har aka iso maternity room hannun ta riƙe da na mijinta, ana shiga da ita ya tsaya yana kallon ta a glass ɗin ƙofa, nan take hawaye ya zubo mai a ido, addu'a yake yi Allah ya sauke ta lafiya, yana juyowa sai ya kusa karo da Mallam Zailani , ganin shi a wani yanayi sai ya tambaye shi ko lafiya, nan yake sanar mishi Mero aka kawo yanzu, wani nannuyan ajiyan zuciya ya sauke tare da musu fatan sauka lafiya.
Alhaji Abubakar da Malam Zailani suka nufi hanyar masallacin da ke cikin asibiti.
Sosai likitoci ke ƙoƙarin ganin sun samu Hajiya Maryam ta haihu da kanta amman Abu ya ƙi yiwuwa, Dr Balkisu ne ta fito domin duba Alhaji Abubakar amman bata ga kowa ba, komawa ta sake yi ta bayar da umurnin a shirya operation za'a yi mata idan ba haka ba zasu iya rasa twins ɗin da ita kanta Hajiya Maryam ɗin.
Mero kuwa ko awa ɗaya ba'a ɗauka ba ta santalo twins ɗinta Maza, jarirai kamar ka sace ka gudu.
Alhaji Abubakar da Malam Zailani kuwa suna cikin masallaci zaune suna azkar da addu'a Allah ya sa matansu sun buɗe ido lafiya, sun ɗauki lokaci sosai sannan suka fito, tafiya suke yi kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa, suna isowa maternity likitoci kowa da jarirai a hannu guda biyu.
Mallam Zailani ya kalli Alhaji Abubakar, cikin jin daɗi suka nufi likitocin suna murmushi, Kallan yaran suke yi gwanin burgewa, Alhaji Abubakar ya tambayi ko ya jikin iyayen yaran.
Kafin a bashi amsa sai ga Dr Balkisu da Dr Rabi'atu sun fito, Bayan sun musu congratulations sai suka kalli juna , sai da Dr Balkisu ta sauke ajiyan zuciya sai ta ce " I'm sorry to say, mun rasa su duka sai dai kuyi haƙuri." 😭😭😭
🅿️ 13-14
Wani irin shiru mai nauyi ya sauka a cikin asibitin.
Maganar da Dr Balkisu ta faɗa kamar an harbeshi da bindiga haka Alhaji Abubakar ya ji.
“Mun rasa su duka…” Alhaji Abubakar ya faɗa, idanunsa suka cika da hawaye amma ya kasa zubarwa.
“Me kike nufi?” ya tambaya cikin murya mai amo.
Dr Rabi’atu ta sunkuyar da kai, “Mun yi iya ƙoƙarinmu amma Allah ya yi ikonsa.”
Nan take ƙafafunsa suka kasa ɗaukar sa, Malam Zailani ne ya riƙe shi kafin ya faɗi ya ce “Ka yi haƙuri Alhaji jarabawa ce daga Allah.”
"Amma wace zuciya za ta ɗauki wannan Malam Zailani, ga jarirai da suka zo duniya amma zasu tashi ba tare uwayensu ba."
Sosai mutuwar ya gigita mutanin asibiti gaba ɗaya, yaye biyu kuma ga kowacce ta haifi twins, Allah ka jiƙan iyayenmu.
Blessing da Peace suna gefen ƙofa suna kuka mai sauti.
Muzaffar ya jingina da bango yana share hawaye.
Anas kuwa ya fice waje, ya kasa tsayawa kallon wannan yanayi, a rayuwarsa bai taɓa ganin rana irin wannan ba.
Likitoci suka miƙa jariran, twins ɗin Mero maza guda biyu, sai twins ɗin Hajiya Maryam Aryan da Zarah
Jarirai huɗu kenan.
Alhaji Abubakar ya karɓi jariran hannunsa na rawa, ya kalle su, nan take hawaye suka wanke mai fuska.
“Maryam… kin bar min wannan babbar amana anya nan zan iya kuwa?”.
Malam Zailani shima ya karɓi jariran Mero ya riƙe a hannu.
Bayan an kammala komai aka sanya gawan Hajiya Maryam da Mero a ambulance aka kama hanyar gida, kafin su iso labari ya zagaye ko ina a Jigawa, kasancewar Alhaji Abubakar babban mutum ne, sosai gida ya cika da jama'a ana jiran dawowansu.
