Share this page
3 / 9
shiga ɗakinsu ita da mahaifinsu kai tsaye ba tare da an ba su izini ba. "Abba! Abba ka zo Abida wani abu take yi ba ta da lafiya." Fauwaz ya furta a ɗan ruɗe, daga can ɗakin mahaifinsu ya ce. "Kai waye nan?" Cikin sauri Fauwaz ya ce, "Ni ne Abba, Abida ba ta da lafiya wani abu take yi." Kamar wanda ya watsa wa ruwan zafi a hassale Abba ya ce, "To ni zan ba ta lafiyar ko yaya? Ko kuwa kawai don ka tashe mu ka katse mana bacci?" Yana daga waje ya ji muryar Tani tana cewa, "Ni ban san mene ne matsalar yaron nan ba. Wallahi da uwarsa tana raye cewa zan yi ita take kitsa masa duk wani abu da yake aikatawa. To ban da rashin lissafi yanzu idan ya faɗa maka me za ka yi mata? " "Shi ne abin da na gani, kai Fauwaz ka wuce ka tafi zuwa safiya sai a san abin yi." Abba ya furta daga cikin ɗakin, hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar Fauwaz kamar an yi masa gorinsu. Har ya juya zai tafi ya ce, "Abba amma da Mama tana raye ba ka mana haka. Na san da tana nan haka ba za ta faru ba..." "To ka tafi maƙabarta ka dawo ita mana." Tani ta furta da wata irin murya, shi kuma Abba ya ce. "Lallai wuyanka ya isa yanka Fauwaz." "Ba irin abin da nake faɗa ba kenan, kai ma ka ga rashin kunyarsa ko?" Tani ta furta cike da zuga da son ƙara tunzura Abba, sai dai har Fauwaz ya fita daga ɗakin bai sake tanka musu ba. Duk da cikin dare ne hakan bai hana Abba ya cigaba da surfa faɗa ba, zuciyar Tani fes ta cigaba da ingiza shi yana hawa. Sai da ta tabbatar da ya gama cika fal da haushin Fauwaz sannan ta sake kwantar da murya ta ce. "Ni fa Alhaji ina son faɗar wata magana, amma sai ruwan tsoro ya mamaye ni." Tani ta sauya fuska cikin alamun damuwa, hasken ƙaramar fitilar touchlight ɗin da ke hannunsa ta sake bayyanar masa da zallar damuwar da fuskarta take ciki. "Faɗi mana Tani, ni a kan yaran nan tamkar mahaifiyarsu haka nake kallonki." Abba ya furta cikin damuwa, Tani ta gyara zama ta cigaba. "Ni fa sai nake ganin kamar ba iya abin da ya kawo Fauwaz ɗakin nan ba kenan." Cikin rashin fahimta Abba ya ce, "Ban fahimce ki ba Tani." Tani ta sake muskutawa kusa da shi sannan ta ce, "Ni fa ina zargin sata ce ta shigo da shi." "Sata!" Abba ya furta da wata irin murya mai cike da zallar tashin hankali, gaban Tani sai da ya faɗi da ganin mummunan yanayin da ya shiga. Har sai da ta fara tsammanin ko haƙonta a zai cim ma ruwa ba, sai kuma ta dake zuciyarta ta ce. "Ƙwarai kuwa, saboda ba rana ɗaya ba, ba kuma biyu ba da na taɓa ganin ya shigo mana ɗaki idan muna kwance. Don ko jiya sai da na nemi ɗari biyuna sama da ƙasa na rasa." Ganin zancan kamar yana shigarsa ya sa ta wara hannuwa tana taɓe baki ta ce. "Ka san an ce idan ba ka iya kama ɓarawo ba, sai shi ya kama ka. Ba na son na dinga yawan faɗa maka laifin yaron nan ka ga kamar ba na ƙaunarsa, ni kuma na ga ɗa ai na kowa ne..." "Haba Tani, amma me ya