fara tsagaitawa. Iskace take kaɗawa, sai walƙiyar da ake yi jifa-jifa. Shiru Malam Hassan ya yi, yana bin babbar hanyar da kallo, musamman yadda ya ga babbar hanyar ta shafe da ruwa. Kusan dama haka hanyarsu take, matuƙar damuna ta shigo haka suke fama da matsalar hanya. Wannan dalilin ne ma ya sa duk nisan hanyar masu abin hawa ba sa yarda su shiga, ko fasinja suka ɗauka sai dai su ajiye shi daga gefen titi.
Rakiya ce ta gaji da tsaiwar, don haka ta sauko Fatihu daga bayanta tana ƙare ruwan rigar jikinsa. Ganin yana rawar ɗari ya sa ta yi saurin lulluɓa masa ɗankwalin da ta rufe shi duk da shi ma a jiƙe yake. Jigum-jigum suka yi kowannensu da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, suna cikin haka har Malam Hassan ya lura da ruwan da ke tafiya a hanyar ya fara ja baya. Don haka ya dube ta ya ce.
"Rakiya mu bar wurin haka, mu ƙarasa kada dare ya yi mana kin ga yanzun ma duhu ya yi."
Malam Hasan ne ya fara tsoma ƙafarsa a ruwan, ita ma Rakiya ta biyo bayansa. Sai dai bisa tsautsayi ta ji ƙafarta ta taka wani abu mai kaifi, silar haka ya sa ta gurɗe ta kifa cikin ruwan. Fatihu da ke hannunta ya zame, ganin haka ya sa ta saki ƙara mai ƙarfi. A hargitse Malam Hasan ya shiga lalubensu ita da Fatihu, don ita kanta ji ta yi ruwa yana ƙoƙarin fisgarta. Fatihu kuwa sautin amonsa suka ji sau biyu, daga haka ba su ƙara jin amonsa ba.
"Fatihu" Fatihu! Fatihu!"
Rakiya ta furta a haukace tana rarrafe haɗe da laluben cikin ruwan, haka shi ma Malam Hasan ya shiga lalube yana kiran sunanta da na Fatihu. Riƙo hannun Rakiya ya yi, sai ya ji kamar su ma yana fisgarsu, cikin tashin hankali ya janyo ta suka koma saman dakalin gidan kallon.
"Ka ƙyale ni na ɗauko Fatihu malam, na ji kamar kukansa don Allah ka bar ni kada ruwa ya tafi da shi."
Rakiya ta furta a haukace cike da zallar tashin hankali, a ɗan tsawace Malam Hasan ya ce.
"Me kike yi haka ne Rakiya? Ki dakata na duba shi mana, idan kika biyo ni sai ranki ya ɓaci."
Yana gama faɗar haka ya sauka daga cikin rumfar ya shiga lalube da hannunsa yana kiran sunan Fatihu kasancewar babu haske a hannunsa. Sai da ya zura ƙafarsa a wani wuri, ya ji ruwa yana bin hanyar da rami a wurin. Wanda hakan ne ya sa ya ji gwiwarsa ta yi sanyi, lakar jikinsa ta mutu. Ƙwarin gwiwarsa ya tarwatse, jarumtarsa na neman rikiɗewa zuwa rauni. Cike da zafin nama ya cigaba da laluben a yunwace, jin ruwa yana niyyar jansa zuwa ramin ya sa shi yin baya cike da ɗacin zuciya.
Cikin rumfar ya koma, Rakiya tana ganinsa ta miƙe zumbur ta ce.
"Ina Fatihun?"
Sunkuyar da kai ƙasa Malam Hasan ya yi ya ce. "Mu ɗauki dangana Rakiya, ina ji a jikina mun rasa Fatihu..."
"A'a ba ka duba da kyau ba, ni zan nemo shi da kaina."
Rakiya ta katse shi, sai ta miƙe cikin zafin nama tana ɗingisa ƙafarta saboda har lokacin wani irin zugi take yi mata. Sai dai firgicin da take ciki shi ya hana ta fahimtar yanayin da take ciki.
