An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[17/01, 10:35 am] Ashantyluv: 【HAMZAH】
𝓂𝓎 𝓅ℴ𝓈𝓈ℯ𝓈𝓈𝒾ℴ𝓃𝓈!
✆-08140754777
𝑩𝒂𝒓𝒌𝒂 𝒅𝒂 𝒔𝒉𝒊𝒈𝒂 𝒔𝒂𝒃𝒖𝒘𝒂𝒓 𝒔𝒉𝒆𝒌𝒂𝒓𝒂 2026! 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒚𝒂 𝒔𝒂𝒅𝒂𝒎𝒖 𝒅𝒂 𝑨𝒍𝒌𝒉𝒂𝒊𝒓𝒂𝒏 𝒅𝒂𝒌𝒆 𝒄𝒊𝒌𝒊𝒏 𝒘𝒂𝒏𝒏𝒂𝒏 𝒔𝒉𝒆𝒌𝒂𝒓𝒂, 𝒚𝒂 𝒃𝒂𝒎𝒖 𝒛𝒂𝒎𝒂𝒏 𝒍𝒂𝒇𝒊𝒚𝒂 𝒄𝒊𝒌𝒊𝒏 𝒂𝒍'𝒖𝒎𝒎𝒂!
𝑯𝑨𝑷𝑷𝒀 𝑵𝑬𝑾 𝒀𝑬𝑨𝑹!!
WhatsApp group!
https://chat.whatsapp.com/DaatWeTyf3M59ZwHORMsIi
﷽
❶
A cikin dukkan shekarun da na shafe ina zaune cikin wannan katafaran gida, na san cewa na sami wuri mafi dacewa da zan zauna har ƙarshen rayuwata. Shin wa zai ƙi son zama wannan wuri, saboda irin kyakkyawar alak'a da kuma zamantakewa mai tsafta. Shi wannan katon gidan da nake ƙauna tsawon waɗannan shekarun mallakin uwar rik'ona ce, Mommy Jannat, wadda ta ɗauke ni ta raina, ta d'auke ni bayan da na rasa iyayena a hatsarin mota tun ina da shekara takwas cur a duniya. Ita d'in ta kasance yayar mahaifina ,haka kuma su biyu cur wajen iyayen su.
Me ya sa nake ƙaunan zamana wajenta ? Bayan kyakkyawar soyayyarta a gareni, a nan na sami komai… na sami shiru, na sami sabuwar rayuwa, na sami mafarkai na, na sami SOYAYYA.
Na sami Mommy Jannat, wadda ta zama mahaifiyata ta biyu. Daga gare ta, na samu cikakkiyar kulawa da ƙauna irin ta uwa ta gaskiya. Ta ba ni komai. Ɗaki na musamman kamar na princess, kyawawan tufafi, kayan ado masu tsada, makaranta ta kashin kai, alawus mai yawa. Ku faɗa, kusan komai na samu—duk wani abu da mutum zai taɓa buri a kansa. Kuma abin da ya fi komai, Mommy Jannat zata cika min buri da mafarkine, zata ba ni abin da zuciyata ke tsananin muradi —ɗanta.
Ranan dana tsinci kaina a wannan gida ,a ranan na fara ganinsa, nan take na san cewa yana da wani abu na musamman. Duk da ƙarancin shekaruna a wancan lokaci, haka na tsinci kaina ina Desiring na shi. A zahiri, ya girmeni da shekaru biyar. A wancan lokacin, saurayi ne kyakwawan gaske dake da tarin masoya da yawa a makarantar sa. Yawancin ’yan mata suna haukacewa saboda shi. Haka yawancin samari kuma suna marmarin zama abokansa. Lallai shi d'in ya cancanci sunan NOBLE kaman yanda ake masa kirari. The king of my heart .
Abin da na ke ji a kansa sa ya fara ne a matsayin ƙaunar irin na yara masu ƙarancin shekaru kuma na jini , yazo ya bunƙasa ya zama abu mai ƙarfi da girman gaske. Ban fargaba bare shiri , na faɗa dumu-dumu cikin kogin ƙauna da soyayyar sa!
Duk irin soyayya da y'anci rayuwa dana samu a wannan gida , shi ne abu mafi girman da daraja a gareni. Shi ya sa nake tsananin so da ƙaunan kasancewata cikin wannan ahli. Babu abunda na nema na rasa.
