƙon akwai abinda ya faru, bata tsaya mai tambayoyi ba ta yi mai sannu da dawowa , ta ce yaje ya watsa ruwa abinci ya kammala, ba yabo ba fallasa ya amsa mata ya haura sama domin yin wanka, a ƙalla 1hour ya ɗauka ya fito, yana fitowa ya nufi dining ya zauna, ta tashi ta haɗa mai abinci, bai wani ci da yawa ba ya ce ya ƙoshi , ta tattara kayan ta ajiye , ya tashi ya koma ya zauna a kujera, ita ma ta tashi ta biyo shi, tana kallan shi bata ce komai ba .
Sun ɗauki minti talatin a haka sanan ya nisa ya ce " Maryam " sai kuma ya yi shiru.
Jin ya ambaci sunan ta sai da gaban ta ya yi mummunan faɗuwa , domin har ta manta rabon da ya kira sunan ta, nan take cikin ta ya murɗa, Salati kawai ke fita a bakinta , kafin Alhaji Abubakar ya ankara har jini ya fara zuba mata, a ruɗe ya fito yana ƙwala ma Muzaffar kira , sai Mero ta fito da sauri jin wannan kira tasan balafiya ba gaskiya.
Muzaffar kuwa kaman wanda aka jefo haka ya fito da ga ɗaki, Alhaji ya bashi izinin ya tayar da mota Madam ba lafiya, sannan ya kalli Mero da ke bakin ƙofa a tsaye tana kallon su, ya mata alama da hannu , alamun ta biyo shi.
Nan ta taimaka mai suka ɗaukota suka fito waje, Muzaffar kuma ya tayar da mota, babu ɓata lokaci suka sanya ta ciki ya ce ma Mero " Bismillah, san Allah muje ki taimaka min ."
Sai a lokacin Malam Zailani ya fito da ga banɗaki yaji ana ta hayaniya, ganin abinda ke faruwa yasa butan hannunsa ya faɗi ƙasa ya ƙaraso ya ce "Mero ki shiga kuje mana, Allah ya bata lafiya."
Suna shiga Muzaffar ya tayar da mota already an buɗe get daman , a guje ya fito da ga gida yana mamakin wannan al'amari, ko mene ya samu Hajiya, bai gama tunani
ba kawai ya ga an tare musu ga ba da baya babu hanya, a ruɗe ya zaro ido yana ganin wannan wani irin hauka ne.
Kafin ya yi wani yunƙuri sun fito da ga mota , kowannen su da baƙin kaya fuska a rufe gasu kaman samudawa tsaban girma da tsawo, kana ganinsu kasan ba ƴan Nigeria ba ne.
Nan take suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa.
Kasancewar hanyar ba na kowa da kowa ba ne yasa babu mutum ko ɗaya , Har suka gama ɓarin harsashi babu mota ko mutum da ya gitta hanyan, bayan sun lafa da harbin, mutum ɗaya ya matso kusa da motan ya leƙa ya tabbatar da babu abinda ya same su , sai ya ce " wannan gargaɗi ne kawai ba'a ba mu daman kashe ka ba, razana ka aka ce mu yi " sai ya juya suka shiga mota suka tafi.
Alhaji Abubakar tsaban firgita da tsoro yasa idan ka kalle shi za ka ɗauka ya suma ne , sosai hankalin shi ya tashi da wannan al'amari, Muzaffar ma ya tsorata sosai, Mero kuwa daman tun harbin farko ta suma.
Muzaffar kuwa ganin waɗannan mutanin sun tafi yasa ya ja motar da ƙarfi suka bar gurin, tafiya suke yi tamkar zasu tashi sama, awa ɗaya suka ɗauka a hanya suka iso Daama Specialist Hospital Jimeta , cikin hanzari Muzaffar ya fito ya buɗe ɗayan ƙofan ya kamo Mero shi kuma Alhaji Abubakar ya ɗauko Matarsa.
Cikin hanzari ma'aikata suka zo da kujeran ɗora mara lafiya aka ɗauki Mero , gado Kuma aka ɗora Hajiya Maryam kasancewar tafi jikkata sosai , Emergency aka nufa da ita kai tsaye, babu ɓata lokaci Doctor ya shigo, suka duƙufa kanta, kowanne cikin su ya yi zufa sosai , kasancewar 3hours suka ɗauka amman numfashinta bai daidaita ba, sai suka yanke hukuncin bari su gwada na ƙarshe idan har bata farfaɗo ba mun rasa ta kenan . 😔
Ɓangaren Mero kuwa bayan an shiga da ita ɗaki daban kusa da Emergency kasancewar suma tayi, ba'a sha wahala ba ta farfaɗo , amman anyi mata alluran bacci saboda cikin da ke jikinta.