"Kada ki fita Rakiya, Allah Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ƙaddara mana haka."
Malam Hasan ya furta yana riƙo hannunta, duk yadda ta so fisgewa haka ya riƙe ta tsam a jikinsa. Cikin wani irin yanayi na kewa da shaƙuwa ta fashe da wani irin gunjin kuka, kukan da sauraronsa zai iya raunatar da zuciya har ya saka zubar hawaye. Kuka take tamkar ranta zai fita, dalilin haka ya sa duk dakiya da ƙarfin zuciyar Malam ya fara zubar ƙwalla. Sun ɗauki dogon lokaci a wannan yanayin, har suka ji wasu masallatan suna kiraye-kirayen sallar Isha'i.
Tsirarun mutane ne suka fara wucewa, jin irin kukan da Rakiya take yi har lokacin ya sa wasu magidantan maza guda biyu da za su wuce, suka hasko wurinsu suna tambaya.
"Malam ne yake faruwa? Lafiya?"
Cike da ƙarfin hali Malam Hasan ya ce, "Lafiya ba ƙalau ba."
Duk da hanyar ba ta da kyau, amma ta cikin ragowar ruwan da ya kwanta mutanen suka naɗe ƙafar wando suka ƙarasa, a karo na biyu suka sake wurga masa tambaya musamman yadda suka ga Rakiya tana kuka kamar ranta zai fita.
"Ɗan mu ne tsautsayi ya faɗa masa..."
Malam Hassan ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da su, lokaci ɗaya suka ɗauki salati cikin tashin hankali. Ɗaya daga ciki ya ce, "Wannan ba maganar da za a zauna a yi ta kuka ba ce, mu gayyato jama'a."
Yana gama faɗar haka ya tafi da sauri yana yekuwa da shela, a hankali maza suka fara fitowa. Tsirrarun mata kuma suka dinga leƙowa da fitilu suna haske-haske, sai dai yawanci babu wani abu da suke iya gani duba da nisan da ke tsakaninsu da wurin da su Rakiya suke.
Kafin wani lokaci maza sun taru sosai, wasu suka shiga ba wa Rakiya da Malam Hasan baki, yayin da wasu suka shiga haske-hasken wurare. Amma duk haske-hasken da suka yi na kusan tsawon awa biyu babu Fatihu sai iya ɗankwalin Rakiya ko zanen goyonsa ba a gani ba. Da ƙyar da suɗin goshi aka ba wa Rakiya baki ta daina kukan da take yi, wani mutum daga cikin mutanen ya ce su zo gidansa su kwana kafin zuwa wayewar gari a sake fitowa duba gawar Fatihu.
Ɗaki guda aka ba wa Malam Hasan da Rakiya, sun lura matar gidan mace ce mai karamci ce. Sai da suka yi sallah sannan ta kai musu abinci, fir Malam Hasan ya kasa cin abinci. Amma sai ya shiga rarrashinta yana ba ta baki a kan ta ci, cikin zubar hawaye ta ce.
"Malam kana tsammanin zan iya tauna ƙwayar hatsi a bakina, a ranar da na yi bankwana da Fatihu? Fatihu fa ya tafi ya bar ni shi kenan."
Ta sake fashe wa da kuka, jikin Malam Hasan ya yi sanyi. Cike da lallashi ya ajiye abincin a gefe ya janyo ta jikinsa ya ce.
"Ki yi haƙuri Rakiya, Allahn da ya ba mu Fatihu, Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ɗauke shi a daidai wannan gaɓar. Kada ki yi fushi da lamarin Ubangiji, domin ta yuwu mutuwar Fatihu a wannan gaɓar ta fi zame mana alkairi a rayuwarmu."
