Yanzu yana da shekara ashirin da biyu kenan ko a lissafi, kuma a yanzu ya gama karatun sa kenan ko?
A bakin ƙofar naci birki k'irjina na harbawa bakina sai motsi yake amma ko kalma ɗaya , na kasa furtawa. Ina dai kallonsa kawai. He has changed. Ya zama, me zan ce nema? Taya zan fassara changing da ya yi?. Farar tshirt ce jikinsa da tayi masifar kama faffaɗan k'irjinsa. Hannun rigar tattare yake wajen damtsen hannun sa da koya ya motsa hannun sai jijiyoyin sun motsa. Wani irin yawu na had'iye daya tsayamin a makogaro. A koda yaushe ina yawan hasashen irin kyau da zaiyi idan ya zama cikakken namiji. Amma ban taɓa tsammanin zai zama this f# handsome ba. Domin ya wuce duk yanda nake tunani.
At thesame time kaman yanda nake kallonsa, shima haka yake kallona ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba.
Sai naji kaman duniyar ta tsaya chak, ta daina motsi.
Wait! Anya bazan duba zuciyata ba ko har yanzu tana cikin kirjina! Har yanzu na kasa gasgata abunda nake gani.
Mommy ce ta katse shiru daya lullube ɗakin.
“Aiza, finally our Jay ya dawo!” ta faɗa cikin farin ciki.
A hankali na sauke numfashi da saita nutsuwa ta . Da kyar na d'aga k'afata na k'arasa inda suke. , sai naga na sake zama wata y'ar ƙanƙanuwa sanda na tsaya gabansa , saboda mugun tsayi daya sake, kusan ƙafa shida da wani abu.
“sannu da zuwa…” na gaishe shi, kafin na sake cewa“Na yi tunanin ba za ka dawo ba…”
Na faɗa a kunyace, ina ƙoƙarin hana hawayen idona zubowa. Na yi matuƙar farin ciki da ganinsa har ban san abin da zan yi ba.
Ina ta aika maka da saƙo kusan sau talatin a kowace rana. I have been waiting ka amsa, ko da da sauƙaƙƙen kalmar “hi” ne, amma baka taɓa amsawa ba. Na yi tunanin zan mutu ne ina zaman jiran ka…
Abubuwa da yawa nake so in faɗa masa. Ina so ya san cewa shekarun huɗu da nayi babu shi sun kasance mafi tsawon lokaci a rayuwata baki ɗaya.
Kamar kasancewar wannan lokacin ba shi da wani muhimmanci a wajensa, Hamza ya amsa cikin sanyi,
“as if i have a choice…” ya faɗa yana kallona tun daga saman kaina har zuwa ƙafafuna
“Jay,” Mommy Jannat ta katse shi, “tabbas kana da zaɓi mana, kana da Aiza, ita ce zaɓinka nan gaba, InshaAllahu ”
Wani iri dauke kansa ya yi ya watsawa Mom manyan idansa yana cewa ,har yanzu muryar sa so cod, “Don Allah Mom, na zo nan ba don muyi wannan useless magana ba… nazo ne don mu tattauna abu mai matuƙar muhimmanci. Amma a yanzu, ina jin yunwa sosai.”
Ya k'arasa maganan yana k'ok'arin zama. Wato dai nice useless abu mara amfani wajen sa?
Da hannu Mommy Jannat ta yi min alama da in zauna. Na zauna a kujerata ta yau da kullum, dake fuskantar Jay.
Muna cin abinci ne , amma ban iya hana kaina kallonsa ba lokaci zuwa lokaci . Girar idonsa masu kauri da jan hankali da kayatarwa sun sake cika fiye da wancan lokacin kafin ya tafi. Hancinsa yana nan kaman biro .haka lebensa, masu kauri, ja, kuma masu tsananin jan hankali. He is the definition of perfection.
Duk da cewa a ɓoye nake satar kallonsa, magana yake da Mommy yana faɗa mata irin shirin da yake kan business nashi kamar bai sanda wanzuwata wajen ba,like I'm nothing, like i did not exist at all.
