ƙarfi.”
Amma a ƙofar ɗakin asibitin wani mutum yana tsaye cikin duhu yana kallon ɗakin da aka kwantar da Haris.
Ya ɗaga waya.
“Bai mutu ba,” ya faɗa cikin ƙasa da murya. “Amma yanzu ya san su waye ya zai taɓo.”
Washe gari da asuba, asibiti ya yi shiru,Haris na kwance, ƙafarsa a ɗaure, Zarah na zaune kusa da shi, idonta duk ya kumbure saboda kuka da rashin barci.
“Wayata…” Haris ya faɗa a hankali.
Zarah ta miƙa masa sabuwar wayan da ƴan sanda suka kawo, amma ba ita ba ce wadda yake nema.
“Tsohuwar wayarka ta ɓace a gurin da abun ya faru,” haka jami’in ya faɗa."
Zuciyar Haris yayi wani irin bugawa.
A cikin wayar ne ya ɗauki hotunan asalin takardun filin, a ciki ne ya adana sautin magana da tsohon ma’aikacin rajista ya bashi, a ciki ne shaida mafi muhimmanci yake.
“Laptop ɗina fa?” ya tambaya da sauri.
Zarah ta sunkuyar da kai.
“Na koma gida ɗazu…” ta faɗa cikin rauni. “An karya ƙofa, an shiga ɗakinka.”
Numfashin Haris ya tsaya na ɗan lokaci.
“Sun ɗauke komai?”
“Eh.”
Shiru mai nauyi ya sauka a ɗakin na wasu lokaci .
Wannan ba gargaɗi ba ne kawai, wannan shiri ne na rufe gaskiyar gaba ɗaya, tabbas dole sai na ƙara jajircewa .
Da yamma, wani jami’in bincike ya zo asibiti.
“Muna zargin an bibiyi motsinka,” ya faɗa wa Haris.
“Duk wanda ke bayan wannan yana da iko.”
Haris ya lumshe ido,
“Ba za su dakatar da ni ba.”
Amma a karon farko, ya ji wani abu a cikin ransa ba tsoro ba ne, amma akwai alamun karaya.
Zarah ta riƙe hannunsa.
“Ka rasa shaidu, amma ba ka rasa gaskiya ba,” ta faɗa cikin natsuwa.
Ya kalleta yace.
“Ba tare da shaida ba, gaskiya labari ce kawai.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ta ce.
“Akwai abin da ban gaya maka ba."
Haris ya kalleta da mamaki.
“A ranar da na ba Faisal kuɗin, ban ba shi duka ba.”
Zuciyar sa ta buga da ƙarfi.
“Me kike nufi?”
“Na cire wani ɓangare na kuɗin na ajiye su a wani asusu na sirri, domin zuciyata ba ta yarda da abin da ake shirin yi ba.”
Haris ya miƙe kaɗan duk da raunin da ke ƙafarsa.
“Me ya sa baki faɗa min ba?”
“Saboda ban san zan iya amincewa da kowa ba a lokacin.”
“Har da ni?”
Hawaye suka cika mata ido.
“Na ji tsoron cewa za ka ga ni, kuma banasan ka kamani da laifi a ɓangare na.”
Shiru ya sake sauka.
Amma wannan karon, akwai haske kaɗan a ciki.
“Wannan asusun…” Haris ya ce cikin tunani, “za a iya gano inda aka tura sauran kuɗin.”
Zarah ta gyada kai.
“mu hanzarta kafin su gano cewa akwai ragowar kuɗi a cikin wani asusu.”
Amma a waje har yanzu wannnan mutumin yana sauraren komai.
Sai naga ya ɗaga waya, cikin wayan ake tambayan shi, “Har yanzu suna da wani abu.?”
“Eh,” ya amsa. “Suna da sauran hujja .”
Mutumin ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Idan haka ne, lokaci ya yi da za mu fito fili.”
Ga mai buƙatar wannan littafin tun daga farko ga number.
👇
09016853353, Whatsapp only
🅿️04
Yaw ya kama mako guda kenan da harin da aka yi ma Haris.
An sake komawa kotu.
Kowa ya yi tunanin shari’ar ta zo karshe saboda ɓacewar shaidu da hujjoji.