Hajiya Maryam kuwa likitoci sunyi iya bakin ƙoƙarin su amman sun kasa ceto rayuwar ta, Doctor ya cire kayan aiki yasa a kira mai Alhaji Abubakar, kafin ya ƙarasa fita yaji na'urar dake lura da numfashi ya yi ƙara alamun numfashinta ya dawo , cike da mamaki Doctor ya dawo da sauri ya ƙara duba ta da kyau.
Doctor ya ce " her breathing is back but she is mentally unstable at the moment, ohh my God she's in danger, please take care of her, and don't let anyone in."
Nurses " Ok sir , as u said ."
Alhaji Abubakar shi ma an duba shi aka tabbatar mai jinin shi ya hau ya kamata ya kwantar da hankalin shi, bayan an gama duba shi ya fito kenan Doctor shi ma yana fitowa daga Emergency room, da sauri Alhaji Abubakar ya ƙaraso yana tambayan shi jikin marasa lafiya.
Sai da Doctor ya yi ajiyan zuciya sanan ya ce " Sir I'm sorry to say, your Wife she's in serious danger, and about her pregnancy, the baby's are fine don't burder your self ok , and we will take care of her , she will be ok."
Alhaji Abubakar jikin shi ya yi sanyi sosai da maganan likita, ya ɗan nisa kaɗan ya ce " Doctor zan iya ganinta yanzu."
Doctor " gaskiya kayi haƙuri domin tana buƙatar hutu yanzu, anjima za ka iya ganinta, amman Kai kaɗai, ba za mu iya cewa yawshe zata farfaɗo ba , shi yasa bamu buƙatar hayaniya komin ƙanƙantar sa ka kwantar da hankalin ka, she will be fine in sha Allah."
Muzaffar ya yi matuƙar tausaya ma Alhaji, cikin tausayawa da ƙasa da murya ya ce " Alhaji dan Allah kayi haƙuri, duk abun da ya faru da bawa daga Allah ne , kuma wannnan ƙaddara ne Allah ya bamu ikon cinye wa."
Alhaji Abubakar ya ji daɗin maganan Muzaffar sosai, ya ji sanyi a zuciyarsa fiye da ɗazu da ya ke ji kamar dutse aka ɗora mai a zuciya, godiya ya yi mai , sannan ya ce suje su duba Matar Malam Zailani.
Ɗakin kusa da Emergency room suka shiga, su na shiga tana farkawa, kallon ɗakin da take ta fara yi, sai lokacin ta tuna abin da ya faru, ashe bata mutu ba tana a raye, hamdala tayi sosai ga Allah, bata tsorata sosai ba saboda baccin da tayi da yawa yasa ƙwaƙwalwar ta ya sassuta daga tsoron da taji.
Alhaji Abubakar ya ce " Sannu, ya jikin da sauƙi sosai, fatan babu wani abun da kike ji yanzu."
Mero " Alhamdulillah Alhaji da sauƙi sosai ba na jin komai, ya jikin Hajiya?."
Alhaji Abubakar " Jikin Hajiya da sauƙi Alhamdulillah, yanzu ki shirya Muzaffar zai mayar da ke gida, likita ya faɗamin kina da ciki, kuma cikin babu abun da ya same shi, kawai ana buƙatar ki huta sosai ne, Muzaffar dan Allah ka kula sosai ka Kaita gida yanzu."
Muzaffar " Alhaji ai karka damu in sha Allah za mu isa gida lafiya, takwarar Hajiya muje ko."
Alhaji Abubakar " takwarar Hajiya kuma sunan ta Maryam ne, kai Masha Allah, wannan babban suna ne sosai, Muzaffar ka cika surutu ku kama hanya ka ga har an kusa kiran magrib."
Miƙewa Mero tayi suka fito daga ɗakin, kai tsaye hanyar fita suka nufa, sai da Alhaji Abubakar ya tabbatar da sun tafi sannan ya dawo ya tsaya gaban ɗakin Emergency, kallon ta ya ke yi cikin so da ƙauna, hawaye ne ya zubo mai ba tare da ya sa ni ba, addu'a yake yi Allah ya kare masa matarsa daga sharrin waɗannan mutanin da bai san ko su waye ba, ya ɗauki kusan minti talatin a tsaye sanann ya nufi masallacin da ke cikin asibiti.