Amma matsalar ita ce yadda yake mu’amala da ni. Ya kasance ba ruwansa da ni kwata-kwata—ba kulawa, ba damuwa, ga halin ko-in-kula da sanyi da yake nunawa a gareni. Da farko abin bai ruɗe ni ba sai daga baya da ya nuna karara bai taɓa son kasancewata a nan . Da wuya kaga ya min magana , kai ko kallo ban ishe shi ba, in kaga ya yimin magana ko ya kalleni to nina bishi—ko kuma in ce ina binsa a ɓoye(stalking)—zuwa lambu, haka zakaga yana korata da ihu da hargagi kaman yaga barawo ko ince y'ar maula,amma InshaAllahu hakan ba zai hana gobe na sake binsa ba duk inda yake.
Sosai yake nunawa baya son ganina kusa dashi. Ya tsaneni, tsana mai ƙarfi dana rasa dalilin ta.
♡♡♡♡
Kwanciya ta na gyara da sauke numfashi tare da lumshe ido ina ƙoƙarin yin ɗan barci nan gefen kwami dake cikin garden wata safiyar Asabar, naji sawun tafiya dana gane masu shi tsab.
Ina sane da muhimmancin wannan rana, domin ranan ce nake cika shekarar goma sha uku da haihuwa. A wancan lokaci ina cikin baƙin ciki ne ƙwarai, domin ** Hamza Jay El-Turajj** yana shirin tafiya ƙasar waje karatu a jami’ar da ya daɗe yana buri.
Ina ƙoƙarin yin ɗan barci ne domin in manta, na ɗan lokaci, da tafiyarsa da ke matsowa, sawun tafiyar sa dake cike da nutsuwa da izzar sa like the lion he is,ya ratsa dodon kunnena. Ina buɗe ido kuwa, sai ga fuskarsa sunkuye a kaina. Wannan ingarman jikin nasa duk da kasancewar sa matashi d'an shekara goma sha takwas, haka yake da girma da tsayi. Ruf ya rufeni har inuwata ba'a gani na tabbata.
“so… kina nan abun ki duk tsawon wannan lokacin, princess?”
Ya faɗa cikin murya mai laushi, amma tsab na fahimci izgili cikin sautinsa lokacin da ya ambaci kalmar princess.
“H-huh?” na tambaya cikin rashin wayo da ruɗewa dan ban gane me yake nufi ba.
“Yayin da kowa kecan yana wahala da shirye-shiryen liyafarki na yau da daddare, ke kuma kina nan kina jin daɗin rayuwarki,” ya sake faɗa cikin salo na ba’a. “Wannan abin kirki ne sosai, ko ba haka ba?”
“Huh?” na kuma furtawa a hankali da tunani kafin can na tuna da fahimtar cewa lallai kowa na gidan yana ta kai da kawowa da shirye-shiryen birthday d'ina.
Me yake nufi da hakan? Shin yana tsammanin in taimaka wajen shirye-shiryen walimar ne? Hala shine dalilin da ya sa ya kira ni da*princess*, saboda tunanin sa kenan ina abu kamar gimbiyar alhali yasa bani da haƙƙin aikata hakan? Daga inda nake kwance, na tashi na zauna domin in gyara lanƙwasa na ɗan gajeren siket ɗina. Da na miƙe tsaye, sai ya kamo gwiwar hannuna.
“Ina za ki?”
“z-zanje na taimaka…” na amsa murya ta na rawa.
“Babu buƙata,” ya faɗa bayan ya sake maidani na zauna kan bargon. Yanzu kuma gabana ya dawo ya durƙusa . Na zuba masa ido duk cewa bana iya karanta abin da ke fuskarsa ba.
“you know what?, ina farin ciki na kusa tafiya” ya ce yana kallona kai tsaye ido cikin ido.
“Me kake nufi?” na tambaya.
“Mako mai zuwa zan tafi ƙasar waje. Finally ,zan bar nan”
“Ka na farin ciki ne da barin gidan?” na sake tambaya cikin matuƙar mamaki. “Me ya sa ba ka son nan? W–wannan fa gidanku ne…”
Ban gama magana ba, sai ya miƙa jikinsa ya yi stretch tare da sunkuyowa daidai tsayina da dake zaune, yanda kwayar sa zasuyi daidai da nawa. Wani irin juyi hanjin cikina sukayi. Me yake yi haka? Fuskar sa ya ƙara kusanto ta da tawa fuskar, kamar mai shirin sumbata ta…
Da idona dake buɗe so wide, nake kallon yadda gashin girarsa suka haɗu wuri guda, ga kaifin idansa dake cikin nawa kaman zasu hudamin kwanyar kai.