Amma ba su san cewa wani sabon abu na shirin fitowa ba.
Zarah da Haris sun shigo tare, duk da raunin da ke ƙafan Haris ya tsaya cikin karfin hali da ƙarfin zuciya.
Idanunsa sun nuna cewa wannan karon ba zai bar komai ya kuɓuce masa ba.
Alƙali yana shigowa, aka fara zaman kotu.
Lauyan gwamnati ya miƙe.
“Mai girma alƙali, muna da sabon shaida.”
Aka kira Zarah, ta tsaya a gaban kotu, hannunta na rawa amma zuciyarta cike da ƙuduri da ƙarfin hali.
“Na ɓoye wani ɓangare na kuɗin da aka fitar ranar hatsarin,” ta faɗa cikin natsuwa. “Na ajiye su a asusu na sirri.”
Kotu yayi shiru domin jin abinda alƙali zai ce.
“Wannan bayanin banki ne,” lauyan ya ce yana miƙa takardun hannunsa.
“Yana nuna cewa daga asusun Alhaji Sulaiman, an tura wani ɓangare na kuɗin zuwa wani kamfani.”
“Wani kamfani?” alƙali ya tambaya.
Lauyan ya ɗaga murya.
“Kamfanin Northern Star Holdings.”
A wannan lokacin ne aka ji wata murya daga bayan kotu.
“Wannan ba zai yiwu ba."
Kowa ya juya.
Wani sanannen ɗan kasuwa ne, Alhaji Kabiru Danladi, mai kamfanin da aka ambata fuskarsa ta canza launi.
Haris ya kalli takardun kamfanin, nan ne aka sayi filin da ake taƙaddama a kai bayan mutuwar mahaifinsa.
Zuciyarsa tana raya masa abubuwa da yawa, kuɗin diyya da ba su isa hannun iyalinsu ba, maguɗin takardun fili,
Harin da akayi masa, duk sun haɗu wuri guda.
Lauyan gwamnati ya ci gaba,
“Shaidar banki ta nuna cewa daga wannan kamfani an biya wasu mutane kuɗi kwanaki kaɗan kafin a kai wa Haris hari.”
Kotu ta cika da hayaniya.
Alhaji Kabiru ya yi ƙoƙarin magana, amma alƙali ya katse shi.
“Za a kama ka har sai an kammala bincike.” cewan Alƙali.
Jami’an tsaro suka kama Alhaji Kabiru.
Zarah ta kalli Haris.
Idanunsa sun cika da wani sabon yanayi ba fushi ba, ba baƙin ciki ba.
Amma sai Malam Bashir ya sake miƙewa.
“Akwai abu guda,” ya ce cikin sanyin murya
“Marigayin ya bar wasiƙa kafin ya mutu, cewa idan wani abu ya same shi na bayyana wannan wasiƙa.”
Sai kotu ta sake yin shiru.
Haris ya juya cikin mamaki.
“Wasiƙa?”
Malam Bashir ya ciro, takarda daga aljihunsa.
“Na ajiye wannan wasikar tsawon lokaci na yi zaton hatsari ne kawai, amma yanzu lokaci ya yi.”
Alƙali ya karɓa yace. “Za a karanta a zaman kotu na gaba.”
Bayan sun fito harabar kotu Zarah ta riƙe hannun Haris a waje tace:
“Me kake tunani?”.
Ya kalli sama.
“Idan wasiƙar ta tabbatar da cewa ba hatsari ba ne?".
Sai ya yi shiru.
“Komai zai canza.”
Washe gari Kotun ta sake cika maƙil.
Kowa na jiran karanta wasiƙar marigayi.
Alƙali ya buɗe takardar a hankali.
Murya ta cika kotu yayin da aka fara karantawa:
“Idan wani abu ya same ni, to akwai abubuwan da nake so duniya ta sani, na gano cewa takardun filinmu an sauya su ba tare da sani na ba.
Na fuskanci Alhaji Kabiru Danladi kan wannan lamarin.
Ya nemi in yi shiru, amma na ƙi, idan na mutu ku duba hulɗar kuɗi tsakanin kamfaninsa da wasu mutane kafin hatsari,
ban taɓa zargin abokina Sulaiman da shirya mutuwata ba, amma na san yana cikin matsin lamba daga wasu manyan mutane.”
