Share this page
6 / 9
daga yau za ku cigaba da raba kwana bibbiyun da kuke yi a baya. Idan kuma hakan bai yi miki ba sai na sauwaƙe miki, ƙarƙari na ɗauki matata na bar garin ba tare da kowa ya sake gani na ba." Yadda ta ga ransa ya ɓaci jikinsa har yana rawa ya sa ta shiga hankalinta, don ta san shi sarai yana da matuƙar haƙuri amma idan ransa ya ɓaci ba ya ji ba ya gani. Jiki a mace ta koma gefen gado ta kwanta, Malam Hasan ya miƙe ya zira doguwar rigarsa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce ɗakin Rakiya. Tana gani ta gefen labule ya shiga ɗakin Rakiya, amma yadda take ƙaunar Malam Hasan ya sa ta ji ba ta shirya rabuwa da shi ba. Don haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saboda wani irin zafin kishinsa da take ji. Tun daga wannan ranar Malam Hasan ya raba musu kwana, kuma koda Inna ta ga haka da ta fara faɗa Zuwaira da kanta ta shiga kare Malam Hasan da cewar ita ce su cigaba da kwanansu kamar yadda suke yi saboda ta samu lafiya. Hakan ya sa Rakiya ta samu 'yancin kwana da miji, sai dai wasu ƙalaubalen da ba a rasa ba waɗanda ta yi sabo da su har suka zamwemata jiki. An yi haka da wata biyu Zuwaira ta samu ciki, tun bayan da ta yi ɓatan wata ta fara tsiro da rashin lafiya duk da cikin mai sauƙi ta same shi. Inna tana ganin haka ta tasa ta a gaba suka tafi asibiti, sai ga shi gwaji na farko aka tabbatar da tana ɗauke da cikin wata ɗaya da sati ɗaya. Tun a asibitin Inna ta kira Malam Hasan ta sanar da shi, bayan da suka je gida a ranar wuni ta yi tana habaici da yarda wa Rakiya maganganu. Malam Hasan abu biyu ne ya haɗe masa, na farko yana farinciki da Allah ya sake azurta shi da rabo. Sai dai ya so a ce a jikin Rakiya ne, na biyu kuma yana fargabar sabon ƙalubalen da Rakiya za ta fara fuskanta daga wurin Inna. Don tun a ranar da aka tabbatar da cikin Inna ta kira Rakiya, ta kafa mata dokaki dangane da aikin cikin gidan. "Ke Rakiya ina ce dai kin lura arziki ya ƙwanƙwanso mana ƙofa, wacce ta kasance irin albarka ta buɗe masa." Shiru Rakiya ta yi, don ba ta fahimci kalaman Inna ba. "To ina nufin ciki Zuwaira gare ta, don haka ba kowanne aiki za ta dinga yi ba. Na faɗa miki ne domin idan kina da wani shiri ki ɗaura ɗamara, domin wannan cikin sai an haife shi lafiya kuma ya taka ƙafa shi ma ko ita ma sun hayayyafa. Domin mu gadon haihuwa ne ba juya ba." Rakiya ta ji wani abu ya soki zuciyarta, amma sai ta danne ta saki murmushi ta ce. "Ma Shaa Allah, wannan abin farinciki ne. Allah Ya buɗi ido lafiya." Inna ta yamutsa fuska tana taɓe baki ta ce, "Amin, idan ma bai kai zuci ba kanki. To ina son ki sani yanzu aikin gidan nan gabaɗaya ke za ki dinga yi, har zuwa lokacin da cikinta zai yi ƙwari." Zuwaira da ke gefen Inna tana cin ɗata tana yatsina ta yi zaraf ta ce, "Inna hatta girkin ma ta dinga haɗawa ranar kwanana." Rakiya ta ɗago suka haɗa ido, Zuwaira ta murguɗa baki ta cigaba da cin ɗatarta. Inna ta dubi Rakiya ta ce. "Kin ji dai abin da ta ce? Za ki dinga komai na gidan nan, idan cikin ya girma sai mu san abin yi." Muryar Rakiya a raunane ta amsa wa Inna, bayan Inna ta sallame ta ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta zauna ta fara zubar da hawayen tausayin kanta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [16/05, 