Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
batamun rai kayan dake jikinta wasu y'an iskan riga da atamfa da sukayi masifar kamata, wuyan rigar duk rabin k'irjinta a waje kuma si turo k'irjin take gaba. Mom da ita fuskarta ke cikin raha da annuri tana ganina tayi kici-kicin ta b'ata rai. Da kyar na iya d'aga k'afata na k'asara naja kureja ta dake fuskarta sa zauna har zuwa lokacin yana kallona kaman yanda nima nake kallonsa. Saida yaga na zauna ya d'auke kai na sauke wata y'ar k'aramar ajiyar zuciya tare da maida hankalina kan mom nace cike da ladabi. "Mommy ina kwana?" "Lafiya " Ta amsa min fuskarta babu yabo babu fallasa. Ta gefe ido naga Jay ya kalleni mom kaman da d'an mamakin yanda ta amsamun. Murmushi nayi ban damu ba na miƙe da sauri na k'arasa zuba mata abincin na ajiye mata gabanta. Bata kalleni ba ta d'auki cokali ta faraci na sauke ajiyar zuciya a hankali. A hankali na sake juyawa na kalli barin da yake zaune daidai yana d'auke kansa daga kallona muka had'a ido da Jennifer. Wani mugun kallo ta watsamin dake tattare da wani murmushi nima na mayar mata da martani. D'an mamaki ya nuna kan fuskarta da alama batayi zaton zata ga rashin tsoro kan fuskata kaman jiya ba. Ni abincin ma kasa ci nayi sai cokalin da nake ta juyowa cikin kwano. Gaba d'aya hankalina yana can ta yanda zan fara tunkarar Jay da wannan maganan tunda Allah ya dawo dashi. Ban taɓa tsammanin zai dawo ba yau bayan munyi wayar nan. Kafin ya koma dole na warware masa dukkanin matsalar dake faru cikin gidannan before Jennifer taci nasara. Miƙewar da ya yi yasa na d'ago na kalleshi unexpected ni yake kallo muna had'a ido ya d'auke kai ya yi waje . Tunanin miƙewa nake na bishi Jennifer ta riga da hanzari tayi waje bayan ta jefamin wani mugun kallo. Zama zakiyi to? Zuciyata ta ingizani na yunƙura da sauri zan tashi mom tace "Ina zaki? Kul ki ka kuskura naga k'afar ki wajen Hamzah. Sai na sassaba miki walahi. Wato ya dawo zaki fara masa wannan shegen nacin naki na jaraba ko? Wai ke wace irin zuciya ke dake ? Ace mutum bashi da zuciya, ance ba'a sonshi ko dole ne sai kin aure shi? To ki bude kunnen ki kije, Hamzah, Jennifer zan aura masa InshaAllahu domin abunda ya kawoshi gidannan kenan. Saboda haka ina gargadin ki har ya koma kar naga k'afar ki inda yake. Kar ki jefa zargi tsananin sa da yarinyar kirki mai mutumci data san ya kamata. Wacce ta rike tarbiyar da iyayenta suka bata bata kawo maza har cikin gida saboda lalacewa" Tunda ta fara maganan zuciyata ke wani irin ciwo na had'iye kukan daketa taso min. Kai kawai na sunkuyar ina jin irin diban albarkan da mom kemin. Babu abunda yafi tsayamin a rai sai kar na shiga tsakaninsu kuma abunda ya kawo Jay kenan, auren sa da Jennifer. Saida ta gama muryata na tsanani rawa nace "Kiyi hak'uri, InshaAllahu zan kiyaye mo..." "A'a kul ki ka k'arasa domin ni a yanzu ai ba uwa ki ka d'aukeni ba tunda har ki ke neman b'ata min suna a gari. Munafuka sai k'asa-kasa ki ke da kai kaman mutuniyar kirki. To ai anyi walkiya mun gani. Allah ya shirye ki" Tana gama fad'an ta ta miƙe ta haura sama ta barni nan a zaune. Duk yanda na jure saida wasu hawaye masu zafi suka wankemin fuska. Karki manta Aiza ,mom bata san abunda take ba kar ki riketa a rai. K'afad'ata da aka