Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
Hajiya Nawwara ta dawo take cewa Jennifer zata zauna a nan na d'an wasu kwanaki kafin Hajiya. Nawwara ta dawo daga US taron yan siyasa da zata. Ina kallo Jay yazo ya wuce ko kurar data nebomu bai kalla ba hakan kuma ya d'an kwantar mun da hankali. D'akina mom tace muje mu kwanta idan mun gama kallo ta wuce sama ta barmu nan zaune. Shiru ya ratsa tsakanin mu dana gaji da zama nime nayi d'aki Jennifer biye dani. Muna shige kai tsaye gadona ta haye ta kwanta abun ta tunma kafin nayi mata izni. Ikon Allah. Kai na girgiza na d'auko kayan barci na chanza zuwa doguwar riga mat santsi kafin na koma kan kujera da bargo a hannuna na kwanta ina addu'a. Nayi tunanin ma tayi barci danaji tayi shiru saida naja bargo zan rufe jiki naga ta yunƙura ta tashi ta hau cire nata kayan. Kai na girgiza na juya mata. Washegari, i planned not to be visible in the mansion. Bayan the humiliation dana fuskanta wajen Jay jiya , i was as thesame time hurt. Mutane baza su fahimci dalilin da ya sa yarinya ’yar shekara goma sha bakwai za ta ji haka ba, ta kuma ɗauki abun da matuƙar muhimmanci haka. But what can i do, this is what i felt. Na jira shi tsawon shekaru huɗu, yanzu da ya dawo gida , a yanzu da na faɗa masa abin dake cikin zuciyata, sai ya zage ni . He called me a fool! Da zaifi kyau ya ce mini bai jin abunda nake ji. Aƙalla hakan gaskiyar sace. Amma maimakon haka, sai ya ce i was a fool to feel that way saboda kawai ya yi shattering heart d'ina. He regarded me a fool. That really hurt me much. Don mantawa da shi na ɗan lokaci—kamar iyawa zanyi— na kulle kaina a ɗaki. Mom sau biyu tana shigowa fuskantar da tayi ina son kad'aicewa bata takurani na fito. Can kasan zuciyata nata azalzalata dana fito kasancewar Jennifer na gidan but ina son samun dignity nima ko na warke daga ciwon daya kunsa kin. Tunda har ke baki samu chance ba wajen HAMZAH shekara da shekaru, ina ki ke tunanin ita zata iya samu daga shigowar ta gidan jiya? Wannan ne abinda zuciyata keta gayamin hankalina na d'an kwanciya. Ina tsaye gaban mudubi ina taje gashina dana wanke bayan nayi wanka sai gata ta shigo da wani isa har abun ta bani mamaki. Daga jiya zuwa yau nunawa take kaman ta fini iko nida d'akina. Wani kallo ta watsamin tayi hanyar toilet. Numfashi naja mai k'arfi saboda wani azababben kamshi daya doki hancina bayan ta wuce. Wannan kamshi kaf duniya mutum d'aya me nasan yake irinsa koda yaushe. JAY!!. Yanda zuciyata take wani irin tsananin harbawa saida na kai hannu na dafe ina d'an hak'i. Me yasa take kamshin Jay? Taya akayi kamshin turaren sa ya shafeta? Koni bai taba bari na ratsa kusa dashi haka ba bare har nayi kamshin turaren sa haka. What happen da bana kusa? Kar dai, kar dai... ke Aiza ke nemo nutsuwar ki. Zuciyata tayi saurin katseni to amma taya zan nemo nutsuwata cikin wannan yanayi. Hawaye naji masu zafi sun cika min ido nayi saurin had'iyewa jin motsin fitowarta daga toilet. Sanye da tawul nawa ta fito daya tsaya mata kugu ta wuce wajen jakarta ta fito da kaya doguwar riga y'ar kanti da yar top kaman jacket sai