[17/01, 10:35 am] Ashantyluv: 【HAMZAH】
𝓂𝓎 𝓅ℴ𝓈𝓈ℯ𝓈𝓈𝒾ℴ𝓃𝓈!
✆-08140754777
❸
“Hamza, yau ranar zagoyowar shekarar haihuwar Aiza ce. Ba ka tuna ba, Dear?”
Da Mom ta ambaci sunana, wannan ne kaɗai lokacin daya sake kallona. Da wannan big black eye nashi da idan ya kalle ka dasu saboda tsananin duhun su, sai kaji kamar ka faɗa cikin wani trap ne mai tsanani da ba za ka iya tserewa ba.
“yau take cika shekara goma sha bakwai. Dubi yadda ta girma yanzu. Doesn't she look lovelier?”
Mom ta faɗa da alfahari. Wata kunya naji ta rufeni sosai, musamman ganin yadda yake kallona. Sosai nake son jin ra’ayinsa a kaina, tun da ya shafe shekaru huɗu baya nan, kuma ina matuƙar son sanin yadda ya ke gani na yanzu.
“Shekara goma sha bakwai har yanzu ƙarama ce, Mom, don haka ki daina batun nan.” Muryarsa ta yi k'asa kaman yana roƙo. “Don Allah ki daina haɗa ni da Aiza.”
“ai baza tayi ta zama a ƙarama ba har abada ba, Hamza. Za ka aure ta a lokacin da ya dace.”
“Ba zan aure ta ba. Na riga na faɗa miki ba tun yau ba, Mom.”
Ya amsa nan take, kamar furta hakan abu ne mafi sauƙi a gare shi .
Wayyo waɗannan kalmomi masu kaifi kamar wuka! Sun tarwatsa mun zuciya.
“To, wacece za ka aura?”
Mommy Jannat ta yi magana muryar ta yanzu akwai alamun ɓacin rai. Daina cin abinci tayi ta tsaya tana kallonsa da irritation kan fuskarta.
“Zan auri macen da na zaɓa, ba wadda ki ke so ki zaɓa min ba, Mom,” ya faɗa, idansa chak cikin nawa!
Wayyo, wai ba zai iya daina kallona haka ba alhali yasan duk abin da yake faɗa kalmomi ne masu raɗaɗi da kona zuciya!
Ji nayi kamar na rushe da kuka.
♡♡♡♡
A hankali na miƙe daga kan dadduma da nayi sallah isha na ninke ta na ajiye gefen drawer. Jikina gaba d'aya a mace yake murus kaman anyi min duka saboda kalaman Jay dake ta yimin yawo a kai. Wai shin menene zanyi ya k'arbi tayin zuciyata ne? Zama nayi gefen gadon bayan na cire hijabin dana d'ora kan sleeping wears nawa riga da wando nasu laushi. Gashina na tufkeshi tsakiyar kai tare da dora hula . Kafafuwana na hade a k'irji na rungume kaman marainiya, ko da yake marainiyar ce. Abunda Jay yake min yana min ciwo, zuciya ciwo take a koda yaushe, da ina da hali cireta zanyi na ajiye ki na huta nima da wannan bak'in cikin da wulak'anci.
"Aiza, my dear"
A hankali na d'ago jin muryar mom da banji shigowar ta d'akin ba saboda yanda nayi zurfi cikin tunani. Kusa da Kafafuwana dana rungume a k'irji ta zauna tana kallo da hijab a jikinta da charbi hannun ta tana ja. Ganinta sai naji hawayen dake kwance cikin idona sun zubo shar mom tayi saurin matsowa ta rungume tana d'an buga bayana tace
“Kada ki damu da abin da ya faɗa d'azu, Aiza,” tayi maganan cikin raɗa a kunnena.
“I promise you, zan yi duk abin da zan iya domin ya aure ki.”