Haris ya ji zuciyarsa ta cika da wani sabon yanayi.
Wasiƙar ta tabbatar da abu guda, an shirya komai ne, ba hatsari kaɗai ba ne.
Lauyan gwamnati ya miƙe tsaye.
“Mai girma alƙali, wasiƙar da shaida na banki sun nuna cewa, Alhaji Kabiru Danladi ne ya shirya a sauya takardun fili, sannan ya ƙirƙiri yanayin da ya jawo hatsarin domin ya mallaki filin gaba ɗaya.”
Kotu ta sake rikicewa.
An kuma tabbatar cewa shi ne ya ɗauki mutanen da suka kai wa Haris hari.
Alƙali ya buga tebur domin shiru.
“Bayan nazarin shaidu da wasiƙar marigayi,” ya ce cikin murya mai kaifi, “kotu ta same ka da laifin shirya maguɗi, hana adalci, da haɗa baki wajen haddasa mummunan lamari da ya kai ga rasa rai.”
Shiru mai nauyi ya sauka a cikin kotu.
“Hukuncinka shi ne daurin shekaru masu tsawo tare da tarar mai tsoka a cikin dukiyar ka.”
Sannan kotu ta umurci da a kai Alhaji Kabir ɗanladi gidan gyaran hali nan take tare da aiki mai wahala.
Game da Alhaji Sulaiman…
An same shi da laifin ɓoye gaskiya da kuma rashin kai rahoton, an yanke masa hukuncin wata shida a gidan gyaran hali.
Faisal kuma an same shi da laifin karkatar da kuɗin diyya, kotu ta bashi nan da wata ɗaya ya dawo da kuɗin.
Ita kuma Zarah, anyi la'akari da babu abinda ta sani akan wannan rikicin, kotu ta sallame ta .
Bayan an tashi daga kotu, Haris ya tsaya a harabar kotu, yana kallon sararin samaniya.
Zarah ta matso kusa ta ce
“Adalci ya samu.”
Ya kalleta.
“Eh… amma ba zai dawo da mahaifina ba.”
Ta sunkuyar da kai.
Sai ya ɗaga haɓarta a hankali ya ce,
“Amma zai hana a sake cutar da wani kamar yanda akayi min.”
Ya ɗan ɗauki lokaci, sai ya ce:
“Zarah… soyayyarmu ta taso cikin duhu da rikici , idan za ta ci gaba, dole ta rayu cikin haske da kuma soyayya.”
A hankali hawaye suka zubo daga idonta.
“Na shirya.”
A tunanin Zarah da Haris komai ya zo ƙarshe, amman sai dai basu san cewa yanzu ne aka fara wasan ba , Akwai sirrika na ban Al'ajabi da rikitarwa da zasu fara fitowa wanda basu taɓa tsammani ba
A gefe guda kuma wannan wanda yake bibiyan Haris yana kallan su ta cikin mota ,
Sai ya ɗaga waya yace:
"Oga an kama Kabir Ɗanladi komai zai lalace , ya kamata ayi hanzarin fito da shi kodai a gama da su ne ."
Banji abunda aka faɗa mai ba naji ya ce, " An gama oga."
🅿️ 05
Bayan wanann mutum ya kammala waya sai ya shiga mota ya wuce bai ce musu komai ba.
Rayuwa ta cigaba da gudana cikin nishaɗi da annashuwa , kowa ya manta da abubuwan da suka faru, yaw shekara ɗaya Kenan kuma ya kama yaw ne ranar ɗaurin Auren HARIS DA ZARAH .
Gidan Alhaji Ahmed Sani, wato gidan mahaifin Haris , cike yake maƙil da ƴan uwa da abokan arziƙi , sosai ake shagalin biki kamar babu abun da ya faru kwanakin baya .
Zaune yake su na nishaɗi shi da abokan shi , Ajmal, Yaseer , Habib.
Ango kuwa ya ci ado cikin shadda mai ruwan madara da hulla ƙube, komai nashi kalan kayan shi ne, kana ganin shi kaga ango .
Yaseer yace "Angon Zarah kenan irin wannan wanka anya baza kafi amarya kyau ba kuwa?".