hula ta ajiye kan gado. Duk ina kallonta ta nufo wajen mudubin batacemin uffan ba na matsa gefe ina kallon ikon Allah. Saida ta gama shafa mai ta mulke jikinta da kayan kwalliyata da feshe turare sannan ta wuce ta saka kaya hankali kwance. Tana gamawa ta kama hanya zatayi daga bakin k'ofa tace "Mom tace na gaya miki ki shirya ki fito ki rakani shopping. " Ko kafin nace yanzu? Ta fice abunta. D'an turus na tsaya ina kallon k'ofar. Na fuskanci yarinyar tana da rainin hankali fa. Jiya gaban mom don munafurci harda cewa zamu zama best friends, amma ga yanda takemun abu kaman wata y'arta. Yar kwafa nayi taci sa'a ni mutum ne da banson hayaniya da tashin hankali, inba dan haka ba da tuni na taka mata birki. Duk wannan ji da kan da take ni ya kamata nayi saboda idan gata ne da arziƙi nasan sai dai ta shafa taji, to amma nima bani da ikon yin farga da abunda ba nawa ba duk da Mom na yawan cewa duk abunda ta mallaka nawa da Jay. Saboda tace mom shi yasa na shirya cikin riga da wando masu d'an fad'i na d'ora doguwar jacket kan rigar data sauka har gwiwa. Mayafi nasa daya shiga da kayan nayi rolling kaina na fito ko wayata ban d'auko ba. Ina saukowa na sameta zaune falon ita dasu Maryam sai basu umarni take babu daman suki bin abunda tace. Ido muka had'a da Maryam dake k'ok'arin shigewa kitchen. Na fuskanci kaman tana so ta gayamin wani abu. "Muje" Kawai tace tayi waje nabi bayanta da kallo. Ina mom d'in to? Nayi tunanin komawa nace mata sai mun dawo amma gyada kai da tunanin tunda ita ta aiko tasan da fitar. Ina fitowa direba already ya faka mota bakin porch harta shige ta hakimce kaman yar masu gida. Murfin motar na kama zan buɗe nima na shiga naji tace "Ki zauna a gaba mana" Au Allah?? D'an ido na zuba mata na dai gyada kai na buɗe gidan gaban na zauna tunda nasan Hamisu sosai da sosai. Mutum ne mai barkwanci da ban dariya. Yana tashin motar kaman ance na kalli waje. Daga can saman relar kyebantaccen wajen da mom tasa akayi musamman saboda Hamzah, shine tsaye jikin glass daya zagaye wajen hannunsa daya cikin aljihun wandonsa d'aya rike da mug na tea. D'an yawu na had'iye saboda wani irin kyau da ya yi hasken fitilu sun haskashi tako ina kaman rana duk da kasancewar dare ne. Ash riga ce jikinsa da shorts gashin sa iska nata kad'awa . He look so damn handsome and perfect. Idansa kur kan motar har muka fice daga gidan duk da cewa bana tunanin ya ganni. D'an k'aramin sauti naji ya fito daga bakin Jennifer kaman tsaki dake baya na juyo ina kallonta sai naga wayarta take dubawa. Ban kawo komai ba na juya naci gaba da kallon titi Hamisu na d'an kawo zance lokaci zuwa lokaci na raha. Tafkeken mall ne muka tsaya nan kusa da shop right dake bakin teku na abuja. Ita tayi jagora ta fara kwasar kaya ina binta kawai. Kayan makeup ne ta kwasa dasu turare banda uban dogayen riguna da atamfofi. Duk ina kallonta ina mamakin ita kuwa me zatayi duk da wannan kayan haka? Mun jima tana kwasar kaya kafin mu wuce wajen biya. Atm card ta fito dashi wani baki da gold. Kallo d'aya nayi masa nasan nawaye card din. JAY! Har ila yau dai yana ta shattering heart d'ina