Hawaye suka zubo daga idona. Me zan yi? Sosai ina ji zafin abin nan. Share min hawayen tayi daga kuncina tana cewa.
“Ke yarinya ce mai kirki, hankali, nutsuwa da sanin ya makata, don haka ban fahimci dalilin da ya sa yake mu’amala da ke haka ba da nuna miki irin wannan abu. Bai kamata ya riƙa yi miki haka ba!”
Sosai naji alamun b'acin rai cikin muryarta don haka nace “Mom, kada ki damu. Zan yi duk abin da zan yi domin ya so ni.”
Murmushi tayi da dafamin kai jin ƙudurin dana d'auka tace
“Da gaske kina son Jay har haka, Aiza?”
Kai na d'aga da iya kacin gaskiyata. Ta yaya zan iya bayyana waɗannan abubuwan mamaki da nake ji tun shekaru da suka wuce? Butterflies dake cikina, rashin samun nutsuwa, da bugun da zuciyata a ko wane lokacin da yake kusa da ni . Kuma duk shekarun da ya yi baya nan, ciwon da ke cin kirjina da yawan tunanin dawowarsa, kullum sabone a wajena. Ba za mu iya kiran wannan soyayya ba?
“Idan haka ne, nayi miki alkawarib, Hamzah ba zai auri ko wace mace ba sai ke,” ta faɗa muryarta babu wasa da kuma tarin alkwari.
“Na gode, Mommy. I love you.”
“i love you too, darling.”
♡♡♡♡
Washegari ban farka ba bayan nayi sallah sai wajen takwas. A gaggauce nayi wanke na fito zuciyata nata azalzalata da son ganin sanyin idaniyarta. Riga da sket nasa black sket mai dan fad'i sai farar tshirt mai botira da bak'in mayafi dana yafa a kaina. Flat takarmi na saka k'afata fari na fito cikin hanzari rike da wayata. Da Maryam naci karo falo tana jera abinci kam dining.
"Sannu da fitowa, Aiza"
"Maryam , ina kwana an tashi lafiya?, ina mom fa da Ha.."
Bansan me yasa ba naji kunya ta rufeni ambaton sunan sa da nake k'ok'arin yi, duk da cewa soyayyar sa ba boyeyyiya bace ga dukkanin mutanen gidan. Kaf d'in su babu wanda baisan ciwon so da nake fama dashi ba game da Jay.
Y'ar dariya Maryam tayi tace " yau kuma kunyata ake ji? Sir, Hamzah sun fita da mom tace a gaya miki zasuje government house meeting. Naji kaman tana batun wai suna ta aikata mata da sak'o ta shiga siyasa suna son ta k'arbi minister. "
D'an jim nayi raina babu dad'i saboda wanda nake ta Allah-Allah na fito na gani baya gida. Da kyar na iya karyawa na koma d'aki ina ji kaman na kirashi amma wata zuciyar namin gargadin hakan. Har la'asar basu dawo ba bayan na sake watsa ruwa na saka doguwar riga k'irar Turkey maroon ,wacce gaban keda ziff na fito nan garden rike da d'an k'aramin Qur'ani ina so nayi tilawa. Ina son komawa islamiya wannan shekarar tunda munyi sauka don zaman gidan ya fara isata.
Cikin kujerun dake garden din kaman swing chair na zauna dake kewaye da followers masu kyau ga tsuntsuye nata shawagi . Inuwar mutum data tsaya a kaina yasa na d'ago da sauri ko Hamzah ne. D'an numfashi na fesar ganin Ilya ne tsaye bayana da murmushi kwance fuskarsa. Ilya d'an gardiner ne na gidan kusan zance mahaifin sa da mahaifiyarsa a nan suka naireni domin sanda nazo gidan yana kusan sa'a Hamzah ne, kuma Mom tace sun jima a gidan. Saboda jindaɗi da kuma y'anci da suka samu mahaifin Ilya ya kasa barin gidan Mommy Jannat duk da cewa ta basu tafkelen gida saboda halin girma kuma ta basu dama subar aikin zata nemi wasu, amma mahaifin sa yace babu inda zasu nanma inda suke ya ishesu. Bazan iya kwatanta muku irin girman gidq. Mommy Jannat bane, gidane da za'a kira da Aljannan duniya. Masu gadi, masu aiki, cooku, direbobi, masu tsaro duk sun kasance suna da b'angaren su ba kuma gurine k'arami ba, gurine da babu abunda suke nema suka rasa.
