Share this page
3 / 6
WACECE KE kin san Alhaji Suleiman ba mahaifin ki ba ne?." Zarah wani irin mummunan Sarawa kan ta ya yi ga wani irin jiri da ya ke neman ɗaukanta, " Ban fahimci abinda kake cewa ba , anya kuna cikin hankalinku kuwa , Meyasa ma kuka kawo ni nan , ku kaini gidanmu Abbana yana can yana jirana." Alhaji Ahmed yace " ƙalli wannan da ga nan sai ki yanke hukunci " ya miƙa mata wani akwatin katako . Zarah ta karɓa hannunta na rawa tace " wannan fa meye a ciki." Alhaji Ahmed yace " ki duba ki gani ." Tana buɗe akwatin ta ci karo da hoton Haris da Hamid, ta ciro hotunan daga cikin akwatin ta fara kallo ɗaya bayan ɗaya tana mamakin abinda idon ta yake ga ni, hoton da ta ɗauko na ƙarshe yafi girgizata , hoton ta ne tare da mahaifinta da mahaifiyarta harda katin haihuwa. tace " amman ka mutu tsawan shekara 25 kenan , ta ya ya yanzu na ganka a raye? Kuma ya akayi ban taɓa sanin cewa Alhaji Suleiman ba mahaifina bane, meye abinda ke faruwa ne ?." Alhaji Ahmed " tabbas babu wanda yasan ya akayi na kasance a raye , amma wannan amsa ba yanzu zaki sameshi ba , dalilin da yasa na ɗauko ki shi ne , bakisan waye Alhaji Suleiman ba kuma bakisan cewa su ɗin tagwaye bane kamar yanda Haris suke tagwaye , kuma shi ne wanda ya saka a sato ki , a tunanin shi yanzu haka kina hannun shi, sai dai bai san cewa a lokacin da ya tura wani ya sanya fuska irin na Haris ya sato ki mun samu labarin ba, shi ne na tura Hamid a maimakon wancan na sa a kama min shi, yanzu haka yana kulle, shi ne na sa a a kawo ki wannan gurin , na tura Hamid har gidan gwamnati ya sameshi ya faɗa mai kina gurin shi. Sanin wacece ke kafin sanin su waye family ɗin mu da kuma family Alhaji Suleiman ya fi komai muhimmanci." FLASH BACK 🔙 ASALIN ZARAH . ADAMAWA, THE BINDOW ESTATE. The Bindow Estate , guri ne da ya haɗa shahararrun masu kuɗi, ƴan siyasa da kuma ƴan kasuwa, estate ne da ba kowane irin mutum yake shiga ba saboda unguwa ne na manyan mutani. Alhaji Abubakar Ƙasim, wanda ya kasance shi ne shahararren ɗan kasuwa da sunan shi babu inda ba'a san shi ba a faɗin Nigeria har ƙasashen waje, shi ne ma mallakin ( Adamawa Beverage company ) kamfanin da ke sarrafa ruwan tables water 💦 da juice 🧃 ya na da amana da gaskiya, bayasan ha'inci a kasuwanci, ya rasa iyayensa tun yana ɗan shekara 10 a gidan marayu ya girma , ya sha gwagwarmaya da rayuwa kafin Allah ya mai da shi mutum mai ƴanci. Gidan Alhaji Abubakar Ƙasim, gida ne mai girman gaske komai tsaru Masha Allah , tun daga wajen gidan har ciki, falo ne farko sai ɗakuna sankai goma sha amman gidan ɓangare uku ne , bangaren farko na Alhaji Abubakar Ƙasim ne ɗaya kuma na baƙi daya kuma na iyalin shi ne, sai ɓangaren masu aiki ta waje. Matan Alhaji Abubakar guda ɗaya Hajiya Maryam Ishaq, ita ƴar asalin garin Adamawa ne ahalinta su na Yola kasuwanci ya maida su can , Hajiya Maryam mace mai kunya , kyauta , ƙanƙan da kai da kuma sanin darajar mutum, sun haɗu da Alhaji Abubakar ne a gurin wani taro , kasancewa itama ta na business sosai kuma su na da rufin asiri Alhamdulillah, yana gani yace yana so , cikin ƙanƙanin lokaci aka sanya rana wata ɗaya , an sha shagali sosai a bikin, wanda ya samu halartar manyan mutani daga gurare daban-daban. Shekaran su bakwai da aure amman ko ɓatan wata bata taɓa yi ba , wannan abun yana matuƙar damun ta sosai , sunyi yawan asibit daban-daban ƙasa-ƙasa amman babu wata matsala ance dukkan su lafiya ƙalau Allah ne