“Ina farin ciki ne saboda zanyi nesa da ganin fuskarki,” ya furta a hankali, kamar yana magana da kansa.
Idanuwansa har yanzu suna cikin nawa . Sai nakeji kamar wuƙa yake sokamin a ƙahon zuciyata da ruhina. ƙiyayyar da yakemin har takai haka. Akan wane dalili?
“M–me ya sa ka tsane ni?” na tambaye shi hawayen dake cikin idona suka gangaro kan kumatuna.
Nan take ya ja numfashi mai ƙarfi, ya kuma fitar da shi da ƙarfi. Sosai nake jin ƙamshin numfashinsa mai daɗi dake dukan fuskata saboda kusancin mu.
“Ba ki fahimta ba ne?” ya ce. “Ba zan taɓa amincewa da ke a matsayin ’yar’uwata ba. Ba za ki taɓa ɗaukar gurbin **Mumtaz** ba!”
“Mumtaz … Mumtaz?”
Yana magana kan ƙaramar kanwarsa wadda ta rasu kafin na shoga cikin ahlin Turajj. Kamar yadda Mommy Jannat ta faɗa mini, Jay da ita ’yan uwa ne dake tsananin ƙaunan junan su. Sau da yawa suna bata lokaci tare cikin lambu suna zane. Dukansu ƙwararru ne sosai a wannan fasaha… kafin Allah ya yi mata rasuwa sanadiyar cutar kansa.
Ban taɓa niyyar ɗaukar matsayin Mumtaz a rayuwarsa ba. Ni abunda nake buri daban. Amma me yasa yake tunanin nufi na kenan na ganin na maye gurbin Mumtaz?
“Me kake nufi?” na tambaya cikin mamaki.
A hankali ya miƙe tsaye, ya juya yana kallon ruwan tabkin da ke kyalli nan gefenmu gwanin sha'awa.
“Ba ki gane ba, Aiza? Daga rana ta yau zaki fara amfani da sunan Turajj name. Takardun ki da komai ya chanza zuwa TURAJJ. Ke ba Turajj bace. Ke Usman ki ke. That is your name. And you will always be Usman” ya faɗa cikin sanyi. “Ba zan iya karɓarki a matsayin sister ba, do you understand?”
Sai kuma cikin fushi ya ƙara cewa, “Ki je ki yi magana da Mama. Ki gaya mata ba za mu iya zama siblings ba. I will never accept it!”
Kawai ya juya cikin fushi ya ti tafiyar sa ya barni nan zaune ina bin bayansa da kallo, Baki a sake ido tab cike da hawaye!
Ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba, domin ita ce ranar da ya fara magana da ni… har ma ya kalle ni. Ban damu ko yana cikin fushi ba a lokacin. Abin da ya fi muhimmanci a gareni shi ne ya yi magana da ni, kuma a ƙarshe ya kira ni da sunana.
A wannan rana kuma na sake aikata wani haukan da ban taɓa ba a rayuwata
Daga kuma nan ne zan iya cewa labarin soyayya ta mai tattare da kalubale ya fara.
♡♡♡♡
Kai tsaye daga nan ciki na nufa wajen Mommy Jannat inda na sameta a private office nata dake gidan. Ina shiga ta d'ago daga takardun da take dubawa tana murmushi har na samu waje na zauna. Babu shakka ko wasi-wasi na tuntube da maganan da Jay yazo min da ita. Y'ar dariya tayi tana rufe file dake gabanta tare da gyara zama dana glass dake fuskarta tace
"Yanzu menene, baki son amfani da sunan Turajj d'in ne?"
Saida na taune lebe murya da dan sanyi nace
"Mommy bana so "
"Saboda me?"
