Share this page
8 / 9
tabbatar mata da take shi ta yi da ƙafarta. "Wayyo Allahna, na shiga ukuna." Zuwaira ta ƙwalla ihu tana ɗora hannu a ka, saboda zallar tashin hankali. A hargitse Malam Hasan ya shiga ɗakin da gudu, cikin damuwa ya shiga jera mata tambaya. "Lafiya me ya faru?" Rasa bakin magana ta yi, don ba ta san me za ta ce masa ba, cikin inda-inda ta ce. "Dama zame wa na yi na faɗi, sai nake jin ƙafata kamar ta gurɗe." Kallon tsaf ya yi mata, don duk wanda ya ƙare mata kallo zai ga ba ta yi irin zaman da za a ce mutum ya faɗi ba. Guntun tsaki Malam Hasan ya saki ya ce. "Amma kamar ba musulma ba Zuwaira, ai sunan Allah ya kamata ki kira ba ihu ba." Ita dai Zuwaira shiru ta yi tana kukan zuci, don hatta jikibta rawa yake saboda tashin hankali. "Ina ne wurin na yi miki addu'a." Malam Hasan ya tambaye ta yana zama a gefenta, ƙafar da ta taka maganin bokan ta nuna masa ta ce. "Duk ƙafar take yi mini ciwo, ka tofe mini ita." Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi, sannan ya shiga karanta mata addu'o'in yana tofa mata. "Allah Ya sawaƙe, ki dinga kula." Ya furta mata cikin tattausan lafazi ganin duk ta yi laushi ta fita hayyacinta, wani tunani Zuwaira ta yi. Har ya je bakin ƙofa ta ce, "Ko na zo na je gidan Malam Bala mai kamu." Malam Hasan ya juyo ya ce, "Ke da kike fama ina za ki iya fita, ba gara na kira miki shi ba ya zo har gida. Amma ƙafar taki ta yi tsamari haka ne?" Zuwaira dama ta tambaye shi ne don ta samu ta fita daga gidan, ko ta je gidan bokan da ke can gaba da ƙauyensu ta sanar da shi ɗanyan aikin da ta aikata. Amma jin amsar Malam Hasan ya sa ta ce. "Ƙyale dai mu gani zuwa gobe, idan ban ji daɗin jikina ba ka kira shi." Malam Hasan bai kawo komai a ransa ba, ya sake yi mata sannu sannan ya fita. Bayan fitarsa wani sabon kukan ta dasa marar sauti, abin duniya ya haɗe mata don har ji take kamar rayuwarta ta zo ƙarshe. Tun da ta ga an yi sallar magriba zuciyarta ta cika da tsoro, da yake Malam Hasan bai sake fita ba har sai da ya lura da firgicin da take ciki. "Zuwaira wai akwai abin da yake damunki ne?" A firgice ta ɗago ta girgiza masa kai, ana kiran sallar isha'i Malam Hasan ya miƙe zai tafi masallaci da sauri ta riƙo shi ta ce. "Don Allah ka yi a gida." Da mamaki ya dube ta ya ce, "Sallar zan yi a gida Zuwaira? Wai ko wani abu ne yake faruwa ban sani ba na ga duk kin firgice." A wannan karon gyaɗa masa kai ta yi ta ce, "Eh wallahi tsoro nake ji, don Allah kada ka fita." Komawa ya yi ya zauna a gefen gado ya ce, "Ikon Allah, to shi kenan bari na ɗauro alwala sai mu yi jam'in tare." Da wannan maganar Zuwaira ta gamsu, Malam Hasan ya ajiye hularsa a kan gadon ya fita ɗauro alwala. Malam Hasan yana fita kamar wacce aka dasa wa allurar da ke saka bacci, lokaci ɗaya Zuwaira ta ji idanunta suna lumshewa. Duk yadda ta so dakatar da baccin ya gagare ta, nan take ta ɓingire nannuyan bacci ya yi awon gaba da ita. Koda Malam Hasan ya shigo murmushi ya yi ya matsa gabanta, ganin bacci take hankali kwance har da munshari sai ya ƙi tashinta. Ya ce zuwa jimawa kaɗan ya tashe ta, don tun da ta samu ciki idan ta fara bacci da an tashe ta da ciwon kai take tashi. Da yake shi ma ya gaji, kwanciya ya yi da niyyar kishingiɗa sai baccin ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da asuba da ya ji motsin Zuwaira ta