sa kika rufe mini magana mai girma kamar wannan?" Abba ya katse ta a ɗan hassale, cike da kissa ta ce. "Ka yi haƙuri Alhaji In Shaa Allahu ba za a sake ba." Furzar da iska mai zafi Abba ya yi, zuciyarsa tana zafi ya furta. "Yaushe Fauwaz ya zama haka? Sata? A cikin gidana? Ina ba zai yiwu ba." Tani ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Ni kuwa idan har da gaske ka ba ni matsayin mahaifiyar Fauwaz, zan ba ka wata shawara wacce nake ganin ita ce mafita a gare mu gabaɗaya." Tana dire kalamanta Abba ya ce, "Faɗi kowacce iri ce Tani, domin mai sonka ai shi zai faɗa maka gaskiya. Wa ya sani ma ko yana yi a waje mutane suna nan suna ta kallona da abin." Abba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, zuciyar Tani fari ƙal saboda farin ciki. Amma a fili sai ta marairaice murya ta ce, "Ni ina ganin abin da ya fi, tun da yaron nan nema yake ya janyo mana magana. Kuma muna iya bakin ƙoƙarinmu wurin kula da tarbiyyarsu, kawai ka kai shi almajiranci." Tani ta ƙarasa furucin tana satar kallon fuskar Abba. ƊANBATTA A yatsine Inna ta dubi Rakiya da ke gursheƙen kuka, Malam Hassan ya matsa kusa da ita cike da tausayi ya dafa kafaɗarta. "Yau kuma wani sabon kitifin kika ƙullo ba ki warware shi a ko ina ba sai nan a gabana? To ko laƙanin da bokanki ya ba ki kenan?" Inna ta furta cikin masifa, Malam Hassan ne ya yi ƙarfin halin cewa. "Inna Fatihu ne Allah ya yi masa rasuwa." Maganar Malam Hassan ta yi daidai da faɗuwar bokitin ƙullin kunun da ke hannun Inna. "Shi Fatihun ne ya rasu?" Inna ta furta a ruɗe, Malam Hassan ya gyaɗa kai idanunsa suka yi jajir kamar zai zubar da ƙwalla. Hakan ya sa Rakiya ta sake rushewa da kuka, tana sake jin soyayyar Fatihu a ranta. Hannu ya saka ta bayanta ya tallafo shi, Rakiya ta kunto Fatihu da ke bayanta. Malam Hasan yana sauke gawar Fatihu Inna ta zuba salati tana tafa hannu. Zuwaira da fitowarta daga banɗaki kenan ta ƙarasa tana tana faɗin. "Lafiya Inna?" Ganin su Malam Hasan ya sa ta datse kalamanta, ta zuba masa idanu tana kallonsa. "Ina fa lafiya Zuwaira, wai Fatihu ne ya mutu. Shi kenan hankalinta ya kwanta ai." Inna ta ƙarasa furucin muryarta tana rawa, da sauri Zuwaira ta dafe ƙirji tana ja da baya ta ce. "Fatihu ya rasu Inna? Yaya me ya faru da shi? In ce dai ba wata gubar Rakiya ta ɗura masa ba..." "Sai ma kin tambaya Zuwaira? Kamar ba ki san wace ce Rakiya ba." Inna ta yi saurin katse Zuwaira hawaye yana zuba sannan ta ɗora da cewar. "Shi kenan ɗan ɗaya-ɗayan da Allah Ya ba wa Hasan an halaka shi." "Inna don Allah ku tsaya ku saurari abin da ya faru, kada ku yanke hukunci kai tsaye." Malam Hasan ya furta cikin damuwa, a sheƙe Inna ta dube shi ta ce. "Hasan wai yaushe rawanin asirin da yarinyar nan ta yi maka zai warware?" "Don Allah Inna ki daina faɗar haka, Fatihu tsautsayi ne ya faɗa masa. Kuma tun fil azal Allah Ya ƙaddari shi ba mai tsawon kwana