Share this page
6 / 6
ya yi a zuciyarsa ya cigaba da tafiya har ya kai tsakiyar falo sai ya tsinkayi Muryar Aunty Halima da Aunty Zulaihat ashe suba kitchen dukkansu. " Haris baza ka tsaya ka ci abinci ba an kusa saukewa". Da sauri Haris ya ce " Aunty zan dawo anjima". Da gudu ya buɗe ƙofa ya fita. Alhaji Suleiman Yana barin falo ya wuce ɗakinsa, cikin fushi ya ɗaga waya ya danna kira, ringin ɗaya aka ɗauka, bai jira wanda ya ɗauki wayar ya yi magana ba ya fara masifa " Wannan ƙaramin aikin ya gagareku, wawaye kawai, bana buƙatar sake ganin fuskokinku muddin baku kawo min Hamid ba, fatan ka fahimta". Yana gama magana ya katse kiran. 🅿️ 17-18 Haris Bayan Haris ya fita daga gidansu Zarah, kai tsaye gida ya wuce, yana zuwa ya yi horn mai gadi ya buɗe mai get, cikin farin ciki ya gaisa da masu aikin gidan ya wuce ɓangaranshi, kaya ya sauya sannan sake fitowa sai murmushi yake yi. Baba Mai gadi ya kasa haƙuri ya ce " ɗana yaw wannan murshi haka, Kodai Fatima ta dawo ne?." Haris ya faɗaɗa murmushi akan fuskarsa ya ce " uh hmmm Baba tabbas Zarah ne ta dawo, yanzu haka tana gida can zan koma." Baba Mai gadi " Masha Allah, Allah ya ƙara kiyaye gaba, kai wannan yarinya tana ganin ƙaddara daban daban, ta rasa mahaifinta da mahaifiyarta yanzu kuma tana fuskantar ƙalubalen rayuwa." Haris " Baba Mai gadi me kake nufi da Zarah ta rasa iyayenta su kuma Alhaji Suleiman da Hajiya Binta fa?." Ya ƙarasa tambaya cike da mamakin jin wannan magana da ga bakin mai gadin gidansu, har yaushe ma yasan dangin Zarah da zai faɗi wannan magana. Baba Mai gadi jin sakin bakin da ya yi yasa ya sauya zance " yaro na kenan wannan rayuwar ƴar ƙarama ne, zaka fahimci duk abun da nace wata rana, ka tafi kawai, wata rana zan baka labari idan zuwa lokacin na kasance a raye." Haris zai sake magana kenan sai ƙarar horn ɗin mota ya katse su, da sauri Baba Mai gadi ya bar gurin ya nufi get, leƙawa ya fara yi sai ya ga motar gida ne ya yi saurin buɗe get. Aunty Safiya, Aunty Zulaihat da Aunty Halima ne suka dawo gida, parking ɗin mota suka yi sannan kowacce ta fito, ganin Haris a tsaye sai Aunty Zulaihat ta ce " Ango ya sha wahala, domin kai baka sha mai ba tukunna, sai ina kuma kasha kwalliya haka." Aunty Halima ta yi saurin cewa " Yanzu har sai kin tambayi inda Ango zai je, ya wuce gurin Amaryarsa, kinga da ga yau mun hutu da wannan zaman makokin da yake mana." Aunty Zulaihat ta ce " my brother ƙyalesu ka tafi abun ka, kada ka biye musu basa da aikin yi ne, yanzu zan basu aiki idan mun shiga gida, me kake so a dafa maka kafin ka dawo?." Haris murmushin yaƙe kawai ya yi ya ce " Shinkafa da miya ya wadata, ni yanzu zan tafi sai na dawo." Cike da farin cikin ganin ƙaninsu ya dawo hayyacinsa suka yi masa sallama ya shiga mota, har zai fita sai ya tsaya ya ce " Baba Mai gadi idan mun dawo zamu tattauna akan maganar da muka fara ɗazun." Sai ya ja mota ya bar gidan. Yana isowa gidan Alhaji Suleiman kai tsaye falo ya nufa da sallama a bakin shi, amman babu kowa, ya haura inda ɗakin Zarah yake. Zarah Bayan Haris ya fita zarah ta shirya tsaf ciki dogon riga abaya baƙi ta ɗauki hijab ta sanya ta taga gabatar da sallah la'asar, bayan ta idar kenan tana lazimi sai wayanta ya fara ƙara bata ɗauka ba har ta kammala. Tana tsaye a cikin ɗakin, zuciyarta cike da ruɗani, ta zauna bakin gado ta haɗe gwiwowinta tana kallon ƙasa, Kamar ana zare mata wani tsoka a cikin zuciyarta haka take ji, yanda Haris ke nuna mata tsantsar ƙauna yana ƙara ɗaga mata hankali, hawaye suka cika mata ido Amman bata basu damar zubowa ba. A hankali ta furta "Ya Allah me zan yi...? Haris... idan ka san gaskiyar nan ya zaka ji?." Dafe kirjinta tayi saboda wani irin zafi da take ji a zuciya. Tunanin mahaifin Haris da ta gani yana raye da kunnenta kuma taji wace ce ita, maganganunsa suna yawo a kanta. "Kada ki bari Alhaji Suleiman ya gane komai akan ahalinki." Nan take hawaye suka wanke mata fuska. "Zan yi haƙuri, saboda Haris" ta