"Sannu da hutawa "
Ilya yace har zuwa lokacin fuskarsa da murmushi. A takaice na amsa da "yawwa" na maida hankali kan karatuna.
Da kwarin gwiwar sa ya zagayo ya zauna d'aya swing chair d'in dake kusa dani. Sosai nake jin idansa a kaina. What did he think he was doing?
“Na ga kina lilo ke kaɗai, sai nake ga kama kina buƙatar wanda za ki yi hira da shi.”
Da murmushin da bai kai zuci ba nace “Haka aka gaya ma?”
“Eh, haka nake tunani,” ya faɗa, har yanzu yana murmushi.
Na san waye Ilya. He is a weet person ,mutum mai yawan murmushi da wannan dimple ɗin da ke gefen kuncinsa na hagu,sai nake ji ba daidai ba ne in ci gaba da magana da shi haka. Akwai mutane dake cikin mansion d'in nan sun san yana da crush a kaina, kuma idan suka gan mu muna lilo tare, za su iya tunanin cewa namanta da auren da zan yi nan gaba da young master na gidan!
“A gaskiya, ba na buƙatar wanda zan yi magana da shi a yanzu,” na faɗa kai tsaye, har yanzu fuskata da murmushi da bai kai zuci ba.
Da alama bai damu da abin da na faɗa ba, domin har yanzu yana murmushi ya sake cewa
"Sabon kaya ki ka saka ne yau? Kin chanza kala naga ke mutum ce mai son pink abu ko pitch colour ko ash"
This jerk!
“Ina sanye da sabon kaya ne saboda fiancé na yana nan. Konba ka ji labarin zuwan sa ba?”
“Wanene ba zai ji labarin zuwan the young master ba? Abinda ke sa ni mamaki shi ne, me ya sa ba ku tare?”
Who are you to meddle with my lovelife?
“Don Allah ka tafi! Kana bata min rai!” na faɗa, kusan cikin ihu.
“na bata miki rai ne?,” ya faɗa yana yar dariya da k'ok'arin miƙewa tsaye.
“To,shikenan na tafi. Allah ya baki hak'uri. Bye!.”
Haƙorana na cije tare da watsawa bayansa harara. That jerk! I can't stand him !
Saboda wannan ɓacin rai da nake ciki, ban lura da shigowar Hamzah ba saboda haushi. Numfashi naja mai k'arfi na fesar da d'an tsaki kafin na ɗaga kai na. Mutumin da nake ta jira yana tsaye a bakin ƙofa garden d'in.
A take zuciyata ta yi wani irin tsalle da mugun ƙarfi kaman zata fito daga k'irjina.
“what was that? An afternoon visit daga saurayinki ne?” Jay ya tambaya da wata irin cold voice lokacin da idonmu suka haɗu.
“huh?” Tun yaushe yake tsaye a nan? Ko ya ganni da Ilya zaune yanzu kan swing ?
Wani irin nufo ni ya yi a hankali, da irin tafiyar nan kaman an sashi dole . Sanda ya tsaya a gabana, his dominating height made me very uneasy.
Ina k'ok'arin nemo nutsuwa ta da hankalina, sai Jay kawai ya jefeni da wani bombshell dake neman tarwatsa mun tunani.
“Ban fahimci dalilin da ya sa har yanzu ki ke bin son zuciyar mom game da aurenmu ba, alhali kuma kina da saurayi,”
Ya faɗa kamar yana da cikakken tabbaci cewa Ilya saurayina ne, kamar babu buƙatar wata tattaunawa a kai. End of discussion!