ba me..." Gabaɗaya duk abin da ya faru Malam Hasan ya kwashe ya sanar da su Inna. Yana rife baki Zuwaira ta wurga wa Rakiya kallon banza, sannan ta buga uban tsaki ta ce. "Inna don Allah ta yaya wacce ba ta san zafin haihuwa ba za ta riƙe ɗa dama? Wai ki ji Fatihu ya zame a ruwa kamar wani ɗan tayin kifi." A hassale Malam Hasan ya ce, "Kada na sake jin bakinki Zuwaira! Idan kika sake faɗar magana marar daɗi ranki zai yi mummunan ɓaci." Inna da zuciyarta ta gama zuwa wuya ta ce, "Ƙarya aka yi mata? Yanzu idan ɗan da ta ɗauki cikinsa ta sha wahalar laulayi ta yi naƙudarsa ne za ta sake shi a ruwa? Na ce za ta sake shi a ruwa?" Inna ta ƙarasa furucin tana zuba wa Malam Hasan idanu, sunkuyar da kai ƙasa ya yi zuciyarsa a dagule musamman da yake jin shasshekar kukan Rakiya har cikin ransa. Domin shi shaida ne a kan zallar soyayyar gaskiya da take yi masa. A yadda ya san halin Rakiya da kyawawan halayenta, ba zai yi tantama a kan mutuwar Fatihu ba koda ba ya wurin al'amarin ya faru. "Ai ta kashe uwarsa, tun da ta gama da uwar kin ga shi ma dole ta gama da shi yadda za ta kanainaye mini ɗa ba tare da wani ya raɓe shi ba." Inna ta furta cike da masifa, Zuwaira ta taɓe baki ta ce. "Inna ka yi magana cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa." "To ni na faɗa, idan ya ga dama ya yi mini duk abin da ya ga dama a kanta, dama ai ba yau ya saba nuna mini iyaka ta a kanta ba. Wanna baƙar annoba ni kam Allah Ya jarabce ni da ita, ga ki dai juya gaba da baya ba haihuwa kike ba amma kin kashe mai haihuwar shi ma ɗan da aka haifa ɗin kin hallaka shi." Wani irin sabon kuka mai cin zuciya Rakiya ta saki, sai kawai ta fice daga gidan tana jin tamkar zuciyarta za ta tarwatse saboda ɓacin rai. Da wanne za ta ji? Da rashin Fatihu da take jin sa tamkar ɗan da ya ratso ta jikinta ko kuwa da baƙaƙen maganganun ƙazafin da Inna take jifanta da shi? Duk da maganganun Inna ba baƙi ba ne a wurinta, amma na ranar sun fi dukan zuciyarta domin a lokacin ji take yi ko mahaifin Fatihu Malam Hasan ba zai kai ta jin raɗaɗin da take ji na mutuwarsa ba. Malam Hasan yana ganin Rakiya ta fita ya bi ta sauri yana kiran sunanta, hakan ya sa Inna ta yi saurin ɗagowa ta shiga ƙwala masa kira. "Hasan! Hasan! Ba za ka rabu da ita ba ka zo ina yi maka magana." Cike da zuga Zuwaira ta ce, "Ina zai zo zuciyarsa ta tafi Inna, ai wallahi sai kin yi da gaske a kan Yaya don ni wallahi ban taɓa tsammanin abin ya yi tsamari haka ba." Inna ta zuba hannuwa biyu a kumatu cike da jimami ta ce, "Zuwaira kin ga ya fifita waccan juyar a kan gawar ɗansa ko?" Zuwaira ta saka hannu ta ɗauki gawar Fatihu ta saka a wani ƙaramin ɗaki da suke ajiya shirge-shirgensu. Inna ta zauna a kan turmi zuciyarta tana ci gaba da tafasa, don a wannan karon ji take yi sai dai Hasan ya zaɓa ko Rakiya ko ita. Duk yadda Malam Hasan yake sauri sai da ya haɗa da sassarfa