Malam Hasan ya jima yana yi mata nasiha, Rakiya ta tsagaita da kukan sai hawayen da ke zuba daga idonta. Kusan kwanan zaune suka yi, sai gab da asuba bacci mai nauyi ya yi awon gaba da Rakiya. Koda aka kira sallar asuba bai tashe ba, sai da suka fita masallaci shi da mai gidan da suka kwana suka gabatar da sallah. Bayan sun dawo ya tashe ta ta yi sannan, a wannan lokacin masallatai suka shiga shelar abin da ya faru. Limanan ya ce idan gari ya yi haske a fita domin duba inda gawar Fatihu take. Bayan da Rakiya ta idar da sallah gari bai ƙarasa haske ba ta ce za ta je neman Fatihu, duk yadda Malam Hasan ya so hana ta fir ta ƙi hanuwa. Don haka mai gidan ya buɗe musu ƙofa suka fita gabaɗaya har shi, tun suna haske cikin caɓalɓalin da guntun ruwan saman ya kwanta har gari ya yi haske 'yan unguwa suka fito suka haɗu ana duba shi. Cikin hukuncin Ubangiji ba a tsinci gawar Fatihu a ko ina ba, sai a gefen wata ƙatuwar kwalbati. Shi ma dalilin da ya sa aka gan shi wani ƙaton dutse ne ya tokare shi, saboda girman kwatar maza uku ne suka shiga suka ɗauko shi fatar jikinsa duk ta kumbure da ruwa. A cikin buhu aka saka shi, jiki a sanyaye cike da karyewar zuciya suka miƙa wa Malam Hasan. Wani abu ya ji ya daki zuciyarsa, a daidai lokacin Rakiya ta ƙarasa ta ce.
"Ya mutu ko Malam?"
Shiru Malam Hasan ya yi, ganin buhun hannunsa yana ɗigar da ruwa ya sa ta yi saurin fisgewa tana duba ciki. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, sai kuma ta saki buhun ta fashe da wani irin gunjin kuka.
Duka mutanen wurin shiru suka yi, saboda kowannensu zuciyarsa babu daɗi duba da irin mummunan yanayin da take ciki. Malam Hasan ya sunkuya ya fara rarrashinta, a daidai wannan lokacin 'yan jaridar gidan Radiyo suka ƙarasa domin rahoto ya je musu. Sai da ɗan jaridar ya gabatar musu da kansa ya kuma jajanta masa abin da ya faru sannan ya ɗora da cewa.
"Malam Hasan muna son mu ji matsayinka, da kuma yadda wannan al'amarin ya kasance."
Sai da Malam Hasan ya yi ta maza sannan ya faɗa masa abin da ya faru, da ya ji tambayoyin za su yi yawa ya dakatar da su. Haka kuma da suka buƙaci jin ta bakin Rakiya ya hana su, don ya lura tambayoyin ba ƙaramin tayar mata da hankali suke ba. Sai suka koma jin ta bakin mutanen unguwa, su ma suka sanar da su gwargwadon abin da suka sani. Jin dalilin da ya sa Malam Hasan ya fito daga gidansa, ya sa mutane suka kawi taro da sisi suka haɗa musu kuɗin mota. Domin sun buƙaci da a yi wa Fatihu sutura a nan ya ce zai ƙarasa garinsu a yi a can.
Taxi suka tara tun daga titin har cikin ƙauyensu da ke garin Ɗanbatta. Sai da ya sallami mai Taxi, sannan suka ja ƙafa jiki a sanyaye suka shiga, Inna ba ƙaramin mamakin ganinsu da farar safiya ta yi ba. Malam Hasan ne ya gaishe ta ta amsa, Rakiya da fuskarta ta kumbura suntum sabod kuka ta ce.
"Ina kwana Inna."
A wulƙance Inna ta amsa sai ta ce, "Ciwon baki kike yi da ba za ki buɗe baki ki mini magana ba? Ina Fatihun yake? Ai kya miƙo mini jikana mu gaisa."
Rakiya ta sunkuyar da kai ƙasa, lokaci ɗaya ta fashe da kuka.