tashi. Da wani irin ciwon jiki Zuwaira ta wayi gari wanda ko kaɗan ba ta san dalilinsa ba, sai abin ya sake haɗe mata ga damuwar asirin boka Lado da ya faɗa kanta ga kuma ciwon jikin da ya addabe ta. Kuma ta gagara sanar da Inna domin ta san daga lokacin da Inna ta san ta fara zuwa gidan boka daga nan sun rana hanya. Saboda duk miyagun halin Inna ba ta yarda da bin malamai ko 'yan tsubbu ba. Hasali ma ko lura ta yi kana biye-biyen bokaye, daga lokacin ta kafa maka ƙahon tsana kenan duk ƙarfin alaƙar da ke tsakaninku. Ga shi Malam Hasan ya ƙi barin ta fita ko nan da can, don har ƙaryar ciwon ciki ta yi masa ya ce zai raka ta asibiti saboda faɗuwar da ta yi. Da ta ji haka har tsoro ta ji, a ranta ta raya ko dai ya fahimci halin da take ciki. Zuwaira haka ta shafe sama da kwana goma cikin wannan yanayin, duk bayan isha'i haka nannauyan bacci yake ɗaukarta. Malam Hasan ko kaɗan bai kawo komai a ransa ba, domin a tsammaninsa ciki ne yake saka ta yawan baccin da take yi. Musammam da ya tuna marigayya mahaifiyar Fatihu a lokacin da ta yi goyon cikinsa, da yake lafiya ƙalau suka zauna da Rakiya hatta girki wani lokacin ita take yi mata ranar girkinta, musamman idan ta ga tana bacci lokacin ɗora abinci ya wuce. A kwana na sha ɗaya ne Zuwaira ta tambaye shi zuwa kitso, bai hana ta ba don haka ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farinciki. Ko wanka ba ta yi ba ta zura hijabi ta fita, kai tsaye ƙauyen Marke ta nufa, gudu-gudu sauri-sauri har ta ƙarasa bukkar boka Lado. A wannan ranar mata uku ta samu ita ce cikon ta huɗu, saboda yadda ta ƙagu har ji ta yi kamar ta shiga ba tare da an zo kanta ba. Da layi ya zo kanta tana shiga ko kyakkyawar gaisuwa ba ta yi masa ba, har ta buɗe baki za ta yi magana ya ɗaga mata hannu. "Ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya ko?" Tun bai gama magana ba Tani ta hau gyaɗa kai, boka Lado ya cigaba da cewa. "Ki gode mini, ki kuma yi imani ni ne mai taimakon lamuranki da ba ki yi sati biyu cikin wannan yanayin ba." Jin ta yi shiru sai ya wara mata daƙwa-daƙwan idanunsa da suke jajir ya ce. "Ko ba ki yi imani da ni ba?" "Na yi imani da kai boka Lado, shi ya sa ma na dawo wurinka." Zuwaira ta furta murya tana rawa, boka Lado ya saki wata shashashar dariya wacce ta sake munana faffaɗar fuskarsa ya ce. "Tun da kika yi imani da ni kin gama taɓewa duniya da lahira, ni kuma dama da taɓaɓɓu nake mu'amala. Tashi ki saka ƙafarki a cikin ruwan can, idan kika yi haka komai ya warware daga jikinki. Da ace kin wuce makonni biyu, da za ki dawamma ne a haka." Da sauri Zuwaira ta miƙe ta isa gaban wani sihirtaccan ruwansa da ke cikin wata ƙatuwar jar ƙwarya. Ƙafar hagu ya ce ta fara sakawa, sai da ta tsame ta ta saka ta dama sannan ta koma ta zauna. "Me kike so a yi wa kishiyarki? Ko kin janye buƙatarki?" Ya wurga mata tambaya yana tsare ta da ido, furzar da iska mai zafi ta yi ta ce. "Boka ina son a hana ta nutsuwa, a raba ta da mijinmu. Sannan hatta sana'ar da take yi a dakusar da ita, sai dai kuma don Allah..." "Nan ya yi miki kama da wurin ambaton Allah?" Boka Lado ya katse ta a tsawace, sannan ya ɗora da cewa. "Idan kika sake ambaton sunan Allah sai na hallaka ki." Jiki yana rawa Zuwaira ta shiga gyaɗa kai ta ce, "Tuba nake, dama cewa zan yi kada ayi mata wanda za a ba ni ace na saka mata. Ina tsoron