kawai bai kawo ba , sun fawwala ma Allah komai suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da girmama juna. Wata rana yana tafiya ya ga wani mutumi ana dukan shi akan hanya tamkar dabba mara gata , ya yi parking ɗin mota a gefen ya fito ya tambayi abinda ke faruwa. Wani mutumi yace " yallaɓai wannan da ka ke ga ni ɓarawo ne , sata yayi aka kama shi ana duka". Cikin tausayawa Alhaji Abubakar ya kalle shi yace " dan Allah kuyi hakuri ku daina dukansa ya isa haka zan biya abinda ya ɗauka". Ya ciro kuɗi masu yawa ya bayar ya ɗaga wannan mutumin ya sanya shi a mota suka je asibiti, bayan an gama mai treatment suka kama hanyar gidan Alhaji Abubakar. Cikin mamaki wannan mutumin yake kallan ko ina a unguwar kamar a mafarki , ashe zai ga irin wannan guri a duniya. Su na isowa ya yi horn mai gadi ya buɗe mai get ya shiga ya yi parking ya fito, masu aiki su na gaida shi cikin girmamawa, shi kuma yana amsa wa cikin kulawa . Bayan sun gaisawa da ƴan aiki ya kama hanyar falo sai juyo yace " Muzaffar ga sabon aboki kun samu a bashi ruwa ya yi wanka a ba shi abinci anjima zan dawo in sha Allah sai muyi magana". Muzaffar " an gama yallaɓai yanda kace haka za'ayi in sha Allah sai ka fito". " Assalamun Alaikum gimbiyar mata " cewa Alhaji Abubakar bayan ya buɗe ƙofar falo. Amman ga mamakin shi sai ya ga babu kowa a falo , sai ya haura sama inda ya kasance ɗakin su ne , da sallama ya shiga amman shiru babu amsa ga ɗakin da duhu , sai ya kunna hasken ɗakin can ya hango Gimbiyar shi tsakiyan gado ta dunƙule guri ɗaya , cikin sauri ya ƙarasa gare ta . " Maman Aryan lafiya kuwa , meke faruwa ?." Saboda sunan da yake kiranta da shi kenan. Ta ɗago ta kalle shi kawai sai ta fashe da dariya, shi kuma sai ya zuba mata ido kawai yana kallan ikon Allah, wanda ya kasa amsa sallama shi ne yake wannan dariya haka ?. Bayan ta gama dariya sai tace " Baban Zarah kenan ashe haka ka ke so na , wow gaskiya na yi dace miji mai so na , duk ba wannan ba , akwai surprise ɗin da na shirya maka , muje ka ci abinci tukunna." " Maman Aryan wannan wani irin wasa ne , zuciya na ta kusa bugawa , dan Allah kada ki ƙara kinji Please muje." Sai ta kama kunni alamun ban haƙuri. Sai ya yi murmushi yace " an yafe miki 😉 muje , na ƙosa naji wani albishir ne kike san faɗa min." " Kayi wanka ka ci abinci tukun." Bayan ya kammala wanka, tare suka sauko ƙasa , suka tarar da mai aiki ta kammala komai har ta tafi , sai suka zauna , ta zuba mai farin shinkafa da miyan ganda, itama ta zuba nata , babu wanda ya yi ma wani magana har suka kammala. " Baban Zarah" ta kira shi a hankali sai ta fara hawaye. "Maman Aryan meke faruwa ne ki faɗamin dan Allah." " Baban Zarah yaw Allah ya karɓi addu'a mu , ina da ciki." Da sauri Alhaji Abubakar ya ɗago kai yana kallan ta, sai yaji kamar a mafarki, ashe zai ga wannan ra na a duniya , nan ta ke ya yi sujjada har sau uku yana gode ma Allah. Cikin jin daɗi ya rungumi matar shi, abun alfaharin shi yace " Allah ya miki albarka Matana, Allah ya albarkaci abin da ke cikin." Cikin jin kunya tace " Amen mijina." Washegari a sa fe ya riga ta tashi bacci , ya yi wanka ya shirya ya haɗa ma ta ruwan wanka itama sannan ya tashe ta, ta yi wanka ta fito, ita ma shirya wa ta yi suka sauko ƙasa domin karyawa. Su na saukowa suka tarar da mai aikin su Peace da Blessing sun kammala abinci sun jera komai tsaf gwanin burge wa . Blessing da peace suka haɗa baki " morning ma morning