Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
abota Asma''u ta dubi Goggo razane "Wai me ya faru ac? Shim wane saurayi na taba kwasowa? muke yi ni bai taba cewa yana sona ba, mutunci ne kawai da kuma haduwar jini, kuma yana taimakona SOsai makaranta." Duk da Goggo ta san Ma'u ba za ta yi mata Karya ba, "To amma yanzu irin hidimomi da dawainiyar da Salima yake yi musu ya sa Goggo ta fara kokwanto akan maganar Asma'u dan haka take so ta ji gaskiyar al'amart, daga bakin Salim din ta ce "Ni kam Salim ina ga an ya bana ba za kaiwa Aminu Kwacen mata ba? Don kaunar taku da Ma'u abin ya yi tsamari." Yana jin haka ya fadada fara'arsa yana yIwa Goggo dariya "Kin ji ki Goggo da wani zance wa ya gaya miki Asma'u sona take yi? Ai ita idan ba wannan gayen ba babu kowa ranta dan haka ni da Asma'u babu wata alaKa ta soyayya tsakaninmu, Kauna ce kawai da haduwar zuciya amma daga ni har ita kowa da wanda yake so, ai ni na yi zaton Asma'un ta baki labarin yarinya ta, tana can gidan aure, ni kuma ina nan ina jira ko ta tsufa in ta fito sai na aureta. Goggo ta yi dariya "Ai kai da mutuniyar taka dai Kwaryar sama ce take dukan ta Kasa duk jirgi daya ne ya debo ku dan na san me yiwa ba ta ta6a ba ka labarin irin gwagwarmayar da ta sha baya kan soyayya ba." Ya ce "Eh to ta gaya min kadan daga cikin tarihinta amma da yake ba ta fiye son dogon surutu ba, wasu abubuwan ba lallai ne ta sanar dani ba, don duk yawancin hirarrakinmu mun fi yin su akan abin da ya Shafi karatunmu amma ni kam Goggo zan so na ji daga bakinki abubuwa da dama da suka danganci Asma'u." Nan take Goggo ta bashi labarin Asma'u da 49 E"<® tarihinta gaba daya. Washe gari ranar Litinia dukkaninsu sun je makaranta amma ba su hadu ba sai da aka tashi Salim ya kirata waya tana dauka ya ce "Ya ya kun tashi ne? Ni fa har na fito." Asma'u ta ce "Ai ni ina da sauran lakca sai nan da Ya ce "To yanzu ya ya za yi zamu tafi tare ne ko kuma direbanki zai zo?" "Gaskiya bana jin direba zai zo daukata dan kuwa Goggo ta aikeshi amma ka tafi kawai kar na Bata maka lokaci, sai na tafi motar haya." awa daya da rabi za mu fito." "Haba da Allah malama wanne irin motar- haya? Shin ba ke na hana shiga motar kasuwa ba." "To shi kenan yi min afuwa yau dai aya bar ni. in shiga tasi." "Ke wallahi ba ki isa ba." "To na ji amma ka tafi gida in ka je sai ka cewa Momy ta turo direbanku ya kai ni gida shi kenan ko?" Ya ce "Kin ga kawa: bar shi ma ba zan tafi ba gara na tsaya na jira ki ko da dare za ki kai kina daukar lakca in kin fitoina nan inajira." Ta saki wata 'yar dariya "Kai dai Salim ka fiye rigima ina ka taba ganin na kai dare ba mu gama lakca ba?" Ba fa jira amsar da zai ba ta ba ta rufe wayar tana murmushi. Salim yana zaunc akan motarsa sighrin sa yake ta zuka cikin nishadi lokaci-lokaci ya kan duba tsadadden agogon dake daure hannunsa, gefensa wasu abokanga ne guda biyu, Manniru da Dauda suna tsaye suna tayashi 50 fl hira koda yake ba wai damuwa ya y¢ da hirar tasu ba. Musamman da yake tsegumi suke ta yi akan 'yan mata masu wucewa, can dai suka hango Asma'u ta taho, Mannir ya bugi Kafadar Salim "Ya kai ga