sannan ya cim ma Rakiya yana ƙwala mata kira. "Rakiya! Rakiya don Allah ki tsaya mana." Cike da ƙunan zuciya da ɓacin rai ta waigo tana faɗin. "Me zan tsaya na yi Baban Fatihu? Me zan zauna yi a wurin da ba a ƙauna..." Kukan da take dannewa ya ƙwace mata, wani abu ne ya soke shi a maƙoshi cike da lallashi ya ce. "Don girman Allah ki yi haƙuri Rakiya, ni da ke duka mun san halin Inna ba baƙo ba ne a wurinmu. Me zai sa ranki ya ɓaci tun da kin san halinta?" "Me ya sa raina ba zai ɓaci ba ko ni ba ɗan'adam ba ce ba ni da zuciya a ƙirjina? Me ya sa har yanzu Inna ta gagara fahimtar ni ba irin yadda take tsammani ba ce? Me ya sa ba ta iya ɗaga mini ƙafa a wannan gaɓar da zuciyata take cike da ɗacin rashin Fatihu ba. Kasan komai fa Baban Fatihu, ka san dai ba zan iya salwantar da rayuwar ɗanmu Fatihu ba..." Sai ta sake fashewa da kuka, a sanyaye ya matsa kusa da ita murya a tausashe ya ce. "Na san komai Rakiya, na san ba a kyauta miki ba. Kuma duk wanda kika ji an ba wa haƙuri an cuce shi ne, na tabbata watarana Inna za ta fahimce ki yadda ya kamata." "Zuwa yaushe kake tunanin Inna za ta ƙaunace ni? A shekara goma da aurenmu ba ta so ni ba sai daga baya?" Rakiya ta jefa masa tambayar cike da tausayin sabuwar rayuwar da za ta fara tare da Inna. Malam Hasan ya riƙo hannunta ya ce, "Don Allah ki zo mu je ciki, waɗannan maganganun za mu tattauna daga baya." Sai da Malam Hasan ya sake rarrasarta da kalamai masu taushi sannan suka koma cikin gidan. Lokacin da suka shiga Inna ta cika fam, suna zuwa gabanta cike da zafin rai ta ce. "Hasan! Hasan!! Hasan!!!" Gabansa yana faɗuwa ya ce, "Na'am Inna." "Sau nawa na kira ka?" Ya shafa kai a hankali ya ce, "Sau uku Inna." "To idan ni Kulu, ni na ɗauki cikinka na yi naƙuda na haife ka a yau sai ka saki wannan tsinanniyar yarinyar." Inna ta furta tana kafe shi da ido. Duk da a wannan lokacin ɓacin rai ya sa Rakiya tana son rabuwa da Malam Hasan, kalaman Inna ba ƙaramin tarwatsa nutsuwarta suka yi ba. "Hasan a yanzu daga Allah sai kai, ku kaɗai kuka zama gatan Rakiya. Don Allah duk rintsi kada ka salwantar da amanarta da na damƙa maka." Malam Hasan ya tuna kalaman mahaifin Rakiya waɗanda ya yi su yana gab da barin duniya. Nan take ƙwaƙwalwarsa ta sake tarayo masa da kalaman Inna, cikin girmamawa ya ce. "Don Allah Inna ki yi haƙuri, abin bai kai da haka..." Tass! Inna ɗauke fuskarsa da mari, ba Rakiya ba hatta Zuwaira sai da abin ya matuƙar ba ta mamaki. Inna ta nuna shi rai a ɓace ta ce. "Na riga da na gama magana, idan kuma ba za ka sake ta ba. Ka je ka ban yafe haƙƙina da ke kanka na mahaifiya ba." Cikin firgici Malam Hasan ya ɗago yana kallon Inna, ba ta tanka masa ba ta shige cikin ɗakin rai a ɓace. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [12/05, 17:48] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA HUƊU Da wani irin sanyin jiki Rakiya ta matsa kusa da shi, ta zuba masa ido tana karantar mummunan yanayin tashin hankalin da yake ciki ta ce. "Koda wasa kada ka yi ja-in-ja da mahaifiyarka. Tabbas ana sake mata, amma duk duniya babu mai maye maka gurbin mahaifiya. Ba tun yau Inna take gwada mini ƙiyayya ba, amma a wannan gaɓar ta zarce kowanne lokaci." Rakiya ta ja gefen hijabinta ta share hawayenta sannan ta cigaba. "Ban ga laifin Inna ba, domin kowacce uwa tana son ganin zuri'ar 'ya'yanta. Ni kuma kalar ƙaddara ta kenan ta rashin haihuwa, sai dai ba yin kaina ba ne..." Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, Malam Hasan zai yi magana ta katse shi da cewar. "Baban Fatihu ka bi mahaifiyarka, ni kuma zan tafi duk inda Allah Ya ƙaddara zamana zai ƙare a can." "Ba za ki tafi ko ina ba Rakiya." Malam Hasan ya furta cikin hargitsattsiyar murya mai cike da zallar ɓacin rai, sannan ya ɗora da cewar. "Koda ace ba ki kasance matata ba, haƙƙina ne na kula da ke matuƙar ba kya ƙarƙashin wani." Za ta sake magana ya riƙe hannunta da ƙarfi suka fita daga gidan, kai tsaye gidan Kawu Sani suka ƙarasa. A lokacin da suka shiga Kawu yana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana rufewa, kallo ɗaya za ka yi wa su Malam Hasan ka fahimci kwanciyar hankali ta bijirewa gangar jikinsu. "A'a, yau Hasanu ne da farar safiya haka?" Kawu Sani ya furta yana ɗan faɗaɗa fara'arsa. Murmushin yaƙe Malam Hasan ya saki ya ce, "Mune Kawu, barka da safiya." Kawu Sani ya amsa sannan suka gaisa da Rakiya wacce fuskarta ta yi jajir saboda kuka. Iya matarsa ce ta ƙarasa suka gaisa, tana shirin kai su ɗaki Malam Hasan ya ce. "Kawu dama ba zama muka zo yi ba, akwai maganar da take tafe da mu." Kawu Sani ya girgiza kai ya ce, "Hmmm Kulu ce ko?" Malam Hasan ya gyaɗa kai sannan ya kwashe duk abin da yake faruwa ya sanar da shi. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin faɗa-faɗa ya ce. "Indo wai yaushe Kulu za ta yi hankali ne? Wanne irin rashin hankali take son aikatawa haka? Yara sun rasa ɗansu ko gawarsa ba a binne ba take ƙoƙarin sake saka su a wani tashin hankalin." Iya da ke gefe ta furzar da iska mai zafi ta ce. "Wallahi a kullum lamarin Kulu yana sake ba ni mamaki, wai me ya sa wasu iyayen suka fi ƙuntatawa 'ya'yan da suke fi yi musu biyayya? Saboda Allah ina adalci a cikin hukuncin da ta yanke, rayuwa da mutuwa duk a wurin Allah suke, sai kace ba ta san ƙaddara ba." Kawu Sani ya girgiza kai ya dubi su Malam Hasan ya ce. "Ku wuce mu je gidan, wallahi idan Kulu ba ta yi wasa ba sai ranta ya yi mummunan ɓaci." A ɗan sanyaye Malam Hasan ya ce. "Amma Kawu don Allah kada ta..." "Kada ka damu na san yadda zan ɓullo mata." Kawu Sani ya katse shi, sannan suka wuce can wurin Inna. Lokacin da suka ƙarasa gidan a soro suka ci karo da Zuwaira, tana ganin Kawu Sani ta haɗe fuska murya ciki-ciki ta ce. "Sannu da zuwa Kawu..." "Wuce ciki mu je baƙar munafuka." Sum