Cikin nishaɗi yace " Haba kaima kasan Amarya ta fi ni kyau, kawai kana zagi na ne , Amman ka bari ka ganta zaka tantance waye yafi kyau cikin mu".
Suna cikin fira sai ga kiran Ouncly Musa ya shigo wayan Haris .
"Ok gamu nan fitowa ". Ya kashe wayan.
Suna tafiya suna tsokanar shi, shi kuma sai zuba murmushi yake yi bai ce musu komai ba, Har suka iso falo, nan suka tarar da Aunty Safiya, Aunty Halima, Aunty Zukaihat, suna fira suna nishaɗi .
Cikin zolaya Aunty Zukaihat tace " Ango ansha mai irin wannan wanka haka , gaskiya kayi kyau sosai".
Sunkuyar da kai kawai yayi yana dariya ,sai suka kama hanyar fita gurin motocin da aka shirya zuwa ɗaurin Aure .
Zaune take tasha kwalliya kamar ka sace ka gudu Husna da Hanan sai zolayan ta suke yi , kasancewar Zarah bata da ƙawaye , tana cikin yaran Ouncly ɗinsu sune suka zama ƙawayen ta .
Aunty Asma'u ne ta shigo maman su Husna kenan , tace " ku tashi muje ƙasa ana jiran ku muyi hotu na ".
Sai lokacin ta ga Husna da Hanan kwance ko wanka ba su yi ba .
Sai ta fara faɗa " yanzu ku baku shirya ba , kuna nan kun cikata da surutu marar amfani , Allah ya shirya min ku, bansan lokacin da zakusan kun girma ba ".
Sai lokacin suka tashi har su na karo da juna gurin shiga bayi.
Nan ta fita ta ƙyalesu tana mita .
babban masallacin juma'a na garin Kano, ya cika maƙil da mutane kamar kowacce juma'a, bayan an idar da Sallah, aka ɗaura Auren HARIS AHMAD DA FATIMA SUKEIMAN akan sadaki dubu ɗari biyu, bikin ya samu halartar manyan ƴan kasuwa sosai.
Bayan kammala ɗaurin Auren sai aka ɗunguma sai gida , domin ana shirye shiryen walima a gidan su Zarah, bayan anyi ciye ciye da lashe lashe sai aka kama hanyan gidan su zarah domin walima maza da mata ne .
Isowan su kenan gidan su zarah , sai dai abinda suka tarar shine ya ɗaure musu kai , kowa yayi tagumi yayi shiru, mahaifiyar Zarah tana zaune hawaye na bin kuncinta sai taji tsayawan motoci , tana ɗaga kai suka haɗa ido da Haris.
Ganin yanayin ta yasa gaban shi faɗu da sauri ya ƙaraso yace "Mama meke faruwa ne na ga kowa yayi shiru ina Zarah?".
Cikin kuka take faɗa mai ɓacewan Zarah , sun shiga ɗaki suka cidda bata nan , sun yi tunanin cewa tana banɗaki ne sai aka share da zancen , jin shiru yasa suka tura ƙofan bayi wayam.
Kamar wasa aka nemi Zarah sama ko ƙasa ba'a ganta ba, mun share fiye da 1hour muna neman ta a cikin gidan nan amman babu ita babu alamanta.
Cikin firgici Haris ya ɗago kai , Wai mafarki ne kodai da gaske Zarah aka sace, no ba gaskiya bane , haka ya shiga sashin Zarah yana ƙwalla mata kira "Zarah , Zarah, Zarah ",!!!!!! Amman babu alamanta a ɗakin , nan ya durƙusa yana mamakin waye zai ɗauke Zarah , bai gama tunani ba sai yaji ƙarar motar ƴan sanda ya karaɗe gidan , a firgice ya tashi har yana tuntuɓe gurin fita.
Yana shigowa falon ƴan sanda na shigo wa , sai ogan su ya ce
"gashi nan ku kama shi ".
Cikin firgici ya ɗago idon shi da sukayi jajir saboda ɓacin rai ya ce " menayi za'a kama ni?".
Ogan ya ce " saboda kaine ka sace Fatima Suleiman (Zarah) Kuma muna da hujja don haka muje".