mutuniyar ta Salim ya dan dubi hanyar da ta bullo yaym da ya zuba mata ido. Tafiyarta take cikin nutsuwa tana taku hankali na burgewa kai ka ce tausayin Kasa take ji. Salim ya yi doguwar zuka da karan sigarin dake bakinsa sannan ya fesar da hayaki ya miKawa Mannir guntuwar tabar da bai gama busawa ba, ya ciro alewar tom-tom daga aljihunsa ya Gare ya jefa baki Mannir ya karbe tabar ya ci gaba da zuka yana masa dariya "Hala Gimbiyar ba ta son warin ta ba ko?" -gaskiya fa:yarinyar nan muguwar kyakkyawa ce ga ta 'yar hutu; da gani duk mijin da ya aureta zai huta sosai. nan ba yana nema ya mayar da kansa soko, wai shi dole mutunci yake da ita da an yi magana sai ya co shi ba zai yi soyayya ba." Ya dan doki kafadar Salim "Ban da kai banza ne in da ni ne ta ya ya ina tare da zukekiyar yarinya kamar wannan zan wani tsaya muna abota at kawai soyayya zamu Kulla kuma in yi gaggawar aurenta ma ke zuwa makaranta tare." Salim ya saki 'yar dariya gami da kaiwa Mannir duka "Sannu uban tsarki ga ka nan har ka gama tsarawa to ai kune ba ku fahimce ni ba, amma ina Kaunar Asma'u sosai ba ku ga yanda ta shiga zuciyata ba, ina ji da yarinyar nan, dan ba yadda za yi har na kwana, na ka can ta taho." Dauda ya dan dubi hanyar da ta ke tahowa Kai "A to kai ma ka fada." In ji Mannir "Ba ga Salim yini ban dora idanuna kyakkyawar fusakrta ba, kuma sannan bana iya barci kullum dare har sai na kirata waya ha ji sassanyar muryarta, to amma duk wannan Kaunace ta kawo, haka Allah ne ya hada jininmu shi ya sa Kaunarta ta shiga jikina dan ni daukarta nake tamkar wata 'yar uwata, in ka lura ai yarinyar tana mutuntani sosai kuma itama tana Kaunata, amma hakan ba wai vana nufin lallai sai mun yi soyayya ba, tun da ni ina da wacce nake so dan haka babu yanda za yai in tsaya Gata lokaci ina son yarinyar da wani gaye ya dade da dasuwa zuciyarta wanda bana jin za ta iya budewa wani ya sami dan filin da zai shiga ya zauna. Shi fa so masifa ne, don haka ya kamata ku sani shi so daya ne tak kun ga ita Asma'u wani gaye take masifar so, ni kuma Allah ya jarrabe ni da son wata yarinyar, kowa dai da mda ya sa gaba." Dauda ya ce "Kai manta duk wannan shirme ne kawai kamata ya yi duk kuturesu waje guda ku hade tun da akwai Kaunarjuna, soyayya ba za ta rasa muhalli ba, in kuma har ba ka yi kawai ya da ce ka bawa irinmuirinmu waje mu fito mu dan gwada tamu fasahar, ai abin sa'ane." Salim ya doka masa harara "Wai me kake nufi ne?" Ya yi 'yar dariyar shegantaka "Ina nufin tunda kai ka kasa to mu ka bamu fage mu sakar mata dafin tamu soyayya ka gani in bamu kawar da wancan gayen da kake tsoro ba daga zuciyar yarinyar. Mannir ma ya dubi Salim yana-dariya "Ka ga kuwa mutumin naka ba dama ne, wuyarta yarinya ta yi tsayuwar minti biyar dashi yanzu ya badda tunaninta, domin ya Kwarai sosai, wannan Gangare dan duk zafin kan yarinya in ya sameta ya watsa mata dadadan kalamai, tuni zai maida ta ruawan sanyi dan laffuzansa tamkar dafi ne zuciyar 'yan mata." Salim ya ce "Kai tafi can kar ka cika ni da Karyar banza wa ye shi, ku dubi yarinyar dai da kyau ba ta yi kama da irin 'yan matan da kuka saba tsarawa