kada na sake samun matsala." Boka Lado bai tanka mata ba, ya ɗauko wani ruwa mai zarni a cikin wani ƙoƙon kai. Sai ya ɗauko wata yar tsana mai ɗan girma, wacce aka rubuce jikinta da jini. Ta ƙasan 'yar tsanar ya ɗauko ƙusa ya ɓula, sannan ya ɗura fitsarin a cikin 'yar tsanar. Abin da ya fi ba wa Zuwaira mamaki, yadda duk yawan fitsarin aka ɗurewa 'yar tsanar ba tare da ko kaɗan ya zubo ƙasa ba. Miƙa mata 'yar tsanar ya yi ya ce ta duba, duk iya dube-duben da ta yi ba ta ga fitsarin ba. Tana shirin yin magana ya katse ta. "Wannan da kike gani, tsafataccan fitsarin alade ne. Wannan 'yar tsanar da kika gani tana mazaunin kishiyarki ne, fitsarin da na ɗura mata yoyonsa za ta fara. Amma ina son ki sani, kishiyarki tana da ƙoƙarin riƙo da addini, sai dai kin san inda ta ba mu damar da za mu aiwatar da aikinmu a ƙwanciyar hankali?" Da sauri Zuwaira ta girgiza masa kai, Boka Lado ya cigaba da cewa. "Tana da ɗabi'ar zama kai babu ɗankwali, ba iya da rana ba har da daddare tana iya zama babu ɗankwali a kanta. Kuma idan ta zo kwanciya bacci ba ta damu da addu'a ba, mu kuma duk wani asiri mun fi gudanar da shi da dare. Ta wannan hanyar za mu yi amfani mu cimma manufarmu." Cike da ƙeta Zuwaira ta saki dariyar mugunta tana yi masa jinjina da hannu ta ce, "Aikinka yana kyau boka Lado." Wata matacciyar jaɓa ya ɗauko a cikin leda har ta fara wari, ya ɗauko 'yar tsanar ya saka wani zaren guru ya ɗaure sannan ya miƙa wa Zuwaira. A ɗan tsorace ta ja da baya, kallon da ya yi mata ya sa ta yi saurin miƙa hannu ta karɓa. Ya nuna wata tasa da ke kan wuta tana zaɓalɓala da jini a ciki ya ce ta saka tana ambatar sunan Rakiya. Haka Zuwaira ta matsa gaban wutar ta jefa su tana ambatar sunan kamar yadda ya ce ta yi, tana jefawa ya ya saki dariya ya ce. "Kin gama da wannan babin." Cike da farinciki Zuwaira ta kawo kuɗi ta ba shi, sannan ta yi masa godiya. Har ta miƙe za ta tafi ya ce. "A yau da daddare za mu gudanar da ƙarashen aikin a kanta, zuwa wayewar gari za ki ga abin da zai faru." "Godiya nake Boka Lado, haƙiƙa na yarda da hatsabibancinka." Daga haka Zuwaira ta fita zuciyarta fes ta wuce gida, kamar kuwa yadda Boka Lado ya ankarar da ita tana shiga ta samu Rakiya a zaune tana tsintar wake kanta babu ɗankwali. Zuwaira ta saki murmushin mugunta mai sauti har sai da Rakiya ta ɗago ta kalle ta. ABBAN FAUWAZ Mamaki kwance a saman fuskar Abba ya ce, "Tani kin san me kike faɗa kuwa?" Tani ta dube shi ido cikin ido ta ce. "Ƙwarai kuwa na sani, takardar saki na ce ka rubuta mini don ba zan iya cigaba da zama da matsiyaci ba." Matsawa gabanta ya yi, ya kamo hannunta ya shafa ya ce. "Tani kina ji na?" Da zafin nama ta fisge hannunta, cike da rashin mutumci ta ce. "Malam ka kama kanka! Ko kuma takaucin ya fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ne?" A fusace Abba ya ce, "Wai Tani kin san me kike faɗa? Ni mijinki kike faɗa wa haka?" "Wane ne mijin? Mijin irinka mijin banza da wofi, ƙasƙantacce matsiyaci..." Tass! Abba ya sakar mata mari a fuska, da sauri Tani ta riƙe kumatunta tana bin sa da kallo. A madadin ta ji zafin abin da ya yi mata sai ta saki murmushi ta ce. "Tun kafin yau na shirya jin marinka a fuskata, don kaine a makare. Abin da ba ka sani ba, tun ranar da na shigo gidanka nake shiri da tanadin abubuwa a kanka. Ruwanka ne ka nemi mafita, ruwanka