Aunty Safiya, Aunty Halima, Aunty Zulaihat , gaba ɗaya kansu ya ɗaure , sun san su na tare da Haris har aka ɗaura aure taya hakan zai yiwu .
Kafin kowa ya ce wani abu ɗan sanda ya ciro waya a aljihu ya masu playing wani video.
Haris ne a cikin wannan video , ya shigo ɗakin Zarah.
Tana ganin shi ta miƙe ta ce " Haris ta ya akayi ka shigo cikin gidan nan ga mutani ta ko ina?".
yayi murmushi ya ce " saboda inasan naga Matana kodai haramun ne, faɗamin naji, nayi kewanki sosai shiyasa na ce ba zan iya haƙuri ba ".
Tayi murmushi ta kau da kai ta ce" Hmmm haka ne to shi kenan yanzu ka ganni sai ka tafi tun kafin Aunty Asma'u ta shigo ".
Juyowan da zata yi kawai ya shaƙa mata abu nan take ta sume.
A firgice kowa yake kallon wannan video cikin mamaki da tashin hankali.
Haris kuwa tsabar kanshi ya ƙulle kasa magana yayi har aka sanya mai sarƙa aka fara tafi da shi.
Gaba ɗaya garin Kano ya ɗauka da labarin Ango ya sace Amarya .
Bayan an fita da zarah daga gida, aka miƙe hanyar kamar za a bar Kano, daji ne sosai baka cewa akwai mutani a ciki, sai dai abinda ya bani mamaki kuwa shi ne wani ƙerarran gida da na ga ni sai da nayi mamaki , gidan ya gaji da haɗu wa kuma kuɗi yayi kuka sosai kamar baza a mutu ba.
A nan mai kama da Haris ya faka mota ya zagaya ya ɗauko Zarah da har yanzu ta ke a sume bata farka ba ya shiga ciki da ita.
Police station kuwa tun da suka isa da Haris aka sanya shi a cell , sai ga wani ɗan sanda ya zo gurin shi ya miƙa mai waya, da mamaki Haris ya ke kallan shi, yasa hannu ya karɓa.
Sai na wayan ya ce “Ka yi tunanin komai ya ƙare ne?”.
Haris ya miƙe tsaye. “Waye wannan?."
“Ka kama ƙaramin kifi, amma babban kifi yana iyo a ruwa mai zurfi.”
Kafin Haris ya sake magana ɗan sanda ya karɓi wayan.
Zuciyan Haris ya fara bugawa da ƙarfi, me hakan ke nufi ?.
GIDAN GWAMNATI
Wani babban mutum ne zaune a kujera kana ganinsa kasan hutu ya zauna a jikin sa , yana magana cikin izza da isa da mulki, juyowan da zai yi sai naga Alhaji Suleiman mahaifin Zarah.
Magana yakeyi da wannan mutumin da yake kamanni ɗaya da Haris.
Cikin isa ya ce " fatan dai yarinyan tana lafiya babu abun da ya sa me ta, inasan ka kula sosai wannan ba ƙaramin aiki ba ne , fatan ka fahimta".
Sai yace " Na fahimta Daddy kada ka damu babu wanda ya isa ya gano inda ta ke , kuma komai na tafiya dai dai ".
🅿️6
A firgice Zarah ta farka , a tunanin ta bacci ne ya ɗauke ta , batasan kwana ɗaya ta yi har da yini tana baccin dole ba, sai ta fara kallan in da ta ke tukunna kamar ba gidansu ba.
Wani irin zabura tayi ta nufi ƙofa zata fita , sai dai abinda ya ba ta mamaki shi ne ƙofan a kulle yake gam, sai lokacin ƙwaƙwalwan ta ya tuna abun da ya faru .
Cikin masifa ta ke magana , " Meyasa Haris zai kawo ni nan ya ajiye , me yake nufi da ni, bayan an ɗaura mana aure yanzu meye zance ma Aunty Asma'u wayyo na shiga uku na ?."
GIDAN SU ZARAH
Sosai hankalin kowa ya tashi a cikin gidan , Cikin masifa Alhaji Suleiman yake cewa , " Wannan ai rainin hankali ne ta ya ya zai sace min yarinya ranar da ake ɗaura auren su me hakan ke nufi , Wannan ai rashin hankali ne ."