ALHAJI LAWAN
Alhaji Lawan yana zuwa gida cike da murna HajiyaTani ta tare shi, sai da ta kawo masa ruwa ya sha sannan ta ce.
"Alhaji sai kuma na ji ka ce an gama komai."
Alhaji Lawan ya saki murmushi yana miƙa mata takardar ya ce.
"Ga takardu ma sun zo hannu, sai ki adana mini su don kin fi ni iya ajiya."
Hajiya Tani ta zaro takardun ta duba, bayanin fasalin gonakin ne da kusurwoyinsu ta fannin tsayi da faɗi. Sai bayanan masu saya da mai sayarwa, jinjina kai ta yi ta ce.
"Kai amma fa kamar suna da girma sosai."
Alhaji Lawan ya gyaɗa mata kai ya ce, "Girma ma ai ba a magana, so nake sai kayan da muka tura sun sauka mun ga abin alherin da muka samu na ga me ya dace na yi wa wurin. Zan dai gina mana ƙaton gida mu huta da yawon haya, sai ƙatuwar plaza da nake son yi wacce za a zuba shaguna."
Cikin jin daɗi Hajiya Tanj ta ɗaga hannuwa sama ta ce, "Kai Allah mun gode maka, Alhaji Allah Ya kusa yanke mana haya."
Alhaji Lawan ya saki murmushi ya ce.
"In Shaa Allahu kuwa."
Hajiya Tani tana shirin tashi Alhaji Lawan ya ce, "Ni kuwa ina yaran nan? Tun da na shigo ban ji motsinsu ba."
Hajiya Tani ta ɗan gwasale baki ta ce, "Shi dai wancan gantallan ka san ai ba zaman gida yake ba Alhaji. Ita kuma Abida tun da na saka ta wanke-wanke don ba su fita ba, na yi mata faɗa take fushi a ɗaki." Sai kuma ta sake raunatar da murya cike alamun damuwa ta ce.
"Yanzu Alhaji yaran nan ban isa da su ba kenan? Ko don ba ni ce na haife su ba ne oho?"
Ransa Alhaji ya sake ɓaci, cike da damuwa ya ce.
"Don Allah ki daina faɗar haka Tani, yaran nan tamkar 'ya'yanki suke kuma duk hukuncin da ya dace kina iya zartarwa a kansu."
Tani ta rangwaɗa kai gefe ba tare da ta yi magana ba, Alhaji ya sake cewa.
"Kira mini ita, idan ba ta yi aikin gida ba waye zai yi? Yara gabaɗaya so suke su sauya halayensu."
Da sauri Tani ta miƙe ta fita, bayan wani lokaci suka dawo tare da Abida. A rakuɓe can gefe ta zauna musamman da ta lura da mummunan kallon da mahaifinta yake jifanta da shi.
"Ba ki da mutumci ko Abida? Ina ganin kin fi ɗan'uwanki hankali ashe ya fara zuga ki? Me ya sa ba kya son yin aiki yadda ya kamata?"
Alhaji ya furta yana tsare ta da idanu, muryarta tana rawa ta ce.
"Ka yi haƙuri."
Tana son ta ce masa ba ta da lafiya, tana jin tsoron bayan fitarsa kada Tani ta hukuntata. Don haka ta ja bakinta ta yi shiru, tana nan tsugunne ta ji ya ce.
"Kin ci abinci?"
Da sauri ta kalli Tani, sai kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Eh" Sai ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa.
"Idan aka ƙara kawo mini ƙararki wallahi sai na ɓata miki rai..."
Maganarsa ta maƙale sakamakon sallamar da ya ji ta Fauwaz.
"Fauwaz! Kai Fauwaz zo nan."
Ya furta a ɗan fusace, ɗaga labulen Fauwaz ya yi bakinsa ɗauke da sallama sannan ya zauna. Fuskarsa a haɗae take tamau, don a duniya babu matar da ya tsana sama da Tani. Ko kaɗan jininsu bai haɗu ba, musamman da ya fahimci gashin ƙumar da take yi musu.