ba..." daidai lokacin Asma'u Karaso inda suke. Salim da saurinsa ya diro daga kan mota ya kar6i jakar dake hannunta, shi kuma Mannir ya washe baki yana gayar da ita yayin da Dauda cikin hanzari ya bude mata murfin motar, ta shiga ta zauna ya maida ya rufe "Ya yi Gimbiya, Allah ya kiyaye mana ke." Ya fada yana dariya. Mannir ma ya dan matso kusa da ita "Ho sarauniyar mata Allah ya bar mana ke." Ya fada yana murmushi, Ita kuma ta dan dago musu hannu alamar ta gode ba tare da ta ko dubi inda suke ba. Dauda ya dan bugi kafadar Salim "Yi sauri ka tuKa Gimbiyar tamu ka san ba ta jira sai dai jirata." Mannir ya ce "Ka kunna mata a.c. ka san 'yar hutu ce, jikinta bai saba da jin zafi ba." Salim ya dubi Asma'u ya yi 'yar dariya yayin da ya tada motar suka fara tafiya "Lallai kina jin dadi wato har wani kirari ake yi miki." Ta sakar masa shegen murmushin nan nata "Ni me za ka ce min bayan kana ji abokanka suna damuna da ihu amma ba ka yi musu magana ba." Salim ya tabe baki yana dariya "Lallai ma, amma kuwa kin gama dasu Manniru, ihu fa ki ka ce? Wato kirarnn da suka yi miki ne ya zama ihu?" "Yo thu ne mana dan me ya sa zasu cika min kunne da kaudi sai ka ce wasu maroKa." "Kya dai ji dashi imma wani ne ya burgeki cikinsu dan na ga har wani daga musu hannu ki ke." Ta saki dariya "To sai me?" "Shi kenan sai na jonaku daman Dauda ya mato "Wa ye Dauda cikinsu?" "Dan farin ko kuma dogon?" Ya dan harareta "Wato duk zamanmu tare ba ki ma san Dauda abokina ba? Gaskiya ba ki da kirki. "Oh kai kirkin gareka, shi ya sa na ga kana kula Kawayena. "Amma dai ko bana kula su ai ina gaisawa da wasuu cikinsu, ke kuwa Korafin da abokaina suke yi min kullum ba kya magana da kowa tsakaninki da su sai dakiya kin ga ni ina gaisawa da Kawayenla, irin su Rakiya Haruna. Ta ce "Him ai ni na fara dagoka duk yanda aka yi son yarinyar kake shi ya sa kake dama-dama da ita, to bari ka ji Rakiya Haruna dai tana da wanda take so da ta kammala karatunta aure Za ta yi." Ya saki murmushi dan ya san zolayarsa take son yi ya ce "Ayya yarinya kin min Karya ni mutunci ne kawai tsakanina da yarinyar dan tana da hankali sosai ga nutsuwa kuma kin sani wanta abokina ne dangantakar kenan da ke tsakaninmu ba wani abu ba." Ta dan kanne ido tana dariya. Ya watsa mata idanu yana kallonta, shima dariyar yake "Shi kenan kin zolaye ni kin ji dadi ko?" Ta dan tsagaita da darfyar "To yanzu dai bar maganar Rakiya Haruna koma maganar Mina, shin ki bari sai rabon 'ya'yana ya kashe mijinta idan ta gama Ta saki baki tana yi masa dariya "Wai kat dan Allah da gaske kake har yanzu jiran mutuwar mijin Mina kake yi." Ya yi banza da ita har ta yi tsokane-tsokanenta ta gama, zuciyarsa ya ce "Lallai sabo da shakuwa ma wani abu ne, yarinyar da aka taba ba ni labarin miskila ce ba ta da son magana ba ta murmushi bare dartya amma saboda tsabar shakuwa da haduwarjini, yau gashi muna hira har da barkwanci da ita.' Ta katse maza zancen zuci tare da watsa masa idanu tana kallonshi "Wai shin tunanin me kake haka? Ko dai Minar ce har yanzu. Sai da ya dan kanne mata idanu sannan ya saki 'yar dariya "Ke ni ki rabu dani tunanin