⚰️ Shirye-shiryen Jana’iza
Cikin gaggawa aka fara shirye-shiryen jana’iza, gari gaba ɗaya ya shiga jimami, bayan an kammala wanka aka kira Alhaji Abubakar da Malam Zailani domin sallama da yali, sosai suka yi kuka tamkar yara ƙanana, da ƙyar aka samu suka yi shiru sannan aka gabatar da sallah aka kai su gidansu na gaskiya.
Kullu nafsin za'ikatil maut, dukkan mai rai mamaci ne.
Sosai mutane ke zuwa suna yi wa iyalan ta’aziyya.
Bayan kwana bakwai da rasuwar Hajiya Maryam da Mero, gidan ya canza gaba ɗaya, gidan da ya cika da dariya da annashuwa yanzu ya koma gidan shiru da kewar waɗanda suka tafi.
Jarirai huɗu suna cikin ɗaki ɗaya, saboda Alhaji Abubakar ya ɗauki nauyin kula da su.
Aryan
Zarah
Twins ɗin Mero wanɗanda suka ci suna.
Haris
Hamid
Kowannensu na kuka lokaci zuwa lokaci, Blessing da Peace ne suka ɗauki nauyin kula da su dare da rana, canza musu kaya, kwantar da su idan sunyi bacci da lallashinsu idan suna kuka, amma duk da wannan kulawa babu wanda zai maye gurbin uwa.
Alhaji Abubakar ya zama wani irin mutum baya magana da kowa kuma baya zuwa gurin aiki, sai dai ya shigo ɗakin yaran, ya tsaya yana kallonsu.
“Ku ne abin da Maryam ta bari a duniya…”
A gefe guda…
Malam Zailani yana yin aikinsa kamar yadda aka saba, yana taimakawa wajen kula da yaran, amma akwai abu guda ɗaya, Ba ya nuna damuwa kamar sauran mutane, yana kallon yaran amma idanunsa suna ɗauke da wani abu da yake ɓoyewa.
Wata ranar Laraba, bayan kowa ya kwanta, Malam Zailani ya shigo ɗakin yaran a hankali ya tsaya a gaban gadon da aka kwantar da jariran, ya kalli ɗaya daga cikinsu (ɗaya daga twins ɗin Hajiya maryam).
Sai ya ɗauke ta a hankali, ya duba fuskarta sosai,sai ya furta a hankali "Kece mabuɗin komai.”
Numfashinsa ya sauya, sai ya mayar da jaririn ya juya zai fita, amma kafin ya fita ya juyo ya kalli Zarah, ya ɗan tsaya, idanunsa suka sauya launi, sai ya fita da sauri, saboda ya ji motsi.
😱 Abun da babu wanda ya Sani, Malam Zailani ba kawai ɗan aiki ba ne, ba mijin Mero ba ne, kuma ba ma sunansa na gaskiya kenan ba.
Washegari…
Blessing ta lura da wani abu, ɗaya daga cikin jariran yana da wani ƙaramin alamar wata da tauraro a kafaɗarsa, tayi mamaki sosai sai ta tambayi Peace.
“Peace… kin taɓa ganin wannan alamar kuwa?”
Peace ta girgiza kai.
“Ban taɓa gani ba.”
Amma daga ƙofa, Malam Zailani yana kallonsu duk abun da suke yi.
Kwanaki suna ja, makonni suna wucewa…
Gidan Alhaji Abubakar ya saba da sabon yanayin rayuwa, amma raɗaɗin rashi bai gushe ba.
Kullum da safe Blessing da Peace sukan tashi tun asuba, su shirya madarar yaran
suyi musu wanka da kwalliya gwanin burgewa, kasancewar komai nasu iri ɗaya ne.
kowannensu yana ɗauke da labari daban a jininsa ambancin da ba'a fahimta ba a hankali aka fara lura.
Aryan yana da nutsuwa sosai, baya yawan kuka
Zarah tana da wayau sosai, Haris da Hamid kuwa suna da kuzari sosai.
Amma akwai ɗaya daga cikin jariran da ke ɗauke da alamar wata da tauraro, wannan ne Malam Zailani yake yawan kallo.