sir ." Cikin farin ciki Alhaji Abubakar ya amsa " morning how are you doing, hope everything is ok , or is there any problem?." " No sir , everything is ok." Hajiya Maryam " morning too , how is your work today, hope all is well ?." " Yes ma , hope u a fine too ?." " Yes I'm ok too alhamdulillah , u can go now ok ." " Safe journey " sai suka fita zuwa sashen su . Bayan sun zauna sai ta haɗa masu tear ta zuba ƙwai da chips a plate ta ajiye suka fara karyawa , bayan sun gama ta ɗauko mayafi, su ka kama hanyan fita. Bayan sun fito Alhaji Abubakar ya kira Muzaffar , suka yi musabahaje sannan ya tabbatar mai cewa zai fita tare da Madam idan ya dawo zuwa ƙarfe 5 ya zo da ɓakon nan sashin baƙi, sannan suka shiga mota. Suna barin gida kai tsaye Company suka nufa , ma'aikata kowa sai miƙa gaisuwa yake yi, cikin sakin fuska suke amsa ma kowa gaisuwa gwanin burgewa . Bangaren sarrafa ruwa suka fara shiga sai da suka tabbatar komai dai-dai sannan suka fito , ƙasa ya koma suka nufi parking space suka shiga ya tayar da mota suka bar Company gaba ɗaya. Kai tsaye Adamawa specialist hospital jimeta suka nufa , su na zuwa suka nufi hanyan ganin likita kasancewa sun ya yi magana da shi a waya . Bayan sun gaisa da docter Ibrahim sai ya bashi izinin zama yace " docter Madam ne muke tafe da ita za'a duba ta ne ." Docter Ibrahim yace " ta shigo mana." Tana shigo sai suka gaida da doctor , ya nuna mata in da zata hau , bayan ya ya kammala duba ta sai ya buƙaci ayi scaning . Sai ta kwanta ya fara scaning, abinda ya gani yasa ya ƙara bude ido Da kyau " ƴan biyu " ya furta a hankali . Bayan an kammala sai suka tsaya jiran result. Sai ga doctor ya fito yace " congratulations sir ƴan biyu ne mace da namiji." 🅿️ 8 Cikin farin ciki Alhaji Abubakar yace " doctor twins, Alhamdulillah ala ni'imatullah, wani jinkiri alheri ne , Allah na gode maka da wannan kyauta da ka bani." Hajiya Maryam hawayen farin ciki kawai ta ke yi tana hamdala a zuciyarta. Harda kayutan gida da mota aka yi ma doctor, sosai ya yi farin ciki da tayasu murna da fatan Allah ya sauke ta lafiya. Kasancewar sunje ma'aikata da sa fe yasa yanzu suka nufi gida kai tsaye. Bayan ya yi horn mai gadi ya buɗe musu get suka shiga, bayan ya yi parking sai ya fito , ya zagaya ya buɗe mata ƙofa ita ma ta fito , kana kallon su zaka fahimci yaw su na cikin farin ciki sosai. Muzaffar ne ya fito yana musu barka da dawowa , ganin su da ya yi cikin farin ciki yasa ya ce " Alhaji ayimin afuwa ina da tambaya ne?." Alhaji Abubakar yace " ba sai ka tamabaya ba nasan me zaka ce, farin cikin da muke yi ne ya yi yawa har ya bayyana a fuskokin mu, ba komai bane face abinda muka daɗe muna fatan Allah ya azurtamu da shi ne yanzu ya bamu , A taya mu da addu'a Allah ya sauke Hajiya lafiya " ya ƙarasa magar yana murmushi. Muzaffar washe baki ya yi da jin wannan labari mai daɗin gaske, ya yi musu fatan alheri. Alhaji Abubakar yace " Muzaffar ka shigo da wannan baƙon sashen baƙi yanzu ." Cikin girmamawa Muzaffar yace " In sha Allah Alhaji ." Bayan sun shiga cikin gida yace mata yana zuwa akwai maganan da za suyi amman sai ya dawo. Yana fita ya nufi sashen baƙi, da sallama a bakin shi ya shiga , baiyi tunanin sun iso ba sai yaji an amsa sallama. Cikin sakin fuska suka yi musabaha sannan ya zauna yace " Masha Allah Muzaffar sannu da ƙoƙari, bawan Allah zanso nasan waye kai kuma daga ina kake , da girman ka meyasa kayi sata?." Sai mutumin ya