"Daga ina kake? Kuma tun yaushe ka fita?"
Alhaji Ya furta yana tsare shi da ido.
"Ban daɗe da fita ba Abba..."
"Ƙarya kake Fauwaz! Rabon da na gan ka tun safe, ko ka ɗauka ba na lura da kai." Tani ta furta a ɗan kausashe.
Wani wulaƙantaccan kallo ya wurga mata, ya jima idonsa yana kanta har sai da ta ji ɗar a zuciyarta a kan irin kallon da yake yi mata.
"Fauwaz ka kiyaye ni fa? Kana son ka koyi yawon banza da yara ko? Kai wanne irin yaro ne da kullum sai an kawo mini laifinka?"
Fauwaz da takaici ya cika shi ya ce, "Wai Abba duk abin da aka faɗa maka sai ka dinga hawa kana zama, ka dinga bincike wallahi wani abin ƙarya..."
"Ungo naka, gidanku na ce."
Abba ya yi masa daƙuwa da hannu, Tani tana jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta ce.
"Ka ga irin abin da yaron nan yake yi mini ko Alhaji, yanzu tun yana yi mini a bayan idonka har ta kai yana ƙaryata ni a gabanka."
Alhaji ya sake fusata, rai a ɓace ya ce. "Idan na sake jin makamanciyar maganar nan wallahi sai ranka ya ɓaci Fauwaz, sakarai marara hankali ka ba ta haƙuri."
"Haƙuri?"
Fauwaz ya furta cikin sigar tambaya yana kallon Tani, saboda Fauwaz irin yaran nan ne masu taurin kai. Musamman idan ya kasance a kan gaskiyarsa yake.
"Ko ban isa in saka ka ba ne?"
Abba ya furta murya a sama, Tani ta share guntuwar ƙwallar munafurci da ba ta gama sauka ba ta ce.
"Alhaji yaron da yake ƙaryata ni shi zai ba ni haƙuri? Yanzu da Allah Ya ba ni haihu da ban haifi wanda ya fi shi ba."
Alhaji ya saki ƙwafa sannan ya dubi Fauwaz ya ce, "Idan na sake magana wallahi sai ranka ya ɓaci."
Kamar ba zai motsa bakinsa ba haka Fauwaz ya yi, sai bayan wasu sakanni sannan ya ce.
"Yi haƙuri."
Yadda ya yi maganar da ba su kasa kunne ba babu wanda zai ji, Tani ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta amsa masa.
"Tashi ka ba ni wuri sakarai."
Alhaji ya furta masa, Fauwaz da Abida tare suka tashi suka fita. Suna fitowa Fauwaz ya riƙo hannun Abida ya ce. "Abida na gaji da zaman gidan nan." Muryarta tana rawa ta ce, "Ni ma na gaji yaya, tun da Umma ta mutu muke shan wahala."
Ɗakinsu suka shiga, sai a lokacin ya ji jikinta da zafi zau. A ɗan gigice ya ce, "Ba ki da lafiya ne Abida?" Kai kawai ta gyaɗa masa, ya sake ce mata.
"Kin faɗa wa Abba?"
Ta girgiza kai ta ce. "Idan na faɗa masa Aunty dukana za ta yi, ɗazu ma ta dake ni saboda da safe na faɗa masa littafin makarantata ya cika."
Fauwaz ya furzar da iska mai zafi cike da takaici ya ce.
"Abida matar nan ba ta sonmu, ba ta son Abba kina ga ta saka shi ya sayar da filinmu."
Muryarsa ta yi rauni, idanunsa suka ciko da ƙwalla musamman da ya tuna fafutukar da mahaifiyarsu ta yi ta sayi filin kafin ta rasu.
Cike da yarinta Abida ta ce, "Allah zai saka mana, ai ita ma idan ta mutu sai mun sa Abba ya sayar da nata."
Ganin yadda jikinta ya ƙara ɗaukar zafi, ya sa Fauwaz jiƙa tsumma yana saka mata a jiki, saboda tun tasowarsa haka ya ga mahaifiyarsu tana yi idan suna zazzaɓi mai zafi.