into millions pieces. Wai shin ko hakan da yake yana bani sak'o ne nasan matsayi na kuma fita daga sabgarsa? Inba haka ba har Jennifer ta kai matsayin da zai bata card nashi ta fito siyayya da kuɗin sa?. Tabbas I'm the fool kaman yanda yace. Duk yanda nake k'ok'arin rike hawayena saida suka cikamin ido naita sauke numfashi saboda na maidasu. A hankali ta juyo ta kalleni. Yanzu na daina ganin laifin ta. Dole tayi isa da takama tunda ta taka matsayin dani na kasa takawa. "Sorry na manta. Da Allah ko zaki d'an dubamin wani perfume Channel ,sunce suna dashi?" "Ok" Kawai nace muryata na rawa na juya da sauri nayi b'angaren turare saboda gudun rushewa da kuka. Neman duniya nayi banga wani turare channel ba na dawo na gaya mata ,sai me? Tace ajiye ni inda ki ka barni. Nayi tunanin ko ta fita saka kayan cikin mota dan haka na fito cikin sauri amma kaf harabar wajen babu irin motar da muka zo da ita bare kurarta. Innalillahi wa innalillahi raji'un!. Tafiya tayi ta barni a nan a wannan daren?? Taya zan koma gida babu ko sisi a hannuna gashi ko wayata ban fito da ita bare na kira mom?. What is happening!. Shar kawai naji hawaye sun wankemin fuska na samu waje cikin harabar wajen dake cike da mutane na makure waje d'aya. Ok! This Jennifer is a bitch😤.... [17/01, 10:35 am] Ashantyluv: 【HAMZAH】 𝓂𝓎 𝓅ℴ𝓈𝓈ℯ𝓈𝓈𝒾ℴ𝓃𝓈! ✆-08140754777 WhatsApp group! https://chat.whatsapp.com/DaatWeTyf3M59ZwHORMsIi ➎ "Hi. Baby kina jiran wani ne?" A hankali na d'aga kaina daga inda nake takure. Wani handsome black guy ne tsaye da wani guy d'in gefensa. Dukkanin su suna sanye da manyan kaya. Kai na daga tare da miƙewa cikin sauri nayi hanyar waje suka biyoni. Yanzu d'ayan ne ya yi magana "Do Allah ki tsaya ki sauraremu. Munga kaman kina jiran wani ne sai mu rage miki hanya" Murya ta na mugun rawa nace na gode ina tafiya ban tsaya ba saboda yanda zuciyata ke gudu. Gani nake maganan ma kawai dana amsa musu wani mugun laifin nayi. Ganin bazan tsaya ba har mun yi nesa da mall d'in na farkon ya yi saurin bawa d'ayan mukullin motar yana cewa "D'auko motar." Da sauri ya juya shi kuma ya cigaba da bina yana magiya na tsaya na saurareshi. Tafiya nake ni kaina ban san inda zan dosa ba ga wad'annan mayun suna biye dani sai magiya sukemin kaman ,bacin haka sosai mukayi tafiyar da tun ina gane hanyar na har daina. Chak na tsaya wajen wani bada hannu da titin ya kasu wajen hud'u. Yanzu ina zanbi gashi dare na sakeyi? Baki da wata hanya daya wuce ki bari wad'annan mutanen su taimaka miki tunda har suka biyo ki har haka. Idan ma sunzo da wata manufa InshaAllahu bazau samu nasara a kan ki. Maganan da zuciyata tamin kenan na sauke numfashi tare da juyo a hankali na kallesu. Murya can k'asan makoshi nace "Maitama.." "Na'am " Guy d'in matso don ya fuskanci abunda nace. Na sake cewa "Maitama zaku kaini" "Ooh, to shiga mota. Nagode da ki ka bari na taimaka miki" Murfin motar ya buɗemin na d'an zubawa motar ido. Bak'ar BMW ce da har glass nata akwai bak'in tint. Idan na cigaba da tsayuwa a nan bansan yanda zanyi ba wataƙila kuma na banza suzo duk dai wad'annan dinma Allah ne kaɗai yasan