ne ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa." Daga haka Tani ta koma cikin ɗaki ta haye gado cike da rashin mutumci. Saboda mamakin kalaman Tani da ƙyar Abba ya iya jan ƙafarsa ya fita daga gidan, sai dai har ya isa kotun jikinsa a mace yake ga tarun damuwa da tashin hankali da suka zame masa abokan shawara. A wannan ranar da suka fara zaman shari'a aka gabatarwa da Abba tuhumar da ake ƙararsa a kanta, nan take ya amince da ƙunshin tuhumar. Bayan tattaunawa alƙalin ya cewa Abba da ya yi ƙoƙarin nema wa Alhah Dikko haƙƙinsa kafin wani zaman. Da haka zaman kotun ya watse, daga kotun Abba ya wuce gidan 'yar uwarsa Goggo. Kallo ɗaya ta yi masa ta ga duk ya sake fita hayyacinsa, sai da suka gaisa sannan ya sanar mata da abin da ya faru tsakaninsa da Tani. Murmushin takaici ta saki ta ce. "Yanzu ka ga maganar yaron nan tana hanya? Ka ga abin da Fauwaz yake son ankarar da kai, ka rufe ido kake ƙyamarsa." Shiru Abba ya yi, sai zuwa can ya ɗago cikin damuwa ya ce. "Wallahi tallahi ban taɓa tsammanin Tani za ta yi mini haka ba, Tani ta shammace ni ta ci amanata." Ya ƙarasa maganar kamar zai zubar da ƙwalla, Goggo ta jima tana ba shi baki sannan ya yi mata sallama. Da ɗan canjin da Goggo ta ba shi, ya tsaya ya sayi naman miya da zummar idan ya kai gida ko zai shawo kan Tani. Sai dai yana zuwa ya buɗe ƙofar ya ga gidan wayam, a haukace ya dinga duba ɗakunan yana kiran sunan Tani sai dai gabaɗaya kayan sawarta ya ga babu ta kwashe su. Daga kan Tv ya hangi wata farar takarda guda biyu, jikinsa yana rawa ya saka hannu ya ɗauka ya fara karantawa. _Har yanzu na san zuciyarka tana cike da wasu-wasi a kan kalaman da na furta maka, ina son ka sani. Ni Tani dama ina tare da kai ne domin biyan buƙatar kaina, a yanzu kuma na cimma manufa ta dole na wurgar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda. Ina tunasar da kai da ka sani, Tanin da ka sani a shekarun baya, ita ce dai wacce ka yi rayuwar aure da ita a yanzu. Girma da shekaru ba su isa su sauya Tani ba, idan Tani ta ce sai ta yi duk daren daɗewa sai ta zartar da shi. Zan sake sanar da kai, wallahi tallahi ko kana so ko ba ka so dole ka sake ni. Ka saurari haɗuwar da za mu yi a gaba._ Abba yana gama maganar ya ji gumi ya shiga keto masa, ɗayar takardar da ke gefe ya ɗauka sai dai tun kafin ya buɗe ta ya ga a ido ta fi wacce ya gama karantawa tsufa. Yana buɗe ta bayan ya ƙura mata ido ya ji gabansa ya yi mummunan bugawa, zanen rubutun da aka yi da baƙin biron da ke jikin takardar ya tuna masa da tarun al'amauran da suka faru a shekaru goma sha bakwai da suka wuce. Da sauri ya wurgar da takardar, sai ya ji tamkar ya riƙe ruwan dalma a hannunsa. Ya kifa kansa a sama cinyarsa yana faɗin. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Shiru ya yi yana jin zuciyarsa tana yi masa raɗaɗi, raɗaɗin da ya gagara tantance a mahallin da zai ajiye shi. Musammam da ya tuna shukar tsiyar da noma wa Tani a shekarun baya. Gobe za mu gama free pages ɗinmu🥳 jama'a yanzu ne za a fara naɗa GAMMON RAMA, kowa yasan za a sha tsami a cikinsa. Akwai tarin ƙalubale da darussan hannunka mai sanda, kada ku yi sanya domin yanzu ne za a fara wasan.