Ta sake tambaya na da d'an mamaki. Numfashi na sake saukewa murya can k'asan makoshi nace
"Saboda bana so na zama kanwarsa Mom"
Shirun da naji tayi bata amsa ba yasa na d'ago da kaina na kalleta. Sosai na hango damuwa cikin kwayar idanta da fargaba. Wata k'ila ko tana tunanin bana san zama a nan dan haka da sauri ina girgiza kai nace
"Ina nufin bana so na zauna matsayin kanwarsa . Ina so na kasance matarsa in the future, Mommy "
Wani irin shiru ne ya rasta d'akin kaman anyi ruwa an d'auke. A take wani gumi naji ya karyomin zuciyata na cewa shikenan kin jawowa kan ki jan gwangwama. Amma wannan shine abunda nake so tsawon rayuwata. Gaskiya ta kawai nake fad'i.
"Don Allah, Mommy"
Na sake furtawa cike da lallami kaman zanyi kuka don har zuwa lokacin ta kasa cewa komai.
Da na sake maganan ne, na lura kaman maganan ta yi tasiri a gare ta. Fuskarta ta fara sauyawa a hankali—daga mamaki zuwa ruɗani, sannan zuwa fahimta. A ƙarshe na ga murmushi ya bayyana kan leɓenta.
“Wannan shi ne abin da ki ke so da gaske, Aiza?” ta tambaya.
Kai na sake d'agawa alamun, eh!
No turning back now, Aiza, na sake tunatar da kaina.
“To, shikenan,” ta ce. “Haka za ta kasance! Za ki auri Jay ,InshaAllahu . Alkwari ne wannan ”
Saboda wannan confession da nayi, Mama ta sanar a gaban dukkan baƙinmu da y'an uwa, wajen birthday party dina, cewa ni, Aiza Usman, zan kasance matar ɗanta guda ɗai tak, Hamza Jay El-Turajj.
I was engaged at thirteen.
A lokacin sanarwar, Jay bai shirya ba ko kaɗan. Ina tsammani, ya fi Mommy Jannat girgiza sau goma fiye da yadda ta girgiza a d'azu da na yi magana da ita.
Shin abin ya girgiza ka, Hamza?
Wani irin kallo ya watsomin cike da tsananin tsana, tabbas da a ce idansa wuƙa ce, da tuni na sheka lahira saboda kaifin su. He was so disappointed.
Taron da bai zauna an gama dashi ba kenan ,ya fice. Ni kuma, like an idiot, na bi shi a guje. Juyowa ya yi ya kalle ni da wani irin icy glare, kafin ya yi magana cikin muryar da ta fi kowace sanyi da ban taɓa jin anyi min magan da irin taba
“Ba za ki taɓa cin nasara a kaina ba, Aiza.”
Saida tsigar jikina ta tashi saboda yanda ya kira sunana da full venom. Bai bari na bashi amsa ba ya juya da big strides ya barni a tsaye k'irjina na harbawa.
Washegari kuwa ya bar mansion din zuwa k'asar waje. Hakan ya k'ara tabbatar min sosai yake cikin matuƙar fushi da Mama da ni,tunda har bai iya jira mako ya zagayo kaman yanda tafiyar take . He had finally left—.
Lokacin rani ne sanda da ya tafi, haka nan babu wata alama dake nuni da zai dawo nan kusa. Na fahimci cewa, watakila wannan ce rayuwar da yake so—ya kasance shi kaɗai, ya yi rayuwar sa shi kad'ai babu tunanin ƙaramar yarinya dake da buri a kansa . Nasan yana farin ciki da daina ganina.
Zuwan azumi na Ramadan na jira dawowarsa , ina tunanin wataƙila ya zo ya yi sallar Eid a nan—amma bai dawo ba.
Haka, na sake jiran dawowarsa a lokacin fourteen birthday d'ina tunda Mommy tace ta tura masa, sosai na saka rai da zuwan nasa… shima haka shiru ,Malam yaci shirwa..
Haka nayi ta jiran dowawar sa duk Eid … da kuma duk wani lokacin rani , Amma har yanzu, bai dawo gida ba.
Mommy Jannat tana yawan cewa yanayin karatunsa ne ya hanashi dowawa. Yana karatu b'angaren da ya ɗauka na Business Administration . Yanzu shine abunda ya fi fifiko a gareshi.
Sai nake tambayar kaina, me ya sa bai zaɓi Fannin Zane-zane (Fine Arts) ba. Saboda yanda yake da kwazo da basirar zane. Mama ta ce Jay, kasancewarsa shi kaɗai ne magajin arzikin ahlin Turajj, ba shi da zaɓi. Idan ya kammala jami’a, shi ne zai karɓi dukiyoyin ahli da harkokin kasuwancinsu, don haka dole ne ya ɗauki fannin da ya shafi kasuwanci.