gaskiyar su. A hankali na matsa na shiga bakina da bismillah. Guy d'in ya juyo bayan d'ayan ya tashi motar yana murmushi yace "Sai dai baki gayamin sunan ki ba har yanzu" Kallo d'aya na masa na d'auke kai ina kallon window. Y'ar dariya na sakeji ya yi kafin ya cigaba da cewa "Tunda kin ki gayamin sunan ki, ni sunana Nabeel. Wannan kuma abokina ne Jabeer sunan sa" Ko uffan bance ba. Da ace zasu san halin da zuciyata take ciki da wataƙila ya yi shiru ya barni naji da abunda nakeji. Minti talatin muka shiga Maitama sai a lokacin na sauke numfashi duk da cewa guys d'in har zuwa lokacin sai zuba suke amma ko ehm ta kasa fitowa daga gareni. Daga nan ma idan sun ajiyeni zan iya karasawa gida don haka nace da d'an k'arfi "Ku ajiye ni anan." Kallan juna sukayi kafin Jabeer ya faka motar nay saurin kama murfin na buɗe nayi waje. Fitowata ya yi daidai ta wucewar wata dank'areriyar ford a guje amma tana yin gaba kad'an taci wani uban birki kiiii saida kura ta tashi. Ras-ras gabana ya fad'i na zubawa motar ido na kasa motsi daga inda nake tsaye Nabeel ya sani gaba sai roko yake na bashi number wayata. Kaman irin a slow motion d'in nan naga motar ta buɗe ya sako k'afarsa dake cikin wani farin cambus kafin ya sanyo jikinsa gaba d'aya waje. Gajeren wando ne jikinsa ashe daya kai gwiwar k'afarsa sai hoodie riga kaman sweater mai hula dake kife a kansa. And oh boy!. Wani irin b'acin rai ne kwance fuskarsa da zan iya cewa har wani huci naga kaman yana fitarwa. Saida naji kaman na ruga a guje saboda yanda ya tunkaro mu kaman wani bijimin zaki. A yanzu Jabeer da Nabeel suma sun lura dashi don haka suka zuba masa ido yana tunkaro mu. Innalillahi wa innalillahi raji'un. Na shiga uku ni Aiza! "Malam, sannu barka dai. Ka santa ne?" Nabeel ya yi k'arfin halin furtawa bayan ya k'araso tare da mike masa hannu. Wani kallo yabi hannun nasa dashi kafin ya sauke idannan nasa da sukayi wani mugun ja kaman gauta a kaina. Saida na had'iye wani yawu daya tokareni a makogaro ina sake lafewa bayan su Nabeel. Ban taɓa ganin Hamzah a irin wannan yanayin ba. Why is he angry?. A kausashe yace "Move" Ai baima gama rufe baki ba na tsinci kafafuwana na nufar motar da mugun sauri kaman zan kifa, sai dai kafin na kai naji wuff anyi sama dani babu shiri na saki wata k'aramar k'ara tare da rike wuyansa ido waje nake kallonsa fuskarsa dake so expressionless. Tambaya d'aya why is he angry haka? Ko yana tunanin su Nabeel samarina ne? 'Wash'na furta da d'an kara saboda wani irin buɗe motar da ya yi ya wullani baya . Daga Nabeel har Jabeer tsananin mamaki ne ya kamasu da suka kasa tabuka komai suna kallo har yaci wani mugun reverse ya barsu nan tsaye baki a hangame kaman waɗan da aka d'aure. Baza kuso kuji irin tense da motar tayi ba. Ji nake kaman wuta a kannu duk da matsananci Ac dake aiki ,but the tension is so much da nake ji kaina na juya kaman zanyi amai. Bakina sai motsi yake amma na kasa furta ko kalma d'aya saboda ina tsoron abunda zai faru. To menene ma zance? Su Nabeel ba samarina bane? Hmm, kina ta damun kan ki as if ko hakan wani abune wajen sa. Kin manta da kina da