"Haba Abban Zarah yanzu kaima ka yarda Haris ne ya sace Zarah, gaskiya ni dai ban yarda ba ." Cewar maman Zarah .
"Ga abu kowa ya gani , nima abun ya daure min kai sosai , amman kuma wannan video fa kina kallo dai shi ne a ciki ba wani ba."
" Haka ne amman kada kayi saurin yanke hukunci , kayi tunani sosai , kada azo ayi da na sa ni daga baya dan Allah Abban Zarah."
Sosai jikin Alhaji Suleiman ya yi sanyi da maganganun matar shi ya ce
" Allah ya bayyana mana ita cikin ƙoshin lafiya , bari naje police station ɗin inji ya za'ayi ko zasu sa ke shi, amman kuma ai ba mu kai ƙara ba waye ya turo ƴan sanda harda video kenan ?."
" Kaje police station ɗin duk yanda ake ciki za ka ji, zasu faɗa maka wanda ya kawo ƙara da kuma wanda ya basu video ɗin."
Bai ƙara cewa komai ba ya miƙe ya fita harabar gida , yana cikin tafiya sai ga Ouncly Musa sai suka shiga mota suka wuce police station ɗin tare .
Su na isowa harabar police station ɗin Haris ya na sanyo ƙafa zai fito .
Cikin mamaki Alhaji Suleiman ya ke tambayan shi ya akayi suka sake shi , sai yayi shiru bai ce komai ba saboda bayasan ya ƙara musu damuwa.
Haris yacen" Baba daman Faisal ne ya zo."
Kafin ya gama magana sai ga Faisal ya fito daga ofishin ƴan sanda .
Alhaji Suleiman yace ma Faisal.
" Allah ya yi albarka, zanje inyi magana da ogan su , ku kama hanyan gida zamu biyo bayanku, ku kula sosai ."
Alhaji Suleiman ya shiga ofishin Ouncly Musa kuma ya tsaya jiran shi a mota, yana shiga ya tambayi sauran jami'an domin ya yi magana da ogan su, cikin ƙanƙanin lokaci aka bashi izinin shiga.
Da sallama ya shiga ofishin , ogan ya bashi izinin zama sukayi musabaha , bayan sun gama gaisawa yake faɗa kishi abun da ke tafe da shi .
Inspector Mahmud yace. " Ehhhh gaskiya muna office zauna sai na ga yaro ya shigo da saƙo a envelope, sai na karɓa ina tambayan shi waye ya bashi yace baiga ko waye ba domin kuwa a cikin mota yake kuma fuskarsa sanye da face maks , har na ajiye zan fita kuma sai nayi tunanin ƙilla saƙo ne mai muhimmanci , ina buɗe wa sai naga wanna video ɗin a cikin wannan wayan da na nuna muku , address na gidan da komai a wani ƙaramin paper aka rubuta aka sanya cikin envelope ɗin , shiyasa da ɗan uwan Zarah ya zo na yayi bayani akan bakusan da labarin ba sai na sake shi, kaji yanda abun ya kasance."
Alhaji Suleiman ya sauke nannuyan ajiyan zuciya yace.
" Allah ya ƙara kiyaye gaba , amman yanzu ya labari akan binciken ita Zarah, akwai wani abun da aka samu ne ?."
Inspector Mahmud yace, " gaskiya har yanzu babu wata alama , amman ina sha Allah zamu zurfafa bincike, kodai akwai wanda kuke zargi ne , ko akwai wanda ya taɓa yi musu barazana haka?."
" Gaskiya babu inspector, amman zamu tambayi shi Haris ɗin muji duk abin da ke ciki zaka ji daga gare mu."
Sukayi sallama ya fito ya shiga mota Ouncly Musa ya ja suka kama hanyan gida, su na hanya ya na tunanin wannan lamari akwai rikitarwa, har suka isa gida yana saƙa da warwara, amman baya da amsa ko ɗaya da zai ba kanshi.
HARIS.......
Kai tsaye gidan su Haris ya nufa shi da Faisal, suka bi ƙofan baya basu shiga ta babban falo ba , ya na shiga ɗakin shi ya kwanta yayi ruf da ciki ya na tunanin abinda ya faru jiya, Faisal ne ya katse mai tunani.