18:10] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA BAKWAI Sai da Rakiya ta ci kukanta mai isarta sannan ta ɗebi ruwan randarta ta ɗaura alwala a ɗakinta. Don tana gudun kada ta fita, su Inna su ga fuskarta su ɗauka maganar cikin ce ta saka ta kuka su yi mata mummunar fassara. Uwar ɗakinta ta shiga ta gabatar da sallah raka'a biyu. Ta roƙi Ubangiji da ya yaye mata damuwar da ke ƙunshe a zuciyarta, bayan ta gama addu'ar ta ji sanyi a ranta don ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ta yaye. Rakiya ita ta cigaba da duk ayyukan cikin gidan, tun daga kan shara, wanke-wanke, wankin banɗaki da sharar turken awaki zuwa girki duk babu mai tallafa mata. Hatta abinci wani lokacin Inna cewa take ta zubo wa Zuwaira, ita dai Zuwaira sai dai idan girki ya zagayo kanta ta karɓi miji. Don ta lura a yanzu yana ba ta kulawa, kuma duk abin da ta ce tana so bakin gwargwado yana yi mata. Sai dai abu ɗaya ne ba ta jin daɗi yadda ta ga har lokacin bai fifita darajarta a kan ta Rakiya ba. Amma abin da yake damunsa bai wuce yadda ake yake cakuɗewa Rakiya ba, tun da ya lura a ɗan tsakanin nan har duhu ta yi duk da hasken fatar da take da shi. Da ya yi yunƙurin yi wa Inna magana sai Rakiya ta hana shi, saboda ta san ko ya yi maganar ba za ta sauya zane ba sai ma wani ƙalubalen da za ta sake fuskanta. Watarana Rakiya ta gama aikin gidan tas, har ta ɗora abincin rana da yake rana ta yi. Inna ta ɗebo mata kayan wankinta, ta ce ta wanke mata nan take. Ta gaji sosai, domin bayanta har ciwo yake mata. "Na ce Inna idan babu damuwa ko na bari zuwa gobe da sassafe sai na tashi da wankin?" Rakiya ta furta a ɗarare, Inna da har ta nufi ɗaki ta waigo ta ce. "Ai da uwarki ce ta ba ki wankin ba za ki faɗa mata haka ba ko?" Shiru Rakiya ta yi, Inna ta gama zazzage mata rashin mutumci ta yi gaba. Babu yadda ta iya, haka ta ja kujera ta zauna, ta haɗa ruwan wankin don ba za ta iya wankin a sunkuye ba. Tana cikin wankin Zuwaira ta fito da nata kayan, tana zuwa kan Rakiya ta watsa mata cike da izgilanci ta ce. "Ga nawa wankin nan, ciki ne ya hana ni iya taɓa ko rigar mama na wanke ballantawa kayan sawa." Da ido Rakiya ta bi kayan, saboda tsabar wulaƙanci har da wandunan pant da rigar mama waɗanda suka yi duƙun-duƙun saboda datti. Rakiya ta dube ta ta ce, "Ba zan yi miki wanki ba." Zuwaira baki ta buɗe cike da mamaki ta ce, "Au ni kike faɗa wa haka?" "Na faɗa miki Zuwaira, ko kin ɗauka tsoronki nake ji? Ko kuma kin yi zaton ni baiwarki ce?" Rakiya ta furta a hassale, Zuwaira ta saki dariyar izgilanci ta ce. "Mene ne marabarki da baiwar to? Ko kin ɗauka kina da sauran amfani wanda ya wuce ki ci ki yi kashi da aikin gida?" Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da wanke kayan Inna, Zuwaira ta koma ta gabanta ta sake cewa. "Ki yi ki mayar da hankali ki wanke mini su tas, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci. Banza juya marar mamora ballantana amfani." Furucin Zuwaira na ƙarshe ne suka daki zuciyar Rakiya, kamar ba za ta kula ta ba sai ta ɗago ta ce. "Da Ubangiji kike, domin Shi ne ya ba ki cikin, kuma na tabbata ni ma bai manta da ni ba." Cikin shewa irin ta izgilanci Zuwaira ta ce, "Ahayyee! Lallai fa sumumu-kasau an samu bakin