samari da baki dasu Hamzah did not care. Akwai abunda ya sashi fushi amma ba keba kima daina hoping. Jikina ya sake sanyi da gargadin da zuciyata tamin. Tabbas akwai abunda ya sashi fushi. Muna karya kwana layi na hango su mom a tsaye dasu Jennifer. Sai naji kaman na rushe da kuka. Allah sarki mom na sata cikin damuwa. A guje aka wangale gate ya danna kai motar ciki kota kansu mom bai tsaya jira ba. Yana fakin na yunƙura zan buɗe motar ya rigani. Da wani irin zafin rai ya fisgoni daga cikin motar ya yi ciki dani bai sauri Mom dake kwala masa kira ba. A yanzu na fara tsorata da yanayin sa. Tsananin azabar yanda ya murdemin hannu yasa nace muryata na rawa "Kana jimin ciwo" Ko kallona baiyi ba saida muka shiga main falo ya wani wullani kan cushion. Auch that hurts! "Aiza, ina ki ka je haka ne kin d'aga mana hankali?" Ko kafin na buɗe baki nayi magana Jennifer ta rigani "Kiyi hak'uri Aiza, Hamisu ne yace min kince akwai inda zaki mu tafi zaki tawo. Kuma da kin jirani ai sai mu sauke ki in yaso anzo a d'auke ki ko mu jira ki gama abunda ki ke" What????? Wani irin ido na zuba mata bakina a hangame saboda tsananin mamaki. Murya a sanyaye ta sake cewa "Mommy kiyi hak'uri, laifina da bamu tsaya neman taba saboda nayi tunanin ko zata rigamu dawowa gida" This bitch!! "Haba Aiza, yawon dare kuma?ina ki ka je? " "Mom, ba haka bane ...." " kiyi hak'uri don Allah Mommy. Kar kiga laifinta laifina na ne dana barta ta tafi ban jira taba" Jennifer ta sake katseni cikin sauri muryar ta yanzu na mugun rawa kaman zatayi kuka. Wai menene wannan bitch ke nufi? Jay da har zuwa lokacin ke tsaye yana huci ina jin yanda idansa ke kallona kaman kaifin wuta. Jiki na rawa na yunƙura na miƙe daga inda ya yi watsi dani nace "Mom wallahi ba haka ban..." "Shut up" Muryarsa ta sauka falon kaman aradu. Dukkanin mu babu wanda bai firgita ba bari ni da saida nayi baya kaman zan fad'i. A kausashe yace "Mom, kece ki ke pampering nata kaman wata jaririya shi yasa take abu like a brat(wawuya). Yanzu look, can na ganta da wasu samari sun sauketa but nasan bazakiyi mata fad'a ba ,dubi yanda ki ke mata magana da lallami saboda baki son laifin ta. Nonsense " Fuu ya wuce ya barmu a tsaye kaman guguwa. Wani irin shiru ne ya ratsa bayan wucewar sa har na wasu y'an sakanni kafin mom tayi k'arfin halin cewa "Me nakeji haka Aiza?" Yanzu kam kuka nema yaci k'arfina na kasa magana saboda tsab naji disappointment cikin muryar ta. A guje na haura sama bayan na rushe da matsananci kuka. Key na sawa d'akin nawa kafin na fad'a kan gado nayi kuka kaman raina zai fita. Kusan zan iya cewa kwana nayi ina kuka saida kaina ya yi ciwo zazzab'i mai zafi kuwa ya rufeni. Yanda nayi zato mom zata biyoni taji baasi amma shiru har barci ya d'auke ne mai wahala. Abunda ban taɓa yi ba, wajejen asuba na farka da wani irin matsanancin ciwon mara kaman zan mutu. Da kyar nake numfashi ina juyi kan gadon dafe da marata sai kiran sunan Allah nake. Cikin fita hayyaci naji kaman an dafa kaina tare da kiran sunana cikin damuwa. A wahalce na buɗe idona da sukayi ja tsabar wahala. Ha ciwon kai, ga zazzab'i ga ciwon