" Haris ya kamata mu san abin yi akan wannan lamari , waye kake zargin zai aikata maka wannan mummunan ƙazafi , ga Zarah kwana ɗaya har da wuni babu labarin ta."
Haris yace " hnmmnn Faisal kenan abinda ni ke tunani kenan nima, gaba ɗaya kaina ya gama ƙulle da wannan al'amari, kuma duk ba wannan ba, waye wanda yayi amfani da fuska na har ya shigo gidan nan babu wanda ya sa ni , wannan abu shi yake daure min kai sosai?"
Faisal " gaskiya akwai mamaki sosai , Allah ya bayyana mana ita cikin ƙoshin lafiya."
Bayan sun gama tattaunawa akan lamarin sai ya shiga ban ɗaki ya watsa ruwa, a ƙalla ya ɗauki 1hrs ya na wanka, daman wannan dabi'an shi ne daɗewa a ban ɗaki, ya na fitowa Faisal ya shiga ya ɗauro alwalla, Haris shi ma ya kammala sai suka sauko zuwa falo.
Cikin mamakin ake kallon su , yawshe su ka shigo.
Aunty Zulaihat da Aunty Safiya da Aunty Halima duk sun zuba tagumi , kowa fuskan sa cikin damuwa, sai ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
Duk miƙewa su ka yi su na mai sannu da zuwa, sunyi farin cikin ganin ya dawo kuma cikin ƙoshin Lafiya, bayan sun gama gaisawa suka nufi hanyar fita don zuwa Masallaci .
Zarah.....
Bayan ta gama kallon komai na gurin sai ta zauna a a kujera mai zaman mutum ɗaya , tana jiran ko wani zai shigo amman shiru, ta ɗaga kai ta kalli agogo ƙarfe 7:00pm tanasan ta yi Sallah amman bata da hijabi, haka ta cigaba da zaman jira har ta fara gyangyaɗi a zaune, ƙarfe 10:30pm kamar a mafarki taji ana taɓa ƙofa a firgice ta tashi ta zauna ta na jiran ta ga waye zai shigo.
"Assalamun Alaikum" sai aka turo ƙofa aka shigo.
Wani irin zabura ta yi cikin firgici da tsoro da mamakin abinda idon ta ya gani mafarki ne kodai ƙarya ne kai kodai gizo ne?.
Bakinta yana rawa tace " daddy " ( daddyn Haris, Ahmad Sani ) shi ne wanda ta ga ni , nan ta ke ta faɗi ƙasa a sume.
🅿️ 7 Zarah...........
" Fatalwa!!!! , fatalwa !!! " Zarah ke wanann ihun.
Ai kuwa ta na buɗe ido ta gan shi a gaban ta, wani irin ihu ta tsala sai da suka toshe kunnuwa.
Alhaji Ahmed ya ce :
" Ki rufe mana baki yanzu, idan ba haka ba za ki ga abin da zan yi."
Zarah ta yi tsit ta na raba ido kamar an tsare ɓera a rami.
Alhaji Ahmed ya kalleta zai yi magana sai wayan shi ya yi ƙara , ya ɗauka " eh ya shigo yanzu " sai ya ajiye wayar
Sai aka turo ƙofan a hankali.
Zarah ta na ɗaga ido sai ta ga Haris , ta miƙe a guje ta faɗa jikin shi tana kuka, ta ce " Haris me nake yi a nan kuma daman kasan mahaifinka ya na raye , ka mayar da ni gida, tun ɗazu ina jiranka bangan ka ba."
Sai ya kalle ta ya yi murmushi ya ce , " su na na Hamid , ni ne ɗan uwan Haris mu ɗin tagwaye ne."
Zarah ba wai kawai suman tsaye ta yi ba, aaa , jinta ɗaukewa ya yi na wasu daƙiƙu , a firgice ta janye jikinta ta na kallan shi cikin mamakin abun da yace mata , sai ta ke tambayan kanta , anya ba mafarki ba ne, zata yi magana Alhaji Ahmed ya yi sauri ya dakatar da Ita.
Alhaji Ahmed " akwai tambayoyi masu tarin yawa da kike buƙatar amsan su, amman kafin kiyi tambaya kinsan