magana, ai ke da haihuwa sai dai ki ga ana yi. Ko mugun halin bokan ubanki ya isa ya hana ki haihuwa...' "Kada ki sake zagin mahaifina!" Rakiya ta furta mata da wata irin murya gargaɗi, cikin raini Zuwaira ta ce. "Uban naki wata tsiyar ce da kike kumfar baki a kansa..." Tas! Rakiya ta sauke wa Zuwaira mari a fuska, zaro ido waje Zuwaira ta yi tana mamakin wacce ta mare ta. Don haka ta wage murya cikin kururuwa ta ce, "Ni kika mara?" "Na mare ki, ko yanzu kika yi gangancin sake zagin mahaifina sai na ninka miki wanda ya fi shi."Rakiya ta furta tana tsare ta da ido, Zuwaira ta tsorota da yadda ta ga ran Rakiya ya ɓaci. Amma don kada ta nuna mata ta ji tsoro ya sa ta dake ta sake cewa, "An zage ki, uban naki ba boka ba ne mashiriki? Ko ba shi ya mallake Yaya..." A wannan karon ma Rakiya ta sake sauke mata mari a fuska, ihu ta saki ta yi zaman 'yanbori a ƙasa ta ɓarke da kuka. Da sauri Inna ta fito tana tambayar abin da ya faru, Zuwaira ta dafe cikinta cikin kukan makirci ta ce. "Ina wai don na ce ta taimaka ta haɗa da kayana shi ne ta hau zagina, don na rama shi ne da hau cikina da duka." "Duka a ciki?" Inna ta tambaya a razane, Zuwaira ta gyaɗa kai tana sake murƙususu kamar wacce aka doka da gaske. "Amma ke dai an yi baƙar muguwa, yanzu saboda rashin imani yarinyar tana da ciki kika dake ta don ki kashe ta? Wallahi bari Hasan ya zo a yi wacce za a yi." "Gara ya zo ɗin, domin ni ma na gaji haka. Hasan ko ɗan autan zinare a cikin mazan aure ne na gaji da shi." Rakiya ta furta a zuciye, don a wannan gaɓar ta gama zuwa bango. Da mamaki Inna ta ce, "Ni kike faɗa wa haka?" "Duk abin da kika ɗauka Inna, na faɗa na gaji wallahi. Ai ba baiwa aka ajiye muku ba, wallahi duk abin da zai faru sai dai ya faru amma zaman gidan nan daga yau na gama shi." Rakiya tana gama maganar ta miƙe tsaye ta yarfe ruwan hannunta ta juya za ta shiga ɗaki. Da sauri Inna ta bi ta ta ce, "Au Allah rashin kunya za ki yi mini? Wankin ba za ki zo ki yi mini ba?" Rakiya ta juyo a hassale ta ce. "Ba zan wanke ba, ita 'yar gwal ɗin gabanki ta wanke miki. Ai da ni da ita duka 'ya'ya ne." Tana gama faɗa ta shige ɗaki tana jin zuciyarta tana tafasa. Sai da ta yi da gaske sannan ta taushi zuciyarta, don ji take kamar ta fita ta wanke Inna tas sannan ta koma ɗaki. Daga Zuwaira har Inna kasa magana suka yi, sai zuwa bayan wani lokaci Inna ta fara kumfar baki. Har aka yi sallar Isha'i kowannensu da abin da yake saƙa wa a zuciyarsa, Malam Hasan yana shigowa Inna ta fashe da kuka. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, sai da ya lallashe ta sannan ya fara tambayarta abin da ya faru. "Wallahi yau yarinyar nan Rakiya babu irin zagin da ba ta yi mini ba, daga kawai na ba ta wanki don Zuwaira ta kawo mata 'yan ƙwayayyaki ta ce ta matse mata ta hau ta da duka. Don na yi magana ta zage ni ta ce wankin ma ba za ta yi ba." Bayan Inna ta gama faɗa masa ƙarya da gaskiya ta haska masa tulun kayan wankinta, sai bokiti da ke gefe wanda ta fara wankewa. Ransa ne ya ɓaci, don haka bai tanka wa Inna ba ya nufi ɗakin Rakiya. Koda ya shiga a madadin ya ji ta bakinta sai kawai ya rufe ta da faɗa. "Rakiya me ya sa kika zagi Inna? Ko don kin ga ina bin bayanki ne? Kada ki manta fa mahaifiyata ce, zan iya