👌🏻 500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [20/05, 16:30] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA GOMA Abba ya jima a zaune cikin rashin daɗin yanayi, jikinsa a sanyaye ya miƙe ya shiga ɗakin su Fauwaz. Tsaye ya yi yana ƙarewa ɗakin kallo, abubuwa da dama suka shiga dawowa cikin kwanyarsa ciki har da mutuwar Abida. Sai a lokacin yake tuna irin kalaman da Tani take yi masa a kan 'ya'yansa, da irin shakulatan ɓangaro da ya yi a game da amanar da mahaifiyarsu ta ba shi kafin ta bar duniya. "Kaico Abidata, Allah Ya sabunta rahama a gare ki da mahaifiyarki." Ya furta a sanyaye, sai kuma Fauwaz ya faɗo masa, cikin nadama da danasani ya ce. "Yanzu ɗan cikina ne a almajiranci? Shin me ya faru da ni a wancan lokacin da na gagara gane gaskiyar da yaron nan yake son nusar da ni?" Amsar da ya gagara ba wa kansa kenan, shi kaɗai ya shiga surutan nadama a kan cuzgunawa su Fauwaz da suka dinga yi a baya shi da Tani. "Ya zama wajibi na je na dawo da shi gabana." Ya furta a sanyaye, sai kuma wani tunani ya faɗo masa don haka y furzar da iska mai zafi ya ce. "A ina zan samu kuɗin mota?" Saboda a wannan a gaɓar da yake hatta naira ɗari ta kansa wuya take yi masa, ganin rubuta wasiƙar jakin da yake yi ba za ta kai shi ba. Sai ya miƙe ya fito, ya shiga ɗakin kwanansu. A nan ma ɗakin ya shiga bi da kallo ganin Tani ta yashe komai nata, hularsa da ke yashe a ƙasa ya ɗauka ya saka. Tunanin zuwa gidan kawun Tani ne ya faɗo masa, don haka cike da ƙwarin gwiwa ya rufe gidan ya nufi shagon Nalami da ke bayan gidansa. Nalami yana ganinsa ya haɗe rai, Abba ya saki murmushi don ya san dalilinsa na sauya fuska. 'Tabbas rayuwa darasi ce, sautari idan kana da shi mutane kowa ƙaunarka yake. Amma da zarar wata jarrabawa ta afka maka a nan ne za ka fahimci wanda zai mu'amalance ka tsakani da Allah.' Abba ya raya a ransa, sannan ya yi sallama a shagon. A ɗan daƙile Nalami ya ce. "Wa alaikassalam." Abba ya ɗan yi jim sannan ya ce. "Don Allah Nalami kada a gaji da ni, yanzu ma aron ɗari biyu za ka ba ni, idan aka haɗa da waɗancan sun kama dubu ɗaya." Kamar Nalami yana jira ya yi zaraf ya ce, "A gaskiya Alhaji ba za ta samu ba, waɗancan ma yanzu nake shirin aika maka kuma sai ga ka." Nalami ya ƙarasa kalamansa yana ƙara tsuke fuska. "Alhaji kana da canjin ɗari takwas fa." "Alhaji ka biyo ni ɗari biyar jiya." "Kullum dai Alhaji ba ka gajiya, to an gode Allah amfana." "Gaskiya ne Alhaji, ni fa duk unguwar nan na fi jin daɗin cinikinka, saboda ko babu komai mutum zai ƙaru da 'yan canji." Abba ya tuna ire-iren kalaman Nalami a baya, a lokacin da kuɗi yake gara masa idan ya zo sayayya wurinsa. Don a wancan lokacin canji indai ba mai yawa sosai ba ne bar wa masu shago yake, musamman Nalami da ya fi kusa da gidansa. Amma shi ne a kan dubu ɗaya Nalami yake ɗaure wa fuska har yana nuna masa iyakarsa. 'Marar shi ba ya zuciya.' Abba ya sake raya wa a ransa, don haka ya ce. "Don Allah ka taimaka mini Nalami, zan yi ƙoƙari na haɗa maka kuɗin cikin ƙanƙanin lokaci." "A gaskiya wannan ne na ƙarshe indai ba ka kawo wani abin ba na gama ba ka rancen kuɗi." Nalami ya furta sannan ya zaro ɗari biyu ya miƙa masa a wulaƙance, idanun Abba ne suka ciko da ƙwalla. Ganin a kan ɗari biyu ana ƙoƙarin cin zarafinsa, ɗari biyun da yake ganin ba komai ba ce a wurinsa. Karɓa ya yi ya masa godiya ya tafi, a wancan lokacin da yake kuɗi suna da daraja. Ɗan achaɓa ya tara ya nufi unguwar Sheka gidan Kawun Tani. A lokacin da ya ƙarasa