Kai na ɗaga kalle shi, mind nawa na processsing maganganunsa a kwakwalwata. Hawaye naji sun taru cikin idona.
“A’a, ka yi kuskure… Ilya ba saurayina ba ne,” na faɗa murya ta na rawa.
“ohh so, Ilya ne sunansa…”
“Ba saurayina ba ne,” na sake faɗi da ƙarfi, ina ƙoƙarin kare kaina.
“Kina tsammanin zan yarda da hakan?” ya tambaya. “Ta yaya zan yarda da ke alhali duk lokacin da na gan ki, shi ma yana nan tare da ke?”
Ban san abin da yake nufi ba. Ganina tare da Ilya… yaushe ne kuma ya gan mu tare?
A ƙarshe, hawayen daya taro idona suka zubo kuncina nayi saurin sauke kaina katsa. Don hana kaina rushewa da matsananci kuka , na matse hannuwana da ƙarfi kan igiyar swing da nake riƙe da ita.
“Aiza, me yasa bazaki gayawa mom gaskiya ba?”
A wannan karon, muryarsa ta yi kaman yana roƙoba. “Ki faɗa mata gaskiya kawai, let ends this once and for all”
Saida na share hawayen fuskata, na sake kallonsa nace “Ko ka yarda ko ba ka yarda ba, Ilya ba saurayina ba ne. I'm engaged to you, kuma ba zan auri kowa ba sai kai! Wannan ita ce gaskiya!”
Wani irin zubamin ido ya yi, sosai yake kallona ido cikin ido saida zuciyata ta motsa— unexpected, kawai, sanda numfashike barazanar tsayawa, sai ya yi wani faffaɗan murmushi kaman yana mocking d'ina yace
“Da gaske kina son mom har haka da zaki sadaukar da soyayyarki ta Ilya saboda ita?”
Da kyar nayi ƙoƙarin tashi daga swing din da nake zaune na fuskance shi, amma da na miƙe, his chest is right at my face. That masculine dreamy chest mai matuƙar ɗaukar hankali.
“ Ilya ba saurayina bane, kuma zan aure ke ne—ba don mom ba.”
“Da gaske?” ya tambaya yana kama habata da yatsunsa. Wani irin ware idona nayi ina kallonsa cikin matuƙar mamaki lokacin da yatsunsa suka taɓa kumatuna. Sai kuma ya matse kumatun nawa da k'arfi bakina ya motse waje daya , karkatar da fuskarsa ya yi gefe bayan ya sunkuya da kanshi wajen tawa fuskar.
“tell me, me ya sa kike son aure na?”
Na kalle shi kai tsaye ido cikin ido, a ƙarshe na faɗi abin da nake ji a kansa tun ba yauba.
“Saboda ina son ka.”
Kai, na faɗa! Finally i have said it?
I think he was so shocked da confession nawa and flabbergasted daya hana shi motsi, ya kasa cewa komai . Ya kawai zuba min ido . Mun dauki tsawon mintuna haka muna fuskantar juna na --- it feel like an eternity.
Sam, na kasa karanta abin da ke zuciyarsa . Kawai unexpected idanunsa, ba zato ba tsammani, suka koma babu expressionless. Kawai ya wani saki fuskata daya rike… kafin juyamin baya.
“dont be a fool,” ya faɗa da wata irin hoarsed cold voice… kawai ya shiga cikin mansion ya barni a tsaye ba bu ko waiwaye.
Hmmm.malam. JAY, i feel jealously in the air😏
[17/01, 10:35 am] Ashantyluv: 【HAMZAH】
𝓂𝓎 𝓅ℴ𝓈𝓈ℯ𝓈𝓈𝒾ℴ𝓃𝓈!
✆-08140754777
WhatsApp group!
https://chat.whatsapp.com/DaatWeTyf3M59ZwHORMsIi
❹
Bana tunanin zaku fuskanci irin tsananin embarrassing it was for me. Finally, i confess feelings d'ina. Abune mai matuƙar kunyatarwa ga yarinya ta furta yadda take ji kan mutumin da take ƙauna, just to get rejected afterwards!