Har ila yau Mom na sake tabbatar min cewa Jay ,ba shi da wani zaɓi face ya aure ni nan gaba. Saboda ni, nayi imanin mom zatayi komai domin taga ta ba ni abin da nake so. Bayan haka ma, ni ce ’yar da ta daɗe tana fata ta samu.
Tabbas, za ku iya cewa na kasance mutum mai son kai. Eh, watakila gaskiya ne—na kasance mutum mai son kai na. Kuma a wancan lokacin, ban damu da hakan ba sam.
♡♡♡♡
So this is life. A yau ne nake cika shekara goma sha bakwai cir a duniya. Shekara hud'u kenan da tafiyar Hamza abroad karatu, har yau bai sake waiwayo gida ba. Tun fourteen birthday d'ina na daina celebrating saboda ko anyi bana jindaɗin sa, tunda wanda nakewa ba zuwa yake ba. I want him to come and see how much i have grown. Ko waya sai ya d'auki lokaci bai kira ba sai Mom ta kirashi tayi fad'a sosai. Nasan kuma duk yanayin hakan ne saboda ya gujewa magana dani. Tun safe nacewa Mom yau bana buk'atar wani celebrating nida ita ma kawai ya isa. Bata musa ba dan haka bayan anyi la'asar na fita kasuwa da kaina siyo d'an fruits da chocolate da zanyi amfani dashi wajen had'a mana dinner. A Daidaita na d'auka har bakin kasuwa na shiga na siyi abunda zan siya kafin na fito nayi mall don siyan kayan desserts. Nanma ban jima ba na fito ganin akwai sauran lokaci na wuce gidan su Teemah.
Kasancewar muna hutun k'arshen mako, kusan duk k'awayen nawa sun tafi hutu. Teemah ce kad'ai ke gari saboda bata cika san yawo ba kamanni. Can gidan nasu na shashante da hira ban fargaba dare ya yi. A gaggauce na fito bayan nayi sallah magriba nayi gida kai tsaye. Bakin layin mu duk da cewa titine sambal daya shiga har bakin gate namu, a bakin layin na sauka na shiga da k'afa. Karya kwanata kuwa keda wuya na hango wata dank'areriyar Bentley fake tsakiyar titin kaman mutuwa tayi. D'an jim na tsaya ina kallon motar saboda layin ya yi shiru sai hasken fitilu daya haske. Jikina ya bani wannan motar wajen Mom tazo dan haka na nufi motar da d'an sauri dan na taimaka, sai dai kafin na kai motar ta tashi.
Chak na tsaya ina kallon motar dake tunkarar gate namu a mugun hankali . Hakan kawai k'irjina ya harba sanda aka buɗe gate motar ta kunna kai ciki. Tambayar guda d'aya ce cikin raina, waye yazo wajen Mom?? Me yasa zuciyata ke bugawa da k'arfi?
Share fisabillahi!!
[17/01, 10:35 am] Ashantyluv: 【HAMZAH】
𝓂𝓎 𝓅ℴ𝓈𝓈ℯ𝓈𝓈𝒾ℴ𝓃𝓈!
✆-08140754777
❷
“Ina Mom?” na tambayi Maryam, ɗaya daga cikin masu aikin gidan, lokacin da na shiga falo.
“Tana ofis. Ta ce in tunatar da ke game da abincin dare.”
“yanzu zan shirya cikin mintuna goma sha biyar,InshaAllahu ” na faɗa ina murmushi yayin da nake hawa sama don canza kaya.
“Af, waye baƙon da yazo?” na joya ina tambayar Maryam, amma tuni ta ɓace daga wajen..
Da wannan tambayar da babu mai amsa ita a rai, na wuce d'aki da sauri don kimtsawa.