Alhaji ya jima yana ba wa Tani haƙuri sannan ta sauka, daga haka ya tashi ya fice daga gidan. Tana ganin ya fita ta ciro waya ta latsa wata lamba, ba a jima ta ɗauka tana ƙasa da murya.
"Ina fatan komai ya tafi daidai?"
Daga can ɓangaren aka ba ta amsa da cewar. "Kada wani abu ya ɗaga miki hankali, kuɗi ga su a hannuna tun da ciniki ya riga da ya faɗa. Ragowar maganar idan mun haɗu ma tattauna."
Sallama suka yi, Tani ta saki murmushin farinciki mai cike da tarin manufa sannan ta ce.
"Alhaji Lawan kenan! Idan har ni Tani ina raye, daga yau ka fara irga asara ba riba ba."
Sai ta sake sakin murmushi ta koma tana ƙare wa takardun gidan da ya damƙa mata ajiya kallo mai cike da tarin manufa.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[11/05, 16:08] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA UKU
Fauwaz ya jima yana saka wa Abida ruwa a jikinta, har sai da ya ji zafin ya ragu sannan ya matse rigar ya shanya. Bacci ne ya ɗauke ta, don haka ya fita daga ɗakin yana tunanin yadda za a yi ya saya mata magani. Don har zuciya ta ayyana masa ya je ya samu mahaifinsu ya faɗa masa, amma da ya tuna irin makircin da Tani take ƙulla musu ba su cika kwashewa ta daɗi da shi ba, sai kawai ya haƙura. Ya yanke shawarar fita tsintar gwangwanaye kamar yadda ya ga abokinsa Musa yana yi. Kusan tun gabanin sallar Magriba da ya fita, ba shi ya dawo gida ba sai kusan tara saura na dare. Zuciyarsa a cunkushe take, sakamakon ya sha yawo sosai ya tsinci gwangwanaye da jarkoki, har ya sayar amma bai samu mai chemist ɗin layinsu ba. Sakamakon Peter mai chemist ya je garinsu kirsimeti, kuma shi kaɗai ne mai kemis ɗin da ke zagayen unguwarsu. Tani tana ɗaki ba ta ji shigarsa ba, Fauwaz yana shiga ɗakinsu ya samu Abida a zaune. Sai dai daɗin da ya ji da zazzaɓin jikinta ya sauka, tana ganinsa ta saki murmushi sai shi ma ya mayar mata da martanin murmushin.
"Ya Fauwaz, idan na girma zan gina mana gida mu tafi mu bar su Abba a nan."
Abida ta furta a hankali don kada Tani ta ji, zama ya yi a gefenta ya ce.
"Ai ni ne babba, ni zan fara gina mana gida mu tafi, kuma har sababbin kayan wasa zan saya miki."
Jin haka ya sa Abida ta saki murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana.
"Fauwaz! Don Allah, koda wani yanayi da zai gifta wanda zai sauya maka rayuwarka, ka kula da ƙanwarka. Ku biyu Allah Ya azurta ni da su, ku haɗa kanku, ka ja ƙanwarka ka ji Fauwaz."
Kalaman mahaifiyarsu ne ya dawo cikin kwanyarsa ana gobe za ta rasu, idanunsa suka ciko da ƙwalla. Gudun kada Abida ta fahimci damuwarsa ya sa shi saurin kawar da kansa. Suna nan zaune Tani ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce.
"Kai Fauwaz! Fito ka ɗebo mana ruwa."
Shiru ya yi kamar bai ji ba, saboda gabaɗaya ya ɗora rushewar faruncikinsu a kanta. A karo na biyu ta sake yi masa magana, kai tsaye ya ce.
"Yanzu dare ya yi."
Ai kuwa kamar wacca ya kwara wa ruwan zafi a hassale ta ce.