mara duk abun ni kad'ai. Ina ganin tsananin ciwone yasa nake gani kaman Jay ne durkushe gefen gadon hankali tashe yana kirana. Maida idona nayi na lumshe in har mutuwa zanyi da wannan kyakwawan mafarkin a shirye nake na koma ga mahalicci na. Ganin bata responding ya wani fisgoto gaba d'aya ya d'aga kaman baby. D'agata keda wuya kuwa sai sha blood ya biyo kafafuwanta harya b'ata masa farar shirt dake jikinsa da bak'in wandonsa. Bai damu ba ya yo waje da ita a guje mom dake k'ok'arin hayowa jin ya kwala mata kira hango Aiza hannun sa kaman matacciya ya ta saki wani uban salati gaba d'aya sukayi waje harda su Jennifer dasu Maryam dake zaune falon .don karyawa suke Maryam take cewa har yanzu Aiza bata buɗe d'aki ta fito ba. Da kaman zai shareta but kuma sai ya kasa don shima jiya zuciyar sa nata azalzalalsa da bai kyauta mata ba. For the first time ya nufi d'akin nata da kanshi saboda yanda yake ji kinsa na gaya masa tamkar akwai matsala. Bugun duniya ya yi bata buɗe ba don haka cikin fargaba ya daki k'ofar bugu d'aya ta buɗe. Wani private hospital nasu suka je da babu nisa da nan. Mom da kanta ta ginashi ta kuma zuba manayn likitoci dake duba family da mutane. A guje aka k'arbeta zuwa emergency. Numfashi ya sauke bayan sun shiga da ita zuciyar na wani irin racing. Daga Maryam har mom basu da nutsuwa har ita Jennifer dake zaune gefen mom rike da hannun ta tana kwantar mata da hankali jefi-jefi tana kallon Jay dake safa da marwa k'ofar emergency d'in. D'an taune harshe tayi kome take tunani Allah masani. Basu jima ba suka fito da ita kwance kan gado na hutu tana barci lakadan. Saida aka sata d'aki sannan dr ke cewa babu wata matsala ciwon marane kawai ya sata wannan zazzab'in haka mai zafi, amma sun bata magani idan ta farka za'a sake bata wani. Sai a lokacin gaba d'aya hankali su ya kwanta. Marya ce ta gyara Aiza dake barci da taimakon wata nurse suka saka mata riga da ake sawa ta patient bayan mom ta saka ya siyo pad da pant an saka mata. Har wajen la'asar bata farka ba saboda k'arfin allurar da akayi mata. Jennifer ita ta d'an lallaba mom suje gida ci abinci suyi wanka duk cewa an kawo abinci asibitin. A hankali na buɗe idona da nake jin kaina kaman an doramin dala da goran dutse. Wani dum nake ji kan nawa saboda ciwo. Kaman jira ake kuwa na farka marata ta sake motsawa nayi saurin sake maida idona na lumshe da k'arfi wasu hawaye masu zafi suka biyo kuncina. Wannan wane irin ciwon marane haka? Kaman a mafarki naji lallausan hannun sa yana sharemin hawaye. Ko dai har yanzu mafarki nake ne? A hankali na buɗe idona kan Jay dake tsaye gefen gadon ya d'an rankwafo da kansa gashinsa ya bazo wajen idansa kaman bai daɗe da wanke kan ba. Kamshin sa dana mint breath nashi sai dukan fuskata yake. Ash shadda ce jikinsa k'aramin d'inki. Sosai ya yi bala'in kyau ko dan ban tab'a ganinsa cikin manyan kaya ba? Kusan zan iya cewa numfashina d'aukewa ya yi haka duniyar ta tsaya cak ta daina motsi. Ido muka zubawa juna har zuwa lokacin hannun sa rike da fuskata yana sharemin hawaye da babban yatsan hannun sa. A hankali naji ya furta "Does it hurt?"