ɗago ya kalli Alhaji Abubakar yace " Alhaji ina matuƙar godiya da abinda kayi min Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, sannan kuma suna na Malam Zailani, kuma Ni ɗan Adamawa ne iyalina kuma suna ƙauyen Gwadabawa da ke Jimeta, ƴan uwana duk a nan suke , kasancewar aiki yana wahala shi ne na fito neman aiki saboda yaw sati ɗaya kenan rabon da muyi girki a gidana , satan da nayi ka tarar ana dukana ma saboda yunwa ne , dubu biyar na sata, wannan shi ne labari na." Alhaji Abubakar ya sauke nannuyan ajiyan zuciya yace " Allah ya kiyaye gaba, in sha Allah zan baka aiki , kuma zaka ɗauko iyalin ka ku dawo nan da zama ga dakuna nan ku zaɓi ɗaya , yanzu zan haɗa ka da driver kuje Gwadabawa ku ɗanko abin da kuke buƙata sai ku dawo tare." Cikin farin ciki Malam Zailani yace " Alhaji na gode Allah ya saka da alheri Allah ya jiƙan iyaye Allah yayi ma zuri'a albarka Allah ya ƙara arziƙi." Alhaji Abubakar ya ji daɗin wannan addu'a da malam Zailani ya yi sosai , cikin farin ciki yace " Na gode da addu'a Allah ya yi mana jagora gaba ɗaya. Da amen suka amsa , daga nan Alhaji ya umurci Muzaffar da ya kira Anas driver ya yi mai bayanin in da zai kai Malam Zailani , kuma su dawo tare . Yana gama magana ya tashi ya tafi , suma miƙewa su kayi suka kama hanyar fita. Alhaji Abubakar gurin gimbiyar shi ya koma , yana zuwa ya sameta a inda ya barta, tana ganin shi ta gyara zama , kasancewar yace za su yi magana idan ya dawo. Bayan tayi mai sannu da dawowa ya zauna yana sauke numfashi yace " Maman Aryan da Zarah, Allah zai cika mana burin mu , Allah ya sauke ki lafiya, bazan iya misalta irin farin cikin da nike ciki yaw ba , Allah na gode maka da wannan ni'ima." Cikin farin ciki ta ce " wannan gaskiya ne , Allah ya azurta mu da yara biyu llallai wani jinkiri alheri ne, Allah ka na gode maka." Alhaji Abubakar ya ɗan nisa yace " Daman inasan na faɗa miki ne akwai wani ɗazu da na ga ana duka akan hanya " Nan ya bata labarin komai har wanda malam Zailani ya bata. Cikin tausayawa ta ce " Ikon Allah amman gaskiya na tausaya masu , Kai kuma Allah ya baka lada , Allah ya ƙara arziƙi da lafiya." Cikin jin daɗin addu'a ya amsa da Amen. JIMETA , ƘAUYEN GWADABAWA, MALAM ZAILANI Wata mata ne ɗauke da bokitin ruwa tana tafiya, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci ƙarfinta ya ƙare , tana cikin tafiya sai gani nayi bokitin ruwan ya faɗi ƙasa, juyowan da zanyi sai na ga ta faɗi ƙasa, sai lokacin na lura ashe tana da ciki wanda bai wuce wata biyar ba. Faɗuwan ta ya yi dai-dai da lokacin Malam Zailani suka shigo layin da mota , yana yi ma Anas driver kwatance idon shi ya sauka akan wacce ta faɗi ƙasa, Anas ma akan idon shi ya faɗi ya yi saurin tsayawa da mota, bayan sun fito da ga mota sai suka nufi inda wannan matan ta faɗi. Su na ƙarasawa Malam Zailani yace " subhanallahi Mero meke faruwa haka ?," ya yi sauri ya ɗagata. Anas driver yace " sannu baiwar Allah ." . Malam Zailani yace " Matana ne ." Anas driver yace " ku shiga sai mu ƙarasa gidan ko, sannu Madam." Sai suka shiga mota suka cigaba da tafiya , kasancewar sun kusa isa hakan yasa basu yi wani dogon tafiya ba suka ƙarasa gidan. Gida ne matsakaici, duk da kasancewar gidan talakawa ne amman komai a gyare yake gwanin sha'awa. Bayan sun shiga cikin gidan, Malam Zailani da kanshi ya ɗauko musu tabarma ya shimfiɗa masu suka zauna , ya ɗebo ruwa a ba Anas, cikin jin daɗin da sakon fuska ya amsa ya sha . Bayan sun zauna ne ya yi ma Mero matarsa bayanin duk abinda ya faru, ya tabbatar mata yanzu zasu tafi tare. Hawayen farin ciki ne ya zubo mata , cikin farin ciki ta ɗaga hannu sama ta na gode ma Allah da wannan sauyi da Allah kawo masu. Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama haɗa kayansu, Anas driver ne ya taimaka musu suka fito da kayan waje akan sanya a mota, bayan sun kammala sai suka kama hanyan komawa. 🅿️ 9 Bayan sun kammala ɗaure kaya mota sai Anas driver yace " muje ko karfa dare ya yi mana a hanya." Malam Zailani da matarsa suka shiga , za'a tayar da mota kenan sai ga wata tsohuwa tare da wata yarinya ƙarama , yarinyan ba zata wuce shekara goma sha biyu ba , da sauri suka sha gaban mota. Tsohuwar matar ne tace " Zailani me zan gani haka , na ga ka kwashe komai ina zaka je , ni Laraba na shiga uku yanzu barin gari zaka yi baka faɗamin ba ?." Cikin mamaki Anas driver yace " Malam Zailani meke faruwa ne wace ce wannan ta dami mutani da hayaniya, kodai masu bara ne , Kaka ga wannan kiyi haƙuri akan hanya muke dare zai yi mana ." Ya miƙa mata dubu biyar. Ai kuwa Laraba ta hau salati " yaro ungo nan ni ce mabaraciya, yanzu Zailani a gaban idon ka ake zagina, nice mabaraciya , na shiga uku na lalace wayyo ni Laraba ina zansa kaina." Ai kuwa yarinyar itama kaman jira take yi, ta yi zaman ƴan bori a ƙasa ta fara ihu iya ƙrafinta " wayyo Allah jama'a ku kawo mana ɗauki ƴan birni sun zo za su sace mini baffa , wayyo Allah," iya ƙarfinta take ihu . Cikin ƙankanin lokaci mutani suka taru a gurin. Sai lokacin Malam Zailani yace " Haba Mama yanzu meke amfanin wannan abin, ki duba yanda kika tara mana Mutane, dan Allah kiyi, yanzu fa zance ya kaini gidanmu na sallami kowa , amman kinzo hanya kina wannan hayaniya , ke kuma zaki tashi kodai sai nayi ƙwallo da ke." Laraba tace " Eh Lallai Zailani ka kyauta nine kake ma sharri a gaban mutani, ba dole nayi ihu ba na ga kana shirin barin gari gaba ɗaya, kuma baka faɗa mana ba , jikalle na tashi kinji kada wanann mai kama da bijimin ya dakarmin ke." Yanda kasan ba ita ta gama birgima a ƙasaba ta tashi tana washe baki. Anas da kallo yake binsu, a zuciyarsa yake raya cewa tabbas wannan idan tazo gidan Alhaji akwai drama sosai. Malam Zailani yace " Mama muje dan Allah kada ki tara mana ƴan kauyen duka , nasan halin ki." Sai sannan suka kama hanyan zuwa gidan saboda babu nisa da ƙafa suka ƙarasa. Da sallama suka shiga gidan , wani dattijo ne zaune a ƙalla zai kai shekara saba'in ( 70yrs ) ya amsa sallama, suka shiga suka zauna a gefen tabarma , bayan sun kammala gaisawa, nan yake sanar da su komai yanda suka yi. Cikin farin ciki dattijon yace " Allah mun gode maka , Allah ya saka ma wannan mutumin da alheri, Allah ya albarkaci zuri'arsa ga ba ɗaya." Da amen suka amsa. Laraba tace " gaskiya wannan abu ya yi daɗi kai masha Allah, jikalle tashi ki ɗauko kayan ki ku tafi kada dare ya yi muku a hanya , Allah ya yi ma wanann Alhaji albarka." Cikin damuwa Malam Zailani yace " haba mama ya za'ayi in tafi da wanann yarinyan yanzu ki bari idan naje na ga yanayin guri sai na dawo na ɗauketa , amman gaskiya babu inda zata je yanzu." Sai ta hau masifa " wanann yaro akwai baƙin hali , yanzu baƙin ciki kake ma jikalle na , Wallahi sai dai ka fasa zuwa birnin kaima kaji na faɗa maka ." Ita kuwa nan take ta ɓare baki ya hau birgima a ƙasa , wayyo Baffa ya daina so na , wayyo Abbana ka dawo, meyasa ka gudu ka