sum sum Zuwaira ta juya ta shige ciki, tun daga tsakar gida Kawu Sani ya fara ƙwala wa Inna kira. "Kulu! Ke Kulu ko sai na shigo ɗakin?" Inna ta fito fuskarta a cunkushe ta ce, "Ga ni Yaya." Kawu Sani ya janyo hannun Malam Hasan ya ce, "Maza zo ki tsine masa, na ce ki zo ki tsine masa sakarai wacce ba ta da hankali. Wato so kike ki sabauta yaron nan ko ki saka masa hawan jini ki tsugunnar da shi ko Kulu?" Inna ta sake haɗe fuska ta ce, "Yaya kai ne ba ka san abin da ya faru..." "Idan ba ki yi mini shiru ba sai na ci mutumcinki, wai Kulu yaushe za ki gane Allahn da ya busa miki numfashi, Shi ya dasa miki ƙwan da kika haihu ba tare da sisin kwabo ko wayo da dabararki ba? An ya Kulu kina son ki wanye lafiya kuwa?" Gabaɗaya shiru suka yi wurin ya yi tsit, Kawu Sani ya nuna Zuwaira da yatsa sannan ya ce. "Ke kuma daga yau, idan na sake jin kin faɗa wa Rakiya wata magana ke ko kallon banza kika yi mata wallahi tallahi sai na tattaka ki." Ya waiga wurin Inna ya ce. "Yanzu zan samu mai gari da Malam Liman a suturta yaron nan, zuwa nan da dare za mu zauna mu tattauna." Kawu Sani ya juya zai fita, har ya je bakin ƙofa ya waigo ya ce. "Idan kun ga dama bayan na fita ku cigaba da rashin mutumcin da kuka saba. Kai Hasan zo mu je." Ajiyar zuciya a fili Malam Hasan ya saki, jiki a sanyaye ya rufa wa Kawu baya suka fita. Bayan fitar Kawu daga Inna har Zuwaira babu wacce ta yi mata magana, ganin haka ya sa Rakiya ta ɗan samu ƙwarin gwiwar shiga ɗakin da gawar Fatihu take. Tana tsoma ƙafa cikin tsawa Inna ta ce. "Kada ki sake ko da wasa ki taɓa mini gawar jikana. Idan kin so kuma kin ga dama kina iya haihuwar naki, tun da ke dai kin zama ƙaddara wacce ba ta da zuciya." Shiru Rakiya ta yi sannan ta fito bakin bishiyar darbejiyar da ke tsakar gidan ta zauna. Tana nan zaune Zuwaira ta fita ta fara sanarwa da maƙota, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota da abokan arzikin Inna da suka cika gidan. Sai dai a yadda Rakiya ta lura kowacce mace ta shigo da irin wulaƙantacan kallon da take jifanta da shi. Wanda hakan ne ya alamta mata ruwa ba ya tsami banza, don ta tabbata akwai maganar da Zuwaira ta sanar da su a kanta. "Don Allah ki dubi yarinyar nan kamar mutuniyar arziki, yanzu wa zai ce za ta iya aikata rashin imanin nan haka." Rakiya ta ji wata tsohuwa ta furta ƙasa-ƙasa, tana cikin nazarin kalaman tsohuwar ta sake jin wata ta ce. "Ke kuma Tatu kamar ba ki san karuwancin matan birni ba? Yoo shi ma Hasan ɗin ai an ce ba banza ta bar shi ba." Wata tsohuwa da ke kusa da Inna, wacce kana ganin yanayinsu za ka fahimci ita ce babbar aminiyar Inna ta karɓe zancen da cewar. "To Allah na tuba kya ce ita, ai ki ce ubanta tuni ya gama da Hasan. Abin da tun bai san kansa ba ake ba shi a ruwa da abinci yake ci me ya rage kuma? Ai wallahi matuƙar kika cigaba da zama Kulu za ki zaunau ganin idonki." Inna ta sake