faɗa a hankali. Daidai lokacin wayarta ta yi ƙara, cikin firgici ta ɗauka da sauri ta dubi lambar, numfashinta ya ɗan sauya, "Hamid" da sauri ta ɗaga. Zarah "Hello." Hamid "Kin isa lafiya?." Zarah ta share hawaye "Eh..." Hamid ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce "Ki yi haƙuri, na san akwai ciwo amma kiyi haƙuri." Zarah ta rufe ido "Yanzu me zamu yi?" Hamid ya sauke numfashi "Abba ya ce muyi taka tsantsan akan wannan aiki, saboda Alhaji Suleiman yana da matuƙar wayo, mun fara bibiyar wasu mutane da suke aiki da shi, muna zargin akwai wasu sirrika da ya kamata mu ƙara sani. Zarah ta yi shiru, sai kuma ta tuna abu ɗaya, da sauri ta miƙe tsaye "Hamid ya labarin ɗan uwana!" Muryarta ta soma rawa. Hamid ya yi shiru tsawon wasu dakiku. Zuciyar Zarah ta fara bugawa "Hamid ka yi magana mana. Can cikin sanyin murya ya ce "Abbanmu ya ce akwai yiwuwar yana raye." Kalaman suka tsaya a kunnen Zarah, "Me...?" Hamid "Mun samu wata alama, amma har yanzu ba mu da tabbas." Wayar ya kusan zamewa daga hannun Zarah, wani sabon hawaye ya fara gangaro mata, a hankali ta ce "Ɗan uwanta, zai iya kasancewa yana raye?." Tun kafin ta ƙarasa magana ta ji an turo ƙofa, da sauri ta juya. Haris ne, riƙe da tire mai cike da abinci a hannunsa, domin har ya kamo hanyar ɗakinta sai Mommy taji motsinsa, daman ta haɗa mai Zarah abinci kenan, sai kawai ta bashi ya wuce mata da shi, ita kuma sai ya juya, tsayawa ya yi yana kallonta, sai ya lura da hawayen fuskarta, sai fuskarsa ta sauya a hankali ya ƙaraso gabanta ya tsaya ya ce. "Qalbey..." Zarah cikin firgici ta kashe wayar. Haris ya tsaya yana kallonta, "Wa kike magana da shi?" Nan take gabanta ya faɗi, bata da tabbacin Haris ya ji muryar Hamid Kodai, sai ya haɗiye miyau ƙyar. Haris ya sake matsowa kusa, a hankali ya ce "Zarah, da wa kike waya?" Hannunta ya soma rawa, zuciyarta kuwa bugawa take yi da ƙarfi, Haris ya tsaya gabanta idanunsa ƙur a kanta yana jiran amsa. "Ni... ni..." Sai ta kasa ƙarasa maganar. Haris ya ajiye tiren hannunsa a hankali a kan tebur, ya matso kusa da ita sosai, fuskarshi cike take da damuwa. "Qalbey..." ya kira ta a hankali "Me yake faruwa ne? Tun da kika dawo kin sauya sosai." Zarah ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta rasa me zata ce, shin ta gaya masa gaskiya? A'a ta tuna alƙawarin da ta yi, "Kada ki bari ya san komai..." Nan take ta goge hawayenta sai ya ce "Ba komai..." Haris ya ɗaga gira, "Ba komai?" Ta gyada kai. "Mutanen da suka sace ni ne..." Da sauri ya dago kai, "Me suka yi?" Zarah ta runtse ido, "Na tuna abubuwan da suka faru ne shi yasa..." Shiru ya biyo baya. Haris ya sauke numfashi sannan ya janyo ta jikinsa ya rungumeta, "to shikenan..." Ya shafa bayanta a hankali. "Ki manta komai, kina gida yanzu." Wannan kalmar ce ta sake karya zuciyar Zarah. "Kina gida..." Wane gida? Gidan mutumin da ya kashe iyayenta? Wani sabon kuka ya ƙwace mata. Haris ya yi saurin riƙe fuskarta. "Wayyo Qalbey..." Sai ya share mata hawayen ya ce, "Kada ki sake kuka, wallahi zuciyata ciwo take idan kina kuka." Zarah ta kasa jurewa, ta rungume shi da ƙarfi ta fashe da kuka, a zuciyarta kuwa tana cewa: "Ka yafe min Haris..." "Ka yafe min." Alhaji Suleiman Alhaji Suleiman ne zaune a falo yana ta faman duba wayarsa, fuskarshi a haɗe tamkar wanda aka yiwa mutuwa. Can wayar ta yi ƙara, da sauri ya ɗaga "Hello." Muryar ɗayan ɓangaren ya ce "Ranka ya daɗe mun gano inda Hamid yake." Nan take Alhaji Suleiman ya miƙe tsaye. "Ina?!" "Yana wani tsohon gida ne kusa da..." Kafin ya ƙarasa ƙarar bindiga ta tashi daga ɓangaren wanda Alhaji Suleiman ke wayar da shi. TAAA!!! Sai ihun mutane kawai yake ji, sai wayar ta yanke. Alhaji Suleiman ya zaro ido. "Hello?! Hello?!" Amman shiru, gaba ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, a hankali ya furta "Hamid..." Sai ya matse wayar da ƙarfi. Idan Hamid ya tsira, komai zai lalace. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6