"To tun da ba za ka ɗebo ba, sai na bari idan ubanka ya dawo ya ɗebo mana."
Wani irin ɗaci ya ji a ransa, cike da damuwa ya ce.
"Ki daina zagin mahaifina."
Za ta yi magana ta ji motsin shigowar Alhaji, yana ƙarasawa ya ce. "Me yake faruwa hayaniyar me nake ji?"
Tani tana jin haka ta yi zaraf ta ce, "Wai don na ce Fauwaz ya ɗebo mana ruwa yake yi mini rashin mutumci. Ni dai ina jin Alhaji zan bari ka dinga yi masa magana da kanka, don ina gudun watarana na yi masa magana ya zage ni." Fauwaz da zuwansa bakin ƙofar kenan, ya bi Tani da kallon mamakin sharrin da ta yi masa.
Tass! Alhaji ya ɗauke fuskar Fauwaz da mari har sai da ya bugu da jikin bango, da sauri Abida da ke gefe ta riƙe shi a tsorace da hukuncin da Abba ya zartar masa. Abba ya nuna shi da yatsa ya ce.
"Daga yau idan aka sake yi maka magana ka musa sai ranka ya yi mummunan ɓaci. Ka yi maza ka wuce ka ɗauki bokiti ko na tattakaka, sakarai marar mutumci."
Goge hawayensa Fauwaz ya yi, Abida ta ja hannunsa ta yi tsuru-tsuru saboda tsoro. Wani irin kallo suke yi wa mahaifinsu tamkar sun ga sabuwar hallita, domin gabaɗaya ya sauya kamar ba mahaifinsu mai sonsu da nuna musu kulawa ba. Fauwaz yana fita Tani da Alhaji suka rufa masa baya har lokacin bai daina faɗa ba. Fauwaz ba shi ya gama ɗiban ruwan ba sai kusan sha ɗaya saura don Tani har ta kwanta, a lokacin ne ya shiga kicin zai ɗebi abinci ya ci. Sai dai yanq zuwa ya ga sai burbuɗin shinkafa da ƙanzonta. Yadda cikinsa yake ƙugi ne ya kawar da ɓacin ransa, hawayen idonsa ya share sannan ya saka hannu ya kankaro ƙanzon ya zuba da mai ya zauna ya ci. Sai da ya ci ya wanke hannu sannan ya shiga ɗakinsu, a takure a can ƙarshen bango ya hango Abida a duƙunƙune tana rawar ɗari. Da sauri ya ƙarasa wurinta ya ɗago ta yana faɗin.
"Abida! Sannu zazzaɓin ne?"
Jikinta yana rawa ta gyaɗa masa kai, da sauri ya ƙarasa ya ɗauki rigar da ya shanya ya sake jiƙa ta ya shiga saka mata.
"Sannu kin ji Abida, ɗazu na samo kuɗi don na sayo miki magani amma Peter ba ya nan."
Fauwaz ya furta muryarsa tana rawa, ba ta iya amsa masa ba saboda yadda take jin jiki. Ya jima a haka har ya samu jikin nata ya rage zafi, yana nan zaune rungume da Abida ya ji bacci ya ɗauke ta. Ido ya zuba mata yana kuka, yana tuna rayuwarsu a lokacin da mahaifiyarsu tana raye. Yana cikin wannan yanayin har bacci ya yi awon gaba da shi. Wani irin kakari yake ji sama-sama a cikin baccinsa, jijjigar da jikinta yake yi ne ya farkar da shi daga wahalallan baccin da yake yi. Ɗakin baƙiƙƙirin yake, sakamakon fitilar da ke ɗakin kalanzir ɗin cikinta ya ƙare. Kiran sunanta ya shiga yi a hargitse yana jijjiga ta, sai ya ji jikinta zafi zau kamar wuta. A hargitse ya fita daga ɗakin kai tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Tani, daga bakin ƙofa ya tsaya zai fara kiran mahaifinsu. Domin tarbiyyar da mahaifiyarsu ta yi musu kenan, babu wanda yake