Malam Zailani
Wata daren juma’a…
iska na kaɗawa, ni'ima mai daɗi ke sauka a garin Jigawa, gidan Alhaji Abubakar kuwa kowa ya kwanta domin huta gajiyan aiki, Malam Zailani ya fito daga ɗakinsa a hankali, ya duba kowa yana barci sai ya nufi ɗakin yaran, ya buɗe ƙofa a hankali, ya shiga, yaran suna bacci, sai ya ɗauki jaririn da ke da alamar wata da tauraro, ya lulluɓe shi da wani baƙin zani ya fita da shi zuwa bayan gida.
A can akwai wani ƙaramin hanya mai duhu sosai kamar an daɗe ana amfani da shi a ɓoye, zama ya yi yana kallon yaran sai ya ce, “Lokaci bai yi ba amma dole ne ki rayu cikin jindaɗi.”
Ya ciro wani ƙaramin abu kamar laya ya riƙe shi yana karanta wasu kalmomi cikin ƙasa da murya.
A wannan daren ne Alhaji Abubakar ya kasa bacci ya tashi domin ya duba yaran kamar yadda ya saba, yana isa ƙofar ɗakin ya lura ƙofar a ɗan buɗe take, ya tsaya.
“Blessing?” ya kira a hankali.
Babu amsa.
Zuciyarsa ta fara bugawa, tura ƙofar ya yi a hankali, ya tarar gadon ɗaya babu yaro, numfashinsa ya tsaya ya ce
“Subhanallah…”
Nan take ya juya da sauri ya nufi waje, yana fita harabar gida ya hango inuwa daga bayan gida, ya fara tafiya a hankali zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, yana ƙara matsowa sai ya fara jin muryar Malam Zailani, ba irin muryar da ya saba ji ba ce, muryar ta canza sosai, mai cike da firgitarwa.
Alhaji Abubakar ya leƙa daga gefe sai ya ga Malam Zailani riƙe da yaro, sosai ya tsorata har sai da danunsa suka zazzaro waje.
“Zailani?!” Alhaji Abubakar ya kira shi.
Zailani ya juya da sauri, suka haɗa ido da Alhaji Abubakar, lokaci guda fuskar Zailani ta canza.
Cikin sauri Zailani ya ɓoye abun da ke hannunsa, ya dawo da Muryar sa irin ta yau da kullum.
“Alhaji… na ga tana kuka ne, shi yasa na fito da ta domin ta sha iska.”
Alhaji Abubakar bai yi magana nan take ba, idanunsa na kan Malam Zailani, zciyarsa tana cewa,
“Akwai wani abu da wannan mutum ke ɓoyewa.”
Ya karɓi yaran daga hannunsa, ya kalli fuskarsa, sai ya sake kallon Zailani, "daga yau babu wanda zai sake ɗaukar yaran nan da dare ba tare da izini na ba.”
Zailani ya sunkuyar da kai.
“in sha Allah , Alhaji.”
Amma a zuciyarsa yasan Alhaji ya kusa gano sirrinsa.
Da Alhaji ya tafi, Zailani ya ɗaga kai a hankali, fuskarsa ta sake canzawa, ya furta cikin sanyin murya
“Ba za ka gane komai ba… har sai lokaci ya yi.”
Washegari da safe…
Alhaji Abubakar ya kira Blessing da Peace.
“Daga yau… ku riƙa duba yaran nan a kowane lokaci.”
Sun yi mamaki sosai.
“Alhaji… me ya faru ne?”
Ya kalli ƙofar ɗakin Zailani kafin ya ce, “Ina son tabbatar da cewa babu abun da ke faruwa a bayana, ku ƙara kulawa sosai zaku iya tafiya.”
Alhaji bai tsaya nan ba, ya fara lura da motsin Zailani, har ƙauyensu ya je amman kowa ya ce bai san waye Zailani ba, hasali ma ko mai kama da shi babu a ƙauyen .
Kasancewar ya bashi aiki a Company yasa ya tambayi wasu ma’aikata game da shi, nan ya gano abu guda mai ban mamaki, babu cikakken tarihin Zailani a form ɗinsa haka a ƙauyensu, ba'a san daga ina ya fito ba, ba'a san danginsa ba, sosai wannan lamari ya girgiza Alhaji Abubakar, ya tattara ya koma gida.