Bayan ya yi alwalla ya shiga Masallaci ya tayar da sallah raka'a biyu ya zauna yana addu'a, har aka kira sallah magrib, bayan an idar da sallah bai fita ba, ya zauna yana karatun Alqur'ani, sosai yaji zuciyarsa tana rage nauyi, sai da ya yi Isha'i sannan ya baro masallaci, ya kama hanyar zuwa Emergency room.
Yanda ya barta haka ya sameta, sai dai likita da ya gani a ciki yana duba ta, har yanzu tana numfashi amman bata farfaɗo ba tukunna, likita ya fito da sauri Alhaji Abubakar ya zo yana tambayar shi ko zai iya ganin matarsa, likita ya ce ya shiga babu matsala amman kada ya yi hayaniya sosai, godiya ya yi ma likita Sannan ya tura ƙofar ɗakin da sallama a bakin shi duk da yasan babu wanda zai amsa.
Bayan ya shiga ɗakin zaunawa ya yi a kujeran da ke gaban gadon, hannun ta ya kamo ya riƙe sosai cikin nashi nan take hawaye ya zubo mai cikin sheshsheƙa yake magana " ya Allah ka tsare mu da sharrin Mutum ko Aljan, Allah ka shiga tsakanin mu da maƙiya, Allah ka baiwa mata na lafiya, Allah ka bamu ikon cin wannan jarabawa."
Sosai ya yi addu'a yana hawaye, bayan ya kammala ya gyara mata hannu ya ɗora a saman cikinta ya fito, masallaci ya zarce lokacin ƙarfe 9:30 ta yi, alwalla ya yi sannan ya shiga Masallaci ya cigaba da faɗa ma Allah danuwarshi.
SHAWARA GA ƳAN UWA NA MUSULMAI MAZA DA MATA.
Ya kamata mu sani cewa dukkan abin da ya faru da bawa muƙaddari ne daga Allah,
mu rinƙa tawakkali, kuma ruƙa komawa ga Allah a duk lokacin da wani mummunan abu ya samemu kada mu manta da Ubangiji akowane yanayi muke ciki, Alqur'ani yana wanke zuciya sosai, ka tashi cikin dare koda raka'a biyu kayi ka karanta Alqur'ani kayi addu'a iya ka faɗa ma Allah damuwarka wallahi Allah zai ji kukan ka , domin baya bacci, Allah ya bamu ikon yarda da ƙaddra na alkhairi ko na sharri, Amen.
❤️🔥 ƁOYAYYEN SIRRI 🔒🔐
Na
Hafsat Umar
🤍 Amintacciyar Jajirtattu ✍️
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
Wannan page na sadaukar da shi ga mahaifiyata, Allah ya ƙara miki nisan kwana.🙏
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
🅿️ 12
DAAMA SPECIALIST HOSPITAL JIMETA.
A kwana a tashi asarar mai rai, yaw watan su Alhaji Abubakar bakwai a asibiti, Alhamdulillah jikin Hajiya Maryam da sauƙi sosai, cikin ta kuma wata tara kenan, yaw aka yi sallama suna shirin komawa gida, anyi anyi Alhaji Abubakar ya barta har ta haihu annan yaƙi yarda, ya ce ya gaji da zaman asibiti.
Muzaffar da Anas driver da Malam Zailani suka turo ƙofa da sallama a bankinsu, bayan sun ƙaraso suka gaggaisa.
Bayan sun kammala gaisuwa sai suka kwashe kayayyakin zuwa gurin mota, reception suka nufa, Alhaji Abubakar ya ce su kama hanyar parking space zai sallami likita, suka kama hanyar fita, bayan sun isa gurin motan suka sanya kaya a boot Hajiya Maryam kuma ta shiga mota ta zauna, basu ɗauki wani lokaci ba sai ga Alhaji Abubakar ya fito, kai tsaye mota ya shiga suka kama hanyar gida.
Baba Mai gadi jin horn ya yi sauri ya buɗe get daman yasan za su dawo yaw.
Su na yin parking suka fito, Mero itama ta fito d byaga ɗaki da murmushi a fuskarta, sannu da dawowa su ka yi masu sannan suka shiga ciki, Mero ne ta shiga da wani kayan a hannunta, Blessing da Peace su na gyara kulolin abinci su ka ji sallama, cikin farin ciki suka yi musu maraba da zuwa suka shiga ciki, Blessing da Peace Kuma suka tambayi ko akwai wani kaya, jin akwai sai suka fita har da Mero su ka ƙarasa kwaso kayan.
Alhaji Abubakar fita ya sake yi saboda zai je Company ya kwana biyu bai je ba, yana shigowa harabar Company ya nufi parking space, bayan ya fito office ɗin shi ya nufa.