wani gaye ne ya dameni yana can ya gudu Turai ni ko ina nan Najeriya amma sonsa ya kusan nakasa mini zuciya, in baa yisa'a ba ma Kaunarshi nema take ta zautani dan bana iya~ soyayya da kowane irin saurayi in ba shi ba." Yana gama fadin haka Asma'u da saurinta taryi Kwafa "Ka dau bashi kuma zan rama." "Haba da Allah wa ya gaya miki da ke nake?" daidai lokacin Asma'u ta dan dafe Kirjinta da yaushe za ta fito mu je zawarci. Sai da ya dan ciji yatsa, sannan ya girgiza kal "Sai takaba sai mu je mu aurota. 55 o* hannu gami da yatsina fuska "Ba ni fa da lafiya Salim." "Me ke damunki?" Ya Kura mata idanu razane. Ya saki dariya dan ya zolayeta "Oh sannu kin ji ai ba wani ciwo ne ba kawai Kaupar gayen nan ce take pema ta yi miki Karfi, shi ne take shirin fasowa ta fito kowa ya ganta fili, kin san dama gayen shi kadai ne ya mamaye lungu da sako na zuciyarki. Ta dan yi tsaki tana hararashi "Kai fa dadina da kai kenan komai ba ka daukarshi da muhimmanci, shin me gayen nan ya tsare maka ne? kullum sai ka ambaceshi?" "Why? Ba dole na ambaceshi ba, tun daya rikita rom 'yar Kanwa ya hana zuciyarta samun sukuni. Ta basar da zancen "Da Allah Salim serious da gaske nake bani da lafiya. "To shi kenan ki shirya gobe zan kai ki ki ga likita, Ta ce "Wallahi ture cen wasa Kirjina ne yake dan yi min ciwo kadan-kad mi ma ganin ciwon naki ba wani magani yake so ba, shawarar likita kawai yake buXata.' me ka ce haka?" nima na yi makamancin irinsa, akwai lokacind nake jin Kirjina yana yi min ciwo daidai fangaren zuciyata da na je asibiti likita shawarwari ya bani (may be) kema hakan ce take faruwa dake tunda matsalarmu da damuwar tamu kusan iri daya ce, musamman ma yanda na lura kina yawan sa damuwar yaron nan zuciyarki, gashi ma Goggo ta yi min Korafin ba kya rabo da yawan tunani, kuma ba kya samun wadataccen barci. Sabo da me?" Ta dan lumshe ido sannan ta bude tana murmushi "Ka da ka ga laifina Salim ba wai ni nake jefawa zuciyata damuwa ba. kawai nima tsintar kaina nake irin wannan vanayin kai ma ka san fa irin wannan matsalar." "To Allah ya kyauta abin sai du'a'i ki dinga yawaita addu'o'i." Ta yi dan murmushi "Addu'a kam kullum cikinta muke."Lokuta da dama Salim ya kan ji tausayin Asma'u fiye da kansa in ban da so masifa ne ta ya ya kyakkyawar yarinya kamar wannan za ta Ki auruwa, ta yi ta zama saboda saurayi daya, shin anya ko gayen nan im ta aureshi zai iya rike amanarta? Gaskiya kam yarinyar ta yi halacci tun da ta kasa zaman aure, saboda shi Allah dai ya sa Aminun nan mutumin kirki ne. Ya fada ransa daidai lokacin suka zo daidai wani shagon sai da katunan waya ya faka motar shi sannan ya dan dubeta "Bari in shiga in sayi credit dan nawa ya kusan Karewa. "Gaskiya Salim kana saurin zuke credit ka fiye Kona kudi da yawa.".. Ya yi dan murmushi "To ya ya za yl? Ai duk mutum mai jama'a haka abin yake." Ta ce "To nima bari in shiga akwai wanda nake son bugawa waya amma ta commercial." Ya watsa mata idanu "Ke kin fiye rigima in dai lambar ki ce ba ki so gani, un go wayata ki yi kira da ita dan ni bana so ki shiga wannan business center din." Ta kawar da kanta daga kallonsa "Na Kiya ba zan buga da lambar ka ba dan bana so akc damunka da tambaya ni dai ka bar ni na yi ta kudi." "Shi kenan na ji amma ki zauna zan sa su kawo rok." .. Ya bar ta cikin mota ya fito yaron kantin na biye dashi har suka iso gindin motar Salim ya kar6i kan phone din daga hannun yaron ya miKawa Asma'u ta kar6a, ta fara danna lambobin Ahmed cikin sa'a kuwa bugu biyu ya sadata dashi. Ahmed ya dauka "Hello!!" Da da farko bai fahimci ko wace ce ba sai da ta ce "Hello! Ahmed ni ce Asma'u da saurinsa ya aki wata wawlyar ajiyar Zuciya. "Asma'u ashe kina nan kwana biyu kin 6uya, gashi yanzu ko kirana ba kya yi waya. Ta ce "Ka yi hakuri al'amurane wallahi suka. yi po yawa."To na ji amma dan Allah ki daure ki gaya min. adireshin inda kike. Ta saki 'yar dariya "Ahmed kenan, kai yanzu kana zaton ina nake?" "E, to ni dai da can na ji an ce kina Sokoto kina karatu amma yanzu ban san inda ki ke ba amma ina so ki taimaka ki sanar dani inda ki ke?" "Kar ka damu Ahmed duk inda nake ma ina nan cikin Koshin lafiya, amma garin da nake yana da nisa sosai danni yanzu ba Sokoto nake ba." "Amma Asma'u inda aki yi mana adalci ai ya dace mu san inda kike wai shin kin san kuwa halin~ da mutumin naki yake ciki? Yana can sonki ya yi mai yawa, yana neman zautuwa amma ya kusan dawowa 58 Nijeriya....." Ta katse shi, "Wannan kuma ku ya shafa damuwarku ce, don ni yanzu na riga na yi aure." Ta dan kannewa Salim ido tana murmushin tsokana "Ahmed ko ba ka ji abin da na ce ba ne? Na ce ma na y1 aure, ina tare da mijina sunansa Salim." Ya ce "Haba da Allah ke kya fara?" "Gashi kuwa na yi Karewar farawa. ka sake Kaunarki ta kashe min aboki sai mun yi sharia. Sannan ya sassauta murya kamar yana rarrashi "Haba Asma'u kin ko san irin mawuyacin halin da Aminu ya shiga kanki? Har aikin zuciya aka yi masa.a asibitin can Rasha, ashe ba za ki ji tausayinsa, ki dawo gareshi ba." Da sauri ta katse layin domin jin bayanin Ahmed din ya haddasa mata Kunar rai. sanyaye ta juya ta juya ta bawa Salim kan wayar shi kuma ya mikawa yaron saan ya, zaro kudi na iya mintunan da ta ci ya mika masa. Yana shirin tada motar wayar shi ta yi Kara, ya dauka. Ashe abokinsa ne Musty, sai da ya gama amsa wayar, sannan ya dauko credit din da ya sayo ya Zuraa cikin wayar, ya mika wa Asma'u nata. Amma sai ya fura hankalin ta sam ba ya gareshi yana can ya tafi duniyar tunani, dan haka bai katse ta ba. Sai ya lallaba ya zare jakarta ya zura hannu ya lalubi kan wayar, ya fiddo maida ya loda mata credit sannan ya cikin jakar, ya tashi motarsa suka tafi. Shiru babu wanda ya yi maga, kowa da tunanin da zuciyarsa take. fusace ya far magana cikin fada Wallahi bari ki ji Asma'u kar ki yarda ki ce za ki yi aure idan kuma ki 'a Sai da ya ajiyeta za ta shiga gida sannan ta juyo ta ce masa "A sauka lafiya, gaida min Mommy." Tun da ta shiga gida ta kwanta, cikin rashin sukuni ta Karasa yinin ranar da Goggo ta dameta da tambaya sai ta ce kanta ne ke ciwo. Da yamma tana dakinta kwance Alhaji Yahaya tsohon mijinta ya kirata waya, ta yi kamar ba za ta dauka ba, amma kuma da ta tuna mutum ne mai yawan raha Kila ya yi mata