yin tsumu abin duniya yana sake damunta, cike da sanyin jiki ta ce. "Abuwa ya zama dole na ɗauki matakin da ya dace." "Atoh ke da ɗanki amma wata juyar banza ta fi ki iko da shi ina dalili." Abuwa ta amsa cike da taƙama tana jifan Rakiya da mugun kallo, don yadda take ɗaga murya da gayya take faɗa don Rakiya ta ji. Suna cikin tattaunawa Malam Hasan da wasu maza biyu suka yi sallama domin ɗaukar gawar Fatihu. Kai tsaye ƙaramin ɗakin da aka suturta shi suka shiga, lokacin da Malam Hasan ya rungumo Fatihu suka haɗa ido da Rakiya. Wani sabon kukan ta fashe da shi, duk yadda ta so tausar zuciyarta sai hakan ya gagara. "Yaya haka kawai nake jin kamar ba zan rayu da Fatihu ba, don Allah ga amanarsa nan, ki yi masa duk abin da mahaifiya za ta yi wa ɗanta. Domin na yarda da ke, kuma Fatihu ɗanki ne. Zan so ki tuna da wasiyar nan tawa a ranar da Fatihu ya zama magidanci, a ranar da za ki aurar da shi domin wannan ranar ita ce mafi mafarinciki ga kowacce mahaifiya." Kalaman bankwanan da mahaifiyar Fatihu ta yi mata a baya suka faɗo mata a rai, cikin wata irin murya da ba ta yi zaton kalaman za su fito ba ta ce. "Shi kenan ba zan ga auren Fatihu ba? Shi kenan yadda na rasa Hafsatu mahaifiyarsa shi ma na rasa shi? Na rasa Fatihu mai ɗebe mini kewa kenan Baban Fatihu?" "Ban yi zaton Ruƙayyar da na sani mai sanin hukunci da dokokin Ubangiji za ta cigaba da furta waɗannan kalaman ba. Na yi tsammanin ke ce mutum ta farko da za ta lallashe ni a kan babban rashin da muka yi." Malam Hasan ya furta mata haka a lokacin da ya ƙarasa gabanta da gawar a hannunsa. "Ruƙayya!" Ya kira sunanta da wata irin muryar mai taushi, wacce take bayyanar da zallar soyayya, kulawa da tausasawa. Ba ta iya amsa masa ba sai ido da ta zuba masa waɗanda suka kaɗa jajir tana hawaye, ya sake kwantar da murya ya cigaba. "Yana da kyau ki tuna, Ubangijin da Ya ba mu Fatihu yana iya ba mu ninkinsa a lokaci guda..." "Amma ba da wannan juyar ba." Furucin Inna ya katse shi, waigowa suka yi lokaci ɗaya suna kallon Inna. Matan gidan da suka shigo gaisuwa duk suka yi carko-carko, don tun lokacin da ya ƙarasa wurin Rakiya suka saki baki da hanci suna bin su da kallo. Wasu su ce ta mallake shi, wasu kuma su ce mahaifinta ne ya mallake mata zuciyarsa, shi ya sa yake mutuwar sonta ya gagara rabuwa da ita. "Hasan kai muke jira fa." Kawu Sani ya furta, ganin Inna ta yi tsaye a gabansu ya sa shi cewa. "Lafiya dai Hasan ko da wani abu?" Cikin sauri Hasan ya ce, "A'a babu komai mu je Kawu." Daga haka ya wuce suka fita da shi, sai dai har ya kai soro yana jin gunjin kukan da Rakiya take yi mai tsuma zuciya. Inna kuma ta koma ta zauna ƙawayenta suka cigaba da ƙus-ƙus suna zuga ta. Cikin lokaci ƙanƙani aka sallaci Fatihu aka kai shi makwancinsa, da yake rasuwar ƙaramin yaro ce daga mutanan ƙofar gida har matan cikin gidan ba su wani daɗe ba kowa ya

Chapter 3 of 9