Yana zama Yusuf PA ya shigo, zama ya yi suka fara tattaunawa akan kasuwanci, sun ɗauki lokaci sosai sannan ya tashi ya shiga toilet ɗin da ke cikin office ɗin shi ya kama ruwa sannan ya yi alwala domin gabatar da Salla azahar.
Ƙarfe biyar na yamma ya kama hanyar komawa gida, har ya yi nisa da tafiya sai ya lura ana bin bayan shi, ya tsorata sosai amman haka ya cigaba da tafiya har ya isa unguwar su ya yi horn mai gadi ya buɗe mai get, da sauri ya shiga yana hamdala a zuciyarsa.
Mero ne zaune da cikin ta a ƙalla shi ma zai iya kai wata takwas ko tara, Dije ne kusa da ita ta na yi mata tausa a ƙafa tana gunguni, Malam Zailani ya fito daga ban ɗaki kenan ya hango Dije na tura baki.
Malam Zailani "Khadijah yawshe zaki yi hankali ne tausan ƙafar kike tura ma baki, ki faɗamin amfanin ki a gidan nan banda wannan, ja'irar yarinya kawai ƙauye zan mai da ke kowa ya huta."
Dije jin za'a mayar da ita ƙauye sai ta koma fuskan tausayi ta ce " Haba Baffa ba sai an yi haka ba daga yaw nine zan rinƙa sanwa, shara, wanke wanke, wankin kaya, harda bacci idan anayi ma wani zan muku ".
Malam Zailani yace " Khadijah kenan ai duk wanda ya ci abincin da ki ka yi wallahi sai ya zama gawa, balle wanki da wanke wanke, ki fara iya wanka ma tukunna kafin kiyi waɗannan ayyukan".
Su na cikin magana sai Alhaji Abubakar ya katse su " Ƴata ƙyalesu kinji babu wanda zai mayar da ke ƙauye, zan sanya ki makarantar boko da islamiyya nasan kina so, kuma zaki rinƙa koyan girki, wata rana zaki musu girkin da sai sun manta hanyar ƙauyensu".
Dije da sauri ta miƙe kamar mutumiyar kirki har da tsugunnawa tana mai godiya.
Anas driver Wanda shigowar shi kenan ya ga wannan dramer dariya kawai ya yi, sosai Dije na burgeshi, saboda bata da shiga abin da bai shafe ta ba shiyasa, barta kawai da ƙazanta da rashin aikin gida da sauransu, iya kanta cin abinci da bacci shikenan.
Anas sosai ya yi nisa da tunani akan dije kawai kamar daga sama ya ji ance " Anas meye kake yi ne, ana kiranka tun ɗazu ka ƙyale mutani."
Muzaffar ne ya ke kiran Anas, tsaban ya yi nisa kallon Alhaji Abubakar da Dije shi ne bai ji ba.
Anas a firgice ya juya yana kallon Muzaffar, yana tunani a zuciyarsa yawshe ya kira shi, yasan ƙarya ne ma, be gama tunani ba ya ƙara jin Muzaffar na ƙwala mai wani kira.
Alhaji Abubakar yana gama magana da Dije ya wuce sashen shi, da sallama ya tura ƙofan falon babu kowa sai ya haura sama.
Ɗan kishingiɗa tayi a gefen gado tana addu'a saboda jikinta har yanzu babu ƙwari ga tsohon ciki, tana jin sallama tasan mijinta ne, amsawa tayi sannan ta ɗan gyara zama, turo ƙofar ya yi ya shigo.
Alhaji Abubakar " Maman Aryan da Zarah kenan anyi nauyi, ya jikin da sauƙi ko, fatana yanzu ku sauka lafiya ke da takwarar ki domin ga dukkan alamu tare zaku haihuwa."
Hajiya Maryam " in sha Allah za mu sauka lafiya ka daina damuwa ka ji ko, ya aikin fatan komai lafiya, kuma fatan kaima kana lafiya,
Alhaji Abubakar " Alhamdulillah sai gadiya, ina lafiya, ya jikin fatan da sauƙi sosai?."
Hajiya Maryam " jiki da sauƙi mun gode Allah."
DIJE POV
Sosai take jin daɗi har da tsalle jin Alhaji Abubakar ya ce zai sanyata makaranta boko da islamiyya, Mero kuwa murmushi kawai take yi, tana fatan Allah ya nuna mana ranar da Dije zata yi hankali, Malam Zailani kuwa tun da Alhaji Abubakar ya wuce shima ya ɗauki buta ya yi alwalla don gabatar da sallan magrib.