barkwancin da zai jefa mata nishadi zuciya dan haka ta amsa da fara'arta. "Hello ya aka yi ne Alhajin Allah?" "Haba Ma'un Aminu amsa wayar ma sai an gama yanga an j2 min aji sai ka ce ni ne Aminu." "Kai Alhaji abin 'yar tsokana ce, to ai Asma'u taka ce ba ta wani ba, gashi nan ka sace min zuciya kullum tunaninka nake amma dan rashin tausayi ka Ki Zama dani ka koroni. Ya kwashe da dariya "Ku ji yarinya da wayo, ke Asma'u ina kika koyi yaudara? Wato Salim ne ya wayar da kz haka ko?" "Allah sarki kar ka dau alhakin dan bawan Allah." "Shin Asma'u yaushe ne Aminun naki zai dawo ku aure'?" Nan take ta wayance ta Ki zancen ta shiga zolayarsa "Wai shin Alhaji yaushe ne za ka zo mu maida aurenmu, tun tuni fa kai nake jira." Ya yi dan murmushi "Kina son ki ji ranar maida ke gidana?" Ta ce "Kwarai kuwa?" Ya ce "To ki saurare ni zuwa lokacin da jaki zai yi 60 Kaho, duk ranar da jaki ya yi Kaho zan zo mu maida aurcnmu." Daga nan ya rufe wayar yana dariya. Itama hirar tasu ta bata dariya, har sai da ta ji damuwarta ta dan ragu, ta tashi ta yi wanka ta yi sallar magariba ta zuba abincin dare ta ci. Ta tafi falo suka yi ta hira da Goggo da kuma Tabawa mai aikinsu. Sai dare sosai ta yi sallar Isha'i ta kwanta sai da ta gama 'yan addu'o'inta na neman tsari duk ta tofe jikinta sannan ta kashe wuta ta Kudunduna cikin bargo amma sam barci ya Ki zuwa, tunanin Aminu ne cunkushe zuciyarta ta damu Kwarai ~saboda bayanin da Ahmed ya yi mata. Tana kwance ta nutsu sosai cikin tunanin gwarzonta can dare misalin sha biyu arabi wayarta ta yi Kara alamar ana krianta, ta dan yaye bargo ta haska agogo ta ja dan tsaki, 'ko waye mai son magana da ni daidai wannan Jokaci.' ta fada ranta sannan ta yunkura ta ciro kan wayar daga jikin charging ta kar akunne. "Ya ya aka yi Salim?" ta fada yayin da take kwanciya akan gado. "Me ki ke har yanzu ba ki yi barci ba?" Tattausar muryarshi ta ratsa dodon kunnenta, ita kam koda yaushe muryar Salim ta na yi mata dadin sauraro ta ji ta kamar da Aminunta take magana, sam ba ta gajiya da hira da shi sai da ya sake maimaita tambayarta sannan ta ce. "Kai din me ya hanaka barci zuwa wannan lokaci?" Ya saki murmushi "At ni ina nazarin wani littafi ne." "Mhm, ko kuma nazarin al'amarin Mina ba." 61 "Kat haba da Allah sai ka cc wata ke, gashi nan tunanin saurayi guda daya ya hana miki barci." "Wa ye ya cc maka tunanin Aminu ne ya hanani barci?""Ai ko ba ki fada ba tuni na fahimci hakan, don haka dan Allah ina roKonki ki daure ki dinga rage yawan damuwa, ko kadan ban son ganinki cikin damuwa, kina yuna ko ki nutsu ki fuskanci karatun dake gabanki." "Shi kenan Salim na ji in sha Allahu zan dan rage na gode mu kwana lafiya. Amma kaima ban amince ka yi tunanin Mina ba ka kwanta ka yi barci kurum." Tana jin yanda abin ya bashi dariya ta kashe wayar ta kwanta. Washe gan da safe ta gama shirin tafiya makaranta ta dan zauna tana jiran direba ya Karasa wanke motar su tafi. Tana zuane falon Goggo suna dan taba hira ita kuma Goggon tana karya kumallo sai suka ji sallamar Salim. Goggo ta ce "Wa na ke ji haka kamar mutumin ki?" Asma'y ta ce "Shi ne." Ba su rufe baki