sauya kowa da komai a duniyar nan ban da ita. Don kawai ta ce ki mata wanki, yanzu idan mahaifiyarki ce za ki ce ba za ki wanke mata ba?" Tun da ya fara faɗa ido ta kawo ta zuba masa, ranta ya sake ɓaci a kan wanda ya mamaye ta. Sai da ya gama faɗan har ya juya zai fita ta ce. "Hasan ba ni takarda ta na gaji." Da mamaki ya ce, "Hasan! Sunana kike kira kai tsaye?" "Na faɗa ka ba ni takardata na ce maka, don ina mai tabbatar maka da ko kai ne autan maza na gama zaman aure da kai. Na gaji, na gaji da cin kashin da ake yi mini duk don saoda laifin da ake ganin ni na ɗora wa kaina." Rakiya ta furta a hasaale, saboda idonta ya gama rufewa da zallar ɓacin rai. Malam Hasan ya saki dariyar yaƙe ya ce, "Ni da ke ai aurenmu mutu ka raba ne Rakiya." "Ai ba a aure dole ko? To ai kuwa yau ba zan ƙara kwana a gidan nan ba. Wallahi sai ka ba ni takarda ta, ka zauna da 'yar'uwarka wacce mahaifiyarka take son ku kasance tare." Tana gama faɗar haka ta shiga haɗa kayan sawarta, duk da a lokacin ita ma ba ta san inda za ta dosa ba, amma ji take yi gara ta bar gidan ko ta samu salama. Yadda ya ga Rakiya tana faɗar maganganu ya tabbatar da an gama ƙure haƙurinta, a shekarunsu goma da aure ba ta taɓa yin wannan fito na fito da shi kamar haka ba. A fusace ya fita daga ɗakin, bayan ya dawo ya same ta har ta saka hijabinta. Wata farar takarda ya miƙa mata, cikin wani irin yanayi ta dube shi ba tare da ta tanka masa ba. Duk yadda ta so rabuwa da Malam Hasan sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi, ta dube shi muryarta tana rawa ta ce. "Sakina ka yi?" Bai amsa mata ba, ya ga ta ɗauki jakar kayanta za ta fita. Cikin sauri ya bi ta ya ce. "Wannan hukuncin ina ganin shi ne zai fiye mana alheri gabaɗaya, amma kafin nan ina son ki zo mu je gidan Kawu Sani ki kwana a can." "Babu ruwanka da inda zan kwana, idan na ga dama na kwana a titi ma damuwa ta ce." Rakiya ta furta tana fita, duk abin da yake faruwa Inna da Zuwaira suna tsakar gida suna ji. Saboda farinciki Zuwaira ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, Rakiya ta fita ko kallonsu ba ta yi ba ta fita daga gidan. Ganin haka ya sa Malam Hasan yana bi bayanta yana kiran sunanta, ta cigaba da tafiya ko waigensa ba ta yi ba. ABBAN FAUWAZ Abba yana ɗaga labulen ɗakin ya saki salati cike da mamaki ya ce. "Tani lafiya kike kuka? Ko wani abu ne ya faru?" Sai kuma ya waiga wurin Fauwaz da ya yi suman tsaye yana bin ta da kallon mamaki, Abba ya ce. "Kai Fauwaz me yake faruwa ne?" Fauwaz ya wara hannuwa a daƙile ya ce, "Abba kukan makirci take yi." Sototo Abba ya yi yana kallonsa, a ɗan faɗace ya ce. "Ka san me kake faɗa kuwa? Ko kuwa rashin mutuncin da tarbiyyar da kake yi ka gwada mata?" Kafin Fauwaz ya sake magana Tani ta ce. "Alhaji wallahi sai ka sake ni a yanzu ba sai an jima ba. Kamar ni ina matsayin matarka wai Fauwaz ya ɗaga hannu ya mare ni, saboda Allah ɗan da a haife da ace na haihu da wuri na haifi wanda ya fi shi ma." A razane Abba ya dubi Fauwaz ya sake mayar da kallonsa ga Tani ya ce, "Mari fa Tani?" "Au tantama kake Alhaji zan yi masa ƙarya ne? Ai shi ya sa na ce gara ka sake ni don wallahi ba zan iya zama gida ɗaya da wannan yaron ba." Tani tana rufe baki a fusace Abba ya rufe Fauwaz da mahaukacin