A GEFE GUDA,COMPANY.
Company ɗin Alhaji Abubakar na tafiya dai dai PA ne ke kula da komai, riba na shigowa sosai
sabbin kwangiloli na ƙaruwa, komai na tafiya lafiya a zahiri.
A daren ranar, Zailani ya amsa wani kira, muryar na waya ya ce, "lokaci ya kusa, ka tabbata yarinyar tana nan lafiya?”.
Zailani ya kalli ɗakin yaran.
Ya amsa cikin ƙasa da murya "tana nan amma akwai wanda ya fara zargina da bin bayana.”
Alhaji Abubakar tun bayan daren da ya ga Malam Zailani da yaro bacci ya ƙaurace masa, kullum zuciyarsa na faɗa masa, "wannan mutum ba yadda kake tunani ba ne…”
A safiyar wata ranar Lahadi, ya zauna a falonsa nisa a tunani, sai ya kira Muzaffar a waya, a hankali ya ce kazo sashe na, Muzaffar ya zauna, Alhaji ya kalle shi da idanu masu cike da shakku da damuwa.
“Ina so ka riƙa lura da Zailani amma a ɓoye.”
Muzaffar ya ɗan firgita, "Alhaji akwai matsala ne?”.
Sai ya ce “Ban sani ba tukunna amma zan gano.
Bayan kwanaki takwas Alhaji Abubakar bai ji komai daga Muzaffar ba sai ya yanke shawara zai bi Zailani da kansa, ba zai sake aika kowa ba.
Kamar koda yaushe, dare na tsalawa Alhaji Abubakar ya fito ya ɓoye a inda ba za a gan shi ba, yana jira…
Bayan minti talatin da fitawar shi sai ga Zailani ya fito kamar kullum, ya nufi sashen Alhaji Abubakar, a tunin shi ya yi bacci, kai tsaye ya wuce ɗakin yaran, ya ɗauki mai tambarin nan ya fito, bayan ƴan mintoci Alhaji Abubakar ya bi shi a baya, Zailani ya shiga ɓoyayyen ɗakin da ke gidan.
Alhaji Abubakar yana biye da shi har ciki, kasancewar ɗakin tamkar kogo yake yasa bai lura ana bin bayan shi ba.
Alhaji Abubakar yana isowa ya tsaya daga nisa yana leƙawa.
ya ga Zailani riƙe da yaro, yana kallonsa kamar wani abu mai muhimmanci, ya tattara hankalinsa akan wannan yaro.
Malam Zailani ya ce, "lokaci ya kusa za mu dawo da abin da aka ƙwace mana.”
Alhaji Abubakar ya ɗaga ƙafa zai matsa gaba ƙafarsa ta taka wani abu, kafin ya juya ya bar gurin, Zailani ya juya da sauri, suka haɗa ido, sai ya fito fili yana kallon sa cike da mamaki ya ce "Waye kai?."
Zailani ya kalle shi ba tare da tsoro ko firgici ba, sai wani shu'umin murmushi da ya yi.
“Lokaci ya yi da zaka je inda matarka da Mero suka je."
A hankali ya sauke jaririyar a kan tabarma, sai ya miƙe tsaye ya kalli Alhaji Abubakar ya ce,
“Ni ba Zailani ba ne kamar yadda kake tunani suna na Alhaji Suleiman." Sai ya yi murmushi ya juya baya nan take ya cire fuskar da ya sanya na bogi, asalin fuskar Alhaji Suleiman ya bayyana fuskarsa na bahaushe ne.
Numfashin Alhaji ya ɗauke na wasu daƙiƙu.
Malam Zailani. “Ni na ɓatar da matarka da kuma Mero, a tunaninka Mero Matana ne ko, inaaa matar ɗan uwana ne Alhaji Ahmed, shima na tura shi inda zan tura ka yanzu.”
"Wannan kuma ya nuna Zarah a guri na zata tashi, zan reneta tamkar ƴar da na haifa, idan lokacin buƙatar ta ya yi zan turo ta inda kake."
Kafin Alhaji Abubakar ya yi wani yunƙuri, Malam Zailani ya jefa mai wani laya nan take ya ɓace.
Washegari da safe.......