bar shalelen ka a gurin maƙiyanta , wayyo ni dije , Wallahi ina da burin zuwa birni tun ina cikin Mamana , shi kenan Baffa yana min baƙin ciki kada naje birni." Anas driver dariya yake yi har da riƙe ciki, Lallai wanann yarinyar akwai iya drama . Malam Zailani kuwa tun da yasan halin kayan shi , beyi mamaki ba , kawai binta yake yi da ido , yana mata fatan shiriya. Labarai tace " yi shiru jikalle za'a tafi da ke , ai Sai dai a fasa tafiyar ga ba ɗaya. Anyi juyin duniya Laraba taƙi yarda sai an tafi da Dije, ai kuwa tanajin ance ta ɗauko karanta sai ta miƙe a guje har tana tuntuɓe da ƙafan Anas. Cikin farin ciki ta shige ɗakin ta , wani bakko ta ɗauko ta zazzage ta koma bayan ƙofa ya ɗauko wani kayan , babu ko linkewa haka ta haɗa su guri ɗaya saboda murnar zuwa birni, a guje ta fito ɗakin zaka rantse biyo ta akayi Laraba harta miƙe zata riga a guje , sai Malam Zailani yace " Mama wata rana sai kin karya ƙafa akan rashin jin Khadijah , babu wanda ya biyo ta kawai rashin natsuwa ne , dan Allah Mama kiyi haƙuri ta zauna tukunna." Laraba " Amma anyi ja'irar yarinya , maza ki taho nan yanzu , kai kuma Zailani ka fita ido na kaji na gaya maka , Wallahi sai kun tafi da ita , sai dai idan kunje hanya ka jefar da ita ." Ba yanda Malam Zailani ya iya haka ya jawo hannun Dije suka fara tafiya , hanya fita suka kama bayan sun gama sallama da iyayensa. Sun iso inda motar yake kowa ya shiga sai Dije da ke rafka uban ihu , tana ihu Laraba na ihu , " Wayyo jikalle na !!!! ." Haka take ihu , sai da Malam Zailani ya yi da gaske Sannan ya tura Dije cikin mota , Amsa kuwa banda dariya babu abinda yake yi. Bayan an tura ta cikin motar , zata sake buɗe baki tayi ihu Malam Zailani ya ranƙwashe ta a kai , ai kuwa ta nan take ta haɗiye kukan da zata yi. Har sunyi nisa da tafiya sai Dije ta fara gyangyaɗi, cikin ƙufula Malam Zailani yace " kai wannan yarinya bansan yawshe zata yi hankali ba , bansan meyasa Mama ta da ge akan sai an zo da wannan yarinyar ba , Allah ka shiryar min da ita ." Anas driver yace " Haba baban Dije ko ba komai ai zata ɗebe mana kewa sosai, kuma ai Dije zata sauya idan taje can , ka daina damuwa dan Allah." " Wayyo fitsari, Wayyo fitsari!!!!!!!!. Dije ke wannan uban ihun kamar an sanya mata bindiga a kai. Malam Zailani da ya kishingiɗa a firgice ya ɗago a tunin shi ɓarayi ne suka tare su, da mamaki yake kallon Dije da har yanzu take rusa ihu akan zata yi fitsari, Anas driver kuwa tsabar Dije ta firgita shi bai san lokacin da ya sake mota ba, ƙirisa ya ra ge suyi karo da trailer. Cikin takaici Malam Zailani ya kalleta ya aika Mata da wani mugun kallo , take ta haɗiye sauran ihun da take shirin yi. Malam Zailani " Wallahi Khadijah bansan yawshe za kiyi hankali ba , fitsari ne sai kin sanya mun kusa mutuwa a cikin mota , kai wannan hali naki Allah ya shirye ki, zaki sauka kodai sai na wurgaki tukunna." Yanda kasan wacce tayi ƙarya haka take raba ido a cikin mota, bata da niyyar sauka , sai da ta ga da gaske ƙwallo da ita zai yi sai tayi sauri ya sauka, Mero matan Malam Zailani kuwa in da sabo ta saba da rigiman Dije, shi ya sa bata tsorata ba. Da ƙyar Dije tayi tsarki suka koma mota suka cigaba da tafiya , kasancewar sun kusa ƙarasawa minti talatin suka ɗauka a hanya, su na isowa horn ya yi aka wangale mai get ya kutsa motar, Dije kuwa banda raba ido babu abinda take yi har aka yi parking. Malam Zailani " zaki fito kodai na jefoki

Chapter 3 of 6