duka. Ta ko ina yake kai masa duka, tun Fauwaz yana yunƙurin kare kansa har ya faɗi a ƙasa Abba bai daina dukansa ba. Sai da ya gaji don kansa, bayan ya ga Fauwaz yana fitar da numfashi da ƙyar sannan ya miƙe yana huci. Tani da daɗi ya gama mamaye ta, ta sake kwaɓe fuska ta ce. "Ni fa bayan wannan hukuncin dole ka san abin yi Alhaji, don yadda ka hukunta shi wallahi na san idan ya ji daɗin jikinsa sai ya yi mini abin da ya fi haka." Yarfe gumin fuskarsa Abba ya yi yana huci ya ce, "Gidan horo zan kai shi, kada wani abu ya dame ki don babu abin da zai raba ni da ke Tani. Ni da na rabu da ke gara na rabu da kowa a rayuwata." Sai a lokacin Tani ta saki murmushi ta ce. "Shi ya sa nake ƙaunarka Alhaji." Fauwaz da ke kwance cikin mummunan yanayi ya ce, "Abba... matar nan ba sonka take ba... wallahi..." Naushin da Abba ya kai masa a baki ne ya katse shi, bakinsa ya fashe jini ya fara zuba. Kafin wani lokaci tuni fuskar Fauwaz ta sauya gabaɗaya. A nan take Abba ya riƙo hannun Fauwaz cike da jin haushi, ya wurga shi ɗakinsa ya janyo ƙofa ya saka mukulli ya rufe. Sai da Tani ta haɗa masa ruwan wanka, wanda ya sha miyagun turarrukan da ta karɓa a wurin malamanta sannan Abba ya shiga ya yi wanka ya fito. Zaman da ya yi yana cin abinci a nan yake ba ta labarin cinikayyar da suka yi, da biyan bashin da ya yi. Sai kuma adadin ragowar kuɗaɗen da ake bin sa. Farinciki ne ya mamaye ta, har sai da fuskarta ta gagara ɓoye halin da zuciyarta take ciki. Don haka Abba ya ce. "Amma akwai wani albishir ko labari da kika samu ne Tani? Na lura kamar kina cikin farinciki." 'Dole na shiga farinciki haƙa ta, ta kusa cimma ruwa. Lokacin da zan kaɗa goge na ya zo.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Wani abu na tuno, amma ba yanzu zan sanar da kai ba sai ya tabbata In Shaa Allah." Shi ma murmushi ya saki ya ce, "Wato kina son ki ce za ki ba ni mamaki kenan?" "Tabbas za ka sha ruwan mamaki, don wataƙila tun da ka zo duniya ba a taɓa shayar da kai ruwan mamaki kamar wanda zan ba ka ba." Shiru ya yi ya zura mata ido, har sai da ta ji tsoron ko ya so fahimtar inda zancanta ya dosa. Sai kuma ta ga ya bagarar suka cigaba da hira, daga cikin hirar da suka tattauna har ta kai Fauwaz gidan horo. Bayan ya yi zaman gidan horo na wata biyu, daga nan za a ɗauke shi zuwa almajiranci. Kamar yadda Tani ta tsara masa haka Abba ya ɗauki Fauwaz ya kai shi gidan kangararru da ke titin Hajj Camp. Sai dai tun kafin a kai shi gidan horon suka fara da yi masa horon yunwa, don tun ranar da ya sa shi a ɗaki kullum sau ɗaya ake ba shi abinci da ruwa shi ma ba wani na kirki ba. A haka sai da ya shafe kwana biyar a cikin ɗakin, sai dai kafin Abba ya fita ya raka shi banɗaki ya yi uzurin da zai yi da ya gama ya mayar da shi cikin ɗaki ya kulle. Ana gobe za a kai shi gidan horon Abba ya shiga kai masa abinci, har ya juya zai fita a wahalce Fauwaz ya ce. "Abba na san abin da ba ka sani ba, don Allah ka ba ni dama na yi maka bayani. Ba na son ka yi danasani a lokacin da bayanina ba zai yi maka amfani ba." Dawowa Abba ya yi yana daga tsaye ya ce, "Ina jin ka, idan ka nemi yi mini shashanki ranka ya yi mugun ɓaci." Fauwaz ya ji daɗi sosai, duk da yunwa ta sa muryarsa ba ta fita amma ya yi ƙoƙarin