Peace da Blessing sun zo suka shirya yaran, shiru basu ga Alhaji ya fito ba, a tuninsu yana bacci, suka cigaba da harkokinsu, abinci rana ya kammala amman babu Alhaji, akayi na dare nan ma shiru, Abu kamar wasa, Blessing ta fito waje ta tambayi Muzaffar da Anas ko Alhaji ya je office ne, suka ce bai fito, sun kira wayoyinshi amman baya tafiya, sosai hankalinsu ya tashi, a ranar babu wanda ya yi bacci sai ɓarawo.
Kamar wasa yaw sati kenan amma babu labarin Alhaji kuma ba na Zarah ga kuma Malam Zailani ake domin shima ranar ya ɓace da daddare bayan ya ɗauke zara, sunyi kuka har sun bar ma Allah ikonsa.
wannan ne labarin Zarah da yanda jininsu ya haɗu da Haris har suka haɗu ba tare da Alhaji Suleiman ya sani ba sai ranar ɗaurin Auren da ya haɗa na Zarah.
🅿️ 15-16
CIGABAN LABARI..........
Zarah
A firgice zarah ta ɗago kai tana kallon mahaifin Haris, fuskarta ya yi ja saboda kuka, zancen zuci ya hanata furta koda kalma ɗaya ne, kenan wanda ta rayu da shi shine maƙiyinta, ya kashe mata mahaifi ya kashe mata mahaifiya, ya rabata da duk wani jin daɗi na duniya, kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace mata, Hamid ya yi yunƙurin dakatar da ita amman mahaifinshi ya ɗaga mai hannu alaman ya ƙyaleta, kukanne kaɗai zai sa zuciyarta ya rage raɗaɗin da take ji, ta ɗauki tsawan lokaci tana kuka har idanunta sun kumbura sosai.
Zarah "yanzu wanann ne tarihi na, Alhaji Suleiman ka cuce ni ka cuci rayuwata, wallahi bazan taɓa yafe makaba, Allah sarki Haris idan yaji wannan labarin ya zai yi kenan, Abba ku maidani gida dan Allah kada ya cutar da Haris, kenan ya labarin ɗan uwana yake, dole ina buƙatar wannan amsa shima, ya kashe shi ne kodai?." Zarah ke magana tamkar wacce ta fara hauka.
Mahaifin Haris ya ce " Zarah, ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru in sha Allah, yanzu ya kamata mu mayar da ke ba tare da kowa ya san hannun mu kike ba, domin idan har Alhaji Suleiman ya gane akwai matsala zai iya kashe mu duka domin besan ina raye ba, Hamid la ɗauki Zarah ka mayar da ita gida domin sai mun samu ƙwararan hujjoji akan kashe iyayenta da ya yi sannan zamu iya ƙarar shi, kada ka bar makama koda guda ɗaya ne Please, Zarah ki kwantar da hankali idan kinje, kice wasu ne suka sace ki kuma fuskarsu a rufe yake babu wanda za ki gane, kada ki bashi damar fahimtar komai, ki kula sosai, zan neme ki in sha Allah, kada kice za ki faɗa na Haris ina raye ki riƙe wannan sirri ne tsakaninmu."
Zarah kuka kawai take yi tamkar ranta zai fita, zata iya cigaba da zama da makashin ahalinta kuwa?wanda ya rusa mata rayuwa, zata iya ɓoye ma Haris mahaifinsa yana raye?.
Cikin ƙaraji ta ce " hakan bazai yiwu ba, gidan wannan azzalumin zan koma, Abba kada ka mayar da ni dan Allah, zan iya kashe shi, bazan jureba!!!!!!!."
Cikin tausasa murya ya ce"ƴata kiyi haƙuri dole mu kafa mai tarkon da bazai iya fita ba idan ya faɗa, dole ki haɗiye duk wani baƙin ciki kiyi abun da zai sa ya faɗa takonmu, Hamid ku tafi yanzu, ka kula sosai."
Babu gardama Zarah ta bi bayan Hamid, suna fita mota suka kama hanyar unguwar GRA da ke birnin Kano, bai ƙarasa shigowa unguwar ba ya yi parking ɗin mota a gefen hanya, tattaunawa suka yi sosai sannan ya buɗe ƙofar mota ya yi kamar ya jefo ta, zarah kuwa bayan ya ajiyeta gefen unguwarsu, sai ta cigaba da tafiya, har ta kusa zuwa gida sai ta haɗu da Haris a mota zai sha kwana kenan ya hangota, ya yi tunanin gizo ne kawai, zai juya mota ya cigaba da tafiya sai ya ji tana ƙwala mai kira, Qalbeey, Qalbeey.!!!!!!!!!!