dafa ya dawo dani daga tunanin dana fad'a na d'ago a hankali. Shamsiya ce tsaye idanta ya yi jazur kaman zatayi kuka. Murya a raunane tace "Kiyi ta hak'uri Aiza kiyi ta gayawa Allah. InshaAllahu zamuyi k'ok'arin taya ki da Addu'a kuma zamu taimaka domin ganin an tona mata asiri wajen Sir Hamzah. " D'an murmushi nayi na goge hawayen dake bin kuncina na miƙe ina cewa na gode. D'akina na koma ina tunanin ta yanda zan raba Jennifer da wannan y'ar tsanan da take juya tunanin mom. Taya zan samu nasarar hakan?. Tunda na shige d'aki ban sake lek'owa ba don nemawa zuciyata salama da lafiya . nima ina so nayi healing zuciyata. Ina so nayi moving on kan mutumin da baya jin komai a kaina, amma kuma hakan ba yana nufin zan bari Jennifer ta aure shi bane. Washegari ma ban fito na sai Maryam ce ta kawomin abinci da safe. Sai bayan azahar na fito duk da kashedin mom ya zama dole nayi magana da Jay. Kintata nayi a yanzu nasan duk sanda yake gida yana garden nashi don haka na fito sanye da doguwar riga y'ar kanti da mayafi dana lulluba a kaina. Saida na fara dubawa na tambayi Maryam tace min mom na d'aki na fito da sauri nayi waje. Tunda na tunkari garden d'in zuciyata ke harbawa da k'arfi. Ile kuwa ina saka kaina ciki na fara cin karo dashi zaune yana zane Jennifer gefen cikin riga da wando. Daga nan inda nake tsaye yanda rana ke reflecting a kansu Jennifer tana y'ar dariya ta kissa ,idan tayi dariya ta wani d'an kwanta gefensa kaman zata kwanta masa a k'irji. Zakayi tunani wani abu ya gaya mata dake sata farin ciki duk da cewa fuskarsa tana nan very emotionless. Babu ta yanda zaka fuskanci abunda ke ransa. Fararen kayane jikinsa na Pakistan da sukayi masifar yi masa kyau ya tufke gashin sa tsakiyar kansa. K'afarsa sanye cikin silifas fari daya k'arawa kafar kyau. Abu daya tsayamin makogaro na had'iye zuciyata na wani irin zafi. Baki na cije ina jan numfashi da kiran sunan Allah. Abun da ciwo duk da cewa ba wani attention yake bata ba, yanda take zaune ga hips nata ga nashi va tare da ya yi snapping tana tab'a shi ba. Kaman mashi ya sake sokamin a kahon zuci. Is like kaman yana k'ara bani warning ne I'm not his type. Kai na jijjiga da ajiye emotions nawa gefe na tunkaresu. Chak naga ya tsaya da abunda yake ya wani irin juyowa da mugun slow ya kalleni. Zuciyata tayi wani tsalle nayi saurin basarwa bayan na tsaya gabansu. Dariya ta kusa kwacemin saboda kallon da Jennifer tamin. Tayi ta gama domin bata ita nake ba. A hankali nace "Can we talk, please ?" Wani irin kallona ya yi tun daga sama har k'asa da sai naji duk na tsargu kafin ya miƙe da wata izza yace "Ok" Kawai ya wuce. Kallon Jennifer nayi dake kallonsa da b'acin rai na mata murmushi a hankali nace "Tsoron me ki ke ji? " Wani mugun harara ta watsamin tana miƙewa tsaye tace "Naga kaman kan ki har yanzu yana rawa. Kina tunanin tsoron ki yasa banga k'arshen ki a gidannan ba? Baki gane bane? Ke wata k'aramar abace a gareni da yatsuna kawai zan murza ..and boom babinki ya shafe a gidannan. Kina underestimating nawa ne saboda kinga ina raga miki. But not anymore" Ta wuce fuu ta fice daga wajen na sauke ajiyar zuciya da cewa Allah ya fiki. Can wajen wata kyebantacciyar bishiyar mango na same jingina. Zuciyata na bugawa na nufeshi da tararradin