Dattijon yana zaune a kan bencinsa ƙofar gida, cikin girmamawa Abba ya russuna ya ce. "Barka da yamma Baba." Faɗaɗa fara'arsa Dattijon ya yi ya ce, "Barka dai, au Lawan ne da yammacin nan?" Abba ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ni ne Baba, ya mutanen gidan?" Baba ya nuna masa tabarmar da ke gefen bencin ya ce, "Ga wuri ka zauna mana, ya su Tani?" Abba har ya miƙe domin ya je ya zauna, sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi da tambayar da Baba ya yi masa. A saɓule ya zauna ya yi shiru ya faɗa tunanin wurin da Tani ta tafi, har sau biyu Baba ya yi masa magana bai ji ba. Sai da ya taɓa shi bayan Abba ya amsa Baba ya ce, "Lawan ko wani abu ne ya haɗa ka da Tani? Ina fatan dai lafiya ko?" Abba ya shafo gemunsa ya ce, "Eh to gaskiya ba lafiya ba Baba..." Duk abin da ya faru Abba ya kwashe ya ba wa Baba labari, sannan ya ɗora da cewa. "Shi ya sa na ce bari na zo nan, don na san duk garin nan babu wanda take da shi sama da kai. Da har zan je gidan abokin mahaifinta, sai na ga nan ne ya dace na zo tun da ka fi kusanci da ita." Gyaran murya Baba ya yi ya ce. "Eh kam tabbas haka ne, ni na fi kusanci da ita a kan Alhaji Harisu, tun da a lokacin da muka yi zaman Shagamu da mahaifinta Alhaji Harisu bai zo garin ba sai dab da mahaifinta zai rasu. Ni da shi bacci ne yake raba mu amininsa ne ƙud da ƙud." Da ɗam rashin fahimta Abba ya ce, "Baba kana nufin kai ba yayan mahaifinta ba ne?" "Yayan mahaifinta? Ita Tanin ce ta ce ni ne yayan mahaifinta?" Baba ya furta da sauri, Abba ya gyaɗa kai ya ce. "Eh haka ta ce mini bayan haɗuwarmu, shi kuma Alhaji Harisu abokin mahaifinta." "Tirƙashi! Lallai yarinyar nan makira ce, ashe haka ta iya yaudara? To wallahi yaro babu abin da na haɗa na jini da Tani, ni ban san ma yadda aka yi ta lalubo gidana ba. Ta zo da kukanta wai aurenta ya mutu ba ta da wurin zama, ganin irin zaman mutumcin da muka yi da mahaifinta ya sa na ba ta ɗaki. A lokacin har zance ta tafi dangin mahaifinta ko mahaifiyarta, to sai na ga kamar ba za ta ji daɗi ba tun da ta san da can ɗin ta taho wurina." Baba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, sannan ya ɗora da cewa. "Ni ban san lokacin da Tani ta lalace haka ba, kodayake tun haɗuwarta da wani ɗan iskan yaro a shekarun baya duk ya lalatata. Allah dai ya kwashe masa albarka, duk ya gurɓata tunanin yarinyar nan." Shi dai Abba zuru ya yi kamar an jiƙa ɓera a buta, haka kawai jikinsa yake ba shi kamar shi ake kwashe wa albarka yana zaune. "To yanzu Baba a ina kake ganin zan iya ganinta?" Abba ya tambaye shi cike da damuwa, cikin sauri Baba ya wara hannuwa ya ce. "Allah masani Lawan, don wallahi ba na ce ba. Ka leƙa gidan Alhaji Harisu ƙila ko can ta nufa, ni kuwa dama ta gama zaman gidana don ba za ta haɗa mini masifa da kafirar ƙaryarta ina zaune ƙalau ba." A sanyaye Abba ya miƙe har zai saka takalminsa ya ɗan sunkuyo ya ce. "Amma Baba ya sunan yaron da ka ce ya cuce ta ya gurɓata mata tunani..." "Kai da ka zo neman matarka ina ruwanka da wani ƙato?" Baba ya katse shi a fusace sannan ya ɗora da cewa, "Wai me ya sa wasu mazan sun cika kishin masifa ne? Idan na faɗa maka sunan me za ka yi da shi bayan wannan zancan da nake yi maka ya doshi shekara goma sha biyar zuwa sama." Da sauri Abba ya zura takalminsa ya yi wa Baba sallama,

Chapter 8 of 9