Haris da ya ji kamar a mafarki ya yi sauri ya taka burki, ko jiran motar ya gama tsayawa bai yi ba ya fito da sauri, sai da ya tsaya yana kallon ta kamar ya ga sabuwar halitta, jin har lokacin bata daina ƙwala mai kira ba yasa ya tabbatar bafa gizo bane itace, ai da gudu ya ƙarasa gurinta yana zubar da hawayen farin ciki, itama Zarah hawaye take yi, amman ita hawayen tausaya ma kanta da Haris take yi.
Haris na zuwa ya rungumeta da sauri kamar za'a ƙwaceta, Zarah kuwa wani marayan kuka ta saki, kuka take yi tun daga ƙasan zuciyarta, Haris ganin kukan bana ƙarewa bane yasa ya ɗago da fuskarta suna kallon juna, kai ya gyaɗa mata alaman kukan ya isa haka, da ƙyar ta daina kuka sai hawaye da ke bin kuncinta.
Sai a lokacin ya tuna yaw 1week da ɓacewarta ya fara duba jikinta ko akwai abun da ya sameta, amman ya ga babu komai, hamdala ya yi sannan ya ɗauketa kamar ƴar baby ya sanyata a mota ya tayar sai gida, kasancewar kaɗan ya rage su ƙarasa, sai ya koma tafiya a hankali har suka tsaya ƙofar gidan Alhaji Suleiman, Zarah ganin inda aka yi parking sai da zuciyar ya buga, Haris da ke gefenta ganin irin kallon da take ma gidan ya bashi mamaki, amman ya yi tunanin kawai dai tana a tsorace ne ko kuma ta gaji ne, horn ya yi mai gadi ya buɗe mai get ya shiga ciki.
Parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya kuma zagayo inda Zarah take tana ƙare ma gidan kallo cikin tsana da ƙyama, batasan lokacin da Haris ya buɗe kofar ba sai kawai taji anyi sama da ita, bata tsorata ba kasancewar tasan wanda zai yi hakan.
Haris kai tsaye falo ya nufa da Zarah ko kunya babu, da sallama ya shiga, Alhaji Suleiman da sauran yaran gida da ƴan uwa kowa ya hallara a gidan.
Haɗa baki sukayi gurin amsa sallama, amman ganin Haris ya ɗauko mutum a hannu sai suka tsaya kallon shi, kowa jira yakeyi ya ga waye, Zarah kuwa ɓoye fuskarta ta yi saboda kunya domin harda ƴan uwan Haris a ciki, sai da ya tabbatar ya kawo tsakiyar falo sannan ya sauketa, Zarah na juyowa ta haɗa ido da Aunty Halima, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, Haris kuwa sai murmushi yake yi.
Aunty Halima ta riga kowa miƙewa da sauri ta nufi Zarah sai sauran suka mara mata baya, nan take suka zagayeta suna mata sannu, Hajiya Binta kuwa rungume Zarah ta yi a jikinta tana hawaye, zarah da ƙiris take jira aikuwa sai ta fashe da kuka, sosai suka baiwa kowa tausayi, da ƙyar sukayi shiru, Aunty Zulaihat ta ja hannu Zarah zuwa gaban mahaifinta Alhaji Suleiman.
Alhaji Suleiman kuwa tun shigowarsu ya fahimci Zarah ne, yana tunanin ya akayi ta kuɓuta?. Bai gama tunanin zuci ba Aunty Zulaihat ta iso da Zarah gabansa.
Zarah kuwa tana isowa gabanshi ta ƙura mai ido, hawayen baƙin ciki kawai ke zuba a idonta, ji take kaman ta shaƙeshi ya mutu kowa ya huta, ganin irin kallon da Zarah take masa ya yi saurin tashi zai rungumeta, amman Zarah ta juya zata wuce, ba Alhaji Suleiman kawai ba kowa da ke falon sai da ya yi mamakin abun da ta yi, sai dai kowa ya yi tunin gajiya ne, babu wanda ya ce mata komai ta haye sama tana kuka.