Shekara goma sha bakwai. Tabbas Lokaci na tafiya . Hoda nake shafawa da ɗan blush a kan kumatuna da kuma *lip gloss* a lebena, kafin na zubawa fuskata ido ta cikin madubi . Da ace Mame da Abey suna raye, da sai sunyi matuƙar farin ciki da yanda na zama na kuma girma zuwa… kyakkyawar budurwa. Sau da yawa Mommy Jannat tana gaya mini yadda nake da kyau, amma sai a kwanan nan ne na fara gasgatawa da kuma yabon kyau da Allah ya bani. Mutane kullum suna cewa ina da kyawawan idanu. Mom ta taɓa cewa na gaje su ne daga wajen Mama ta. Tabbas mahaifiyata kaman tayi ka ki ne ta tofar dani. Daga gashin kaina dake curly baki, zuwa idanuwana masu launin ruwan kasa masu bayyana motsin rai, dogayen gashin idanu na masu lanƙwasawa, jajayen lebena kamar ceri, har zuwa siririyan jikina da farin fatata — komai na gaje su daga Mama na.
Amma tsananin imani na ga soyayya da sha’awa, da kuma son samun *rayuwa mai daɗi ta har abada?*, daga Abey na gaje su. Shi ne ya buɗe min idanu cewa soyayya koyaushe tana yiwuwa, ko da a mafi lokaci na tsanani da wahala ne. Abey ya kasance mutum da ya yi tsananin imani da soyayya.
Sosai ina kewar su! Idan na tuna haɗarin da ya sukayi sosai zuciyata ke raɗaɗi da ciwo.
Ƙarar bugun ƙofata da aka kwankwas ya katse mun tunani. Hawayen da suka gangaro kumatuna na share, kafin na nufi ƙofar na buɗe da sauri.
“Aiza, Mommy Jannat ta aiko ni in sanar da ke cewa abinci ya kammalo”
ɗaya daga cikin ma'aikata gidan ce mai suna Mansura..
“Na gode, Mansura. Yanzun nan zan zo nan da minti ɗaya, InshaAllahu ” na amsa mata ina murmushi, kafin na yi sauri na koma ciki domin na ƙara duba kaina a mudubi , zaman mayafina na gyara dake kaina na d'aure gashina kasancewar doguwar riga ce a jikina y'ar kanti mai ɗan hannu daya kai cinyar hannu, saman rigar anyi masa tattara daga wajen kugu zuwa kirji ,hakan ya bawa madaidaitan boobs nawa sake tasowa sunyi das gwanin sha'awa cikin rigar.
Turaren na sake fesawa masu daɗin kamshi da sanyi kafin na saka flat takarmi nayi waje. Sam ban damu da yanayin shigata ba saboda nasan cewa gida nake kuma idan har ba baki da ban sansu ba, bana fita haka saida mayafi ko hijabi.
A hankali nake saukowa daga bene ina d'an humming na wankar larabci don har yanzu zuciyata cike take da kunci da damuwa. Ina fargaba da tsoron ɗan baƙin ciki da damuwar dake zuciyata zai lalata min wannan dare. A yau, shekara tara ke nan da na zama marainiya… but , i have Mommy Jannat dake bani kulawa da shiga damuwa a irin wannan lokaci da nake buƙatar wanda zai sharemin hawaye. Tsakani na da ita sai godiya domin bani da abunda zan saka mata da alkhairin da take mun.
Duk ina na wuce sai naci karo da masu aikin gidan dake zubamin murmushi da Addu'a na sake zagayowar shekarar haihuwa ta. Sosai kuma suka yaba da shigata da zuzuta kyau da nayi. Ina y'ar dariya nace musu“na gode.”
“Dukkannin mu nan muna matuƙar taya ki farin ciki , Aiza. Akwai kyauta ta musamman a gare ki,” Huzaimat d'aya daga cikinsu wanda zan iya cewa sa'a tace ko ta d'an girmini kad'an tace tana dariya a hankali. Na lura kamar kaman tana jin kunyar wani abu. Kunyar me take ji?
Shin suna shirya mini suprise party ne? Na wuce da wannan tunanin. Ban fahimci abin da take nufi ba har sai da na kai bakin ƙofar da ke kaiwa ɗakin cin abinci.
Ya Rabbi! Chak na tsaya bakin kofa zuciyata na barazanar tsayawa.
can, tsaye kusa da Mommy, jingine da gefen jikinsa a kan babban teburin cin abinci na irin zubin tsohon zamani, is my long lost Jay!
Hamzah Jay El-Turajj! Shi ne baƙon? Shi ne mutumin da ke cikin motar nan? Lallai wannan babbar kyauta ce a gareni!
Shekaru nawa ban sashi a ido na ba! . 4 years?