mahaifinsa ya fahimce shi. "Abba akwai abin da Tani take shiryawa a kanka..." "Dakata Fauwaz!" Abba ya katse shi yana ɗaga masa hannu, domin duk wani abu da ya danganci kushe ko laifi matuƙar a kan Tani ne ba ya ji ba ya gani. "In dai a kan Tani ne mun dinga samun saɓani da kai kenan. Matuƙar ba za ka ɗauki Tani a matsayin mahaifiyarka ba, sai dai ni da kai mu kasance a mabambamtar inuwa." Daga haka Abba ya fita. Tun bayan da Fauwaz ya tafi gidan horo Abba da Tani suka cigaba da rayuwa, sai dai kusan malejin rayuwa suke yi domin al'amura da dama a ɓangaren kasuwanci sun tsaya masa cak. Sakamakon yana samun kuɗi yake kai wa Alhaji Dikko a rubuta su cigaba da lissafi. Suna cikin haka har Fauwaz ya shafe watanni biyu cif a gidan horo Abba ya ɗauko shi ya dawo da shi. Duk wanda ya san Fauwaz a baya, idan ya gan shi a wannan lokacin ba zai gane shi ba a tashin farko. Ya yi wani irin baƙi ya rame, kamar ba shi ba. Haka kuma wasu daga cikin ɗabi'unsa sun sauya sosai, duk da dama can ba mai magana ba ne. Amma a wannan lokacin sai rashin maganarsa ta ƙaru, ya koyi taurin kai fiye da yadda yake da shi a baya. Idan ya ce ba zai yi abu ba, duk horo ko hukuncin da za a yi masa ba su sa ya aikata ba. Haka kuma ya fita daga sabgar Tani, ita kanta a wannan lokacin har tsoron a bar su daga shi sai ita take yi a gida. Daga ƙarshe ma sai take kulle kanta a ɗaki idan Abba ya tafi kasuwa, duk wani abu da za ta buƙata saka shi a ɗaki take yi. Sai ta ga fitar Fauwaz sai ta fito da sauri ta rufe gidan sannan ta ɗora girki, idan ta gama sai ta buɗe gidan ta shige ɗakinta ta rufe. A haka suka cigaba da rayuwa har Abba ya ɗauke shi, ya kai shi garin Gombe almajiranci. Satin Fauwaz biyu da tafiya watarana da sassafe suna zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, Abba ne ya fita yana zuwa ya ci karo da 'yansanda a ƙofar gidan. Gaisuwar mutumci suka yi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce. "Alhaji mun zo gayyatarka zuwa ofishinmu ne, sakamakon wata tuhuma da ake yi maka." Da mamaki Abba ya ce, "Tuhuma kuma?" Lokaci ɗaya suka gyaɗa masa kai, sai Abba ya ce. "To ku je In Shaa Allahu..." "Am sorry to say hakan ba zai yuwu ba, dole za mu tafi da kai ƙafarmu ƙafarka." Suka ba shi amsa kai tsaye fuska babu walwala. Jama'a za ku iya fara payment daga yau💃🏻 free pgs suna gab da ƙarewa. Naira 500 ne kacal ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [18/05, 18:15] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA TAKWAS Abba ya yi mamakin jin furucinsu, don haka ya ce. "Amma don Allah ko zan san wanda ya turo ku wurina?" Wani baƙi daga cikinsu wanda ya kasance mai ƙaton ciki ya girgiza kai ya ce, "Babu buƙatar haka, idan mun je ofis za ka ji bayanin gayyatarka." Abba ya yi jim sannan ya ce. "To shi kenan, amma don Allah ku yi mini afuwa zan shiga na sanar da iyalina." A nan ba su musa masa ba, jikinsa a sanyaye ya shiga ya samu Tani a kan gado tana bacci. Tashin ta ya shiga yi a gaggauce, cikin magagin bacci ta ce. "Lafiya Alhaji." A gefen gadon ya zauna ya ce, "Ina fa lafiya Tani, ina cikin tashin hankali. 'Yansanda ne a ƙofar gida suka zo tafiya da ni." Firgigit ta wartsake idonta, cikin sauri ta ce. "Yan sanda kuma? Me ka yi musu? An

Chapter 6 of 9