yanda zai d'auki maganan da zanzo masa da ita mai girma. Sai dai me, Maryam ce ta shigo a guje tana kiransa wai ga Mommy cen ta faɗo daga bene. Dagani harshi muka wuce da bala'in gudu cikin gida. A rud'e nake kiran mom sanda muka shiga tana zaune kan kujera Jennifer gefen k'afarta rike da k'afar tana matsawa dayi mata sannu. Wani relief naji ya saukan min sanda ta d'ago ganin Jay ya tunkaro ta cikin tashin hankali. Tana d'an murmushi ganin yanda yake ta tambayar ta lafiya tace "Bafa wani abu bane, k'arshen step ne na d'an zame na fad'i. Babu komai kar ka damu ka gani.." Kafar take nuna masa daya k'arba hannun Jennifer yana dubawa. "Sannu mom" Nace muryata cike da damuwa. Ina ga ki bata kula dani ba ne sai yanzu ai kuwa ta juyo rai a b'ace "Au wato duk kashedin da nayi miki, binsa ki ka yi?" Kai na sunkuyar katsa bance komai. A hankali ya d'aga kai ya kalli mom dake jefan Aiza da mugun kallo. Mamaki sosai ya kamasa da wannan changin. Tun jiya daya dawo ya lura akwai abunda ke faruwa a gidan. Amma har menene haka ya b'atawa mom rai da take yiwa dear Aiza nata irin wannan fad'a da tsawa haka? "Wai meke faruwa ne?" Ya yi tambayar yana kallon mom. Aikuwa mom ta fara cikin fada kaman zata ari baki "Menene ma bai faru ba. Kaga wannan yarinyar mara mutunci bayan tafiyar ka halayyar data tsira? Banda yawace-yawace data tsira saboda bata da mutunci har d'aki ta kawomin gardi cikin gidannan. Turmi da tabarya na kamata da wani k'aton namiji kan gado" "W....w...What??" Ya yi magana muryar sa na tsananin rawa. Kaina dake sunkuye na d'ago na kalleshi da idona dake cike tab da hawaye. Kallona yake cikin tsananin mamaki da tuajjabi. Amma kuma is like kaman bai yarda da abunda ake gaya masa ba. "Taya hakan zai faru mom? Aiza d'in ne da bin maza? Kuma har cikin gida?Anya kuwa?" Aikuwa mom ta sake hayyakowa. "Ok ga jahila da batasan abunda take ba ko? Kanaso kace sharri zanyi mata ko me? Ni in baka yarda da maganata ba, aiga shedu nan a gidan. Jennifer gaya masa sa abunda ki ka sani ko . Ina su Maryam?" Tana kiran sunan Jennifer na kalleta da sauri muka had'a. K'asa-kasa ta kashemin ido a fakaice kafin ta d'auke ta kalli Jay dake kallona kaman yaga wata sabuwar halitta. "Mom kiyi hak'uri na b'oye miki saboda gudun b'acin ranki. Ranan walahi har asibiti na rakata tayi abortion na k'aramin ciki. Rokona tayi na rufa mata asiri saboda kar ki tsaneta. Idan baku yarda ba akwai takardu da sheda har asibitin dana kaita aka zubar mata da cikin" Wani irin tafa hannu mom tayi tana salati sai kuma ta rushe da kuka. Tsananin mamaki da tuajjabi yasa na kasa motsi sai Jennifer dana zubawa ido ina jin yanda idan Jay ke kaina kaman zai huda min kai. Kaman wacce aka mara na juya a guje nayi kitchen. Kai tsaye kan kanta nayi na d'auko sharbibiyr wuk'a sabuwa fil na fito da wani bala'in gudu nayi kan Jennifer. Yau wahali sai dai ko ni ko ita a gidannan. Idan ita makirace ni kuma mahaukaciya ce..... Yes Aiza. Ci uban shegiya! Shin ya kuke ganin wannan tafiyar zata kaya? Hamzah zai yarda da wannan kazafin da aka yiwa Aiza? Wane makoma soyayya su zata kasance nan gaba? Ya makomar Jennifer? A hanzarta ayi payment a nuna min kaunan nan dai da ake nunawa.! An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6