Dije kuwa da ƙyar aka samu tayi alwala domin daman bata da mu da Sallah ba, kakanta cewa take yi bata isa hukunci akan Sallah ba, tun Malam Zailani ya na jin haushi har ya haƙura ya zuba musu ido.
RANAR JUMA'A ƘARFE 2:00PM
Yaw watan ɗaya kenan da dawowar su Alhaji Abubakar daga asibiti, daren ya yi shiru sai walƙiya da ake yi, sosai gari ya fara duhu aka fara ruwa kamar da bakin ƙwarya.
A cikin gidan Alhaji Abubakar kuwa Hajiya Maryam ne zaune akan sallaya, bayan ta idar da Sallah ta zauna tana azkar, domin gaba ɗaya yaw haka ta wuni ba ta jin daɗi sosai, wani irin tsawa aka yi mai ƙarfin gaske sai da alƙalamina ya faɗi ƙasa, da sauri na lalubo shi domin kawo muku rahoto, Hajiya Maryam kamar wasa maranta ya fara riƙewa, zata tashi kuma tashi ya gagara, wani uban salati tayi har sai da ya firgita ya ɗauka ɓarayi ne a gidan, ganinta ya yi a durƙushe tana salati, a ɗari biyar ya diro daga kan gado ya yi falo, tsaban ruɗewa har ya nufi ɗakin shi sai ya tuna falon ƙasa zai sauka, da sauri ya dawo ya nufi hanayar falo, tun kafin ya buɗe ƙofa ya fara ƙwala ma Muzaffar da Anas kira ba ƙaƙƙautawa, yana fitowa ya nufi sashen ƴan aiki Peace ya fara buga na ƙofa, Peace da bacci ya mata daɗi jin bugun ƙofa da ƙarfi ta zabura ta miƙe tana raba ido, a tunanin ta ɓarawo ne, nan ta fara kiran Yesu Almasihu ba ƙaƙƙautawa, a karo na ba adadi Alhaji Abubakar ya sake buga ƙofa yana kiran sunanta, Peace Jin an ƙara buga ƙofa da ƙarfi ta sake zabura tayi toilet da gudu ta kulle, Alhaji Abubakar kuwa jin Peace shiru ya koma ƙofan Blessing, buhu ɗaya ta buɗe domin tun bugun farko da ya yi ma ɗakin Peace ta farka da farko ta tsorata, amman da taji Muryar Alhaji sai sanya after dress a saman kayan baccin da ke jikinta, tana shirin buɗe ƙofa kenan taji ya kira sunanta, Muzaffar da Anas kuwa tun kiran su da ya yi na farko suka fito su ji ko lafiya wannan kira haka da tsakan dare ga ruwan sama anayi.
Alhaji Abubakar Muzaffar ya yi ma magana ya tayar da Baba Mai gadi ya buɗe get Hajiya ba lafiya, Anas kuma ya tayar da mota, kafin ya gama bayani Malam Zailani ya fito da sauri domin yaji kiran da Alhaji yake ma kowa cikin tsakiyar dare, bayan ya yi musu bayani ya ce Blessing ta kira Peace su kamo Hajiya babu lafiya, ɗakin Peace ta nufa tana zuwa ta kira sunan Peace ya Kai sau biyar amman shiru, har ta juya zata wuce sai taji karan ƙofa, Peace ne riƙe da mofinstick a hannu tana zare ido, Blessing batasan lokacin da dariya ya kubuce mata ba, bata tsaya tambayanta me zata yi da abun da ke hannunta ba ta faɗa mata saƙon Alhaji, da sauri ta fito yana bin bayan Blessing suka shiga cikin falon.
Ganin Alhaji Abubakar ya haura sama sai suka tsaya jiran sa domin doka ne babu wanda yasan kalan ɗakin Hajiya Maryam, baya yarda kowa ya shiga masa turakar matarsa, minti biyar ya ɗauka sai ya fito da ita da sauri suka ƙarsa domin tallafa mata, suna fitowa harabar gidan, Amsa ya riga ya tayar da mota suka shiga sai asibiti.
Ko minti talatin ba'a ɗauka ba Mero ta fara naƙida itama, Muzaffar ne a gidan da Peace, saboda Blessing ta raka Hajiya Maryam, wani mota suka ɗauka suka nufi asibiti su ma ganin Mero har ta fita hayyacinta.
DAAMA SPECIALIST HOSPITAL JIMETA.
Da sauri Alhaji Abubakar ya fito yana ƙwala kira "Nurse!!! Nurse!!! " Cikin hanzari ma'aikata suka fito da gado aka ɗora Hajiya Maryam, sosai ta fita hayyacinta banda salati babu abun da take yi,