Oh, it so embarrassing. Wataƙila na yi tsammanin wani abu zai faru , kamar yadda nake yawan gani a fina-finan soyayya da nake so, inda bayan yarinya ta furta soyayyarta ga saurayi, sai shi kuma ya rungume ta ko ya sumbace ta saboda furucinta.
Amma Jay bai yi hakan ba. Maimakon haka, he called me a fool.
Fool. Fool. Fool. Wannan banzar kalma ta ci gaba da damuna a raina. Zaku iye kyestima how embarrassing was that?. Saida na sake b'ata lokaci zaune wajen in a daze ni banyi kuka ba sai zafi da rad'ad'i da zuciyata take. Wataƙila dana yi kukan na samu sassaucin abunda nake ji. Ana Kiraye-kirayen sallah magriba na yunƙura zan mik'e saiga Mansura ta shigo garden wai nazo Mom na kirana. Ban musa ba na bita tunda dama niyata kenan. A main falo dake katsa na sami mom da bakuwa tare da wata yarinya budurwa. Saida na samu wajen kusa da kafan mom na zauna kan kafet sannan na gaishe da bak'in cike da ladabi.
Da fara'a sosai babbar matar ta amsa min tana cewa
"MashaAllah, Jannat. Ai bansan haka Aizan taki take da kyau ba ga hankali. Yau dai naga Aiza da kullum baki da magana sai tata"
Dariya sukayi gaba d'aya da mom na sauke kaina katsa cike da y'ar kunya ina kwalolo murmushin dole.
"Jennifer, ga Aiza .ina fatan zakuyi abota mai tsabta don kinganta nan sam bata son shiga cike k'awayena"
Kiran sunan yarinya da mom tayi yasa na d'aga kai na kalleta wanda already ni take kallo. The girl is very pretty. Gatanan kaman irin Ethiopian girl d'in nan duk da na fuskanci kaman yarece ita da mahaifiyarta. Kaman dai zamu kira da half yarabawa, half hausawa. MashaAllah. Murmushin yarinya tayi dimples nata suka lotsa muryarta kaman an busa sarewa tace
"Yes mom, we will ne best friends "
Hakanan kawai naji wani abu ya daki zuciyata kaman kishi. To kishin me? Saboda ta fini kyau, ko kuma saboda ina ganin kaman irinta, sune matan da maza kaman Hamzah ke so. Daga nan inda take zaune i can see her full breast dake boye cikin less dake jikinta, d'inki riga da sket. Less ne mai mugun tsada haka daya sha stones da wani azababben d'inki na yan gayu gashi kayan ya kamata matuƙa dalili da yasa kana hango saman boobs nata da suka hauro ta sama. Yanda take a zaune tsab zaka fahimci shes so f# curvy don shape nata sosai ya nuna tana da hips.
Now, i know zakuce what is wrong with you! The thing is, kun gane i have everything amma not curvy as her. Bani da manyan nonuwa haka kaman nata. Bani da uban hips haka da zakayi tunanin suna rinjayar mutum. Ina b'angaren more of slim da d'an k'aramin kugu dake da hips dake a baje. Tsab idan kasa hannu zaka ritsa cikina. Boobs nawa suma suna ta b'angaren medium size wanda hakan yasa suke a tsaye cur kaman an hura ballons. But despite that, ganinta sai naji insecure d'in kaina. Ko tsakanin nida mace idan aka ce na zabi tsakanin nida ita, ita zan zaba. Bare kuma maza irin su Jay!
Jay ya ganta?why ki ke tunanin hakan, bayan kinsan definitely ya ganta??. Zuciyata tace a take wani abu ya sake dannemin zuciya ta sake nauyi. Ina jinsu Mom nata hira da mahaifiyar yarinya data kira da Hajiya. Nawwara. Yanda naji kaman a can dubai suka had'u da mom sanda taje siyayya da tayi tayi muje tare nace bana so saboda ina gudun Jay ya dawo ban samu ganinsa ba. Kuma dai na kasance mutum ba bai yawon son yawo ba musamman ma fita da zai kaini hawa jirgi don zuwa wata k'asar.