(har yanzu yana ciwo?) Bansan ya akayi na tsinci kaina da d'aga masa kai ba. Wani mugun numfashi naja da ware ido kaman zasu fad'o kasa you know what??? Hannun Jay ne kan marata ,fatar cikina yana shafawa a hankali kaman yanamin massage. Shin hannun ya tura cikin rigata ko kuwa rigar ya tattare? Ban sani ba? And i honestly doesn't care. It was so amazing da yanda hannun nasa ke shafa marata kan pant nawa a hankali idansa cikin nawa. Sai nake gani kaman fuskarsa a yanzu dab take da tawa fuskar. Ok pause!!!..... i can't say ga yanda akayi. The next abunda na sani shine Jay kiss MEEEEEEEE!... Oohhh my f heart. Arrgggggggg!!!🤧 [17/01, 10:35 am] Ashantyluv: ❻ Masu tambaya, yes this book is a paid book akan 500n kacal. Zaku iya fara payment through wannan account 8140754777 Aisha sani hassan Opay. Shedar biya O8140754777 WhatsApp group! https://chat.whatsapp.com/DaatWeTyf3M59ZwHORMsIi Da farko lips nashi sauka sukayi kan nawa kaman iska ,kaman kyeftawar ido ya d'auke su wush. I was so shocked da numfashina ya tsaya chak haka idona ke a ware ina kallon fuskarsa dake tattare da shock shi kansa mamakin abunda ya aikata ya yi. Hannun sa dake kan marata ya d'auke cikin sauri kafin ya tashi daga kan gadon kaman wanda ke kan wuta. Can k'asan makoshi naji yace "Get some rest" Kawai ya juya ya fice kaman babu wani abu daya faru. Aiza,AIZA!! Breath. Zuciyata ta kwalamin kira da k'arfi daya saka ni jan wani irin dogon numfashi na fesar. "Mafarkine, Mafarkine " Na fara furtawa a fili ina jan numfashi da k'ok'arin sake runtse ido ina buɗewa. Despite all that effort. D'an kamshin breath nashi ina jinsa kan lebena yana lingering. Don sake son gaskata gaskiya ne ko Mafarkine na daga hannu da d'an k'arfi kad'an na kwadawa kaina mari. Ouch! Idan ma ban gama farfaɗowa ba yanzu kam na tashi ras, kuma ba mafarki nake ba. Jay ya sumbace ni duk da bazan kirashi da sumbata ba. Yanzu me zan kira hakan? Hope!! Shigowar su Mom da Jennifer ya katseni daga tunanin da nake fuskata da murmushi kaman bakina zai yage. Sai bayan sun shigo ne na fuskanci gadon asibiti nake kwance. Hankalin mom sosai duk ya tashi haka na Jennifer dasu Maryam. Ita kuma menene nata na damuwa kaman ance zan mutu? This girl? Despite wannan innocent look da take tattare dashi akwai wani boyeyyen abu game da ita . Yanda Mom ta damu duk sai naji guilty na jefata cikin damuwa. Ina so na bata hak'uri saboda laifin da nayi mata jiya duk da cewa ba laifina bane. Zuwansu mom ,dr ya shigo ya sake dubani tare da yimin yan tambaboyi na bashi amsa. Fuskantar da ya yi babu abunda yake damuna ya sallameni da hadani da magunguna. Sanda muka fito daga asibitin ina ta baza ido naga Jay amma ko kurar sa babu sai direba ne ya kaimu gida. Ko a gidan i was hoping na ganshi ko na sake tabbatar da abunda ya faru, amma har mom tasani nayi wanka naci abinci nasha magani na kwanta banga keyar Hamzah ba. See i was hoping for nothing!. Kusan da kyar na iya barci na kuma jidaɗi da yauma Jennifer bata kwana d'akina ba. Maryam ce ta kwanta dani sai lokaci zuwa lokaci mom ma dekowa komai dare taga lafiya

Chapter 3 of 6