Haris ganin zarah ta hau sama sai ya mara mata baya, Aunty Halima har zata dakatar da shi Aunty Safiya ta dakatar da ita, kowa ya koma ya zauna, Alhaji Suleiman kuwa mutuwar tsaye ya yi, ganin kowa yana kallonshi sai ya zauna ya ciro waya.
Alhaji Suleiman " Hello inspector Mahmud Zarah ta dawo gida yanzu, ku dakatar da binciken". Bai jira amsa ba ya kashe waya.
Haris yana zuwa ya tura ƙofa amman a kulle nan ya fara knocking amman shiru, har ya juya ya ji karan ƙofa, da sauri ya juya suka haɗa ido, sai tayi ƙasa da kai, Haris ya zo har ƙofa ya ɗauketa ya shiga ciki da ita ya kulle ƙofa,kai tsaye banɗaki ya zarce da ita, ya haɗa mata ruwan wanka ya zuba turaruka da ƙamshi kala kala, tana tsaye tana kallonsa har ya kammala, sai ya ɗago ya kalleta bai tsaya wani tunani ba ya ɗagata sama ya sanyata cikin bahon wanka, ko cire kaya batayi ba, Zarah kuwa jinta cikin ruwan ɗumi yasa ta ƙara lafewa a ƙirjinshi, domin ya zo sakata cikin ruwa ta janyo shi suka faɗa tare.
Kallan kallo aka fara, za ta tashi ta gudu kenan ya yi sauri ya janyota ta faɗo jikinsa, wani irin shock sukaji a tare, suka ƙura ma juna ido tsawon minti biyar.
Haris " yaw kam Allah ya kamaki tare zamuyi wanka ko Qalb, kinsan halin da na shiga lokacin da kika ɓace, hmmm koda yake daga baya zamuyi wannan maganar, yanzu dai wanka farko sai abinci, hutawa da kuma bacci".
Bata Ankara ba sai ji ta yi ya matseta a jikinsa sosai, ya fara cire mata kayan jikinta, Zarah kuwa gani ya kusa gama cire kayan yasa ya buɗe baki zata yi ihu ya yi sauri ya haɗe bakinsu guri ɗaya, Zarah jin bakinsu guri ɗaya sai da ta yi suman tsaye.
Haris kuwa kissing ɗinta ya keyi sosai yana zame kayan jikinta, sosai ya shagala har ya manta a banɗaki suke, sosai ya yi nisa, bayan ya kammala cire mata kaya sai ya ɗauketa sai cikin bahon wankan ya mayar da ita, ya cigaba da wasa da kowanne sassa na jikinta Zarah kuwa tun tana jin tsoro har saƙo ya fara kaiwa ƙwaƙwalwarta sai ta fara mayar da martani, hannunta ta sanya a cikin gashin kansa tana yamutsawa, Haris kuwa kamar ana zuga shi haka ya cigaba da wasa da ita, Zarah kuwa jin zai fara wuce gona da iri sai ta fara ƙoƙarin ƙwacewa amman Haris ya riƙe ta sosai ko motsi bata iyawa sosai, dai dai kunnen shi ta bakinta ta raɗa mai magana, sai lokacin ya buɗe ido ya kalleta, ita kuwa da sauri ta kulle ido, fita ya yi daga bahon ya sakar ma kanshi ruwa, ya tsarkake jikinsa ya ɗaura towel ya fita, Zarah sai da ta ga fita da sauri ta sanya sakata ta sauke nannuyan ajiyan zuciya, ta cigaba da wanka, ta ɗauki lokaci sosai kafin ta fito itama ɗaure da towel a ƙirji.
Ganinshi tayi yana zagaye ɗaki, bata ce mai komai ba nufi gurin kayanta, hijab ta ɗauko ta sanya, dai lokacin take tambayan shi ko lafiya, yake sanar da ita kayan shi ya jiƙe, waro ido Zarah ta yi, ta ga ba ɗaya ta manta, tunanin mafita suke yi, can sai Zarah ta tuna da kayan da ta siya zata bashi kyauta, da sauri ta ɗauko mai ya sanya.
Yana gama sanyawa ya mata kiss a goshi ya fita, kai tsaye falo ya nufa cikin sa'a babu kowa a falon hamdala