"Aiza, nuna mata d'akin ki kuyi sallah sai kuzo muyi dinner "
Da ladabi nace to na miƙe ko kafin nace ta taso muje Jennifer ta miƙe. Ashe kallon da nayi mata ma na tsoro ne tafi yanda nake tunani sai dai na nuna mata d'an tsayi kawai. Wannan da waje tashi she's going to be a model.Sama na haye tana biye dani a baya hakan kawai nake ta addu'a Allah yasa har mu shiga d'aki Jay bai fito ba. Da fara'a na nuna mata toilet don tayi alwala na koma gefen gado na zauna tare da zubawa k'ofar toilet d'in ido. Bata jima ba ta fito da dankwalin ta a hannun tana gyara gashinta daya sha uban attachment. Muna had'a ido da ita bayan fitowar kawai naji gabana ya yanke ya fad'i. Da sauri na miƙe na shige toilet d'in nima don d'aura alwala cike da tarin tambayoyin dalilin da yasa zuciyata da hankalina ya kasa samun nutsuwa da kasancewar ta a nan.
A tsaye na sameta kaman tana jirana nayi saurin k'arasowa ina cewa
"Ooh, I'm sorry don Allah na manta ban baki abun sallah ba "
D'an murmushi tayi da dimples nata tace da y'ar siririyar muryarta very innocently
"Babu komai"
Dadduma na shimfiɗa mana na d'auko mata hijabi mukayi sallah. Tana idarwa ta cire hijabin da sauri kaman an kunna mata wuta ta ajiye gefe ta fara k'ok'arin miƙewa tsaye. D'an kallonta nayi bakina na kaikayi zance bakiyi addu'a ba sis, na daiyi shiru da gargadin da zuciyata takemin na ina ruwan ki?. Saida na shafa addu'a sannan na miƙe na cire hijabin dake jikina wajen cireshi na had'a da hula dake kaina dana tura gashina ciki banma lura ba saida naji tayi magana.
"Ooo.. gashin ki ne wannan? "
Saida na kai hannu na tattare gashin waje d'aya ina d'an yake nace mata eh. Hmm kawai tace tana kallona da kallo dana kasa fahimta ko fassarashi. Duk sai naji na tsargu da kaina.
"Muje ko, su mom na jira"
"Ok"
Kawai tace ta miƙe tayi gaba ta barni ina bin bayanta da kallo. Kai na girgiza tare da kawar da tunanin dake raina na fito cikin sauri nima. Tuni suna zaune kan dinner har Jay dake sanye da wata black riga data kamashi matuƙa. Kirjinnan kaman zai fasata. Gashinnan yasha mai sai shek'i yake ya tufkeshi a tsakiyar kansa. Wani abu naji ya daki k'irjina sansa taja kureja kusa dashi ta zauna. Da kyar na iya daga k'afata na k'arasa naja tawa kujerar na zauna dake fuskantar sa. Dagani har ita babu wanda ya d'aga ya kalla sai abincin sa da yake ci cikin nutsuwa yana duba had'addiyar wayarsa kirar Samsung fold dake cikin zara-zaran yatsun hannunsa dake dauke dawi diamond ring da agogon rolex tsinyar hannun. Everything he did makes him more beautiful.
Da kyar na iya rarrashin zuciyata to never look at him. Mom da Hajiya Nawwara su kad'ai suke ta hira abunsa itama Jennifer tayi shiru kaman ruwa ya cinyeta sai kallon Hamzah da take sata k'asa-k'asa.
Nayi mamaki don muna gama cin abinci Hajiya Nawwara tayi sallaman damu ta tafi banda Jennifer data samu waje falon ta zauna. Sai bayan mom ta raka