ba ya yaye labulen gami da sallama. Asma'u ta dan fadada murmushinta "Sannu da zuwa mijin Mina ya ya su Mina da yaranta?" Ta fada tana dariyar zolaya. Ya sakar mata idanu kawai sannan ya girgiza kai yana murmushi "Duk suna nan Kalau sun ce gaishe k1 ke da Aminu." Daga nan ya dan rusuna ya gaida Goggo "Kai Goggo kina jin dadi yanzu duk wannan hade- haden ke kadai aka shiryawa." Ta yi 'yar dariya "Kaima ai sai ka zuana mu yi kalacin tare. "A'a ci abin ki ni tuni na yi breakfast dina." 62 "Ai mun dama mutumin naka, akwai kicin." Ya dan dubeta "Me ku ka dama?" Ta ce "Kunun gyada mana." daidai lokacin direba ya shigo ya Shaidawa Asma'u ya wanke motar, ya goge. Ta dan dubi Salim "Ko in yi gaba ka taho." "A'a ban ba ki izini ba." Ta sallami direba "Ka tafi yawanka amma bayan Azahar zan nemaka." Salim ya dubi Goggo yana dan murmushin Zolaya "Goggo ki shirya bana aure za ki yi zan kawo miki bazawari. Ta ture kofin shayin dake gabanta tana dartya "Kwa gama shegantakarku kai da Ma'u kaima da kake zuwa Zawarci guna yanzu bana yi da kai ni bazawarina yana can Kasar waje." Asma'u ta gangame baki "Lah ku ji tsohuwa da rgima shin waye bazawarin naki Kasar waje?" "Mhm wanda nake bege kullum, wanda sonsa yake nema ya yi min illa." Suka kwashe da dariya gaba daya. Salim har da tafi "Lallai Goggo kema kin ce wani abu." "O.k. to zubo min cup daya." Goggo ta ce Ki yi kiran mai aikinsu sannan ta kawowa Salim kunun gyada da soyayyen Kwai Asma'u ta rataya jakarta yayin da ta dubi Salim "Ka ga tashi mu tafi in ka daka ta Goggo sai mu makara." Salim ya mike "To Goggo zamu tafi daga makaranta zamu Zarcc asibiti Asma'u za ta ga likita." 03 "To ba laifi sai kun dawo." Suka fita tare har gindin mota tana shirin shiga ya manna mata makulli hannu "Malama yau fa ke za ki ja wm." Ta dan yatsina fuska "So dai ka ke ka hadani da "Haba ke kenan kullum sai dai ki kwanta baya direba na jan ki alhalin kin iya tuki amma Kiwa ta hanaki tukawa. "Ka san fa har yanzu hannuna bai gama fadawa ba 7an yi tuki sai na liKa (L)" "Ai ke kin fiye tsoro in ba haka ba ya dace ace ke ki ke kai kanki makaranta. "Rufa min asiri in ba so kake maza suke biyont har gida ba."daidai lokacin suka shiga ta tada motar,s uka fara tafiya. Tui take sannu-sannu cikin nutsuwa, saida suka hau babban titi ta dan Kara giya, ya dubeta "Lakca nawa gareki yau?" "Daya kacal." "Ashe da wurl za mu dawo." aiki "Kal nawa gareku? "Yau ba zamu shiga lakca ba, kawai ke na rako, kina fitowa sai mu tafi ganin doctor, tun safe na yi masa waya zamu zo." Daga nan suka saki zancen suka dauko want."Af Salim na manta ban sanar da kai ba bikin Zaliha Kawata fa ya kusa." Ya dan Kura mata idanu "Ki ce Zaliha bana za ta amarce?" 64 "Kwarai kuwa inda Allah ya taimakeni muna hutu ga yi bikin, dan haka nake murnar bikin nan gashi rabona da Kano na dade dan ma ita Zaliba tana yawan ziyartata in ta sami hutu ta kan zo Sokoto ta yi min wana biyu." "Kai ni ma na yaba da kirkin yarinyar, gaskiya gayen ya more da macen Kwarai. Shin mijin nata shima Bakano ne?" "E, dan Kano ne dan wani abokin babanta ne hada auren kawai aka yi ka

Chapter 4 of 7